Jawaheera Complete Page 8


Health College

Jawaheera Complete Page 8

 ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


       *JAWAHEER* 


☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️



PART 8


NASU


NUSAIBA ALKAMAWA


PROFICIENT WRITER'S ASSOCIATION


TARE DA


SAYYADA (Barrister)


MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION




____tsayawa yayi yana karewa palour kallo kujerune a jere set da labulayen amman duk sunji jiki carpet dinma,  baza a' iya gane wane kala bane dan duk ya fita hayyacinsa....


"Ah dan saurayi Barka da shigowa" mahaifin Rufaida ya katse masa tunanin da yakeyi.


"Yauwa" ya fadawa yana mai neman wajen zama ya zauna akan 1setter da duk dullop din ya lotsai sai katako, ji yayi daram katako yayi kara aikuwa babu shiri  ya silale kasa ya zauna"


"Abba wannan shine doctor Jawad"cewar Rufaida.


"Barka da warhaka Abba  nasameku lfy? " cewar Jawad.


"Lfynmu lau likita bokan turai ashe kaine tafe? ya faɗa yana washe baki.


"Eh Abba nazo ne akan neman Auren Rufaida indai bata da manemi.


"Lah wane manemi indai kanaso ae an wuce wajen ko yau a daura...


"Shigowar kannen ta da yayunta da kuma mahaifiyarsu ne yasa mahaifin nasu shuru.


__________Bataliya guda suka shigo ikon Allah wannan duk ace mutan gida ɗaya ya juya yasake kallonsu yayun nata da alamu babu mai aure aci balle kuma kannenta.


"Doctor barka da zuwa ya aeki kazo lfy" cewar mamar ta wanda shigowar ta kenan.


"Alhamdulillah nasameku lfy"


Ta washe hakura tana "lfynmu lau ya wajen su mamanka tafaɗa tana me zama akan kujera"


"Suna lfy,yafaɗa cike da gajiya harya kosa ya tafi shifa baya son dogon zance.


_______Yayunta da kannenta suka gaidashi ya amsa ta kawo mai ruwa da lemo bai sha ba, SBD shi mutum ne mai ƙyanƙyami,ya ajiye musu rafar 500 a duk kule ya mike yace " tou ni zan wuce zuwa sati mai zuwa sai ayi bikin amman ba yau ba,ba kuma gobe ba,yana faɗar haka  ya fice yayi wajen motar da ya tada ta yayi wajen cin abinci yana mamaki irin wannan ahalin.


"Suko yana fita suka daka tsalle kan kuɗaɗen da ya ajjiye suna ni zan raba wannan ma tana nice zan raba uwar tace ku bari ni na raba"


Daya daga cikin yayun tace " taba Ummu ae ana baki ba bamu zakiyi ba keda son kudi"


"Shegiyar yarinya in banso kudi ba ubanki zanso? ina ni da Rufaida muka tashi tsaye kafin wannan mutumin ya fito?


"Fusararriyar kanwar ta tace"Ummu anya kuwa zakiga annabi saboda ke shu'umammiyace ba irin bukayin da baki zaga ba tafaɗa,tana  mai turo baki fuska duk ta ƙode SBD bleaching.


"Inna zo ganin sa ki rufe min ido ja'irar yarinya"


Mahaifinsu dai sai ido dan bashi da tacewa sai abinda uwarsu tace. Da kyar aka samu aka kasabta kudin suka raba daganan kowa yasan inda dare yayi mai,"itako Rufaida ta fice yawon ta zuwa gidan kawarta sakaninsu akwai dan tafiya, tana shiga tace


"Shegiyar kawata kina wuta ina binki da fetur yau akwai lbr"


Shalelen duniya itace kawarta tare suke sheƙe ayarsu ta fito daga ita sai gajeren wando da wata shegiyar vest fuska ta koɗe ga gashi attach cikin muryan ta mai kama da na karti tace!


