Kurkukun Ƙaddara Book 2Page 39

Kurkukun Ƙaddara Book 2Page 39

Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️

Adai dai lokacin Su parveen suna a zazzaune tsakiyar gadonsu Batul, sun  kewaye juna, sai faman zazzare idanuwansu suke yi don har yanzu basu daina jin fargabar macijin nan ba.


Motsin buɗe ƙofa ne Yaja hankalinsu ga kallonta, Atare suka shigo hannun su ruƙe cikin na juna, wani irin farin ciki ne ya lullu6e su, da gudun gaske Jemimah da Azeeza suka diro daga saman gadon suka nufi unaisah, tunkafin su ƙaraso ta ware masu hannayenta fuskarta dauke da yalwataccen murmushi, zubewa tayi saman gwiwowinta yadda tsawonta zaiyi dai dai da nasu, gaba ɗayansu ta haɗasu ta rungume a ƙirjinta, tare da zagaya hannayenta saman bayansu, jemimah tuni ta fashe mata da kuka hada bubbuga bayan Unaisah alamar ranta ya 6aci.


 Batul dake a tsaye tana kallonsu sam bata ji takun tafiyar Parveen ba, Sai dai taji muryarta"Batul tun ɗazu muna ta jiran ki shiru baki zo ba, Ina fata babu wani abu daya same ki"?


  Kallonta Batul tayi da ido tayi mata alamar tayi shiru bata son Unaisah taji komai daya faru, jinjina kai parveen tayi don ta fahimci me take nufi.


   "A ina kika sami kayan jikin ki masu kyau"? Ta fada tana duban Kayan sanyin jikin batul"

Murmushi batool tasaki kafin tace"Aunty ummi ce ta Bani su"

Parveen tace"ko a ina ta same su, ban ta6a ganin kayan da suka yi maki kyau ba kalar waɗannan" kafin batool tayi magana muryar Jemimah ta katse mata hanzarinta, A lokacin sun ɗago da kansu daga rungumar da Unaisah tayi masu, fuskokinsu sharkaf da hawaye kamar waɗanda suka yi shekara basu ganta ba.


 "Meyasa jiya kika tafi kika barmu? Inata kiran sunanki baki amsa ba, tsoron wannan abun ya kamamu"


 Shafa fuskarta Unaisah tayi"Am sorry nasan ban kyauta ba, amma kuyi haƙuri, bawani wuri na tafi ba, Ina atare da ɗan uwanmu Danish bashi da lafiya......"


Tunkan ta ƙare maganar, hankalinsu yai mugun tashi jin cewa danish dinsu baida lafiya, damuwace ƙarara akan fuskokinsu


 "Unaisah meke damun shi? Meyasa jiya ba kizo kin kaimu mun ganshi ba"? Acewar parveen 

 Batul tace"ni da ma saida naji araina ɗan uwanmu baida lafiya, Allah sarki danish din mu, Yanzu yana a ina? Ina son ganin shi" ta fada idonta akan unaisa dake ƙoƙarin miƙewa tsaye tana dubansu.


  Ruƙo hannunta Azeeza tayi acikin nata"dan Allah ki kaimu wurin shi, muna son ganin shi" idanuwanta sun ciko tab da ƙwalla tayi maganar.


Numfasawa Unaisah tayi kafin ta soma yin magana"na yanke shawara ƙwara na faɗa maku halin da danish yake aciki, saboda bana son ku guje shi ko ku dinga jin tsoron zuwa wurinshi......." shiru ta ɗanyi na wani lokaci duk sun ƙura mata ido cike da zumuɗin son jin ƙarashen zancen.


  "Amma kafin nan inason ganin sauran ƴan uwanmu, naga babu Hannah! Ina taje ne"? Atare suka hada baki wurin bata amsar cewa suma basu sani ba, tun daren jiya basu ganta ba.


