Kurman Baƙi Page 7

Kurman Baƙi Page 7

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 07

"Ba inda zaije,bashi da lafiya,kuma har yanzu kwanana ne" a nutse ruqayya ta waiwaya ta dubeta sama da qasa,ta ganta wata harikicibayya cikin zanin wata atamfa da yayi musu waccan sallar,ta Zainab din ruwan madara ne,atamfar kudinta duk daya ta doshi dubu goma sha takwas amma cikin qasa da wata goma tata har ta doshi hanyar zama tsumma,ta rune daga milk ta koma brown brown da torches na dattin abubuwa mabanbanta,bakin zanin yayi leb'atu wani ya zarta wani yana lilo


"Haba amarsu bakya laifi,baki lura bane azahar har ta gota?,ko kin manta ke kika tsara mana hakan dama?,kiyi haquri kwana biyu rak zan dawo miki dashi da kaina" ta fada mata tana murmushi dariyar daurin dankwalijta yake a jirkice yana kama ruqayya. Sau tari bata fiya jin kishin zainab cancan ba, saboda tasan bata da abinda zata kara da ita,saidai hali kawai irin na zuciya da kuma abinda takeso.


               Miqewa saleem din yayi yace


"Minti daya"


"A fito lafiya" ta amsa masa tana maida dubanta ga tv din dake aiki, wadda rabinta tayi baqi saboda yadda su haneefa suka ragargajeta duk girmanta kuwa,shi kuma yayi rantsuwar bazai canza mata wata ba,saboda bayan wadda ya siya musu ita da ruqayya ya sauya mata wata,wannan din shine karo na biyu kenan da yake sauya musun bayan ta farko.


"Ba inda zashi,yana nan" zainab din ta fada tana juyawa tabi bayanshi dakin.


              Aikin da ya gagara bai gama jiya ba yake hada kan takardun nasa sai yaji motsinta,koda ya waiwayo ta fara zare t.shirt da zanin jikinta,ta fara takowa inda yake tana girgiza kafadunta


"Mene hakan?" Ya fada a mamakance,take fuskarta ta sauya kamar yadda bata iya cinye bacin ranta ba


"Ragowar haqqina nake buqata,kuma kaima aina lura bawai ka gama nutsuwa bane" Dariya ce ma taso kamashi,yadan kauda kai daga nan yana jiyo yadda smell na jikinta ya canza da alamu tana da buqatar tayi wanka amma ta kasa gane hakan. Abu na biyu kuma ya fahimci tana so ne tayi abinda zata batawa ruqayya lokaci,saidai kash bata iya durfafar miji da salon zai dauke masa hankalin ba tare dashi kansa yasan ya akayi hakan ta faru ba


"Lokaci ya fice yanzun kema kin sani"


"Eh amma hakkina ne ai a wuyanka ko?" Tsaiwa yayi yana kallonta kafin daga bisani ya girgiza kai yaci gaba da hada takardunsa. Maganganu ta shiga yi na bacin rai har ya gama,ya miqe tsaye yana zuba mata idanunsa abinda ya sanyata rage kaifi bakinta


"Kiyi qoqari ki tabbatar ba wani abun kika zubamin jiya ba,don muddin na gano hakan kinsan sai na hukuntaki tabbas!" Ya qarashe maganar yana kewayeta ya fice,saboda yasha mata gargadi akan hakan,yayi dukkan abinda zaiyi ya koya mata hade haden vegetables din da ruqayya keyi masa da suke da matuqar amfani ga lafiyarsa da auratayyarsu,amma tsabar son jiki ta kasa tsaiwa ta dinga yi masa a kullum kamar yadda yake da buqatar ya dinga ci din.


              Har wani sakakken numfashi ya saki sanda suka isa sashen nata,wata ni'ima da nutsuwa suna saukar masa. Ruwa me dumin sosai ta hada masa kamar yadda tace,koda ya sanya hannu cirewa yayi da sauri yana dariya


"Wai ashe da gasken kike gasanin zakiyi?,na dauka kin fada ne kawai saboda kishi?" Yadda ya rutsata da ido yana tambayarta sai abun ya bata dariya,ta murmusa tana qoqarin danne kishinsa da takeji yana cin qasan zuciyarta


"Amma dai kafi kowa sanin ruqayya,idan tace eh tana nufin eh din,idan tace a'ah shima tana nufin hakan" murmushi ya saki yakai hannu yana shafar dukiyar fulaninta da yanayin dinkin da akayi mata ya fidda shape dinsu sosai. Har yanzun yanajin wannan yanayin a jikinsa,saidai hankalinsa na kwanciya idan ya tuna ya fado hannun da zai samu dukkan kowacce irin nutsuwa. 


