DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✊✍️💋🤍
A tsiyace yai parking din motar, tsabar sauri a buɗe yabarta, da gudun gaske ya nufi cikin gidan batare da jin shakkar komai ba, Shigar shi keda wuya cikin falon ya soma jiyo sautin kukan yarinyar nan mai fama da ta6in hankali, ta dage sai zazzaga masifa take yi tana fadin"wallahi saina tona maku asiri ranar lahira, dukanku sai kun shiga wuta tun da ku ka ta6a min yaya jazz ɗina". Zuciyarshi ce ta soma dukan uku uku, zaro bindigarshi dake soke a ƙugunshi yai, cikin sanɗa yake tafiya yana tunkarar Upstairs, Ya haura second floor, daga ƙofar ɗakin Ya la6e Yana sauraronsu.
"Ki daina magana mana, bakiji suna bada hakuri ba? Kuskure suka yi wurin bugunshi, bada son ransu ba"
Jin muryar mutuminsu yasa shi yin wuff Ya afka cikin ɗakin, Jin takun tafiyarshi ne Ya janyo hankulansu ga dubanshi, kusan atare suka ɗago suna kallon shi.
Nauyayyar ajiyar zuciya big guy ya sauke haɗi da furta"Ya Allah" kafin Ya daura eyes dinshi akan face din mutumin yace"meke faruwa ne ? Waya ta6a khadeeja take kuka? ya akai naga yaran duk sun farka daga bacci"?
A ruɗe yake jefa mashi tambayoyin, sam bai lura da Sojojin ba, waɗanda tun da ya shigo suke dubanshi da mamaki.
da ido mutumin Yai mashi nuni da sojojin"gasu nan, mahaifin Jazz ne yazo tare dasu, wani abune ya faru na rashin fahimta da yajawo har suka bugi jazz shine take ta kuka"
A hanzarce ya mayar da dubanshi ga Sojojin, Kusan atare suka buga ƙafa tare da Sara mashi.
Jinjina kanshi yaɗanyi da mamaki ya furta"Tiger ! Army Boy! Ya akai kukazo gidan nan?
"Tsautsayi da ƙaddara" acewar Tiger, Army ya kwashe duk abunda ya faru ya sanar da Big guy, sai lokacin ya lura da jinin dr jazz daya daskare saman floor, ga kuma Dressing mirror da daya fashe ta silar buga kan jazz jikinshi, cikin matsanancin tashin hankali ya furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji!"
Cikin sanyin murya Army Boy yace"sai haƙuri yalla6ai, rashin sanine, tabbas munyi kuskure, amma shima jazz din hada laifinshi, Yakamata ace komai zai yi ya sanar da Sir mubarak a matsayin shi na mahaifinshi bawai yayi gamon kanshi ba, kuma a yanayin yadda Sir mubarak yake riskarshi Yana yin waya ta sirri, kalaman da yake furtawa sun yi kamanceceniya dana masu safarar mutane"
Tiger ya ɗaura da cewa"yanzu haka sun tafi asibiti dashi, Muna jira muji daga gare su, In sha Allah zaiji sauƙi"
Numfasawa big guy yai, jikinshi duk yai sanyi kamar wanda aka zarewa laka, babban tashin hankalin shi halin da suka jefa jazz basu ta6a tsammanin abun zai jaza mashi matsala ba.
Tuni idanuwan big guy sun kaɗa jawur tamkar zai fashe da kuka Ya soma yin magana"ba laifin shi bane, laifinmu ne da muka hanashi yasanar ma kowa dangane da aikin da muka sanya shi, saboda bama son kowa ya sani"
komawa yai daga gefen gadon dakin Ya zauna, Yana duban Yaran dake raku6e jikin bango, idanuwansu sunyi luhu luhu.
Mai ta6in hankalin tuni tayi shiru, sai faman zazzare idanuwanta take Yi tana dubansu.
