Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 24

Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 24

 


BossLadiesWriters



           💋KURKUKUN ƘADDARA💋



Middle step


          سجن القدر❤🤍❤



              THE PRISONERS E24🔥💫




Daga alƙalamin Boss Bature




Confusion of the heart💫



lokacin da ta ware idanuwanta akan screen din wayar wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta ganin fuskarta, hotonta ne tun tana ƴar shekara goma sha ɗaya a duniya, tsabar farin ciki Ya hanata rufe baki, hada hawayenta saboda farin cikin ganin hotonta ne yaya shureim yake kallo, bata kawo komai aranta ba saboda ta yarda da shi.


   Ɗagowa tayi idonta acikin nashi ta furta"yaya shureim dama hotona kake kallo"? Ɗaga mata gira yai alamar eh, ta kuma cewa"yaya shureim wannan ai tsohon hotona ne a ina ka same shi"


 Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"nima tsohuwar ajiyace a cikin memory dina, saboda inason hoton bana so na rasa shi, bama shi kaɗai ba akwai sauran hotunanki a gallery ɗin wayar zaki Iya dubawa ki gani" 


Yatsun hannunta na kerma ta bubbuɗe sauran hotunan tana kallonsu hada wanda tun tana jaririya akayi mata shi, abunda ya ɗaure mata kai gaba daya gallery na wayarsa hoton mutun biyune acikinsa daga hotonta saina ƙanwarshi benazir.


  "Yaya shureim tun yaushe kake kallon hotuna na"? ta faɗa da mamaki akan fuskarta.


  Muryarshi ƙasa ƙasa tamkar tame yin raɗa ya furta mata"tun lokacin dana fahimci kece ƙaddarata" wurga mashi blue eye balls dinta tayi akan face dinsa.


 "Ƙaddararka? Kamar yaya kenan"? Cikin rashin fahimtar kalaman shi ta ambaci hakan.


    "Lokaci zai ƙure mana zeenatu, ki bari idan muka dawo gida zan fahimtar dake abunda nake nufi" amsa mashi tayi da toh, haɗi da miƙa mashi wayarshi Ya sanya hannu ya kar6a, ya turata a aljhu, har cikin ranshi ba ƙaramin daɗi yaji ba, ganin bata kawo komai aranta ba, Duk da ya 6oye mata ainihin hoton da yake kallo.


  "Allah sarki aunty benazir, nayi missing dinta Yaya shureim, tsawon lokaci babu ita, Allah dai yasa aganta da ranta da lafiyarta" cikin sanyin murya zeenatu ta yi maganar, ya amsa mata da ameen.


   Yana ƙoƙarin tada motar, ba zato ba tsammani yaji zeenatu ta kwantar da kanta saman kafaɗarshi, wata irin kasalace ta soma baibaye shi sakamakon ƙamshin turarenta dake kashe mashi jiki.


  A hankali motarsu ta miƙi Hanyar babban gate din gidan, Gate security officers ɗin dake tsaron gidan suna ganin motarshi gaba ɗaya suka yunƙuro suka nufo motarsu, hannunsu ruƙe da jibga jibgan bindigu, ba arziƙi dr. shureim Yaci burki, Jin ya dakata da yin driving din yasa zeenatu ɗago da kanta daga saman kafadarshi ta dube shi.


  "Yaya shureim meyasa ka dakata da yin driving din"


 "Masu tsaron gidan nan ne suke tunkaro mota ta," ya bata amsa a takaice.


   Dafe kai tayi da hannu ɗaya"Namanta ban faɗa ma daddy ba, Ni nasan daƙyar zasu bari mu fita, idan har bai basu umarnin su ƙyale mu ba, gashi baya agidan, Mommy ma har yanzu bata dawo daga office ba" ta faɗa tana faman zare ido.


"Yaya shureim ka kira daddy awaya ka sanar dashi" a tsoroce take yi masa maganar don ita kanta mugun jin shakkar masu tsaron gidan nasu take ji, ƙirar jikinsu kaɗai abun tsoratarwa ne, sannan basa wasa da aikinsu, gashi babu annurin akan fuskokinsu.


