*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 22
Kusan dukansu a galabaice suke daga ita har raliyan,saboda ba wanda baiji jiki a cikinsu,wannan ya sanya ko hirarma sama sama suke tabata,har zuwa sanda me napep din ya ajjiyesu a qofar gidan. Zainab ce me qwari qwari a jikinsu,ita ta zaro kudin ta miqa masa yayi gaba.
A qofar gidan suka samu rabi ita da wata,su dinma kana kallonsu kasan anji jiki
"Mu shiga kawai,mu shiga" Zainab da takeji kudinta kamar sunfi na kowa yawa ta fada,ko banza tana saka ran samun koda rabin kudinne idan ma duka basu samu ba.
Tun daga soron gidan zakasan cewa tsafta ta tattara kayanta tayi gabas da gidan,tako ina sunyi hannun riga basa hada hanya ba. Hatta da Zainab yau d'ari d'ari takeyi kada ta taka kashin kajin dake karakaina abinsu cikin soron.
Sanda suka amsa sallama kuwa basira data karkace a gefen kwatar data raba gidan biyu tana dahuwar kaza sam bata jiyosu ba. Hasalima waqe waqe take abinta cikin nishadi gami da jin dadi,gefe guda kuma tana jin zuciyarta tayi fess,saboda dawa tayi nama,domin kuwa dubu sha biyar ta karba a dahuwar kazar da duka dukanta naira dubu daya ce,sai tarin tarkacen magungunanta da suke amfani dashi ita da yara da ta yiwa gamje gamje ta zuba suka bada taste mara dadi,wanda shi makamin da zata bada hujjar cewa kazarta tasha hadin maganin mata me inganci.
Cikin rawar jiki da washe baki ta miqe tana musu sannu da zuwa,cikin ranta tana jin yau farar rana ce a tare da ita,don dukkansu ba wanda bata samu kudi dashi ba
"Sannunku da zuwa customer,eh lallai magunguna sunyi aiki, emergency ya kawo wuta yadda ya kamata,sabon hadi kuka zo ayi muku kenan......ahayyeeeeee cassss,saini basira me gyaran turaka......"
"Ke da'alla malama ki yiwa mutane shuru ko na zazzabgeki da mari,macuciya azzaluma,ke kisa kikeyi ma inajin,kin bamu abinda kadan ya rage kwananmu ya qare" baya basira tayi baki galala tana qarewa zainab kallo
"Ban fahimceki ba me kike nufi ne baiwar Allah?"
"Koma meye ki shiga ciki ki lalubo mana kudadenmu da dukiyoyinmu da kika karba billahillazi ko na lahira ya fiki jin dadi"
"Ahto,don ba zamu dauki asara goma da ashirin ba,ba wan ba qanin?" Raliya da qafarta ke rawa saboda rashin qarfin jiki ta fada rai a bace ta biyo bayan abinda zainab ta fada tana kada hannu. Guda basira ta saki tana yarfa hannu gefe guda
"Ni zaki shigowa gida ki yiwa barazana?,to anqi a baki dukiyar taku....nace anqi a baku din duk abinda zakuyi kuyi" bacin rai da kuma ganin samu da rashi duka lokaci daya yasa idanun zainab suka rufe,ta tunzura da maganganun izgilanci da rainin wayon da basira ta fara kwararo musu,sai kawai ta kaiwa basira duka. Cikin tsananin sa'a kuwa ta sameta a fuska,ji kake qummmm......
Wani razanannen ihu basira ta saki tana dafe da fuskarta
"Da kin dauka da wasa mukeyi miki 'yar rainin hankali,maza wuce ki dauko mana kudadenmu tun ban canza miki kamanni ba"
"Ni kika yiwa wannan dukan?"
"Nayi miki kuma na daki banza"
"Wallahi wallahi sai kinsan ba kowa ake tabawa a kwana lafiya ba" basira ta fada tana juyawa afujajan zuwa dakinta
"Duk abinda Zakiya kiyi,ina nan ina dakonki,karki fito saida kudina" zainab din ta fada tana huci gami da jan kujerar tsugunno da basira ta tashi a kai tana ci gaba da hayagaga da kumfar baki.
Har kusan minti biyar shuru babu batun basira suna tsaye carko carko suna maida magana a tsakaninsu. Rabi ce ta dubesu cikin qosawa
"Ko zuwa zamuyi mu tafi matar nan ba ita ba dalilinta fa,kada muje ta shirya mana sharri"
"Wallahi indai ba batan dabo tayi tabar gidan nan ba inda zan motsa sai kudina sun fito,ta gama zamanta ta fito ta sallameni koda kuwa ku tafiya zakuyi,ni na fita bariki wallahi" zainab ta fada tana tafa cinya,tana jin kamar ta jawo basira ta bata kudadenta. Ko minti biyar bata rufa da rufe bakinta aka bubbuga qofar gidan da qarfi,ta bude baki zatayi magana cikin fusata sallamar wata mace me gurbatacciuar hausa ta sauka a kunnensu. Gajeriyar macace sanye da kaki na 'yan sanda(uniform),baqa me fadi da qiba,tana takowa tinqis tinqis
"Hajaju........hajaju woooo" ta fada tana leqe leqe cikin gidan
"Madam,ganinan,bazan iya fitowa ba,ko tashi bazan iya ba,haduwa sukayi suka yimin dukan tsiya,kin ganni a yashe a daki" maganar ta basira dake kwance a daki ta sanyasu kallon kallo a tsakaninsu,suka kasa cewa komai,saidai kowa zuciyarsa ta cika da tsoro
"Aeaeaeae........sune wadacan mata na sakar geda ko?"
