Kurman Baƙi Page 4 Complete by Huguma

Kurman Baƙi Page 4 Complete by Huguma

 


https://chat.whatsapp.com/HeRo2w8C8gdG0Et1lqafjk

*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 04 

"Halan baki iya sallama ba bare gaisuwa haneefa?" Ta tsorata ainun,don duk yadda yake sakewa da iyalansa amma sun sani,muddin ya dauki zafi da kai ko fushi to zakaji babu dadi


"Sannu da zuwa abba,ina wuni?" Ta fada tana hade maganganun duka guri daya


"Koma kiyi sallama" ruqayya ta fada a sanyaye. Sakin labulen yarinyar tayi ta juya zuwa waje,haushin tsawar da akayi mata tana cikata,tana ji a ranta maamantata ce ta jawo mata.


            Irin yadda taga su alhussain din sukayi haka tayi,ya amsa yana dauke kai,saidai cikin ransa yaci alwashi bazai dauki wannan sakarce sakarcen da yayi imanin laifin na Zainab ne,dole ya zauna da ita ya kafa mata sharudda da qa'idojin da zata yawaita tunawa kanta bazai dauki irin wanann ba.


             Ledar hannunsa ya miqawa ruqayya babbar


"Ga mutanen naki" murmushi ta saki cikin jin dadi,kamar yasan a daren tana da buqatarsu,duk da al'adarsa ce tunda kayan suka zama abebadan shanta


"Na Gode qwarai qwarai,kaima Allah ya faranta maka ya qara budi da wadata"


"Ameen ya hayyu ya qayyumu, your prayers are my strength" ya fada yana dan lumshe ido. Idanunta ta kada masa tana murmushi,ya zare nasa idon da sauri yana yin gaba


"Inda zan zauna n qara awa daya tak zaki cikamin kunne da magiyar na tashi na tafi yanzun kuma kina yin abubuwan da sun saba doka da qa'ida irin ta yau" dariya ya bata sosai,sai ta rungume ledar ta juya zuwa cikin kitchen don ta wanke kayan ta kuma adanasu cikin fridge.


              Shigowar haneefa ya sanyata dungure man data dauko zata shafa ta waiwayo tana bada hankalinta ga yarinyar. Tun kafin ya gama shigowa ta kasa jumurin jira


"Me ya shigar musu dashi?,ina ledar?" Baki haneefa din ta tura alamun dake nuna tsiwa ta zauna mata sosai a jikinta


"Ina zamana kin saka anyimin fada harda tsawa" 


"Ba wannan na tambayeki ba leda nake tambaya" ta fadi tana zaro idanu cikin takaicinta tana duban haneefar


"Ya bata" ta amsa mata a a taqaice


"Ya bawa wa?" Zainab ta fada tana zaro idanu cikin jin bala'i da tashin hankali


"Mommyn alhassan"


"Lallai yau an taro fitina a gidan nan,wallahi bazan dauki irin wannan abun ba" ta fada tana jin kamar zata dora hannu a kai ta rusa kuka. Tako ina saleem cikin jawo abubuwan da zasu kawo rudani a zamansu yakeyi,rashin adalci tako ina yake gwadawa rayuwarta,duk qoqarin da ita din keyi na ganin sun zauna lafiya ita kuma ta faranta masa.


               Tana tsayen da daurin qirjinta hannunta riqe a qugu ya tura qofar dakin hadi da sallama ya shigo.


            Kamar me ciwon wuya haka ta waiwayo da qyar tana amsa sallamar,bakinta zaka dauka ya cusa lomar biredi ne data hanata yin magana da kyau.


            Tuna fadan da ya gama yi mata yanzu yanzu ya sanya haneefa juyawa ta fice a dakin. 


                 A nutse ya qara takowa ciki yana karantar yanayin dakin. Mutum ne shi me wani irin qaqqarfar halittar jiyo qamshi ko warin abu,don haka a yanzun ma kusan abinda hancinsa ke jiyo masa sam baiyi daidai da abinda zuciyarsa keso da muradi ji cikin gidan sa ba.


