Kurman Baƙi Page 8

Kurman Baƙi Page 8

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 08

           GIDAN HAJIYAR MATA daya daga cikin jerin gidaje guda goma sha biyar kenan dake layin.


              Faffadan gida ne dake da soro makeke guda,yalwataccen tsakar gida dake da bishiyar mangwaro a tsakiyar gidan,sai dakuna guda biyar manya,wanda kowanne cike yake da kayan jere na alatu wadanda suka fi qarfin a zubasu a gida kamar wannan,duk da gidan fes yake,baya rabo da fenti da 'yan gyare gyare kodon saboda baqi dake yawan zirga zirga a gidan.


            Kusan duk sanda zaka shiga gidan zaka samu dakuna hudun nan a rufe,musamman uku daga cikinsu,har gwara dayan ana yawan budeshi saboda baqi dake zuwar mata. Daki guda kuwa kulli yaumin yana a bude,saboda shine ainihin ma'assasar neman kudi da dukka wata taqama na hajiya zeena din. Akwai masu aikin dake zirganiya daga dakin zuwa tsakar gidan sanye da riguna koraye masu dauke da tambarin HAJIYAR MATA musamman idan ta kammala hada magungunanta za'a yi packaging.


             Saidai ko su din akwai wasu kebantattun lokutta da bata barinsu shiga dakin har sai ta kamala hada magungunanta saboda boye sirrin kasuwa kamar yadda takance


"Mutane ba amana,kasuwa ai sirri ce"


            Ko a yau din ma masu aikin nata na zaune a tsakar gida suna hirarrakinsu tare da jiran hajiyan dake dakin ta sallami baquwarta ta kuma gama hada magungunan nata su shiga suyi aikinsu,don yau din akwai kaya da yawa tace musu akwai matar da zata sara.


                Daga cikin fallen babban dakin da yafi kowanne girma mata ne zaune saman kujeru guda biyu,dayar kana kallonta kasan itace matar gidan,don kanta daurin ture kaga tsiya ne tayi,qwaiwayayyen gashinta ya bullutso ta qasan daurin,yayin da d'ayar ke sanye da hijabinta saidai ta sabashi saman kafada


"Shi carwash din yanzun saidai botiki uku?,botiki biyar naso saboda zanyi sabulun tsarki dashi me yawa wallahi" 


"Masu nema ne sukayi yawa hajiya,kuma kalolin da za'a sakawa koren ne babu,ke kuma koren kike da buqatar yayi ko?"


"Eh mana,yo banda abinki ta yaya za'a yarda sabulun magarya ne babu koriyar kala?" 


"Ba matsala zanyi qoqarin hada miki cikin satin nan in sha Allahu" 


"Shikenan,zan jalauta haka" ta fada tana ninke takardar lissafin nasu,ta jawo wata lalita a qugunta ta zuge ta lissafo kudade ta miqa mata


"Gashi babu kare bin damo,idan kin kawo sauran koren na baki kudinsa iya shi kadai" kudin ta jujjuya a hannunta


"Haba hajiya,na zaci zaki bani kudinsa shima kafin na kawo"


"Kije kiyimin irin ta wancan lokacin ko?,saiji nayi kin bawa wata,to kar nake kallonki"


"Karmuyi haka dake mana,duk zaman nan ace ba aminci tsakaninmu?,kudin nan fa kafin ki tashi a nan na tabbatar kin maida ninkin baninkin dinsu" daurin dankwalinta ta sake turowa gaba ta bararraje tana jawo wani farin botiki dake cike da garin masara me azabar fari da laushi da yasha tankada da kyau,hakan ya nunawa matar da take kira da saude ba zata cika mata din ba


"Kinga miqomin botikin zumar can" dariya saude ta sheqe dashi


"Zuma ko dafaffen sugar cakude da dan zaqi?(sweetner)" Baki ta tabe cikin nuna halin ko in kula


"Koma menene ke kika sani,miqomin nayi nayi na hada,basira zata shigo sari tace akwai gidan sunan da zata je yau din"


"Hajiyar mata hajiyar mata" saude ta fada gana dire mata botikin.


