New: Kurman Baƙi page 1 by Huguma

New: Kurman Baƙi page 1 by Huguma

 

Kurman Baƙi

https://chat.whatsapp.com/LP1fwEwAkejETakHaD59VO

*_Bismillahir rahmanir rahim_*

*_KURMAN BAK'I_*

*H U G U M A*

PAGE 01

_Akwai saqonni masu tarin yawa a ciki,saidai kuma KURMAN BAQI ne me wuyar fassaruwa,ga duk me nisan zangon hankali da tunani zai tsinkayi hakan,DAN JAGORA NE ga mata,musamman masu KISHIYA,kuma hannunka me sanda ne ga masu sana'a  data shafi labarin dake cikin littafin_

*NOTE:qirqirarren labari ne wanda ya dace da matsalolin da mata ke fuskanta a yanzu,komai dake ciki qirqirarre ne,idan ya dace da zahirin rayuwar wata to arashi aka samu*

          Zaune take zaman farar stool din dake ajjiye gaban dressing table din dakin. K'afarta daya kan daya tana kuma karkadasu da wani irin sauri. Kallo daya tak zaka yiwa fuskarta ka fahimci akwai zallar bacin rai mai mugun yawa shinfide a saman fuskarta,bacin ran da ko shakka babu yana yiwa zuciyarta wani irin fusga da kud'a me ciwo.

             Hatta da launin idanunta zuwa fuskarta sun sauya,abinda zai alamta maka kuka tasha bana wasa ba,da alamu kuma ba wani lokaci me tsaho ta dauka da gama kukan ba.

           Har cikin zuciyarta takejin wani irin masifa da tashin hankali suna sadakarta. Qoqari take tayi ta taushi zuciyarta amma kuma kamar hakan yana neman gagararta. 

            Ita din tana cikin jerin sahun matan da basu iya cinye fushi da bacin rai ba tare da zukatansu sun furta ko sun furzar da shi ga dukka wanda yayi silar afkwarsu a wannan yanayin ba.

"Idan ba damuwa don Allah zan dan fita yau din,amma bazan wuce awanni biyu ba zan dawo in sha Allah" Sautin muryar dake tashi sama sama ya ratso ta cikin windows dinta,ya kuma keta labulayenta ya isa ga kunnuwanta.

             Isar sautin muryar kadai ga kunnuwanta amma sai taji kamar an sakar mata guduma cikin tsakiyar zuciyarta. Tana da muradin jin amsar da wanda akayi maganar dominsa zai bayar,wannan ya sanyata miqewa zumbur ta kuma kai ga labulen ta yaye a zafafe.

            Fes take iya hango mutum biyun wanda ke magana cikin wata irin nutsuwa a tsakaninsu. Tsayayyen namiji ne wanda ke tafe da tsaho da kuma qibarsa gaba daya,wanda hakan ya bashi wani irin kyakkyawan murjajjen jiki da ya qara masa kyau da cikar zatin da kai tsaye ya isa ya amsa sunan NAMIJI. Duk kuwa da cewa shi din ba wani mugun kyakkyawa bane,amma sam sam bai hada koda hanya da kalmar MUNI BA. Baqi ne da bahaushe kan kira da wankan tarwada,wanda yayi wani irin kyau me cike da nutsuwa cikin wani lallausan yadi ruwan sararin samaniya a jikinsa. Ganinka na farko da shi zaka tabbatar da cewa shi din gwanine wajen iya murza hula da sanya sutura ta zauna a jikinsa,hakanan telansa ya qware qwarai da gaske gurin baiwa dinki haqqinsa,dukka wadannan abubuwa suna da cikin abubuwan da suka hadu suka qarawa SALEEM kwarjini da cikae kamala da kuma siffa.

