Jawaheera Complete Page 7

Jawaheera Complete Page 7

 ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


         *JAWAHEER* 


☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️PART 7


NASU


NUSAIBA ALKAMAWA


PROFICIENT WRITER'S ASSOCIATION


TARE DA


SAYYADA (Barrister)


MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
_______Suna shiga parlour suka tarar da Mamy azaune tana kallo a tanƙameman plasma hannu ta rike da remote.


"agajiye suka nufi gurinta bayan sunyi sallama ta amsa musu,suka zauna atare sukace, wash! Mamy mungaji wllh!.


 "sannun ku ƴaƴana  yanxu dai kuje ku huta tukunna sai kubani bawa tsarabar tawa mamy tafaɗa cike da tsokana."murmushi jawaheer tayi tace "Mamy Aikuwa nazaɓo miki wani abu mai kyau,Mamy tace dan Allah fa ƴata? Aikuwa Ngd ,Jahan tace nidai mamy ban ɗaukar miki komai ba Dady kawai naɗaukarwa,cike da hararar wasa mamy tace wato Dadyn ki  kika sani ko? xan rama ne Nima ƴata jawaheer kawai zanbawa wani Abu,Mamy menene shi ??basai kinji ba kutashi kuje ku huta.


______ mikewa sukayi suka shiga da kayan daƙin Jahan suna shiga suka faɗa gado cike da gajiya jawaheer tace "Jahan besty kinsan me ?"a'a besty Jahan ta mayar wa da jawaheer amsa,"jawaheer tace nifa Wannan yaya *Jawad* ɗin yabani tsoro sosai, lokaci ɗaya kawai ya canza kodama haka yake ne ?"dariya Jahan tayi tace a'a besty jawaheer inaga fa dole akwai abinda ya sashi haka SBD baya yin haka,Kinga lokacin da muka tafi lafiya kalau yake akwai dai wani babban dalili, nifa wllh har saura kaɗan nayi fitsari  a wando ,,"Aikuwa kinbani dariya ina juyowa naga bakyanan,yo ba dole ba nandai suka cigaba da hirar su .


________Washe gari.

Yana zaune har yanxu ranshi bai gama saki ba ɗaci yake ji azuciyar sa ,hakan yasa yafito parlour ko zaiga Mamy domin ko xaiji sauƙi aransa karo suka kusan yi da jawaheer saurin matsawa tayi tabashi guri batare da tace masa komai ba ,shikuwa nunawa yayi kamar baisan sunyi ba Amman aranshi yaji takaici da bata nuna tasan dashi ba ,"shiga dakin mamy yayi yatarar da ita tana lazimi,durkusawa yayi cike da ladabi yagaisheta ta amsa masa cike da soyayyar ɗan nata."Mamy wai yaushe yarinyar nan xata tafi gidansu ne ??


"Wacce yarinya kuma Jawad?Mamy ta nuna tamkar bata gane inda zancenshi ya dosa ba .


Mamy jawah take kome? Yakamata ace ta koma tunda angama taron tuntuni yafaɗa kamar bayaso yayi magana.Mamy tace au jawaheer ƴata zakace yo ai yau ma ,mukayi waya da mamanta na roke ta da tabarta tayi mana ko sati dayane.


"mamy har sati daya kuma ??"ah ai ba akanka zata zauna ba .


______Azuciyar shi yace lalle yazama dole na koma abuja kuwa, dan bazan zauna a inuwa daya da ita ba ,Amman afili yace mamy gobe idan Allah yakaimu zan koma abuja dama zuwa nayi na faɗa miki,ai nazáta kabar aiki acen tunda yanxun mahaifinka ya gina maka naka asibitin? 


"Mamy dama akwai wasu shirye_ shirye da ban gama acen ba Amman idan naje na kammala sai na dawo nan yanxu xan saka shabbir da mus'ab akan komai zan tsara musu komai kafin nadawo .


"To shikkenan yanxu idan kaje cen kwana nawa xakayi??wata ma daya zanyi Tom Allah yakaimu amen mamy saiki yiwa Dady bayani yafaɗa tare da mikewa .


"ohk to baka da matsala. "Ngd Mamy Bara naje ɗakina Tom shikkenan.______Bayan yanufi dakinshi yaciro waya yashiga app yayi booking din jirgi Aikuwa yayi sa' a yasamu azman wanda xasu tashi da safe karfe bakwai nan kuwa yasai ticket._______Washe gari yaje yayi wa su Dady sallama sukayi masa addu'oi da fatan nasara, sannan yawuce airport  sai 


Abuja."Jahan tana tashi daga barci mamy take faɗa mata cewa Jawad yatafi,cike da kukan shagwaɓa Jahan tace "Mamy yanxu yaya yayafi shine ko sallama baxai min ba kuma ai kwatasheni daga baccin narasa meyasa yaya Jawad yanzu yasauya min baitaɓa tafiya batare da yazo munyi salama ba takarashe maganar tana matso da ƴar kwalla .Mamy tajawota jikinta tana rarrashi tace Jahan baby tafiyar ce tazo masa bagatatan Amman ai yace zaimiki waya idan ya isa ,Mamy tafaɗa haka domin ta kwantar mata da hankali Aikuwa tasamu nasara, to shikkenan mamy Bara naje naga besty na ta tashi ?"ohh to nan tamike tashiga dakin Amman taga JAWAHEERA anyi dai _dai ana bacci murmushi kawai Jahan tayi taja mata kofa tanufi kitchen.

