Kurkukun Ƙaddara Book 2 Page 31

Kurkukun Ƙaddara Book 2 Page 31


❤ANEELERH❤

A zaune take saman mirror chair, bata jima da fitowa daga wanka ba, ta zauna ne domin gyara jikinta, ƴar rigar wanka ce a jikinta, ta kasa ta6uka komai hannunta na a ruƙe da wayarta layin hajiya adama take dannawa kira, phone din na fara ringing taji sanyi ya ratsa zuciyarta, bayan hajiya adama tai picking call din Aneelerh ta yi mata sallama, on the other hand muryar Hajiya adama ta bayyana da alamun kasalar bacci"wa'alaikum salam daugher in-low, ya ki ke ya gidan yasu mami da ummi"


  Da fara akan fuskar Aneelerh tace"Lafiya lou mommy, yasu daddy fatan duk kuna lafiya"

  "Alhamdulillah Aneelerh, halan kin ji ni shiru yau ban neme ki ba shiyasa kika kira"

 Cikin jin kunyar maganarta Aneelerh tace"haka ne dama nakira ne don mu gaisa" da zolaya Hajiya adama tace"kodai kin kira ne don ki faɗa min jibi zaki zo ɗaukar baby junaid tun da time ya cika"


  Ƙumshe dariya Aneelerh tayi kamar tana agabanta sai faman noƙe kai take yi, jin tayi shiru yasa Hajiya adama cewa"dama nasan ba zaki faɗamin ba, to ki kwantar da hankalinki, in sha Allah friday zanzo dashi gidan naku"


Abeelerh taji dadin maganarta"nagode mommy, Allah yakaimu lafiya.

  "Nima ngde ki kulamin da kanki, ki kuma gaishe min da su mami, junaid din bacci yake yi zuwa anjima idan ya farka zan kira ki video call ku gaisa, dama yanata sambatu yana ambon shi wurin mommy zaije"

Murmushi Aneelerh tadan saki kamar tana agabanta"zasuji nima agaishe da daddy, " daga nan suka yi sallama da juna.


❤A washe garin ranar Alhamis❤


Wuraren sallar Asuba Unaisah tana zaune saman darduma ta zumbula hijabi, Batul tana akwance agefenta saman dardumar, tun jiya da suka fara sallah da zarar sun gama sai ta kwanta    wahala take ji idan tana yin sallah hada ƙarin rashin sabo har ƙwara ita akan su azeeza masu yin kalle kalle in suna yin sallah, mazan cikinsu sunfi natsuwa shi kanshi Boss man yayi mamakin yadda suka Iya sallah da karatunta ya ƙara jinjinama Unaisah akan ƙoƙarinta, yanzu karatun addinine zasu ƙara koya masu dana boko kafin asanyasu makaranta bayan kammala bincike akansu.


   Tafin hannayenta biyu ta ɗaga sama tanayin addu'a muryarta abuɗe take fadin 


 "Ya Allah ka jiƙan ƴan uwanmu da suka rigamu gidan gaskiya, Ya Allah kakai rahama ƙabarinsu, Ya Allah kabamu ikon cinye jarabawarka, Ya Allah ka bamu haƙuri da juriyar rungumar duk wata ƙaddara da zata riske mu mai kyau ko mara kyau, Ya Allah ka tsare min sauran ƴan uwana da nake atare dasu da sauran al'ummar musulmai, ya Allah ka bamu nasara akan burinmu da muke son cimmawa na ganin mun kawo ƙarshen azzaluman mutanan da suka ƙasƙantar da rayuwarmu suka cutar damu Allah kada ka basu nasarar cigaba da aiwatar da zalunci.........." cikin shessheƙar kuka ta ƙare maganar, hawaye tuni sun wanke fuskarta tunawa da rayuwar sauran ƴan uwansu ƙananun yara da ake cutarwa a cikin kurkukun ƙaddara, tasan ba zasu fasa cin zarafinsu ba suna lalata rayuwarsu kamar yadda su ka yi silar mutuwar ƴar uwar su Unaiza ƴar gidan daddy da Majnoon yaran da ba suji ba basu gani ba.


  Sautin kukan Unaisah ya karaɗe cikin ɗakin, batul ko motsi batayi ba, tunda ta kifa kanta saman darduma bacci mai dadine yai awon gaba da ita ko addu'a bata samu damar yi ba.


  "Bazan ta6a mantawa da wasiƙar da kika bani ba, kuma bazan manta sunan mugun mahaifinki ba, In sha Allah zan ɗaukar maki fansa koda kuwa zan jefa rayuwata ne cikin haɗarin da zaiyi silar mutuwata ne....." cikin karyayyar murya take furta kalaman masu ta6a zuciya, idanuwanta sun kaɗa sunyi jawur, hawaye sun kwanta saman fatar fuskarta har zuwa gaban hijabin dake a jikinta.


 "Ya Allah ka bayyana min daddyna idan yana araye, Inason nasake ganinshi shi kaɗaine nake da burin haɗuwa dashi a duniyar nan" 


Tunda ta fara karanta addu'o'i, yana la6e bakin ƙofar dakinsu Yana sauraronta, basu jima da dawowa daga sallar asuba ba, ya rakosu Sajeed ne tuni sun nufi bedroom dinsu.


  Zuciyarshi ta karaya da jin kalamanta, abubuwa dayawa sun so su rikitar dashi, kamar yarda take zubar hawaye haka shima yake zubar da su saman fuskarshi, farar jallabiyace a jikin shi ya sanya mask akan fuskarshi, Ji yake kamar ya faɗa ɗakin Ya rungumota a jikinshi, duk a tunaninshi Unaisah ta manta dashi ashe ba haka bane yana aranta har addu'a tana yi mashi, haƙiƙa yayi farin ciki mara misaltuwa, cikin sanɗa Ya juya zaibar ƙofar ɗakinsu kwatsam muryar Jemimah ta tona mashi asiri da ƙarfi ta furta"BOSS MAN!!!" cak Ya dakata da tafiya, hatta Unaisah dake a ɗaki saida taji sautin sunanshi da jemaimah ta ambata, aiko da sauri ta miƙe ta nufi kofar fitowa daga ɗakin.


  A hankali Ya waiwaya baya yana duban jemimah, tasha dogon hijabi ajikinta kamar zatayi tuntube da gudu ta nufo shi, Azeeza ma ta fito tabiyo bayanta itama hijabin ne a jikinta.


