Kurman Baki page 16 by Huguma


Health College

Kurman Baki page 16 by Huguma

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫


*HUGUMA*


PAGE 16



*_RUK'AYYAT GRAPHICS_*


*_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_*


*_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_*


*_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_*


LOGO

INVITATION CARDS

BANK STICKERS

BUSINESS LOGO

SAVE THE DATE

P.O.S BANNERS

BIRTHDAY CARD

BOOK COVER

DATA FLAYER

BIRTHDAY VIDEOS

VIDEO INVITATION

AI PICTURES


_KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_


*_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_*


*RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku


_KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_


https://wa.me/+2347084515410


_ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽

_____________________________



           Da gudu surajo ya cilla ya fice daga gidan,saboda yasan indai umman ta fito ta karbi kudinta to ya shiga uku gurin wasila. Hakanan 'yar naira ashirin dinsa shima ta shiga rububi.


          Umma na daga kitchen tana mitar halin wasilan na zabe zaben abinci


"To wai umma idan bakiyimin ba waye zaimin?,kuma ai ansan banason tuwon aka tashi akayi mana,kinga kuwa bazan kwana da yunwa ba". Suna tsaka da wannan taqaddamar Surajon ya dawo. Tasa hannu ta karba tana cewa


"Surajo me abun arziqi da na tsiya,yanzu dai sai gaka sharp sharp,to ga kudinka" ta miqa masa ashrin din. Hannu yasa ya karba yana cewa


"Ana sallama ma sake a waje" fuska tadan bata


"Waye?"


"Isma'il ne" ya bata amsa dai dai sanda umma ke fitowa daga kitchen


"Bawan Allah dan albarka,je kace tana zuwa kaji" juyawa yayi ya fice abinsa,yayin da fuskar wasila ta canza ta jawo ledarta tana budewa. Kallonta umma tayi


"Nayi tsammanin zakije ki fara saurararsa kada abar mutum haka a tsaye?"


"Ni yunwa nakeji wallahi umma,sai naci abinci tukunna,idan bazai iya jira ba ya tafi" 


"A'ah,kedai kiyi da jiki ki gama" umman ta fada tana kade gefan tabarmar da suke kai din ta sanya hijabinta ta tayar da sallar isha'i.


              Da gayya ta dinga laqai laqai harta gama,siririn mayafi kawai ta yafa saman doguwar rigar jikinta tadan sake shafa turare tayi hanyar soron. Haushin isma'il takeji,wannan shige matan da yakeyi,sai taga kamar yana nesanta ta ne da irin mazan da take sa muradi,yaqi ya gane yaqiyin zuciya kuma ya barta.


             Kansa a qasa yana danne danne a wayarsa,jin takunta ya sanyashi daga kai daga abinda yakeyi yana dubanta,sai ya saki qaramin murmushi yana fadin


"Barkanki da fitowa ranki ya dade" 


"Yauwa,barka" ta fadi kadaran kadaham. Ita kanta tasan isma'il bashi da wata matsala ko makusa,amma an riga an gaya mata ba shine alkhairi a tattare da ita ba,kuma itama ta gamsu da hakan,tunda baikai arziqin da takeson mijinta ace yana da shi ba,yadda take da tarin magauta din nan,tanason ta auri mijin da idan ta shiga gidansa za'a san yes!,ta auri me arziqi,mijin da first night dinta zai bata kyautar mota,mijin da zata dinga zuwa umra da aikin hajji har sai ta gaji,mijin da zai dinga sauya mata kalar motocin da zata ji dadin takota ta shigo unguwarsu tana fankama da hura hanci,ta bule maqiya da mahassada da qura,ana kiran hajiya wasila tana kyautar sabbin kudi,dukka tasan isma'il bazai iya affording wannan ba,duk kuwa da tasan ci sha sutura da wirin zama duk ba zata raza ba,don bai rasa komai din ba,hasalima Lagos yake zuwa yayi sari na shagonsa me yawa. Ya siya fili kuma gini yakeyi me kyau,amma yace mata idan bai samu kammalawa ba har lokacin aurensu zai kama musu haya kafin ya kammala daga bisani sai su tare.