"Ah kawata da alamu abin nema ya samu kamar kinsa ina neman ki waccen shegen Alhaji sai kirana yake yana min magiya wai yayi kewar ki"


"Ae wutsiya raƙumi tayi nesa da kasa sha_sha sha ma irin sa mai maƙo kawai mutum ace baza kaci kudin sa ba aeko yasake kirana sai na danna masa ashar"


Suka tafa suna dariya 


"Tou ban lbr mana"


"Umm ina mutumi na doctor Jawad yau ya shigo hannu har gida yazo kuma yace nan da sati ɗaya zamuyi Aure"


"Kai bari dan Adam"


"Wlh nake gayamiki kinga bounch na kudin da ya ajjiye mana yanzu ma rabonki na kawo miki" ta mika mata"


"Wannan shine tsunsu gasheshshiya daga sama kice yashigo hannu ehhhhh muna da gagarumin biki sai yanxu Allah yayi wajan wata nawa muna binsa Amman yake miki wulakanci"


Nan dai sukai ta hirarsu har suka watse.


___JAWAD dai jinsa yake a wani yanayi shi dai yasan lfyarsa klau amman kuma yana jinsa ba lau ba tunda ya dawo daga aeki yake ta sake_sake ta yadda zai sanar wa 'yayensa zancen aurensa da Rufaida dan a yanzu ji yake in bata zama mallakinsa ba zai shiga cikin yanayi mai wuya ya yanke shawarar zai kira mahaifinsa ya sanar dashi, da wannan tunanin yayi bacci.



          *KANO* *STATE* 


___Mamy na zaune a palo tana kollon News mahafin Jahan (Dady) yashigo ya zauna tai mai Barka da shigowa"yauwa barka dai ke kadai ina yaranne?


"Ae tunda JAWAHEER tazo jahan tasami ƴar hira ba kasafai take zama a palour ba suna cen suna hirarsu"


"Ina ruwan kawaye ni ae shakuwarsu birgeni tayi damu burina mu haɗa zumunci mai karfi a tsakanin mu kuma Alhamdulillah tun kan mu haɗa su cikin hikimar Ubangijin sun hada kai"

 

Dady yana cikin maganarsai ga

Fitowar su, sunyi kyau sai ƙamshi suke sukace "Abba sannu da zuwa" a tare suka hada baki.

"Yauwa yarana ya ya karatu ana taɓawa ko?


"Eh Abba munayi" 


"Allah yayi muku Albarka"


"Ameen"suka faɗa a tare"


Mamy tace "tunda kun fito sai muje Dining Area dan cin lunch ko!


Gaba daya suka wuce suka ci suka sha daga bisani dadynsu ya wuce side nashi mamy ta mara masa baya. Sukuma suka zauna a nan palo sukaci gaba da kallo *JAWAHEER* tace" wai ni jahan tun jiya banji ɗuriyar yayankin nan ba! Tai murmushi ae na manta ban faɗa miki ba ya tafi Abuja kinsa acen yake aekin yanzu haka tafiyar gaggawa ce ta kamasa"


JAWAHEER taji sanyi aranta sai ta saki jiki sukai ta kallo suna hira cikin raha.


___Bayan Mamy tabi bayan Abbansu jahan ɗakinsa ta samesa zaune yayi tagumi ta zauna a kusa dashi " mai ya faru harda tagumi Alhaji? Dady" yayi ajiyar zuciya Sannan yace   lamarin JAWAD ne ya fara damuna ina ga the best thing shine yadawo nan kano yacigaba da aekinsa a kusa damu duk da mun bashi tarbiyya dai_dai gwargwado ina tsoron kar ya dauko wata ɗabi'a ta yahudawa tunda acen yayi karatu sawon shekaru kamin ya dawo gida Nigeria"...