"Ahto,meye amfanin sana'ar da babu riba,tunda dai sunyi imani kuma yana musu aiki aimu alhamdulillahi......ina fiddausi?,zoki hada dan matsin nan yasha iska kafin anjima" ta qwalawa biyu daga cikin amintattun masu aikin nata kira.


            Wani kwali ta jawo dake dauke da zanen mace babu komai a jikinta sai pant,an fiddo abinda zai nuna maka tallan abubuwan da zasu qara masa girma akeyi


"Balle capsule dinnan ki watsa a hadin garin qara girman nonon can za'a kai niqa"


"Kinsan sirrin kasuwa hajiya" saude dake dariya ta fada


"Yo mu din na wasa ne?,ke kinga yadda mata suke wasoson garurrukana?,to kina sha zai fara aiki,su dama haka sukeso,wannan zai fara miki aikin da idan hadin Allah kikayi musu sai yayi wata uku mace tana sha bataga canji ba,yanzu zakiji an bata miki kasuwa ana cewa bashi da kyau,bayan shine me kyan,tsabar gaggawa ce dasu to kinga gwara kawai kayi musu abinda sukafi ganewa,wanann garin duk yawansa bazaikai jibi be qare ba" ta fada hautsina garin masarar dake cikin botiki,da niqan aya da saqe saqen da batasan adadin yawa da kuma dame dame ta game waje daya ba. A hakan garin masarar yafi yawa,ganin yayi haske da yawa saita debi garin kala me dan duhu ta watsa


"Yauwa,sai a dauka tsabar soyayyar ayace da ta wadata" hajiya ta fada a ranta tana qissima yawan ribar da zata fitar a wannan hadin da tayi.


*******A nutse ta kammala komai,hatta da abincin dare harda farfesun kayan cikin da saleem ya aiko daga kasuwa. Ta shirya tsaf cikin atamfar black prince me kyau data dace da kalar fatarta. Wani irin sassanyan dressing,ita din gwanace gun hada ado da yakan dace da kowacce kalar unguwa. Hannunta riqe da key din motarta ta fito babban falon gidan da zai wuce da ita harabar gidan.


              Sauka idanunta yayi akan sassan zainab. A rufe yake gam,ta kusa awa hudu da tafiya tuntuni. Aike ta dinga yo mata ba qaqqautawa akan ta fito su tafi,ita kuma ta aike mata ta tafi kawai ta taho. Hakanan al'adar zainab take,indai taji batun fita gurin wani sha'ani ko taro jikinta har rawa yake,ba kasafai ranar abincinta ke ciyuwa ta dadin rai ba idan ma ta tsaya tayin. Wani murmushi ya qwace mata data tuna wani abu,ta girgiza kai kawai tana isa ga motarta,tabbas ta yarda wasu matan basu da wayo kam.


              Minti talatin ya kaita unguwar,suna akeyi na 'yar qanwar mahaifiyar saleem din. Kana gani kasan gidan cike yake,don kuwa duk da gidan yalwatacce ne amma har ta waje kana iya hango zirga zirgar jama'a. Tunda ta ajjiye motarta ta fito taketa gaisawa da mutane cikin mutuntawa da ganin kima,can qasan zuciyarta mamaki yana dan mamayarta,tana sake gasgata cewa tabbas ME HAQURI YAKAN DAFA DUTSE HARMA YASHA ROMONSA. Mutanen da wasunsu a baya suka daina magana da ita,wanda ita tasan ba komai bane ya jawo hakan sai saboda zainab da saleem ya auro da suke ganin 'yaruwarsu ce sunfi kusa da ita akan ruqayyan,duk da tarin kyautata musu da ruqayyan keyi amma suka shafawa idanunsu kwalli,sai gashi lokaci yanata nuna kansa, gaskiya kuma tanta halinta bayan ta watsar da damuwar kowa ta maida hankalinta ga addu'a da mu'amala da kowa da zuciya daya.