  Kallon da yake binsu dashi tamkar kallon da uba yake yiwa ƴa'ƴanshi ne, saboda yana matuƙar ƙaunar yaran ya dauke su kamar jininsa, musamman yadda suka fara nuna mashi yarda, Jiya izuwa yau sun saki jiki dashi, duk in zai gifta sai sun ambaci sunanshi kamar su suka raɗa mashi.


  Jemimah na ƙarasowa ya sanya hannu biyu ya ɗagata sama, ta kama tiƙar dariya tana fadin"dan Allah kada ka sauke ni ƙasa"


 Fuskarshi dauke da murmushi yace"raini ya fara shiga tsakanina dake ko? Tun jiya badama kiga na gifta sai kin ƙwala min kira kamar wani tsaran wasanki, bakisan ni baba ba ne"?


  Tace"to aini daɗin sunan nake ji, Boss man shiyasa nake kira," tana magana yana kallon jajayen kumatunta bakomai yake tunawa ba face Angel ɗinsa, lokacin ƙuruciyarta yaci wuyarta yakuma ji dadin shiriritarta.


  "Jemimah Ina fata yau kinyi sallah ta hankali, don jiya Azeeza ta faɗa min abun kunyar da kika yi" ya faɗa yana sauketa ƙasa, duban Azeeza yai har ya miƙa hannu zai ɗauke ta ganin ta tsare shi da ido yayi tunani ko itama so takeyi ya daga ta sama, da sauri ta maƙe mashi kafaɗa tana fadin"ai ni ba ƙarama bace, Na girmeta da shekaru" dariyace ta kubce ma Boss man.


 "Oh saboda kin girmeta shine bakyaso in ɗauke ki? To aini a wurina jinjira nake kallonki" ya faɗa tare da ɗaukarta ya ruƙeta a hannunshi, Kunyar duniya ta cika Azeeza sai faman noƙe mashi kai take Yi.


  "Kasan Allah Boss man itama Azeeza bata Iya sallaba, ko karatun sallah ma bata iyaba, idan nayi ƙarya kace ta maimaita maka Rabbighfir li" tuntsirewa yai da dariya.


Ran Azeeza ya 6aci tace"wallahi ƙarya take yi min, ai acikin zuciya nake yin karatun sallah tayaya har tasan abunda nake faɗi acikin zuciyata" gwalo jemimah tayi mata"oho dai, ni dai duk rashin Iya sallana nasan yadda ake karatun sallah"


 Idanuwan Azeeza tuni sun cicciko da ƙwalla, boss man yace"badai kuka zakiyi min ba"? Cikin shessheƙar kuka tace"wallahi ƙarya take yi min na iya karatun sallah, kaji na rantse maka, idan ma kanaso sai in faɗa maka kaji, itace fa bata Iya komai ba, jiya muna sallar isha'i tana buga min dundu abayana, kuma ban rama ba" 


 Kwantar da kanta yai saman kafaɗar shi haɗi da daura hannun shi saman kanta Yana lallashinta.


  Idanuwanshi akan jemimah dake ta dariya, dama tun jiya da yayi tozali da fuskarta ranshi ya bashi daƙyar in bata iya rashin ji ba, kamar dai Angel dinsa da tana ƙarama .


 Lallashinta yai"yi hakuri my daughter, kuruciya ke damunta dama kince min kin girmeta don haka inaso ki ruƙe girmanki kada ki biye mata, idan tayi ba dai dai ba kiyi mata nasiha a matsayinki na babba mai hankali da tunani, in sha Allah wata rana zata daina ne" tunda ya fara magana Azeeza take amsa mashi da toh, jemimah kuwa sai faman ta6e mashi baki take yi hada ruƙe qugu, tana fadin"tab ita ɗin zata min nasiha, Allah ya kiyaye, ai ni bana jin maganar kowa idan bata Unaisa ba"


  Mamaki jemimah take bashi gata ƴar ƙarama idan tana magana sai kayi tsammanin ta ɗare shekarunta. 


 Sauke Azeeza yai saman floor, yace da ita"ki ruke hannun ƴar uwarki ku tafi ɗaki, da anjima idan nashigo zamuyi magana" ta amsa mashi da toh nagode, kafin ta ruƙo hannun jemimah tuni ta watsa da gudu ta nufi hanyar komawa ɗakinsu duk don kada azeeza ta ruƙe hannunta.


  Murmushi ya saki yayin da yake bin bayansu da kallo, Har ya ɗaga ƙafa zai nufi hanyar fita ɗakin, Muryar Unaisah ta dakatar dashi"Boss" A hankali ya juya baya yana dubanta tun ɗazu tana tsaye tana kallon su, sai da ta bari su Azeeza sun tafi tukunna ta yanke shawarar yi mashi magana.


  Ta wanke hawayen fuskarta, tana tafiya hijabinta na ja da ƙasa, har gabanshi ta ƙarasa ta tsaya, tsananin tausayinta ne Ya kamashi, ji yake kamar ya rungumeta koya rage radadin da yake ji acikin zuciyarshi, sai dai ba halin yin hakan yasan yadda take da masifa idan Ya kuskura yai hugging dinta tsaf zata mare shi tunda batasan wanene shi ba.


  Ido cikin ido suke kallon juna, tsawon mintuna kafin ta numfasa tace"ina kwana? Ka tashi lafiya? ya fama da mu"

 Cikin sanyin murya yace"lafiyalou Unaisah, ya akai naga idanuwanki sun canza launi, ko baki da lafiya ne"?


 Girgiza mashi kai tai, cikin disasshiyar murya ta furta"lafiyata qalou, kasalar bacci ce,"


 Jinjina kanshi ya ɗanyi, ji take kamar tace mashi ya cire face mask dinshi sai dai bata son ta takura mashi don ta fuskanci bayason su san wanene shi.


  "Kin tsare ni da ido kina kallona ko akwai wani abu da kike son fada min ne"?


