Cuta ta Ɗau Cuta Page 29

Cuta ta Ɗau Cuta Page 29

 *_Typing📲

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*

             _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na ashirin da tara_


______________Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846


Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria


Ummu khalifa 01017018846


_______________......Sunyi zama na kusan mintuna ashirin an gaggasa da ƙyau kafin ai musu rakkiya inda akace sashen amarya. Ai su Gwaggo Safina ma sai suka gagara cewa komai ganin daular duniya. Salla sukai zaman gabatarwa yayinda Khadijah ta kwanta dan zazzaɓi ne sosai a jikinta. Zuwa yanzu ma har ɗan rawar sanyi take yi. Amma tanata ƙoƙarin daurewa ta kuma ƙi sanarma kowa har sauran mutanen da suka taho a mota suka samu isowa. Anan fa gida ya sake ɗaukar harama. Ga tarin abinci iri-iri an kawo musu al'amarin dai sai sambarka kam.

      Aunty Firdausi ce ta fahimci Khadijah babu lafiya. Dan an zuba mata abinci tace ta ƙoshi. Tsoffin iyayenta suka mata caa da faɗa wai tana abu ita ba budurwa ba. Ya kamata ace ta haƙura haka ta kuma godema UBANGIJI da wannan ni'ima da yay mata. Taso matan da sukai ya tilastata yin lauma ɗaya ta abincin sai ga amai. A sannan ne Aunty Firdausi data kawo mata ɗauki taji jikinta da zafi sosai shine ta ke sanar musu bama ta da lafiya. Duk kuma sai jikinsu yay sanyi suka shiga mata sannu da jera mata kalaman lallashi. Dole wanka ta samu tayi da ruwa mai zafi ta canja kaya. Sai kuma aka shiga tunanin ina za'a samo magani, gashi su ba gama wayar ango sukai ba balle a nemosa ace amarya babu lafiya. Da kunya kuma aje wajen mahaifiyarsa daga zuwa ace mata amarya babu lafiya. Dole suka haƙura har zuwa yamma da aketa shirye-shiryen Fulani event ɗin da suka shirya zasuyi anan harabar gidan. Dan har an gama tsara ko'ina da adon fulani ma. Ana idar da sallar magrib aka kawo kayan da amarya zata saka itama.


         Sosai kayan sukaima Khadijah ƙyau tamkar ka saceta. Ga shi itama kuma ALLAH ya azurtata da gashi, dan har Aunty Firdausi na tsokanarta da ai da ansan zasuyi wannan wasan da an mata kitson fulanin itama tunda dai ta alaƙantu da su ta fannin uwa. Dariya wanda ke ɗakin sukayi kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Ita dai Khadijah bata tanka musu ba dan takanta take. Ga zazzaɓi ga fargabar tunanin kowane irin miji kuma zata tarar a yanzu. Shin shima irin Dafeeq ne ko yamafi Dafeeq abubuwan mamaki. Dan itakam a yanzu bata jin bayan mahaifinta al'amarin wani namiji na birgeta a wannan rayuwar. Kawai dai ayi sha'ani ne.

        Sai da aka yafa mata gyale aka rufe mata fuska sannan suka fito. Duk da ba ganin fuskarta akeba sai ambaton masha ALLAH dangin ango keyi ganin yanda kayan sukai matuƙar zama a jikin amaryar tasu. An zaunar da itane kusa da surukarta daketa faman jin daɗin sake ganin wannan rana da ranta, ta riƙe hannunta cikin nata. Zafi taji sosai da ya sakata ambaton “Ya Salam daughter baki da lafiya ne haka amma baku faɗa ba?”. Kasa cewa komai Khadijah tai, dan duk da bataga fuskar matar ba har yanzu wani kalar kwarjini da girmanta take ji cikin ranta. Jikinta ta ɗan saka Khadijahn tare da kiran wata ƙyaƙyƙyawar matashiya mai tsananin kamanni da ita. Gabansu ta tsugunna tana murmushi da dafa ƙafarsu su duka biyun, sai kuma ta ɗaga gyalen zata leƙa Khadijah. Harararta Mamy tayi da buge mata hannu. Tai ƴar dariya da faɗin, “Kai Mamy na ƙagarane fa naga amaryan Hamma”.

       “To bazaki gani ba”.

   Mamy ta faɗa tana hararta. Hannu ta ɗaga alamar surrender tana murmushi. “Shike nan na haƙura Mamy, amma kamar jikinta da zafi.”

        “Eh shine dalilin da yasa ma na kiraki nan ai. Yayanki basu iso ba har yanzu, inaga kiyi magana da Yafendo ayi komai a takaice Dota ta koma ciki, sannan ki nema min number doctor”.

    “Okay Mamy”.