  Kafin dr shureim Ya zaro wayarshi tuni sun cimma masu, ƙawanya su ka yi mata motarshi.


 Ɗaya daga cikin su ne yai knocking glass motar, da kakkausar murya yake ya ce "wanene acikin motar? Muna baka umarnin ka zuge glass din motar ka"


 zeenatu ce ta sauke glass din, Ya zuƙunno Yana dubansu A tsanake miryarta na rawa tace"yanzu zai kira daddy awaya, yayana ne shureim zamu fita yawo ne"


Security guard ɗin yace"oh, meyasa baki faɗa mashi ba'a fita dake waje ba tare da iznin daddyn ki ba"?


  Still muryarta arude ta furta"ai mantawa nayi ban fada mashi ba" jinjina kai mutumin yai"okey, Muna jiran umarninsa" 


  Kusan Sau uku dr shureim yana jaraba kiran layin Alhaji musa bai ɗaga ba, zeenatu tace dashi"ka jaraba kiran Layin mommy, idan tayi masu magana zasu barmu mu fita" kiran Layin Hajiya sarah yayi ringing biyu ta ɗaga, bayan sun gaisa ya sanar da ita halin da suke aciki, tace dashi yaba ma Security guard din waya suyi magana da shi.


 Miƙa masu wayar yai, bayan sun kar6a ya dubi zeenatu, yayi mamakin ganin zufa na wanke fuskarta duk da sanyin A.c na motarshi, ya fahimci tsoron su take ji.


 "Ki kwantar da hankalinki zeenatu kina atare dani"


 cikin sanyin murya ya ambaci hakan, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"yaya shuriem ni bana son tashin hankali, duk laifin daddyne ni banga amfanin ajiye waɗannan ƙattan ba acikin gidanmu, ai Allah ne ke tsare bawansa bawai mutun ba" da shagwa6a ta ƙare maganar, ruƙo hannunta yai acikin nashi, da sauri ta mayar da kanta saman kafaɗarshi tare da lumshe idanuwanta tana faman sauke ajiyar zuciya.


  Miƙo mashi wayar Security guard ɗin yai"an baku iznin fita, amma bisa sharaɗin zaku koma mazaunin baya na motar, Ni zanyi driving dinku duk inda zaku je" zeenatu tamkar zata fashe da kuka tsabar jin takaicin jin abunda Security guard din ya fadi.


 Dr shureim yace "ba damuwa mun gode da kulawa," ya faɗa yana buɗe murfin motar, fitowa su ka yi daga front seat suka koma back seat na motar suka zauna," security guard din ya shiga ciki Ya zauna a driver's seat, Ya tada motar Ya fuce dasu daga cikin gidan lokacin da suka haura saman titi, security guard din ya tambaye su ina zasu je ne, zeenatu ce ta zayyana mashi wuraren shaƙatawar da zasu je, kafin dawowarsu gida sai da suka mori lokacinsu, kamar karsu dawo gida. 



EX-PRISONERS❤


After two days (bayan kwana biyu)


