Cuta ta Ɗau Cuta Page 27

Cuta ta Ɗau Cuta Page 27

 *_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*

             _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Ashirin da bakwai_

__________________

*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_


*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*


*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*


*TSUTSAR NAMA Billynabdul*


*GUDUN K'ADDARA Huguma*


*AMEENATU Mamuhghee*_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*_MARABA  LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃________________.......Jin kamar mutum a gefenta da azababben ƙamshin daya gama ɗaure motar ya sata juyawa gefenta kamar a ɗan razane. Wani irin bugawa ƙirjinta yay da ƙarfi har tana ƴar zabura. Sai kuma duk ta daburce cikin lalube take son kama handle ɗin ƙofar amma tama kasa sai dibi-dibi take. Yanda take yi ɗin harga ALLAH ya bashi dariya, dan sai yi take kamar makauniya na laluben hanya. A hankali ya saki wani ɗan gajeren murmushi batare da ya daina abinda yake a laptop ɗin saman cinyarsa ba ya furta, “Awwal muje”.

         Murmushi shima Awwal ya saki cikin ƙunshe dariya. Harga ALLAH yana a cikin matukar farin ciki da yanda al'amarin nan ya kasance haka. Dan jin komai yake ma kamar wani mafarki ko almara gaskiya. To amma ikon ALLAH yafi gaban komai ai. Fara tafiyar motar ya saka Khadijah jin kamar ta fasa kuka. Idanunta cike da ƙwalla ta sake kallonsa a karo na biyu. “Dan ALLAH ku sauke ni zan koma ciki nayi mantuwa”.

        Kusan mintuna biyu kamar bazaice komai ba, ga Awwal kuma baida alamar tsayawa. Itako jikinta sai wani tsuma yake zuciyarta na duka kamar zata fito waje.  

     “Wannan shine gaisuwa?”. Ya furta cikin sassanayar muryarsa mai cike da kamala da dattako batare da ya ɗauke idanunsa a laptop ɗin ba. Gaba ɗaya sai kunya ta lulluɓe Khadijah. Cikin sanyin jiki da jin bata ƙyautaba ta sake ƙasa da kanta. Ai koba komai basu cancanci haka a gareta ba kodan alkairin da suka taɓa mata a rayuwa, dan tun ganin Awwal shima yayan nasa ta ganesa. “Ina yinin ku”. Ta faɗa muryata na ɗan rawar jin kunya. Murmushi ya sake saki mai sanyi hankalinsa dai na ga aikinsa. Shiru bai amsa mata ba har tsawon wasu sakanni, kafin ya rufe laptop ɗin ya ɗago yana mai juyowa gareta. “Mi kika manta acan ɗin?” ya faɗa maimakon amsa mata gaisuwa. 

        A hankali ta ce, “Abu ne!”

    Shima a hankalin ya furta, “Bashi da suna?”

      Shiru ta gagara amsawa. Sai ya zubama yatsun hannunta da taketa faman cuɗawa ido, yanda ƙunshin yama hannun nata ƙyau a take yaji wani iri a ransa. Idanunsa ya kauda da sauri yana jan numfashi. Laptop ɗinsa ya sake buɗewa a can ƙasan maƙoshi yana furta, “Ki faɗi ko miye kika manta ɗin, in har ana saida shi za'a saya miki shi”. 

      Yanzu kam jitai kamar ta tsilga a motar ma kawai ta hutama. Jikinta har wani yamm-yamm yake saboda yanda sautin muryarsa ke wani ratsa mata zuciya. Ga ƙamshin turarensa yay masifar addabarta kamar yanda shima nata ke matuƙar masa daɗi da sakashi a wani yanayi. Jin tai shiru ya sashi ɗan ɗagowa ya kalleta, sosai ta takure jikinta a jikin murfin. Kamar ance ta juyo itama karaf suka haɗa ido. Da sauri ta sake maida kanta. Murmushi kawai ya saki ya ɗauke nasa kan shima. Daga haka babu wanda ya sake cewa komai sai shi da kan amsa waya lokaci-lokaci yana ta aiki a laptop har suka iso ƙofar gidan su Khadijah. Kafin ma Awwal ya gama kashe motar harta buɗe ta fita ita, “Nagode sosai, ALLAH ya saka da alkairi” ta faɗa dai-dai lokacin da take ƙoƙarin rufe motar. Shi dai kallonta kawai yake dan ya fahimci burinta kawai tabar wajen ne, kafin kace mi ko harta faɗa gida cikin sassarfa da harɗewar ƙafafu. Kansa ya ɗan girgiza da sakin guntun murmushi kawai ya maida kansa ga laptop ɗin yana faɗin, “Awwal muje”.

        Cikin girmamawa Awwal dake ta jin daɗi kamar ya taka rawa ya ce, “To Yaya”. 