             Matar dake a gefansa kuwa duka duka shekarunta ba zasu haura ashirin da takwas ba,idan tayi nisa da yawa ashirin da Tara zuwa talatin. Ita dinma baqa ce kamarsa,saidai nata baqin har yafi nashi gogewa,chocolate color ce sosai,mai matsakaicin tsaho,ba gajeriya bace,saidai kuma bata kai tsahonsa ba sam sam. Tana da manyan idanu masu matsaikatan girma,hakanan hancinta yana da tsaho da tudu. Komai nata matsakaici ne,itama tana da wani kyau na daban,wanda baiyi yawa ba.

"Ina zuwa kenan?" Ya tambayeta yana duban fuskarta da murmushi ya subuce mata


"Gidan aunty khadija mana"  kai ya jinjina yana murmushi 


"A dawo lafiya Allah ya tsare" ya fada yana same fadada murmushinsa. Qaramar dariya ce ta qwace mata


"Da sauri haka?,saboda kaji gidan aunty deeja ne?" Ido ya fiddo yana sakin wani murmushin


"Ta yaya zan hanaki zuwa nan?,ai nasan ta samu ne" ya fadi qasa qasa. Siririyar dariyar da ta ajjiyeta musamman saboda shi ta saki,cikin salon nuna jin kunya tace


"Ni bance ba,amma dai sirri ne"


"I know,bance sai naji ba nima,Karki jima please" ya fada cikin tausasawa yana takawa zuwa muhallin ajiyar mota na gidan dake dauke da motoci gida uku kamar yadda iya adadin abinda zai iya dauka din kenan


"Nasan ba ka son yin dare a waje daddynsu,ba zan kuma saba ba in sha Allah" dakatawa yayi da tafiyar ya waiwayo yana dubanta. Wani murmushi ne saman fuskarsa wanda ya sani bai isa ya hanashi fita daga fuskar tasa ba. Tattausan murmushin itama ta saki sannan tadan rausaya kanta cikin alamun jin nauyin kallon da yake matan. Tamkar an saya hannu an finciko zuciyarta daga qirjinta haka ZAINAB taji. Taji na zata iya qara koda second daya a tsaye tana kallon wannan abun ba. Sai ta saki labulen da sauri ta kuma juya da sassarfa tana rufar qofa zuciyarta na sake soyewa da wani irin zafi da radadi.


           Ya za'a yi mutumin da tun daren jiya ta rasa ganin walwala koda qanqani saman fuskarsa?,hatta da abincin darensa ma bai samu ci ba,ya kuma gaya mata baijin dadi ne a haka suka kwana amma shine yake rausaya da idanu da wani irin shu'umin kallo irin haka?. Bayan ko yau da safe a tsaitsaye ya shirya,ko fuskantarta suyi magana ya kasa yi,sai baya da ya juya mata,ya gama shirinsa a gaggauce ya fice?. Ta dauka ya jima da barin gidan ma,ashe yana tare da wannan makirar baqar matar tasa.


"Allah ya bada sa'a,ya tsare mana kai,ya baka ikon nemo halak ka ciyar damu da ita,a dawo lafiya" idanunsa ya lumshe kadan,addu'arta tana masa tasiri har tsakiyar zuciyarsa. Wanann addu'ar na cikin jerin abubuwan dake faranta zuciyarsa duk safiya,ta kuma yi masa rakiya har zuwa shagonsa na kasuwa.


            Da fara'ar shimfide akan fuskarsa ya bude idanunsa yana motsa labbansa. Sai idanun nasa suka sauka akan zainab wadda ke tsaye tana numfarfashi nata idanun itama a kansa. Janye dubansa yayi daga kanta ya mayar ga RUQAYYA yana cewa


"Ameen ameen,na gode qwarai,Allah yayi albarka"


"Ameen" ta amsa masa tana shafa tafukan hannuwanta dukka biyun saman fuskarta,sannan tayi taku biyu taja baya daga kusa da zainab din,ba tare data dubeta ba saboda sanin cewa ko meye zata gani saman fuska da idanunta ba alkhairi bane,sai ta saka kai cikin gidan tana zarcewa sashenta.


