Kurman Baƙi Page 23 by Huguma

Kurman Baƙi Page 23 by Huguma

 *_KURMAN BAƘI_* ⚫⚫⚫


*HUGUMA*


PAGE 23


https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr


*_Assalamualaikum warahmatullah_*


*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*


*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,akwai bonanza time to time da nakeyi,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*


       

             Sallamarsu ta amsa tana binsu da kallo cikin mamakin abinda ya shigo dasu dukka haka a tare


"Ina zainab taje?" Ya tambayeta yana tsareta da kallo cikin salo na tuhuma. Idanu ta zuba masa na wucin gadi kafin tace


"Bata tayi?" Ta amsa masa da salo na gatse,don ba wannan amsar taso bashi ba. Ya karanci ko mene a idanunta,maimakon yayi qasa sai yaji ransa ya sake baci,gaba daya kaman sun rainashi kenan ita da Zainab din


"Kina cikin gidan nan amma abar yara su wuni da yunwa don wulaqanci?,ita ta saka qafa ta fice bata gayamin inda zata je ba,ke kuma kinsan suna cikin gidan a barsu a guri su kadai,yanzun inda ace sun taba wani gurin sun hadawa kansu gobara fa?"


"Uhmmm.....Allah sarki" kawai tace dashi taci gaba da jan carbinta. Hakan data masa ya sake qular dashi,idan ta saba share masa da qin yarda suyi zancan da ya danganci zainab ai issue din yanzu ya banbanta da na ko yaushe ko?.


"Kai alhassan,ku dauki abincin ku qaro muku ku wuce dakinku kuci tare dasu haneefa"


"To daddy,alhussain dauko plate din,ke haneefa bari a zuba muku naku ke da iftee" sai yaja yaran suka wuce.


                Kallonsa ya maido kanta bayan yaran sun wuce


"Dake nake fa" kai tsaye ta sake kallonsa,duba daya ya fahimci da yunwa ya dawo daga kasuwa,ita ya kwaso take kuma tunzurashi(muddin kinsan kina barin mijinki da yunwa......muddin kinsan kina barin mijinki yana jiranki saikin kammala abinci to billahillazi daga yau ki taimaki kanki ki daina,yunwa tana jawo fushi,shi kuma fushi mabudin dukkan sharri ne,hanyar da zaki mallaki zuciyar mijinki shine ki kula da cikinsa ki tsare masa shi)


"Wai nikam ajiyarta ka bani?,ko munyi yarjejeniyar zata dinga neman izinina kafin ta fita?"


"To amma ai kece babba cikin gidan ko?,meye amfaninki da har irin hakan zata faru yara su wuni da yunwa a sashen ba tare da kin sani ba?" Dan qaramin murmushi ne da bata shirya ba ya subuce mata,tadan girgiza kai kadan


"Allah sarki,yau kuma ni ake baiwa girman ake bani muqamin na saka ido cikin gidan nan?,bayan togaciya sharadi da iyakokin da aka taba gindayamin a baya?, gaskiya ne.......to kayi haquri ranka shi dade,indai ba fitina kake nemowa ba kuma,yara dai bansan su kadai bane a sashensu,da babu i zaa yi na barsu da yunwa,kafi kowa sanin bada abinci ko dafashi bai cikin matsaloli na.......Abinci ne gashican an basu,ita kuma bansan ta fita ba bansan kuma ina taje ba,shikenan?" Ta tambayeshi tana tsareshi da idanu itama.


               Wani numfashi ya saukar,kamar bazai motsa ba sai kuma ya juya ya nufi qofa,tana kallonsa qasan ranta tana hadiye dariya da mamakin halin da namiji,kamar ba'a wannan falon ya zauna ya qidanya mata dokoki da sharadai akan matarsa shalelensa wadda dangi kaf suka aza tazo ta cika gidan da 'ya'ya ba,ta nunawa ita ruqayya cewa ita din cikakkiyar juya ce,kaman bashi ba yanzun ya taho da confidence dinsa zai kawo mata qabli da ba'adi. Tasan yunwa ce take sasaqarsa,ita kuwa tun a wancan zamanin da ya watsa mata qasa a idanu ta daina bashi abincinta muddin ba ranar girkinta bane,gashi kuma shi din ba gwanin cin abinci a waje bane.


               Har ya isa dab da qofa wayarsa ta dauki burari,ya dakata yana fiddo wayar,ya sake qufula sanda yaga sunan zainab din.


              Koda ya daga wayar saqon da ake gaya masa sai yaji ya girmimi kansa,dole bayan ya ajjiye wayar ya waiwayo yana duban ruqayya,don ita kadaice yakejin zata tayashi tallafar nauyin da zuciyarsa da qirjinsa sukayi. Matarsa ta aure?,matarsa ta sunna a kulle a station.


