Kurman Baki page 17 by Huguma

Kurman Baki page 17 by Huguma

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫


*HUGUMA*


PAGE 17




             Tana tsaka da wannan nazarin akayi sallama qofar soron,isma'il ya miqe a nutse ya karbo saqon ya dawo ya zauna yana ajjiyewa gabanta


"Kada ki damu,amma kije kiyi nazari,saidai am sorry to say....koda baki shirya aure ba in sha Allah zanyi aure a wannan lokacin,don haka kiyi tunani a hankali kina da sati daya cif,duk abinda kikaji zuciyarki bata kwanta da shi ba kada ki yanke shi,ki zabi abinda kikaji kinfi aminta dashi,zaman aure zamuyi wanda muke saka ran mutu ka raba,bawai aje a dawo ba" da wadan nan maganganun yayi mata sallama ta dauki ledar takeaway dinta ta wuce gida.


            Da farko jikinta yayi sanyi sosai,har ma ta dinga juya lamarin,wata salihar zuciya daga qirjinta tana gaya mata


"Me zaki jira?,kin cika shekara talatin fa kenan wasila,ki yarda da isma'il kiyi aurenki ki huta,tunda bazai barki da yunwa ko a wulaqance ba" zuciyar dake da gamayya da shedan na tuna mata


"Shi kuma faisal ya zakiyi dashi?,idan kika amincewa isma'il shi kuma faisal yana da niyyar aikowa kinga kin yiwa kanki asara,yanasonki Faisal yanason kuyi aure,akwai jifan da ake miki ne ansan da arziqi a jikinsa ba'a so ki shiga gidan hutu shi yasa,amma da tuni kin jima da zama matarsa" kai ta jinjina tafi yarda da shawara ta biyu. Su masu jifan nata qila an duba musu sunga wahala zatasha a gidan isma'il shi yasa basu maida hankali su rabasu ba,sun hango arziqi jikin faisal wannan dalilinne yasa sukafi maida hankali a kansa.


"Bari kiga" ta fada ita kadai tana janyo wayarta,wata number dake dauke da sunan MALAM ta lalubo ta dannan masa kira.


                 Sai data kusa katsewa ya daga,suka gaisa da kakkaurar muryarsa sannan ta fara masa bayani


"Isma'il ya matsa malam,yanzu haka zancen turowa yakeyi,ni kuma tun kafin ma ka shaidamin babu alkhairi tsakanina da shi nafison faisal gaskiya,don Allah malam a taimaka asa faisal ya turo ko yayi maganar kafin isma'il ya dawo" kai ya jinjina,yanzun haka a buqace yake da kudi


"To ai shi kansa faisal din ba maganar aure a ransa kwata kwata,saidai zamu bullo masa ta bayan gida,bazai wuce wata guda ba tare da ya aiko din ba" 


"To na gode sosai malam Allah ya saka maka da alkhairi"


"Ameen........yanzuuuu ......akwai turare da zamu siya,daga Syria ake kawo wannan turaren,sai wasu duwatsu daga misra a cikin ruwa ake samo ire irensu"


"Kamar nawa kenan ane buqata malam?" Dan shuru yayi sannan yace


"To,ai wasila ke abar tausayi ce,dole me imani ya tausaya miki saboda irin jifa dake jikinki Allah yayi yawa dashi,ki bayar da dubu ashirin,abinda bai cika ba na cika miki cikin aljihu na" Taji dadi sosai,godiya ta dinga yi masa kamar ta durqusa,sukayi sallama ta kashe wayar.


                  Ranta fes ta soma cin takeaway dinta,a yanzu tunaninta inda zata hada kudinne kawai,don ba komai takeson gayawa umma ba,wani abun sai ta doje akai,tafison kome zatayi tayi abinta kai tsaye ba'a kawo mata cikas ba.


                Wayarta ta jawo sai tayi tunanin tayi kiran faisal(sau tari dama wasu 'yammatan suna qarewa ne da kiransu,kafin ya kirasu sau daya sun kira biyar). Duka yau basuyi waya da shi ba,amma takan bashi uzurin cewa harkokinsa ne sukayi masa yawa.


