Cuta ta Ɗau Cuta Page 38 by Bilyn Abdull ce


Health College

Cuta ta Ɗau Cuta Page 38 by Bilyn Abdull ce

Zafafa Biyar 2024

 *_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*

             _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na talatin ta takwas_

*_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._*

*_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_*

*_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_*



*_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_*



*_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_*



_Littatafan sune kamar haka 👇🏻_.




   *_KWANKWASON JIMINA....._*

        _(NA MSS XOXO)_



*_GUDUN ƘADDARA_*

         _( NA SAFIYYA HUGUMA)_



*_TSUSTAR NAMA....._*

          _(NA BILYN ABDULL)_



*_AMEENATU_*

           _(NA  MAMU GEE)_





_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥


_________



........Murmushi Nadwa tayi, sai kuma ta gyara kwanciya a jikin Doctor Giɗaɗo tana faɗin, “Ni dai shawara zan baki kamar yanda na saba. Kainaat ki nema iyayenki ki koma garesu, dan in dai Abaan ne ya miki nisa, kamar yanda yaƙi yarda da tayin aurena da naketa jelan masa, kema wlhy sai dai ki rasa dan ya miki nisa. Nisa irin na tsakanin samaniya da ƙasa. Shiyyasa nake ta fargar dake. A yanzu haka yana tare da ƙyaƙyƙyawar matarsa a gidansa cikin aminci da kwanciyar hankali. Dan haka ki riƙe shuga boy ɗinki yafi miki. Nasan zakiyita tunanin mune kuwa. Humm mune ɗin dai, a tunaninki bazan taɓa jin kishi a raina ba ne. Kefa ba ƴar kowan kowa bace. Mune mika ɗauke ki muka suturtaki da sutura ta ƙawa, muka kaiki ƙasar waje kikai ilimin da ya fiddoki har irinsu Abaan ɗin suka kalleki. Saboda mu ahalinsa suka yarda ya aureki ma. A tunaninki banda zuciyar da zanji a raina ni ya kamata na samu wannan bake ba. Nice fa keda komai ɗin, amma sai kika koma komai a kaina. Shiyyasa nai alƙawarin sai kin gama tattara mana mu kuma muji daɗin, dan na lura sam ke ba ƴar halak bace ba baki san halacci ba. Akwai fa lokacin da har gwadaki nai nace ki aramin 10mil zan fara Business amma matar nan kika nuna min baki da shi, ashe ƙarya kikeyi sai daga baya na gane hakan. Hummm kar dai na cikaki da surutu maybe idan kin haihu zan zo suna, ko in matar Abaan ta haihu nazo miki barka, a gaida angon jego Dafeeq byeeeee!🖖”.

      Ba Kainaat ba hatta shi uban gayyar jikinsa kakkarwa yake yi. Jin hajijiya na neman yadda shi ya wani zube a kujera. Dai-dai nan Kainaat ta fita gabansa. A bazata ta ɗaukesa da wani kalar wawan mari irin na bazatan nan. Domin kuwa bai tsammani zuwansa ba sai saukarsa yaji. A gigice ya ɗago, ta kuma sake ɗaukesa da wani haggu da dama. Rikicewa yay har kunnensa na masa wani dommmm.

     Nuna shi tai cikin fashewa da kuka ta ce, “Matsiyaci ɗan mage baka daɗin goyo. Azzalumi tsinanne, ashe da kai ma aka shirya komai” ta sake kai masa wani dukan. Gam ya riƙe hannunta yana huci, yanda nata jikin ke tsuma haka nashi keyi. Cikin rufewar idanu ya shiga kaimata duka tako ina. Ƙarfin mace da namiji ba ɗaya ba koda ace ta girmesa. Amma duk da haka tayi ƙoƙari itama ba kamar Khadijah ba. Dan duk abinda taci karo da shi wawusowa take tana ƙwala masa. Cikin ƙanƙanin lokaci sukaima kansu jina-jina. Sai da maƙwafta suka shigo aka rabasu anata mamakin yaushe ma suka zo gidan tunda ansan yanzu Dafeeq ɗin yayima gidan ƙaura. Tuni kuma an garzaya an sanarma Baba Hakimi abinda ke faruwa.