     Wata ajiyar zuciya mai ƙarfi Khadijah dake jikin ƙofar soron tana leƙensu ta saki tana mai dafe ƙirjinta. Tama rasa wane kalar tunani zatayi akan al'amarin. Kenan mutumin nan daya taimaketa a randa ta baro Adamawa nada alaƙa da mazajen su Zuhrah. UBANGIJI kenan mai hikima. Ita tamayi zaton bazata sake ganinsu ba a rayuwarta har abada. Ashe akwai alaƙa a tsakani duk da dai bamai ƙarfi bace ba... Fara isowar motocin da suka kwaso ƴan dinner ya sata barin soron ta ƙarasa shiga cikin gidan itama...


      Tunda ƴan dinner suka dawo aketa labarin abinda ya faru a hall ɗin yau akan Khadijah da ogan anguna Abaan da kuma matashin saurayi mai suna Yassar. Kowa da yanda yake fassara al'amarin da kuma fatan da yake yi akai. Ita dai Khadijah ko kanzil batace ma kowa ba, ta kuma ji daɗin yanda babu wanda ma yasan ogan angunan ne ya kawota har gida. Bayan sun wuce gidan makwafciyarsu da zasu kwana Ni'ima ke cemata itafa sai taga kamar mutumin nan shine suka kawota ɗin nan dan Awwal bai ɓace mata ba. Shiru Khadijah tai mata taƙi ta tanka, dole Ni'imar ta ƙyaleta itama dai dan tasan halin auntyn nasu in bataso asan abu ba....._______________★


           Watanni shida kenan da faruwar komai daya buɗe sabon littafin babin rayuwa a garesu. Dan tun randa suka baro garin Kano bayan ƙarasa gundile igiyar aurensa da Khadijah komai ya sake kwaɓewa. Dafeeq bai sake tabbatar da yana son Khadijah haka da yawa ba sai a wannan lokaci. Dan ji yake tamkar bazai iya rayuwa babu yarinyar nan ba. Luff Kainaat ta masa tare da komawa gefe tana kwasar dariya. Dan duk yanda ta takalesa suyi faɗa baya tanka mata a lokacin nan saboda halin jiyyar zuciya da yake a ciki. A haka suka cinye wata ɗaya da dawowa. Anan ne fa hankalinta ya fara tashi dan babu abinda tafi buƙata sama da saki a yanzu. Saboda a lissafinta Abaan na gab da shigowa Nigeria ne bikin buɗe katafaren Companyn sa anan Adamawa, ita kuma bata fatan ya dawo ya sameta da auren wani a kanta. A yanzu kam ta tabbatar shiru bazai mata ba, dan haka ta ɗauki salon kissa. Tabbas mace mace ce in har taso nuna kanta a macen, dan kuwa a cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sanyaya yanayin Dafeeq ɗin ya ɗan rage yanayin ƙuncin da yake ciki akan rasa Khadijah . Cikin kissar ta fara hillatar sa da son karɓe takardun hannunsa da wayarta, sai dai fa anan ya nuna mata shima ɗin namiji yake. Dan tamkar ta farkar da shi a nannauyan barcin daya tafi ne na kwana biyu. Rikici suka fara a hankali game da hakan inda fa Kainaat taga lallaɓa Dafeeq bazai kaita ko ina ba sai ɓata mata lokaci, dan dama tana lallaɓashinne saboda bata son wasu mutanenta su san irin auren da tayi. Ƴan sanda tasa su kama Dafeeq, labari kuwa ya dawo masa. Hakan ya sashi tattara inasa-inasa da duk abubuwan nata daya sata ya bar garin Adamawa baki ɗaya. Sai wayar gari Kainaat tayi babu Dafeeq a gidan.

        Haukacewa kawai ya rage Kainaat tayi dan tashin hankali. Dan kuwa duk inda ake tunanin zaije ƴan sanda suka gama bincikawa babu shi babu dalilinsa. Kamar wasa ƙaramar magana ta nema zama babba. Dan kuwa dai har Kano Kainaat tazo neman Dafeeq tare da jami'an tsaron amma sun samu baima zo ba, sai ma birkice masu da mahaifiyarsa tayi akan Kainaat tasan ina ɗanta yake. Tayama za'ai su tafi tare sannan azo ace mata wai ana nemansa. Zance kamar waya ya zama babba. Dan kuwa komai ya juye akan Kainaat ne. Wasu abokan Dafeeq da Kainaat bata san dasu ba sun haɗe kai da Mamansa sun kai ƙara police station akan Kainaat ta sace Dafeeq. Case ɗin dole ya baka mamaki, dan tako ina an gagara fahimtar gaskiya, tunda babu wanda yaga sanda Dafeeq ya gudu. Tuni aka fara tuhumar Kainaat akan laifin kidnapping. Zo kaji yanda ƙananun magana ke tashi, ruɗewa yasa Kainaat kasa kare kanta. A cikin wannan harmutsin nasu har akai bikin buɗe Companyn Abaan batare data tuna ba, dan lokacin ma tana a hannun ƴan sanda. Sai da akayi da kusan sati biyu sai ga ƴan sanda wai sun gano inda Dafeeq yake a wani gida a kulle. Sai dai yace shi ba Kainaat bace ta saceshi wasu mutanene da bai sani ba. An wanke Kainaat daga laifin sannan Nadwa taje ta fiddo ta. Gaba ɗaya Kainaat ta gama fita a hayyacinta da tashin hankali, tsakaninta da Dafeeq sai kallan kallo. Bayan an kaisu asibiti an duba lafiyarsu aka sallamesu suka dawo gida. Suna shigowa Dafeeq ya fara dariyar shaƙiyanci. Cikin ɗage gira sama da kallonta sheƙeƙe ya ce, “Wannan kaɗanne daga makircin da Dafeeq zai iya shiryawa Hajiya Kainaat. Dan haka ya rage naki ki kama kanki, ki bani takardu salin alin na baki sakin ki ko kuma mutafi batch b dan inada plans daban-daban na makirci, idan kuma na ƙulleki a wani wlhy bazaki taɓa iya kwance kanki ba. Wannan ɗin ma nayi niyyar kwancekin ne shiyyasa kaka fito”. Ya ƙare maganar da kashe mata ido cike da salon iskanci.

