Kurkukun Ƙaddara Book 2 Page 32

Kurkukun Ƙaddara Book 2 Page 32


❤EX-PRISONERS❤

Sam ya kasa ƙarasawa gare ta, slowly yake bin jikinta da kallo, tun daga kan fararen ƙafafuwanta har izuwa saman gwiwowinta da suka kasance jawur da su kamar bata ta6a yin rarrafe ba, ɗagowa yai da eye balls dinsa zuwa saman Waist dinta da ya faɗaɗa, ganin irin mayataccen kallon da yake binta dashi ne yasa ta juya da gudu ta nufi can cikin dakin wurin closet dinsu, har sai da yaji gabanshi yaɗan faɗi lokacin data watsa da gudun mazannanta suka girgiza rigar ta bayyana shape dinsu, yawu ya haɗiya adam's apple dinsa Ya motsa sama da ƙasa.


  Yaɗan ji shock ganin baƙon al'amari ajikin Babe unaisah dinshi, bai ta6a ganin girmanta ba sai yau da yai tozali da ita cikin short gown, Kayan arzuƙa sun fara ha66aka.


   Cikin sanɗa take tafiya tana tunkaroshi, idanuwanshi akan fuskarta, still shu'umin murmushin nan take sakar mashi, hatta Yanayin tafiyarta ya canza, dogon wandon bacci ta zura a jikinta duk don Ya daina kallon mata jikinta.

  Dab dashi ta tsaya tana duban backpack din hannunshi, har cikin ranta taji dadin ganin jakar, daɗi kamar zai kasheta, haɗa ido sukayi da shi, mutumin duk ya susuce kamar wanda aka zare ma laka, sam babu kuzari a jikinshi tunda yai arba da hips dinta.


  Harara ta jefa mashi haɗi da murguɗa mashi soft pink lips dinta, muryarta da shagwa6a tace"kallon ya isa haka, bani  jakar nagode" ta faɗa tana ƙoƙarin ruƙo hannun backpack din, da sauri ya ƙanƙameta a wide chest dinshi, alamar bazai bata ba, ɗaure mashi fuska tai"wai meye haka? Baka ga dare yayi ba, yakamata kaje ka kwanta, ni bansan ma ya akai boss man ya baka back pack din ba, ai daya sani shiya kawo min da kanshi" bada wata manufa ta furta maganar ba, amma da yake jarabar kishi ce dashi, sai yaji kamar tana nufin tafi son ganin boss man akanshi shiyasa tace haka, aikuwa nan take Ya haɗe rai, babu annuri ko misƙala zarratin, ganin ya fusata yasa tace"meye faru my man"? Wurgar mata da jakar Yai ƙasa, da sauri Ya juya Ya nufi ƙofar fita kamar zaiyi tuntu6e, Jiki na rawa tabi bayanshi tana ambaton sunanshi"My man! Dan Allah ka tsaya muyi magana, Ni ce na bata maka rai ko? Pls am sorry bazan ƙara ba, Ka yafe ni pls, bazan Iya bacci kana fushi dani ba" 


Har ya kusa fucewa daga ɗakin, Can kuma sai ya dakata kamar mai tunanin wani abu, Ba zato ba tsammani taga ya juyo a sukwane, ƙiris Ya rage ta hade kirjinta da nashi, gadan gadan Ya tunkarota hakan da yai ba ƙaramin tsoro yaso ya bata ba, Juya tayi da niyar ta faɗa toilet, ta 6oye sai dai kafin ta kai ga shiga taji Ya damƙi waist dinta da ƙarfi Ya ɗaga ta sama kamar ɗiyar roba, tadinga ihu tana fadin Am sorry my man dan Allah kada ka 6alla ni"


 Batul dake a kwance tana sharar bacci, koke koken Angel ya fara takura mata sai faman mutsu mutsu take Yi alamar zata farka.


  ya tsareta da reddish eyes dinsa da launinsu Ya ciza tamar zallar red, da kakkausar murya ya furta"meyasa kike son 6ata min rai"? Ya fada batare daya sauke ta ƙasa ba,

 Jikinta na kerma tana faman wutsil Wutsil da ƴan ƙafafuwanta tace"danish dan Allah ka ƙyaleni, kaga Batul dake bacci tafara takura da surutunmu, kuma ni bansan laifin me nayi maka ba, amma ina baka haƙuri ka tafi ɗaki ka kwanta"


  Ta6e la66ansa Yai alamar bai damu ba, kafin ya sassauto da Voice dinsa"Kin hana zuciyata sakat, tunda safe da kika rungume ƙaton nan Hankalina ba akwance yake ba, nakasa samun sukuni, ni kaɗai nasan irin raɗaɗin da nake ji, ke ko ajikinki, baki leƙo dakina kin duba halin da nake aciki ba,saboda ke banci dinner dina ba, baki damu dani ba, ko nema na bakiyi ba, saboda kin samu wanda yafi ni ko"


  Runtse idanuwanta taɗanyi, hadi da dafe kai da hannu ɗaya, dama saida ranta ya bata bazai ƙyaleta ba, saboda jarabar kishinshi, shiyasa yau ta hana shi ganinta, duk dan ta tsira daga fushin  shi.


  Shirun da tayi mashine Ya ƙara 6ata mashi rai, Baisan sa'adda Yai zazzafan taku Ya nufi Saman shimfidedan gadonsu, Ya jefar da ita Ta faɗa saman  lallusar mattress din, da sauri ta juyar da jikinta tai kwanciyar rubda ciki, gudun kada Gyaran gashin da akayi mata ya tarwatse, Cikin shessheƙar kukan ƙarya Take Fadin"Nifa bada son raina ya rungume ni ba, Hijab din jikina ce ta taɗiyoni na tafi zan kife ƙasa shine Ya tarbeni na faɗa chest dinsa, kaima ka sani bani marmarin kasancewa da wani ɗa namiji idan bakai ba, dan Allah kadaina tayar da hankalinka akaina, saboda Ni taka ce kai kaɗai, shi mutumin ma da kake Yin kishi akanshi babbane ba matashi ba, Ya isa ya haifemu nida kai"


 Tun da ta fara yin magana, Ya rasa sukunin shi, Gyaran gashinta Yai matuƙar jan hankalin shi, kamar princess, twisting din da akayi mata guda biyu saman gashin ya ƙara mata kyau, sam bata ji motsinshi ba, ta dage sai haƙuri Take bashi, jin hucin numfashinsa a jikinta Yasa tai wuff Ta juyo Tana fuskantar shi, har saida gabanta Yaɗan fadi ganin Yadda yai mata rumfa, tuni tasha jinin jikinta, muryarta na rawa ta furta"meye haka"

 Lumshe mata ido yai tare da waresu saman fuskarta, abun ya ɗaure mata kai, Yana neman ya rikitar da ita.