  Murmushin gefen fuska ta saki, Har dimples dinta suka lotsa,


  "Dan Allah taimako nakeso kayi min sai dai bani da ko sisi a hannuna"

  "Kada kiji komai ki faɗi koma menene zanyi maki shi in sha Allah"


 Tana faman noƙe kai tace"um dama waya ce da Aunty laura ta bani kyauta ɗaya daga cikin likitocin da suka kula da lafiyarmu a america, to wayar babu sim aciki gashi inason in fara amfani da ita"


  ta faɗa tana duban fuskarshi, ya natsu yana sauraronta idan tana magana kuruciyarta yake tunawa, yarinyar data sanya shi ciwon kai da zazza6i, cikin ikon Allah yanzu ta ƙara girma ta zama kamilar mace ta mallakin hankalinta.


  "Sim kaɗai kike buƙata"? Girgiza mashi kai tayi"a'a, da Allah kada kace na takura maka, " aranshi ya ayyana takura kuma ta nawa My Angel, nida nayi jinya gadon asibiti saboda ke" 


 "Cikin Kayan da aka tsunto mu da su a daji, akwai backpack ɗina inason jakar, gadonmu ce bansani ba ko sojoji sun haɗo mana da su" ta tambaya tana dubanshi.


  "Duk wani abu naku yana atare damu, saboda muna buƙatar abubuwan da zasu taimaka mana wurin yin bincike tamkar shaidune agare mu, amma kada ki damu zan ɗauko maki backpack din, da anjima zan shigo maki da ita tare da sim din da zaki sama wayar" wani irin farin cikine Ya lullu6e Unaisah, godiya tadinga yi mashi, yace mata yaji daɗin ganin farin cikinta, juyawa tayi da niyar ta koma ɗaki, hijab din jikinta dake jan ƙasa ta harɗe ƙasan takalmin ƙafarta, gaba ɗaya ta tafi zata kife kasa da zafin nama Boss man Ya ruƙo damtse hannunta Ya janyota ta faɗa saman kirjinsa, har saida taji gabanta ya fadi, ƙanƙameta yayi da hannayensa biyu daya zagayo dasu ta bayanta, Jikinta yai wani irin sanyi kamar wadda aka zare ma laka, bawan Allah tunda ya rungumeta yai tighting dinta kamar karya saketa, ita kanta takasa raba jikinta daga nashi, saima hannayenta data zagayo dasu saman bayanshi, ta ƙankameshi, Jini ɗaya ba wasa ba, sai faman sauke ajiyar zuciya suke yi at same time, batasan ya akai ba ta tsinci kanta da jin hawaye sun cicciko idonta, shi kuwa tuni sun wanke face mask dinshi.A hankali yake ɗan bubbuga bayanta kamar yana lallashinta, tsawon shekaru rabon daya ji ɗumin jikinta anashi, bazai ta6a manta ƙaddarar data afka masu ba, wadda tayi silar rabuwarsu, bazai ta6a manta sautin shesshekar kukanta da muryarta a lokacin da yake gudu dasu cikin mota tana daddy hancina jini, haka zalika bazai ta6a manta lokacin da ya jefar da ita cikin ruwa ba duk don ya ceci rayuwarta Sai gashi cikin ikon Allah ta rayu Allah ya tsare mashi ita, Allah kaɗai yasan irin wahalhalun rayuwan data fuskanta da ƙananun shekarunta.....


 Kamar yadda yake tariyo rayuwarsu haka itama take tunano daddynta, ji take kamar shine ya rungumeta, shiyasa ta ƙara narke mashi tayi lamo saman wide chest dinshi...... 


Gaba ɗayansu sun shiga yanayi mara misaltuwa, ba zato ba tsammani Boss Man yaji dirar wani abu saman bayanshi, da sauri ya ɗago da kanshi idanuwan shi sun canza launi sun kada jawur kamar mai fama da ciwon ido, yayi mamakin ganin pillow da aka jefo mashi ya fadi ƙasa, da sauri ya ɗaga ido sama don ganin wanene ya wurgo mashi pillow saman bayanshi, karaf idanuwan shi suka sauka akan Danish dake tsaye can second floor, hannun shi ruƙe da wani pillown Yana niyar ƙara jeho mashi, fitowar shi kenan daga ɗaki idanuwanshi suka hango mashi Angel ɗinsa rungume da wani ƙato, shine fa yaje ɗaki ya ɗauko fululluka har biyu Ya jeho mashi ɗaya.


   Ya haɗe fuska babu annuri, kayan bacci ne ajikinshi riga da wando launin pink sunyi bala'en yi mashi kyau.


   Harara ya watsa ma boss man, ganin Angel taki barin ƙirjin mutumin yasa shi ƙara daddagewa ya wurgo mata pillow, da sauri boss man Ya tarbe pillown a hannun shi, Lamarin ya ɗaure mashi kai, sai yanzu ya gane dalilin dayasa yaron yaƙi sakar mashi fuska tun jiya yake daure mashi fuska, ashe kishi ne ke damun shi.


  "Unaisah"! Jin boss man ya ambaci sunanta yasa ta ɗago da kanta tana kallon shi, mamaki ne ya kamata ganin pillow a hannun shi, da ido yai mata nuna da bayanta, da sauri ta juya don ganin wanene, a tsaye ta hango shi ya ruƙe qugu yana aiko masu da harara.


  Batasan sa'adda ta tuntsire da dariya hada dafe ciki,

 da zolaya boss man yace"kishine ya addabe shi shiyasa yake jifar mu da pillow, faɗa min meke a tsakaninki dashi.


  Tana dariya tace"babu komai, shaƙuwace a tsakaninmu, baya son yaganni tare da wani idan ba ƴan uwanmu ba, haushi yake ji" 


  "Kice ƙwara in lalla6a in gudu, tunkan ya sauko don wannan har buguna zai Iyayi, " ya fada tare da damƙa mata pillow din hannun shi, Ya juya da sauri ya nufi ƙofar fita Yana faman sakin murmushi, bai ta6a ganin namiji mai kishi ba irin Danish.


  Zukunnawa tayi ƙasa ta ɗauki ɗayan pillow, ta haɗa dana hannunta, ta nufi upstairs, Har tsoron tunkarar shi take Ji, saboda yadda ya kumbura fuska, soft red lips dinsa sunyi suntum da su"

  Koda ta haye up din, taga Ya dunƙule hannu kamar zai nausheta, wurga mashi pillows din tayi saman faffadan kirjinshi, da gudu ta sauko down tana tiƙar dariya, akan idonta ya tattara pillows din ya nufi dakinshi ya shige.