             Mayar da dubansa yayi gareta,tana tsaye qerere tana binsa da kallon da baisan daga ina  ta samoshi ba. Cikin daurin qirji,gashin kanta me tsaho da laushi ya samu guri ya cure abinsa saman kanta,wanda hakan ke nufin akwai dauda da rashin tajewa da ya zama silar wanzuwarsa a haka. Kauda idanunsa yayi,don idan da sabo za'a iya cewa ya riga ya saba. Cikin ranakun mako guda bakwai zaiyi wahala zainab din ta tsallake kwana biyu ba tare da ya ganta da daurin qirjin ba,walau da safe ko da dare kamar haka,ko yanzunma yasan qilan dashi ta wuni,bayan tasan babu abinda yafi tsana irinsa


_Note:Da yawan maza sun tsani wannan al'adar,domin bata da wani alfanu sai canzawa mace yanayi,musamman idan ta hadu da nau'i na qazanta irin ta zainab,akwai wasu lokuta da mace kanyi daurin qirjin don jan hankalin miji,in a stylish way,ta yadda zaki daure bakin zanin a tsakiyar qirjinki kamar kin qulle abu,ki koma sassauto da zanin zuwa rabin qirjinki wanda hakan zai bashi damar gano pant da wasu sashe na breast dinki,bawai daurin qirji irin wannan na gargajiya mara ma'ana ba da fallen zani me dauda_


"Sannu da zuwa" ta fada da qyar a hakanma tana tausar zuciyarta ne gudun kada daren yau din ta sake tafka asara kamar yadda tayi a jiya


"Yauwa,ya gidan ya yaran"


"Lafiya lau.....mu ina tamu ledar?" Ta tambayeshi kai tsaye tamkar ita ta aikeshi. Daga kai yayi ya dubeta yana maimaita tambayar da tayi masan,qasan ransa mamaki yana cin ran nasa. Ya akayi tasan ya shigo da leda?,har yanzu bata daina wannan dabi'ar tata ba kenan ta shegen sanya idanu a shige da ficen kowa na gidan?.


"Oh wadda kika aikeni da ita?" Dan sararawa tayi kadan,saboda amsarsa ta bata hasken inda ya dosa


"A'ah,ni ban aikeka ba,wai saboda naga yara sun ganka da leda ya kamata suma ace an basu ko tunda suma 'ya'ya ne kamar kowa" ta fada tana murmushin yaqe.


               Takaici ya qumeshi sosai,wai ita a hakan fa ta qure dukkan iyawarta ta gaya masa magana me dadi kenan. Miqewa yayi daga dosana zaman da yayi saman stool dinta


"Abinda yake ciki ba cimarki bane,fruits ne,ke kuma nasan babu daya a ciki da kike ci,itace me ta'ammali dasu kullum shi yasa nakai mata na dibarwa su haneefa,duk da su dinma sun koya ba lallai su iya shanyewa" ya bata amsar yana nufar qofa.


            Kallo ta bishi dashi tana tabe baki,a ranta tana jin kawai zallar mugunta ta sanya ruqayya ta sakashi siyo fruit din. Wannan shan fruit da cin ganyayyakin nata yana masifar qona mata rai,aikinta kenan kullum kamar wata raquma


"Ni bazan zauna ina fama da 'ya'yan itace ba,nafi qarfin gaban nan,mu saidai mu rungumi qwaryar qwayoyi musha muyi tatil mu gigita mutum" ta fada qasa qasa tana shafe fuskarta da mai,koda ta gama kuma bata nemi powder ba bare turare ta fara laluben kayan da zata saka.


             A gajiye ya tura qofar dakin nasa da shirin fidda kayan jikinsa ya watsa ruwa ya wuce masallaci yayi aallar magariba. Cikin qasa sa second biyar dukkan wannan karsashin nasa da dokin ya fita a kansa gaba daya.