Tiger yace"shi kanshi Chief Owais bazai ji dadi ba, ranshi zai Iya 6aci amma nasan zai fahince mu"
Ganin yadda yaran suketa Yin hammar bacci, yasa Big guy yi masu magana"Kuje ku kwanta, Zuwa gobe idan Jazz Yaji sauƙi zamu dawo maku dashi"
Miƙewa su ka yi a jere suka nufi hanyar fita daga ɗakin jikinsu babu ƙwari, hankalinsu ba kwance yake ba saboda Jazz dinsu da babu lafiya.
Har sun kusa fita daga ɗakin, Big guy ya kwaɗawa ɗaya daga cikinsu Kira "Hawwa! zonan, matashiyar daya kira da hawwa ta juyo tana dubanshi, Ki ruƙe hannun khadeeja ku tafi da ita daki ta kwanta" ya fadi hakanne don yasan su kadaine zasu Iya control dinta har asamu tayi bacci.
Muryarta ashaƙe take fadin"ni bazan bisu ba, kuma bazan Yi baccin ba, wallahi sai kun dawo mun da jazz dina"
Lallashinta mutumin dake ruƙe da ita ya somayi"kinsan dai bazanyi maki ƙarya ba khadeejata, da kaina zan dawo maki dashi, Yanzu dai kije ki kwanta gobe zaki ganshi, amma idan har bakiyi bacci ba, toh bazan dawo maki dashi ba"
Kwa6e mashi fuska tayi"kayi alƙawari"?
Jinjina mata kai yai"in sha Allah" ta amsa mashi da toh, sakarni inje in kwanta" sakinta yai, tafiyarta sam babu natsuwa da sauri ta nufi su hawwa ta ruƙe hannunta acikin nata suka fuce daga ɗakin.
Bayan fitarsu, Big guy ya miƙe ya dubi mutumin"Muna buƙatarka da gaggawa, ka koma ɗaki ka sanya sutura a jikinka, idan kuma zamu Iya tafiya haka toh," ya fada yana nuna gajeran wandon jikin shi da hannu.
Mutumin yace"bari naje na sanya jallabiya, ƙwara aganni da mutuncina" da zolaya ya faɗa, murmushi sojojin suka saki, fice wa yai daga dakin.
"Yalla6ai wani abu na faruwane"? Tiger ne ya jefa ma Big guy tambaya"kusan haka sai dai kasan yanayin aikin mu" jinjina kai big guy yai don ya fahimce me yake nufi
Shigowa ɗakin matashin saurayin yai, Jikinshi sanye da jallabiya fara tayi mashi kyau.
Miƙewa big guy yai tare da kallon su tiger"zamu tafi gidan chief, babu tabbacin zamu dawo yau, wani muhimmin aikine me girma agaban mu, dan Allah ku kula da yaran, babu wadataccen tsaro agidan" amsa mashi sukayi da toh, army boy yace"Amma yalla6ai zaku sanarma chief abunda ya faru tsakanin Jazz da sir mubarak"?
Big guy yace"ya zama dole mu sanar dashi, sai dai ba yanzu ba tunda shi kanshi hankalin shi ba akwance yake ba, amma idan komai ya lafa zamu fada mashi" gyaɗa kai army yai"okey, Allah ya tsare hanya"
Amsa mashi yai da ameen, kafin Yaja hannun mutumin suka fito daga gidan, jin ƙarar tashin motarsu, Yasa Army da tiger suka sauko down, zuwa sukayi bakin gate din gidan suka datse shi, kafin suka koma palour suka zauna saman sofa suna fuskantar juna
Army boy yace"tiger ya kaga yaran? Nayi mamakin kyawunsu, Allah yasa oga ya amince min in samu matar aure acikinsu" tunkan ya ƙare maganar tiger ya wurga mashi kallon harara"amma baka da hankali, kai waɗannan yaran sunyi maka kama da matan yaku bayi? Ka manta matsayinka ne? Karfa ka cika zaƙewa, wallahi yazu kaji ka a saman kujerar lantarki kana kar6ar punishment, ni kaina ƴan matan sun burgeni, gaskiya Oga ya iya kiwo, fatarsu har ƙyalli take Yi sunji hutu abunsu, yara kamar matan aljanna gashi har gadon baya, gaskiya dakyar idan iyayensu ƴan nigeria ne"
Ya fada yana yin hamma"ni yanwa ma nake ji, Allah yasa suna da abinci agidan, nasan ba za'a rasa farfesu ba tunda Chief owais ne ke kula da cinsu nasan za'ayi harka ta arziƙi, duba mana kitchen dinsu" yai maganar Yana duban Army boy, miƙewa yai da sauri ya nufi hanyar kitchen, har zai wuce yaci karo da freezer, buɗewa yai ya leƙa ciki, Kayan marmarine nunannu, da drinks"
washe baki yai yana faman shafa ciki yace"mutumin yaufa kakarmu ta yanke saƙa"
Tiger yace"ba kallo zaka tsaya yi ba, ka shiga kitchen ka dauko tray ka kwaso mana sauran abincin da suka rage" amsa mashi yai da toh, da sauri ya shiga kitchen.