   Aruɗe Unaisah take dubansu, Kafin ta furta magana, sallamar Big Guy taja hankalinsu ga duban ƙofar, shigowa cikin ɗakin yai hannun shi ruƙe dana Hannah, daga bayansu Ƴan uwansu ne maza tun daga kan Sajeed, Haris, Javed and Naufal, ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, Hannah sai faman zare ido take yi kamar wadda aka faɗa ma saƙon mutuwarta, sakin hannunta big guy yai jiki na rawa ta nufi Unaisah ta rungumeta, sunyi farin cikin ganin ƴan uwansu, Sajeed ya nufi azeeza fuskarshi dauke da murmushi yai hugging dinta, Naufal yajanyo parveen ya rungumeta Yana bubbuga bayanta da hannu ɗaya,

  Batool da Haris suka rungume junansu, Ran jemimah ya 6aci ganin babu wanda ya rungumeta, harta fara tatta6e la66anta za ta yi masu kuka, javed yai saurin ɗaukarta saman jikin shi, Fashewa tayi da dariya saboda an dauketa.

  Big guy dake a tsaye yana kallonsu ya goya hannayensa saman broad chest dinsa, Yaran sun yi matuƙar burgeshi.


  Tsawon mintuna suna a manne da juna, kafin daga bisani kowan nan su ya rabu da jikin ɗan uwanshi, gyaran muryar da Big guy yai masu ne yasa suka mayar da hankalinsu gare shi a tsanake Ya soma yin magana.


  "Inaso ku natsu ku saurareni, dalilin dayasa na tara ku a ɗakin nan, saboda na fahimci haryanzu baku daina jin fargaban abunda ya faru jiya ba, Ga ƴar uwarku nan Unaisah zatayi maku bayanin komai yadda zaku fahimta, sannan please bama buƙatar ganin gifcin kowan nan ku a falo! Ku tsaya a ɗaki, mai buƙatar shiga toilet ya shiga, wanda zai yi bacci ga gado nan ya kwanta,........" kafin Ya ƙare maganar Parveen tayi ƙasa ƙasa da murya tana fadin"breakfast din mu fa? ni ina jin yunwa, Jiya da dare bamu ƙarasa cinye abincinmu ba" murmushi big guy ya saki ta cikin face mask dinshi

 Da zolaya yace"ki kwantar da hankalinki foodie, Indai abincine har sai kin gaji da shi, kamar kina a gidan manomi ne, Yanzu zansa a kawo maku lafiyayyan breakfast" ya faɗa tare da nufar kofar fita yana fadin"Unaisah Ki kula da su" amsa mashi tayi da toh, kamar jira su ke yi ya fita, Har suna haɗa baki wurin tambayarta meke faruwa da Danish.


  "Zanyi maku bayani, amma kafin nan ku jira waɗanda basu yi salla ba su yi tukunna, batool tace min ba ta yi sallah ba"

Badan sunso ba suka amince mata


 "Kunyi sallah"? Ta jefa masu tambayar

Sajeed yace"munyi a ɗaki"

  "Kufa" ta faɗa tana nuna su Azeeza

 Girgiza mata kai su kayi alamar a'a, Hannah ma tace nima banyi ba, saboda babu hijabi. 


 "Okey, yanzu abun da za'ai ku shiga toilet ku yi alwala, kafin ku fito zan dauko maku hijabin" amsa mata sukayi  toh.


 Ɗaya bayan ɗaya suka shiga toilet, bayan sunyi alwala kowaccensu ta sanya hijabi, asaman carpet din da ta shimfiɗa masu su ka yi sallar, bayan sun kammmala suka cire hijaban suka bata ta ninke ta maida su a wardrobe.

 

  Zama sukayi kan carpet din gefen gado, mazan suna fuskantar matan, sun ƙurama Unaisah ido suna jiran jin me zatace masu.


   "Kin yi shiru ba ki ce komai ba sister, ke muke sauraro meke faruwa da ɗan uwan mu"? Acewar Haris

 Sajeed yace"tun jiya da abun nan Ya faru mun ganki kina kuka kina fadin danish ya rikiɗa ya koma maciji, abun ya tsaya min araina" da damuwa a fuskarsa yai maganar.

 

  "Akwai abun da na 6oye maku tun muna a prison ban samu damar faɗa maku ba......." a tsanake Unaisah ta labarta masu dukkan abun da ya faru tun daga kan tattaunawarsu da Salsabeel farkon haɗuwarsu a gidan kurkukun ƙaddara da kuma gwagwarmayar da suka yi wajen shawo kan Danish da ruwan zam zam, Har izuwa kan abunda ya faru jiya daya rikiɗa ya zama maciji, tunda tafara basu labari hankalinsu ya tashi matuƙa, sun girgiza da jin cewa Danish dinsu GIANT ne, Kallon kallo suka soma yi a tsakaninsu, idanuwansu a zazzare, Jikin ta ƙaura yai la'asar, wato an gudu ba atsira ba.


