Kurkukun Ƙaddara Book 2 Page 38

Kurkukun Ƙaddara Book 2 Page 38

A katafaren Villa Mallakin Hateem Obinna, haddadiyar daula kuma aljannar duniya wadda idan ka zura ƙafarka acikinsa sai ka yi tsammanin ƙasar dubai ka shiga, Hamshaƙin Gidanshi a kewaye yake da Jami'ae sojoji da ƴan sanda, mugun tsaro ake yi mashi, babu wanda ya isa ya ƙetare gidan hateem cikin sauƙi idan ba Mahaifinsa ba da yayyansa, amma bayan wadanda kafin mutun ya samu iznin shiga ciki sai ya ci baƙar wahala don kuwa daga ƙasa har sama zasu bincike ka da na'ura, har ƙwara mutun ya shiga masarauta yafi mashi sauki, akan Gidan prime minister, tsaruwar ginin gidan kuwa da haduwarshi ba'a magana, gaba ɗaya Obie estate babu gidan da yakai Na prime minister In ka cire Villah din Owais.*Gimbiya Mujeedat👑*
A kishingiɗe take saman Katafaran gadonta na alfarma, kalar na sarakuna waɗanda suka gaji Arziƙi, gadon a kewaye yake da labulaye launin royal blue, an ƙawata shi da lallausan zanen gado fari ƙyal, haɗi da matassan kai launin blue and white, gefe da gefen gadon bedside drawers ne suma launin royal blue, daga saman su Fitilune masu bada haske launi daban daban, an zuba mata tsadaddun furniture a ɗakinta, ya ƙawatasu sosai da kayan alatu.


  ta ɗaura kanta saman pillow, Rigar dake a jikinta Silk robe ce launin ice blue, tabi shape dinta ta bayyana dirarran dirin jikinta, A halitta Gimbiya Mujeedat doguwace, fara sol tana da dogon wuya, hutu ya zauna mata ta ko'ina Allah Ya hore mata, Kyau kamar ita ta zana kanta, fararen idanuwanta tamkar an ɗiga masu zaiba, launinsu dark black ne, ga tarin ziraran eye lashes dinta da suka ƙawata kewayen idanuwanta sun yi mashi rumfa, dogon hacinta a tsaye yake babu lanƙwasa, siraran la66anta launin ja tamkar na jarirai tsabar ƙarantarsu da laushin fatarsu, tana da yalwatacciyar sumar kai baƙa wulik mai santsi da silbi, har gadon bayanta, Tabarakallahu ahsanul khalilin Gimbiya mujeedat maƙurace afagen kyau, uwa uba ta fito daga tsatson masarautar daular larabawa, bugu da ƙari First Lady ta ƙasar Canada, ajin farko ce ita, zan iya cewa baba Hateem Ya more mata 😉


  Ziririyar sarƙar wuyanta ta zallar diamond ce, haka zalika Ziraran yatsun hannunta na dama suna sanye da Ring set na Gold komai nata me tsadane ita kanta lu'u lu'un ce.


Yanayin yadda ta kwanta da alamun kasala atattare da ita, ta ɗan lumshe idanuwanta, fuskarta sam babu walwala, kamar akwai wani abu dake damunta.

 

A lokacin da bata yi tsammani ba, muryar prime minister Hateem ta karaɗe kunnuwanta, sallama ce yai mata yayin da yake shigowa dakin, Cikin shiga ta jallabiya launin maroon, daddaɗan ƙamshin turarenta dana ƙamshin turaren wuta ne Ya daki hancinsa Har saida Ya lumshe idanuwanshi, mutunne shi ma'aboci son ƙamshi, sai kuma Allah Ya haɗa shi da mace ma'abociya son kamshi da son ado, shiyasa a kullum take ƙara shiga ranshi, soyayyarsu bata tsufa, Idan suna atare da juna daukar kansu suke Yi tamkar sabbin ma'aurata.Bata samu damar amsa mashi sallamar shi ba, daƙyar ta iya buɗe idanuwanta da sukayi mata nauyi, launinsu ya rikiɗa zuwa ja, saboda rashin baccin da batayi ba adaren jiya kuma shine sila, Ya hanata sukuni, bai ta6a burkice mata ba irin Na jiya, Ƙiri ƙiri Ya takura kanshi, Ya hana kanshi runtsawa, kuma yaki fada mata abun da ke damun shi, daga ita har shi jiya babu wanda ya runtsa, saboda ta maida damuwarshi tata.      Koda ya shigo dakin, a hankali ya daura idanuwanshi kan fuskarta, sai yaji ba daɗi har cikin zuciyarshi yasan bai kyauta mata ba, tunda ya riga da yasan halinta na damuwa da damuwarshi.


  Daga gaban gadon Ya dakata dayin tafiyar, ya goya hannayenshi on his broad chest yana fuskantarta.


   Ba zato ba tsammani, yaga ta galla mashi harara haɗi da murguɗa mashi ƙaramin bakinta.


    Nan take ya fahimci fushi take yi da shi, ranta ya 6aci.

  Cikin harshen turanci tace"Sannu da dawowa" 


Ta inda gimbiya mujeedat take burge shi, duk mun fushin da zatayi dashi hakan bai hanata kula da shi


  "Yawwa, fatan na same ki lafiya"


 Yamutsa fuska tayi fuskarta babu annuri ta soma magana tamkar bata son furtata.


  "Mijina baka kyauta min ba, ka hana kanka runtsawa nima kuma ka hanani runtsawa, nayi koƙarin faranta maka duk don na kawar maka da damuwarka amma babu abunda ya canza, Ka jefa ni cikin wani hali daga daren Jiya zuwa yau, meyasa ba zaka fadamin meke damunka ba? Ko ban isa nayi maka magani bane? Nasan ka yarda dani, sannan baka 6oye min komai, sirrinka nawa ne amma meyasa jiya kaƙi fadamin damuwarka" sautin muryarta tamkar ana busa sarewa tsabar daɗinta.


