Kurkukun Ƙaddara Book 2 Page 35

Kurkukun Ƙaddara Book 2 Page 35

The appearance of SALSABEEL😳🔥

On the other hand ƙasaitacciyar muryar mutumin ta furta mata"babu buƙatar ki sanar dani, na riga da nasan da zuwanki Nigeria"! Cikin nuna isa Ya furta mata hakan.

    Yayi matuƙar bata mamaki, muryarta da alamun ruɗi tace"tayaya akai kasan nazo nigeria? Bayan ni ban faɗa ma kowa ba"!


    "Saboda ina kallonki, duk wani motsinki a tafin hannuna yake Ummi"


  "Okey, idan har dagaske kana gani na, Yanzu faɗa min wasu kayane na sanya a jikina"! Ta faɗa yayin da take shafa kirjinta da hannu ɗaya.


  Ba zato ba tsammani taji yace"skirt launin yellow, tare da riga white colour sun yi tighting dinki, sun bayyana zazzafar surar jikinki mai jan hankalina"


  Har saida gabanta ya faɗi rass jin ya canka dai dai, tsabar ruɗu kiris Ya rage ta saki wayar hannunta, a firgice ta juya tana ƴan waige waige don taga ko yana acikin ɗakin ne! Muryarta adabarbace ta furta"am... ma tayaya akai kasan launin kayan dake a jikina"?

 Sautin wata shu'umar dariyar daya saki ce ta karaɗe kunnuwanta,

  "Meyasa kake yi min dariya? Ka amsa min tambayar dana maka"?

   "Kin manta dawa kike yin waya? Idan kin manta bari na tuna maki....." bata bari ya ambaci ƙarashen zancen ba, tayi hanzarin katse shi da cewa"ni ba wannan na tambayeka ba..." 

   Da kakkausar murya ya furta sunanta"Ummi!" amsa mashi tayi da na'am babe.

  "Duk duniya babu macen da ta isa ina magana ta katse ni sai ke! Meyasa"?

 Farfari tayi da ido tamkar tana agabanshi tace"saboda ka mutu akaina, babu yadda ka Iya dani, na zame maka ƙarfen ƙafa, mutu karaba takalmin kaza, sannan ni kadaice macan da zata Iya sarrafa ka cikin sauƙi nake rikatar dakai" ta ƙare maganar tana cizon lower lip dinta da tongue dinta, cikin jin shauƙin shi.


  Duk wannan wayar da take Yi, Batul tana sauraronta, baiwar Allah, jikinta ya gama sandarewa da sanyi, sai kakarwa takeyi, tuni azababbiyar mura ta rufeta, kasa jurewa tayi gani take kamar sanyin zai halakar da ita, hakan yasa ta yunkura ta miƙe cikin duhu ta nufi ƙofar fita daga ɗakin ta fuce ba tare da sanin Ummi ba.


     Sautin hucin numfashinshi har ta cikin kunnanta, shiru bai tanka mata ba, Hakan Yasa tace"Naji sautin numfashinka Ya cika min kunne na, ko jarabar taka ce ta motsa? gashi bana akusa balle in ɗebe maka kewa"


   Muryarshi ƙasa ƙasa ya furta"Ummi, muryarki kaɗai tayarmin da jarabata take Yi, abuƙace nake dake, Inason ganinki ayanzu ya za'ae"


   Shu'umin murmushi tasaki, muryarta da kwarkwasa tace"babu halin ganina, nayi maka nisa, kayi tunanin zan baka damar ganina cikin sauƙi? Bayan irin wahalar daka bani? Ka tafi ka barni da kewarka, ba ka damu dani ba, kasa ina kokwanton anya dagaske kana ƙaunata? Saboda kawai mun samu sa6ani shine ka nesanta kanka dani? Ka hana rayuwata sukuni....." bata samu damar ƙare maganar ba, ya katse mata hanzarinta"bazan iya jurewa ba, nayi kewar jikin ki, nasan ni mai laifine agare maki amma inaso ki sani kina araina.


   Ta6e baki tayi tana sauraron shi

"Ki bani dama, zan gyara kuskura na, adaran nan" dariyar shakiyanci tasaka mashi"fadamin me zaka yi min"


  " zan kiraki video call, i wanna show u something that will make u happy" 


    Murmushin gefen fuska tasaki"okey my baby, amma fa kada ka nuna min abunda zai hanani runtsawa adaren nan" ta ƙare maganar tare da juyawa ta nufi toilet ta bude kofa ta shige ciki.


  


*CHIEF OWAIS✊❤*
Babu alamun zai iya runtsawa a daren yau, duba da abubuwan da suka sha mashi kai, idan har bai shawo kan matsalar ba to kuwa hankalin shi bazai ta6a kwanciya ba, halin shi ne hakan.


Safa da marwa yake yi a room dinsa, Ya zura hannayensa biyu cikin aljihun short dinsa, babu riga a jikinshi hakan ya bayyana zazzafar surar ƙirjinshi, jefi jefi yakan dan wurga eye balls dinsa kan wall clock din dakin domin duba lokaci, akan kyawawan idanuwanshi ƙarfe 1:30 na dare ta buga, a hankali ya kau da idanuwan daga kan agogon.