     Yanda suka jigata juna da raunika yasa dole suka nufi asibiti da su. Baba Hakimi kuma ya hana a sallamesu a ranar dan yamma tayi sosai sai washe gari. Da farko daya tambayesu abinda ya haɗasu shiru sukayi, sai dai bafade ya musu tsawa sannan Kainaat ta shiga zayyane komai tana kuka. Dan a ganinta mafitar da zata rabu da Dafeeq ɗin ce ma tazo mata. Sai dai me, maimakon samun yanda take ai nasiha Baba Hakimi ya musu. Batare daya kawo komai a ransa ba ya ce, “Kai Dafeeq in ma Khadijah ce ka kwantar da hankalinka. Dan yanzu haka tana gidan mijinta tai aurenta. Garama ka riƙe matarka ku zauna lafiya ku kuma ɗauki abinda ya faru matsayin ƙaddara. Dan kai da ita ɗin duk CUTA TA ƊAU CUTA ce kawai”.

        Tashin hankali kenan. Dan yanda Dafeeq ya miƙe zambar yana ɗura ashariya sai ma ka ɗauka ya haukace. Fadawa zasu saka a masa duka Baba Hakimi ya hana. Sai dai ya saka an fiddashi a fadar. Aiko a ɗimauce ya nufi gida ya fara haɗa kayansa sai Kano. Wannan al'amari ya sake haukatar da Kainaat, dan duk wanda ya ganta a ranar sai ta bashi tausayi. Kamar ba Kainaat ɗin nan ƴar gayu ƴar ƙwalisa mai ji da kuɗaɗe a gidan sanyi ba. Ta harmutse, ta hargitse, ta gama fita a hayyacinta abun ba'a magana....


       A haukace Dafeeq ya iso Kano, sai dai kuma ya samu amsar da yaji inama bai zo ba. Dan ta tabbata dai Khadijah tayi aure. Yanda ake zuzuta masa labarin ta auri wani babban mutum mai kuɗi a Abuja ya nema saka zuciyarsa bugawa. Sai ga Dafeeq da kwanciya ciwo rejiff. Mamansa taso wannan karon ma taje tayi tujara a gidan su Khadijah baban Dafeeq ɗin ya taka mata birki da tuna mata gargaɗin d.p.o, dole ta haƙura ta cigaba da tsine-tsinenta a cikin gida kawai.

     Washe gari sai ga Kainaat itama ta iso Kanon kamar sabuwar kamu a hauka. Ta tada musu hankali akan sai fa Dafeeq ya saketa. Babansa yace idan har ya saketa sai ya saki mamarsa shima ya kuma tsine masa. Ai sune dai-dai da juna dan haka su cigaba da kasancewa a tare. Dan kuwa a haukar Kainaat ta kwancema iyayen Dafeeq ɗin komai ne wai dan su sakashi ya saketa. Sai kuma ta ɗaure kanta da kanta. Da farko itama Maman Dafeeq ta ce ya saketa jin kuɗi dai babu su. Sai dai furucin mijinta ya gigitata. Sai kuma cikin da Ƙainaat ke ɗauke da shi ya sake saka jikinta yin sanyi, dan duk duniya kuma babu abinda take buƙatar gani a yanzu sama da jinin Dafeeq ɗin. Wannan shine sanadin zaman Kainaat da Dafeeq a Kano dan su duka biyun ciwo ya kwantar dasu. Ita laulayi shi jiyyar zuciyar rasa Khadijah. Akwai randa harda su aman jini, sai da aka garzaya da shi asibiti. Kusan satinsa uku sannan aka sallamosu. Itama jikin Kainaat ya rikice, nanma suka garzaya asibiti, sai ake sanar musu ai cikinta a bayan mahaifa yake, dole sai sun lura da bata kulawa har lokacin haihuwa a ciresa ta hanyar cs dan yana cikin ƙoshin lafiya. Ina kainaat ta birkice musu akan sai dai fa a cire ciki, dan wata ƙawarta data samu irin hakan cire mata akayi tun yana wata uku. Anta tafka bala'i Dafeeq da Mamarsa sukace bazasu yarda ba, daga ƙarshe dai sai da aka dangane da police station, acan ne aka musu iyaka. Babu yanda zatayi dole ta haƙura dan bata da gurin zuwa yanzu, saboda satinta ɗaya da zuwa Baba Hakimi ya lodo kayansu a mota da ƴan rakiya aka kawo Kano. Acewarsa ya amshi gidansa Dafeeq ya cigaba da zama a gidansu. Dole fa aka share musu ɗakin ajiye-ajiye na gidan suke zaune anan. Idan fatara ta ishesu a zari wannan a siyar, a cire wancan a siyar, wataran ma Maman Dafeeq ɗin ke sata ta sayar basu sani ba. Dama dai kayan Ƙainaat ne masu daraja a ciki. Ga faɗa kullum kamar kaji. Yanzu basa jin nauyin ɗaga hannuwa su shararama juna mari. Saboda yana marinta itama take ware hannu ta sauke masa. Sai in zasu harƙume dambe ne Babansa ya tsawatar tare da tuna musu lalurar dake jikin Kainaat ɗin....