  Ganin dagaske kamar wani abu yake so yai matane yasa ta fara canza mashi fuska, zuwa ainihin true colour dinta, runtse ido tai da masifa tace"danish ka tashi ka tafi ɗaki, wallahi kada ka bari na buɗe ido na ganka ranka zai Iya 6aci" saida ta gama zazzaga mashi faɗan ta buɗe ido a hankali don taga idan ya tafi, ko gizau baiyi ba yana nan yadda yake, Cikin zafin nama ta daddage ta ɗaura hannayenta saman ƙirjinshi da niyar ta ingije shi, sai dai takasa yin hakan sakamakon wani abu daya tayar mata hankali, a ruɗe take kallon shi ayayin da take kokarin mikewa zaune ta jingina bayanta jikin headboard na gadon, Cikin sanyin murya ta furta sunanshi"My man"


  Idanuwanshi tuni sun fara canza launi, numfashinshi na fita da huci hucin zafi.


  "Faɗamin meke damunka? Baka da lafiyane? Meyasa naji zafi ajikinka"?

  Da wata irin kasala Ya kwantar da kanshi saman mattress dinsu, kasancewar Gadon Yana da fadi Batul tana daga can 6angare guda.

  "Kayi shiru baka bani amsa ba, kasan bana so Ina magana kana shareni,"

    Daƙyar Ya iya buɗe baki Ya furta"am sorry idan na 6ata maki rai, yanzu zan tafi na kwanta" ya ambaci hakan tare da miƙewa ya sauko daga saman gadon, da sauri ta biyo bayanshi tana ƙwala mashi kira, sai dai kafin ta isa gare shi, tuni Ya fuce daga ɗakin, ƙofar tayi locking, kwantar da kanta tayi saman glass door Din, Jikinta yai mugun yin sanyi, hankalinta Ya tashi ssai, ta girgiza da jin zafin jikinshi tamkar hucin garwashin huta, taya zata iya runtsawa bayan bata da masaniya akan halin da yake aciki? Gashi ya faɗa mata baici dinner ba duk don saboda da ita! Ruwan hawaye ne suka taru acikin idonta, da sauri ta juya tana duban hadaddiyar wall clock din dakin ƙarfe 10 na dare, badan taso ba ta haƙura da bin bayanshi amma taci alwashin da asuba zata je ta dubashi, kamar yadda taga rana haka taga dare, bacci ya ƙaurace ma idanuwanta, sai faman juyi take Yi saman gadonsu, duk ta takura kanta ta hana zuciyarta sakat.


*FRIDAY MORNING🥳💃💃💃*


Bayan tasowa daga sallar asuba, dattijon arziƙi Ya nufi Sashen da bedroom dinsa Yake hannun shi ruƙe da sanda, Farar Jallabiyace a jikinshi, lokacin daya ƙarasa bedroom dinshi, da sandar hannun shi Ya tura ƙofar shigar shi keda Wuya kafin ƙyaftawar ido Hasken ɗakin Ya ɗauke, duhu Ya mamaye idanuwanshi, Abunka ga tsoho duk Yabi ya ruɗe, muryarshi Adabarbace yake fadin"subhanallah, Waye ya kashe min hasken ɗaki? jazz bana son shaƙiyanci nasan kai kaɗaine zaka Iya min haka? Wai jazz baka ji Ina magana" ya fada Yana cigaba da yin tafiya cikin duhu, Ya daura hannu ɗaya jikin bango Yana laluban Switch don Ya kunna hasken dakin, Cikin 6acin rai Yake Fadin"Jazz wallahi kada ka bari in kunna hasken ɗakin nan, ranka zai 6acine, wato raini Ya fara shiga tsakanina dakai shiyasa har kake Yi min shegantaka ko"?


 Daƙyar Ya samu Ya shafo switch din, a harzuƙe Ya danna button din, A hankali Hasken ɗakin Ya soma gauraye ko'ina, tamkar da rana, Juyawar da zaiyi unexpected Yaga abunda Ya bashi mamaki da al'ajabi, wato gaba ɗaya furannine launin ja da yellow tun daga saman head boad har izuwa saman zanin gadonshi, An ƙawatasu masu kyan gaske har ƙyalli suke Yi, tamkar a mafarki Yake kallon ikon Allah, A hankali yake dogara sandarshi Yana tunkarar gadon tamkar maijin tsoronshi, saida Ya matso kusa Ya ƙura ido Yana so ya gane rubutun me akayi da furannin, karantawa yai


  *"HAPPY 80TH BIRTHDAY TO OUR BACKBONE"*


  Lokaci daya ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, Farin ciki mara misaltuwa ya lullu6e shi, Sai faman sakin murmushi yake yi kamar wani zautacce, daga end bed din Ya zauna, Yana ƙarewa furannin kallo, ranshi yana bashi cewar ƴa'ƴanshine suka shirya mashi furannin, tabbas sune, Yayi mamaki babu wanda ya sanar dashi zasuyi mashi hakan, Kuma atare dasu ya dawo daga masallaci, tun a babban falon gidan suka rabu da juna kowa ya kama hanyar part dinsa.


    Yayin da yake bin adon furannin da kallo, cikin sa'a idanuwanshi suka yi mashi tozali da birthday cards birjik aka ajiye mashi don Ya karanta, kusan guda bakwai daga saman kowani card an ɗaura fure, hayewa yai saman gadon har zuwa gaban cards din Ya ɗago dasu a hannunshi kowanne yana da tittle dinsa da kuma sunan mamallakinsa, Card din farko Sunan senate lateef ne, buɗewa yai ya soma karantawa kamar haka.

   

_"To my dear father, thank you for always being there for me, guiding me, and making me the person I am today. Your support, love, and encouragement have made me who I am, and I'm so grateful for that"_


 tuni idanuwanshi sun cicciko da ƙwallar farin ciki, Ajiye card din lateef yai, ya buɗe card na biyu mallakin Sir mubarak Yana duban sakon cikin shi


  _"From the bottom of my heart, I want to wish you a very happy birthday, Dad! Your wisdom, kindness, and sense of humor have always brightened my days" annurin fuskarshi sai ƙara nunkuwa yake Yi, haƙiƙa sunyi matuƙar faranta mashi da daɗaɗan kalamansu, Yana matuƙar ƙaunar ƴa'ƴanshi.


  Ajiye card din sir mubarak Yai, ya buɗe Na Sharafuddeen calmly ya ke reading dinsa

   "Happy birthday, Dad! You are the best father in the world and we are so lucky to have you. May your day be filled with happiness and love." hawayen da suka taru acikin idanuwanshi tuni sun jiƙa fuskarshi, sumbatar card din Yai, kafin Ya daura shi saman wadanda ya karanta, Ya duba sakon Prime minister 


   _"I'm so glad to have a father like you, who has been a rock of support through the ups and downs of life. You've always encouraged me to be the best I can be, and that means the world to me. On this special day, I just want to say thank you for everything you've done for me. Happy birthday Baba tsoho much love"_ 


Dariya ya saki har fararen haƙoranshi suka Bayyana, Kalmar ƙarshe ta saƙon Hateem ne Ya bashi dariya daya ce baba tsoho.