  Alert ne Ya shigo wayarshi, a hanzarce Ya nufi wayar tashi dake ajiye saman bedside drawer, ya duba ta, ƙofar room dinsa ne ake buƙatar shigowa, Unclock button ya danna, nan take ƙofar ta soma zugewa, agaban dressing mirror Ya tsaya yana jiran ƙarasowar su.

  

  Big guy ne tare da Mutumin nan, nesa da bayanshi suka tsaya tare da Buga ƙafa suka sara mashi atare, cikin girmamawa Big guy ya soma yi mashi magana

 

  "Assalamu alaikum Sir Barka, yanzu muka samu damar ƙarasowa gidan, aimin afwa na 6ata lokaci"


   Koda big guy yai maganar, basu samu damar ganin fuskarshi ba, saboda Ya juya masu baya, ta cikin mirror yake dubansu.

 

  "Yalla6ai fatan na same ka lafiya" mutuminne ya furta maganar.


  Lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kafin calmly ya furta"barka da zuwa, ina fata Big guy ya fada maka komai, Dangane da halin da ɗan uwanka ke a ciki"


 Jinjina kanshi yai cikin girmamawa yace"eh yalla6ai, ya sanar dani komai, Inaso na fara ganin shi"


   "Okey, Big guy you can take him to the room, but before that...."  gently ya waiwayo baya batare daya kallesu ba.


 Ya ɗaura da cewa"Ina so na saurari komai da zaku tattauna"


  Amsa mashi yai da okey.


  "You Can Go" amsa mashi sukayi da toh, kafin suka juya suka nufi ƙofar fita dakin.


   Bayan fitarsu, hayewa yai saman shimfiɗeɗɗan gadonshi, yayin da yake fuskantar jigunannan ceilling din  room nashi.


   Slowly ya daura wayar hannunshi on his broad chest, yadan lumshe sexy eyes dinshi.


  Idan muka koma 6angaren big guy da mutumin, cikin takun sauri suka nufi elevator, bayan sun shiga tayi sama dasu zuwa second floor ta sauke su, fitowa sukayi daga ciki, a hanzarce suka nufi bedroom din Danish.


  Abakin ƙofar dakin suka dakata dayin tafiyar.


  "Ina buƙatar face mask" mutuminne Ya furta maganar.

 Kallon shi big guy yai"meyasa? Ko bakasan taga fuskarka ne"


  Jinjina kanshi yai alamar eh big guy yace"bazai yiwu ba, dalilin dayasa nace hakan, yarinyar bata da kwanciyar hankali daga ita har yaron, silar ganinka da zasuyi shi zaisa suji sauƙin radadin abunda ke damunsu, Ina fata ka fahimce ni"


 Gyaɗa kanshi yai"na fahimta ba damuwa mu shiga ciki"


 Dafa ƙofar room din dakin big guy yai da tafin hannun shi, a hankali ƙofar ta zuge kanta, shi yafara shiga kafin mutumin yabi bayanshi, tunkafin su ƙarasa shiga ya hango abunda ya basu mamaki da al'ajabi, har kallon juna sukayi kafin suka mayar da dubansu garesu, wato abunda yabasu mamaki ƙarfin halin Unaisah, Ta lullu6esu da bargo daga ita har Giant snake din, kana Iya hango ƙafarta da jelarsa.  "Ban ta6a ganin ƙauna irin wannan ba,   arayuwar mu ta zahiri, ƙarfin halin unaisah da jarumtakarta ba ƙaramin burgeni suke yi ba" big guy ne ya fada.

  Mutumin yace"Ni shaida ne akan ƙaunar dake a tsakaninsu, tamkar anta da jini ...." bai ƙare maganar ba, big guy yai mashi nuni da abun sauraron daya sanya a kunnanshi, da sauri Yaja baki yai shiru don ya fahimci abunda yake nufi wato chief yana sauraronsu ta hanyar earbuds din kunnan big guy.


Abakin gadon suka dakata suna ƙare masu kallo.

 Kiran sunanta big guy yai"Unaisah! Muna son yin magana dake" shiru babu alamun zata farka

 Ɗaga murya yai da karfi ya ambaci"Unaisah Angel, ki tashi zamuyi magana"

  Har cikin dodon kunnanta kiran ya kai mata, firgigit tafarka tana sambatun ambaton sunan Danish, saboda ta kwanta dashi aranta, jin shi ajikinta yasa taji hankalinta Ya kwanta, sai kuma ta fara tunanin wanene ke kiran sunanta, kafin brain dinta ta tariyo mata muryar mai magana ya kuma cewa"Ni ne Big guy, ki fito daga cikin bargon muyi magana" ya fada ne don ya lura tafarka duba da yadda bargon da suka lullu6a yake motsi.


 Ta rasa ya zatayi ta raba jikinta daga giant snake din, Ya shige mata sosai, sai faman jan numfashi take Yi da sauri da sauri.

  "Kinyi shiru Unaisa!" muryarta da kasalar bacci ta soma magana


 "Ƙoƙari nakeyi in fito, ya rurruƙeni ne"


 murmushin gefen fuska mutumin ya saki jin muryar daya daɗe yana kewarta.

