Cuta ta Ɗau Cuta Page 39 by Bilyn Abdull ce

Cuta ta Ɗau Cuta Page 39 by Bilyn Abdull ce

 

Sababbin Zafafa Biyar Hausa Novels 2024

*_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*

             _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na talatin da tara_

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR MUNA SAYAR D KAYAN KITCHEN D FURNITURES N TURKEY D ABAYA AKAN FARASHIN SARI DA CAPSULES MASU KYAU D INGANCI.

___________


........Rayuwa taima ango Abaan daɗi fiye da yanda yay hasashe. Hakama amarya Khadijah dake samun kulawa a garesa da ahalinsa. Idan kaje gidan dolene rayuwar cikinsa ta burgeka musamman yanda kowa ke girmama ɗan uwansa. Tsakanin ango da amarya kam ai ba'a cewa komai. Dan soyayya ce mai tsafta da tarin birgewa, tuni Abaan ya kaɓar da ƴar sauran kunyar Khadijah musamman idan an shiga daga ciki. Yanda soyayyarta tai tasiri garesa haka itama tashi tuni ta mata shigar sauri saboda nagartattun halayensa. Bayan sun dawo Kano ya bar ƙasar. Ya barta da damuwar rashinsa kusa da kaɗaici, sauƙinta ma ta koma zuwa wata babbar islamiyya anan kusa da su. Sashenta kawai masu aiki ke gyarawa, nasa kuwa ita da kanta take wannan aikin batare da jin gajiyawa ko ƙosawa ba kullum duk da baya nan. Takan shiga sashen Mamy susha hirarsu, dan Noor ma tana zuwa aiki. Satinsa biyu ya dawo aka cigaba daga inda aka tsaya. Ita ke tsaye kan hidimar mijinta da safe. Hakama idan lokacin ɗora abincin rana yayi tayi musu da kanta dan in har Abaan na Abuja zuwa ake a amsar masa abincin rana daga gida akai masa office. Dan haka nan ma ta riƙe ragamar girkin rana. Bana safe da rana kawai ba, na daren ma ita ke shirya musu abincin mara nauyi, sannan ta koma sashensu tarbar mijinta duk da in har ya shigo gidan ƙa'idarsa ce sai yazo ya fara gaishe da mahaifiyarsa sannan, hakama idan zai fita sai yazo ya mata bankwana. Idan sun kamala ƴan hidimominsu kamar taimaka masa yay wanka da sauransu zai wuce massalaci har sai anyi isha'i ya dawo. Sukan nufi sashen Mamy ita da shi suyi dinner acan. Daga haka ai zaman hira. Goma nayi Mamy ke korosu, wani lokacin ma tara da rabi tace suje sashensu su ƙarasa hirar acan tagode. Noor kan dinga musu dariya dan su sunfi son ayi hirar anan. Saboda Mamy mace ce data san kanta. Dolene ma idan ka zauna da ita komanta ya dinga birgeka. A koda yaushe cikin gyara Khadijah take batare da Khadijahn ta farga ba. Dan ita dai sai dai kawai a bata abu ace ta shanye ko ta ci. Ita kuma saboda biyayya bazata taɓa tambayar Mamyn minene wannan ba balle ta musa sha kota zargi wani abu. Halayen Khadijahn na sake saka ƙaunarta a zuciyar mijinta da mahaifiyarsa harma da ƙanwarsa ɗaya tilo data zame mata ƙawa a yanzu duk da ta girmeta.

      A wannan hali kwanci tashi Khadijah da Abaan suka cika wata goma da aure. Akan samu sassaucin yawan faɗa ko rigima ta ma'auratan zamani, ba komai yasa hakan ba sai kasancewar su su duka biyun masu haƙuri ne. Sannan Abaan ya girmi Khadijah nesa ba kusa ba, takanyi abu da yawa yay masa kallon ƙuruciyace kawai ya share. Wanda kuma ya zama dole yay magana a kansa sai ya zaunar da ita cikin nasiha ya ankarar da ita kaza ba dai-dai bane kazane dai-dai. Hakan da yake na ƙara saka girmansa da kimarsa a wajen Khadijahn, dan takanyi ƙoƙarin ganin ta kiyaye duk abinda zai ɓata masa rai. Takanyi waya da iyayenta a wayarsa, dan ita har yanzu bata da waya, bai siya mataba ba kuma ta taɓa masa magana ko nuna ta damu da son a sai mata ba duk da tana buƙatar hakan. Ko magana yake son yi da ita idan yana office sai dai ya kira wayar Mamy yace ta bata dan yasan da rana suna a tare idan bataje islamiyya ba. Idan kuma zatai waya da ko su Zuhrah ne tashin take amsa kota Mamy ko Noor. Bata taɓa nuna damuwar hakan ba garesa ko waninsa ko taji a ranta ana raina mata wayo. Sai dai ma takan ɗan ji kunyar cewa su ara mata tai wayarne wasu lokutan, koda tana da buƙata sai kawai ta haƙura. 