 Yau da wuri suka yi breakfast dinsu, saboda gyaran jikin da ummi zatayi masu.


A Katafaren Home beauty station ɗin dake a cikin part dinsu, saboda su aka tadani komai na cikinsa, ɗakin Ya haɗu, bangon dakin beauty shelf ne An jera Kayan gyaran jiki kala kala, dana gyaran gashi acikin kowani shelf, hada foot care product and skin care product, Ga wani faskeken mirror a jikin bango, daga gabanshi wasu hadaddun kujerune kusan guda takwas, A saman kujerun kowa Ya samu wuri Ya zauna su shidda ne matan dake acikinsu, banda mazan tun bayan da suka kammala yin breakfast suka tafi ɗaukar karatu a inda suke Yin sallah. Suma matan acan za'a dinga yi masu karatu.


Kowaccensu tana sanye da bathrobe a jikinta, Ummi ce ta basu rigunan, saboda da taji daɗin gyara masu sumar kansu.


Kujerar farko Unaisah ce zaune asamanta, ta biyu batul ce akusa da ita, sai Parveen itama ta hakimce saman tata kujerar, daga gefenta Jemimah da Azeeza ne saman nasu kujerun bayan su sai Hannah.


sun natsu suna kallon faces dinsu ta cikin madubi sai faman sakar ma juna murmushi suke yi kamar wasu zautattu, daɗi suke ji za'a gyara masu sumar kansu, har sun fara imaginning din kyawun da zasuyi


babu mai magana acikin su, saboda ummi tana acikin dakin ta hanasu surutu 


  tana a sanye da dogon wando ƴar rigar data sanya daƙyar ta rufe cibinta, babu mayafi akanta.


  "Dawa zamu fara" ta faɗa tana dubansu, har suna haɗa baki wurin furta Ni,

   "bari in za6a da kaina" ta fada tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, a ƙarshe ta tsayar da idonta Kan Unaisah da Batul, daku zan fara, saboda yawan sumar kanku" saukowa su ka yi daga saman kujerun, ta juya ta nufi Corner din da Sink Yake, gefen shi beauty cabinet ne mai ɗauke da jerin shampoo da conditioner da suran mayukan gyaran gashi.


    Taci baƙar wahala wurin gyara masu gashi, musamman mutun biyun nan Unaisah da Batul, saboda yawan gashinsu ga tsawo, da ruwan zafi ta jika sumar bayan ta jiƙu ta shafa shampoo ta cuccuɗa ko'ina na gashin, bayan ta wanke shampoo din ta sanya conditioner na tsawon mintuna kafin ta wanketa, tayi masu amfani da Hair dryer ta busar masu da sumar kansu, ta fara shafa masu smoothing serum ta ɗauki comb taci gaba da sharce gashin, tunkafin ta kammala take santin kyawun sumar kansu, bayan ta gama sharce gashin ta kwarara masu hair oils kala daban daban saman sumar taci gaba da cuɗasu da hannuwanta, tuni gashin ya ciza launin shi dark brown sai ƙyalli yake yi da ɗaukar ido, ƙamshin hair oils din data shafa masu Ya cika hancinansu.


  Lokacin da suka kalli sumar kansu ta cikin madubi, Ihun farin ciki suka saki suna faman yi mata godiya tace su koma zu zauna, bata gama gyara masu ba, su Azeeza sunyi zuru suna jiran suma ayi masu, sai faman santin su Unaisah da Batul suke Yi har suna fadin suma kalar nasu za'ayi masu.


    Ummi tayi ƙoƙari wurin gyara su, Yara kamar ƴa'ƴan wani shege maiji da raina, saida tayi amfani da almakashi ta datse sumar kansu ta rage tsayinta ta dawo dai dai tsakiyar bayansu, hair style din da tayima Batul da Unaisah Triple twist half up ne, Bayan ta gama dasu ta bi sauran ɗaya bayan ɗaya ta wanke masu sumar kansu kamar yadda tayi masu Unaisah haka suma tayi masu banbancin wurin hair style ne, saida ta miƙar masu da gashinsu ta hanyar yin amfani da Straightener, kafin ta ɗaure ma Azeeza da Jemimah gashinsu da ribbom guda biyu gefe da gefe wutsiyar gashin ta sauko har saman kafaɗunsu.


  Duk wannan gayun da akayi masu, Jemimah bata gode ba, ta sanya rigima akan sai an maida launin gashinta kalar nasu Batul, Ummi taci dariya, bata ta6a tsammanin zata ji ƙaunar yaran ba sai yau, su kansu sunyi mamakin yadda ta dage damtse wurin Yi masu hidima, Abu kamar wasa Jemimah ta fashe masu da kuka, ita damuwarta launin gashinsu Yafi nasu kyau, da ita da azeeza sumar kansu blonde ne kalar na turawa, ita Azeeza bata damu ba sai murna take yi an gyara mata gashi, jemimah daice ta matsa lamba, ummi harta fara tunanin ta canza mata launin gashin da yake suna da Hair dye cikin jerin Kayan gyaran gashin su, Unaisah ce tace abar mata launin gashin kanta, saboda yana dakyau ba lallaima idan aka maida mata kalar nasu yayi kyau ba," daƙyar suka lallashi Jamimah tadaina yi masu kuka.


   Tsawon lokaci kafin Ummi ta kammala Gyara su, hatta skin dinsu da akaifunsu da tafukan ƙafafuwansu duk saida ta gyara masu, ko'ina ka kalla na  jikinsu saiya burgeka, kamar basu ta6a shan wahalar rayuwa ba, tun bayan da aka gama kowannansu Ya koma bedroom dinshi, bacci mai nauyi ya dauke su, duk don saboda gyaran gashin da akayi masu kada Ya 6ace yasa suka kwanta ta rubda ciki.