               Har ta katse bai daga ba,sai data qara kira bugu biyu ya dauka. Ranta fes ta shagwabe masa,shima ya biye mata suka bata kusan awa biyu suna waya,don leqowar umma biyu amma bata gama wayar ba.


             Suna tsaka da wayar dai dai lokacin da tasan yafison hira da ita ta katse wayar,sai bayan minti kusan biyu ta kunna ta kirashi


"Nayita trying kuma naji a kashe"


"Uhmmm wallahi,qawata ce ta shigo,bikinta ya kusa,ta kawomin anko amma nikam gaskiya na gaji da yin ankonnan,nima burina yanzu ace yau nice na fitar da nawa ankon kamar kowa?" 


"Nawa ne kudin ankon?" Ya fada yana share maganarta ta biyu


"Dawainiya baby?"


"No,kada ki damu abinda kakeso kake wahaltawa ai ko"


"Gaskiya ne" ta fada da wata siriryar shu'umar muryarta cikin son sake shigar da kanta zuciyarsa


"Lace ne 20k,sai atamfa 10k"


"Alright,to ba damuwa,zan saka miki 40k harda kudin dinki"


"Wow.....Allah ya biya, godiya nake" a cikin ranta tana jin ta samu kudin da zata biya malam harda riba.


               Wannan abun da ya faru a ranta sai ta sake jin me zatayi da isma'il?,mutumin da qarshen kyautar bajintar da zaiyi mata itace 10k,itama sai bisa abu me amfani tare kuma da qwaqwqwaran dalili. Tun a daren ta yankewa kanta shawarar sallamar isma'il,indai aikin malam yayi kyau Faisal yana magana zatace a saka wata biyu ma,tasan daga umma har yayunta duk a shirye suke mijin dama kawai ake jira.


********Tun da tayi sallar asuba bata koma ba ta wuce kitchen don hada abincin yara da nasu da wanda za'a kaiwa zainab asibiti.


                Shima saleem din da ya dawo daga masallaci zama yayi saman abun sallah yayi lazumi da karatu kamar yadda ya saba,bayan ya kammala bacci yadan daukeshi.


              Koda zai farka ta kusa gama sallamarsu,don uniform kawai suke sakawa,ya shiga dakin ya iskesu kowa yana saka uniform dinsa. Alhassan ya gama iftee yake sakawa socks. Su alhassan suka fara gaidashi,ganin haka kuma sun hada ido da haneefa sai itama ta matso tana gaidashi.


                Gefe ya koma yana karantar kowa. Tare ya canza musu uniform da komai na makaranta,amma idan kaga nasu haneefan zakayi tunanin sai da suka shekara biyu sannan aka dinka nasu alhassan,a haka ma kuma wai a wanke suke. Yana daya daga cikin abinda yasa daraja da martabar ruqayya ke qaruwa a idanunsa,sau tari idan zai canza musu abu takance yabar nasu alhassan din tunda nasu baiyi komai ba, musamman idan ta fuskanci baya da kudi sosai a hannunsa. Saidai karamcinta yakan sanya bayan wani lokaci itama yayi mata kyautar wani abun da yake kaman madadi na wannan sadaukarwar da tayi (hakan yana da kyau,bawai kice don an yiwa kishiyarki ba koda miji yadan shiga yanayi kema ko a mutu ko ayi rai sai an miki ba ke ba ruwanki,a'ah.....zuciya fa tanason me kyautata mata,sannan duk abinda ke faruwa namiji yana ankare,saidai ba kowane zai nuna ba amma a qasan zuciyarsa yasan da hakan. Bugu da qari ke kanki idanma ba zaki iya haqura ba,akwai hanyar da hankali kwance zaki fanshe kudin ba tare daya ankara ba,kema kuma baki rasa wannan darajar ba cikin wayo hikima da dabara).