Jim kaɗan sai gashi ya fito hannunshi ruƙe da katon tray, daga saman tray din plate biyu ne, ɗaya na fried rice daya kuma na chicken wings, saida ya fara tsayawa agaban freezer ya buɗe ya dauko masu kayan marmari ya jera gefen plates din ya ƙara da robobin juice masu sanyi, tiger sai faman haɗiye yawu yake yi,.
Zama su ka yi saman lallausar carpet din falon, kamar masu fama da ciwon yunwa haka suka dumbuza hannu, sunaci suna fira.
Kamar daga saman suka jiyo muryar matashiyar nan mai fama da ta6in hankali tana fadin"wayyo Allah, mayu zasu cinye mana abincinmu!" afirgice suka ɗago suna kallonta, daga can saman bene take zazzaga masu masifa, gashin kanta duk ya rufe gefe da gefen fuskarta, da gudu ƴar uwarta hawwa ta fito daga ɗaki, Taja hannunta suka koma ciki, ta rufe kofar ta yadda bazata sake fita ba.
Tiger yace"jarababba, wallahi hartasa gabana ya fadi" ya fada yana dariya
Army yace"ai daga ganinta anyi rashin ji a ƙuruciyarta, kunnuwanta tsaitsaye suke irin na zomo, gata kyakkyawa da ita" cigaba da cin abincinsu sukayi hankalinsu kwance, bayan sun kammala army boy ya tattara kayan abincin ya maidasu kitchen, a saman sofa suka kwanta ga sanyin A.c, sufa ashar kakarsu ta yanke saƙa.
*Daular Alhaji Musa*
*BENAZIR💔*
Tayi nisa acikin baccinta, ba zato ba tsammani taji an shaƙe mata wuyanta, shaƙa bata wasaba, nan take numfashinta ya soma kiciniyar ɗauke wa, mutsu mutsu ta somayi yi tana harba ƙafafuwanta, hannayenta biyu ta daura saman wuyanta a ƙoƙarinta nata kwace kanta daga hannun mutumin dake yunkurin kasheta, wata irin zuface ta soma tsastsafo mata saman goshinta, zuciyarta tashiga harbawa da ƙarfi da ƙarfi, ta zazzare idanuwanta cikin duhu bata Iya ganin komai saboda sun kashe ƙwan dakin, duk yadda taso ta ƙwaci kanta ta kasa, an toshe mata baki babu halin ta ƙwala kira don azo ataimaketa, hannunta tadinga lalubawa saman mattress cikin sa'a ta cafko hannun zeenatu dake akwance gefenta, cikin fitar hayyaci take tsunkulinta har saida zeenatu ta farka tana shessheƙar kuka ta furta"wai.. wanene ke cunkulina" tunda zeenatu tayi magana, Benazir taji an sakar mata wuyanta, fashewa tayi da matsanancin kuka, sakamakon raɗaɗin azabar da taji wuyanta nayi mata, a matuƙar ruɗe zeenatu takai hannu saman bedside drawer ta kunna fitila haskenta ya haskaka saman gadon, muryarta adabarbarce take fadin"Auntyna meya faru kike kuka? Baki da lafiya ne"? da rarrafe ta ƙarasa gaban benazir tana duban fuskarta, a lokacin ta zabura a furgice ta mike zaune tana faman sauke ajiyar zuciya hannunta biyu ruƙe da wuyanta, fuskarta tayi sharkaf da zuba, maƙoshinta ya bushe ƙamas, tsananin rudanine ya kamata, kokwanto ta somayi akan abunda ya faru da ita shin dagaske ne wani ya shaƙe mata wuyanta ko kuwa mafarkine take yi"?