                 Sanda yake gayawa ruqayyan ita kanta abun sai ya bata mamaki ya girmimi kanta


"Me tayi har ya kaita police station?,yaushe 'yan sanda sukazo da ni da nake cikin gidan nan banji ba har suka tafi da ita?" Tayi tambayar wadda daga shi har ita basu da amsa


"Wata rigima ya debo na tabbatar da haka" ya fada cikin gamsuwa


"Babu lallai,kaidai ka bincika"


"Wallahi ko kaffara bazanyi ba idan na rantse,nasan halinta ciki da bai,taimaka kizo ki rakani muje" da sauri ta kada hannunta


"Wa?,ni?,daga qarshe zance ya juye ace ni na saka aka kulleta?,Allah ya tsare hanya a dawo lafiya" ta fada tana nade abun sallarta. Haka ya tsaya yana binta da kallo harta gama nadewa ta wuce daki gurin yaran.


                  Yana tuqi a hanya zuciyarsa tana dada zafi,cikin mintuna qalilan ya isa police station din. Muryarta ya fara cin karo da ita suna sa'insa da wani dan sanda,fadi yake cewa


"Banda aure dake wuyanki da saikin raina kanki,yanzunma kuma kici gaba da cikama mutane guri kiga idan ban saka su Monica sun sassaba miki kamanni ba" tasan yadda yake da zafi iya awannin da sukayi a wajen,don haka ta rage sautinta,saidai kuma bata fasa maganganun ba.


                Kunya baqinciki da takaici suka ishi saleem sanda ake karanto masa statement na dalilin zuwansu gurin


"Maganin mata da shiga har gida su doki mace har dakin mijinta" ji yayi kaman zai mutu saboda takaici,wanne irin tonon silili ne wannan?. Banda darajar su haneefa da khalil babu abinda zai hanashi tafiyarta ya barta a wajen ta nemi me belinta,to amma yaran kawai ya tuna ya karbi belinta harda tararta da sukaci,saidai kuma suna fita farfajiyar gidan yace ta nemi gidan zuwa,kada ta sake ta dawo masa gida,yaja motarsa ya wuce abinsa.


                Sanda ya koma yaran duk har sunyi bacci a dakinsu,shi Khalil dama cikinsa yana dauka ya haye tattausan gadon alhassan, komai iri daya aka siya aka zuba musu,to amma rashin kulawa da rashin tsafta yasa yaran suke ganin dakinsu alhassan din kamar yafi nasu kamar nasu dakin wata aljannar duniya ne.


                Wanka tayi data tabbatar sunyi bacci,ta saka rigar material mara nauyi. Abinka da me yaron ciki sai taji tana son shaqar iskar waje,don haka ta saka qaramin hijabi a kanta,ta dauki qaramin littafin hisnul muslim da taketa qoqarin haddace wasu addu'o'i masu muhimmanci a ciki ta fita waje.(akwai addu'o'i masu tarin muhimmanci a ciki,kada ki zauna ace baki haddace kowacce addu'a ba 'yar uwa,akwai babban hatsari,kaman ka gina gida ne babu qofofi ko winduna).


                 Bata jima da zama ba taji hon dinsa,yaron gidansu da bai tafiya sai 12 na dare shi ya bude masa ya sako motar ciki. Tana zaune har ya saita parking ya tako zuwa cikin gidan kai tsaye kuma ya nufo sashenta.


                Daga kai tayi tana amsa sallamar sa tare da nazarin ganinsa shi daya


"Ya na ganka kai kadai?,ko ta wuce ciki?" Ta tambayeshi tana gyara zamanta cikin kujera. Kai ya dauke gefe guda


"Me zanyi mata?,na karbo ta amma saidai ta wuce gidansu,don ni bazan iya zama da ita ba da wannan abun kunyar da ta jawomin"


"Ban fahimceka ba,kaman yaaya?" Ta tambayeshi fuskarta a dan yamutse


"Eh nace ta tafi gidansu" kai ta ya shiga girgizawa


"A'ah, bazaiyiwu ba,ta tafi gidansu ta barwa waye yaranta?,haka kawai mace na gidanta ka sallameta?"


"Au haka kawai ne ma?"


"Eh mana,don tayi laifi?,waye baya kuskure?"


"Ganganci ne wannan zallar taurin kai da rashin jin magana"


"Hakanan zakayi haquri da ita,amma ba inda zataje,don ban shirya riqon dan kowa ba,koda nan gaba aure  ka qara to ka saka a ranka mutu ka raba kai da ita,nima nawa ban gama wahalarsu ba"


"Sai naga ta yadda zakimin dole" ya fada yana shirin wucewa sashenta


"Bafa kwanana bane,kada ka shigarmin gida ka tayarmin da yara" ta fada tana miqewa tsaye.


                A zafafe ya waiwayo yana dubanta,yana jin kamar tanason tunzurashi ne,wai wacce irin macace ita?wasu matan suna murna suna jiran irin wannan damar?,amma ita ta samu tana tankwabewa?.


              Baikai ga cewa komai ba aka buda can qofar get aka shigo. Akwai wadatar hasken fitilu a farfajiyar,don haka kana iya gano zainab.


               Dakatawa yayi da shirin shiga ya nufota rai bace


"Ba gida nace ki wuce ba?"