 La66an Sajeed na kerma ya furta"kina nufin Danish Giant ne'? Jinjina mashi kai tayi alamar eh, dafe kai haris yai da hannu ɗaya da wata irin karyayyar murya ya furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Mun shiga uku! Wai su waɗannan azzulaman mutanan wani zunubi muka aikata masu ne? Da suke azabtar da rayuwarmu? Meyasa suka cutar da rayuwar Danish? Me bawan Allahn nan yayi masu"? Idanuwanshi tuni sun kaɗa sunyi jawur da su

 "Ni dama nasani bazasu ta6a ƙyale mu ba, zasuyi amfani da danish ne donsu maida mu kurkukun ƙaddara"!

  Cikin sanyin murya Batool tace"bawan Allah danish, shine abun tausayi, wallahi ina jin baƙin ciki da takaicin azabtar mana da rayuwar ɗan uwanmu da suke Yi, danish tun yana ƙarami suke juya shi, sun hana rayuwarshi sakat, narasa gane dalilin dayasa suke yi mashi haka, Ya Allah ga bawanka nan kai kadai kasan a wani hali yake aciki, Ya Allah Ka fitar dashi, ka kawo mashi ɗauki acikin rayuwarshi', tuni hawaye sun wanke fuskar Batool.


 Cikin shesshekar kuka Azeeza tace"Allah ya isa ba zamu ta6a yafe masu ba, Mugaye azzalumai ƴan wuta, In sha Allah tun agidan duniya zasu fara danasanin cin zalunmu da su ka yi da kuma ƙuntata rayuwar ɗan uwanmu da suke Yi"


 Azeeza na rufe baki, Naufal da takaici ya ishe shi, cikin jin ƙunar rai Ya soma magana"wannan wace irin rayuwace? ya zamuyi da ranmu? Ni yanzu na fahimci KURKUKUN ƘADDARA RAYUWARMU CE!! mune kurkukun ƙaddara saboda duk inda zamu kasance gidan kurkukun ƙaddara yana atare damu, Meyasa!!!"? Ya jefa tambayar idanuwanshi akan fuskar Unaisah, wadda tayi shiru tana sauraronsu, tabbas maganar Naufal abun dubawace, Yanzu ta fara zargin wani abu.


 "Naufal, kamar yadda ka faɗi nima haka nake tunani, rayuwarmu itace gidan kurkukun ƙaddara, amma meyasa zai kasance haka? Su wanene suka sadaukar da mu?...." ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta.


 Sajeed yace"yakamata mu fallasa asirin komai ke faruwa agidan kurkukun ƙaddara ga mutanan da suka taimaki rayuwarmu ina da tabbacin zasu taimaka mana don ganin an gano su wanene munafukan dake sadaukar damu ta hakanne zamu tabbatar da zarginmu"


  Javed yace'nima ina goyan bayanka Sajeed! Mu tona masu asiri kawai, idan da rabon mu rayu zamu rayune duk runtsi duk wuya, kai koda ace zamu mutu ne bayan mun tona masu asiri wallahi munci galaba akansu, tunda har muka yi nasarar guduwa daga cikin kurkukun ƙaddara, wanda ko a tarihi ba'a ta6a samun prisoners da suka gudu suka tsira ba sai akanmu"! 


 A hankali unaisah take binsu da kallo, ta fahimci ransu yakai maƙura wurin 6aci, Jininsu akan akaifarsu yake, kowannansu atsorace yake da  abunda ke faruwa da danish.


    Fashewa da kuka jemimah tayi haɗi da ɗaura hannayenta biyu saman kanta tana fadin"Wayyo Allahn mu mun shiga uku, Yanzu shikenan danish din mu ya zama dodon kurkuku zai ɗauke mu ya maida mu can mu cigaba da cin ganye" fuskarta sharkaf da hawaye, ruko hannunta Unaisah tayi acikin nata"Ya isa haka, Ki daina kuka, kanki zai Iya yin ciwo," girgiza kai ta dinga yi tana fadin"genie ba zaki gane ba, wallahi banason komawa kurkukun nan, haushinsu nake ji, Allah zuciyata zata Iya bugawa in mutu kowa ya huta"

  Gaba ɗaya idanuwansu na akan fuskar jemimah, ta haƙiƙance tana yin magana shatun jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu saman fatarta.