"Aunty Benazir dina, dan Allah kiyi min magana, meyasa ki yin kuka? Ko kinyi mafarki ne? Sam takasa buɗe baki tayi ma zeenatu magana sai faman zazzare manyan idanuwanta take Yi tamkar kwayar zasu faɗo kasa, haƙika ta shaƙi ƙamshin mutuwa.
Dafa kafaɗarta zeenatu tayi"mafarki kikayi aunty? ko wuyanki yana yi maki ciwo ne" ta fada cikin kulawa da nuna damuwa take duban fuskar benazir.
Dogon numfashi benazir taja yayin da zuciyarta ke harbawa da sauti mai ƙarfi, tsantsar tashin hankaline da fargaba akan fuskarta, gaba ɗaya ta dabarbace tarasa gane meke shirin faruwa da ita! Idan mafarki ne tayi an shaƙe mata wuya meyasa take jin raɗaɗin bayan tafarka daga bacci?
Shessheƙar kukan zeenatu ne Ya fargar da ita, tana faman haɗiyar yawu idanuwanta da fargaba take duban zeenatu
Daƙyar ta iya buɗe baki ta yi mata" magana"zeenatu ruwa! Ruwan zan sha"
Tsagaitawa zeenatu tayi da yin kukan jiki na rawa ta sauko daga saman gadon, ta nufi ƙaramin frigde din ɗakin, ta buɗe ta ɗauko mata bottle water me sanyi ta dawo ta haura saman gadon ta miƙe ma benazir, yatsun hannunta na kerma ta kar6i roba ruwan tacire nurfin ta kafa abaki tana sha, maƙoshinta har sauti yake badawa kwat !kwat!. zeenatu ta natsu tana kallonta, gaba ɗayansu sleeping dress ne ajikinsu.
Bayan ta gama shanye ruwan ta daura bottle din saman drawern gefen gadon,
Ajiyar zuciya tadan sauke, kafin ta dubi zeenatu data kwa6e fuska idanuwanta sunyi luhu luhu bacci bai isheta ba an tashe ta daga bacci
"Aunty ki faɗamin meke damunki"
Lumshe ido benazir tadanyi kafin ta waresu akan fuskar Zeenatu
"Babu komai ƙanwata, mummunan mafarkine nayi"
Ajiyar zuciya zeenatu tasauke"amma aunty kin tada min hankalina, nayi tsammanin wani abunne ke damunki ko baki da lafiya, kuma naji kina cunkulina" ta fada tana nuna mata damtsen hannunta, fatar wurin tayi jawur saboda tsunkulin da benazir tayi mata kiris ya rage ta fashe.
Jikin benazir ba ƙaramin sanyi yayi ba, ganin irin illar da tayi mata
"Kiyi haƙuri ƙanwata, bansan nayi ba, cikin magagin baccine na cunkule ki"
Murmushi zeenatu tasakar mata"kada ki damu auntyna, na fahimce ki," ƙaƙalo murmushi benazir tayi yarinyar ba ƙaramin burgeta take Yi ba, ta damu da ita sosai,
"Ki koma baccinki, kada ki makara a school gobe"
Muryar zeenatu da shagwa6a tace"ae bana zuwa makaranta tunda na kammala secondry school daddy ya hanani cigaba da karatu, yace wai sai idan nayi aure mijin da zan aura ya amince min in cigaba da karatu tukunna zani barni"
Jinjina kai benazir tayi har yanzu bata warware daga fargabar abunda ya faru da ita ba, dauriyace kawai take Yi don kawar mata da damuwar dake atare da ita.