 Kallon big Guy yai"bari na taimaka mata" clapping hands dinsa yai sau uku, wani abun mamaki macijin ya farka, Ya warware jikinshi daga nannaɗetan da yai, ya soma ƙoƙarin yakice bargon don ya fito, hannu mutumin yakai Ya ruƙo ƙarshen bargon ya yaye shi gaba daya ya jefar dashi gefe ɗaya.


  Biji biji Unaisah take dubansu, idanuwanta sun kumbura sunyi mata nauyi bata iya ganin su dakyau, a kasalance ta miƙe zaune tana faman sauke ajiyar zuciya, baiwar Allah gyaran gashin da take ta kaffa kaffa dashi don kada ya tarwatse tuni yafara fita hayyacinshi.


  Abun da ya ɗaure ma Big guy kai, ganin yadda macijin duk yabi ya ruɗe, ƙoƙarin saukowa yake Yi daga saman gado, kuma ga dukkan alamu wurin mutumin yake son zuwa, Allah sarki ɗan uwa yaga ɗan uwanshi.


  Hawa saman gadon mutumin yayi, agaban giant snake din Ya tsaya, cikin rauni na murya furta"ko baka furta min ba, nasan halin da kake aciki Danish! Saboda ina jin raɗaɗin acikin zuciyata, amma kada ka damu, Allah yana atare dakai muma kuma muna atare dakai, wallahi duk runtsi duk wuya ba za su ta6a cin galaba akanka ba, tunda har su ka yi kuskuren haɗaka da ƙaddararka wadda tayi silar barinka *GIDAN KURKUKUN ƘADDARA!!* Tun da ya fara magana Unaisa ta dabarbar ce, tarasa gane a ina ta ta6a jin muryarnan, sai da yazo ƙarshen maganarshi ya amabaci sunan kurkukun ƙaddara, tamkar ya buga mata guduma a kirjinta, la66anta na rawa ta soma ambaton sunanshi"SAL...  SABEEL! SALSABEEL! MAFARKI NAKE YI KO GASKE NE KUNNUWANA SUKE JIYO MUN MURYARKA" amatuƙar ruɗe sai faman ƙoƙarin murza idanuwanta take da yatsun hannunta duk don ta samu damar ganinshi.


 Muryarshi ce ta dakatar da ita daga ambaton sunanshi da take Yi

  "Angel! Nine ba mafarki kike yi ba, SALSABEEL ƊINKU NE NA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA" daƙyar ta iya ware idanuwanta akan fuskarshi, kwamtsa duk ta kakkama idanuwanta saboda kukan da tayi idon ciwo yake mata, sosai ta zazzaresu tana dubanshi tamkar wadda taga abun tsoro, ruɗani ya hana ta yi magana, lamarin yayi mugun ɗaure mata kai, ko amafarki bata ta6a tsammanin hakan zata Iya faruwa ba, kamar yadda take kallonshi haka shima yake kallonta, fuskarshi dauke da murmushi, yayin da idanuwanshi suka cicciko tab da ƙwalla, macijin kuwa tuni Ya ɗaura kanshi saman laps din salsabeel.


 Miƙa mata hannu yai alamar tazo gare shi, ta zabura ta nufeshi, haɗi da faɗawa saman kirjinshi ta ƙanƙameshi, lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya.


  Big guy dake atsaye yana kallonsu zuciyarshi tuni ta karaya, duk irin dauriyar shi baisan sa'adda ƙwalla ta cika idonshi ba.


  Muryarshi arauna ce ya furta"Sir, are you listening?"

 

 On the other hand, chief owais dake a kwance saman tattausar mattress na gadon shi, Ya amsa mashi da"Yes, I'm listening."


 Ajiyar zuciya big guy ya sauke, ya fahimci sautin kukan Unaisah ba ƙaramin ta6a zuciyar chief yai ba, tun daga kan yanayin muryarshi.


  Bubbuga bayanta Salsabeel yai da hannun ɗaya cikin sigar lallashi, yayin da ɗayan hannun nashi yake asaman kan giant snake din"


  Tamkar yana ƙara tunzurata, kuka take yi na fitar hayyaci.


    Big guy dake amanne da earbuds, muryar Chief ce  ta janyo hankalinshi ga sauraronshi"


   "Tell her to stop crying, I don't want to hear it.(Ka faɗa mata ta daina kuka, bana son ji") amsa mashi yai da toh, kafin ya ɗaga murya yace da salsabeel"ka lallashi ƴar uwarka, tadaina yin Kuka, umarni ne daga chief"

  Jinjina mashi kai yai, da karyayyar murya ya ambaci sunanta"Unaisa, Ki daina kuka, danish baya jin dadi, ya fadamin idan baki daina ba shima zai fara kukan saboda kina ƙara tayar mashi da hankali" jin wannan maganar yasa tayi saurin haɗiye kukanta, a hankali ta dago da kanta tana duban fuskar salsabeel, tsananin tausayinta ne Ya kamashi, kumatunta sunyi jawur, pink lips dinta sunyi suntum dasu, tasha kuka baiwar Allah.