*OBIE ESTATE*


Danƙara danƙara motocine masu numfashi suke ta kurɗaɗowa ta cikin babban gate din Obie Estate a ƙalla sunkai goma sha wani abu gaba da bayansu motocin fusatattun sojoji ne sun mimmiƙe tsaitsaye hannayensu ruƙe da manyan bindigu, jiniyar motocin jami'an ta karaɗe ko'ina na yankin, da matsakaicin gudu suka haura saman titin da zai sada da su da Airport, Motar farko zungureriya tana ɗauke da dattijon arziƙi tare da Dr.Jaz, mota ta biyu sanate president lateef ne zaune a mazaunin baya shi da Iyalansa Hajiya madina da ya'yan ta biyu Ziyad da zuhra, Mota ta uku Hajiya saratu ce a cikinta tare da twins zayn da zaid, da shi kanshi pravin din, Motar bayansu Sir mubarak ne tare da Hajiya Turai, daga motarsu sai ta sauran ƴan uwa da abokanan arziki da suka hallara domin zuwa tarban babban baƙonsu, kowan nan su yayi shiga ta alfarma, mazan cikinsu shaddojine ajikinsu, matan kuma wankan abaya suka ɗauka, har sun kusa isa Airport din ba zato ba tsammani suka soma hango wasu hamshaƙan motocin daban sun biyo ta titin da zai jagorance ka zuwa Aso Villa, Ƙarshen Haɗuwa ta glass din motocinsu suke hangen su, tunkafin suga su wanene acikin motocin ransu ya basu Mr.president ne tare da muƙarrabansa shima yazo tarban ɗan uwan nashi, abun yayi matuƙar ƙayatar dasu, basu yi tsammani zai halacci zuwa Airport din ba, zuwan bazata yai masu, Motocin shugaban ƙasa na ƙarasowa suka haɗe da nasu motocin Yawan adadin motocin suka ƙaru, hankalin kowannansu akwance yake sun ci burin haɗuwa da babban baƙon nasu, duk sun ƙagara su ƙarasa Airport din.


"Ziyad Ina fata baka faɗa ma Ƴan uwanka ƴan jarida ba ko"? Sanate lateef ne yai maganar a yayin da yake zaune gefen Hajiya madina a back seat na motarsu.


 Ziyad na murmushi yace"ai daddy tuni na sanar dasu ku jura zuwansu kawai"

   Buɗe baki sanate yai"amma dai wasa kake min ko? Kadai san Kawun naka bai san taron ƴan jarida,"


  Ziyad na sakin murmushin shaƙiyanci ya zuge mashi glass din motarsu, har sai da gaban Senate yadan buga ganin motocin ƴan jarida birjik sai faman sharara gudu suke yi har sunfi nasu motocin sauri duk dan su ƙarasa su dauki rahoto.

  Dafe kai Senate yai"ziyad kana da matsala, yanzu menene na gayyatar waɗannan mutanan ina amfanin yin hakan"?


 Sai lokacin Hajiya madina ta sanya masu baki a maganarsu"ai indai ziyad ne dama ka daina damun kanka, ka riga da kasan halinshi, jikin shi har 6ari yake yi idan ya samu abun daukar rahoto"


 Dariya ziyad yai jin abunda mommyn shi tace, shi dai senate lamarin ya ɗaure mashi kai.


Kusan atare motocin suka yi parking a wurin da aka tadana domin ajiye motoci, jami'an suka diddiro daga saman motocinsu suka soma bubbuɗe masu murfin motocin, ɗaya bayan ɗaya suke fitowa, Ƴan jaridan ma suka fito Hannayensu ruƙe da Cameras, wasu a wuya suka rataya cameran su, wasu kuma sun ruƙe welcome sign a hannun su duk da akwai tazara a tsakanin su saboda mugun tsaron dake wurin dan ma yan jarida ne masu naci da ba wanda ya isa ya tsaya a wurin.


Lokacin da Sharafudden Ya fito daga cikin Motarshi gaba ɗaya ido Ya dawo kanshi, mutumin babu wasa a fuskarshi, kamanninshi sak da mahaifinshi Obinna, launin fatarsu ne ba ɗayaba, Yana da hasken fata sai dai bai kai na Obie ba, nashi yadan yi duhu, fatarshi taji hutu, babban mutunne mai cikar kamala, ya iya dattako ga wadatar arziƙi, kusan duka halayan Owais shiya ɗauko babu abunda ya bari mashi, hatta kyawun fuskarshi na mahaifinshi ne, Yana da tsawo da fadin ƙirji, wankan suit ne a jikinshi, ya manna farin glass a idonshi, security detail din dake take mashi baya sunyi mashi rumfa, Cikin takun ƙasaita Ya nufi mahaifinshi dake ta faman aiko mashi da sakon murmushi, rungume juna sukayi, ƴan jarida kamar jira suke yi nan fa suka fara daukarsu hotuna, bubbuga bayanshi obie yai da hannun shi yana fadin"Nayi kewarka son, tsawon lokaci ka hanani ganinka sai yau, da yake ɗan uwanka zaizo yanzu zan dinga ganinka akai akai"dagowa yai da kanshi daƙyar yake murmushi kamar yana yi mashi wahala ya motsa baki ya furta"aymin afwa baba, kana araina koba dan shi ba, nayi niyar shigowa gidan yau saboda nayi kewarka" obie yaji dadin kalamanshi, da hannu ya nuna mashi sauran ƴan uwanshi, Jiki na rawa dr jazz da twins suka ƙaraso suna gaishe shi cikin girmamawa, ɗaya bayan ɗaya yake amsa masu, bayan sun kammala ƴan gaishe gaishen nasu, suka ɗunguma gaba ɗayansu suka shiga Arrival area din, duk Inda suka gifta ma'aikatan airport din sara masu suke yi, sau da ƙafa suke Yi masu biyayya, a katafaren waiting area kowannansu Ya samu wuri Ya zauna sun natsu suna jiran ƙarasowar jirgin baƙon nasu.


  Jami'an suna a kewaye da su, Ƴan jaridan ma suna a tsaitsaye acen baya suna jiran Ya ƙaraso don su fara ɗaukar rahoto.


Vip Area din Ya cika maƙil da ɗaruruwan mutane wasu ma daga baya suka zo, Ko'ina ka kalla kawunan Bil'adama ne, kowanene wannan Babban baƙon daya tara dubban jama'a dake cike da ɗaukin ganinshi? lallai ba ƙaramin mai farin jini bane, shi ɗin na musamman ne.