  Lumshe idanuwanshi yaɗanyi yayin hawaye ke cigaba da wanke fuskarshi, abu ɗaya ne yake fargaba a duniyar nan ranar da zai barta saboda ƴa'ƴanshi, bai sani ba tsakanin shi da su wanene gawar fari, bai fata ma Wani daga cikinsu Ya riga shi tafiya, bazai Iya jurar rashinsu ba, Ya ƙwammace mutuwa tafara Yin awon gaba dashi.


  Sumbatar card din Hateem Yai, kafin Ya buɗe na saratu

   

- On this special day, I want to let you know how much I appreciate everything you've done for me, Dad. You've always been my biggest fan and supporter, and I can't thank you enough for that. Wishing you a very happy birthday, with lots of love My Baba, Allah yabarmun kai, madubin dubawata" manna ma card din kiss Yai kafin Ya duba na sauran ƴa'ƴan nashi, waɗanda basu kaiga ƙarasowa Gidan ba, suma sun bada saƙon da aka rubuta masu a cards dinsu.


  Farin cikin duniya ya cika Obie, kwanciya yai saman furannin idanuwanshi na fuskantar ceilling.

  Ba zato ba tsammani Yajiyo sautin muryoyinsu acikin kunnuwanshi, Suna faɗin"Happy Birthday To You, Happy birthday to You, Happy birthday to our Baba" zumbur Obinna Ya yunƙura ya miƙe daga saman gadon Yana duban ƙofar room dinshi.

  Dr. jazz ne Ya fara shigowa hannunshi ruƙe da madaidaicin Cake mai hawa huɗu daga saman shi an jera candle, ga cake knife gefe ɗaya.


  Shigowar dr.jazz ke da Wuya, Manyan ƴa'ƴan shi suke shigo ajere kowannansu sanye da hadaddun jallabiyoyi, Mutun Na farko Sir mubarak ne daga bayanshi Senate lafeef ne, wanda ke abiye dashi His excellency Abdul Razak ne Gomnan Jihar lagos, baisan Yaushe Suka shigo garin abuja ba, Yayi mamakin ganinsu, zuwan bazata suka yi mashi, ga kuma His excellency Deen Obinna Na jihar kaduna state, Daga bayanshi mai girma sharafudden Obinna ne, Hannun shi ruƙe dana ɗan uwanshi Prime minister hateem obinna, abun gwanin ban sha'awa, bayansu sai Saratu data shigo itama jallabiyarce a jikinta ta yafa mayafi akanta, Fuskar kowannansu ɗauke da annurin farin ciki, maimakon Ya taso Ya karaso garesu, sai kawai su ka ga ya fashe da kuka, haɗi da sanya tafukan hannayenshi biyu Ya rufe fuskarshi.


Jikinsu duk Yai sanyi, duk da ransu yana basu cewar kukan farin Cikine Ya ke yi, gefe da gefen gadon kowan nan su ya zauna kamar masu neman gafara, Senate lateef Ne Ya fara magana

  "Baba meyasa ka yin kuka? Dan Allah kada ka karya mana zuciyoyin mu, munci burin mu faranta maka a wannan ranar mai albarka rana mafi daraja agaremu, ranar da abun alfaharinmu Yazo duniya" ta tsakankanin yatsun hannunshi Yake satar kallonsu, Muryar saratu da shagwa6a tace"baba please kadaina wallahi bamu jin daɗin ganin hawayenka masu tsada suna zuba ƙasa"

  "Baba idan baka daina kukan nan ba, muma zamu fara" acewar Sir mubarak

  Mr.president sharafudden Yace"Daddy ka bamu dama mu share maka hawayenka da hannayenmu please"

 His excellency Deen Ya kar6e da cewa"daddy saboda kai, muka kamo hanya tunda duku duku muka shigo abuja, saboda muhimmancinka agare mu, dan Allah ka buɗe fuskarka ko mun samu damar ganinka, munyi kewar mahaifinmu" kalamansu ba ƙaramin karya mashi zuciya suke Yi ba, sai dai yakasa cire takufan hannayenshi daga saman fuskarshi, Allahu akhbar, wato Iyaye dabanne, duk mun muƙamin mutun shi bakomai bane agaban Iyayenshi, gaba ɗayansu nan manyan mutanene masu ruƙe da manyan muƙaman ƙasa, masu ƙima da daraja a idon duniya, Yau gasu zazzaune gefen gadon mahaifinsu, sun tasa shi agaba suna lallashinshi, abun da yake ƙara haddasa mashi jin ƙaunarsu Biyayyar da suke yi mashi, tun suna ƙanana har zuwa girmansu bai ta6a danasanin kasancewarsu a matsayin ƴa'ƴanshi ba, basu ta6a sanyashi ciwon kai ba, samun ƴa'ƴa nagartattu irinsu abune mai wuya a zamanin nan, damuwarshi tasu ce, suna matuƙar ji dashi suna gatanta shi suna kyautata mashi shiyasa suke damun cigaba arayuwarsu saboda albarkar dayake sanya masu.

 Muryar His excellency deen Ce Ta katse mashi tunaninshi

  "Baba munji kayi shuru baka ce komai ba, Idan akwai abunda ke damunka please Ka faɗa mana, baka da tamkar mu a duniyar nan, ashirye muke da mu share maka hawayenka"

  da zolaya Sir mubarak Ya dubi jazz"faɗamin gaskiya kodai kaine ka 6ata mashi rai"?

 Jazz na murmushi yace"wallahi bani bane..." daƙyar ya ƙare maganar ganin irin kallon tsiyar da hajiya saratu take watsa mashi, Muryarta a kausashe tace"tunda ka kawo cake din miƙo min shi ka fuce kabamu wuri," Jiki asanyaye Jazz Ya nufeta Ya miƙa mata tray din, Tasa hannu ta ƙarba tana faman jifarshi da harara, sam bayason barin Ɗakin, idan Yana atare da su ji yake kamar Yana acikin danginshi mantawa yake yi da shi bakowa bane a family dinsu.

 Har Ya juya zai fuce Muryar Hateem ta dakatar dashi"Zonan jazz" dakatawa yai dayin tafiyar da sauri Ya koma gaban gadon, Hateem Ya sanya hannu ya kar6i cake din hannun saratu Ya miƙa mashi"kamar yadda ka kawo shi kai nake so ka fara bashi" ɗaure fuska hajiya saratu tayi badan tana jin shakkar Yaya hateem ba da kuwa babu abunda zaisa ta bashi cake din, bawan Allah Jazz sai faman sakin murmushi yake yi, ya kar6a Yana fadin"nagode daddy hateem," jinjina mashi kai Yai batare daya ƙara furta komai ba.

