GASAR KOFIN BUNDESLIGA TA MATASA YAN KASA DA SHEKARA 13 A KADUNA
An gudanar da wasan karshe na Gasar Matasa ‘Yan kasa da shekara 13 na Kofin Bundesliga Kaduna wato (Under-13 Bundesliga Cup Kaduna ) makon da ya gabata, an fafata a wasan karshe tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Athletic Football Academy Kaduna da takwararta Kuso Boys Football Academy Kaduna an kuma tashi wasan Athletic na da ci 3-0 abin da ya ba ta nasarar lashe kofin Matasa ‘Yan kasa da shekara goma sha uku a karon farko, kungiyoyin Matasa 24 ne suka shiga gasar wadda aka fara a watan Augustan shekara ta 2023, wasan ya ja hankalin masoya kwallon kafa da dama a kaduna.
Tsofaffin ‘yan wasa da suka buga gasar Premier Najeriya da kuma wadanda suka buga a wajen kasar nan ne suka halarci wasan na karshen da ya gudana a filin wasa na Secret Heart da ke barakin ‘yan sanda Kaduna, Bakin na daga cikin wadanda suka mika kyaututtakan da aka lashe a wasan karshen, Kungiyar Athletic kuwa ta samu Babban kofi kuma dan wasan ta Yassir Awwal ya fi zura kwallo a gasar inda ya jefa kwallaye 7 kuma mafi kwazo a gasar ya samu kyautar takalmi da kwallo na zinare, Ita Kuma kungiyar Kuso Boys Football Academy ta samu kyautar karamin kofi.
Kawowa yanzu tagomashin Gasar Bundesliga ta kasar Jamus na bunkasa a nan Kaduna da ma arewacin Najeriya. Musamman ganin yadda irin wadannan gasa ke jawowa gasar farin jini a tsakanin Matasa, Kuma gasar ta bundesliga na kara yin fice.
Mohammed Mohammed wakilin tashar DW Hausa a Kaduna, Kuma Jakadan Bundesliga wanda ya shirya gasar Ya bayyana cewa: wannan ba shi ne na farko da aka fara shirya Gasar cin kofin Bundesliga ba a Kaduna, sai dai wannan ce gasa ta farko na Matasa ‘Yan kasa da shekara 13 da aka gudanar, Na kwashe shekara 5 ina shirya wannan gasa, sai dai mun yi tunanin farawa ta Yara wanda hakan zai karawa Yara kwarin gwiwa da kuma jawo hankalin su akan wannan gasa ta Bundesliga da ake bugawa a kasar Jamus.
Ya ci gaba da cewa Gaskiya ya ji dadin yadda matasan suka taka rawa a gasar kuma abin ya birge kowa da kowa sai dai kuma akwai bukatar Hukumar da ke shirya gasar Bundesliga wato DFL da kuma ita kanta Bundesliga da ke kasar Jamus su bada ta su gudummawar domin gasar ta fi haka, kuma hakan zai karawa Bundesliga suna a Kaduna da manyan birane irin su Kano da arewacin Najeriya baki daya.
A karshe yace nan bada jimawa ba za a fara shirye-shiryen sake yin wata gasar a cikin shekara ta 2024, kuma ana sa rai gasar za ta yi armashi sosai.