Idan muka koma 6angaren prisoners sai dai muce Alhamdulillah, domin kuwa tafiya ta kankama, tun bayan da sojoji suka ƙulla yarjejeniya da ummin america, A ranar wuraren ƙarfe shidda na marece, sojojin suka zo kawo masu ziyara domin duba lafiyarsu, a ɗakin hutawar dr Laura, suka tattarasu gaba ɗayansu, sunyi matuƙar jin daɗin ganin Yaran sun samu sauƙi musamman Danish da suka barshi Yana ta faman sharar bacci, dama sun ƙwallafa rai akan son ganin ya farka, duk da bai sakar masu fuska ba sai da suka ja shi ajiki, kafin tafiyar sojojin sai da dr laura ta nemi izni akan tana so abata dama ta ɗauki Yaran zuwa gidanta na tsawon kwana uku, saboda tana so gobe zata kai su saloon agyara masu jikinsu da sumar kansu, sannan tana so zata siya masu suturar da zasu sanya, sojojin basu amince da buƙatarta ba, saboda chief na Isod Ya hana a fita da yaran ko'ina, yace kada a kuskura a fitarsu daga asibiti sai Airport idan zasu tafi, Sun bata haƙuri akan ƙin amincewa da buƙatarta sun kuma nuna mata illar yin hakan tun da su Yaran suna hasashen cutar da su akayi kuma dole asamu masu bibiyarsu, ba dan taso ba ta haƙura, sai dai kamar yarda tace zata siya masu suturar sanyawa tayi ƙoƙarin yin hakan duk da Commender yace kada ta wahalar da kanta, Chief na isod Ya ɗauki ɗawainiyar yaran duk wani abu da zasu buƙata a duniyar nan shi zaiyi masu, dr laura tace taji amma dole ta siya masu wani abun da zasu dinga tunawa da ita akai akai, commender yace mata ba damuwa, bayan tafiyar sojojin, tsabar farin Ciki awurin Angel kamar zata zuba ruwa ƙasa tasha, dr laura ce ta faɗa masu komai dangane da tafiyarsu Nigeria, da kuma damƙa case ɗinsu a hannun Chief of Isod, daren ranar da aka faɗa masu ko bacci bata yi ba, kwana tayi tana yin Nafilfili, har sai da idanuwanta suka kumbura saboda hawayen dake fita acikinsu, ƙafafuwanta suka fara yi mata zogin azaba, tukunna ta dakata dayin sallar asaman prayer mat bacci ya ɗauke ta.


  Tsawon kwana Biyu Kacal, a tsakani Shugaban Isod, Ya shigo birnin San Antonio Texas, Ya kama Yau kenan Monday, Kuma A yau din zasu Bar America, Da zarar ya fito daga meeting din da suka shiga ahead quarter tare da Chief of army staff, da commender da sauran sojojin dake da alhaki akan Tsintar Yaran A daji, tattaunawa ce ta musamman da zata dauki tsawon awa nni suna Yinta.


UNAISERH ANGEL💋


Mutuniyar tun da ta farka, bakinta awashe kamar wadda akayima Albishir da gidan Aljanna, sai faman zarya take Yi a ɗakin ta kasa zama, jefi jefi ta kan wurga eye balls dinta kan wall clock dake a ɗakin don ganin lokaci idan yana tafiya, ta ƙosa su kammala meeting din azo a ɗauke su, don ita a takure take da zama america.


Ta zuba hannayenta biyu acikin aljihun wandonta, bakomai take tunawa ba face Aunty Aneelerh da daddynta, ta sanyawa ranta cewa idan suka koma Nigeria, zata ganshi a gidansu.


   Zame hannayenta tayi daga cikin aljihun wandonta, ta goya su saman ƙirjinta, abun nayine.


   "Masoyiya Angel," muryar dr Laura ce ta fargar da ita ga kallonta, har batasan lokacin da ta furta"Sun gama meeting din"? Fuskar dr Laura dauke da murmushi ta ƙaraso ciki, hannunta ruƙe da ƙatuwar shopping bag.


     A gefen gado ta ɗaura jakar kayan, tare da miƙa hannu ta rungumo Angel a jikinta.


  "Zanyi missing dinki masoyiya Angel, sai dai na lura kamar ke ba za kiyi kewata ba ko"? Ta fada tana raba jikinta daga na Angel.


  Duƙar dakai Angel tayi cikin jin kunyarta tace"Idan nace bazan yi missing dinki ba, Nayi ƙarya, ba ma ke kaɗai ba, duka nurses da likitocin da suka taimaka mana wurin samun lafiyarmu, zamuyi kewarku sosai"


  Shafa gefen fuskarta dr. laura tayi da tafin hannunta.


 Cikin karyayyar murya ta furta"masoyiya Angel, saura mintuna ƙalilan suka rage maku a asibitin nan, Ƴan uwanki duk sun shirya cikin sabbin Kayan da na Siya masu, Kema ga naki nan" ta faɗa tana nuna mata jakar kayan data ajiye mata saman mattress.