  Baba, zamu tafi bamusan ko mune ke bakason gani ba, His excellency abdul razak ne Ya furta hakan, Sai lokacin Dattijon arziƙi Ya zame tafukan hannayenshi daga saman fuskarshi, tsufanshi Ya ƙara bayyana sosai, tamoji tamoji duk Ya kame fatarshi, Zaro hanky Sir mubarak Yai daga cikin aljihun shi, Ya soma share mashi hawayenshi, Bayan Ya kammala yasoma dubansu ɗaya bayan ɗaya, bi da bi, gaba ɗaya kamannin fuskarshi suka ɗauko, Musamman sharuffudeen da hateem tamkar yai kakinsu, hatta hasken fatarsu kalar nashi ne, launin idanuwansu ne dai kalar na mahaifiyarsu reddish brown.


Ganin yadda duk suka damu ya sanya shi sakar masu fuska, cikin sanyin murya yace"kai nifa ba wani abu ke damuna ba, Farin Cikin ganinku ne ya sanya ni kuka, don haka ku kwantar da hankulanku, Jazz miƙo min cake din nan" Ya faɗa Yana ƙoƙarin saukowa daga saman gadonshi, mimmiƙewa sukayi tsaitsaye suka kewaye shi, Tuni damuwar fuskarsu ta washe

  Miƙa mashi cake din Jazz Yai, sai da suka fara kirga mashi one two three kafin Ya hura Iska Candles din jiki suka mutu, tafa mashi hannu sukai, sai faman sakin murmushi yake Yi, 

   "Wazai fara bani cake din" ya fada yana dubansu, 

  Matsa ma jazz hanya sukayi Ya matso kusa dashi, Hajiya saratu ji take kamar ta ingiza ƙeyarshi taji haushin kasancewarshi acikinsu, aganinta bashi ya dace Ya shigo cikinsu ba, Ina laifin su twins suda su ke jikokinshi.


  Shikuwa Hannunshi Har kerma yake yi wurin daukar wuƙa, Ya gutsiro cake din Ya miƙa mashi abaki, Ya soma ci atsanake Yana duban Jazz hada ɗaga mashi gira Ya furta"Waye ya haɗa min wannan? Yai min daɗi"

 Jazz yace"mommyna ce ta haɗa maka shi" jinjina kai yai"amma ta iya na jinjina mata" daɗi jazz yaji An yabi cake din mahaifiyarshi, saratu kuwa takaicin duniya ya isheta.

   Daya bayan ɗaya suka soma bashi cake din Yana ci, Kafin shima Ya kar6a Ya bi kowannansu Ya bashi abaki, Bayan sun kammala ci, Ya daura cake din saman table,

 Rungumarsu Ya fara yi ɗaya bayan ɗaya yana bubbuga bayansu da hannayenshi kamar yadda ya saba yi masu tun suna Yara.

 Saman gadonshi Ya koma ya zauna yace masu duk su zazzauna yana son yaita kallonsu, hakan ba ƙaramin daɗi yai masu ba, kamar yadda ya basu umarni haka suka samu wuri saman mattress din suka kewaye shi.


  Banda jazz wanda tuni Yajima da komawa ƙofar ɗakin, ganin irin kallon barazanar da hajiya saratu take Yi mashi kamar zata shaƙe shi.


Tun wuraren ƙarfe goma sha biyu na safe, Hamshakan motoci keta kurɗaɗowa cikin gidan tunkafin  lokacin da za'a fara gudanar da shagalin Ya gabato, sun Cika gidan, kasancewar Baba Obie mutunne mai tarin jama'a, wasu ma ba a ƙasar suke zaune ba, amma aranar sai gasu sun shigo Nigeria duk don saboda su halacci taron taya murnar ranar haihuwarshi, Masu aikin gidan sai zarya suke Yi wurin Kaima baƙi abinci dana sha, kitchen ya zama Dandalin magulmata, Bakunansu ko gajiya ba su yi da surutu.


  "Yau zamu ba idanuwanmu abinci har su ƙoshi" Safa ce tai maganar,

 Sophia tace"Hmm, aini yin aiki agidan nan gaba ta kai ni gobarar titi ajos, waiku kunga haɗuwar Prime minister Hateem da matarshi! Wow masha Allah, Allah Yayi halitta"

   Marwa tace"shi kaɗai kika gani kenan, baki ga Mai girma sharafudden ba, ai hadashi jiya cikin waɗanda sukaje airport tarbo prime minister, wallahi mutumin ba ƙaramin burgeni yake Yi ba, dashi da ɗan uwanshi hateem, mutanan badai aji ba, komai nasu da dattako suke Yin shi.


  Abla tace"yau zamuci uwar sabada, zamu tashe mu watse, Mu raƙarƙashe don nasan dole agayyaci mawaƙa da makaɗa, Ni nama rasa wani kaya zan sanya wallahi"


 da zolaya safa tace"kalar dangi, Uban wa kike tunanin zai barki ki shiga hall din taron? Ke kin isama? Sannu isassa mai walkin sa, ai kawai ki tsaya a iya matsayinki, Ta ina zaki nemi haɗa kafaɗa da Manya manyan hamshaƙan attajiran masu kuɗi, ai idan kin ganki a hall din can to amatsayin mai raba abinci zaki je" dariya suka saki.


  Abla tace"Nima fa da wasa nake wallahi, Ai ni tsoronma shiga zan ji, jiya izuwa yau bani da kwanciyar hankali saboda jami'an sojojin da suka kewaye estate din ciki da waje, nasan duk zuwan hateem ne yasa aka ƙara tsaro har haka"


  Marwa tace"niko inaso na tambaya, abun yaɗan tsaya min araina," har suna haɗa baki wurin tambayarta menena,

  Numfasawa tayi kafin ta soma magana"kunsan ni ban jima da fara aiki acikin gidan nan ba, abun da yaɗan ɗaure mun kaina, taya akai hateem da yake ɗan kasar Nageria Yake mulkar ƙasar turawa mai girma kamar canada, dama hakan yana iya yiwuwa? Ta tambaya tana duban fuskokinsu,