 Idanuwanta aruntse take yi mashi magana, don ta fahimci idan tana kallon cikin idanuwanshi bazata samu ƙwarin gwiwar yi mashi magana ba"


  Sauke hannayenshi yai daga saman kirjinshi, ya zagayo ta gefen da take a kwance Ya zauna, yana duban fuskarta

   Ƙayataccen murnushine kwance kan la66ansa, yasan ta kan mace, idan ranta ya 6aci cikin sauƙi yake faranta mata


    "Uwar gida sarautar mata, Gimbiyata, Ina neman afwarki ranki shi daɗe, bai kamata gimbiya tana fushi da bawanta ba, Ni fa a karkashin inuwarki nake, da taimakonki nake samun natsuwa da kwanciyar hankali, taya zanso na 6ata maki rai? Bayan kece linzamin dake sarrafa ni...."

Tun da yafara gaya mata daɗaɗan kalamansa, ta fara sassauta fushin fuskarta,

A hankali ta buɗe idanuwanta kan fuskarshi, da sauri ya kama kunnuwansa Yana fadin"Am sorry My wife, na gane kuskurena"

Ta6e mashi baki tayi"Ni so nake ka fadamin meke damunka? Da har yai silar hanaka runtsawa, kalli fuskarka duk ta yamutse, idanuwanka sun ƙanƙance saboda rashin baccin da baka yi ba" ta faɗa tana faman 6ata fuska, yayi shiru yana kallonta batare daya furta mata komai ba.


 "Kai nake sauraro! Meke damunka? Sannan naji kana waya ɗazu, akan za'a tura da jet zuwa sudan, wa za'a ɗauko"? Ta jefa mashi tambayar cike da son jin amsar shi.


   Ya rasa amsar da zai bata, Ta kafe shi da ido.

  Gyara muryarsa yadanyi kafin yafara magana a tsanake.


 "Sheikh imam nake son gani, baya a ƙasarne ya tafi sudan, Ina buƙatar ganinsa da gaggawa akwai taimakon da zaiyi mani"


Fuskarta da alamun mamaki ta furta"meyasa kake son ganin shi? Wani kalar taimako zaiyi maka"


  "Wani matashin yarone yake fama da aljanu sun hana rayuwarshi sakat, jiya ina zaune tare da baba muna yin firar yaushe rabo, a lokacin da bamuyi tsammani ba, yaron ya faɗo falon gwanin ban tausayi, duk mai imani idan yaji irin jarabtar da yaron yake fuskanta sai ya tausaya mashi....." tun da ya fara magana gimbiya mujeedat ta yunƙura ta miƙe daga zaune tana dubanshi, Ya fayyace mata komai sai dai bai faɗa mata da suffar da ya ga yaron ba.


  "Na yanke shawarar yin magana da sheikh Imam akan halin da yaron yake aciki, Ina da tabbacin zai taimaka mashi In sha allah, yanzu haka da nake yi maki magana, sheikh imam Yana akan hanya, Ina tsammanin nan da ƙarfe goma jirgin daya ɗauko shi zai yi sauka a nigeria.


  Yanayin fuskartane Ya canza, yayin da take kallonshi, Ya rasa gane kallon menene take yi mashi, har dai yagaza jurewa jin shirun yayi yawa yace"baki fahimci abunda nake fadi bane? Ko bakiji dadi bane"?

Girgiza mashi kai tayi"ko ɗaya mijina, wani abune yadan bani mamaki, nasan halinka ne yin taimako, indai abune daya shafi aikin Allah kana akan gaba, amma tunda nake arayuwata ban ta6a ganin tausayi da ya kai wannan ba atare dakai, saboda yaron jiya ba ka yi bacci ba, aduk lokacin da ka dawo gida a yanayi na damu nasan yadda zan shawo kanka in kwantar maka da hankalinta harma kayi bacci, amma adaren jiya saboda damuwar halin da yaron yake, waɗannan dabarun nawa basuyi maka aiki ba, bayan haka ka tura da jirgin da zai dauko malamin da zai duba shi daga Sudan zuwa Nigeria, saboda kana buƙatarshi da gaggawa don ya duba yaron...." ta faɗa fuskarta da alamun ruɗani, yayin da Hateem ya natsu yana sauraronta abunda bata sani ba ayanzun ma da take yi mashi magana hankalin shi yafi karkata kan agogon dake sanye a wrist din hannun shi, burinshi goma ta buga.


   "Abunda yafi ɗaure min kai mijina, wanene yaron? Menene alaƙarka da shi? Yanayin yadda ka nuna damuwa akanshi ko ɗan cikin ka sai haka"  Jim ya ɗanyi kafin ya furta"bani da alaƙa da shi, bansan shi ba! Kuma ban ta6a ganin shi ba, kamar yadda na faɗa maki adaren Jiya idanuwana suka fara yin tozali da shi, tun daganan sai naji ƙaunarsa ta kama ni, har naji ina son na taimaka mashi, sai nake jima kamar nike da alhakin ciwon shi, idan har ban taimaka mashi yaji sauƙi ba Allah zai iya kamani da laifin ƙin tallafa masa da banyi ba"


Murmushin gefen fuska Gimbiya mujeedat ta sakar mashi har fararen hakoranta suka bayyana.


"Kai din na dabanne mijina" ta faɗa tana matsawa kusa dashi, ta ɗaura hannunta na dama saman sumar kanshi.