"Idan kina son karatun, meyasa ba zaki fidda miji ba? Duk da ni aganina kinyi ƙaranta da aure, gaskiya uncle bai kyauta maki ba"
Sunnar dakai ƙasa tayi cikin jin kunyar benazir tace"to ai nima inason nayi auran kuma ma ina da mijin da zan aura" da zolaya Benazir ta zaro idanuwanta masu dauke da bacci, da sauri zeenatu ta daura kanta saman pillow tana dariya
Kallon bayanta benazir tayi fuskarta dauke da murmushi,
"Faɗamin sunan saurayin naki inji idan yayi mani"
Muryarta ƙasa ƙasa tace"ki tambayi yaya shureim, yasan shi zai fada maki sunanshi" benazir bata kawo komai aranta ba, tace"to zan tambayeshi idan Allah yakaimu gobe, yanzu dai mu kwanta muyi bacci" amsa mata tayi da toh, atare suka kwanta, hankalin benazir yaƙi kwanciya gani take tamkar abunda ya faru a mafarkinta zai faru gaske, hakan yasa ta rungume Zeenatu ajikinta, gudun kada aƙara shaƙeta, addu'o'i ta karanto ta tottofa masu kafin ta lumshe idanuwanta.
Bakomai take tariyowa ba face fuskar tajuddeen, da fuskar baby din data bari acikin kwamin wanka, tuni hawaye sun wanke fuskarta, taƙosa su dawo ƙasar, fatanta Allah Yasa taj dinta baiyi aure ba, da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita.
*Ex-prisoners💔*
Tsoro da fargaba ya hanasu runtsawa, sunyi zazzaune saman dining chairs, ummin america bata ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, sam takasa samun natsuwa, jefi jefi takan dago da ido ta dubi su Batul, Har yanzu hanna bata fito daga ƙarƙashin table ba.
Jemimah tana azaune saman laps din Haris Ta ƙankameshi tuni bacci yajima da yin awon gaba da ita, abun duniya ya ishi Parveen, Jikinta sai rawar ɗari yake yi saboda ruwan data watsa ma rigarta, ta jiƙe sharkaf, ga sanyin a.c abu goma da ashirin, azeeza data suma ta farfado tun bayan da sajeed Ya yayyafa mata ruwa, sai faman firgita take Yi, macijin tamkar Yana yi masu gizau, ga bacci a idanuwansu sai dai sun kasa runtsawa, kowa da abunda ke damunshi basu san meke wakana acikin gidan ba.
"Dan Allah Ku bani mayafinku In lullu6e jikina sanyi nake ji" parveen ce tayi maganar, babu musu Batul Ta curo mayafinta ta miƙa mata ta sanya hannu ta kar6a ta lullu6a shi ajikinta.
"Ni nakasa gane meke faruwa! ya akai maciji Ya shigo gidan nan? Ummi ce ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta.
Shiru sukayi babu wanda ya tanka mata, babban abunda suke jima fargaba kada ace mutanan prison ne suka kawo masu hari, shiyasa duk jikinsu yayi sanyi.
"Ni abunda ke damuna, Danish dinmu da unaisah, bansan awani hali suke aciki ba, Allah yasa babu abunda ya same su" In a cool voice Batul ta furta maganar.
Tamkar ta tsokano Jemimah, cikin bacci ta fashe da kuka tana sambatun"wayyo Allah genie dina, dodo zai cinyeta, kuje ku dauko mun ita" da sauri Haris Ya toshe mata bakinta da tafun hannunshi"kiyi mana shiru, ko so kike dodon Ya jiyo kukanki yazo wurinmu"?