"Kayi haquri don Allah,wallahi bazan sake ba, tsautsayi ne wannan ma"


"Banason na sakejin komai daga bakinki,gida nace ki tafi"


"Bafa inda zataje,waye baya kuskure?,sai ka zauna ka fahimceta ai,idan da hali a bata uzuri ko?" Shi da zainab din dukansu ita suka kalla,zainab din bata taba kawo zata sanya baki ko ta bata kariya ba,amma duk da hakan da tayi bataji ta burgeta ba


"Wannan ba hukuncin ki bane ba kuma huruminki bane,hukunci na riga na yanke"


"Eh haka ne.....to jirani nima na hado nawa kayan mu tafi tare" ruqayya tace tana juyawa zuwa cikin gidan. A yadda taga tayi maganar ya tabbatar tana nufin abinda ta fada din,ya waiwaya ya dubi ruqayya sake shigewa ciki ya kalli Zainab dake tsaye saroro


"Ki wuce ciki,amma wallahi saikin gane kurenki don bazan lamunci wannan zubda mutuncin ba" baqinciki da farinciki ne dukka suka gaurayar mata lokaci daya,tabbas badon ita ko domin Allah saleem ya barta ta koma dakinta ba. Yanzun kamar ita ace albarkacin kishiya taci?,wanne irin babban abun takaici da abun kunya ne wannan?.


                Wannan abun yayi wata wawuyar tsaiwa a zuciyar Zainab,a daren ranar baccinta ragaggge ne,duk sanda ta juya sai abun ya fado mata,wutar qiyayyar ruqayya ce kawai take sake ruruwa a zuciyarta.


            To wai banda don a gallaza mata a tozartata me yakai saleem aurota yasan ruqayya nada wadannan qualities din?,wato amfaninta kadai a wajensa dai dai yake da machine na haifar yara?,eh mana ......tazo ne kawai kenan don ta cike masa gibin haihuwa?,a yanzun kuma da haihuwar ta samu daga gurin ruqayyan sai komai ya sake zama wani iri. Ya akayi a komai sai ruqayya ta fita ne?,iya cikin jikinta kadai ya isa abunda yake hana ma zuciyarta da kwanyarta nutsuwa da kwanciyar hankali. A daren taji burinta na qarshe a rayuwa shine taga bayan ruqayya,ta tabbatar shine abinda  zaya sama mata nutsuwa da kwanciyar rai.


******Cikin kwanakin gaba daya damuwa ta yiwa wasila yawa,duk idan ka ganta zakasan bata cikin nutsuwarta,faisal yayi mata dukkan wata bazata da bata taba kawowa ba. Da ruqayya kadai tayi zancan bayan ummanta,saboda da ruqayyan ta amince,don kowa kallonsa take a matsayin wanda zai iya zaka mata hannu a lalacewar maganar aurenta. Duk yadd kaso ga bawa wasilan shawara ba lallai tayi tasiri,don haka iya gwargwadon hali ruqayya ta lallasheta ne tare da bata shawarar dagewa da addu'a,duk da tasan babu lallai addu'ar tayi mata tasiri tunda ta riga ta raba qafa. Dan man da take shafawa kwana biyu ta aje saboda bacin rai,hakan ta fada qibar ta dan janye kadan.


               Cikin wannan lokacin yara suka kammala exams, za'a yi musu hutu,hakanan an gayyaci dukkan iyayen yara don su halarci makarantar za'a yi taron tafiya hutu da bada kyaututuka ga haziqan dalibai.


               Farko ruqayya cewa tayi ba zataje ba,tunda duka makarantar yaran nasu daya ne Zainab din ta wakilceta kawai. Saleem ne yace a'ah,dukkansu suje kawai,bataso zuwa din ba don cikin yazo mata da zaman daki zuwa falo,batason leqawa ko ina,amma hakanan dai tunda yace aje din ta kira wasila tace tazo suje tare tayi mata rakiya.


            Kowa a motarsa zashi,don haka koda ta tashi tafiya bata cewa Zainab din komai ba. Tunda ta lura ta dauki wata gagarumar gaba da ita tun daga ranar da tace zata bita suyi yaji tare,sai itama ta sake kama kanta fiye da baya,don a nata ganin meye nata a ciki?,fadanta dama tsakaninta da mijinta ne,abinda ya sanya harta sanya baki ma shine ganin za'a bar mata wahalar yara,wanda ba ita ta fara tarbiyyarsu ba,so batasan ta ina zata dauko gyara ba.*_ZAZZAFAN ALBISHIR GAREKU MASU KARATU_*😊😊


*NACE BA*👂🏼👂🏼👂🏼


*ZAFAFA BIYAR FA!*


*SABUWAR SHEKARA CE!!!*2024😍😍


*Abun ba'a magana*🥰🥰🥰


*_KUSAN WADANNE ZAFAFAN LABARAN SUKA DAUKO MUKU?_*AMEENATU mamuhghee


KWANKWASON JIMINA Miss xoxo


TSUTSAR NAMA Billynabdul


GUDUN K'ADDARA Huguma


*_kedai ki shirya kawai hajiyata,abun ba'a cewa komai_*


*_akwai zazzafar tattaunawa da zazzafar muhawara_*


*HUGUMA*👑

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post