              Itakam babban abun kunya ne a gareta ace wai yau ita wasila.......wasila guda tana a gidan haya,me yafi wannan abun kunya?,duk wadanda duka sanya ido suga ya zaka qare suyi maka dariya suyi shewa son ransu kenan,Allah sitru buqui inji kishiyar me doro.


             Shi ya karba daddumar da ta fito da ita ya shimfida sannan suka zauna akai. 


               Kusan fiye da rabin hirar shi yakeyi,har zuwa wani lokaci da yaga ta fara hamma da lumshe idanu duk kuwa da cewa duka duka baifi minti arba'in da zuwa ba


"Yadai?" Ya tambayeta cikin kulawa. Fuska ta yatsina ta danja tsaki


"Bacci nakeji,kuma ma dai yunwa ma nakeji,haka kawai umma tayi mana tuwo yau" 


"Subhanallahi" ya fada cikin dan gajeran nazari. Bayan dan shuru da ya biyo baya na sakanni sai kuma yace


"Ai bai kamata ki kwana da yunwa ba seela ta" ya fada yana fiddo wayarsa a aljihu. Bugu biyu aka daga suka gaisa


"Ina layin nan dake kallon gurinku........eh takeaway nakeso a hadamin me kyau.......yauwa komai da komao,ya miqo layin sosai sai yazo gaban wani gida me farin fenti ina daga ciki...... alright na gode" daga haka ya cire wayar a kunnensa ya maida aljihunsa


"Ai da ka barshi wallahi" Ta fada kawai don jin baki


"A'ah,ba za'a yi haka ba ai,so kike nima na kasa bacci?" Murmushi ta saki tana jin dadi a ranta


"Yauwa ni da albishir mafa nazo miki,ga yunwa kuma kina ji,anya albishir din nan zai fadu?" Wata zaquwa ce ta kamata, zuciyarta na hasaso mata waya zai sauya mata 


"Fadi kanka tsaye yallabai,ai dukka kunnuwana suna tare da kai"


"To shikenan yallabiya" ya furta cikin dan salon tsokana,yaza hannu ya tura hularsa baya sannan yace


"Zuwa yanzu wasila ina gani lokaci yayi da zamu maida alaqarmu ta ainihin gaske,tunda iya fahimtar juna mun yishi tsahon shekarun da muke tare,ina so ki shaidawa umma,ta yiwa su kawu magana in sha Allah qarshen watan nan zan aiko da kudin aurenmu hade da kudin sa rana,kuma banason duka a wuce wata hudu in sha Allah ba'a yi bikin ba" tunda ya fara zancan ta zuba masa ido gabanta yana faduwa. Bata shirya auren isma'il ba bata kuma son ta rasashi tun yanzu,tafison koda zai tafi sai idan FAISAL ko wani kaman faisal din ya kawo mata kudin aurenta tasan ta kama dahir


"Kudin aure kuma isma'il ka gama ginin ne?" Ta fada tana dubansa. Dan nazarinta yayi kadan


"A'ah,yanzu ba magana ake ta gama gini ba,gini na yana da buqatar a zuba masa kudade da yawa,inason nayi abu me kyau me tsari,wanda duk wanda ya kalla zai san na mori nemana" Fuska tadan bata tana girgiza kai


"Gaskiya nidai nafi buqatar ka kammala tukunna"


"Wasila" ya kira sunanta kai tsaye a maimakon seela da yakan kirata da shi,abinda yasa itama tayi hanzarin daga kai tana dubansa


"Ni na shirya aure magana ta gaskiya,sanann hajiya kanta kullum maganarta kenan nayi aure taga 'ya'yana kafin ta Allah ta kasance a kanta tunda ban rasa komai ba,hankalina nima yanzu ya karkata ga hakan,in sha Allah bazan wuce wannan lokacin ba tare da nayi aure ba,idan kin shirya nima na shirya"