  "Sun kashe mun majnoon dina, sun kashe mana Unaizah, Yanzu kuma mu suke son kashewa fa" ta ƙare maganar tana faman jan majina'

  Kwanto da kanta Angel tayi saman cinyoyinta, ta ɗaura hannunta kan sumarta cikin sigar lallashi take yi mata magana"in sha Allah bazamu ta6a komawa gidan kurkukun ƙaddara ba, Har bada, munbarshi kenan bi'iznillahi mune zamu kawo karshen kurkukun da fasiƙan Shuwagabannin su, zamu tarwatsa baƙin tarihin da suka kafa, zamu shafe babinsu a doron duniyar nan, zasu ɗanɗanin kuɗarsu har sai sunji inama ace ba'a halitto su a duniyar nan ba, wannan Alƙawarine!" da ƙwarin gwiwa unaisah ta ƙare maganar.


 Shiru jemimah tayi tuni ta haɗiye kukanta, Jikin kowannansu yai sanyi, maganganun da suke yi yai silar fama masu tabon dake acikin zuciyoyinsu.

  Daƙyar Hanna ta Iya buɗe baki tace"ni yanzu damuwata a wani hali danish yake aciki"? Tayi tambayar idanuwanta cike tab da ƙwalla 


    Angel ce ta bata amsa da cewa"har yanzu bai dawo mutun ba, amma ɗazu boss man ya fada min cewa malamin da zai duba jikinshi ya ƙaraso Ina da tabbacin Yana acikin gidan nan, shiyasa Big guy Yace mu zauna a ɗaki bayason ganin gifcinmu, yakamata mu tayashi da addu'a, ita yake buƙata daga gare mu" tunkan ta rufe baki, sukayi saurin daga hannayensu sama, Itama ta ɗaga nata,

 "Jemimah ki tashi muyi ma ɗan uwanmu addu'a" Unaisa ce tayi mata magana, daƙyar ta ɗago da kanta haɗi da ɗaga hannayenta sama kamar yadda sukayi 

  Addu'o'i unaisah ta soma karantowa suna amsa mata da ameen ameen, bayan ta kammala kowan nan su Ya shafa saman fuskarshi, kafin su zame hannayensu, kunnuwansu suka soma jiyo masu motsin buɗe ƙofar dakinsu, A hanzarce suka ɗago suna kallonsu.


   Big guy ne ya shigo hannun shi ruƙe da faffaɗan tray Na kayan breakfast dinsu, Daga Bayanshi Ummin america ce, Ta ɗauki wankan turkish gown launin brown anyi mata adon stones launin yellow, mayafin da tayi rolling kala ɗaya ne da stones din rigar, ta sanya high heels a ƙafarta, daga sama rigar ta matseta ta bayyana surar kirjinta, daga bayan rigar tudun mazaunanta ya fito sosai.

 Tunda batool taji ƙamshin turaren ummin america hankalinta ya tashi, tasan dole ta hukuntata akan fitowar da tayi daga ɗaki batare da saninta ba.

  A tsakiyarsu big guy ya ɗaura tray din kayan abincin kafin Ya soma yin magana.

 "Ga auntynku nan Ummi, zata zauna atare daku don ta ɗebe maku kewa, idan kuna buƙatar wani abu, ita zaku faɗa mawa" amsa mashi sukayi da toh.


  Big guy ya maida dubanshi ga ummi dake atsaye ta ruƙe qugu da hannu ɗaya, Hadaddiyar agogon hannunta sai ƙyalli take yi.


  "Ummi, ki kula da su, bana so asamu matsala, malamin ne ya buƙaci a tattara sauran yaran wuri ɗaya sannan aja hankalinsu gudun kada suji sautin abunda zai rikitar da su"

 Lumshe mashi ido tayi, alamar taji mai yace, shi kanshi daurewa yake yi, domin kuwa wankan da ummi ta ɗauka yaja hankalinshi, musamman shu'umin ƙamshin humran dake fita a jikinta.


 Muryarta da kwarkwasa tace"okey, baka da damuwa"


 Bayan fitar big guy daga ɗakin.


Ummi ta kalli su unaisah, atare suka haɗa baki wurin gaishe da ita.