              Yadda ya fita yabar dakin da safe haka ya sameshi,babu wani abu da ya sauya. Hatta da comb da ya taje kansa kafin ya fita yana zaune abinsa dungurgur saman madubin. Numfashi ya zuqa ya kuma fesar zuciyarsa na wani irin tafasa. Ya sha gaya mata,a duk sanda qazantarta ta motsa taje ta qarata,tunda yayi iya yinsa,to amma ta tabbatar qazantar bata shafi komai nasa ba. 


            Murfin qofar ya saki bayan ya jingine briefcase dinsa jikin bango ya koma da baya falo inda yabar yaran. Duban ledar da ya ajjiye musu yayi,sun gutsutstsura fruit din kawai sun barshi sai ma bata gurin da suka sakeyi. Daga khalil dake da shekara shida har haneefa din dake da shekara goma cikin ta sha daya rasa me hankali yayi a cikinsu. Alhassan da alhussain dake da shekaru takwas cikin ta tara ya tuna,a wadan nan shekarun nasu sun iya share guri suyi mopping fes,sun iya wanke wanke da wanke qananun undies dinsu na mamansu dana qanwarsu,a yawancin lokuta har fada yakan yiwa ruqayya,saidai ta langabar da kanta


"Ka bari sunyi mana daddynsu,idan basuyimin ba wa nake da da zaiyimin,sannan wataranma fa suma mazan auren wasu ne,idan suka iya ai kaga har matan da zasu aura sun huta suma,wataran sayi karba a aikin gidan,ko kuma wata lalurar idan ta samu matayen ko?" Hanci ya lakace mata


"A fakaice dai ni kike zagewa fa rukky" dariya ta saki tana riqe yatsunsa


"A'ah wallahi daddy,rainon inna ne fa kai?,kaima ai koda bata koya maka aikin gida ba aita koya maka abinda yafi wannan muhimmanci,iya kula da iyali,zuciyar soyayya da tausasawa da kuma kyautatawa" yadda kalaman suka fita a bakinta sun sake ninka kimarta a zuciyarsa,sun kuma sanyashi yana sake jin nauyinta da kuma rashin son tuna wasu abubuwa da suka wuce a baya.


"Kiramin mamarku" yace da khalil,bayan ya wuce ya kalli haneefa


"Haneefa"


"Daddy" ta amsa


"Ki tattare wannan abinda kukaci din ki sakasu a fridge,sauran ki saka a shara,duk abinda bakuci idan na kawo ku daina lalatashi irin haka,saboda qannenki zasu gani su koya ne"


"Tom" kawai tace tana miqewa cikin sakalci ta soma gyaran wajen,wanda kana gani kasan bata saba ba kwata kwata.


             Kanshi ya girgiza kawai ya koma bedroom din nasa. Tsaho wasu mintuna bata iso ba,har ransa yaso ya soma baci,sai kawai ya miqe ya soma rage kayan jikinsa yana dorasu saman wadanda ya ciresu da safe.


             Sai da ya kammala sannan yaji ta turo qofar,still da uban daurin qirjinta na dazu,ya rasa me takeyi tun shigarsa dakin da fitowarsa kawo yanzu da bata nema wani abun ta saka ba ta raba kanta da daurin qirjin nan


"Gani" ta fada tanason nemo dakiya a ranta,saboda tun shigowarta ta gama gano abinda ya farun. Shaf ta manta da wani batun gyaran dakinsa gaba daya,tunda ta zauna yau qoqarin neman maganin da zaiyi mata aiki sharp sharp shi da ita takeyi,kuma ko yanzun alhamdulillah ta fara jin alamun hakan cikin jikinta,saura shi.


               Waiwayo yayi yana qoqarin hadiye bacin ransa ya dubeta,sai ya hangi khalil kusa da ita


"Wuce falo wajen haneefa" yace da yaron,bacin ransa yana sake tasiri. Kwata kwata basu da tsarin shiga guri daga shi har 'yar uwarsa,ko ina ma suna iya bin iyayen ko su shiga ba tare da rarrabe dacewa ko rashin dacewar hakan ba,yau ya kawo qarshe kuma dole ya sanyata ta gyara ginin data bata,bazai bari suci gaba da girma akan haka ba.