   Cikin shessheƙar kuka take fadin"Sal... Sal... Sabeel, ka fadamin ya akai ka tsira daga gidan kurkukun ƙaddara? Ina ƴan uwana suke? Ina deeja take da mubeen? Suma sun rayu ko sun mutu? Inaso nasani, gaba ɗaya na rikice"


 Shafa gefen fuskarta yai da hannun shi, Cikin sanyi murya yace"Unaisah, ki kwantar da hankalinki, yanzu bana acikin natsuwar da zan Iya yi maki bayanin komai, nayi maki alƙawarin zan fayyace maki komai idan Danish ya dawo mutun, amma fa sai kin daina yin kuka, kin kuma natsu" jinjina mashi kai tayi alamar zata daina.


   "Danish yana yi min magana, yanzu haka"  ba ta yi mamakin jin abunda yace ba, tunawa da cewa shima giant ne, abune mai yiwuwa suyi magana ta sirri acikin zuciyoyinsu harma su Iya jin juna, big guy ne kadai al'ajabi ya cika shi, tun yana daga tsaye har yakai ga samun wuri saman sofa din dakin ya zauna yana dubansu

  "Ina son jin me yake fada maka" acewar big guy

  A lokacin Unaisah ta mayar da kanta saman kirjinshi, ya tallabeta da hannu ɗaya, zazza6i jikinta sai ƙara nunkuwa yake yi.

  Calmly Salsabeel Ya soma faɗa masu tattaunawar da suke Yi da danish.


  "Ya faɗamin bayason unaisah tana yin kuka, Zuciyarshi tana karaya, sannan yana roƙona akan in taimaka mashi ya rikiɗa ya koma mutum baya son ganinshi a suffar maciji, yana jin ƙyanƙyamin kanshi, yana acikin mawuyacin hali na ƙunci da raɗaɗi, idan har ya ɗauki tsawon lokaci bai dawo mutum ba Giant's heart dinshi zata motsa ne, idan kuwa ta motsa gaba ɗayanmu zai Iya cutar damu, saboda awannan matakin babu  wanda zai Iya sarrafa shi har ita unaisah" hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yai ba jin abunda salsabeel yake fadi, ita azatonta giant's heart dinshi ne ya motsa shiyasa har ya iya rikiɗa ashe ba zuciyar bace ta motsa.


  Ba ita ba hatta big guy ya ɗan girgiza da jin kalaman salsabeel, har saida ya daura eye balls dinshi akan macijin dake a nannaɗe saman gadon har yanzu bai ɗago da kanshi daya daura saman laps din salsabeel.


   Cigaba da yin magana yayi"danish yana acikin damuwa, ina jin shessheƙar kukanshi, roƙona yake yi akan mu taimaka mashi ya canza halittarshi ya gaza rikiɗa baisan ya zaiyi ba, bayason ƴan uwanshi su guje shi, idan kowa ya ƙyamace kamar yadda ya ƙyamaci kanshi hakan zai yi silar motsawar giant's heart dinshi kuma idan ta motsa zai nesanta kanshi da kowa saboda baya son ya cutar da mu, zai koma inda yasan baza a ƙyamace shi ba, yana nufin tushen shi gidan kurkukun ƙaddara...." tunkan salsabeel Ya ƙare maganar, Unaisah ta tari numfashinshi "A'a danish, ka daina fadin zamu ƙyamace ka, Ni yanzu ma nafara ƙaunarka saboda ina tausayin rayuwarka nasan cewa bayin kanka bane, mugayan mutanan can ne suka assasa faruwar hakan duk don ka koma garesu, sunyi maka hakanne don mutane su guje ka kai kuma kaji ka ƙyamaci kanka saboda sunsan ta wannan hanyarne kadai zakaje gare su, Ni kuma wallahi bazan ta6a bari hakan ta faru ba, Yanzu nafara sonka, Danish ba maciji ba, kowace irin halitta zaka koma a duniyar nan ina atare dakai, har abada har ƙarshen numfashina, kai koda ace zaka dinga cutar danine bazan rabu dakai ba, sai inda ƙarfina ya ƙare, akanka babu gudu babu ja da baya wallahi bazan barka ba......." kukane yaci ƙarfinta har ta kasa ƙarasa maganar.


  Macijin yana sauraron duk abunda take cewa, ya ɗago da kanshi daga saman laps din salsabeel, mitsi mitsin idanuwanshi na fuskantarta.


  Big guy bazai Iya jurar tausayinsu da yake ji ba, Jikinshi yai sanyi laƙwas kamar wanda aka zare ma laka.


  Duk abunda ke faru Chief Owais Yana sauraronsu, yayin da yake a kwance cikin bedroom dinshi saman gadonshi, Muryar unaisah ta cika mashi kunnuwanshi tamkar agabanshi take Yin kukan, A hankali ya dauki wayarsa daya daura saman broad chest dinshi ya dawo da ita saitin kunnanshi, don yaji dadin sauraronta dakyau.


   Shafa sumar kanta Salsabeel yai da hannunshi"Ki daina kuka yace min in fada maki bayaso" da sauri ta hadiye kukanta tana fadin"toh na daina, bazan ƙara ba my Man," ta faɗa tana kallon macijin har girgiza mata kai yake yi, batasa sa'adda tasaki murmushi ba, ta fahimci lallashinta yake yi.