"Samun miji kamarka a duniyar nan abune mai wuya, kana da tausayi da jinƙan na ƙasa dakaina, sannan kowa naka ne, burinka ka faranta ma wanda yake acikin kunci koda ta silar hakan kai zaka rasa naka farin cikin, ni kaina ina ilmantuwa da kyawawan ɗabi'unka da halayanka, shiyasa nake alfaharin mallakarka da nayi a matsayin mijina" lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kalamanta ba ƙaramin faranta mashi suke Yi ba, tamkar tana ƙarfafa mashi gwiwane.


  Zame hannunta tayi daga kan sumar shi zuwa gefen fuskarshi idanuwansu cikin na juna

"Kamar yadda ka sani, duk abunda kakeso nima inason shi, koda bana son shi saina yi kokarin koya ma kaina yadda zanso shi saboda mijina yana son shi, don haka nima ina goyan bayanka akan Yaron, Allah ya baka sa'a mijina ya cika maka burinka na ganin yaron ya samu lafiya, A shirye nake dana bada gudummuwata wurin ganin mun inganta rayuwarshi"

Murmushine ya bayyana akan fuskar prime minister, kallonta kadai da yake yi natsuwa yake samu, musamman idan tana ƙarfafa mashi gwiwa da daɗaɗan kalamanta.

"In sha Allah zamuyi nasara, yaushe zaka bani iznin zuwa ganin yaron"?


  "Na yanke shawara idan yaji sauƙi, zan gayyace shi zuwa gidan mu, zamu shirya mashi dinner."


Tsantsar farin cikine akan fuskarta"naji dadin jin hakan mijina, wallahi har na ƙosa naganshi, duk na kagu gashi bazamu daɗe a ƙasar ba, kwanaki kadan suka rage mana" ta fada tana 6ata fuska alamar bataso hakan ba.

  Damƙo hannunta yai da take kokarin shafa wuyanshi, fari sol dashi, ga wani shu'umin kamshi dake fita sako da lungu na jikinta, sumbatar tafin hannu yai, ba tare da ya sake shi ba ya dago da reddish eyes dinshi akan fuskarta"yaron marayane bashi da kowa, Owais ne ke kula da su, zan nemi alfarmar yabar min shi mu tafi canada atare, inaso ya maye min gurbin abunda narasa" sai yanzu ta fahimci damuwarshi.


Tausayinshi ne ya kamata, tuntuni tasan yana da burin samun ɗa Namiji, yaso ta ƙara haifa mashi ƴa'ƴa sai dai shiru babu alamun zasu sake samun ƙaruwa, kuma lafiyarta ƙalau saboda shi yasa bata yin tsarin Iyali, Allah ne bai nufa zata ƙara haihuwar ba.


  Kafin ta buɗe baki tayi mashi magana, wayarsa dake ajiye cikin aljihun shi ta soma yin ringing, ya riga da yasan wanene Ya kirashi.

  Da sauri Ya saki hannun Gimbiyarsa, Ya zura hannu ya zaro wayar picking call din yai tare da karata a kunnanshi, gimbiya mujeedat ta kura mashi ido tana kallon shi

  "Alhamdulillah, Allah ya kawo ku lafiya," iya abun da taji ya furta kenan, zame wayar yai daga kunnanshi yana dubanta yace"sun sauka lafiya"

Gimbiya mujeedat tace'shiyasa naga farin ciki akan fuskarka, sheik imam yaƙaraso kenan, bari nayi magana da masu aiki su shirya maku breakfast dinku"

Ta fada tana kokarin daukar phone dake ajiye on nightstand da sauri ya ruƙo hannunta, ta dago da ido suka kalli juna

 "An shirya mashi breakfast dinshi, tun acikin jirgi, ina da tabbacin babu yunwa ko gajiya atare da shi, nafi buƙatar idan ya ƙaraso mu tafi gidan Owais din"

 "Amma kaifa? Baka ci komai ba, Yakamata kayi breakfast dinka, zaka fi samun kuzari"

Girgiza mata kai yai"Bana buƙata, saboda bani da natsuwar cin abinci, Idan har yaron nan bai dawo dai dai ba, nafi son idan Ya samu sauƙi, muci abincin atare da shi" 

Tsantsar mamakin kalamansa ne ya daure mata kai, bata ta6a ganin ƙauna kalar wannan ba, Ko a shirin film.


 "Amma kasan bana iya yin breakfast ba atare dakai ba, idan har baka ci ba, nima bazan ci komai ba, har sai  ka dawo gidan" cikin tausasa harshe tayi maganar.


"Yau kawai, Kiyi hakuri kiyi breakfast tare da su Yazrin, bazan jima ba, in sha Allah atare zamu yi lunch dinmu"


 Kwa6e mashi fuska tayi hadi da marairaice mashi tamkar zatayi mashi shagwa6a ta furta"bazan takura maka ba, Na kar6i uzurinka"


"Ki tashi ki shirya inaso ku gaisa da shekh imam kafin mu wuce gidan owais" amsa mashi tayi da toh, kafin ta sauko daga saman gadon, shima ya miƙe yana bin bayanta da kallo, har ta 6ace ma ganinsa, jim kadan ta fito sanye da Abaya launin Maroon tayi rolling mayafi akanta, ruƙo hannunta yai acikin nashi, suka nufi kofar fita daga dakin.

 Lokacin da suka shigo babban katafaren palourn gidan, masu yi masu hidimane suke ta gudanar da aikace aikacen su, kowan nan su sanye da uniform baƙin wando da farar shirt, matasan ƴan mata, duk inda Suka gifta jiki na 6ari suke gaishe dasu cikin girmamawa, yayin da su kuma suke amsa masu da fara'a.


  Yanke shawarar zuwa bedrooms din Ƴa'ƴan su suka Yi, kafin ƙarasowar Ya sheikh, Yana da buƙatar suma su kasance cikin shiri donsu yi mashi kyakkyawar tarba.


     elevator suka hau ta daukesu zuwa upstairs, bayan ta sauke su suka fito batare da sun saki hannayensu da suka ruƙe acikin na juna ba, kaitsaye suka nufi bedroom din ƴan matan su.