"Haka ya kamata dakina ya zama?" Ya fada yana tsareta da kallon tuhuma bayan ficewar khalil din. Hannu ta saka ta sosa kanta


"Wallahi na sha'afa ne inata aiki tun safe"


"Eh naga alama a gidan ai" ya amsa yana juyawa abinda ya shige bandakin.


              Bai iya wanka a ciki ba saboda Allah ya zuba masa tsantsami,sai daya zazzaga garin klien hypo da ruwan izal ya wanke toilet din fes da kansa sannan ya hada ruwan wanka. A gurguje yayi wankan saboda gudun qwacewar lokaci,saidai duk yadda yaso ya fita akan karin sai da lokacin ya kusa qwace masa,abu na biyu daya tsana ya rasa jam'i,yana fitowa ya zura jallabiyya kawai a gaggauce ya fice.


               Bazai iya tuna randa yayi missing sallahr magariba ba duk sanda yake sashen ruqayya,saboda komai da tasan yanaso tana tanadar masa kafin yazo ga buqatarsa. Akwai banbancin da tazara me dinmbin yawa tsakaninta da ita,yana dukka iyakar qoqarinsa ne kawai wajen kamanta adalci da boye hakan a mu'amalarsa da su gwargwadon iyawarsa,amma ko sau daya zainab din idanunta basa gani.


             A kullum zancanta daya ne zuwa biyu,ruqayya ta mallakeshi shi yasa sai abinda takeso ake gani,baya kamanta adalci a tsakaninsu duk da qoqarin kyautata masa da takeyi. Ya rasa wanne adalci take bida bayan wannan?,me takeso yayi mata?,da wannan tunanin ya isa masallacin ya zare takalmin qafarsa ya shiga.


               Bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i,don gaba daya bashi da wani karsashi da dokin zama a gidan gaba daya.


              Kallon takaici kawai yabi dakin dashi,ya kada kai yana wucewa ciki ya ajjiye abun sallarsa. Sanda ya dawo falon da niyyar zama ba komai dake kai kawo sai qaurin abinci,ya kalli kitchen din kaman zaiyi magana sai kuma ya sake dauke idonsa. Wannan na daya daga cikin dalilan da ya sanya kullum ta Allah muddin zai zagaya backyard na kitchen dinta sai ya taras da uban lalataccen qanzo,qudaje da sauran qananun qwari suna parade akai iya son ransu. Duk yadda zaiyi wajen kwatanta mata ta daina amma hakan ya gagara,a taqaice ma abicin store dinta shine yake fara qarewa cikin gidan. Bama abincin ba,zai iya cewa kusan komai ma.


              Kamar ko yaushe a nutse ta shirya cikin wani sassauqan riga da wando na pakistan masi taushi da hasken launi,dan qaramin mayafin da kayan yazo dashi mai qarancin kaurin da kana iya hangen gashinta dake gyare a matse cikin band ta lullubawa kanta,ta lakaci oil perfume dinta ta shafe jikinta da shi sannan ta soma nufar qofar dakin.


            Tuntuni saleem ya sanya haneefa ta kirayi yaran,har fateema iftee ta bisu. Su da yake yara ne ba kasafai suke damuwa da yanayin dandanon abinci ba,koda sun gane dinma ba wanda ke mata maganar don bata basu fuskar dauko zance su gaya mata ba.


               Cikin rawar kai da karsashi taketa kai kawon jera abincin saman table mat din da suke shimfidawa a qasa suci abinci. Yau din tana da hope tana kuma da mafi rinjayen yaqinin zata shayar da saleem din abinda baya taba samu daga gurin ruqayya.