       Mutuwar tsaye Kainaat tayi a wajen kawai, sai kuma ta rushe da kuka mai cin zuciya. Tabbas ta ɗakkoma kanta CUTA a rayuwarta, amma zata nuna masa itama shegiya ce. Tun daga ranar ta tattarashi ta ajiye gefe, bayan ta bincika cewar Abaan yazo an kammala bikin buɗe Companyn har ya koma taci kuka harda zazzaɓi. Dama dai wannan itace damarta, gashi ta kuɓuce mata, dole sai ta sake sabon plan kenan tunda ɗan iskan yaron nan ya wargaza mata komai. 

       Salon gidan ya canja a watannin da suka cigaba da shuɗawa, kowa yana ƙullama ɗan uwansa ne, duk sanda ta masa batun ya saketa, Shiko zai mata batun ta bashi takardu idan tana buƙatar sakinta, shi bata gabansa takardun kawai yake buƙata. Takan ji kamar ta shake banza ya mutu kawai, sai dai tasan hakan ba abune bamai sauƙi ba dan Dafeeq shegen kansa ne. Dan kuwa duk yanda suke damben tsiyarnan hakan baya hana idan yaji buƙatarsa zuwa gareta ya nema hakkinsa. Haka zasu ci uban fitina su wajiga rayuwar juna ya kuma sami abinda yazo neman. Duk da abin nan bawai ita kaɗai ce a tashin hankali ba, shi kansa a cikin damuwar yake dan kullum kamar sake kunna masa wutar soyayyar Khadijah akeyi, a kuma biye yake da al'amarinta dan koda yaushe yana a hanyar Kano ne a watannin nan kamar mara aikin yi...


        *_WASHE GARI_*


    Alhamdullah yau an wayi gari safiyar ɗaurin aure. Amare sun sha ƙyau iya ƙyau kamar ka sacesu ka gudu. Hakama Khadijah duk da taƙi yarda dai ai mata kwalliya sam. Tadai saka kaya da sukai matuƙar amsar jikinta tai kwanciyarta dan ji take kamar ma zazzaɓi na neman rufeta. Ga ƙirjinta wani irin zutt-zutt yake mata batare data san dalilin hakan ba. Sai kawai ta dinga addu'a a zuciyarta har taji nutsuwa, sai dai jikinta duk babu wani ƙarfin kirki. Zuwa sha biyu layin nasu ya rage hayaniyar maza sai mata dake ta isowa da baƙi. Maza kam sun wuce massalaci sallar juma'a da ga can kuma za'a ɗauro auren...


        A massalaci ana idar da sallar juma'a aka fara ɗaure-ɗauren aurarraki. Dan bana su Ni'ima ɗin bane kawai za'ayi akwai wasu daban. Kusan aure bakwai aka ɗaura. Mijin Zuhrah shi ya fara kiranta ya sanar mata an ɗaura aurarrakin. Cikin sanyin jikin da aka san duk wata amarya a irin wannan lokacin ta sauke wayar a hankali hawaye na silalo mata. Daga ita har Ni'ima a jikin Khadijah dake zaune tsakkiyarsu suka kwanta suna kuka. Hakan ya sakata hawayen ita ma. A take falon ya ɗauki ihun ƙawayensu harda masu guɗa. Suna tsaka da wannan shaƙiyancin wa amaren biyu sai ga wata abokiyar wasan su Khadijahn da aka zo da ita daga kura. Kai tsaye inda Khadijah take ta nufa. Khadijah na lallashin su Zuhrah kawai taji ana mata wanka da turare tare da callara guɗa a kanta dake ratsa mata har tsakkiyar ƙwaƙwalwa........✍️


____________INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_


_KU MARMATSO KUSA...🔊_  _ZAFAFA BIYAR 2024_


_ZAFAFA BIYAR!!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_


_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_


_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_


 _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA  ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_


_________


         _1_

 *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_


           _2_

*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_


              _3_

*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_


        _4_

*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)__GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post