           Da dukka lunch box dinsu ta shigi,tuni haneefa ta biyewa khalil suka dinga doka tsalle bayan sun bude sunga meye a ciki. Rabon da suje da sabon girki har sun manta,sannan koda zasuje da shi dinma ina yaga dadi da haduwar wannan. Dubansa ya maida kanta ta duqa kadan daga tsaye tana gyarawa iftee hijabinta. Yadan lumshe ido,ko yaushe abinda zai sanya yaga kyanta cikin idanunsa takeyi. Rigar baccin jikinta me wani irin taushi da sulbi sabuwa ce, gray color me wani irin daukan idanu,tabi tattausar chocolate color din skin dinta ta kwanta sosai. Baya taba gajiya da kasancewa tare da ita,koda komai bazai hadasu ba ta jingina da jikinsa kadai yana shaqar daddadan qamshinta yana shafar soft skin nata kadai yana sakashi nishadi. Hular kanta tadan zame bata,gashinta duk da baikai tsahon na Zainab ba amma yafi na Zainab bashi sha'awa da qayatar dashi. Don kafin ta karba girki shekaran jiya taje aka wanke mata shi fes aka mata stretching don ba kasafai ta fiya ma sanya relaxer ba. Qamshin hair mist kawai yakeyi da hair oil.


"Zauna ki huta" ya fadi yana amsar agogon iftee da take shirin daura mata. Dagowa tayi sai suka hada ido,ta sakar masa murmushi ganin yadda yake faman qare mata kallo,har albarkatunta dake cikin riga idanunsa sai da sukakai kai


"Na gode" ta fada a tausashe taja baya tana zama. Dan murmushi ya saki,qamshin kanunfari na fita daga bakinta,sai zainab ta fado masa,ya tabbatar da itace tayi masa magana a irin wannan lokacin saidai ya kauda kai.


             Da kansa ya kadasu farfajiyar gidan wajen driver,sai da ya tabbatar sun fice sannan ya dawo gidan da dan sassarfa,don ta riga data tsomoshi.


                Tana qarasa gyaran falon ya sameta tsaye gaban tv. Ta bayanta ya tsaya ya rungumota jikinsa yana cewa


"Aiba wani aiki,aiki kuma ya qare,aji da dan hajiya malam saleem" qaramar dariya ta qwace mata,don ya tuna mata da tsohon sunan da ake kiransa shekarun baya


"Haba malam saleem,da safen nan?"


"To me zan jira?,bayan jiya qwalele kikayimin,wai ina isowa na tarar kinyi bacci ko tausayina ma bakiji" ya fadi yana shafa kafadarta har zuwa tsintsiyar hannunta. Tsigar jikinta ce ta zuba wannan ya sanyata noqe kafada


"Kuma kika saka wannan rigar don kawai daukan alhaki ko?" Ya sake fada yana juyo da ita tare da saka hannunsa ya fara balle bottom na rigar. Shigewa jikinsa tayi wannan ya bashi damar riqeta sosai suka wuce bedroom dinta dake a gyare fes don dama ba ciki suka kwana ba. Yanayin bedroom din ya sake qara masa shauqi qwarai da gaske,ya tsumu da turaren wuta qwarai,hakanan bata gajiya da yiwa bedsheets pillow case da blanket dinta kabbasa.


(Ko da magani sai da tsafta,ko da gyaran HQ saida gyaran tukunya,gyaran lafazin baki iya mu'amala da gyaran muhalli. Koda wadannan sai kina updating yanayin position na auratayyarku,ba ko yaushe ki shirgice ki jibge kaman kayan wanki ba,KINSAN AMFANIN DIRTY TALK?KINA MASA KO SAIDAI 'YAMMATA A WAJE SUYI MASA KINA ZAUNE?IDAN KIKA GA KUMA AN MASA KICE WANE YA ZAMA DAN ISKA MAZINACI?,BAYAN KEMA KIN TAKA RAWA?,TURQASHI.....nauyinku nakeji amma zan bincina muku kadan cikin littafin nan ta hanyar data kamata idan na samu chance😄,ragowa kuma zai shige a littafin GUDUN ƘADDARA 2024 in sha in sha Allah.


*HUGUMA*👑

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post