                Hankalinsa na kan waya yana amsa kiran sanda take zirganiyarta. Maimakon qamshi ya zamana abokin rakiyarta a duk lokacin da zata gifta din saidai akasin hakan ya biyo baya. Duk da tayi wanka saidai za'a iya kiran wankan da jiqa jiqa kai tsaye,uwa uba ta hada gumi wajen kammala girkin waje daya,bata saka koda alum ba bare turare,sai rigar data cire jiya ta maida jikinta,a cewarta tunda dare ne kuma kwanciya zasuyi,ba sai tayi asarar ware wankakkun kayanta ba. Gumin ya cakude da tsumammiyar rigar wanann yasa wani abu me kama da qari qari ke tashi kadan kadan.


               Dai dai sanda ya gama wayar ruqayyan tayi sallama a tausashe. Ya kashe wayar ya ajjiye ta a gefe yana dan murmushi. Itama fuskarta a sake ta qaraso


"Sannu da gida maman haneefa" ta fadi da zuciya daya


"Yauwa" ta amsa mata saboda darajar idanun saleem din,sai dai a gajarce murya can qasa, zuciyarta na quntata da ganinta a gurin. A son ranta taso ya qyaleta ko da iya yau kadai ne suci abincinsu su biyu.


            Daga gefe ta zauna,sannan tayi masa barka da warhaka a tausashe. Idanunsa yadan lumshe yana amsa mata cikin kulawa,abinda ya motsa zuciyar zainab,sai ta dire masa plate din abincin tana guna guni qasa qasa. Tayi bala'in tsanar dressing din ruqayya,takanji inama tana da dama da kuma iko,da tabbas zata cinnawa sutturunta wuta ne su kama su qone qurmus.


             Tanaso tayi bore akan hakan,amma tasan koda tayi aikin banza ne wai harara a duhu,ranar data fara magantuwa akan hakan tayi qara wajen saleem amsarsa batayi mata da kyau ba


"Nifa ban fahimci kwalliyar da maman alhassan ke shigowa da ita ba,bayan cin abinci akwai akace tazo tayi ba nuna ado ba" ta fada fuskarta babu digon walwala a kai,don ba abinda ke mata yawo a lokacin sai kallon da saleem yabi ruqayya dashi. Tasha jin ana cewa baqaqen kaya basa yiwa baqi kyau,amma yau ita da kanta ta qaryata hakan saboda yadda baqar atamfar tayi mata wani irin mahaukacin kyau


"Kaman yaya?,dama ita tsafta tana da ranakun yinta ne a taki fahimtar?" Sarai ta fahimci kamar magana yakeson gasa mata,saita waiwayo itama tana dubansa tare da sake tsuke fuska


"Idan taso ta zama agwagwa ma sarkin wanka,amma ta tsaya iya ranakun girkinta,ban shiga hurumin kowa ba,nima ba za'a shiga nawa ba"


"Bazan taba ce mata ta daina kwalliya ba idan ma wannan shine burinki,kema idan zakiyi babu wanda zai hanaki,hasalima ina maraba da hakan kuma sai nafi kowa farinciki,haka siddan kinason zama qadangaren bakin tulu "sai ya wuce toilet ya barta kawai.


"Kadangaren bakin tulu" tayita maimaita kalma,kasancewarta macace me bala'in tsarguwa da sawa rai abu. Wayarta ta dauko saboda ta kasa nutsuwa da abinda yace. Ta bude data ta shiga group dinsu ta kuma antaya tambayar bayan taqaitaccen bayanin abinda ya farun.


         Cikin qasa da minti biyar kalolin amsoshi suka dinga fitowa,kasancewar group din group ne da baya rabo da jama'a,amsoshin da kai tsaye suka fito mata da ma'anar abinda saleem din ke nufi. Wayar ta ajiye ta koma gaban madubi ta zauna tana duban kanta. Har rana wayau ta kasa gane me tayi wai da ya saka mata da tsanani yake mata kallon qazama,dame ruqayyan ta fita banda baqar fata?.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post