   Safa ce tafara Kora mata jawabi"bazai yiwu ba sai dai idan ya kasance, shima ɗan kasarne, Misali kamar idan acan canada aka haife shi, kinga yana da ƴancin da zai Iyayin duk wani abu da ɗan kasar zai yi, ko kuma idan mutun ya zauna a wata ƙasa wadda ba tushen shi ba, har na tsawon adadin shekarun da zai iya cika duk wasu sharudda daya cancanta ya zama ɗan kasar shima yana da right da zai Iya aiwatar da duk wani abu da ɗan ƙasar zaiyi, shi kuma Hateem da kika gani asaline dasu a kasar canada, tushen mahaifiyarsu ne, Allah yajiƙanta, ta fito daga babban family daya shahara a  ƙasar canada, bakomai nasani dangane da tarihinsu ba nima hajjaty ce tafara bani, kinsan mahaifinsu yayi yawon duniya sosai, kuma yana da farin jinin al'umma, duk inda ya shiga saiya samu kyakkyawar tarba, Ya zauna a kasashe daban daban tunkafin Ya auri matarshi ta farko, mariganya Hajiya kudirat, Allah yakai rahama ƙabarinta, itace ta haifa mashi Yan ukun shi, Senate lateef, sir mubarak da abdul razak na lagos, bayanshi sai Deen obinna, da kuma saratu autarta, Hajiya kudirat jinin sarauta ce, ta fito daga tsatson sarkin yarbawan jihar lagos, marwa tace"Ikon Allah shiyasa hajiya saratu take da jinkai, Ashe suma Izzar sarautace a jininsu" murmushi kowannansu ya saki, Safa ta numfasa kafin ta ɗaura da cewa"sharafuddeen kuma da Hateem uwa ɗaya uba ɗaya suke, Idan kika lura sunfi kamanceceniya da juna, duk da gaba ɗaya ya'yan obie dashi suke kama, babu wanda ya ɗauko mahaifiyarshi, har ƙwara Saratu ta ɗauko kama da Hajiya kudirat, bari in baki amsar tambayarki, Hateem dai a hannun dangin mahaifiyarshi can ƙasar canada Ya taso acan aka haife shi, kuma acan aka raineshi, mahaifiyarsu bata ta6a zama a kasar nigeria ba, Idan kinga tazo to zamane na ɗan lokaci, sai dai shi obie din ya taka yaje inda take tare da ahlinsa, shiyasama har family house garesu a ƙasar canada, shi kuma sharafudden da kika ga Ya taka matsayin shugaban ƙasa a nigeria bayan mahaifiyarsu ta haifeshi a canada, to shi ba a kasar aka raine shi ba, Ya zauna a hannun dangin mahaifinshine anan nigeria tun Yarintarshi har zuwa girmanshi, Idan kina neman ƙarin bayani game da hateem, Ki binciki tarihin Barack obama tsohon shugaban ƙasar america Kusan tafiyarsu ɗaya kinsan shima mahaifinshi ba ɗan kasar america bane, tushen mahaifinshi daga africa ne" murmushi kowannansu Yasaki, Marwa tace"ai basaima na bincika ba, Na gamsu da bayaninki sosai, Kin wayar min dakaina, Da ina kokwanton taya haka zata yiwu ɗan nigeria ya mulki wata ƙasa, amma yanzu kin goge min kokwantona, gaskiya abun Ya ƙayatar dani, balle shi hateem ma da ba Iya haihuwarshi acan akayi ba, Tushen mahaifiyarshi ne"


  firar da sukeyi bata dauke masu hankali Ga yin aikinsu ba, kasancewar sunada yawa, akwai wadanda ke zaryar kai abinci, ba iya su kadai bane.

  "Ni dai fatana Allah yasa uban Ƴan ji da izzar nan yazo yau" sophia ce tai maganar,

 Abla tace"Ai ga ƴar uwarshi nan uwar ji da Izza, Itama ta duro gidan, zanso inga haduwarsu"

  Safa tace"Kina nufin Nazli"? Jinjina kai Able tai"ita nake nufi, Yarinyar badai Ji da kai ba, ta Iya haɗe fuska bata da fara'a, Har ƙwara Yazrin tafi sakewa da mutane duk da itama bakowa take hulda dashi ba"

  Marwa tace"ke kuwa ai dole suyi izza, jinin sarautar dubai, Jikokin sarkin sarakai, Ga uba shugaban ƙasa sukutun da guda, uwa uba ga kyau kamar su suka tsara halittarsu, Ni wallahi burgeni suke Yi, takun tafiyarsu kadai abun kallone"

 Safa tace"ga kuma Hindu, nasan itama yau zata shigo gidan, itada mahaifiyarta Hajiya sarauta, mace mai ji da izza"

  Ta6e baki Sophia tayi"Um, nifa mutun ɗayace bana son ganinta, Hajiya laurat saboda bata da mutunci matar, ƙyamar talaka gareta"

 Dariya Abla tasaki tana fadin"kin kuwa san dole ta halacci taron nan, zata haɗu da ƴar uwarta Aunty masifatu, mu kuma mun shiga uku" dariya suka sanya gaba ɗayansu kafin suka maida hankalinsu akan aikin dake gabansu.


*HAJJATY❤*


A kwance suke saman gado, manne da juna, yahanata sakat tun ɗazu take son leƙawa kitchen pravin Ya hanata motsawa, ga tarin ayyuka dake jiranta, tun asuba ya shigo ɗakin.


   Muryarta da kasala take ambaton sunanshi"Pravin pls ka tashi ka tafi ɗakin matarka, baccin Ya isa haka, Ina da ayyukan da zanyi kada aji ni shiru a matsayina na babba acikin masu aikin gidan nan" 


  A hankali Ya buɗe idanuwanshi da suka kaɗa jawur yana dubanta dasu.


  Sai faman lumshe su yake yi, don ba ƙaramin nauyi suka yi mashi ba, Short ne ajikinshi babu riga jallabiyar shi tana a saman mattress din, Ita kuma Iya undy ne tayi daurin gaba dashi, shara shara kana Iya ganin tsiraicinta.

  Kamar baisan furta maganar yace"dan Allah ki ƙyaleni, bana jin daɗin jikina ne, ki kwantar da hankalin ki babu wanda zai damu don baki aiki"

  Ya faɗa haɗi da ɗaura hannunshi saman sumar kanta dake akwance saman bayanta, a hankali yake shafa gashin

 Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Na roƙe ka, ka tashi ka tafi dan Allah, Matarka zata Iya nemanka"

  "Meye damuwarki aciki, duk kin wani ɗaga hankalinki"


  Murguɗa mashi baki tai"Pls my baby boy, kasan yau babbar ranace agaremu, yakamata mu shiga cikin dangi ai hidima tare damu"

 Jinjina mata kai yayi'okey, naji zan tafi but before that, Inaso zan gargadeki, kinga yau akwai manyan mutanan da zasu halacci taron nan, banason inga gifcinki awurinsu, don na lura ba ƙaramin jan hankalinsu kike yi ba"


  Farfari tayi mashi da ido"idan kaga banje wurinsu ba to bana numfashine, hakanan kawai kake min baƙin ciki, don kada in samu mijin aure, kai kayi aure ni kuma ka hanani sakat" da zolaya tayi mashi maganar.