  "Abun da Unaisah ta faɗi gaskiya ne, tsammaninmu yazo ɗaya, azzaluman kurkukun ƙaddara ne suke sarrafashi ta ƙarfi da yaji bada son ranshi ba, kuma sunayi mashi hakanne don mutane su ƙyamace shi kowa ya gujeshi, shi kuma zaiji ya tsani kanshi saboda ƙyarar da mutane suke yi mashi, daga haka zai fara tunanin komawa prison wannan shine abunda suke ƙoƙarin yi" 


  Tun da yafara magana big guy yake jinjina kanshi alamar gamsuwa da jawabin shi, Muryar chief ce ta sa shi dakatawa yana sauraronshi, babu mai iya jin voice dinshi sai shi da yasanya abun sauraron akunne.


 Cikin harshen turance yace "Ka faɗa mashi, muna atare dashi, bazamu ta6a rabuwa dashi ba har iya ƙarshen numfashinmu, babu wanda zai ƙyamace shi, duk runtsi zamu kasance atare dashi don mu bashi ƙwarin gwiwa kuma zamu tallafa masa don ganin mun raba shi da miyagun dake atare dashi, in sha Allah komai yazo ƙarshe ya kwantar da hankalinshi"


  Jinjina kai big guy yai haƙiƙa yaji daɗin kalaman Chief owais, magana yasoma yi masu"chief yace in isar mashi da sakonshi zuwa ga Danish ....." mayar da hankalin sukayi akanshi suna sauraronshi, a tsanake ya faɗa masu abunda chief yace.


  Wani irin farin cikine ya lullu6e Unaisah, har cikin ranta taji daɗin kalaman shi duk da batasan wanene shi ba, ba ta ta6a ganin fuskarshi ba, ko ɗazu da taji an dauketa lokacin data lullu6e Danish da bazar rigarta batasan wanene ya dauketa ba saboda bata acikin hayyacinta, idanuwanta sun makance.


   "Wanene chief? Yaushe ya faɗa maka sakon"? Ta jefa ma Big guy tambayar yayin da take dubanshi.


  Nuna mata earbuds din kunnanshi yai da yatsan hannun shi, nan take ta gane abun jin magana ne a ear dinshi tanan suke yin communicating da shi.


  Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke muryarta adisashe ta furta"idan na samu natsuwa zaka kaini wurinshi muyi mashi godiya" Big guy yace"a'a shi ba'ayi mashi godiya, sai dai idan kinason ganinshi zan nema maki izni daga gare shi, amsa mashi tayi da toh inaso"


   Kallon salsabeel Yai"menene mafita? Muna son musan wani hali yake aciki" kafin ya bashi amsa unaisa tayi saurin cewa"nayi magana da boss man, na fada mashi inda na ajiye wasiƙar adreshin gidanku daka bani, inda zamu samu ruwan zam zam din"


 Fuskarshi da matsanancin damuwa yace"ai babu zamzam din nan! Tun lokacin da kuka faɗa hannun sojin america suka damƙa case dinku hannun hukumar Isod, nasan da zamanku, munyi ƙoƙarin samu ruwan zam zam saboda gudun kada giant's heart dinsa ta motsa, sai dai kash lokacin da muka je gidanmu na kaduna tare da jami'an isod bamu samu komai ba, Gidan ma an canza mashi kamanni, magada ne suka koma da zama cikinshi, su kansu da mukaje basu san Wanene ni ba, munyi ƙoƙarin yi masu bayani amma sai suka fada mana cewa babu komai na habibullah dayai saura agidan...." aruɗe Unaisah tace"ya zamuyi yanzu"? Ta faɗa tana zazzare idanuwanta.

  Salsabeel yace"akwai hanyoyi da dama, da zamu Iya samun ruwan zam zam sai dai bamusan wasu irin addu'o'ine ko ayoyin alƙur'ani ake amfani dasu ba wurin tofe ruwan ba" ya faɗa yana dubanta.


  "da za'a samu babban malamin addini kamar mahaifina habibullah ina da tabbacin zai iya taimaka mashi"


  Shiru suka ɗanyi suna kallon kallo atsakanin Salsabeel da Unaisah, ga macijin yayi kwance saman jikinshi daya nannaɗe.


  Chief Owais dake a kwance saman bed matress dinsa Yana sauraronsu, ƙarar shigowar message ce ta janyo hankalinshi ga buɗe eyes dinshi, phone dinsa Ya ɗago da ita yana duban screen din.


  Text message ne aka turo mashi, yayi mamakin ganin saƙon Uncle dinsa, A irin wannan lokacin ƙarfe biyu da rabi na dare, hakan na nufin bai runtsa ba.


  Karanta text message din Ya soma yi acikin zuciyarshi.