 


Gaba ɗaya ta tattara hankalinta akan Apple laptop din dake agabanta, yayin da take zaune a tsakiyar katafaren gadonta dake acikin hamshaƙin ɗakin kwananta daya gaji da haɗuwa, ko dakin sarauniya Albarka, farace sol kamanninta sak dana Mahaifinta Hateem, yadda kasan ta macen aljanna saboda kyanta da dirinta, kamanninta sun 6aci dana Hateem, tamkar yayi kakinta, Hasken fatarta ne kadai ta dauko na mom mujeedat da doguwar sumar kanta, mace ce mai aji, mai ji da ƙasaita da izza, bakowa bace wannan face NAZLI, itace first born dinsu, a ƙalla zata kai shekara ashirin da takwas a duniya, tana asanye da  lace Camisole daga sama ta ɗaura silk robe launin hot pink,  a tsanake take operating laptop dinta cikin ƙwarewa, yayin da kyawawan idanuwanta dake a manne da farin glass suke akan screen din laptop nata, daga gefen gadon ƙayataccen round table ne daga saman shi china tea set ne, jefi jefi takan kai hannu ta dauki cup ta kur6i coffee din dake aciki, Nazli agogo sarkin aiki bata gajiya tana da hazaƙa da ƙwarewa a 6angaren Iya kasuwanci, Company guda take juyawa na mahaifinsu dake a ƙasar Canada, ƙamshin turaren jikinta ya buɗe ko'ina na room dinta, hatta sumar kanta kamshin turaren data turara ma gashinta ne ke fita, kullum ne sai ta turara jikinta da gashin kanta, Nazli badai tsafta ba.


"Assalamu alaikum" Muryoyinsu ne suka janyo hankalinta ga duban ƙofar shigowa room dinta dake a kulle, daga inda take tana Iya hangen su ta cikin kofar, saukowa tayi daga saman gadon, sumar kanta ta rufe bayanta tamkar hijabi tayi mata, daura idonta tayi akan cashmere slippers dinta dake ajiye saman lallausan carpet, ta zura su cikin kafarta, kafin ta nufi kofar cikin takun izza, ta sanya hannu biyu ta ruko handle din kofar ta buɗe ta.

  Fuskokinsu dauke da murmushi suke kallonta, sai dai ita babu alamun murmushi akan fuskarta, haka take bata da fara'a, taji dadin ganinsu amma bazaka Iya gane hakan ta yanayinta ba saboda tsabar ji da izzarta,

  Cikin harshen turanci tace


"Good morning, Mom and Dad! I'm so glad to see you, yau kun riga ni zuwa room dina, yanzu nake koƙarin kammala aikin da nakeyi a laptop...." 

  

Ta ƙare maganar tare da matsawa ta rungume daddynta, hannu biyu ya daura saman bayanta"barka da safiya daughter, Ina fata kin tashi cikin koshin lafiya" 


  Muryarta ƙasa ƙasa ta amsa mashi da cewa"


"I'm doing well, Dad. I've been thinking about you since yesterday. I've missed you."


 Gimbiya mujeedat tace"oh shi kaɗai ki ka gani shiyasa kika rungume shi ko? Da zolaya tayi maganar.


 Ɗagowa Nazli tayi tare da miƙa hannu zata rungume mujeedat, da sauri gimbiya mujeedat taja da baya tana fadin"nayi fushi, ba tun yauba na lura kinfi ji da daddynki, shiyasa nima nafi ji da Yazrin daboda tafi nuna damuwa akaina"


 Marairaice mata fuska Nazli tayi haɗi da kama kunnanta"agafarce ni sanyin idaniyata, mahaifiyata abun alfaharina"

 Sakin fuska mujeedat tayi"nayi hakuri amma kada ki ƙara yi min hakan, Daga yau ni zaki fara hugging kafin daddynki" ta faɗa tana kallon Hateem dake kallonsu, fuskarshi dauke da murmushi yace"na fahimci kishi kike yi dani akan Nazli, Yarinya tafi son ubanta, da ni da ita ƙaunace mai ƙarfi, baki ga kamannin fuskarmu ba? Shiyasa take ji dani, ke kuma kije da Yazrin itace take kama dake"


 Farfari tayi mashi da ido batare datace komai ba, ta rungumo nazli ajikinta tana ɗan bubbuga bayanta da hannu tace"sannu agogo sarkin aiki, tun da sassafe ko breakfast bakiyi ba kin fara danna laptop, Ina fata na same ki lafiya"?

 Ɗagowa tayi da kanta tana fadin"Ina lafiya mommy, bana so aiki yai min yawa shiyasa nake ragewa" ta fada tana dubansu.


"Naji dadin ganinku, duk da ni yakama naje na sameku, ban samu damar yin hakan ba,"


Prime minister yace"bakomai daughter, muma munji dadin ganinki, Inaso ki shirya Zanyi baƙo Ƴan mintuna suka rage su ƙaraso, daga sudan zaizo, gaisawa zakuyi da shi,"

 Batare da ta tambaye shi wanene zaizo ba tace"in sha Allah daddy, yanzu zan sauko down"


 Amsa mata yai da toh, kafin ya dubi mujeedat, muje ko" ya runƙo hannunta suka juyawa zuwa dakin Yazrin,


A lokacin Yazrin tana daga kwance cikin bathtub dake a bathroom dinta, ta jiƙe jikinta da ruwan kumfa mai ɗumi, ta lumshe idanuwanta yayin da take shaƙar ƙamshin bath soft dinta daya karaɗe toilet din tamkar an fesa turare, A kalla zata kai shekaru ashirin da biyar, Yazrin ƙarshe ce afagen haduwa bata baro komai na mahaifiyarta mujeedat ba, launin fatartane kadai kalar na hateem, haskenta bai kai na mujeedat ba, daga ita har Yazrin babu wanda yafi wani kyau, ta inda suka banbanta Yazrin tafi Nazli sauƙin Kai da iya mu'amala da mutane, Ita Nazli bata son bare, ƙiwuya gareta kamar ƙaramar yarinya ga ji da izza, magana ma wuyar furtata take ji.