  Lumshe mata ido yai, ya tsare kirjinta da kallo kamar ba yanzu ya gama tsotsarsu ba.


  "Nidai na faɗa miki kuma na ƙare maganata, idan kika ƙara yi min irin wannan maganar zanyi maganinki ne"

  "Ashirye nake dana kar6i kowani irin hukunci da zakayi min, nasan dai bazaka Iya cutar dani ba" ta faɗa tana tura mashi kirjinta, aiko da karfi Yakai masu cafka, ta fasa ihu tana dariya, kutsa kanshi yai cikin undy dinta Ya cigaba da wasa da jikinta, tsawon mintuna kafin ya fito da kanshi ya haɗa uban gumi, sai faman sakin nishi take Yi tana haki kamar wadda tasha gudu

  "Ki rakani toilet muyi wanka, jikina ya 6aci sosai" harara ta jefa mashi"ni bazan bika ba, kaje wurin hajiya saratu tayi maka wanka" zaro ido yayi"ahaka ɗin" ɗaga mashi gira tai alamar eh.

  'Idan ta tambaye ni waye yai silar jefa ni yanayin Nan me kikaso in fada mata"

 Da shagwa6a tace"saika fada mata nice" da karfin hali ta furta hakan

 Dariya pravin yai"aiko da wa'adin aikin ki agidannan Ya ƙare, har kashe ki zata Iyayi, don ba ƙaramin kishine da ita ba, daga ni harke zata yi mana korar kare"


  "Kaga sai mu koma ƙauyanmu na indiya mucigaba da yin bautar shanu" dariya suka sanya gaba dayansu

 Bayan sun lafa ya sanya hannu biyu ya cuccu6eta Ya nufi bathroom da ita, Jim kadan Ya fito da ita ya ɗaurota saman kafadarshi, asaman gado ya kwantar da ita Yasanya mata bargo ya lullu6eta yana fadin"ki kwanta ki huta pls, bana son kina aikin wahala, inyaso da anjima saiki shiga cikin gidan" amsa mashi tayi da toh badan taji maganarshi ba.

 Shaf shaf Ya zura jallabiyarshi Yai mata sallama kafin ya fuce daga Cikin ɗakin, Fitarshi keda wuya wayar shi daya manta saman bedside drawer ta soma yin ringing,

 Ba tare data futo daga cikin bargon ba, Ta mika hannu tana laluban wayar har tayi nasarar Cafkota, ta fiddo da kanta tana duban screen din

   A tsanake ta furta sunan daya bayyana da manyan haruffa.


    *Jan le6e* ta6e baki ta ɗanyi aranta ta ayyana kowane ne wannan mai suna jan le6en? Sunan ma dariya yaso ya bata wai jan le6e, bazata Iya picking call dinba saboda Ya hanata ɗaga mashi phone idan aka kira, ko wayar bai bari ta ta6a ba, Sau ɗaya kiran ya shigo tai rejecting ba'a ƙara kira ba.


    Ajiye mashi wayar tayi saman drawer, ta dan lumshe idanuwanta yayin da zuciyarta ke tariyo mata fuskar kyakkyawan ɗansu da suka rasa, taji baƙin cikin mutuwarshi har yau idan ta tuna shi sai hawaye sun cika idanuwanta, tana matuƙar ƙaunar yaron, tsawon mintuna kafin ta yunƙura ta sauko daga saman gadon, donta kimtsa ta nufi kitchen.


Idan muka koma 6angaren Unaisah, tun bayan kammala sallar asuba, ta nufi ɗakin danish ba tare da sanin kowaba, tana shiga ta same shi kwance saman lallausar carpet din dakinshi amaimakon saman gadonshi, dogon hijabi ne a jikinta launin maroon, zuciyarta duk ba daɗi, daga gefenshi ta zauna tana duban kyakkyawar fuskarshi, lokaci ɗaya taji gabanta na faɗuwa, sakamakon ganin yadda yake firgita acikin baccin shi, da sauri ta ɗaura Hannayenta saman ƙirjinshi Nan fa hankalinta Ya ƙara tashi Jin temperature dinshi, kamar na daren jiya, lamarin Ya ɗaure mata kai, Ga sanyin A.c har yayi yawa amma shi zafi ne a jikinshi, babu sassauci,

 Muryarta na rawa ta soma ambaton sunanshi"Danish! my Man? Wake up! Meke damunka? Why nake jin jikinka da zafi" can cikin baccinshi yake jin miryarta.


  "Dan Allah ka tashi kayi min magana meke damunka? Baka da lafiyane"?

  Daƙyar ya samu damar ware idanuwanshi Akan fuskarta, 

A daddafe ya samu Ya miƙe zauna yana dubanta, Short din Jiyane a jikinshi da singlet.

   Yaji dadin ganinta a room dinshi, Jiya yai zaman jiranta yai tunanin zata zo gare shi har bacci yai awon gaba da shi bata leƙo ba, till now.

  "Kayi shiru baka ce min komai ba, danish zafin jikin ka yai yawa, kodai inje in faɗa ma Boss Man Yazo Ya duba ka"? Girgiza mata kai yai, kafin ya motsa la66ansa Ya furta"babu abunda ke damuna, Lafiyata qalou, kece kika 6ata min rai"

 Hankalinta bai kwanta da kalamanshi ba, aɗan ruɗe ta furta"ba haka bane danish, dole akwai abunda ke damunka ba Iya 6ata maka rai da nayi bane, cos babu yadda za'ai Jikinka yadau zafi rau batare da dalili ba, Please ka faɗamin idan ba haka ba hankalina bazai kwanta ba, sannan kayi hakuri dan Allah, abunda ya faru Jiya wanda ya 6ata maka rai, In sha Allah bazan ƙara bari Hakan Ya faru ba"

Cikin kulawa take Yi mashi magana, Jinjina mata kai yai"kiyi min alƙawarin ba zaki ƙara rungumar wani ƙato a jikinki ba, idan bani ba koda su Naufal ne" kiris ya rage ta saki dariya jin abunda yace

  Jinjina mashi kai tayi"in sha Allah My man kai kaɗai kawai," ajiyar zuciya ya sauke Ya samu sassaucin radadin da zuciyar shi ke yi mashi

 "Tunda naga yanzu hankalin ka ya kwanta fada min meke damunka? Menene ya haddasa maka zafin jikinka"? Ta faɗa tana duban ƙwayar idonshi, la66ansa duk sun bushe ƙamas.

  "Dagaske nake Yi maki babu abunda ke damuna, Nima bansan ya akai jikina ya ɗauki zafi ba"

  "Nidai hankalina bai kwanta ba, ka ba ni dama inje in faɗa ma boss man halin da kake aciki," haɗe mata fuska yai jin ta ambaci sunan boss man, sam bayason ji.