          _ABUJA_ 


        *JAWAD* 


_____ Sanye yake cikin jallabiyar sa kirar Japan light brown yatsarsa na manuniya makale yake da counter yana lazimi ka'idansa shine dazaran ya tashi sallar asuba baya komawa bacci.


Alarm na 7:00Am ne buga kuma alokacin ya kammala lazimin sa ya mike ya faɗa toilet SBD shirin zuwa office watsa ruwa yayi ya fito ya shirya cikin shigarsa wacce ya saba indai zashi wajen aiki Black suit da ƴar ciki pink color da Nick tide ma pink yayi matukar kyau yayi cumbing kwantaccen gashin kansa wanda yashe gyara sannan ya feshe jikinsa da turaren Black man sannan ya makala white glass nasa ya dau wayarsa da keyn mota ya fito ya shige mota gate man ya buɗe masa ya fice bai dau wasu lokuta ba ya iso wajen aiki yana isowa yayi parking  kai saye office nasa ya wuce.


 *RUFAIDA* 


Cikin takunta irin na wayayyun mata take yi tana kwarkwasa tana mai fatan yau kam hakanta ta cimma ruwa dan tunda Jawad ya tafi Kano da dukufa wajen boka ya bata magani kuma ya shaida mata wannan karon zatai nasara ta iso office nasa tai Nocking jin shuru yasa ta murɗa handle door ta shigo tare da sallama SBD this time batasu tai kuskure.


Bai ɗago ba amman ya shaida muryar ya amsa sallaman.


"My Love saukan yaushe shine zuwa ba sanarwa!"


Yayi banza da ita kaji rainin hankali in zai shigo Abuja sai ya sanar da ita sai ya tsuke fuskar ya maida hankalnsa kan system dinsa.


Tou yauwa sai ya kulata zata tafi ta fito da turaren da boka ya bata ta shafa bayan ta tabbatar hankalin sa baya kanta cikin muryan kisisina tace

"My i really missed you but babu yadda na iyane yasa na hakura, ya kamata kaji tausayini zuwa yanzu ina cikin damuwa na rashin kulanin da kake ni kaina da ina da yadda zanyi zan hakura da kai amman nasani bazan iya ba SBD ina masifar kaunarka" ta karashe sa cikin kuka.


Kamshin turaren da ya ziyarci hamcinsa ya shaka shine ya dakatar da shi da ya ɗago karon sa na farko da yaji yana don ganin ta suna haɗa ido ya kasa kawar da kansa sai yaji ya jin tausayin.


"Tou me kuma abin kuka ba gashi na dawo lfy ba!"


Cikin murya da jin ta fara nasara akansa sai ta sauya salo ta sake narkar da murya wai adole shagwaba takeyi


"Ae kaine duk sanda na so ganin ka kake kauce min baka son kulani ko dai bana daga cikin matan da kake burin samune? Ta kafesa da ido tana jiran amsar sa.


"A'a ba haka bane kinsan irin aekin da nakeyi ni kaina bani da lokacin kai na amman zan kokarta naje gidanku sai muyi magana"


Sabagen murya kamar tayi ihu amman ta dake ta cigaba da shawo kansa sai da ta tabbatar ya fara biye mata sannan sukai sallama ta fita tana fita ya maida hankalinsa kan system ya ci gaba da aekinsa.


Itako tana fita ta wuce yawon ta dan babu mai hanata balle kuma kwaba sai tai ta gantalinta har sai sanda ta gaji ta koma gida SBD itace karfin gidansu mahaifinta ya jima da yin retire a wajen aiki kuma bashi da wata kwakwarar sana'a da yakeyi itama umman tata zaman gida takeyi ga kuma kanne da yayu babu wacce tai Aure    sai tayi yawon duk abinda ta samo wa gida take kashewa.


 _Bayan kwana biyu_


___kwance yake akan makeken bed nasa wanda yasha gyara sai juyi yake ya rasa dalili sai yaji yana son jin muryar *RUFAIDA* ya dau wayarsa ya kirata bugu ɗaya ta dauka cikin rawar jiki wai! Ta washe baki kamar mai tallan maclean tun kan yayi magana ta rigashi "my love ykk ya aeki kamar ko kana raina yanzu nake shirin kiranka sai ko kakirani"shuru yayi yarasa ta inda zai fara cen sai yace"ina son ganinki turomin address na gidanku gani tafe" ya katse wayar ba tare da ya ji ta bakinta ba. 


Shiryawa yayi cikin kananun kaya Black jeans with sky blue t-shirt ya daura agogon hannu yasa white glass nasa ya fice zuwa gidansu RUFAIDA.


Kai tsaye unguwar su Rufaida ya nufa shi burinsa ya kalleta da kyar ya iso layinsu saboda irin unguwar nan da ake kira muna Abuja kofar gidan ya tsaya ya kirata ta fito jiki yana rawa ya kalleta sai yaji zuciyarsa tai masa sanyi.


"Barka da isuwa"


"Yauwa" kawai ya faɗa yana karewa gidan kallo ba laifi gidan ana da dan kyansa SBD a Latin unguwar shine dai mai dan kyau da fadi.


"Ka shigo cikin"


"Tou" suka jera sukai ciki har palourn mahaifinta tai mai isowa
 Comments

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post