    Sautin ƙarar door belt ne ya katse mata jin daɗinta, A hanzarce ta ɗaure jikinta da ruwan dumi, kafin ta fito ta ruƙo towel dake sagale jikin hanger ta ɗaure qugunta da shi, 

  Shigowa Bedroom din tayi da sauri ta nufi wardrobe dinta, shaf shaf ta zura jallabiya a jikinta, ko tsane jikinta bata samu damar yi ba, sumar kanta duk ta nannaɗe saman kafadunta.


  Buɗe kofar ɗakin tayi fuskarta dauke da kayataccen murmushi, dimples dinta biyu sun lotsa


 Su kansu da sukayi tozali da ita saida suka saki fara'a, Yarinyar akwai shiga rai, da wuya kaga fuskarta adaure, kafin su bude baki suyi mata magana ta ware hannayenta biyu ta hadasu ta rungume tana fadin"Mom dad, tunkafin nazo gaishe ku kun riga ni zuwa, kunsa naji nauyin hada ido daku" 


  Ta faɗa tare da ɗagowa da kanta tana faman kare fuskarta da tafin hannunta

 Dariya kowan nan su yasaki, Prime minister yace"barka da safiya daughter, fatan mun same ki lafiya"? Jinjina mashi kai tayi"lafiyalou daddy, amma ni baku kyauta min ba, maimakon ku bari ni in fara zuwa gaishe daku" ta fada tana bubbuga ƙafafuwanta da shagwa6a.


 "Ladar da nake kwaɗayin samu, Kun rigani kwashe ta" dariya mujeedat tasaki tana fadin"Wato ke har yanzu baki girma da shagwa6a ba" 


Hateem yace"barta tayi abunta, don bata da ƙanine shiyasa take yi mana shagwa6a" 


 Nuna kanta tayi da yatsanta"saboda nice auta mommy, dagani babu ƙari, kunga kuwa dole nayi shagwa6a" ta fada tana ruƙe masu qugu,

 Ba ƙaramin nishaɗi take basu ba, Hateem yace"baki fada mana ya kika wayi gari ba," 


 "Na tashi lafiya daddy, tun safe nasha coffe, yanzu haka wanka nakeyi a toilet naji ƙarar knocking dinku shiyasa na fito"


"Kina nufin baki ƙarasa wankan ba"? Acewar mujeeda.

 Yazrin tace"tun ɗazu fa na kammala, kawai inajin daɗin kwanciya acikin ruwane"


  "Okey, Ki koma ciki ki shirya muna jiranku a downstairs, daddynku ne zai yi bako daga kasar sudan, yanaso ku gaisa dashine" 


 Yazrin tace"okey mom, bari na shiga ciki in shirya"


Ta fada tare da kallon Daddynta, harta buɗe baki zatayi mashi magana, sautin ƙarar dirar motocin dake shigowa gidan nasu ya katse mata hanzarinta, muryarta tamkar tame yin raɗa ta furta"bakon ya karaso kenan, bari nayi sauri naje na sanya kayan mutunci" ta juya da sauri ta shige cikin dakin

Murmushi kowan nan su yasaki, mujeedat tace"yazrin kenan, tana bani nishaɗi, sai dai narasa gane halin wa ta dauko atsakanin nida kai"

 Nuna ta yai da yatsa"ke mana, har sai an fadi, ni dai kin san ba haka nake ba, idan kika dubi ɗabi'un Nazli sak kalar nawane"

 Hararar zolaya ta yi mashi"nazli fa hada izza ta sarauta ke ɗawainiya da ita, kai ina kaga sarauta? Nice na gajeta, sai dai ta 6angaren siyasa nan kafi karfi, kuma shi ɗan siyasa da fara'a aka sanshi, hakan na nufin halinkane yazrin ta dauko bani ba" 


 "Gorin sarauta zaki yi min"? Ya faɗa yana kanne mata ido.


 Tana dariya tace"ni dai bance ba, ai kafi ƙarfin ayi maka gori, dani dakai babban gorone magogin ƙarfe"


 Ta fada tare da ruƙo hannun shi"muje kada su jimu shiru, ina tunanin sune suka ƙaraso" atare suka nufi down stair.


Adai dai lokacin zungureriyar motar da ta ɗauko Sheikh imam daga airport, ta karaso bakin entry hall nagidan Prime minister a hankali tayi parking, gaba da bayanta motocin sojoji ne da suka dauko shi domin bashi tsaro, fitowa sukayi daga cikin motocinsu, wani ƙato daga cikinsu ya buɗe mashi murfin mota, A hankali sheikh Imam malik Ya zuro kafarsa ta dama dake asanye cikin takalma na alfarma, kafin Ya ƙarasa fitowa, masha Allah, magadan annabawa, kallon ɗaya zakayi mashi ka shaida maluntakarsa, yayi shiga ta alfarma shiga ta larabawan saudi arebiya, farar throbe ce, daga sama ya daura wata shara sharar riga, kanshi yana asanye da kufi ƴar karamar hula ta malamai, an nannaɗeta da black turban, Yana da godon gemu, babban mutunne ya manyata don harya fara tsufa gashin gemunshi hada furfura ta manyantaka,  duhun fatarsa mai kyau ne, kai daga ganin shi baida wasa irin malaman nan ne masu zafi akan addini, babu tsoro a idanuwanshi, mutunne mai cikar kamala, ya shahara a 6angaren wa'anzartawa da yin da'awa ta addinin musulunci, yayi gwagwarmaya a kasashe daban daban babu inda bai shiga, kuma yana cin nasara akan da'awarsa, shaidanun aljanu kansu tsoronshi suke Ji, Suna jin shakkar zama a inda shekh imam malik yake, mutunne shi mai koyi da sunna ta manzon Allah SAW, Ya ruƙe Allah ɗaya azuciyarshi, kainuwane shi dashen Allah, badai mutun ba sai Allah, ta ko'ina jikinshi ƙamshin turarensa ne mai dadin shaƙa a hanci, hannun shi na dama ruƙe da cazbaha.