      __________★


         Yau ta kasance weekend, dan haka tun kusan sha biyu Abaan da Khadijah suka fita domin ɗan hutama ransu. Tunda aka kawota bayan asibiti babu inda ta taɓa zuwa sai yau. Yawo yayi da ita sosai wajaje daban-daban da suka nema juye kan Khadijah ta sake tabbatar da ganin Abuja yafi jinta ma. Dan wani wajen ma idan suka shiga ita mantawa take Nigeria ce fa. Bata wani ɓoyewa taita santi abunta da nuna al'ajabinta. Shiko Abaan na mata dariya da tsokanarta wai baƙauya. Sunsha hotuna, dan duk inda akeje cewa take suyi hoto dan ta nuna ma su Ni'ima. Tun yana tayata shikam harya gaji ya miƙa mata wayar tasa ta cigaba da ɗauke-ɗaukenta. Sai yamma lis suka dawo gida a gajiye. Washe gari kuma yace ta shirya zai fara koya mata mota. Jitai kamar ta suma a zaune dan sai da ya taɓata tai firgigit. Muryarta har rawa take ta ce, “Hamma mota fa?”.

      Murmushi ya sakar mata mai sanyi, sai kuma a hankali ya kwanto da kansa saman cinyarta. Hannunta ya kamo yasa a ƙirjinsa ya rungume. “Ko jirgi kike son koya zan kai ki a koya miki na sayo miki shi Khadijah. Kin san waye mijinki kuwa. K dai kawai kiyita bani farin ciki wlhy zan zame miki fiye da bawa. Ba koyan mota kawai ba, nan da sati uku zaki fara zana waec ɗinki in sha ALLAHU. Dan ina son ki samu kwalin Sakandire sai mu tattara inamu-inamu mu koma abroad ki cigaba da karatunki har sai kin kammala zamu dawo. In sha ALLAHU sai kin gogema iyayenki hawayen da kika sakasu zubarwa a shekarun baya. Sai kin zama abar kwatance. Yanda mutane da dangi suka dinga jifanki da ALLAH wadai a shekarun baya sai sun koma sanya miki albarka. Yaron nan daya zaluntar min ke sai kin koma kece mai taimakonsa a rayuwa. Fatana ni dai ki zama mai gaskiya, mai amana, mai kuma jajircewa......”

      A hankali hawayen da suke kwaranyo mata suka shiga ɗiga a kan fuskarsa. Murmushi ya saki tare da kai hannu ya share mata su. Sai kwai ta rungume kansa ta saki kukan mai ƙarfi. Tashi yay camak ya ɗauketa yay bedroom da kayarsa. Daga haka labarin ya canja salo...