"Naji sashen shuru ina duka yaran"ya tambayeta sanda take taimaka masa yana fidda kayan jikinsa don ya samu yayi wankan,har yau har gobe muddin tana free irin haka itace ke taimaka masa da wannan,hakama shirin muddin ta gama nata ayyukan


"Na korasu gidan kakaninsu don nayi jinyar daddynsu da kyau" wafta ya kawo mata,ya jawo qugunta ya riqeta suna musayar numfashi. Idonsa cikin nata,hakanan duk wani fitar numfashinta sai ya hado da sassanyan qamshinta. Sai ya tuna wata rana irin hakan da ya gwada yiwa zainab hakan,daga qarshe da hannunsa ya saketa saboda bala'in rashin tsaftar baki,wanda hatta da numfashinta da irin wannan yanayin yake hadowa ya fito.


"Wannan jinyar ta tsaye miki a rai ko?,to kada ki damu,kema yau ki daure ki jinyatani hakan mana" ya fada yana kashe mata ido daya. Hannu biyu ta sanya ta turashi baya tana dariya


"To bismillah ko an gaya maka raguwa ce?,ai dai kafi kowa sanin wace ni" dariya ya saki yana kai mata cafka,sai ta zame ta fice,don sam ba zata yarda ya rabeta daga barowarsa sassan zainab ba,tafi son ya tsaftace jikinsa duk da fes yake,amma hakanan take da wannan kishin a zuciyarta.


           Kafin ya fito ta hada masa hadin salad na musamman,bricole,spinach,cocumber,parsley cabbage lettuce cornflower,ta yayyankasu ta wankesu da ruwan gishiri,ta diga masa mai kadan. Tuni ta haramta zuba maggi me yawa a abincinsa bare akai ga farin magi,don haka gishiri ta zuba mishi kadan da yaji wanda tasirinsa bazai fito ba bare ya dameka. Blender dinta ta jona ta markada kabewa dabino da kanunfari yayi laushi qwarai kaman yoghurt ta wadatashi da zuma.


             Duk inda ta gifta saita aje masa qamshinta,hakanan tasirin maganin jiya da bai bar jikinsa ba ya dinga tsomoshi. Sai data gama shirya masa komai sannan ta dawo ta zauna tana dubansa cikin wani lallausan kallo data aje kawai saboda shi,zata iya cewa duk duniya ba wanda ya taba ganin makamancin kallo irin wannan a idanunta saishi daya tal


"Ga abinci ya kammala,ka fara tabawa kafin na dora girkin dare" kumatunta yaja yana murmushi


"Emergency kika hadamin ne?,naga harda pumpkin smoothie" farrr tayi da idanunta tana murmushi


"A'ah,ya za'a yi mu hadu muyita tara maka gajiya?,so nake kaci ka qoshi ka kwanta ka huta,qwarin jikinka ya dawo" mintsininta yayi kadan yana murmushi, muryarsa qasa qasa yace


"Ban yarda ba,tunda kikace kin tafi gidan aunty deeja nasan there's something special yau,naga wani abu me zaqi zaqi ma a fridge dinki" idanu ta fiddo tana kallonsa


"Sai kuma kasha?" Kai ya girgiza yana langabe mata shima


"Dandanawa kayi nayi fa,Allah bansha ba" shagwabe masa tayi sosai kaman zata saki kuka


"Amma dai daddynmu kasan ba kyau bincike dai ko?" Dariya ta qwace masa


"Ni ruwa naje sha ba bincike nayi ba" ya fadi yana daga hannunsa sama duka biyun yana dariya


"To nidai na yafe yau din,an baka hutu" ta qarashe maganar idanunta nakan labulen window dinta dake ta veranda din waje. Idan idanunta sun nuna mata gaskiya shatin tsaiwar mutum take hangowa,karon farko kuma taji zuciyarta tafi kakata da cewa zainab ce. Sau uku qanwarta da maqociyarta suna gaya mata Zainab din tana mata labe,amma bata taba daukan abun da muhimmanci ba tunda bata taba kamata ba.