Agogon bangon Nigeria Yana bugawa ƙarfe goma shabiyu adai dai wannan lokacin sautin katafaren jirgin shugaban ƙasar dake shawagi bisa sararin samaniya Ya karaɗe Kunnuwan mutane, gaba ɗaya ransu ya basu cewar jirginshi ne Hakan yasa su ka fara sakin murmushin farin ciki,


A katafaren Filin tashi da safkar jirage masu zaman kansu, Jet din ya sauka a hankali Yake bin runway har Ya ƙaraso dai dai Inda zai dakata, tsawon mintuna kafin ƙofar Jirgin ta buɗe matattakalar shi ta sauko ƙasa, hadadden red carpet, ma'aikatan airport din suka shimfiɗa mashi tun daga bakin stair din har izuwa entry din Vip area, mutanan dake aciki tuni sun mimmiƙe suna atsaitsaye curko curko suna jiran ƙarasowarshi.


Musamman Ƙungiyar masu daukar hoto da 'yan jarida sun Harzuƙa Jira suke kawai Ya duro da ƙafarshi waje don su fara haska shi da kyamarorinsu kowa burinshi ya kasance mutun na farko da zai fara ƙyalla mashi camera, 


Jami'an sun kewaye Jirgin saboda su bashi tsaro, Maimakon mutumin da suke tsammani Ya fara saukowa sai suka ga Security detail dinshi Royal Canadian Mounted Polices suna fitowa daga cikin jirgin, zaratan Maza Ƙarfafa Masu Ƙira Irinta zakuna, Sanye Cikin kakinsu, Qugunansu a soke da bindigu Pistols, A bakin stairs ɗin Suka Tsaya sun haɗe da sojojin Nigeria dake a bakin jirgin.


  Lokacin da Ya zuro ƙafarshi dake sanye cikin wasu hadaddun leather shoe Hankalin kowa ya dawo kanshi, tabarakallahu ahsanul khalikin, ƴan jarida har goga kafada suke Yi garin yin saurin haska shi da camera, A hankali Ya ƙarasa fitowa,  Babban mutunne ya fito sanye Cikin tailored suit, sun zauna mashi, Sunbi shape ɗin Jikinshi, Fari ne Ba irin sosai ɗinnan ba, daga ganin fatarshi hutu ya zauna mashi, kanshi babu hula, Sai ka rantse da Allah matashin saurayi ne, saboda haɗuwarshi da iya ɗaukar wankanshi, sumar kanshi akwance take tasha gyara, tsakiyar gashin kan nashi akwai siraran hurhurar gado, da akayi gayu da ita, ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,Yana da tsayin fuska, Manyan idanuwa, ga dogon hanci, bakowa bane wannan face PRIME MINISTER HATEEM OBINNA! namijin zaki uban dawa, ɗaya tamkar da dubu, gwarzon Namiji mai ɗauke da suffofin jagwaranci, mutun mai daraja da ƙima a idon al'umma. yana da farin jini ba Iya kasarshi ba a ƙasashe da dama rububin shi suke Yi saboda kyawawan ɗabi'unshi da halayanshi, mutumin maƙurane a 6angaren Kyau, ilmin addini dana zamani, uwa uba Ya fito daga babban Gida, kallo ɗaya zakayi mashi ka shaida ruwa biyune, gashi Hamshaƙin Mai kuɗi Ya shahara Aduniya.


  Cikin dattako Yake taka matakalar benan, All eyes on him mutanen dake can nesa suna hangenshi kamar zasu ƙetare Iyakarsu su faɗo gabanshi donsu Tarbe shi, Fitowarshi Keda Wuya Uwar Gidan shi Gimbiya Mujeedat ta sauko daga cikin jirgin, nan fa kallo Ya koma Kanta, Hankalin maza ya tashi, Ko mace ta kalleta saita girgiza balle Namiji, ahaka ma ta sanya Arab gown launin fara ajikinta, Ta rufe fuskarta da Niqab, dirin Jikinta Yafi komai jan hankali, da kuma kyawawan idanuwanta da suka bayyana sun sha uban ado farare ƙyal, price din takalman ƙafarta kaɗai sun ishi wani talakan jari, hatta hannayanta Safa ce ta sanya, Mijinta yana matuƙar jin kishinta shiyasa duk inda zasuje da niƙab a fuskarta, bayan ta fito, matasan ƴa'ƴansu biyu suka fito  tare da Faryat ƴar gidan saratu, sunyi shiga kala ɗaya data mahaifiyarsu dukansu matane, dogaye masu kyan sura, atare dasu akwai advisors dinsa, manyan mutane masu bashi shawara, sun hada da chief of staff, national security advisor, Fararen turawa sun ɗauki wankan black suit, kowan nan su ya manna sunglases a idanuwanshi, ajere suke taka shimfiɗaɗɗan red carpet din da zai jagorance su zuwa Vip arrival area, lokacin da suka karasa jama'a kamar zasu haɗiyesu tsabar murnan ganinsu, Bawan Allah bai nufi kowa ba sai Mahaifinshi Obinna, Hannu bibbiyu ya rungume shi ajikinshi, tsawon shekara basu ganaba sai yau da Allah Ya nufa zai samu damar zuwa Nigeria, Wata irin runguma yayi ma Obinna, gaba daya mutane suka sanya ihu suna tafa masu, Ƴan jarida Sun dage sai daukarsu hoto suke Yi, sautin ƙarar kyamarorinsu ya cika airport din ji kake kyat kyat, Gimbiya Mujeedat,  da fara'a akan fuskarta ta rungume Hajiya saratu, kamar ƴan uwan juna, Faryat kuwa da gudu ta faɗa jikin Zayn tana dariya, bayan ta rungume shi ta kuma rungume Zaid, sai daɗi take ji taga ƴan uwanta, Nazli da Yazrin kuwa kamar basu son ganin mutane, dama suna da wuyar sha'ani har ƙwara Yazrin tafi sakin fuska akan Ƴar uwarta nazli, daƙyar suke rungumar ƴan uwan mahaifinsu, izzace ta bala'e suke fama da ita, su ala dole ga jinin sarautar daular larabawa, Bayan prime minister Ya saki mahaifinshi, Ya rungume ya'yanshi sharafudden kamar zasu koma mutun ɗaya tsabar yadda suka hade jikinsu. Tuni ƙwalla ta cicciko tab a idanuwansu, daƙyar suke yima juna magana, ɗaya bayan daya saida yabi ƴan uwanshi ya rungumesu, kafin ya soma gaisawa da sauran manyan mutanan da suka zo tarbarshi, yaji dadin ganin daruruwan al'ummar da suka taru domin shi, wannan abun farin ciki ne, Obie ne yai mashi magana akan Yan jaridan da ke son yin magana da shi, A hankali yake bin welcome sign din dake a ruƙe a hannunsu.