"Haba Alhaji muyi masa fatan Alkhairi kafa sansa tun kan yatafi kasar waje karatu shi mutum ne wanda bayason hayaniya sannan ba da kowa yake hulɗa ba sai wanda jininsa ya amshesa bare kuma nan gida abuja"


"Ke daman bakiso ae mai faɗa dube jiya kwasam aka waye gari ya wuce *Abuja* ba shiri"...... Ringing wayansa yasa ya dakata da zancen da yakeyi SBD sunan *JAWAD* da yagani a screen na wayarsa ya dauka jawad ne yayi magana"Barka da warhaka Abbana"


"Barka yayi maka kyau ka tashi kai tafiyarka a dole kai likita ne"


Saboda kudirin sa kuma yana son ya shawo kan mahaifinsa yasa ya fara rarrashinsa"Ayi hakuri Abba tafiyar ta gaggawa ce"tou naji kasauka lfy? Lfy Abba dama nakirane akan wani abu..... Sai yayi shuru" wane irin abu Kuma? 


"Abba daman akwai wacce nakeso kuma da Aure shine mahaifinta yace yana so ayi bikin nan da sati ɗaya"



"What! Are you out of your mind, aure!!maganar aure fa kakeyi eh lallai zargina ya tabbata to inkai baka san mai kakeyi ba tou mu munsan abinda mukeyi ban yarda ba" ya katse wayar ya ajiye.


Mamy tace"wai meke faruwa ne naji kana zancen aure waye kuma yayi aure ko zaiyi?"


"JAWAD ne wai Aure zayyi nan da sati guda kuma acen Abuja"


"AURE! Shiyace Aure zayyi?" 


"Kin daiji abinda nake faɗa miki kina karesa tou abin nasa ya girmama"


____________Ta dau waya ta kirasa bugu ɗaya ya dauka "my mamy" Jawad abinda mahaifinka yafaɗa gaskene?"eh mamy gaskiya ne kuma ma, anan suke da mahaifanta mamy dan Allah ki taimaka ki shawo kan Abba ya amince banaso na rasa Rufaida" mamy salati tai tana jin jina al'amarin yaro yabar gari  yau kuma ya tada zancen aure anya lau kuwa ta katse wayar.


"Alhaji kasan Jawad ba yaro bane yasan abinda zai cutar dashi da kuma abu mai kyau da ace ya lalace ae gwara ayi mai aure da wacce yake so"


"A gaskiya nafison Ya Auri mace anan Kano akusa da mu mugina rayuwa mai inganci da annashuwa amman kwasam ba lbr yace nan da sati zaiyi aure anya akwai hankali anan kuwa barni dashi zanyi wa tubkar hanci" Mamy dai tayi_ tayi abin yaci tura ta hakura zuwa wani lokaci in yasauko ko zai amince.


       *JAWAHEER*



Ina kwance bayan na watsa ruwa nayi shirin kwanciya naji wayata na ruri na duba sai naga new number ce kamar bazan daukaba sai na ɗaga batare da nayi magana ba,daga  cen ɓangaren akai sallama


"Baby ta kin ƙini inata begenki amman kin shareni" sarai naganesa amman nayi kamar bansan da wanda nake waya ba nace


"Wai wayene yake damuna a dai _dai lokacin da zankwanta inhuta wa raina.


"Haba my one yau kuma ta inda kika ɓullo kenan ae ko acikin dubban mutane kikaji muryata zaki shaidani" 


Tou inbaka da niyyar gabatar da kanka sai da safe Allah ya tashemu.


Cikin sauri ya katse ta da cewa "HABEEB ne fah"


Au shine kake wahalar da ni kaga ni bani da lokacin ka....


"Cikin murya irin ta mabukaci yace"Please my one ina matukar bukatar ki wlh sonki da sha'awar ki sun addabeni bansan yadda zanyi ba....


Kai dakata dan Allah nayi maka kama da irin matan da kake lalata da sune tou daga rana irin ta yau kada ka sake kirana na katse wayar nayi blocking nasa.


Jahad dake kwance tanajin duk abinda mukeyi tace"Ni wai wannan habeeb dinma anya yana da hankali ace mace kamarki maimakon yayi sha'awan ki kasance a masayin matarsa shine zai nemeki da fasikanci gwanda da kikai blocking nasa kin min dai _dai"


Uhmmm kawata kedai bari Allah ya rufa asiri. 