"Ni kuma ban yafe ba" ya fada yana matsa hannunta dake da wani sulbi da taushi.


               Tana sane ta saki wata shagwababbiyar qara idanunta nakan labulen


"Allah dear......ka bari don Allah,tun ba'a yi nisa ba kada kasa na kasa komai"


"Na bari,amma mu fara salla tukunna kafin muci abincin"


"Yes sir" ta fada tana miqewa. Sai data fara wucewa kitchen ta fiddo sumammen ruwa ta juye a wata roba sannan ta wuce toilet ta shirya masa ruwan yadda zaizo da dumi bayan tayi tata alwalar ta kuma shimfida abun sallah sannan ta zarce kitchen din.


"Na daina raga miki" ruqayya ta fada qasa qasa tana dariya mugunta hannunta dauke da robar ta dawo falon din.


             Sake gyara tsaiwarta tayi da kyau zuciyarta na sake tafasa da bacin rai. Ba zata bar wajen nan ba har sai taji uban me dame sukeyi tas a cikin falon. Gumin fuskarta ta goge tana jin kamar ta rushe da kuka. Babu ta yadda za'a yi ma ta yarda cewa ruqayya ba asiri ta yiwa saleem ba,don bataga wani abu guda daya da zaisa saleem din ya dinga wannan rawar jikin a kanta ba,bayan itace tafi cancanta da hakan.


             Ai bata dire tunaninta ba taji saukar ruwan qanqarar da ya kusa tafiya da numfashinta gaba daya. Ta taqarqare ta kunzuma ihu ta mance ma shaf da muhallin da take a tsaye. Da sauri ruqayya ta bankade labulen da qofar gaba daya ta fito tana salati


"Jar uba!,ni kika jiqa da ruwan qanqara,wallahi tallahi yau ko sama da qasa zasu hade bazan yarda ba" ta fada tana gyara daurin qirjin da tayi a saman zanin atamfar jikinta. Wata dariya ta tasowa ruqayyan yadda tayi tsamo tsamo da ruwan har tana rawar dari,amma dai sake gyara masoyinta takeyi wato daurin qirji


"Aike za'a tambaya,me kikeyi a nan gurin?" Tambayar data daukewa Zainab din wuta difff musamman da tambayar ta fado dai dai sanda saleem yake fitowa daga falon saboda ihun zainab din daya riskeshi har bandaki.


           Ido tahau rabawa, ganin yadda shi da ita gaba daya suka zuba mata ido suna sauraren amsarta sai tahau tafa hannu


"Ni zaki yiwa wannan tambayar?,ko kin manta yadda gidan nan yake naki nima haka yake a wajena?,ko wucewar ma mutum bazaiyi ba saboda window din daki ne?"


"Wucewar ce harda kujera?" Saleem ya sake jefa mata tambayar yana nuna mata kujerar data aje a wajen. Dif wuta ta dauke mata,yayin da shi kuma yaci gaba da kallonta yana hadiye wani abu me tauri.


"Allah ya kyauta" ruqayya ta fadi tana kewayeshi ta wuce ciki abinta,ko babu komai ya gani da idanunsa,bata bude baki ta fadi ba bare ace sharri ne da yarfe irin na kishiyoyi.


            Batasan yadda suka qare ba,saidai har alwalarta ta bushe bai shigo ba,sai daga bisani ya shigo yana ware hannun rigarsa,fuskar nan cike fal da bacin rai,saidai bata bari hakan yaci gaba da damunsa ba ,don bayan sun gama sallar sai data tabbatar ta mantar dashi komai ta hanyar biye masa ya sauke sauran nauyin da Zainab ta dibga ma cikinsa ba tare daya sani ba,sannan ta shiriritar dashi suna wata daddadan hirar gado wadda ta musammance data warewa lokuta irin wannan. Lokutan da suka gama kasancewa da juna a lokaci irin wannan da babu kowa daga shi sai ita. Yanason irin wannan moment din da take creating musu,yana sakin jiki qwarai yayi sirrika masu tarin yawa da ita,suyi shawara da juna ta kuma sauke masa damuwar da yakejin duk duniya ita daya keda wannan power din.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post