   Ta faɗa tana miƙewa. Kamar jira tashinta babu jimawa aka wangale gate. Motace ta shigo, rashin wadatacce fili kasancewar sun mamaye harabar gidan yasa sukai parking can nesa. Kowa yasan ango ne ya iso, dan can Kano suka barsa sai yanzu yake isowa. Jirgin ƙarfe bakwai suka biyo alhmdllh kuma gashi har sun iso. Driver da yaje ɗaukarsu ne ya fara fitowa. Sai Awwal dake gefensa shima ya fito. Shiko yana baya bayansa jingine da kujera idanunsa a lumshe. A kallo ɗaya zaka fahimci a gajiye yake. Dan koda driver ya buɗe masa motar ya ɓata kusan minti ɗaya kafin ya fito. Cikin rashin hayaniyar nan tasa yacema drivern “Thanks you Baba. Mun hanaka barci ko”.

     Murmushi Baba yay da faɗin, “A haba Alhaji ai yima kaine. Sannunku da zuwa dai, ALLAH kuma ya sanya alkairi a cikin wannan aure. Yasa yanda muka taru anan baɗi i war haka muna nan muna shagalin suna kuma”.

        Awwal ne ya amsa da amin yana ƙumshe dariya. Shiko ya ɗan murmusa kawai batare da yace komai ba sai dai a zuciyarsa ya amsa da Amin. Dan sosai yake son yara shima, kawai dai ana ganin kamar bai damu bane saboda bai cika yawan furtawa ba. Idanunsa ya kai inda ake taron, hankalin wasu duk na garesu ne, yayinda wasu kuma ke hidimarsu batare da sun farga da su ba. Tunanin ta yanda zai shige sashensa batare da wani ya tsaida shi ba yake. Sai dai bai kai ga samo mafitarba ma ƴan uwa suka fara zagayesa ana masa sannu da zuwa da jera masa kirarin ango ango kasha ƙamshi. Kamar yanda ya saba ne, murmushi kawai yake musu a taƙaice. Ganin suna neman cika wajen ya zare jikinsa ya gudu ta baya zuwa sashensa dake manne dana amarya. Sai dai da yake akwai ƙofa ta gaba da baya da basai  dole yabi ta cikin falon Khadijahn ba yasa zaka iya ɗauka ma daban-daban ne. Shigewarsa babu jimawa Mammy tasa aka maida Khadijah ciki dan rawar sanyi take yi. An cigaba da gudanar da shagali Noor kuma taje ta sanar ma Yayanta amarya bata da lafiya a kira Doctor. Fitowarsa kenan daga wanka sallamarta ya sashi zira jallabiyya ya fito falon. Agogo ya ɗan kalla sai kuma ya dubi ƙanwar tasa ɗaya tilo a duniya. “Amma miyasa tun ɗazun k baki kirashi, yanzu fa kusan 10 ake tafiya. Sannan kun zo da ita a wannan sanyin ita da bata da lafiya kuma”.

       “Sorry Hamma Ab. Ai ba'asan bata da lafiya bane fa sai yanzu Mamy ta gane. Kuma yanzu haka ma an maidata ciki. Na kuma kira Doctor ɗin bai ɗauka bane maybe baya kusa”. Baice komai ba face ƙoƙarin sarrafa wayar hannunsa da ya ɗauka. Inda ya fito ya koma yana kai wayar kunnesa da yima Noor alamar taje kawai...


     Noor na zaune a bakin gadon da Khadijah ke kwance ƙudundune cikin bargo kiran Yayanta ya shigo mata. Tana ɗauka umarnin kawo Khadijah kawai ya bata sashensa ya yanke kiran. Koda ta sanarma su Aunty Firdausi cewar Hammanta yace ta raka Khadijah likita yazo babu wanda yay yinƙurin hanata. Sai ma sake birgesu da take dan Noor akwai surutu, tun ɗazun hira take musu abinta kamar wata ƙaramar yarinya. Khadijah ce ma taso taɗan turje Inna Zulai ta fara mata faɗa, dole ta miƙe Noor ɗin ta kama mata hannu suka fice tana tafiya cikin ƙarfin hali dan jikinta sai rawar sanyi take.

        A hankali ya ɗago idanunsa dake kan tv yana sauraren hirar da doctor ke masa ya zubama ƙofar tare da amsa sallamar Noor akan lips. Khadijah da ke tafiya a hankali ya zubama idanu har suka iso gabansa, sosai tai masa ƙyau a cikin kayan fulanin dan ma akwai mayafi jikinta. Kai tsaye Noor ta zaunar da ita a kujerar 1sitter da ke gefensa na dama. Itako da dama da rabin fuskarta gyale ya rufe bata yarda tama kalli ko ina ba sai sassanyan ƙamshin turaren wuta dana fresheners dana jikinsa harma dana doctor ke rige-rigen shigar mata hanci. Noor na zaunar da ita ta naɗe ƙafafunta zuwa saman kujerar ta wani irin dunƙule waje ɗaya kamar ƴar mage. Wani irin fisgarsa yanayin nata ke yi, amma sai ya dake tamkar babu komai tattare da shi yama ɗauke kansa ya maida ga television. Doctor ne ya taso inda take yana jera mata sannu. Kanta kawai ta gyaɗa masa tana ƙoƙarin rufe ƙafarta da ƙyau da mayafin jikin nata. Tambaya doctor ya fara mata tana bashi amsa, yanayi yana ɗan rubutu harya kammala. Dubansa ya kai ga Abaan ɗin cikin girmamawa ya ce, “Sir tana buƙatar abinci haka mai ɗan ruwa-ruwa dan akwai yunwa tare da ita. Sai kuma ƴar damuwa nake gani da malleria haka. Taci wani abun ɗin sai tasha magungunan nan a kuma mata wannan allurar in sha ALLAHU zuwa safiya zata ware”.