Ba tare data buɗe idanuwanta ba tace"a'a amma genie fa? Tana can ita da Danish dodo zai cutar dasu, Ni dai ku ƙyaleni inje wurinsu" ta faɗa tare da buɗe kumburarrun idanuwanta, da ƙarfin hali tasoma kiciniyar saukowa daga saman laps din haris don ta fita daga dakin
Ummi tace"kada ka bari ta sauko ka ruƙeta, idan ba haka ba zata iya janyo mana macijin nan"
Amsa mata yai da toh, ya rurruƙe jemimah ajikinshi.
"Ki kwantar da hankalinki, babu abunda zai samu Unaisah, ai naga mutanan nan masu baƙaƙen kaya, wata'ƙil ma harsun kashe shi"
Javed ne yayi maganar, jemimah dai taƙi haƙura, tacika masu kunnuwa da shessheƙar kuka.
Ƙwanƙwasa glass din ƙofar da akayine ya firgitar dasu, arazane suka dago duka a tunaninsu macijin ne Ya daki glass ɗin, ganin Boss Man yasa suka sauke ajiyar zuciya, jiki na rawa Ummi ta miƙe ta nufi ƙofar, ta bude mashi bai shigo ba daga waje Ya tsaya.
"Ina macijin"? Tambayar data fara jefa mashi kenan"
Yayi mamakin ganin yadda jikinta ke rawa, har saida yadan saki murmushi ta cikin face mask dinshi
"Haba ummi tsoronshi kike ji kema"?
Ta6e baki tadanyi kafin tace"bazaka gane bane, wallahi na firgita macijin yayi girma dayawa"
"Ki kwantar da hankalinki, ba maciji bane mutunne nasan ko nayi maki bayani ba lallai ki fahimce ni ba"
Zaro ido waje tayi"what! Kana nufin mutunne? Tayaya haka zata yiwu"? A rude ta jefa mashi tambayar
"Kodai kana nufin abunda naji unaisa tana faɗi gaskiyane? Na cewa Danish ne ya zama maciji"!
Jinjina mata kai yai"hakane, gaskiya ta faɗi"
Cikin jin faɗuwar gaba ummi tace"ni dama najima ina zargin yaron nan ba mutun bane, saboda kyanshi yayi yawa ashe aljanine"
Boss yace"ba aljani bane, mutunne shi kamar kowa, yanzu bani da isasshen lokaci, zuwa gobe da safe zanyi maki bayani," tsantsar mamakine Ya kamata.
Muryar Jemimah ce tajanyo hankalinshi ga kallonsu"Boss man ina genie ɗita? Dodon nan ya cinye min ita ko"
Shiga cikin ɗakin yai, sam sun kasa motsawa suna jin muryarshi sai dai tsoro Ya hana su je gare shi
Ɗaya bayan ɗaya yake dubansu,
"Dan Allah ku kashe abunnan bamu son ganinshi duk ya firgitar damu" parveen ce tayi maganar tana dubanshi
Batul tace"boss ina ƴan uwanmu suke ne? Bamusan awani hali suke ciki ba"
Goya hannayensa yai saman ƙirjinshi Yana dubansu
"Basai nayi maku bayani ba, unaisah ce zata faɗa maku komai, abunda nakeso daku Yanzu ku kwantar da hankulanku, Ku tashi muje na raka ku ɗaki ku kwanta kuyi bacci, dare yayi sosai kusan ƙarfe goma sha daya da rabi"
"Nidai bazan kwanta bacci ba, sai naga genie dita" acewar jemimah
Azeeza sarkin tsoro tace"bazan Iya kwana aɗaki ba, wannan abun zai Iya faɗowa ɗakin Ya cutar damu"
Dama yasan da wuya su iya kwantar da hankalinsu.
Kallon Ummi yai"please ki tafi da dasu ɗakinki su kwana kafin zuwa gobe idan komai ya lafa, sai su koma nasu ɗakin"
"Badamuwa, ku tashi mu tafi" acewar ummi.
Miƙewa sukayi daga saman kujerun, matan dake acikinsu, Batul azeeza da jamimah, Boss Yace"Ina ƴar uwarku Hannah"?