  "Bana buƙatar kowa ya dubani, ki kwantar da hankalin ki, zafin jikina baiyi min illa ba, don haka kija baki kiyi shiru" 

 Jinjina mashi kai tay"maganar abinci fa? Jiya kace min ba ka ci dinner dinka ba, ni sam Na shafa'a"

  Yamutsa mata fuska Yai, hada jifarta da harara, murmushi tasakar mashi

  "Bari naje na duba dining, idan an shirya mana abincin breakfast dinmu, zan shigo maka da naka a ɗaki tunda baka son fita" ɗaga mata gira yai alamar okey.

  Miƙewa tayi da sauri ta fice daga dakin ta sauko down stairs, koda ta duba ɗakin cin abincin ba a jera masu komai ba, saboda time din da suke zama Yin breakfast bai cika ba" yanke shawarar neman ɗakin Ummi tayi don ta fada mata game da ɗan uwansu dake jin yunwa, wata'ƙil ta sama mashi abunda zaici kafin a shirya masu abincinsu.

 Batasan ina zata nemo room din ummi ba, tadaisan acan upstairs Yake, cos ta ta6a ganin tana saukowa saman bene, da sauri ta nufi stairs din tana tafiya Hijabin Jikinta naja da ƙasa, babu kowa a palourn duk suna adaki.

  A hankali take taka stair cases din Har ta samu ta haura can sama, Ta rasa wace hanya zata bi wadda zata sada ta da bedroom din Ummin america, Tafiya taci daga dayi tana bin ko'ina da kallo, aranta tana ƙara jinjina haɗuwar ginin, tana ta ƴan kalle kalle kamar baƙauya harta zagayo ta 6angaren Hagu batare data gano hanyar da zatabi ba, Ƙofar wani katafaren room Ta dakata da yin tafiyar, aranta ta tace"idan kuwa wannan ne ɗakin aunty ummi duk Yafi namu kyau" Ta cikin glass din ƙofar take hangen zallar haɗuwar kayan alatun cikinsa, kifa kanta tayi jikin ƙofar har ta danna madannin Jikinta batare data an kare ba, da alama mamallakin ɗakin Yayi recieving alert na neman iznin shigowa shiyasa ƙofar tafara ƙoƙarin zugewa slowly take sliding, da sauri Unaisa Ta saki glass din Jin yana motsi, abunka game karanbani, ganin ƙofar ta wage, sai kawai ta haura ƙafarta ciki, yau ta ga maƙurar aljannar duniya a ɗakin data faɗo, wuyanta kamar zai 6alle, tana tafiya tana ƴan waige waige kamar zatayi tuntube, tayi mamakin dukiyar da aka narka wurin tsara Kayan furniture din dakin, Yana da fadi da tsayi, ga wannan floor to ceilling window din a left hand din bangon ɗakin, Ta jikin glass din zaka Iya hangen wajen ginin Harma da manya manyan gine ginen dake acikin burnin abuja, bayan haka daga cikin bedroom ɗin zaka Iya hangen komai na cikin bathroom ta glass din ƙofar, sai dai da alama ba haka akeyin wanka acikinshi ba, da akwai hanyar da ake rufe glass din yai duhu idan mutun zaiyi using dashi.


  Sai faman jinjina kai Unaisah take Yi, tajima tana mamakin wanene mamallakin daular nan da suke acikinta, bata ta6a yin tozali da shi ba, tadai ta6a jin sunan Chief of isod abakin Dr Laura.

     Tabbas Da ace tasan ɗakin wanene da batayi gigin shigarshi ba, ta zaƙe sai kurɗaɗawa take Yi can ciki ta shige kamar ɗakin baba tajo, shi kanshi bedroom din Yana da katafaren falonshi Har yaci uban na down stair haɗuwa, tana ƙoƙarin giftawa ta wata ƙofa dake a ɗakin, kwatsam kunnuwanta suka soma Jiyo mata sautin daddaɗan kiɗa Yana tashi, na taken waƙar satisfya


  Wani irin daddaɗan ƙamshi Ya ratsa hancinta sosai ta shaƙeshi, a hanzarce ta ɗaura idonta saman kofar ɗakin rubutun sama ta karanta kamar haka

   *Gym room" nan take ta fahinci dakin menene, wato wurin motsa jiki ne" aranta ta ayyana bari ta dan leƙa taga wanene Ya kunna sautin kiɗa.

  Kasancewar ƙofar abuɗe take, Unaisah ta zura kai kamar 6arauniya tana bin ko'ina da kallo, an ƙawata room din da injinan motsa jiki, kala kala, ga kayan jin sauti, sam bata lura da shi ba, kamar yadda shima bai lura da mutun ba, Yadaisan akwai wanda ya shigo dakinshi saboda alert din da yai recieving awayarshi, saida Ya bada iznin shigo ciki tukunna ƙofar ta buɗe.


Sai faman wurwurga eye balls dinta take tana bin ko'ina da kallo, lokacin da tayi arba dashi wani irin mugun bugu ƙirjinta Yai, har saida ta dafe shi da hannu, tayi matuƙar firgita da ganin shi, Ya tattara hankalinshi gaba ɗaya akan Punching bag din da yake kaima naushi da hannayensa waɗanda ke sanye cikin boxing gloves, Cikin zafin nama yake motsa jikinshi, Ya haɗa uban gumi, zufa ta ko'ina take tsattsafo mashi, ƙirar ƙarfinshi Ta bayyana ga wannan sick pack din ƙirjinshi ruɗu ruɗu, Damtsen hannayenshi sun murmurɗe, Yana naushin jakar motsa jikin Breast muscles dinshi na shaking, babu riga ajikinshi, black short ne kaɗai Ya sanya wanda Ya tsaya mashi dai dai gwiwarshi, bata samun damar ganin fuskarshi dakyau ba, saboda ba ita Yake fuskanta ba.