"Har ka warke kenan?" Zainab ta jefa masa tambayar kai tsaye tana ci gaba da dubansa, tambayar da tazo da salo ma titsiye da kuma son qure mutum


"Dama ai ba ciwo nakeyi ba,nace dai miki bana jin dadi ne kawai,kuma kowa yana tsintar kansa a irin wannan yanayin"Ya fada yana janye dubansa daga kanta,baqinciki na lasar zuciyarsa. Ita sam kwata kwata ma kamar bata kishin kanta?,bata taba damuwa da ta sauya wasu abubuwa ba ko don ruqayya. Ruqayya din bata taba zamar mata abar kwatance ba,tafi bawa abu guda daya muhimmanci,sannan wannan abu dayan tafi bashi himma kima da darajar data zarce ace an bashi din.


"Kaji dai tsoron Allah kada ranar qiyama ka tashi da shanyayyen barin jiki wallahi.....koda yake ba laifinka bane,kaci ka sha,duk da shima asirin ai yana tadda hali ne" ta fada a zafafe sannan ta juya abinta tana komawa cikin gidan da sauri saurinta.


            Bai dakata da kallonta ba har ta bacewa ganinsa,ya sauke numfashi mai nauyi ya zura key yana qoqarin bude motarsa yana girgiza kai hadi da jan wani qaramin tsaki. Ba abinda ke yawo a idanunsa sai rigar baccin jikinta wadda duk dalli dallin maiqo ne a jikinta,abinka da abu silk jirwaye da maiqo bashi da wuyar nunawa a tattare dashi. Iya tsaiwarta a wajen,qamshin jikin ruqayya ya baje ya koma inda ya fito,ba komai a wajen sai wani yanayi dake nuni da lokaci yayi da gangar jikin mutum ta fara buqatuwa zuwa ga wanka,wankan da yayi imanin koda za'a yishi to saifa idan ya dawo ko kuma yana dab da dawowa idan an tafka sa'a a ranar. 


             Zuciyarsa cike da qiyasce qiyasce da juya al'amuran zainab ya tashi motarsa sannan ya sulale ya fice a gidan yana son daidaita nutsuwarsa kota halin qaqa.


               A nutse ta tura qofar parlor din nata da bata gama rufewa ba saboda tana sauri ta cimmasa ta gaya masa zata fita din a yau. Ko ina a gyare yake tsaf a killace,sai ka rantse bata da yaro ko guda ko kuma amarya ce,saboda sassanyan qamshin turaren wuta da burner din dake kunne take bayarwa. Gurin burner din ta isa ta kasheta,ta gama bata qamshin da takeso ta kuma biya mata buqatarta. Sassanyan qamshin da tasan saleem din yafiso a ko yaushe bata taba yarda ta rabu dashi,bata damu ba da ranar girkinta ne ko ba ita ke da girki ba,itadai burinta a ko yaushe wannan qamshin ya zamana shine abu na qarshe da ya shaqa dag wajenta don ya zama abokin tayashi tunata tsahon yinin da zaiyi gurin neman halal dinsa.


             A nutse ta buda daya daga cikin qofofin dake parlor din. Madaidaicin dakin yara ne me dauke da qananun gadaje guda uku,cikin dayan gadon yarinya ce ke kwance tana bacci. Sai data leqata ta tabbatar babu wata matsala sanann ta dawo a nutse ta rufe qofar,ta isa ga madaidaicin dining dinta me kujera hudu tana tattare plates din da ta gama breakfast. Yau duka tayi abincin karin tare da yara ta diba nata saboda tanason fita din,batason tsaiwa hada wani lokaci ya qurace mata.


           Tsaf ta gama hada plates din da cups din,zata debe ta wuce kitchen taji an banko qofar babu zato ba tsammani,abinda ya sanyata waiwayowa da sauri tana fadin


"Hasbunallahu wani'imal wakil,waye haka?"