"Ameen insha Allahu zaki sami mai sonki tsakanin sa da Allah"


Muna cikin hira kiran wayarta ta katsemu Ya IMRAN ne,ta dauka sukasha hirar soyayyar su har nayi bacci.


         _WASHEGARI_


__Bayan muntashi wanka mukai, bayan mun idar da sallah mukeje muka gaida Dady da Mamy sannan muka dawo Dining Area mukai breakfast baki dayanmu sannan muka wuce skul mukabar su agida.


"Mamy sai faman rarrashin Abba take akan ya amince a daurawa Jawad Aure da kyar ya amince amman sai da ya kira Daddyn JAWAHEER sukai shawara yace kada ya damu shi zaije har Abuja ayi komai sannan yadawo ba matsala.


Haka ko akayi bayan kwana biyu da faruwar haka daddy yaje Abuja ya sauka agidan wani abokinsa tare da abokin nasu sukaje nemawa Jawad Auren Rufaida kuma sun bashi sunce nanda kwana Hudu sai a daura haka dai Daddyn JAWAHEER yazauna har sai da aka daura aure sannan ya dawo Kano.


_____Bangaren gidansu RUFAIDA ansha biki dan wannan shine karon farko agidan sannan Jawad ya sakar musu kudi sukai ta bidirinsu komai shi yayi kama daga kayan ɗaki, palour, kitchen da dai sauransu gidan da ya kama hanyar sa babu nisa daga gidansu RUFAIDA.



Andauko Amarya kamar yadda akeyi da 'yan rakiyarta akai ta yabon gidan bayan kowa ya watse ne ango ya tare da Amaryar sa sai dai shi duk da baitaba sanin 'yamace ba ya tabbatar Rufaida ba cikakken bace but bashi da bakin magana dan andaure sai ido.


____Gari yawaye  baibi ta kantaba ya fito palour sai sake_sake yake aransa yaji sallaman garada da 'yanmata manya da kanana yajuyo yana kollonsu ɗaya bayan ɗaya kallon daga ina kuke kuma mekukazo yi danshi baison hayaniya.


Wajen zama suka samu kowa ya barbaje suna "muntashi lfy Uncle"


What! Uncle garada dasu suce masa uncle acikin yayunta ma akwai sa'ar mamy yace "sannunku"


Suka amsa suna ina amarya rangida. Ya fara fusata kawai ya wuce ɗakinta tananan kwance shabe ko wankan tsarki babu balle kuma aje ga sallah tayi doguwar hamma tana "wai har gari yawayene?"


"A'a yanzu dare ya fara tashi kije ki sallami bataliyanki suna nan a palour ya wuce ɗakinsa tana mamaki suwaye kuma bataliyanta aeko tana fitowa taga 'yan'uwanta tana "kan uba mai zangani haka jiya akawoni kuzo ku kashe min aure harda Audu dan sholy wlh baku isaba kutashi kutafi zan kiraku muyi magana a waya"


"Yayarta tace sannu su miji manya yaushe akayi aure har anmanta damu aiko wlh baki isa ba kinsan ba komai agida karyawa mukazo yi dan haka abamu abinci muci kuma mutafi da wanda zamuci anjima. Tirkashi wannan shine anraka amarya tadawo wai! Audu dan sholy yace "eh mana babbar yaya eyane aɗan dubumin na sigari mana! " Nace kaci ubanka Audu ni kanwarka ta biyar kakecemin babbar yaya lallai ƙwayar da kasha jiya bata sake kaba" haka dai tajido musu breakfast takowa musu suka zage sukaci sukasha ya fito cikin shigarsa ta kananun kaya yayi matukar kyau black trouser with red t-shirt ya saya yana kollonsu KAIII!!!!!! Me nake gani Audu dan sholy yace Ahmana oga yana hade hannu yana sai oga likita bukan turai.....




Comments and share

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post