             Gaisawa ta dinga yi da mutane,bata kuma zauna ba har sai data lalubi dakin da surukarta take da wasu daga cikin qannen hajiya din.


              Da sallama ta shiga cikin kamala da kuma kunyar da har yanzu batajin ta gushe a tsakaninsu,duk da irin abubuwan da suka faru a baya,da irin ababen da ita hajiyan tayi mata masu dimbin yawa dake da soya zuciya da saka me rauni ya tsani mutum. Taji babu dadi ta kuma koka matuqa da gaske,saidai ko sau daya bata taba jin ta tsaneta ko zata iyayi mata rashin kunya ba,saboda me?. A koda yaushe tana duban hajiyan a matsayin wani tsani na dukka matakin da tahau a rayuwarta,duk tsiya duk kuma inda za'a je a dawo itace dai ta haifa mata saleem din da zuciyarta ke matuqar so take kuma son ta kyautata masa wanzu tare ila yaumil qiyamati,ta bashi tarbiyyar da har ta burgeta ta kuma zame masa silar mallakarta,tana ganin wadannan dalilai kadai sun isa babban dalilin da hajiyan ta cancanci dukkan wani uzuri girmamawa da dagin qafa daga gareta.


             Sallamar ruqayyan yaja hankalin hajiyan. Sai ta far gyara zamanta cikin fara'a da kuma d'ari d'ari,kunya da nauyin yarinyar a yanzu takeyi


"Maraba,qaraso ciki mana,na tambayeki abokiyar zaman naki tace kina gida kina girki" murmushi cikin jin nauyi ruqayya ta saki. Hukumullah ta fada a ranta,duniya juyi juyi,wai yau itace hajiya ke tambaya?,ita din da a baya hajiyan kan fadi cewa kada a sake zuwa mata da ita?,ita din da a baya take cewa ta gaji da ganinta,yadda ta ganta jiya haka zata ganta gobe da jibi ma?. Kauda wannan tunanin tayi,ta zauna saman pillow din da hajiyan ta tura mata ta soma gaidata cikin tsantsar ladabi da kunya. Amsawa tayi cikin kulawa itama,ruqayyan ta waiwaya ta gaida sauran 'yan uwanta dake falon. Waiwayowa hajiya tayi ga wata dake a tsaye


"Lu'ubatu a kawo mata abinci ko?" A ladabce ruqayyan tace


"Bari naga me jegon tukunna hajiya"


"Gasu can acan dakin sun cikawa jama'a kunne da hayaniya" dan qaramin murmushi tayi tana miqewa. Tunda ta shigo take jin tashin hayaniya sosai a dakin,saita ratsa ta isa ga dakin.


               Za'a iya cewa a cike yake dakin,saidai girmansa ya sanya kowa ke zaune a sake ba tare da an takura ba. Hira suke qwarai ba qaqqautawa,zainab na daga cikin 'yan committee na hirar don da alama ita ke bayarwa ana amshewa. Sallamarta tasa hayaniyar ta ragu,sai idanu kuma sukayo kanta,wasu na amsa sallamar yayin da wasu suka buge da qare mata kallo ciki harda Zainab dake tunanin yaushe ruqayyan ta dinka atamfar nan?.