"Idan ban shirya ba fa?" Ta fadi a qasan ranta tana dan satar kallonsa gabanta yana sake tsananta faduwa. Isma'il shine saurayi kusan na biyar da haka ta taba faruwa a tsakaninsu. Abdullahi,abubakar,nasir da sagir ga kuma isma'il. Dukkansu sun tafi ne saboda samun masu kudin da take muradi a irin wannan lokacin,kamar hadin baki dukkansu sai zance ya fara nisa a tsakaninsu sai masu kudin da take buri su bayyana saisu rushe gwamnatinsu,sai bayan ta sallamesu ne saboda ganin wadan nan sai suma daga baya su fece su barta ba wan ba qanin. Tayi qunan rai a sannan ba dan kadan ba,tun daga lokacin ta yanke hukuncin ta daina sallamar standby din har sai ta tabbatar ta kama wadancan din,yanxu gashi ana neman kwatawa

(Yan mata!,yan mata!,wallahi wallahi wallahi kuyi hankali,ku yiwa kanku karatun ta nutsu,a irin wannan yanayin da ake ciki babban arziqi ne ma ki samu wanda zaice yau so nake muyi aure,da yawansu ba aure bane a ransu,saidai suzo su hole da ke kamar uwa su ta haifa musu ke,da yawan 'yammata ba mijin aure suka rasa ba, a'ah.......MIJIN BURI MIJIN MAFARKI suke jira ko ince suke nema,kibar wahalar da kanki kina namena lallai saikin auri me kudi,wallahi wannan din da kika raina qila shine me kudin da kike burin amma kika wulaqantashi,Allah ya rubuta sai ya aureki zakuyi arziqin tare amma kika bijire saboda idanunki sun kulle, ba'a ce ki auri namijin da bazai iya kula dake ba,namijin d a baikai ajinki ba,tunda ko a musulunci akwai KAFAA'A wato dacewa da juna,amma ta yaya a gidanku ana kulawa dake da kwatankwacin kudin da sukakai dubu dari kice ke wanda zai kula dake da million d'ari kike nema?wanne irin buri ne wannan?. A qa'ida dai ba'a son ana kula dake a dubu dari ki auri wanda saidai ya kula dake da dubu goma,ko ina anason aga mace gidan mijinta yafi gidansu ci gaba,AMMA FA👂🏼👂🏼👂🏼 ba tarin dukiya ba. Albishirinku!!!!,akwai tarin dimbin matan da zaki gani cikin leshi na kece alfarma,motar hawa ta isa da qasaita,gold kowanne corners na jikinta bodyguard da sauransu,amma billahillazi la'ilaha illa huwa da zata bude miki cikinta saikin kwana kina sallah kina godewa Allah da ya barki a inda kike,shi aure bawai mutum me DUKIYA kadai ake nema ba,Inaaaaaa........'yar uwa nemi MAI ZUCIYA wanda ko matar da take Jin mijinta wani ne idan kuka jera da ita zatasan lallai kinfi qarfin raini,nemi mijin dake KISHINKI wanda bai yarda matarsa ta rasa komai ba,wanda bai yarda a raina matarsa ba,wanda zai maidake SHALELE kifi qarfin rainin kowacce mace,mijin da zai kula da lafiyarki sai inda qarfinsa ya qare,wanda ya damu da damuwarki me tsare miki mutuncinki da dukkan qarfi da iyawarsa,wanda zai dauki iyayenki tamkar nasa ya basu girma na musamman.ba mai tarin dukiyar da baki da tabbas din zaki cita cikin kwanciyar hankali ma kuwa?. Da yawan 'yammata basu shiga gidan aure sunsan meye ainihin ma'anar miji ME DUKIYA ba dame ZUCIYA wannan shike rudarsu. Akwai wani jin dadin da duk girmansa kome miji yake baki koda kullum million hamsin ce wallahil azeem idan yana miki wasu halayen ba zaki taba jin dandanonsu ba,saikin gwammace naira dubu goma yake baki yake mua"amalantarki cikin nuna qauna tausayi da girmamawa,don Allah qannena yayyena da sa'annina YAMMATA ku farka,KU FARKA,KU DAINA KORE MAZAJEN AURENKU SABODA HANGE DA NEMAN WANDA YA FISHI,Allah ya shiga lamuran rayuwarmu gaba daya 👏🏽👏🏽


*HUGUMA*👑

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post