   _"My son, I can't sleep because of that child, I don't know why I'm so worried about him. Please help me. I want to see him before I go back to Canada next week. na jaraba kiran layin Sheikh imam munyi magana dashi ashe baya kasar ya tafi sudan, na nemi alfarmar inason ganinshi da gaggawa, yace min in sha Allah zai dawo ƙasar a gobe, saƙo daga Prime minister Hateem Obinna_

  

Bayan kammala karanta message din, Owais Yai mashi reply kamar haka

  

   _"Nima ban runtsa ba kawuna, saboda yaron, ƙoƙarin da muke Yi kenan don ganin mun taimaka mashi ya canza halittarshi zuwa ta suffar mutane, amma inaso ka kwantar da hankalinka ka yi bacci, in sha Allah zaka haɗu dashi kafin komawarka kanada, har ma kuci abinci atare"_


   Tura mashi sakon yai, within minutes saiga wani sakon daga prime minister


_thank u, sai mun hadu gobe da wuri zan shigo gidan naka idan sheikh iman ya ƙaraso_


   Lumshe ido owais yai, A hankali ya furta sunan big guy, on the other hand big guy ya amsa mashi da na'am yalla6ai"

   

   "Sako ya shigo min daga Uncle Hateem, Zuwa gobe da safe Sheikh Imam zaizo Nigeria, yayi tafiya ne zuwa sudan, ka yi ma brother din yaron nan magana ya tambaye shi idan yana jin yunwa ya fadi me zai iya ci akawo mashi" amsa mashi yai da toh.

  Ya mayar da dubanshi ga su salsabeel"tun da yana jin maganarka ka tambayar mana shi me zai Iya ci akawo mashi, sannan pls kace mashi ya kwantar da hankalinshi zuwa gobe insha Allah sheik imam zai shigo Nigeria, shahararran malamin addinine muna da tabbacin zai Iya taimaka mashi"


 Gyaɗa kai salsabeel  yai"ay yana sauraronka, Yanzu haka magana yake yi min.


 "Meyasa kuka harbe shi? Duk da harsashin bai fasa jikinshi ba yayi mashi illah saboda babu kakin giant a jikinshi"


  Hankalin Unaisah dana Big guy ya tashi matuƙar, muryarta na rawa ta furta"meya faru dashi? Yaji ciwo ajikin shi"

  "Bazan Iya sani ba, sai ya dawo suffarshi ta mutane tukunna zamu ga illar da yayi mashi, sannan ya fadamin yana son kayan marmari su kadai yake sha'awar sha"


Damuwace ƙarara akan fuskar Angel"meyasa bazai Iya cin abinci ba"? Ta fada tana duban salsabeel.


  "A halin yanzu Danish dinki, ba mutun bane Giant snake nake, bazai Iya cin kalar abincin mu ba, har sai ya dawo cikakken mutun.


 Kwa6e fuska tayi tana duban kan macijin, har yanzu bai dagoba tunda ya kwantar da kanshi saman jikinshi daya nannaɗe.


     Miƙewa tsaye big guy yai"ka zauna atare dasu, zan je na kawo mashi kayan marmarin" amsa mashi salsabeel yayi da toh.


 Bayan fitar big guy, ta ƙura ma salsabeel ido, har yanzu mamakin ganinshi take yi, abubuwa dayawa sun cunkushe mata brain dinta, tana son jin ya akai ya tsira daga kurkukun ƙaddara? Shin ya sauran ƴan uwansu suka ƙare sun mutu ko sun rayu? Tayaya Akai Ya haɗu da jami'an da  suke kula dasu? Ko dai dama shima jami'insu ne!? ta ɗaura mashi alamar tambaya, tadai haƙura ne har zuwa time din da danish zai rikiɗa ya dawo mutun donjin amsar tambayoyinta, kamar yadda take kallon Salsabeel haka shima yake kallonta, yayi kewarsu sosai, kuma yaji dadin ganinsu, da ransu da lafiyarsu, bakomai yake tunawa ba face ranar daya fara haduwa da ita har yakaita dakin da suka tattauna, da kuma ranar da ya ceci rayuwarta lokacin da matsafa sukayi mata wanka da jini, ranar da ta azabtu ta galabaita, Allah kenan mai yadda yaso mai jujjuya al'amurra, yanzu tamkar ba'ayi ba, tayi haske abunta gwanin kyau har girma ta ƙara mashi akan yadda suka yi rabuwar ƙarshe a kurkuku.


Murmushi yasakar mata, itama ta mayar mashi da martanin murmushin,  ya fahimci aƙagare take da son jin labarin ƴan uwanta daga gare shi.

    

*PRISONERS💔✍️*


Tun bayan fitowar Batul daga ɗakin Ummin america, a tsakar dare ta nufi down stair, baiwar Allah tana tafiya jikinta na kakarwa, hatta haƙoranta kerma sukeyi suna hadewa jikin juna, tsoro take ji ita kaɗai kamar aljana, sai faman firgita take yi gani take yi kamar macijin zai kawo mata hari.


  Daƙyar take iya taka ƙafarta saman floor din falo, ga wani azababban tari daya farmata.


     Sam ba ta ji takun tafiyar mutum ba, saboda hankalinta ba akwance yake ba, sai ƴan waige waige take yi tana faman hadiyar yawu.


Yayi mamakin ganin ɗaya daga cikin yaran tana yawo a tsakar dare, babu mayafi a jikinta, ƙura mata ido yai a ƙoƙarinshi naya gano wacece acikinsu,  ya rasa gane batul ce ko Unaisah, saboda launin gashinsu kala ɗaya ne ga kuma nannaɗewar sumar kan nasu daya kasance iri ɗaya, zuciyarshi ce ta raya mashi cewa Unaisah tana adaki fa ya barota tare da salsabeel wannan ba ita bace sai dai ko ƴar uwarta ce Batul.