      Kamar yanda yay alƙawari ya fara koya mata mota da kansa. Sai dai a wajen koyar motar nan ma babu abinda ake sai shan soyayya ziryan. Komai suna yinsa cike da farin ciki da nishaɗi ne. Cikin sati guda ya fara sakar mata steering. Khadijah mai ƙwazo ce tun acan baya. Kawai taso zubar da damarta ne a dalilin busar shaiɗan data Dafeeq. Sai dai yanzu kam alhmdllh. Lokacin da ta cika sati biyu ai sai dai ace Alhamdullah. Bata motar ake ta fita ita kaɗai ma. Sai dai abinda bata sani ba Abaan na biye da ita a ɓoye. Dan shi dai a tsorace yake. Sai da ya tabbatar komai Alhmdllh sannan ya iya dinga daina binta. A haka ta fara exam. Abinka da makarantar masu kuɗi komai ya riga ya mata da kansa, sai abinda ba'a rasaba ne ya kaita ta ƙaƙƙarasa yi kafin farawar, ya kuma dage da koya mata abubuwa shi da Noor. Kai har Mamy ba'a bari a baya ba ta bada tata gudunmawar. A haka dai ta fara jarabawar, cikin amincin ALLAH kuma suka kammala lafiya. Tana cigaba da zuwa ganin doctor duk sati, dan gaskiya zubar mata da ciki da Dafeeq ya dingayi da abinda suka saka mata a jiki yaso mata illa. Amma Alhmdllh da yake akwai kuɗi yanzu kam Abaan ya dage sosai. Sai dai bai taɓa sanar mata abinda Doctor ɗin ya faɗa mata game da matsalar da taso samu ba a mahaifarta. Dan har ɗan ƙaramin aiki sukai mata batare da an warware mata al'amarin kai tsaye ba. Ya kuma gargaɗi likitan akan kada ya taɓa sanar mata komai ya riga ya wuce kawai.


      Watansu uku da aure ya ɗauketa suka nufi Kano. Inda ta samu iyayenta cikin ƙoshin lafiya da wadatar zuci. Ga gidansu yasha gyara sosai kamar bashi ba. Babanta na sake samun kulawa ta musamman ashe har Egypt Abaan ya kaisa amma yace kar a faɗa mata. Sai da suka zo ɗin nan ta sani a bakin Jamila. An buɗema Baba ƙaton store na shinkafa a bakin titi. Aiko bawan ALLAH yay fes da shi kamar bashi ba, duk da dai har yanzu yana ɗan tafiya da sanda haka dan ƙafarsa na shagiɗawa. Jitai kima da darajar Abaan da mahaifiyarsa ya sake girma a idonta. Kai ita kam bata san mizata sakakankama mutanen nan da shi ba a rayuwa.

     Tururuwa matan anguwa da yara da ƴammata suka dingayi ganinta. Dan tuni anguwa ta ɗauka Khadijah tazo a wata mahaukaciyar mota. Dan tsiyar da Abaan yay musu ita kaɗai ya bari ta shiga anguwar tasu a wata zazzafar mota yace mata zuwa dare zai ƙaraso dan yana da meeting a gidan gwamnati. Aifa ta janyo magana, dan har gidan su Dafeeq aka kai ma mamarsa labari. Sai ta dinga koro mutane da zagin cin mutunci da tsinuwa. Mutane kam nata mata dariya sun maidata mahaikaciya. Alokacin Dafeeq da Ƙainaat na asibiti sun je ganin doctor dan sam bata jin daɗi, cikin na matuƙar wahalar da rayuwarta, gashi a bayan mahaifa, ta kumbura matuƙa babu ƙyan gani. Koda suka dawo kuma dare yayi, Mama ta katsatstsare dan kar Dafeeq yaji labarin Khadijah tazo. Washe gari da asuban fari ta sashi gaba suka tafi wani ƙauye wai amsar magani, sai da tai yanda tai suka kwana acan. Sai washe gari suka dawo a randa su Khadijah suka wuce.........✍️



*_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._*



*_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_*



*_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_*



*_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_*



*_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_*



_Littatafan sune kamar haka 👇🏻_.




   *_KWANKWASON JIMINA....._*

        _(NA MSS XOXO)_



*_GUDUN ƘADDARA_*

         _( NA SAFIYYA HUGUMA)_



*_TSUSTAR NAMA....._*

          _(NA BILYN ABDULL)_



*_AMEENATU_*

           _(NA  MAMU GEE)_





_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post