  A hankali Yake bin ko'ina da kallo, Yayin da yake shaƙar kamshin iskar data gauraya da ƙamshin turarensa.


"Ya mu'allim, mu ƙarasa shiga ciki," ɗaya daga cikin Sojojin ne yai mashi magana haɗi da nuna mashi kofar shiga babban falon, ɗaga kafarshi yai atsanake yake yin tafiya, suna gab da zasu shiga falon, Prime minister ya fito tare da gimbiya majeedat, Murmushin dake kan fuskokinsu ne ya ƙara faɗaɗa, da sauri hateem Ya mika mashi hannu suka gaisa cikin girmamawa"Marhaban bika babana,  barka da sauka, ya gajiyar tafiya" ya fada tare da rungumeshi, bayan sun raba jikinsu daga na juna Sheikh imam yace"ai ni babu gajiya atare dani, ni da aka gatantani kamar wani basarake haka aka daukoni a privet jet, hankali akwance naci na koshi na cika tumbina" Ya fada yana nuna tumbinshi da cazbahar hannunshi, gaba daya suka sanya dariya gwanin ban sha'awa, sheikh imam mutunne mai son barkwanci amma fa sai idan yaso.


  Prime minister yace"Akara makallah ai kafi karfin basarake awurinmu, ku fa magadan annabawane, kunfi duk wani mai muƙami a karkashin tafin kafarku Yake"


 Murmushi Shekh imam Yasaki, Tare da daura idanuwanshi kan fuskar Gimbiya mujeedat, kafin yayi magana tayi saurin gaishe shi cikin harshen larabci.


 Da zolaya yace"Hateem dama ana ganin fuskar matarka? Ya akai yau baka rufe lu'u lu'un ka ba"? Koba ita bace matar nan da ake yi mana 6oyanta ba? Kodai Ƴarce"? Kunyace ta rufe gimbiya mujeedat, Ta sanya hannu ɗaya ta kare fuskarta

 Hatta jami'an dake a kewaye da Ya shekh Imam saida suka saki murmushi .


 Dariya prime minister yasaki a fakaice ya harari Jami'an dake atsaitsaye suna kallonsu, jiki na 6ari suka juya kowa yakama gabanshi, don sun fahimci me yake nufi, wato suna kalle mashi matarshi.


  "Ya sheikh Mu ƙarasa cikin falon, mun barka atsaye gashi ka kwaso gajiya" prime minister ya fada tare da ruƙo hannun shi, Suka nufi babban falon Gidan, Gimbiya mujeedat tana abiye da su.


  "Hateem Irin wannan daula haka? Anya kuwa kuna tunawa da mutuwa? Ka ajiye lu'u lu'u agidanka ga kuma kayan alatu ta ko'ina, maimakon ku bari sai mun shiga Aljana muji daɗi" Ya faɗa yana Jijjiga cazbahar hannunshi, Dariya suka sanya gaba dayansu, A saman Royal sofa kowan nan su Ya zauna, suna fuskantar juna da sheikh imam, sai faman jinjina kai yake yi yana bin gidan da kallo, duk maganar da sheikh imam zaiyi yanayin amfani da harshen turanci saboda mujeedat yasan bata jin hausa sai dai turanci da larabci.


  "Yanzu kai hateem, Har kake iya kwana acikin daular nan? Wannan haɗuwa haka ai sai mutun ya manta da tur6aya aka halicce shi"

  Murmushi suka saki suna dubanshi

 Sautin takun takalman Yazrin da Nazli ne Ya janyo hankulansu ga dubansu, 

  Hannunsu ruƙe cikin na juna suke yin tafiya suna tunkarosu, kowaccensu ta yafa mayafi akanta,

 Bayan sun ƙaraso, Cikin girmamawa suka gaishe da shekh Imam, Abunda Ya burgeshi da yaran tarbiyarsu, A saman lallausan carpet din dake a atsakankanin Royal  sofa din suka zauna kowaccensu ta nade kafafuwanta

 "Masha Allah, Matan hurul aini har a duniya, Hateem, wacce zaka bani acikinsu in cike sunnah"? Ya faɗa yana duban faces din Yazrin da Nazli, Yazrin sai famam sakar mashi murmushi take Yi, Nazli kuwa tunda ta gaishe dashi ta sunnar da kanta ƙasa.

   "Duk wadda ka za6a malam, zamu baka Ita" acewar mujeedat,

   Shekh imam yace"Uwargida maganarnan taki bata kai zuci ba, ni nasan kin faɗine kawai, taya zaku ba yarinya auran dattijo? Mai jan cazba, balle ƴan matan zamani basu son auran malamai"

 Murmushi kowannansu yasaki, banda Nazli.

Biyu daga cikin masu aikin gidanne suka nufo falon, hannunsu ruƙe da faɗaɗan farantai daga sama an jera drinks masu sanyi da snacks.