  "Sannan akwai Waya dana siya maki, na yi maki Saving phone number dina tare dana Dr brown dana dr mark, da duk numbers na nurses da suka kula da ku, idan kin sanya layi akan wayar ki kira mu pls" Daƙyar ta karasa maganar, idanuwanta sun cicciko tab da ƙwalla, Jikin Angel duk yai sanyi, zuciyarta ta karaya.


   Cikin murya tamkar tame Yin raɗa, dr laura taci gaba da cewa"Abu ɗaya da ban faɗa maku ba, dama na yanke shawarar Sai mun ke6e dake in sanar da ke, saboda Na yaba da hankalin ki da kuma kaifin basirarki da wayon ki,' Angel ta natsu tana sauraronta.


  "Matar da sojoji suka damƙa amanarku a hannunta, Mistress ce," kai tsaye sunan Ya daki dodon kunnan Angel, cikin rashin fahimtar ma'anar hakan ta maimaita kalmar mistress.


   Jinjina kai Dr Laura Tayi"tantiriyar ƴar bariki ce mai zaman kanta, shaidaniyace a fagen iya karuwanci, ta shahara sosai, babu wanda baisanta ba, tayi ƙaurin suna a America, maca ce mai haɗarin gaske, Namiji baya Iya ganinta Ya kawar da idonshi, saboda kyawun surar dake gareta, Nayi ƙoƙarin Fahimtar da sojojin Akan illar damƙa amanarku a hannunta amma sunƙi su amince min Angel, ni nasan da wuya ta Iya baku kulawar daya ce, in ma bata gur6ata maku rayuwarku ba, Musamman Ƴan uwanki maza........" Hankalin Angel Ba ƙaramin tashi yai ba,   duk da Sanyin A.c na ɗakin zufa ce ke tsastsafo mata saman goshinta, idanuwanta azazzare take kallon fuskar dr Laura dake kora mata jawabi.


  "Ni damuwata depression din dake damunku, da kuma ɗan uwanku mai fama da ciwon zuciya, idan har aka cigaba da ƙuntata maku zaku Iya rasa rayukanku, shiyasa banso suka damƙa amanarku a hannun karuwa ba, donni a sanina da matar masifaffiyace tana da girman kai, bata ta6a yin aure ba, kuma bata san ciwon haihuwa ba, abunda ta sani shine ƙwacewa matan aure mazajensu tayi fasiƙanci da su, matar ta zama tamkar annoba, ta raba aure da dama saboda hatsabibancinta" dakatawa tayi da yin jawabin idonta akan Angel, tsantsar tashin hankali take gani acikin ƙwayar idonta, Jikin Ta ƙaura Yai la'asar, An gudu ba'a tsira ba.


  Muryarta Na rawa ta furta"Aunty, amma meyasa suka damƙa amanar mu a hannunta? Babu wata ne sai ita? Kuma ai mu bamu buƙatar wadda zata kula damu, idan ma akwai abunda zamu buƙata bai wuce jami'an da su bamu tsaro ba...." bata ƙarasa maganar ba dr laura ta katse ta da cewa"dalilin dayasa suka damƙa amanarku a hannun ummin america, kamar yarda major ya sanar dani, matar tamkar ma'aikaciyarsu take, ta saba yi masu aiki wurin jan hankalin tantiran ƴan ta'addan da suka gagara a ƙasa, suna yin amfani da ummi wurin ɗana masu tarkon da zasu kamasu, kuma suna cin nasara, Masoyiya Angel ban faɗa maki hakan donna tada maki hankali ba face don ki dage damtse wurin Yin yaƙi da ita akan ƴan uwanki, kada ki kuskura ki bari ta ke6e da ɗaya daga cikin Samarin dake a jikinku, Idan ba haka ba za'a Iya samun matsala, saboda bata da linzami matar, duk da A yanzu ina kyautata mata zo, tun da har sojojin suka aminta da ita suka damƙa mata amanar ku, hakan na nufin sun san zata Iya ne, Bayan haka sun ƙulla yarjejeniya da ita akan baku kula ta musamman da kuma gujewa duk wani abu da zai 6ata maku rai, kamar yarda na gani dai dai da tsawa tayi maku babban laifine, don haka Zan tura maki sharuddan da sojojin suka gindaya mata akanku ta whatsapp, saboda inaso kiyi amfani da su wurin ja mata kunne idan ta sa6a maku," jinjina kai Angel tayi alamar toh ta ƙara da cewa "bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin yi maki godiya, Allah ne kaɗai zai Iya biyanki, saboda kyautatawar da kukayi mana, gashi kun ɗauke mu tamkar ƴaƴan ku, "