 "Ina kwana aunty ummi" yamutsa fuskarta tayi"lafiyalou, Ina batool"? Ta jefa masu tambayar tana kallonsu, kafin su bata amsa idanuwanta suka sauka akan yatsun hannun batul, ta 6oye kanta abayan haris, duk don kada ummi ta ganta.


Babu wanda ya fahimci wani abu, sai ita data san meya haɗasu.


 "Kunyarki take ji Aunty ummi, shiyasa ta la6e" acewar Unaisah.

  Ta6e baki ummi tayi kafin tace"Ina maganin muran da boss man Ya baki"? Ta fada tana nuna unaisah da hannu.

  sai lokacin ta tuna da maganin batasan tun yaushe ta jefar dashi ba.


 "Kin yada kenan"? Girgiza kai tayi a'a, Yana a hannuna tun ɗazu, namantane ban kaiga bata ba"

  Juyawa baya ummi tayi tana kallon tsakar dakin, Karaf idanuwanta suka sauka akan Blister pack din dake ajiye ƙasa, cikin takun Isa Ta nufi floor din ta zuƙunna ta ɗauki maganin"ajiyar zuciya unaisah ta sauke ganin ta gano shi'

   "Ku matsa min anan zan zauna muyi breakfast," ta faɗa tana nuna tsakankanin Batool da Haris, da sauri Ya matsa mata, taje ta zauna idonta akan batool data ƙanƙame haris, ruƙo hannunta ummi tayi tare da rabata daga jikin haris, duk tabi ta ruɗe, taƙi yadda su haɗa ido.


 Bottle water Unaisah ta ɗauka ta buɗe murfin, ta tsiyaya ruwa acikin cup, ta miƙa ma ummi, kar6a tayi tare da fadin"thanks" kafin ta curo maganin ƙwaya biyu ta miƙa ma batul, yatsun hannunta na kerma ta kar6a ta sanya abaki, ta kar6i cup din hannun ummi ta kur6i ruwan ta haɗiye maganin, Bayan ta gama ta ajiye cup.


  "Bata da lafiya ne"? Sajeed ne ya tambaya, parveen tace"Mura take Yi,"


 "Shiyasa naji muryarta ashaƙe, sis Allah ya baki lafiya" amsa mashi da tayi da ameen, sauran mazan sukayi mata sannu ta amsa masu.

 Kafin ummi ta fara serving dinsu, A plates ta zuba ma kowannansu abinci banda batool, ɗaya bayan ɗaya ta miƙa masu, suka kar6a suna ci, kallon Batul tayi"atare zamu ci" ta faɗa tana sakar mata shu'umin murmushi afakaice batare da su Unaisah sun gani ba.

    A plate ɗaya ta zuba masu farfesun naman kaza, Yaji kayan kamshi ga uban romo.

   Daƙyar batool take iya shan farfesun, saboda Ummi ta hanata sakat, da zarar ta ɗago sai ta haɗa ido da ita, ta rasa gane dalilin dayasa ummi take son takura rayuwarta.  Hankalin Unaisah ba akansu yake ba, saboda damuwar data bijiro mata, ta ƙosa taji me ke wakana da Danish, Malamin Ya fara Yi mashi aiki ko kuwa.......? Shin meya faru bayan zuwan Sheikh Imam malik!? 


Bayan ƙarasowar motarsu akatafaren Gate din shiga gidan Owais Jami'in dake driving dinsu yayi parking a agaban entry hall, Ya fito a hanzarce Ya zagaya ya buɗe masu murfin motar, A hankali Prime minister hateem ya fito daga Ciki, Kafin Sheikh Imam Ya zuro ƙafarshi waje shima Ya fito Yana ƙarema ginin gidan kallo, ya yaba da haɗuwar daular Owais, har saida ya furta masha Allah.


  Kafin su ƙarasa falon, Glass door dinsa ta buɗe, Chief Owais Ne Ya bayyana gefe da gefenshi, Boss man ne tare da Big guy, da kuma sauran jami'an isod da suka hallara domin tarbarsu.

   Murmushi prime minister hateem yasakar mashi, tare da nufarshi tunkan ya isa gare shi, Chief owais Ya riga shi zuwa Ya haɗa hannayenshi biyu yai hugging din uncle din nasa"

Kafin Ya ɗago Ya nufi Sheikh Imam Ya rungume shi, fuskar kowannansu ɗauke da murmushi.


