Kurman Baƙi Page 27 by Huguma

Kurman Baƙi Page 27 by Huguma

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫


*HUGUMA*


27


*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥


*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_


*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*


*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*


*TSUTSAR NAMA Billynabdul*


*GUDUN K'ADDARA Huguma*


*AMEENATU Mamuhghee*_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*_MARABA  LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_


PAGE 27           

"Ba wani wata dake cike da falala sama da wannan watan,dama ce a gareki ki tsaya ki roqi Allah,basu isa su sanya Allah dole ba,ba wanda ya isa ya sanya Allah ya baki abinda bai cikin rabonki ko qaddararki,indai suna da wannan power din me yasa su basu canza qaddarorinsu ba?,me yasa basu zama masu arziqin da zasufi qarfin zama a soro ko jeji suna saurarar buqatun mutane?,kinsan cewa duk matar data taka taje wajen boka ko dan duba,duk da yanzun an canza musu suna nason zuciya da son rai,ana kiransu da malamai ana kiran DUBA da ISTIHARA,muddin mutum zai gaya miki wani abu da yake a boye, kaza ne zai faru,kaza ne yake faruwa,kaza ne zai faru,siyo kaza siyo zakara siyo akuya rago ki yanka kiyi sadaka,daka borkono qona abu kaza binne abu kaza to SALLARKI TA KWANA ARBA'IN BLANK TAKE EMPTY TAKE cikin littafin ayyukanki,kuma kin sani na sani sallah itace abu na farko da ake fara dubawa cikin ayyukan bawa,idan tayi kyau sauran ayyukan sun karbu,idan ka samu matsala tun daga nan ba zaka wuce bama bare a tafi duba ragowar ayyukanka. Awannan lokacin a cikin mata akwai macen da bata rufa kwana arba'in bataje wajen wani malami akan wata matsala ba,kinga a qididdigar lissafin ayyukanta bata da sallah,ki gayan ran qiyama meye marabarta da ARNE?,tunda duka guraben sallarta sun xama empty silar zuwanta gidan malamai yan duba yan tsubbu da yan bori?"


"Wasila,duk abinda kikaje wajen malami yace miki zaki sameshi kuma kika sameshin,wallahi wallahi ba malaminne yayi sanadiyyar samun da kikayi ba,dama can Allah ya rubuta zaki sameshi,kuma da kinyi haquri bakije ba kina zaune a dakinki rabonki zai taddoki ta halastacciyar hanya ba tare da kin sabi mahaliccinki kinje wajen dan duba ba,wata ne wannan da ake ninka ladan ayyuka,ki zage kiyi addu'a kawai tsakaninki da mahaliccinki shine yafi".


             Sosai jikin wasilan yayi sanyi,kamar dai hankalinta ya fara kaiwa wani wajen daban.*********Yammacine lis lokacin da mata da yawa suka fara nisa wajen sauke abincin buda baki hadi da qoqarin kammala gurin da za'a yi buda bakin. A daidai sannan Zainab na cikin labor room na asibitin cikin matuqar farincikin matsalarta zata kawo qarshe.


"Kinyi inserting wani abu ne?"


"Ai kullum cikin matsi nake,waye zai zauna yaga zama?,mazan nan ka gyara ma amma baka tsira ba ina ga ace baka gyara ba?"


"Gaskiya ne,hakane" nurse din ta fada can qasan ranta tana dariya da mamakin Zainab din.


              Har ta gama hada duk waji scissors da sauran tarkace Zainab din batayi ko gezau ba


"Ki shiga toilet ki wanke abinda kika saka din kizo mu fara" 


"Toh nurse" ta fada da rawar jiki tana wucewa bandakin.


              Bayan ta fito ta zare pant din ta ajjiye sannan ta haye gadon ta bubbuda qafafu kamar yadda nurse din ta umarceta sanda take qoqarin balla razor din da zata kankareta biyu 


"Subhanallahi,meye haka don Allah?" Nurse din ta fada ganin irin cunkoson go slow din da gurin ya tara


"Me kenan?" Zainab din ta tambaya


"Tashi ki sauka kiyi aski,wannan ko inda zan dinke mikin ai bazan gani ba" ta fada tana jan tsaki qasan ranta tare da yin Allah wadai da son kudi itama irin nata.


                  A gaggauce ta saisaye ta dawo ba wani cikakken baiwa wajen kulawar tsafta yayin aski,nurse din itama ta kula da hakan amma ganin itama a gaggauce take da ayin sai kawai taja kujera ta saka face mask ta fara aikinta.


               Sai da aka fara din ta gane Allah daya ne,don zata iya cewa batasan azabar stitches ba don bata taba qaruwa wajen haihuwa ba. Kafin a gama tayi wujiga wujiga,sauqinta daya ta taho da safina wadda batasan me za'a yi ba,tadai ga kawai Zainab din ta shige labor room.