  Rubutun dake ajiki ya soma karantawa acikin zuciyarshi kamar haka


 _The entire country of Nigeria, welcomes Prime Minister Obinna with open arms!_


 _A very special welcome to Prime Minister Hateem Obinna, on behalf of the entire nation!_


_- Prime Minister Hateem Obinna, we are delighted to have you in our country!_


_We're happy to extend a sincere and heartfelt welcome to Prime Minister Hateem Obinna!_


Ƙayataccen murmushine ya bayyana akan fuskarshi, ƙwallar da yake 6oyewa baisan sa'adda ta soma gangarowa saman kuncinsa, farin cikine Ya cikashi, yaji dadin kyakkyawar tarbar daya samu, mintuna ƙalilan yayi jawabi ma ƴan jarida yayi masu godiya da irin tarbar da suka yi mashi


Daga bisani Jami'an dake bashi tsaro suka yi mashi ƙawanya da iyalinshi zuwa wurin da aka tanadar masu da jigunannun motocin da zasu yi jigila da su, bayan kowan nan su ya shiga cikin mota, kusan atare drivers din dake tukasu suka tada su, A hankali suke driving dinsu zuwa hanyar komawa Obie estate.


    Duk inda suka gifta Jiniyar motocinsu ya karaɗe ko'ina, cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙaraso Cikin estate din, a harabar ajiye motocinsu suka yi parking, gaba ɗaya kowa ya futo suka dunguma zuwa cikin katafaren falon gidan, Jami'an da yazo dasu tuni an ware masu part din da zasu zauna a babban masaukin baƙin gidan, haka zalika advisors dinshi suma An basu nasu Yankin da zasu zauna, bajimawa zasuyi a kasar ba, Ƴan kwanaki ne zasuyi kafin su koma  Canada, masu aikin gidan sai safa da marwa suke Yi wurin kai masu kayan abincin da aka shirya masu, idan zasu gaisa da mutane harshen turanci suke Yi, har yaren french suna jin shi sosai, Gimbiya mujeedat kuma Tafi jin larabci da turanci, haka ƴa'ƴanta ma hausa wahala take yi masu, faryat dai ce ta ƙware wurin yin hausa sai turanci, Prime minster ma Yana jin harshen hausa amma yafi ƙwarewa wurin Iya yaren mahaifiyarshi turanci da faransanci, sai spanish.


 Yinin Ranar gidan Ya cika maƙil da jami'ae, sojoji da ƴan sanda, sun kewaye ko'ina na sashen Estate din, tsaron gidan Ya ƙaru, Kafin mutun ya samu damar shiga estate din sai sun tantance shi da na'ura daga kasa har sama zasu bincike shi kafin ya samu damar ƙarasawa ciki, babu mahalukin daya isa Ya shiga gidan koya fita lami lafiya batare da jami'ae sun cacike shi ba, tun karfe ɗaya  na rana Ƴan uwa da abokanan arziki suke ta taruwa domin Yima baki barka da zuwa.


Wuraren ƙarfe huɗu Na marece, Lokacin mutane sun ɗan ragu, motocin ma'aikan Companyn su Zahra suka ƙaraso Estete din, basu ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, sun girgiza da ganin jami'ae a kewaye da estate din, Zahra Sarkin tsoro duk tasha jinin Jikinta, Kafin abasu damar shiga estate ɗin saida jami'ae suka basu umarnin su fito daga cikin motocinsu, ɗaya bayan ɗaya suka firfito matasan ƴan mata Ansha gayu, daga ƙasa har sama jami'an suka bincikesu hatta kayan decoration din da suka zo da su a mota. Saida suka duddubasu suka tabbatar babu makami ko wani abun cutarwa tukunna suka basu iznin shiga cikin gidan.


  Da taimakon Hajiya saratu suka ƙarasa 6angaren da zasu fara aikin nasu, saida aka fara tarbarsu da lafiyayyan abinci suka cika cikunansu tukunna suka fara aikin tsara decoration din, acikin wani katafaren ɗakin taro dake acikin gidan suka hallara gaba ɗayansu interior designers din, Zahra da fatima sune gwanaye basu aiki sai dai su nuna ma sauran matasan ƴan matan yadda zasu tsara kayan adon suyi kyau, kasancewarsu ƙwararru a fagen Iya decoration tuni wurin Ya fara ɗaukar ido Ko'ina ka kalla kayan adone ke kyalkyali da walƙiya kamar zasu kashe idon bil'adama.



*CHIEF OWAIS✊❤*



Wuraren ƙarfe takwas na dare, Ya fito daga bedroom dinsa, har yayi shirin kwanciya bacci, sleeping dress ne a jikinshi launin sky blue, rigar tabi shape din broad chest dinsa, ta bayyana strong arms dinsa, walking gently ya nufi bakin handrail, Ya ɗaura faffaɗan tafin hannunsa asaman shi, A hankali yake buɗe kyawawan idanuwanshi Yana ƙare ma ko'ina na downstairs da kallo, tun da ya diro nigeria har Yau bai leƙa cikin estate dinsu ba, kuma babu wanda yasan da zuwanshi, ni'imtacciyar iskar wurin Ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya take yi ba, abubuwa da dama sunayi mashi yawo acikin kanshi.


  "Barka da fitowa yalla6ai" muryar Big guy ce ta katse mashi tunanin shi, Yana daga tsaye gefen shi,

 Ba tare daya juya ya kalle shi ba, Ya amsa mashi da yawwa.

  Cikin girmamawa yace"yalla6ai ina fata kana lafiya" ya tambaya ne don ganin yanayin daya fito daga daki cikin shiga ta kayan bacci.


  "I need coffee" abunda ya furta mashi kenan maimakon amsar tambayar da yai mashi.


  Da sauri big guy ya juya domin ya kawo mashi abunda yake buƙata.


  Badajimawa ba sai gashi ya dawo hannunshi ruke da Mug sai tiriri coffeee din Yake yi, Ya miƙa mashi bayan ya kar6a, sai da ya ɗauki lokacin kafin Ya fara kur6ar shi.


  "Yalla6ai yaushe zamu shiga cikin gida ne"?