  "Owais fatan na sameka lafiya, tsawon lokaci bamu haɗuba, aiki ya 6oye ka," Sheikh imam ne yai mashi maganar

   Calmly ya furta"Ina lafiya, nayi missing dinka, amma naji dadin ganin ka yau, Ina fata uncle dina bai takura maka ba? Nasan shine Ya matsa maka akan zuwa Nigeria" da zolaya ya fada,

 Shekh Imam Yace"kai dai bari, kamar yadda baiyi bacci ba adaren jiya nima haka ya hanani Yin bacci, babu shiri yasa na fara shirye shiryen zuwa Nigeria hada ƙoƙarin turamin jirgin da zai ɗaukoni" Da zolaya yai maganar,

 Hateem dake sauraronsu, baice komai ba sai dai murmushin dake akan fuskarsa bai washe ba.

     Dubanshi chief yai"uncle, sannu da zuwa, Mu shiga daga ciki, nabarku atsaye" 

   Atare suka jera zuwa babban falon gidan, saman sofa mai mazaunin mutun uku, prime minister da Sheikh imam suka zauna, Chief Owais Yana daga zaune kan 2 seater, Yayin da Big guy da Boss suke atsaye sun goya hannayensu saman kirjinsu.

     Kallonsu chief Yai kafin Ya soma magana"Taj wannan uncle dina ne Prime minister Hateem na ƙasar Canada, Kai kaɗaine bakasan shi ba, wannan kuma Sheikh imam kenan, Aminin kakanmu Obie..."


    Cire face mask din fuskarshi Yai, Cikin girmamawa ya soma gaishe da hateem"ina yi maku barka da zuwa, najima ina jin labarin prime minister awurin Owais sai dai ban ta6a ganinsa ba, ashe da rabon zamu haɗu, kuma tunda naga fuskarshi raina ya bani cewar Uncle dinka ne saboda kamanceceniyar dake a tsakaninku"


 Ƙayataccen murmushi prime minister yasaki a yayin da yake kallon fuskar taj yace"Nagode da karramawarka agare ni, kuma naji dadin haɗuwa dakai, Ina fata zamu cigaba da yin zumunci a tsakaninmu"

Tajo yace"in sha Allah" har cikin ranshi mutumin ya kwanta mashi, kuma Yayi mamakin haɗuwarshi donshi a hoto yasanshi, kuma yayi mamakin sakar mashi fuska da ya yi a matsayinshi na babban mutun mai ruƙe da babban muƙamin shugaban ƙasar Canada, koda yake yasha ji awurin mutane cewa baida girman kai ko kaɗan, mutunne najama'a kowa nashine mai kudi da talaka awurinshi duk ɗayane.


 Chief Owais Ya ɗaura dacewa"Uncle sunan shi Taj, Mahaifin Yarinyar nan, dana ta6a baka labari, ina fata ka gane shi"

 Jinjina kai Hateem yai da mamaki akan face dinsa yace"masha Allah, ina ita yarinyar take ne? An gano ta"?


   Ɗaga mashi kai yai alamar eh.

 "Na tayaka murna my son, Allah ya tabbatar da alkhairinsa, Ina fata Yaya sharafudden Yasan da maganar mahaifinta da kuma ita kanta yarinyar"!?


 Chief owais Yace"Ya sani, na faɗa mashi, sai dai basu ta6a haɗuwa da daddynta ba, amma na yanke shawarar zan haɗasu kwanan nan idan muka shawo kan matsalar yaron nan"

  Ga dukkan alamu Hateem yaji dadin ganin tajuddeen, duba da yadda yake kallon shi.

 Gyaran murya sheikh Imam yai masu"Idan kun gama magana ina jiranku, Kun ajiyeni kamar buhun masara, Yakamata ku bari in kammala aikina inyaso kunyi firar taku" gaba ɗaya suka sanya dariya banda Chief daya ɗan murmusa.

  Prime minister yace"ay mana afwa ya sheikh, nayi kewar yarona, Mun jima bamu haɗu ba" Murmushi sheikh imam yasaki, da zolaya yace"wani yaro kake nufi? Wanda yahanaka runtsawa daren jiya? ko kuwa wanda kuke Yin fira da shi a yanzu"?