      Abinda Khadijah bata sani ba Abaan na gwadata ne kawai, dan Mamy tasha masa faɗan ya saya mata waya sai yace tayi haƙuri zai saya akwai abinda yake yi ne. Mamy tasan halinsa, dan haka ta saka masa ido kawai akan hakan. Dan daga baya itama sai ta fahimci dalilinsa akan ƙin sayen wayar. Ana cikin haka yay tafiya waje ya barta bata jin daɗin jikinta, takuma ƙi yarda suje asibiti, to anan ne fa shima abin ya fara cin ransa. Dan da rana dai yakan kira su Mamy su bata. Da dare kam yana son waya da matar tasa ko zaiji raguwar kewarta da lafiyarta babu dama. Da farko ya fara saka Noor ta bata tata, sai kuma nata saurayin yayta kira, wani lokacin kuma sanda shi zai kira saurayin Noor ya riga ya kira sai hakan ya ƙona masa rai. Ai fa babu arziƙi kwanansa goma sha biyu sai gashi ya dawo. Sam babu wanda yama san da dawowar tasa, dan ita Khadijah ma ranar jikinta ya takura mata ko sashen Mamy bataje hira ba, tadai je ta gaisheta ta dawo sashenta ta kwanta.

    Cikin barci sama-sama take jin ƙamshin turarensa na hawar mata kai. Idanunta da sukai matuƙar nauyin barci ta buɗe a hankali. Lumshewa ta sake yi, sai kuma ta sake buɗewa domin tabbatar da shi ɗinne ko mafarkin data saba take yi. Shi ɗinne dai ba mafarkin take ba. Tashi tai da sauri, sai dai mi, ƙamshin turarensa na bugarta a guje ta nufi toilet sai amai. Hankalinsa ya tashi, ya taimaka mata ta gyara jikinta suka fito yana mata faɗan ya akai take barin ƙofa buɗe sauro na shigowa, dan shi zatonsa malleria ce, tunda yaga sanda aka kawota haka taita amai tana zazzaɓi. Ita dai batace da shi komai ba, sai faman toshe hanci ma takeyi.

        Karon farko Mamy tazo sashensu tunda Khadijah tazo gidan, itace ta fahimci halin da Khadijahn ke ciki, tai mata tambayar ƙamshin miye bata so. Da ƙyar ta sanar musu turaren jikin Hamma. Idanu sosai ya waro waje, mi Noor zatayi inba dariya ba. Har sai da ya harareta sannan ya miƙe fuuu ya fita shi yaji haushi. Ita kanta Mamy sai da tai murmushi. Koda ya fitan ma Khadijah ta kasa sukuni, dan tace har lokacin tana jin ƙamshin. Dole aka haɗa turaren wuta da yawa Noor ta saka ako ina. Sai da aka ɗauki lokaci ga ac sannan tace ta daina ji, lokacin kuma Mamy ta kira Abaan da tunda ya tafi sashensa bai dawo ba tace yay kiran doctor.


       Duk wanda ke a cikin wannan ahali yau kasan yana cike da ɗunbin farin ciki mara misali, dan hatta doctor daya tabbatar da ciki a jikin Khadijah yasha ƙyaututtuka. Tuni Abaan ya rungume Khadijah a gaban Mamy babu ko kunya, turaren ko da tace bata son ƙamshinsa duk da tsadarsa haka ya ɗauka ya bama Awwal shi, yace an bar sakawa. Sai ya koma idan ma zai saka turare sai ta zaɓi wanda ƙamshin yay mata koda shi baya so kuwa. A haka ta cigaba da rainon cikinta da kulawa, dan kowa tattalinta yake kamar ƙwai a cokali a gidan. Batun tafiya karatunta kuwa dole ya tsaya dan boss yace sai ta haihu kuma. Bata damu ba, dan abinda mijinta ke so shi take so itama. 