  Ta natsu tana kallonshi, Ko idonta bata ƙyaftawa, ba zato ba tsammani taji an damƙi wuyanta ta baya, harta buɗe baki zata fasa Ƙara taji anyi saurin toshe mata baki, tsoro Ya kamata jikinta ya hauyin kerma, ɗungurugum taji an dagata sama Anjata zuwa cikin bedroom din, sai faman wuntsila ƙafafuwanta take Yi a ƙoƙarinta nata kwace kanta daga hannun mutumin daya dauketa, har ƙofar ɗakin Ya fito da ita Ya direta ƙasa, A firgice take dubanshi, bakomai bane face Big guy, kayan kakinsu ne a jikinshi, ya sanya face mask a saman fuskarshi, idanuwanshi na akan fuskarta, La66anta na kerma ta furta"wa..wa.. Wanene kai? Meyasa ka daukoni? Idanma saboda nashiga ɗakinne aini bansan ya akai na shiga ba, rashin sanine, ɗakin aunty ummi nake nema, danish ne Yake jin yunwa jiya baici dinner din shi ba kuma na duba dining ba'a shirya mana abinci ba" tsabar ruɗune yasa take yi mashi zuba har abunda bai tambayeta ba, taƙi barima Yai mata magana

 Sai da ta dasa aya tukunna Ya soma yi mata magana cikin muryar raɗa"kinsan ɗakin wanene kika shiga"? Girgiza mashi kai tayi alamar a"a gyaɗa kai yai"kada ki kuskura ki ƙara yunƙuri shiga ciki, Idan ba haka ba jikin kine zai gaya maki, Ni nayi mamakin ma taya akai kika samu damar shiga bayan ita kanta ƙofar sarrafata akeyi, Kodai ba mutun bace ke"? Ya fada haɗi da ɗage mata gira alamar yana jiran amsarta.

  Duk tabi tasha jinin jikinta, sai faman zare mashi gray eyes dinta take Yi, daƙyar Ta iya fadin"nifa bansan komai ba, ai na fada maka dakin aunty ummi nake nema" ta ƙare maganar tana murguɗa mashi baki.

 Har murmushi yasakar mata batare data gani ba saboda mask din fuskarshi, dama Yaji labarin rashin jin maganarta, gashi yanzu ya tabbatar dahakan"

  "Okey, ki koma ɗaki, yanzu zanzo in kawo maki abunda shi ɗan uwan naki zaici, kafin Ashirya maku naku abincin" amsa mashi tayi da toh, jikinta har rawa yake Yi wurin yin saurin haura ƙafa ta kama hanyar komawa ɗakin danish, tana tafiya haɗi da waiwayan big guy, Yana atsaye yana kallonta har saida ta 6ace ma ganin shi, tukunna ya kawar da idonshi daga gareta.

  Tun da ta koma ɗakin danish bata daina tariyo suffar mutumin da tayi tozali dashi a gym room ba, Ya tsaya mata aranta, taso ace sunyi ido biyu da shi, don ta samu damar ƙare ma fuskarshi kallo, shin wanene shi? Tabbas tanaso ta sani!

   Bada jimawa ba, Big guy yai sallama dakin danish, hannunshi ruƙe da tray din Kayan abinci ashake, bayan ta kar6a tayi mashi godiya, asaman carpet suka zauna ita da danish, ta dinga bashi abaki Yana ci, suna kallon juna yayin da acan ƙasan zuciyarta tunanin ɗan ta halikin nan take Yi, shi kanshi danish Ya lura da canzawarta, saboda tsabar tunani har a hanci tai ƙoƙarin cusa mashi abinci, saida ya damƙo hannunta tukunna ta ankara, yace mata me take tunanine tace mashi bakomai, badan ya yarda ba ya ƙyaleta,  A ɗakinshi ta zauna duk don ta faranta mashi, sai da tasanyashi yai wanka ya canza kayan jikinshi tukunna hankalinta ya kwanta, damuwarta ɗaya yanzu zafin jikinshi sai ƙara ninkuwa yake Yi.


*Obie Estate*


Wuraren ƙarfe huɗu da rabi Estate din Ya cika maƙil da mutane babu masaka tsinke, manya mutane masu faɗa aji duk sun hallara, kama daga Ƴa'ƴan jam'iyarsu ta Action progressive party ministoci, sanatoci, gomnoni, da sauransu, Kowannansu Ya ɗauki wankan expensive shadda ta kece raini na shiga tsara, jikokin Obinna Na ƙasa  nigeria da wadanda ma basa ƙasar saboda shagalin nan sun dawo Nigeria A yau din nan, daga cikinsu akwai ya'yan sir mubarak mazauna kasar canada, zaratan samari Zaki shine babban ɗanshi mai bi mashi Ibad, bayansu sai ƴa'ƴan His excellency abdul razak, babban danshi Yasir, tare da ƙanwarshi Yusra, sunzo ne tare da mahaifiyarsu Her excellency hajiya muhibbat, bayan su sai Ya'yan his excellency Deen, babban ɗanshi Justice Nadeem mai bi mashi Dr. nawaz tare da mahaifiyarsu suka zo Her excellency hajiya Jamila, bayansu kuma sai ƴar gidan mai girma sharafudden Hindu ƙanwar Chief Owais, tare da matayanshi suka zo Hajiya Malikat sarauta uwar gidanshi da kishiyarta Hajiya laurat, da kuma ƴar wurin Lateef zulaihat kanwar ziyad, gaba ɗayansu dai kowa Ya hallara ga yan matan hateem Nazli and Yazrin, gaba ɗaya matan sun ɗauki wankan Swiss cord lace yayi bala'en Yi masu kyau, A babban hall din dake acikin gidan aka gudanar da shagalin, An ƙawata cikinsa da kayan alatu, ko'ina ka kalla furannine da ƙyalƙyalin sparkling chandeliers, ga Banquet chairs da aka tanada domin baki su zauna, kowani table saman shi an ɗaura bouquet of flowers, tare da Crystal glasses and silverware, da sauransu, floor din hall din kuwa an shimfiɗe shi da ƙayataccen red carpet, daga can gaban hall din Gingirimeman Cake stand ne an ƙawata shi sosai, Mawaƙa da makaɗa hada maroƙa sun hallara, domin suma su kwashi rabonsu, an shirya kayan abinci saman   zungureran table kala daban daban, sai mutun Ya za6a ya darje, duk haɗuwar taron nan mutun ɗayane bai hallaraba, Hakan ba ƙaramin ta6a zuciyar obie yai na, Yaci buri akan zuwanshi amma shiru babu shi babu alamarshi, mutane sai tambayar shi suke Yi, ya akai basu ganshi ba? Iyayenshi sun rasa amsar dazasu basu, sai dai suka dinga cewa bai kaiga zuwa ƙasar ba, farin jini gare shi shiyasa duk wanda yazo sai ya tambayi ina owais Yake, Taro Yayi albarka, Anci ansha anyi kullu wash rabu hani'an, Anyi harka ta arziƙi ta kece raini, daruruwan mutanan dasuka kawo mashi kyauta taban mamaki basu ƙirgiwa, baba obie Ya mori lokacin shi, Yayi farin cikin dabazai Iya misalta shi ba, Ƴan uwa da abokanan arziƙi sun faranta mashi rai, sun gwangwajeshi da Kyaututtuka na ban mamaki, Sun taka rawar girma, sai dai muce Alhamdulillah taro Ya tashi Lafiya, gab da magrib baƙi suka ragu waɗanda suka rage ƴan uwane na jini, da kuma mutanan Hateem. 

  *✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post