          Kanta tsaye ba tare da shakka ko tsoro ba ta ratso cikin falon tana kallon ruqayya. Kallo na tsantsar qiyayya da tsana muraran. A kaf fadin duniya batajin akwai wata halitta da zuciyarta ta tsana bayan ita. Idanunta ta kuma saukewa akan plates da cups din dake riqe a hannun ruqayya,wannan ya sake bata tabbacin eh lallai,bayan ya tsallake breakfast din data shirya masa a nan yazo yayi karin kumallo?. 


           Ta hadiye wani abu me tauri da ya tsaye mata a wuya me mugun radadi,sannan ta watsawa ruqayya wani mummunan kallo.


"Nice nan,zuwa nayi na gaya miki abinda kika kasa ganewa,tunda baki da tsoron Allahn da zai ganar dake hakan,inason ki sani ke din baki isa komai ba kamar yadda baki isa ki rabani da saleem ba,duk yadda kike ganin bokanki tsafinki da tsubbace tsubbancenki sunayin tasiri,wallahi baki isa ki raba alaqar da Allaj ya hada ba,kuma a juri zuwa rafi da tulu da diban ruwa,dole wataran zai fashe" tana kaiwa nan ta juya a zafafe tana jin inama zai yiwu ta rufe ruqayyan da mummunan dukan da zai sanya a rasa gane ainihin halitattarta. Duk kuwa da tayi imanin babu wani kyau dake rudar saleem tattare da ruqayyan,face zallar tsafi da tsubbace tsubbace,tunda dai indai ana batu na kyan fuska da hasken farar fata,ko kusa ko alama ruqayya bata isa ta matso koda gefanta ba,wannan abun shi yake sake bata tabbaci a ko yaushe iyawa da gogewa a bun malamai da 'yan bori suke sanyawa ruqayyan ke shan gabanta a zuciyar saleem,wanda dukkan me dogon nazari da tsinkaye koda ba'a gaya masa hakan ba shi da kansa zai fahimta.


           Kasa ce mata komai ruqayya tayi face binta da kallo data ci gaba da yi har ta bacewa ganinta. Taja numfashi sosai sannan kuma ta sauke tana rausayar da kai. Koda sau daya bata taba tsaiwa ta biyewa shirmen zainab ba,amma a yau abun yayi ta'azzarar da har ta samu qwarin gwiwar shigo mata sashe?. 


              Karamin tsaki taja ganin qananun tunane tunanen matsalolin Zainab da basu taba qarewa cikin gidan ba suna neman bata mata lokaci,saita juya zuwa kitchen zuciyarta na sake fadada da tunani da mamakin halayen Zainab din. Me yasa har yanzu IDON ZUCIYARTA ya kasa budewa?,ta gaza fahimtar abinda ke gabanta a bayyane?.


            Da irin wadannan tunane tunanen ta kammala dauraye plates da cups din da wanke kowanne kwano da aka bata da abinci ya zame mata jiki a duk sanda aka gama cin abincin,ta goge ko ina da kitchen towel ta sakayo qofar. 


             Tsaftataccen killataccen bedroom dinta ta buda ta shiga,ta kalli agogo,sai ta bude wardrobe dinta ta ciro mayafinta daya dace da da A shape din atamfar dake jikinta a dan gaggauce ganin lokaci ya fara ja,tanason taje ta dawo da wuri kafin yaran su dawo daga makaranta,don ta dade da yiwa kanta alwashin muddin ba wani babban uzuri ba ta daina barwa zainab su saboda wani dalili.

          Ta dakin yaran ta biya ta dauki baby fatima dake barci ta sakata a kafada sannan ta maida lallausan mini blanket din yariyar ya lullubeta ta fito.

*FREE BOOK NE,KU SAKI JIKI KUSHA KARATU*😂😂🙌🏼🙌🏼🙌🏼

*_FOLLOW MY AREWABOOKS ACCOUNT_*

*HUGUMA*👑

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post