        Cikinta na wata shida Ni'ima ta haihu. Da farko dai Abaan yaso ya hana zuwan, amma ta saka masa rigima dan tunda sukai aure zuwanta ɗaya Kano bata sake ba. Sai dai Auta da Jamila sun zo mata hutu sau biyu, yanzu haka ma so take jamilar ta dawo kusa da ita saboda yanayin cikinta. Sai da Mamy tasa baki ya yarda taje jin cewa har Mamy zata je. Haka suka ɗunguma sai Kano ta dabo.  

       Sun sami tarba ta mutunci da girmamawa. Dan Mama tata roƙon Mamy akan su sauka anan, hakan kuwa akayi. Kasancewar ana gobe suna suka je washe gari tunda safe suka nufi gidan Ni'ima mai jego, inda suka sami itama Zuhrah na fama da nata cikin, dan tsakaninsu da Khadijah kaɗan ne. Babu zato sai ga Abaan, ta dinga harararsa dan bata san zai zo ba. Shiko yana mata dariya ƙasa-ƙasa dan yana tare da su Adams ne da wasu abokansu. Yaro kuma an masa takwara da Abaan ɗin ne. Zokaga murna wajen Khadijah da Abaan. Aiko yaron nan yasha ƙyautuka. Suna ya ƙayatar sosai, Abaan yasa rigimar ranar zai koma da matarsa har sai da Mamy ta tsawatar masa. Aiko yace in dai bazata koma Abuja ranar ba shima bazai koma ba yana nan Kano har sai sanda zasu tafi.  Mamy tace yaje ya ƙarata.

        Kwanakinsu uku a Kano sukai shirin dawowa Abuja. Kusan sha ɗaya na safe Khadijah ta shirya dan zuwa ta gaida wani kawunsu dake can ƙasan su. Hakan yasa Abaan da yazo yace tazo ya kaita. Dama tare suke da Noor. Tafe suke a mota cike da nishaɗi suna hirarsu. Da wani kalar sauri Abaan ya taka birki dan kaɗan ya rage ya buge wata yamutsatstsiyar mata goye da yarinya a baya ta fito a wani gida a guje da icce a hannu tana ɗura ashar manya-manyan. A harzuƙe ya taka birki, sai dai kafin yay magana sai ga wani mutum shima ya fito da nasa iccen a hannu yana zagin shima na rashin mutunci. Matar ya wulwuloma iccen, saura kaɗan akan Khadijah da ke ta saitinsu tayi zuru tana kallonsu kamar mai son tuna ina ta sonsu.

     Tofa, an taɓo abinda Abaan bazai iya haƙuri ba, tuni ya ɓalle murfin mota Noor na take masa baya. Amma mi yana fitowar ya iso gabansu da nufi masifa yaja yay turuss kamar yanda matar nan mai goyo tai tsaiwar sojan badakkare ta zuba masa ido kamar zata suma. Dan namijin har ya ƙaraso gareta zai wanka mata mari sai kuma shima ya tsaya cak jin cikin wata irin murya mai rawa da karkarwa ta ambaci “ABAAN!!”.

       Kasa amsa mata Abaan yayi, dan shi ƙoƙarin tuno ina yasan fuskar tata ma yake amma ya kasa. Sai da Khadijah data kasa haƙuri ta fito da sassarfa. Kainaat ta nuna sai kuma ta kalli Dafeeq da ya wani mugun rama yay rakwaf a tsaye kamar wani ɗan shekara arba'in da ɗoriya saboda wahala. Cikin son tabbatarwa ta ce, “Wai da gaske Kainaat da Dafeeq ne?”.

           Da sauri Abaan ya kalleta ya ce, “Kainaat kuma Baɗɗo am?! Dama kin santa ne?”.

     “Yess Hamma nasanta, ai itace ta auri Dafeeq gashi nan.”