"Sune madam,sune" basira ta fada tana nishin qarya
"Angama" macen dan sandan ta fada tana fitowa.
Da daya da daya ta qare musu kallo tana muzurai idanunta a kansu
"Ku wuce mu tafi lafiya Allah ko na saka muku karfi" tace dasu
"Ina zaki kaimu madam?,me kuka mukayi?" Zainab tayi qarfin halin tambaya
"Tambaya na ma kikeyi?,to wa yabaki izinin shigowa gida ku dadaki matar gida kuma ku zauna a ciki ba izininta?"
"Mu bamu daketa ba,kuma hakkinmu mukazo karba" zainab ta amsawa matar
"Hey shut up stupid,naga alama kin fisu kwarin ido......hey. ... Samuel shigo ciki" matar ta fada cikin dan daga murya,nan take saiga matashin dan sandan ya sako kai,ya kuma taimaka mata suka tasa qeyarsu zainab sai police station.
****Tunda yace mata zaizo ta kasa zaune ta kasa.tsugunne,kusan ta manta rabon da faisal yace mata zaizo gidansu,ko yanzun ma tafi gasgata cewa aikin malam ne ya ciyoshi,don kuwa tayi dahuwar borkono tsidugu da rubutu,ta saka wuqa a garwashin wuta me dauke da sunansa,hakanan tasa anyi hatimi wanda aka buda aka rubuta sunansa a tsakiya dukka dai gaba daya domin azalzalo zuciyarsa,sai gashi cikin nasara da bakinsa ya furta zaizo din,bayan yazo din kuma yace akwai maganar da zasuyi wadda jikinta da zuciyarta sunfi gasgata mata cewa magana ce ta aure.
Cikin wancan satin data shaidawa isma'il bata aurenshi yayi haquri yace ba komai Allah ya hada kowa da rabonsa sai jikinta dukka yayi sanyi daga baya,har ta dinga ji cewa kamar tayi gwari,kamar bata kyauta ba,kamar tayi wata asara,amma yanzu faisal ya wanke mata zuciyarta fesss da zancan zuwansa.
Kwalliya ta zauna ta dandasa 'yar ubansu,itama umma bata zauna ba,tana ta aike siyo drinks da sauransu. Ta tatse jakarta yau tas,don hatta kudin da yaa bashir ya bata dazun duka sun narke.
Turaren da malam ya bata hadi da kwalli duka ta dauka tayi amfani dasu,da taga akwai sauran lokaci sai ta dauko carbinta ta zauna tana fuskantar gabas ta soma qarasawa don jiya bata samu kammalawa ba.
Ba dadewa suraja ya shigo yace ana sallama da ita. Kafin umma ta amsa ita ta rigata,ta ajjiye carbinta ta dauki mayafinta da duka duka bai wuce ayi dankwali dashi ba ta yafa ta fito kai tsaye ta wuce umman tana cewa
"Bari na shigo da shi"
Wani sanyi ne ya sauka a ranta sanda ta ganshi a tsaye jikin motarsa yana danne danne, exactly irin mijin da takeso. Kallonta yayi yadan saki murmushi ta maida masa
"Bismillah,ka qaraso" ta fada tana juyawa ciki ya bita a baya yana qare mata kallo,don sosai straight gown din jikinta ta fitar da shape din mazaunanta,uwa uba kuma a yanzun da tasha supplement na qiba ta sake cika,kai ba zakace itace wasila 'yar ficika da ake tsokana ba,don har nankarwa yanzu gareta(stretch marks).
Idanu ta juya masa a shagwabe sannan ta miqe tana fadin
"Ina zuwa" sai tayi cikin gida yayin da shi kuma ya bita da kallo. Bayason su rabu amma kuma bai shirya aurenta ba kwata kwata,yanason macen da tafi wanann quality,duk wasu alamu da zasu nuna budewar idanun mace akwaisu a tattare da ita,duk da a iya saninsa bata taba zina ba,amma wasu abubuwan nata suna nuni ne da qarancin tarbiyya.
Bata zauna ba sai data jere komai,komai tanayi ne cikin gwalangwaso iyayi da sanabe shi kuwa yana biye mata. Hira suka shiga yi kadan kadan,komai a shagwabe take masa hadi da kashe ido da karyar da murya kamar ba zatayi magana ba,abinda yasa ya dinga jin feelings a kanta kenan.