 Da ƙarfi ya ambaci sunanta"Batul" rass taji gabanta Ya faɗi, a firgice ta waiwayo don ganin wanene, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskar big guy dake sanye cikin face mask,l.


   Tsabar tsoro da ruɗu yasa ta zabura zata watsa da gudu, sai dai kafin tayi hakan yai saurin haura ƙafa ya damƙo damtsen hannunta ya janyota zuwa jikin shi, ƙanƙame shi tayi  atsorace ga tari da take yi.


 Lamarin ya ɗaure mashi kai, ɗago da kanta yai daga saman ƙirjinshi ya furta"ke! Daga ina kike? Ya akai kika fito daga ɗaki"?

Daƙyar ta Iya buɗe baki tace"sanyi nake ji babu bargo shine na fito zani ɗaki in ɗauko"

  "Awani ɗaki kike"?

"Ɗakin aunty ummi, boss man ne yace muje can mu kwana, saboda munajin tsoron kwana ana mu dakin"


"Meyasa baki tambayeta ta baki bargo ba"?

 A tsoroce take yi mashi magana"tayi bacci ne, kafin ta kwanta ma saida nace ta taimaka ma parveen da kaya ta sanya saboda tayi ma nata fitsari sunjiƙe sharkaf amma taƙi bata sai dai ni na cire nawa muka yi musanya ta bani nata, kuma ɗakinta sanyi sosai"

Tunda tafara magana Big guy yake jinjina kanshi, ga dukkan alamu ya fusata matuƙa, bashi ba hatta chief owais dake acan room dinsa yana sauraron maganganunsu.


   Ruƙo hannun Batul yayi acikin nashi ya juya da ita suka nufi ɗakin.


  A lokacin Ummin america tana ƙoƙarin fitowa daga cikin toilet, ta gama sheƙe ayarta da gardin daya kirata awaya, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, zura ƙafarta keda wuya hasken ɗakinta Ya kama, a firgice takai idanuwanta kan masu shigowa ciki, tunda tayi arba da big guy tare da batul gabanta yai mugun faɗuwa.


  Wani irin kallon tuhuma yake jefa mata, ranshi amatuƙar 6ace ya soma magana.


  "Ke baki da hankaline? Kin ajiye yara aɗaki kin kure masu sanyin A.c ? Idan ƴa'ƴankine na cikinki zaki Iya yi masu haka"?


Muryarta adabarbarce tace"am..ba haka bane ni ai bansan basu iya jure sanyin A.c din ba, na saba kwana....." bata ƙare maganar ba, Ya daka mata tsawar data firgitar da ita, sakin hannun batul yai ya matsa kusa da ita, abunda wani ɗa namiji bai ta6a gigin yi mata ba, da yatsan hannunshi ya nuna ta"ki shiga taitayinki, This is the last time I'll warn you. Don't be reckless in your work. We don't accept mistakes, koda gigin wasa kada ki kuskura ki ƙara maimaita laifin nan" yana huci ya faɗa

  "Yarinya harta fara mura tana tari! Ke ko ajikinki ai nayi tunanin zanzo na sameki kina bacci ashe idonki biyu hakan na nufin da gangan kika kure sanyin A.c din dakinki, Ke bari kiji bana so gobe da safe inji yarinyar nan tana yin mura, ki san yadda zakiyi ta dawo daidai, bama itaba hatta sauran ƴan uwanta kada ki bari ɗaya daga cikinsu ya tashi da mura, idan ba haka ba zaki fuskanci hukunci mai tsanani daga hannun chief.. " hankalin ummin america ba ƙaramin tashi yai ba, duk tabi ta susuce musamman daya ambaci sunan owais,  muryarta na rawa take fadin"na kar6i laifina bazan ƙaraba, kuma aini bansan sanyin zaiyi masu illa ba..." bai bari ta ƙare maganar ba ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu"bana sonji, kawai kiyi abunda ya dace don ki ceci kanki, nabarki lafiya" afusace ya juya zai bar dakin har ya kusa fita karaf idanuwanshi suka sauka akan parveen dake kwance saman carpet tana yin bacci, Arude ummi ta furta"yanzu zan maida ta saman gado, bansan ya akai ta faɗo ƙasa ba" wani ɗan iskan kallo big guy ya watsa mata.


 Kafin ya maida dubanshi ga batul"ke ina yar uwarku take? ya akai naga ku huɗune? Where's hannah"!


 Sai daya ambaci hakan batul ta tuna da babu hanna acikinsu, waige waige ta soma yi jikinta na rawa tace"bansan a ina take ba, tare da ita muka nufo dakin aunty ummi, ni na ruƙo hannunsu ita da Parveen bansan ta kufce min ba, dama aruɗe take"


  Gyaɗa kanshi yai"okey, wuce kije ki kwanta, zanje na nemota" ya faɗa tare da juyawa ya kalli ummi dake ta rawar jiki"ina ƙara jaddada maki kada ki bari yaran nan su wayi gari babu lafiya, idan kunne yaji jiki ya tsira" yana fadin hakan ya haura ƙafa yabar ɗakin.