 Prime minister yace"dukansu biyun nake kewa" 

Sheikh imam yace"yanzu naji magana, bismillah owais Muje ka nuna min ɗakin da yaron yake" amsa mashi yai da okey

 Atare suka miƙe tsaye tare da nufar Up stairs, tunkafin su ƙarasa ɗakin, suka soma jiyo kururuwar macijin Yana gurnani.

  Sheikh Imam yace"Da alama Yasan da zuwana" murmushi kowannansu ya saki, abakin ƙofar ɗakin suka tsaya kafin su shiga sheikh imam Ya dubi Chief owais"naji kace akwai yarinya agidan nan ɗiyar mutumin da naji ka kira da taj ko"? Kafin owais ya bashi amsa Boss man ya riga shi cewa"ba ita kaɗai bace, akwai sauran ƴan uwanta dake rayuwa agidan"


Sheikh imam yace"Toh, ina buƙatar a killace su wuri ɗaya, sannan aja hankalinsu ta yadda baza su iya  jin abun da ke faruwa cikin gidan ba, Idan ba haka ba zasu iya firgita arasa gane kansu" boss man ya amsa mashi da toh.

 Kafin Ya dubi big guy"please kaje wajensu, ka aiwatar da abunda malam yace" da sauri big guy ya nufi hanyar komawa down stairs, Ya rage saura su uku.


 "Bismillah mu shiga daga ciki" dafe ƙofar boss Yai, ta zuge a hankali kafin suka shiga dakin.


 Jin motsin shigowarsu dakin Yaja hankalin salsabeel dake atsaye kai idonshi ga dubansu.


   Hankalinsu na akan narkeken macijin dake zarya tsakiyar gadon wata irin kururuwa yake fitarwa yana huci.


  Gaisawa sukayi da salsabeel, daga bisani, Chief Yai mashi alama da hannu, salsabeel Ya fahimci ƙarin bayani yake nema game da halin da Giant snake din yake aciki"


 "Ni kaina bansan meke damun shi ba, Yanzu ya farka daga bacci, Yana huci, zai Iya yiwuwa saboda rashin ganin ƴar uwarshi akusa dashi ne" 


Hankalin prime minister hateem ba ƙaramin tashi yai ba, sai yanzu yaga girman macijin Ya wuce misali.


Sheikh Imam Yace"Saboda ni yake wannan hucin, ku dan bamu wuri zan fara aikina" babu musu suka fito daga dakin, anan second floor suka tsaya suna jiran tsammani

 Bayan fitarsu ya rage saura sheikh imam da Macijin a ɗakin, Toilet Ya shiga jim kaɗan ya fito da alama alwala ya ɗauro, Bakin gadon Ya tsaya tare dakai hannu Ya damƙi bargon dake a nannaɗe kan mattress, manyan Addu'o'i ya soma karantowa Yana tottofe bargon, kafin ya fara yin karatun alƙur'ani, Yayin da idanuwanshi suke akan macijin dake ta ƙoƙarin saukowa daga saman gadon Hanyar guduwa yake nema sai dai ya kasa yin hakan saboda ɗaurewar da Sheikh imam Yayi mashi da karatun kur'anin da yake yi, Bayan Ya kammala yin ƙira'ar, Ya daddage Ya haye kan gadon, Ya kifa mashi bargon saman jikinshi, Ya daddanne shi da ƙafafuwanshi, da hannayenshi yabi ko'ina ya dafe, wata irin kururuwa macijin yake saki tamkar ana ƙona  jikinshi da wuta, hatta waɗanda ke a wajen ɗaki saida suka jiyo sautin, Har saida prime minister ya dafe kunnanshi da tafin hannun shi.

   Jami'an dake a kewaye da gidan da gudu suka shigo part din hannayensu ruƙe da bindigu, sunyi tunanin wani mugun abunne ke faruwa, daga saman bene Boss Man Yai masu magana akan su koma bakin aikinsu hakan yasa suka juya da sauri suka bar part din.


Sheikh Imam Ya hada uban gumi, zufa ta wanke fuskarshi duk da sanyin A.c na ɗakin, Yaƙi Sakin bargon daya daddanne Macijin, sai ƙoƙari yakeyi donya kubcema ɗaurin da yayi mashi.

  Maƙoshin shekh imam tamkar zai 6allo tsabar yadda yake cigaba da karanta mashi ayoyin ƙur'ani tare da addu'o'in karya sihiri, Yaci gaba da tottofe bargon da yake kudundune.