     Cike da gamsuwa Abaan ya dubi Noor. “Ki sama mata tea”.

    Amsa masa tai da “To Hamma” tana nufar ƙofar fita. Babu jimawa sai gata da kofin tea daketa turiri. Yanda ta fita ta barsu haka ta dawo ta samesu musamman ma Khadijah dake cure a cikin kujera. Tea ɗin ta miƙama masa tana danne dariya, ya ɗan zuba mata ido tamkar bai gane mi take nufi ba. A ɗan shagwaɓe ta ce, “Hamma zanje na kawo maka abinci ne kaima fa in ji Mamy”. Amsar kofin yay da bata amsa a taƙaice. “No ni am ok bazanci komai ba”.

      “Amma Hamma Mamy zatai faɗa, bari dai ko madara mai zafi na amso maka”. Tai maganar tana ficewa wuff batare da jiran amsarshi ba. Kansa kawai ya ɗan girgiza dan shi kam bai san randa Noor zatayi hankali ba kuma. Da'ace ALLAH baima mijinta rasuwa ba da yanzu ƙilama tanada ya ra biyu itama. Ture lamarin Noor yay gefe yana mai maida hankalinsa kan Khadijah, dai-dai nan shima doctor ya miƙe tare da masa sallama ya wuce. 

      Cikin alamun gajiya dake tattare da shi ya maida hankalinsa ga Khadijah bayan fitar doctor. Kamar wanda baya son yin magana ya furta, “Zaki iya tasowa nan?”.

     Jitai kamar ta sharesa, amma kuma sai ta dai kaɗa masa kai saboda tuno nasihar Baba, sannan shi a karan kansa yana da wani girma da kima da hatta a cikin muryarsa zaka iya jin hakan. Dan haka ta miƙe a hankali bayan kamar minti ɗaya. Yanda take ɗan yin kamar layi ya sashi kai hannu ya riƙo nata hannun. Sosai zafin zazzaɓin jikinta ya ratsa nashi hannun har sai da ya ɗan yamutsa fuska. Itako jitai tana neman daburcewa, domin kuwa ta sama ranta wani abu daban akan maza. A gefensa ya zaunar da ita kusa da shi gab dan a 2sitter yake zaune. Da sauri ta ɗan matsar da jikinta tana sake naɗewa gefe sosai dan sanyi take ji, shima kuma ya shaida hakan saboda rawar sanyi da take kaɗan-kaɗan. Idanu ya ɗan zuba mata na kusan sakan ashirin, kafin ya janye a kasalance tare da kai hannu ya ja mayafin ta dake rufe da fuskarta ruff zuwa ƙasa. Kaɗan ya ɗan duƙo gareta yana miƙa mata kofin shayin. Sai hakan ya basu damar samun kusanci da juna, har kowa na iya jin ƙamshin turaren ɗan uwansa sosai. Sosai ta wani rumtse idanunta da yamutse fuska kamar mai shirin sakin kuka ta yanda har shi sai da ya zubama black beauty face ɗin nata ido sosai. 

       “Sorry, ki daure kisha shayin ko kaɗanne sai ki sha maganin”.

   Kanta ta girgiza masa hawayen da take riƙewa tun ɗazun na rige-rigen silalowa. 

      “Uhhm-Uhmm! Shi dama kukan kai amarya baya ƙarewa?”. Ya faɗa a hankali cikin tausasawa da ƴar tsokana. Baki ta ɗan tura kaɗan da ƙoƙarin jan mayafinta zata sake rufe fuskar. Hannunta ya riƙe shima yana ɗan murmushi, a hankali ya sake furta, “Pleasseee!”. 

  Yamutsawa tsigar jikinta tai saboda yanda ya kirayi Please ɗin a wani can ƙasan maƙoshi tamkar mai raɗa ko yaro da ke jin ɗan shwagwaɓan nan nason yima Mamansa wayo ta bashi abu. Bata da zaɓin daya wuce amsa kawai, dan ji take wani abu na mata kai-kawo acikin hannunta daya riƙe. Hannun nata ya saki tare da sake jan gyalan saman kafaɗarta sannan ya ɗan matsar da jikinsa yanda yake da ya zauna da ƙyau. Saboda ya bata damar shan shayin sai ma ya maida hankalinsa ga tv. Karo na farko ta ɗan saci kallonsa, ganin ba ita yake kallo ba takai kofin bakinta dan gaskiyar Doctor ne yunwa take ji. Rabonta da abincin kwarai tun jiya da safe a gida kano.........✍️
*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥


*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_


*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*


*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*


*TSUTSAR NAMA Billynabdul*


*GUDUN K'ADDARA Huguma*


*AMEENATU Mamuhghee*_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*_MARABA  LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post