    Tunkafin su karaso sheikh imam yace"waɗannan fa? Badai ni zasu kawo mawa ba? Bayan abincin da naci acikin jirgi har wani ƙari za'ayi min? A'a gaskiya Ni a koshe nake, Ko ruwa bana jin zai Iya wucewa ta makoshi na"

  Prime minister yace"babana adai daure ko ruwan ne kasha,"

Gyaɗa kai yai toh, naji iya ruwan zansha, Asaman carpet suka daura farantan, mai aikince ta zuba mashi Apple juice mai sanyi a cup ta miƙa mashi, Yasa hannu ya kar6a, Kur6a uku yai ya dawo da dubanshi gasu Nazli"ƴan matan hateem ina fata na same ku lafiya? Ya karatu? Ko da yake nasan kun kammala, to Ya aiki"

 Atare suka amsa mashi da cewa"lafiyalou Alhamdulillah," jinjina kanshi yai"Masha Allah," bayan ya ajiye cup din alamar ya kammala sha, Prime minister hateem Yace"nasan yanzu ka kwaso gajiya, ko zamu bari zuwa anjima idan ka huta sai mu fara shiga gida ku gaisa da baba kafin mu wuce can gidan Owais din inda Yaron yake"?

 Girgiza kai sheikh imam yai"A'a, tun da mahaifin naku baisan da zuwana ba, to ba yanzu zanje gaishe shi ba, nafi buƙatar ganin yaron, don agaskiya ni babu gajiya atare dani, ka tashi mu tafi kawai,"

  Kallon mujeedat Hateem yai"zamu tafi, in sha Allah bazamu daɗe ba, a taya mu da addu'a" murmushi tasakar mashi"ubangiji Allah yasa ayi asa'a, Ina yi maku fatan alkhairi" amsa mata yai da ameen, kafin ya maida dubanshi gasu Nazli da Yazrin"daughters ku tayamu da addu'a, ga mommynku nan zatayi maku bayanin komai dangane da zuwa sheikh imam" amsa mashi sukayi datoh, kafin ya ɗago Ya kalli Ya sheik wanda tuni Ya miƙe tsaye, miƙewa hateem yai atare suka nufi kofar fita falon, tunkafin su ƙarasa Jami'en dake atsaye bakin motar data dauko sheikh daga Airport Yai saurin bude masu motar, Bayan sun shiga daga ciki, jami'en Ya zauna a driver's seat Ya tashi motar, atsanake Yake yin driving dinsu........


*Chief Owais✊❤*


Tun bayan daya dawo daga masallaci, Yin sallar asuba bacci ya addabi idanuwanshi, adaddafe ya shiga bathroom yai wanka, within minutes ya fito waist dinshi ɗaure da white towel, kan mirror chair ya zauna da niyar ya kimtsa kanshi, sai dai yakasa tabuka komai saboda kasalar data kame sassan jikin shi, idan har ba baccin nan yai ba to kuwa bazai ta6a samun sukuni ba, kyawawan idanuwanshi sunyi mashi nauyi daƙyar yake iya buɗe su, miƙewa yai bai nufi ko'ina ba sai saman katafaren gadonshi, Ya haye ya kwanta tare da jan bargo ya lullu6e rabin jikinsa, In a short time bacci yai awon gaba da shi.


Tsawon awanni yanata sharar baccinsa, tun karfe shida har goma da rabi ta buga, Yayin da numfashinshi ke fita cikin natsuwa da kwanciyar hankali, phone dinsa dake ajiye gaban dressing mirror ta soma yin ringing, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa, ringin din ya fara takura mashi, mutsu mutsun farkawa daga bacci ya somayi, A hankali Ya ware fararen idanuwanshi dake fuskantar ceillin din dakin nashi

 Tsawon minutes, kafin Ya laluba hannunshi Cikin kasala Ya ruƙo wayar ya duba sunan me kiranshi, sunan Uncle Hateem ne Ya bayyana akan screen din wayar, 

 Kiran harya kusa katsewa yai saurin yin picking, tare da manna wayar akan kunnansa

  "My son, Ina fata ban takura maka ba"

Yamutsa fuskarshi yadan kafin ya furta"Barka da safiya uncle, fatan ka tashi lafiya"?

 "Lafiyalou, naji muryarka da alamun bacci bai isheka ba"

  "Kiran wayarka ne Ya tashi ni daga bacci, Ina fata lafiya"

 "Banji dadiba amma kayi hakuri da takura makan da nayi, ni kaina bansan dililin dayasa na damu da yaron ba"

 "Ba damuwa uncle"

"Yanzu haka da nakeyi maka magana Muna akan hanyar zuwa Gidan naka tare da sheikh imam"

Lumshe ido owais yai har cikin ranshi yaji dadin jin zuwan Sheikh imam

 "Ina yi mashi barka da zuwa, Allah ya kawo ku lafiya" Hateem Ya amsa mashi da amen mun gode son," daga haka sukayi sallama da juna.

  Daura wayar yai saman side drawer ya sauko daga saman gadon Ya nufi dressing room din dakin shi, badajimawa ba ya fito sanye da jallabiya launin sky blue, tayi bala'en yi mashi kyau, Gaban dressing mirror din dakin ya tsaya tare dakai hannu cikin jerin turarurrukansa ɗaya bayan ɗaya yake dauka yana feshe jikinshi, tuni ƙamshinshi ya karaɗe dakin.

    Diamond wrist watch din shi dake ajiye gaban mirror ya dauko Ya zura a hannunsa, Kafin Ya miƙa hannu Ya dauki Phone dinsa, A tsanake Yake pressing dinta, Layin Boss Ya danna ma Kira, Bugu Uku Yai picking, gaisawa suka farayi kafin Ya furta"Sheikh Imam Ya ƙaraso, Ina buƙatar ganin kowannanku a main falo, domin mu tarbesa"

 

  Boss Ya amsa mashi da Toh, In sha Allah, Yanzu zan sanar da su" daga haka Yai rejecting kiran.