   Juyawa yay ya kalli Dafeeq ɗin da jikinsa ke rawa. Dan wani kalar kallon Khadijah yake kamar idanunsa zasu zazzago ƙasa dan tashin hankali da ruɗanin Ganin Khadijahn tamkar wata baƙar balarabiya, ga cikinta ya fito ɗas yay mata ƙyau. Wani shegen kishi ne ya ziyarci zuciyar Abaan. Hannun Khadijah ya kamo ya riƙota jikinsa. Batare da yace komai ba ya nufi mota da ita. Sakata yay, shima ya shiga ya zauna. Hakan yasa itama Noor dakema Kainaat wani kallon ƙyama da tsana ita da Dafeeq ɗin taja tsaki ta shige mota. Ko kallansu Abaan bai sake yi ba ya birga motar sukai gaba. Har sukaje gidan kawun babu wanda ya sake magana. Kusan awarsu ɗaya a can suka sake dawowa gida. Ƙofar gidan da suka bar su Dafeeq suka samu cike tamm da mutane, Abaan yayi niyyar wucewarsa sai dai kuma ya tsaya jin mike faruwa?.

      Wata mata ce ke sanar musu ai Dafeeq da matarsa ne wani mai napep ya buge yay tafiyarsa. Yay musu horn yay musu amma suna tsaye a tsakiyar titi kamar gunkina shiko yabi takansu dan barikinsu ba ɓoyayya bace a anguwar. Kullum ne sai sunci uban dabe har titi, a garin dabben nasu ne ma suka makema uwar Dafeeq ɗin ido yanzu haka ido ɗaya ne da ita ɗayan ya tsiyaye. Ubansa kuwa tuni ya gudu garinsu yay aurensa. Har Kainaat ɗin nada ciki haka suke zuba dambe, yanzu ma data haihu kuma basu daina ba, a kullum faɗan nasu bai wuce kan abinci sai kace karnuka. Dan shi dai Dafeeq ɗin baya aikin komai balle sana'a sai zaman gulma a majalisar abokai, yanzu haka suma sun gaji sun korosa. Ita kuma Matar tasa wahala tasa tana bin gidajen mutane tana wankau ana bata sauran abinci da kuɗin da basu taka kara sun karya ba. Shi kuma da son zuciya idan ya gani yace zai ƙwace hakan ke haɗasu faɗa kullum a tsakkiyar anguwa. Yau kuma ance wai shi tsohuwar matarsa ya gani, ita kuma tsohon mijinta sun zama mata da miji suma shine sukai sumar tsaye har mai napep ɗin yazo yay awan gaba da su. To yanzu dai gasu can anyi cikin gida da su......

       Noor ce taja tsaki saboda gajiya da surutun matar, cikin hasala tace, “Please Hamma mutafi Mamy na jiranmu muka zauna jin wannan shirmen banzar”. Numfashi ya ɗan sauke kawai yana ƙoƙarin tada motar Khadijah ta ɗaura hannunta a saman nashi. Kallonta yay kamar yanda take kallonsa itama. A hankali ta sakar masa murmushi mai sanyi. Shima murmushin ya sakar mata, sai kuma ya girgiza kansa kaɗan ya ce, “Ya akayi Baɗɗo am”.

         “Hamma mu taimaka musu, Aunty Noor kiyi haƙuri kinji. Babu abinda yafi rama sharri da alkairi nasara a rayuwa. Mu musulmai ne, masu tarbiyyar koyarwar MANZON ALLAH (S.A.W). Ya mana dukkan ni'ima ta rayuwa badan munfi saura daraja da kima ba, sai dan kawai haka yaso. Wannan wata damace UBANGIJI ya bamu, idan mukai amfani da ita mune da riba har abada”.

     Kusan a tare Abaan da Noor suka saki ajiyar zuciya. Wata irin ƙaunar Khadijah na sake ratsasu....


  Da ƙyar suka sami ganin su Dafeeq da aka zagaye anama fifita. Ga mahaifiyarsa da alamu suka nuna bata gani da ƙyau nata kuka a gefe. Haka yarinyarsu sai tsanyara kuka take itama da rauni a goshinta. Hannu Khadijah tasa ta ɗauke ta, duk da kuwa yarinyar duƙu-duƙu take da datti har wani tsami-tsamin dauɗa take da zarni. A zabure Dafeeq da Kainaat suka tashi kamar basu ne kwance magashiyan anama firfita ba suna nishi da ƙyar.

   

        “Da gaske ku ma'aurata ne a yanzu?”. Cewar Kainaat cikin rawar murya da zubar hawaye. Kafin Abaan da Khadijah suyi magana Noor ta amshe a gadarance.