Sama sama yaci abincin,duk da baici da yawa ba amma hakan ya mata dadi,tasan indai ya shiga cikinsa magana ta qare,sai daya nutsa yana goge hannunsa da tissue sannan ya dubeta
"Waseela,inaso muyi magana ta fahimtar juna ni dake"
"Tun dazu nake jira naji maganar ai" ta fada tana sakin murmushi gami da gyara zamanta
"Kome zan fada miki ki dauka muqaddarine daga Allah,kuma shine qaddararmu da ni dake,amma kuma abinda zan fada din bawai yana nufin yankewar mu'amala tsakanina dake ba....." Maganarsa ta qarshe ta sanyaya faduwar gaba,amma ta dake taci gaba da sauraronsa.
"Wasila aurenmu ni dake bazaiyiwu ba,saboda yanxu haka kakata ta dage ta tada rigima harda kwanciya ciwo wai sai na auri naana 'yar qanin mahaifi na" wani mummunan faduwa gabanta yayi,qafafunta sukayi sanyi ta kasa cewa komai saici gaba da tayi da kallonsa
"Kiyi haquri don girman Allah,naso qwarai ni dake mu kasance miji da mata don nayi miki irin gatan da ban taba yiwa kowacce mace...... Amma yanzu ma bata baci ba,ni dake inaso muci gaba da mu'amala,ko meye kikeso zan kashe miki zan kuma baki".
Hawayen da batasan yadda suka samu bane suka balle mata,ta girgiza kai cikin alhini tana dubansa
"Amma me yasa duk lokacin nan baka gayamin ba?,ka barni inata bulayi da zaman jiranka?"
"Banason ranki ya baci ne,kuma da farko na dauka zanshawo kanta ashe abun yafi qarfina,kiyi haquri don Allah karkiga laifina" kasa ci gaba da zama tayi,hankalinta tashe kawai ta miqe tayi cikin gida,tana iya jiyoshi yana kiranta amma bata ko waiwayeshi ba,kiran da hatta umma ta jishi,don tana shiga dakin tana binta a baya itama tana tambayarta ba'asi,saidai kukan da takeyi ya sanya ta gaza bata amsa.
**Da sallama ya shiga sashen bayan barowarsa sashen ruqayya kaman yadda ya saba. Adan zabure Khalil da haneefa suka amsa sallamar tasa. Idanunsa ya sauke a kansu sanda suketa qoqarin daga tv plasma din data fado tayi zaman dabaro a qasan tiles.
Ko da bai tambaya ba yasan abinda suka saba ne suka aikata,wato rikito da Tv din wajen fadace fadacensu da basa qarewa,su biyu kacal amma zaka tsammaci sunyi su goma a sashen
"Waye yayi wannan aikin?" Ya jefa musu tambayar yana tsaresu da ido
"Wallahi shine daddy.......qarya takeyi daddy itace ni ba ruwana,turani tayi kai" dukka sai suka kama masa rantse rantse. Ransa yayi qololuwar baci,ya rasa wanne hukunci zaiyi musu?,yo su idan suna da laifi ma ai kaso mafi yawa laifin na uwarsu ne. Matsawa yayi gaba yasa hannu ua daga tv din,ransa ya sake baci da ganin yadda tayi kwatsa kwatsa
"Ina mamar taku take?" Ya tambayesu qasan ransa yana mamakin ya za'a yi abu me girma irin haka ya fado ya fashe amma baka ji ba ballantana ka fito?
"Ta fita tun da rana" Khalil ya fada kansa tsaye. Tsaiwa yayi cak yana dubansa
"Ta fita kuma?,ina taje?" Ya tambayi yaran
"Bamu sani ba,mudau tace mana mu zauna a nan yanzu zataje ta dawo". Wani mugu mugun bacin rai ne ya sauko masa,a duniya cikin manya manyan abinda ya tsana a wajen matarsa satar fita, saboda shike haifar da wasu matsalolin da mai yiwuwa ba zasu taba gyaruwa ba.
TV din ya maida duk da shi kansa yasan ta tashi a aiki,bata barnar da sukayi bane bama yanxu a gabansa,inda zainab ta sanya qafa ta fita bada izininsa ba tunda rana gashi ana shirye shiryen kiran sallar magariba.
Cikin bacin ran yayi alwala ya wuce sallar magariba yana sanya ran kafin ya dawo ta dawo,saidai ko sanda ya dawo din ba ita ba dalilinta,dole ya tasa qeyar yaran suka wuce sassan ruqayya,don kuwa har sun fara jin yunwa,sunce rabonsu da abinci tun da rana,abind aya sake dugunzumashi kenan. Mutum ne shi da yaqi jinin yunwa ko kadan,wannan ya sanya baya bari a hora kowa da ita,koda baisan mutum ba bare cikin gidansa kuma 'ya'yansa.
Tana zaune tana lazumi,alhassan da alhussain harma da iftee na zaune suna cin indomie da sukace sunan sha'awa ta kunna musu qaramin electric da ta ajjiye dama don saboda su,don wani lokacin qananun dafe dafe sukan iyayi,yaran badai qoqari ba,dafa taliya haka,shinkafa fara,ruwan zafi ruwan tea,tun uban yana fada da qorafi har ya barsu.