     

A dai dai lokacin, Unaisah ta kuma farkawa daga baccin da yayi awon gaba dasu ita da giant snake din, Cikin sanɗa ta sauko daga saman gadon, tana tafiya tana waiwayon gadon, ta kudundune shi da bargo, ta ƙagu da son ganin ƴan uwanta shiyasa zata fita taje gare su, batasan a wani hali suka kwana ba.

    Bayan ta fito daga dakin down ta sauko, Moving quickly ta nufi Hanyar da zata hau bene taje dakin ummi, Har ta kusa haurawa saman staircases  miryar boss man ta katse ta"Unaisah"! Cak ta tsaya haɗi da waiwayowa tana dubanshi, 

 "Ina zakije ne"?

 Muryarta adisashe ta furta"dakin aunty ummi, Inason ganinsu batul ne, ai ka fadamin acan suka kwana"

 "Hakane, Nima dakinta zani je, amma tunda gaki bari in baki sako ki kai mata" ya fada tare da zura hannu cikin aljihu ya curo maganin mura ya miƙa mata.


  "Wanene bai da lafiya"? Hankalinta atashe ta fada tana bin maganin da kallo.


 "Ummi ce ke bata jin dadi, mura ce ta kamata" Ajiyar zuciya Angel ta sauke tayi tunanin ko cikin ƴan uwanta wani ke bai da lafiya.


 Kar6ar maganin tayi, har zata juya muryarshi ta dakatar da ita"Sheikh imam yana akan hanyar zuwa gidan nan, malamin da zai duba ɗan uwanku danish" Waro ido waje tayi lokaci ɗaya ta fashe da dariyar farin ciki, Murmushi yasaki Dama ya fada matane don ya faranta mata rai.

 Idanuwanta cike tab da ƙwalla take fadin"Alhamdulillah, wayyo Allah wallahi naji dadi, fatana Allah yasa ayi asa'a danish ɗina yaji sauƙi ya dawo kamar kowa"


 Boss yace"in sha Allah zamuyi nasara, yanzu kije ki kai mata maganin, idan kin fito ki same mu a falo,

   Amsa mashi tayi da toh, jiki na rawa ta nufi benan ta haye sama, burinta takai mata maganin sannan ta kwantar masu azeeza hankalinsu kafin ta dawo falon don taga sheikh imam"


 Abakin ƙofar dakin Ummi ta dakata tare dakai hannu ta dafi glass door din A hankali kofar ta buɗe, Zura kafarta keda wuya sukayi kicibus da batul, sam hankalinta ba akwance yake ba, ganin ummi ta shiga toilet tsawon lokaci bata fitowa ba shiyasa ta yi dabarar guduwa daga dakin don ba ƙaramin takura tayi ba, baiwar Allah suna haɗa ido da Unaisah, ta faɗa jikinta, Hannu biyu ta ƙanƙameta dasu kamar zata koma cikinta, tun daga kan yadda ta rungumeta ranta ya bata cewar babu lafiya, A hankali  itama ta zagayo da hannayenta saman bayan Batul.


  "Meke damunki sister? Baki da lafiyane"? Ta fada batare data raba jikinsu daga na juna ba

 Muryar batul ashaƙe da mura ta furta"babu komai, Mu tafi dakinmu, Ni kadaice na rage su azeeza sun tafi tun ɗazu, Ni ko sallar asuba banyi ba"

 Hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yai ba, Jin muryar Batul ashaƙe kamar an ɗaure mata makoshi, A hanzarce ta raba jikinsu, ido cikon ido suke kallon juna, ta ɗanyi mamakin ganin kayan dake ajikinta masu kyan gaske.

  Aruɗe ta furta"batul! Dama kece baki da lafiya ba aunty ummi ba? Garin yaya mura tayi maki mugun kamu"?

  Shiru batul tayi mata batare data furta komai ba, saboda tana jin tsoron ummi taji ta fada ma wani.

  Da sauri ta canza akalar maganar tasu"Meke damunki? Naga fuskarki ta kumbura idanuwanki sun yi ja, ko kema baki lafiya"?

 "Ni lafiyata qalou, damuce ta hana ni yin bacci..." bata ƙare maganar ba batul ta kuma cewa

 "Ina danish dinmu"?

"Inaso zanyi maku bayanin komai amma sai mun koma ɗaki, Yanzu ki fada min ya akai mura ta kama ki? Ina kuma aunty ummi"?

 Murya ƙasa ƙasa Batul tace"nima bansan ya akai ta kamani ba, aunty ummi kuma tana a toilet, itace ma ta kira awaya don akawo min magani, kuma kinga ta bani kaya na sanya" tayi maganar tana nuna mata kayan sanyin jikinta.

  Ajiyar zuciya Unaisah ta sauke" mun haɗu da boss man shine ya bani maganin mura in kawo, ni nama yi tsammanin aunty ummice ba lafiya kamar yadda ya fadamin ashe kece"

 Jinjina mata kai batul tayi"Allah ya baki lafiya sisterna, kayan jikinki sunyi maki kyau, a ina aunty ummi ta samu kayan nan dai dai size dinki kamar donke aka dinka su"?


 "Nima bansani ba, Mu tafi daki" atakure tayi maganar, tare da ruko hannun Angel, tajata suka nufi down stairs.*sanarwa, bazan samu  damar yin posting monday Ba, zanyi tafiya fatan za'ayi min uziri, in sha Allah da zarar na dawo za'a cigaba daga inda aka tsaya, game bukatar cigaba da karanta prisoners 500 ne zaku tura ta bank acct dina, ga ta inda za'a tuntu6eni 08103884440*
3196407426


Bature Hafsat Muhammad

First bank 

Idan kin tura zaki bada hoton receipt amatsayin shaida🤗

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post