    “Yess su ɗin ma'aurane. Masoyan juna na bugawa a sararin samaniya bama bango ko dutse ko jarida ba. Gasu ma har ALLAH ya azurtamu da samu rabo, nan da watanni uku in sha ALLAHU ɗanmu ko ƴarmu sun shaƙi iskar duniya. Ya kukaga haɗin dan ALLAH”. Ta ƙare zancen da ƙyalkyalewa da wata shegiyar dariya har sai da Abaan ya harareta. Kuka Dafeeq da Kainaat suka fashe da shi a lokaci guda tamkar wasu ƙananun yara. Yayinda Mahaifiyar Dafeeq ke tayasu. Cikin kuka tana faɗin, “Yanzu duk ƙoƙarina na kar Khadijah kiga Dafeeq dai ko ya ganki haƙata bata cimma ruwa ba kenan. Oh ni oh ni duniya haka zakimin. Yau ga Khadijah gaban ɗana tamkar matar shugaban ƙasa. Ga ɗana a ƙasƙance gabanta kamar almajirin gidanta. Dafeeq ka cuci kanka ka cucemu daka kwaso mana wannan KARA DA KIYASHIN da bakin iyaye ke ɗawainiya da rayuwarta. Gamunan ta goga mana ƙashin tsiyarta matsiyaciya kawai tsinanniya mai yawo da tsinuwar iyaye aka....”

       “Ashaa mama haka bai ƙyautu ba. Ai daga ɗanki har matarsa duk ɗaya suke a gareki. Hakan garesu kuma rubutaccen al'amarine da babu hannun da ya isa ya goshesa a cikinsu. Haka ALLAH ya tsara, batare da mun taɓa sanin juna ba amma ya auri mace ya saka na aura, na saka nima ya aura. Wannan wani hukuncine da ga UBANGIJI......”

       “CUTA TA ƊAU CUTA... ALKAIRI YA ƊAU ALKAIRI ba Hamma”. Noor ta katsesa tana wani balla musu harara. Aiko atake jama'ar da suka cika tsakar gidan duk da ana korarsu sun ƙi fita suka shiga faɗin, “Wannan haka yake.dan babu wanda bai san soyayyar da Khadijah ta gwadama Dafeeq ba. Amma yaci amanarta shi da uwarsa. To gashi nan ya rabu da ita saboda abin duniya ya auro dai-dai da shi mai fama da bakin iyaye. Dan tuni a surutun Dafeeq da mahaifiyarsa sun fayyacema mutane wacece Kainaat. Kullum cikin mata gori ake a anguwa. Tana son zuwa ga iyayenta bata da ko kuɗin motar barin Kano. Data fara tarawa kuma Dafeeq ke sacewa. Haka zasu ci uban dambe su jigata juna ta haƙura. Hakan kuma bai hana ta sake tarawa ya sace su.

      Jin al'amarin nasu dai babu daɗin ji Abaan ya basu kuɗi. A take Khadijah ma ta basu daga jakarta sukace suje asibiti suka fito suka barsu dan Mamy nata kiransu lokaci zai ƙure musu gashi jirgi zasu bi. Haka dai suka dawo gida jiki a sanyaye. Yayinda suka bar Dafeeq da Kainaat da mahaifiyarsa na rusar kuka. Da ga ƙarshe faɗa ya nema hargitsewa tsakaninsu akan kuɗin. Dafeeq na son nuna musu ƙarfa-ƙarfa daga uwarsa har Kainaat ɗin sukace bai isa ba kowa yaje yaji da kansa. Dan haka maimakon asibiti ma camix suka je aka duddubasu kowa ya matse kuɗinsa. Burin kainaat gobe asubar fari ta nufi Niger neman iyayenta ta nema gafararsu ko hakan zai sa ta samu sassauci kamar yanda mutane keta bata shawara. Maybe hakan zaisa ta samu Dafeeq ya saketa ta dawo ta auri Abaan. Shiko Dafeeq nasa hangen ya haɗe kudi ya fara kasuwanci ko shima ALLAH zai azurtashi Khadijah ta dawo garesa.......

✍️    _Niko nace Hummm hauka maganinka ALLAH. Ai an baro shiri tun rani Kainaat da Dafeeq 🥱🥱😆🧑‍🦯._*_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._**_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_**_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_**_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_**_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_*_Littatafan sune kamar haka 👇🏻_.
   *_KWANKWASON JIMINA....._*

        _(NA MSS XOXO)_*_GUDUN ƘADDARA_*

         _( NA SAFIYYA HUGUMA)_*_TSUSTAR NAMA....._*

          _(NA BILYN ABDULL)_*_AMEENATU_*

           _(NA  MAMU GEE)_

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.__GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261

__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post