             Raliya dake zaune daf da zainab ce ta tabota murya qasa qasa


"Kin ganta kuwa sai yanzu,lallai ita me aji" waiwayo zainab tayi sannan ta tabe bakinta


"Tana can miji ya maidata jaka,sai data gama girki da gyaran gidan,kinsan ni duk ranar girki ne lallabani yakeyi,kada na gaji dare yayi ya kasa morar dadi,duk ran girkinta a wahala take qarewa,uban kayan ciki ya hadata da dahuwarsa,a dafa mana,mu koma mu kwashi banza ba tare da mun tsinana komai ba" ta qarashe zancan tana kwarara dariya raliya na tayata suka tafa ji kake fass. Dariyar tasu taja hankulan wasu a wajen,banda ruqayya data tattara hanakalinta ga dan jaririn fatima. Fatima mutuniyarta ce qwarai,zata iya cewa cikin dangin mijinta ba wadda suke dasawa da ita kamarta. Tana riqe da yaron tana duba ciwon idanun da fatiman tace kamar yaron yana yi.


               Batulu ce dake gefansu ta dubi zainab dake dariya saman fuska,amma qasan zuciyarta kamar an watsa garwashi,don sosai black prince din jikin ruqayya ta tsone mata idanu,sai wani sheqi takeyi da daukar idanu


"Wato ke sauqaqqan girki ake baki ko?,sharp sharp"


"Ashe dai kin gane" ta fada tana watsa mata wani kallo. Dariya batulu ta saki


"Yo ni ai banga wani gata a nan ba,hasalima gani nakeyi kamar ya raina sanwarki ne da iyawarki,shi yasa yake dabara ya kawo ranar girkinta don yasan bazai bata kudinsa ba" da sauri ta waiwayo tana duban batulu,dama akwai 'yar tsama kadan tsakaninsu. Batulun irin matan nan ne da basu barin ko ta kwana,hakanan basu da tsoro


"Eh,ai gaskiyar maganar kenan,sanwarta tafi taki dadi,ai na tabacin farfesun naki,hakanan nasha cin girkin anty ruqayya ko wajen hajiya kuwa"


"Hajiya kuma?" Ta tambayi batulu


"Eh,lokaci lokaci ai ruqayya nada qoqarin wannan aiken kam,sai aka dace hajiyan nason sanwarta" sosai maganar ta daketa,don bata taba tunanin kaiwa hajiya koda silin taliya ba a matsayinta na 'yar 'yaruwarta,hajiyan mada tudu biyu a wajenta,babarta kuma uwarmijinta,bata kuma san ruqayya tana yi ba,asalima ita din tana cikin matan da suke ganin kaiwa uwar miji ire iren wadan nan abubuwan ba komai bane sai tarin bautar da kai. Tunda dai komai saleem yana siya yakai mata ai ba buqatar sai an kai mata dafaffe koda sau daya a wata ma kuwa. Idan Allah ya kawota baqunta taci,idan batazo ba haramiyarta a kuma sauka lafiya.


                Ci gaba da hirarta batulu tayi suna gaisawa da ruqayya kuma cikin fara'a da sakin fuska. Sallamar basira ita ta katse sauran tunanin da Zainab keyi ta tattarashi ta watsar,farinciki kuma ya maye gurbin bacin ranta,ganin basira kawai ta tabbatar yau din akwai harka. Muryarta kuwa tafi ta kowa dagawa


"Kaga basira me kayan harka,Allah ya barmu dake ki jima kina yi" mamaki yadan kama ruqayya,don ta tabbatar har yanzu su hajiya na zaune a falon,kuma tayi imani suna iya jiyo komai


"Ai inata sauri hajiya zainab karki tafi"


"Wa?,ni?,Allah ya kasheni musulma naga kayan harka na tafi ban kwasa ba,ke a banza nake zaune a gidan alhaji saleem?,banda wadan nan abubuwan da tuni boka da malam sun jima da tsigeni a gidan" ta fada tana tafa cinya gami da kallon gefen da ruqayya ke zaune a sace tana gogewa babyn idonsa da magani.


                Zaman dirshan basirar tayi ta kuma zazzage jakarta,take mata akayi caaa,na waje ma da basusan me ake ciki ba sai gasu da daya da daya suna gangarowa. Yawancinsu amare ne auren watanni masu haihuwa daya zuwa uku hudu. Yaran mata sosai da sukejin ludayinsu yana kan dawo suka cika cacim.