"Gatanan ƙarƙashin table," sajeed ne ya faɗa tare da duƙawa ya janyota da ƙyar, ta ƙudundune kanta kamar kifin gwangwani,.
"Hanna ki tashi ku tafi" daƙyar ta miƙe tsaye zufa duk ta wanke fuskarta,
"Sannu da jiki" boss ne yai mata maganar, sai faman zazzare idanuwanta take Yi.
"Zanje na rakasu ɗaki, Sajeed ka tafi da sauran ƴan uwanku maza" amsa mashi yai da toh,
Tamkar karsu fita daga dining room din, gani suke kamar macijin zai dawo masu, badan boss na atare dasu ba dakuwa babu wanda zai Iya fitar dasu saboda tsoratar da suka Yi, asaman bayanshi Ya goya azeeza, ummi ta dauki jemimah abayanta, Batul ta ruƙo hannun parveen dana Hannah, Ahaka suka jera suna tafiya har suka ƙarasa ga second floor, a ƙofar dakin ummi suka dakata dayin tafiyar, ta buɗe kofar suka shiga daga cikin, bayan boss Ya sauke azeeza daga saman bayanshi yayi masu sallama ya juya ya fuce.
Sai faman baza ido suke Yi, Yau gasu adakin Ummi, Bedroom ɗinta Ya haɗu kamar na amarya, an zuba mata kayan alatu.
Ganin ya fuce daga ɗakin Yasa tayi saurin zuwa tayi locking din ƙofar, tabi windows din dakin ta zugesu, tukunna hankalinta Ya kwanta.
Dubansu tayi sunyi tsaitsaye curko curko suna jiran umarninta
"Parveen ki shiga toilet ki ƙara tsarkake jikinki" amsa mata tayi da toh, a tsorace ta shiga toilet din.
Kallon jamimah da azeeza tayi"akwai wadda takeyi fitsarin kwance acikin ku"? Girgiza mata kai sukayi alamar a'a
"Ke fa"? Ta jefa ma batool tambayar
Itama tace a'a,
Gyaɗa kai tayi"okey, amma gadon bazai ishemu ba, Ni ban saba kwana atakure ba, mutun biyune zasu samu damar hawa gado, Biyu sai su kwana saman carpet" tayi maganar tana nuna masu carpet din dake a shimfiɗe.
"Ga kuma Sofa wazai kwana asama"? Ta fada tana dubansu
Maƙe kafaɗa jemimah tayi"ni wallahi bazan kwana saman carpet ba, tsoro nake ji,"
"Nima bazan Iya kwana ƙasa ba, dan Allah kibari mu kwana saman gadon mu duka" Azeeza ce tayi maganar tana marairaice mata fuska don taji tausayinta.
Ta6e baki Ummi tayi"takura ke bana so, na saba kwana ni kadai asaman gado"
Cikin sanyin murya batool tace"ni da parveen zamu kwana saman carpet din, Azeeza da jemimah sai su kwana saman gadon"
Ummi tace"kinyi kyan kai, haka akeson babba yakasance mai sadaukarwa ga ƙannansa" ta fada tana sakin murmushin shaƙiyanci.
"Kuje ku kwanto tom and jerry" ruƙo hannun jemimah Aziza tayi suka nufi gado atare suka haye saman mattress din.
Fitowa parveen tayi daga toilet, duk ta jiƙe jikinta
"Dakata daga nan kada ki 6ata min ɗaki da ruwa, meyasa baki tsane jikinki ba"? da wulakanci take Yi masu magana.
Shiru parveen tayi batare datace komai ba sai batul ce tace"kiyi hakuri dan Allah, parveen ki koma toilet ki tsane jikinki, aunty ummi ki taimaka mata da kayan da zata sanya kafin gobe"
Yamutsa fuska ummi tayi jin abunda batul tace"wato raini yafara shiga tsakanina daku ko?! Ke ba ki ji kunyar cewa In ara mata kayana ta sanya ba"!