 Fitar shi keda wuya, Ummi ta ɗaure fuskarta tamau babu annuri, ranta ya 6aci matuƙa, hankalin batul ba ƙaramin tashi yai ba ganin tana tunkarota, girgiza kai tadinga yi tana nufar bango harta kure mashi, 

 "Dan Allah kada ki ta6ani, bani da lafiya..."daƙyar ta furta maganar,

  "Ni ki ka kai ƙarana a wurinsu? Yaushe kika fita daga dakin munafukar banza, harni zakija ma bala'i ina zaman zaman lafiyana? Kinsan wacece ni? Don ubanki!


 Girgiza kai batul tayi tuni hawaye sun wankan fuskarta"aunty ummi kiyi hakuri bazan ƙaraba, dan Allah kada ki ta6ani"

 Tsawa ta daka mata"kashe ki zanyi, kinyi kuskura batul da kika gaya mashi abunda ya faru tsakanina daku, wallahi sai kinyi danasanin sanina da kikayi, don kuwa daga rana irinta yau bazaki ƙara dariya ba zan ƙuntata maki har sai kinji kin tsani kanki" 


  Fashewa batul tayi da kuka mai tsuma zuciya, saboda rashin imani ummi ta sanya hannu ta shaƙi wuyanta tamkar zata kashe ta, 

  "Jibarki dallah, jahila dake, bakisan komai ba sai cin abinci da bacci, ni ban ta6a ganin daƙiƙiya ba irinki"


    "Batul ! Batul! Meyasa kike kuka"? Jin muryar Parveen yasa ummi yin saurin sakin wuyan batul, jiki ba ƙwari ta sulale ƙasa tana cigaba da yin kuka  


  "Kiyi min shiru idan kika bari wani yaji wallahi saina naƙasa ki wawuya" da sauri batul ta haɗiye kukanta, baiwar Allah hada sanya hannu ta share hawayen fuskarta.

   Shu'umin murmushi tasaki kafin ta juya tana kallon parveen data farka tana faman mutsustsuke idanuwanta

  "Ke tashi ki koma saman gado ki kwanta" muryar ummi ce ta fargar da Parveen ta ware idanuwanta sosai akan fuskokinsu

 Muryarta da kasalar bacci tace"batul make faruwa? Meyasa kika zauna a ƙasa"? Tai maganar tana kokarin miƙewa da niyar taje wurin Batul, ummi ta dakatar da ita"cewa nayi kije ki kwanta saman gado, babu abunda ya sameta, kaya zan bata ta sanya ajikinta" jiki asanyaye parveen ta nufi gadon donta kwanta sai dai hankalinta bai kwanta ba da yanayin data riski batul

 "Parveen ki kwanta kiyi bacci, lafiyata ƙalau, yanzu aunty ummi zata bani kaya in canza na jikina sai inzo mu kwanta a gadon" ajiyar zuciya parveen ta sauke jin batul tayi mata magana, hayewa tayi saman gadon ta kwanta batare data rufe idanuwantaba.

   Ta6e baki ummi tayi tare da mayar da dubanta kan Batul, badan taso ba tace"shashasha, Ki jirani in dauko miki kayan" cikin sanyin murya batul tace"toh"

  Wuce wa tayi cikin ɗakin can inda katafaren closet dinta yake, ta bude ta dauko jibgegiyar sweater tare da dogon wando, ta haɗo da duvet, ta nannaɗosu ta dawo inda batul take a zaune ta wurga mata su saman jikinta

  "Salon kuma kiyi min ƙazanta, ni bana sharing kaya da wani don yazamarnin dolene" ta faɗa tare da juyawa ta nufi gaban mirror inda ta daura A.c remote ta kashe ta gaba daya, ta kunna masu room heater, duk don saboda gudun kada gobe aji basu lafiya, shiyasa tayi hakan.

 Miƙewa batul tayi hannunta ruke da sweater din, ta zame hannun doguwar rigar jikinta, da dabara ta zura sweater din, tayi mata girma, haka wandonma yayi mata faɗi, ahaka ta sanya su, kafin ta cire rigar jikinta, anan ƙasa tabarta, ta nufi saman gadon ta haye gefen parveen ta kwanta, ta lullu6e masu bargon su dukansu, kafin ta rungume parveen a jikinta, duk don ta samu sauƙin raɗaɗin da take ji, ta tsorata da ummi kalaman da tayi mata sun tsaya mata arai, fargabanta kada ta kashe ta, tuni idanuwanta sun cicciko da ƙwalla

 Cikin muryar raɗa parveen take yi mata magaba"batul tayi maki wani abu ko? Ni naji ajikina" daƙyar ta iya furta"kiyi shiru parveen kada tajimu, ni batayi min komai ba, bana jin daɗin jikinane" 

    Sautin kuskus din da suke yi ne yaja hankalin ummi ga kallon bargon da suka lullu6a dashi atsawa tace"kada in kuskura in ƙarajin maganarki! Ko tari bana sonji" tsit sukayi shiru suna faman ƙanƙame junansu ......... 

  Mu haɗu gobe idan Allah yakaimu darai da lafiya, game bukatar cigaba da karanta prisoners 500 ne zaku zaku tura ta bank acct dina, ga ta inda za'a tuntu6eni 08103884440
3196407426


Bature Hafsat Muhammad

First bank 

Idan kin tura zaki bada hoton receipt amatsayin shaida🤗

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post