                 Magashiyyan ta kwanta ta kasa motsawa,tana jiyowa ana kiran sallah musulman cikinsu suna tafiya buda baki,ita da azumin Allaha a bakinta amma ta kasa koda kurbar ruwa saboda wata irin azaba dake ratsata kamar ta cire dukka gwiwoyinta zuwa cibiyarta.


*_G I D A_*             Komai sun kammalashi kamar yadda suka saba kafin ayi kiran sallah alhassan da alhussain da sukakai zuminsu daidai da na kowa na zube na jiran kiran sallah wasila na musu dariya 


                Haneefa da khalil ne suka shigo daya yana biye da daya


"Kuzo nan" ruqayya da fitowarta kenan daga daura alwala ta kirasu


"Wasila zuba musu abinci banajin gidan nan Zainab ta wuni"


"Iyalan ci,tunda ba'a gaya miki za'a fita ba basai ki qyalesu ba"


"Ki bari mana wasila" ruqayyan ta fada tana dubanta. Bata sake cewa komai ba ta miqe ta nufi kitchen.


           Gaba daya safina ta kasa tantance me yake faruwa har sai bayan shigarta dakin taji nurse din tana jaddadawa Zainab dokoki. Mamaki ya kamata,itadai tasan ba haihuwa tayi ba bare ace qaruwa tayi,hasalima ko ciki bata dashi,to amma meye hadinta dinki?. Gabanta yadan fadi data tuna wata hira da taji wasu mata sunayi,kenan itama tabi sahun matan dake zuwa a diddinkesu kawai saboda su bawa namiji wani abu ba tare da suna duba makomar lafiyarsu ba?.


               Sanda duka isa gida tamkar 'yar shayi haka ta riqe zainab,takaici ya sake kamata sanda suka isa sassan Zainab din,komai ba bisa kan qa'ida ba,ta tabbatar kuma tsohuwar qazanta ce ba ta jiya ko yau ba. Tun tana aikin tana daurewa harta magantu


"Wai bakwa shara bakwa wanke wanke ne?,kun taba mopping sashen nan kuwa?" Harara Zainab dake fama da azabar radadi ta balla mata


"Ban sani ba,ku me yasa kuka fiya magana ne keda hajiyayye,hala gulmata kuka zama kuyi saboda kalamanku iri daya ne da nata"


"Ba wani gulmarki,inama muka hadu ni?,abunne ya bani mamaki,tunda dai da nazo na leqa sashen anty ruqayya mun gaisa naga ba haka nata sashen yake ba,hakanan farfajiyar gidan nan fes yake ko ina da ina,to sai naki sashen ne zai zama haka?"


"Zanci mutuncinki safina,ki wuce ki bani guri" ta fada a hasale. Baki safinan ta tabe tayi gaba,ba tun yau ba ta sani Sam zainab din bata qaunar a gaya mata gaskiya ko qanqani.


               Sam ruqayya batasan abinda yake faruwa ba,tana can sashenta tana sabgar gabanta,babban abinda yafi damunta kada tasha azumi,kuma Allah ya taimaketa tana samu tana gwadawa wasu lokutan.


               Tsananin son jiki da zallar qazanta ya sanya zainab bata iya shiga ruwa da kyau kamar yadda nurse din ta umarceta,tunda akayi dinkin tafi ganewa ta jabe a zaune a falo,ta lalace tsakanin kallon tv da chart kamar ba azumin ramadan akeyi ba. Tun safina ta murje idanunta,duk wanda yayi ba daidai ba tsakanin khalil da haneefa ubansu takeci,don tace ba zatayi wahalar banza ba,ta sha wahala kafin ta samu tadan kintsa sashen,duk da ba komai ya koma yadda ya dace ace ya kasance din ba,amma ba laifi sassan ya shiga saiti kaso sittin cikin dari,don wani abun idan ya baci baya gyaruwa.


                 Sau tari idan dinkin ya dameta da qaiqayi sosa abinta takeyi,ko tayita mutsu mutsu har sai ta sosheshi,idan kuma yana radadi bankada zaninta takeyi ta kunna qaramar fanka. Sannu a hankali gurin ya fara rurucewa yana sakin wani irin ruwa,amma sanda taga ruwan a pant dinta sai murna ta kamata


"Bayan matsi har ni'ima wannan dinkin yake saukarwa, Alhamdulillah" ta fadi farinciki yana kamata. Batayi wani yunqurin komawa asibiti ba,don nurse din ta gaya mata ta sallameta tunda ta gaya mata ruwan dumi zata dinga shiga,zaibi jikinta basai tazo dubawa ba. Tayi hakanne saboda dokar asibitinsu kora ce ga duk wanda yayi irin wannan,saboda hakan tamkar ya shiga a matsayin cin amana ne da zamba.


********Karfe sha biyun dare ta kammala salllolin darenta da basa wuceta a wanann watan,dukka tana yin addu'o'inta ne akan samun gamawa da duniya lafiya,zaman lafiya a gidanta da mijinta,da shiryuwar yaranta da yaran musulmai gaba daya.