  Ba zato ba tsammani, suka soma jiyo wasu irin muryoyi na baƙaƙen shaiɗanun aljanu suna fadin"kashe ka zamuyi sheikh imam! Dole ka mutu tunda ka shiga sabgarmu, zaka mutu"

 Da karfin hali sheikh imam yace"Idan kunga na mutu lokacin mutuwatane yayi don ubanku, Ni da Allah na dogara bada ku ba, Raina a hannunsa yake, Ku bakusa ku cutar dani ba, face da izninsa, Kunsan bana jin tsoronku tun fil azal......" bai ƙare maganarba, sautin dariyarsu Ya karaɗe ɗakin, tamkar ana buga ganga, Hankalinsu boss man ya tashi matuƙa, damuwarsu kada wani abu ya samu sheikh imam.

  Cigaba da magana sukayi da kakkausar murya suke fadin"mutuwa zakayi sheikh Imam, ajalinka ne Yazo, kai ka sani ba'a shiga huruminmu a zauna lafiya, mun kashe ire irenka da dama waɗanda suka yi ƙoƙarin yi mana shisshigi, Sheikh Imam kadaina janyo mana ayoyin alkurni bazasu ta6a yin tasiri akanmu ba, Mu ba kalar shaiɗanun da ka saba ƙonawa bane"

 Runtse ido sheikh imam yayi, jin numfashinshi na ƙoƙarin ɗaukewa tamkar an shaƙe mashi wuyanshi, idanuwanshi suka kaɗa jawur tamkar garwashin wuta, sautin muryarshi daƙyar yake fita ahaka yake kokarin cigaba da yi mashi karatun kur'anin.........."


"Hankalina bai kwantaba, Inajin fargabar wani abu ya sami malamin nan, Mutanan nan fa ba ƙananun shaidanu bane" salsabeel ne yai maganar.

  Boss man yace"ni kaina fargaba nake ji, gaskiya akwai matsala, kada mu jefa rayuwarshi cikin hatsari,"

  Duk maganganun da sukeyi akan kunnan Chief owais da prime minister Hateem, jikinsu yai sanyi babu mai magana acikin su.


Lokaci ɗaya bugun zuciyar Prime minister ya ƙaru, arude ya furta"ku buɗe kofar nan" ya fada yana nuna ƙofar dakin danish" da sauri Bossman Ya nufi ƙofar ya sanya hannu ya dafe glass din wani iko na Allah ƙofar taƙi buɗewa, gashi sunji shiru babu motsin sheikh imam da kuma kururuwar macijin.


  "Babu lafiya, salsaleel zoka taimaka min mu buɗe ƙofar" matsawa salsabeel yayi gaban kofar, suka haɗa ƙarfi shida boss suka dinga bugun ƙofar taƙi buɗewa.


  Da ƙarfi suke ambaton sunan sheikh imam shiru bai amsa masu ba, babu alamun motsinshi.


  Hankali atashe Chief Owais Ya ɗago da ido suka kalli juna shida prime minister.


  "Bana so wani abu ya sami malamin nan, Ni ne silar kiranshi daga sudan, Idan wani abu ya same shi bazanji dadi ba, zanyi danasani Owais, Yakamata kuyi wani abu akai" damuwace ƙarara akan fuskar Hateem.


  "In sha Allah Uncle babu abunda zai faru da shi, ka kwantar da hankalin ka" chief na ƙarasa fadar hakan, Ya nufi ƙofar ɗakin, da sauri salsabeel Ya matsa mashi hanya, Boss man Yaja gefe ɗaya, bismilla ya furta da kyakkyawar niya, kafin ya daki ƙofar da kafaɗarshi, nan take ƙofar ta zuge da gudun gaske, ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, salsabeel yayi mamakin ƙarfin owais.

   An rasa wazai fara shiga dakin, kowa fargaban ganin abunda zai taras yake yi, hatta shi kanshi chief din....... 😳😳😳

  

  *mu haɗu next page gobe idan Allah yakaimu da rai da lafiya in sha Allah, sannan game bukatar cigaba da karanta prisoners 500 ne zaku tura ta bank acct dina, ga ta inda za'a tuntu6eni 08103884440*
3196407426


Bature Hafsat Muhammad

First bank 

Idan kin tura zaki bada hoton receipt amatsayin shaida🤗

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post