"Duk wadda bata da kudi ma kada ta damu,har adashi inayi,sai na saka kowa a wassuf guruf" basira ta fada cikin jin dadi da farinciki. Tunda take fadi tashi da buge bugen sana'o'i bata taba cin karo da sana'ar dake da wani irin mugun farinjini da kawo zallar madarar kudi a nan take ba irin wannan sana'ar


"Ni wallahi wanann nakeso,da alama aikinsa yafi na dukka magungunan nan" zainab da hankalinta ya dauku ta fada tana daga kwalbar dake cike da wani abu me danqo,an lullube kwalbar da wani rubutun hatimi da wani tsinke a maqale


"Yana da kyau akwai kuma aiki,amma gaskiya duk nan ba kaya me tsadarsa,tafiyayye ne tun daga sakkwato" sai tayi qasa qasa da muryarta


"Kinsan Allah daga gidan malamin aka karbominshi ana kawomin shi na jefashi a jakar nan na fito nayi nan,wannan ma na wata hajiya ne,idan kinaso zan yiwa malamin magana yayi miki naki hadin na musamman" a take Zainab taji qaunar maganin ta shigeta. Kai ta girgiza


"Wallahi ko na uban waye saidai tayi haquri,bani da kudi amma ina da kayan kudi,zan bayar a barmin shi,nawa kudinsa yake?"


"Fisabilillahi a bisa sauqi shi da wannan ruwan....." Ta fadi tana miqa hannu ta dauki wani ruwa da yasha gamje gamje harda su dan tsami da gishiri da sauran tarkace ya koma brown,tana zaune kuma idea din hakan tazo mata


"Idan kika hada aikinsu yafi zuwa dai dai,ki bada dubu arba'in da biyar,amma wallahi tallahi na rantse miki da Allah har dubu sittin na karba a kansa" kai zainab ta girgiza tana juya maganin a hannunta


"Ai kuma na yarda hajiya,ni dama ba kasafai nakeson maganin dari biyar dubu daya ba,ko a baki wani sassaqen bagaruwa ko sassaqen malmo ace wai ka dafa tsumi kasha,tsumin me?,kafin kiga aiki miji ya gaji da jin shuru maqatau?" Ta fada tana daga murya hadi da gatsine duk don ya isa kunnen ruqayya. Ta jita amma ta bawa banza ajiyarta,hasalima dariya ta bata,saboda a wajenta wannan hade haden da zainab ke yiwa kanta tabbas abar tausayi ce ita idan batayi da wasa ba. Kawai fargabarta daya kada ta kwaso abinda zata qunsawa saleem itama kuma ya sanmata.


              Cikin lokaci kadan hannun basira ya cika da kudi dumus,aka kwashe kaya tsaf sai ragowa. Idanu ta shiga wulgawa a dakin tanason ganin wanda bai siya ba taja raayinsa,don so take ta fita da kudinta gaba daya. Ruqayya ta hango sai ta dubi zainab daketa shirya kayayyakinta qasan jaka cike da farinciki. Tasan kishiyarta ce amma ita ba ruwanta neman kudinta takeyi,don haka ta dan daga murya


"Hajiya azo a yiwa me gida gyara mana,kayanmu ingantattu ne sai an gwada akan san na qwarai" kamar ta dorawa Zainab guduma aka haka taji,ita basira zata yiwa haka?.


               Fatima dake zaune tana cin tuwo gefan ruqayya ce ta zunguri ruqayyan,ba tare data kalleta ba murya qasa qasa tace"Don Allah kema anty ki saya mana kiyi gyara" murmushi ta saka bata dubi fatima ba tace


"Hajjaju Allah ya bada sa'a" kai tadan sosa


"To amin,amma ko kudi ne baki dashi ai ina lamuni,idan kika gwada yayi aiki kya biya daga baya"

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post