Idanuwan batul tuni sun ciko tab da ƙwalla
"Kiyi haƙuri in na 6ata maki rai" tsoki ummi taja,
Atsawace tace"kai ni dallah kuzo ku kwanta inaso zan kashe hasken ɗakina"
Jikin parveen yai sanyi ga sanyi da take ji, gani suke kamar ummi ta canza masu kodan saboda sunzo kwana dakinta ne shiyasa take yi masu wulakanci"
"Aunty ummi dan Allah ki kashe mana sanyin ɗakin kodan saboda parveen" harara ummi ta watsa mata
"Bana iya kwana babu a.c, sai dai kuyi hakuri" ta faɗa tana faman sakin shu'umin murmushi.
Gyaɗa kai Batul tayi tare da kallon parveen tace
"bari na baki rigata ki sanya, ni saiki bani taki" dariyar shaƙiyanci ummi tasaki jin abunda batul tace
"Kibarshi batul ke kuma fa"? Idanuwanta acike tab da kwalla ta furta hakan
Murmushin yaƙe batul tasakar mata"kada ki damu dani, zan iya jure sanyin muje cikin toilet din ki canza rigar"
Komawa cikin toilet din sukayi, Batul ta cire rigarta taba parveen ta sanya ita kuma ta zura rigar parveen da ruwa ya jiƙeta, ahaka suka fito hannunsu ruƙe dana juna.
A kishingiɗe suka sami ummi saman gado ta ɗaura kanta saman pillow. Jemimah da azeeza suna can gefe ɗaya sun rungume junansu bacci tuni yajima dayin awon gaba da su.
Ko kallon inda take basuyi ba, tabasu mamaki ga uban space a gadon amma ta hana su kwanciya.
Asaman carpet suka kwanta, sanyi ya fara ta kurama Batul, Jikinta ya hau yin kakarwa, don mugunta ashe bayan shigarsu toilet ummi ta ƙara gudun A.c din dakin, tasan dole su nemi alfarmar ta basu bargo su lullu6e, don taji dadin zabga masu rashin mutunci
Kasa runtsawa batul tayi atakure ta miƙe zaune tana faman ƙanƙame jikinta, tace"aunty ummi ki taimaka mana da bargo, sanyi muke ji"
Tamkar bata ji me batul tace ba, saima ta runtse idanuwanta kamar mai yin bacci.
Batul tayi tunanin bacci takeyi hakan yasa ta ƙara ɗaga murya tana fadin"Aunty ummi bargo dan Allah" banza tayi da ita, a ƙarshe sai dai batul ta haƙura, jikinta nata kakarwa ahaka ta kwanta, sanyi tamkar zaiyi mata illa, bacci ya ƙauracewa idanuwanta, ita kadaice acikinsu batasamu damar runtsawa ba, parveen tuni ta nutsa cikin baccinta.
Sai da ummi ta tabbatarwa kanta cewa bacci ya ɗaukesu tukunna ta sauko daga saman gadonta, leƙen fuskokinsu tadinga yi don taga idon akwai wanda baiyi bacci ba, a lokacin batul ta runtse idanuwanta, sai tayi tsammanin tayi bacci.
Lalla6awa tayi a hankali ta nufi jikin bango ta kashe switch din ɗakin, kafin ta dawo ta nufi gaban dressing mirror inda ta ɗaura wayarta ƙirar iphone
Shu'umin murmushine dauke akan fuskarta, wayar ta dauka ta shiga call logs ɗinta ta dannama wata number kira bugu uku kafin mai wayar ya ɗaga
Muryar babban mutunce ta dako mata sallama.
"Yalla6aina ina da labari mai daɗi agareka". 😳😳😳😳
Mu haɗu monday idan Allah yakaimu darai da lafiya, game bukatar cigaba da karanta prisoners 500 ne zaku tura ta bank acct dina, ga ta inda za'a tuntu6eni 08103884440
3196407426
Bature Hafsat Muhammad
First bank
Idan kin tura zaki bada hoton receipt amatsayin shaida🤗