              Sau biyu takanci abinci,irin wannan lokacin da kuma lokacin sahur shine take samu abincin ya riqeta sosai,tana yawaita shan kankana duk suna cikin abinda ke sauqaqa mata azumi(ga mace me ciki dakeson yin azumi ba tare data wahala ba,ta yawaita shan kankana tana taimakawa sosai).


                Har ta zuba abincin a dining saita dinga jin kamar sheshsheqar kuka a dakinsu iftee,ajjiye abincin tayi ta juya zuwa dakin.


            Wasila ce saman abun sallah sanye da hijabi take kuka kariris. Girgiza kai ruqayya tayi ta qarasa shigowa


"Lafiyarki wasila?,da daren nan?"


"Na shiga uku na shiga jarabawar da bansan yaya zanyi da ita ba,ruqayya ki taimakeni,anya ina da sa'a a rayuwata?,anya ina da rabon yin aure?"


"Me ya faru?" Idanunta da sukayi jajur ta daga


"Dazu na biya ta gida muna magana da yaa bashir saiga yaa zaid yazo zasu fita,sai naji yana gayawa umma zasu bincike ne kan yarinyar da zaid din zai kaiwa kudi bayan sallah......na rasa yaa zaid shima ruqayya don Allah ya zanyi?"


"Malamin naki da kikaje gurinsa daxu ya gaza kenan?,ina tarin alqawuran da yayi miki?,ina mijin daya fasalta miki yace zaizo shi zaki aura?" Sak wasila tayi,don bata taba tunanin ruqayya ta ramfota ba


"Kin yadda yanzu sa zancena kan cewa dukkaninsu maqaryata ne?,kin yarda da maganata akan cewa ba zasu iya ba?,me yasa suka gaza baki abinda kike da muradi tuntuni sama da shekara goma kina yawo a tsakaninsu?" Qas da kanta wasila tayi hawaye suna zuba


"Na miki tambaya mana" kai kawai ta iya gyada mata


"Yanzu misali kece mutum yana qarqashinki,kece cinsa shansa tufafinsa,iliminsa lafiyarsa,ke hatta rayuwar da yakeyi yau idan kikace bakiso zata yanke,amma duk kina bashi wadannan abubuwa,shi kuma yana iqirarin yana sonki saidai kuma baya iya miki biyayya,idan kince yayi gabas yamma yakeyi,idan kince yayi yamma kudu yakeyi,dare da rana haka ne,zaki iya ci gaba da bashi dukkan abinda yakeso daidai da wanda yake binki sau da qafa?" Kai ta girgiza alamun a'ah,sai ruqayya ta gyara zamanta


"Sama da haka kikeyiwa Allah ta'addanci shin kin sani?, ya baki lafiya wadda bai bawa bayinsa miliyoyi da suka fiki yi masa biyayya,ya baki ilimi hankali ya kyautata surarki wadda bayinsa masu yawa da suka fiki binsa bai basu ba,kome kikeso ya baki shi kyauta ba da kudinki ba,amma ya shata miki wasu layuka 'yan kadan yace kada ki tsallake sai kikayi kunnen uwar shegu dasu. Kinsan cewa qarya kadai da kikeyi tana iya hanaki samun duk wani alkhairi a rayuwarki?,SHAFA MAI DON KIYI HASKE da magungunan qarin qiba da kike sha kinsan su kadai taka hurumi da dokar Allah ne?,SAKA FARCE KO AJJIYE FARCW A HANNU,QARIN GASHI DAMA KO MEYE da kikeyi bakisan haramun bane?,ba mijinki ba,ko waye zaki yiwa da sunan ado HARAMUNNE HARAMUNNE HARAMUNNE,kuma billahillazi la'ilaha illa huwa yadda annabi yace meyi ba zatashiga aljanna ba bazataji qamshinta ba,idan duk duniya gatanki ne ba wanda ya isa ya sanyaki shiga aljanna,bare uwa uba zuwa wurin malami ko dame yake aiki muddin zai gaya miki abinda yake gaibu ko abinda yake a boye,don wasu suna rudarku da ajjiye qur'ani da litattafan addini da rawani da carbi"


"Nima tunda nake ban taba shiga jeji ko zuwa gurin wani malami me kayan shirka ba sai wanda na ganshi da litattafan addini........"


"Suma mushrikai ne,suna sanya litattafannne saboda ado su jawo hankalin mata masu sauran imani,duk duniya ki gayamin WAYE YASAN GAIBU?,sai Allah shi daya sai kuma annabawa yakan sanar dasu cikin abinda yayi niyyar su sani,SANIN GAIBU SAI ALLAH.......*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥


*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_


*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*


*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*


*TSUTSAR NAMA Billynabdul*


*GUDUN K'ADDARA Huguma*


*AMEENATU Mamuhghee*_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA  LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post