  Tamkar bazai amsa mashi ba Ya furta"tomorrow"Jinjina kai Big guy yai kafin ya kuma cewa"Yau kawunka na ƙasar kanada ya shigo ƙasar bansani ba ko ka gani a labarai"

  Yamutsa fuska yai da alama surutun big guy ya fara takura shi, daƙyar ya furta"Nasani" 


 Gyaɗa kai big guy yai"bari nabarka ka huta yalla6ai, mu kwana lafiya" ya amsa mashi da okey.

  Juyawa yai da sauri Ya nufi down stairs.

   Yana cikin shan coffee dinshi, yayin da yake bin ko'ina da kallo, Karaf idanuwanshi suka sauka Akan Danish dake ƙoƙarin fitowa daga ɗakin shi, Ya zuba hannayenshi cikin short pockets dinsa, damuwar duniya ta isheshi, Ya kasa runtsawa, saboda rashin ganin unaisah, tun ɗazu yake jiran zuwanta bata leƙo ɗakinsa ba, shi kuma bai Iya takawa yaje ɗakinsu, Kamar anyi mashi Iyaka da shiga, ko falo bai Iya zuwa idan ba Angel ta janyo shi ba, rashin sabone ke damunshi, kasancewar suna fuskantar juna hakan ya bashi damar ganin shi da kyau, duk da akwai tazara a tsakaninsu, dukansu suna a second floor na bene.


    Kamar yadda Owais Ya jingina da handrail haka shima Danish ya ɗaura gwiwowin hannunsa saman handrail, da farko bai lura da shi ba, sai da ya wurga eye balls dinsa saitin inda yake fuskanta tukunna suka yi tozali da juna, ɗaure fuska danish yai, tunkafin ma yasan wanene shi yaji baiyi mashi ba saboda shi baya ƙaunar yaga Namiji idan har ba cikin ƴan uwansu maza ba, duk don saboda Babe Unaisah dinshi, yaji haushi ɗazu da asuba dayaga wani ƙato Ya rungumeta, har zazza6i saida ya lullu6e shi, ko abincin dinner dinshi baici ba, yaso ace Ya damƙeta da babu abun da zai hana ta yabama aya zaƙinta.


Chief Ya natsu yana kallon shi, abun da ya ɗan bashi mamaki Da yaron girman jikinshi, saboda yasan shekarunshi da sojoji suka faɗa mashi a bayanin da Gabriel Ya basu, bai wuci 20 years ba.


  Tsawon mintuna suna kallon kallo a tsakaninsu, kafin daga bisani chief Ya juya mashi baya ya nufi bedroom dinsa ya shige, saukowa down Yai cikin sanɗa yake yin tafiya yana neman room dinsu Unaisah, ya rasa ta wace hanya zaibi ya gano ɗakinsu.


  Firgita yai sakamakon Jin hannun mutun saman Bayanshi, abunka ga mai ji da ƙarfi, yayi tunanin wani ne zai cutar dashi, aiko ya damƙo hannun mutumin da niyar ya wurgo shi ƙasa sai kuma Ya fasa, Ya juya a hankali don ganin wanene, Boss man ne atsaye hannunshi ruƙe da Backpack din unaisa, Da mamaki akan fuskarshi yace"Sannu Iliya ɗan mai karfi, au da buguna zakayi daga kawai na dafa kafaɗarka? Haka ɗazu da safe ka dinga jifana da pillow saboda na rungume ƴar uwarka ko"? Cikin jin kunyar maganarshi Danish ya sadda kanshi ƙasa, ba tare daya furta komai na.


  Murmushi boss man ya saki tare da miƙa mashi backpack din hannun shi"kar6i nan, ka kaima Masoyiyar taka Unaisah kace inji boss man, ta duba cikin aljihun jakar zata ga sabon sim dana sanya mata"


  Hannu yasa ya kar6i backpack din, daƙyar ya iya furta mashi thank, kafin ya juya yanufi inda yake tunanin zai samu ɗakinsu.


  Boss Man yana atsaye yana bin bayanshi da kallo, Har ya 6ace ma ganin shi kafin Ya juya ya nufi ƙofar fita.


  Yayin da Danish keta faman neman ɗakinsu Angel, tana acan cikin toilet gaban madubi, daga zuwa Yin uziri taci karo da abun arziƙi a kirjinta, Duk tabi ta ruɗe ta rasa ina zata tsoma ranta don farin ciki, batasan yaushe breast suka fara fito mata ba, bata ta6a lura ba sai yau data tsaya gaban madubi tana bin jikinta da kallon ƙurulla, guntuwar rigar bacci ce a jikinta, Daƙyar ta rufe gwiwarta, sai faman ɗaɗɗage rigar take Yi tana ƙara leƙensu, sunyi ƙananu dasu basu fara nuna ba, kamar wadda akayi ma albishiri da gidan Aljanna sai faman sakin murmushi take Yi, itama yau irin abin ƴar gidan daddy sun fara fito mata, taci alwashin bazata bari Danish yagansu ba, sai sun ƙara girma sunkai kamar na unaiza tukunna, da gudu ta fito daga toilet ta nufi closet dinsu ta buɗe ta dauko ƙaramin mayafi ta koma cikin toilet, ta tu6e wuyan rigar, ta ɗaure kirjinta tamau da mayafin kafin ta maida wuyan rigar tana faɗin"Allah na gode maka, nan bada jimawa ba nima zan zama budurwa"


Duk wannan haukan da takeyi, batul tana akwance saman gadonsu, tayi nisa acikin baccinta, 

  Adai dai lokacin zata fito daga toilet din tana zuro ƙafarta, tayi arba da danish tsaye bakin ƙofar dakin, Hannun shi ruƙe da backpack, Sai faman baza ido Yake yi don ya ganota, daƙyar ya samu ya gane dakin nasu, 

  Jin motsin mutun yasa shi yin saurin ɗaura idonshi akan fuskarta, ido cikin ido suke kallon juna, wani abu daya ɗaure mashi kai, shu'umin murmushin daya gani kwance saman la66anta, hada ruƙe qugu da hannu ɗaya.




*Boss Bature✍️Mu haɗu Monday Idan Allah yakaimu da rai da Lafiya, ga masu neman ƙarin bayani a tuntu6i layina 08103884440 whatsapp Only*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post