 Shafa sumar kanta dr Laura tayi"Kada ki damu yana daga cikin aikin mu!, Yanzu ki shiga kiyi wanka, Mintuna ƙalilan suka rage maku," amsa mata tayi da toh, Bayan fitar dr Laura, Angel ta nufi Jakar Kayan, zuciyarta a hautsine ta girgiza da jin wacece matar da aka damƙa ma amanarsu, ita babban abunda ta ke jima fargaba garkuwarsu, tunawa da lokacin da aka kawo masu unaiza a kurkuku, yarinyar ta ruɗe shi da big boobs dinta, balle kuma matar da taji ance tana tafiya da imanin namiji saboda dirin jikinta, tashin hankalin da ba'a sanya mashi date. (🤣)


 Har ta fara Imagining abun da zai faru, a gidan da zasu zaune atare da ita, tayi tunanin sun samu sauƙine komawarsu Nigeria ashe akwai sauran rina akaba.


  A hankali ta ruko hannun jakar Kayan, ta zaro kayan dake acikinta, wata haɗaɗɗiyar A-line gown ce launin red colour mai round neck ƴar ubansu awurin haɗuwa, Rigar tayi mata kyau a ido, sai faman jujjuyata take yi, aranta tana ayyana yau wata rana zata sanya  kaya na mutunci wanda ba uniform din prison ba, wannan abun farin ciki ne agare ta.


Bayan ta gama kallon rigar, ta ɗaurata saman mattress, ta zaro kwalin takalman dake a cikin jakar tare da kwalin sabuwar wayar da dr laura ta siya mata, ƙirar iphone 15 pro, Takalman kuma Ankle strap ne masu tsini launin black, hada face mask da mayafi aka basu wanda bakowa bane Ya tsara hakan face chief na Isod, Lokacin da dr laura ta bukaci zata siya masu kaya Sai da aka nemi izininshi, yace ya amince bisa sharaɗin idan zasu sanya kayan a haɗa masu da Niƙab ko face mask da zasu rufe fuskokinsu, a ƙalla ta shafe tsawon mintuna biyar tana kallon kayan, bakomai yafi burgeta ba face wayar da aka bata kyauta, tunawa da lokaci yasa tayi saurin nufar toilet ta shige ciki, shaf shaf tayi wanka kafin fitowarta, Nurse jessica ta shigo ɗakin hannunta ruƙe da gift kit ƙaramin akwati na kayan shafa, ta ɗaura shi gefen gadon Angel, ta zauna  saman kujera tana Jiran fiowarta, bayan ta fito daga wankan, suka gaisa da nurse din cikin girmamawa, daga bisani tayi mata bayani game da care kit din data kawo mata donta gyara jikinta, godiya Angel tayi mata bayan ta ɗauki kayan shafar da rigar ta juya ta nufi toilet dasu saboda jin kunyar kada aganta tana sanya kaya, murmushi nurse jessica tayi yayin da take binta da kallo.


Bayan ta shafe ko'ina na jikinta da body oil mai tsadar gaske, skin dinta har glowing take yi, rigar tayi bala'en yi mata kyau, duk da bata da jiki tana da tsawo, white in red abun ba'a magana, lokacin da ta fito daga cikin toilet ɗin, ita kanta nurse din sai santin kyan Angel take Yi, daga saman rigar ta tsuke daga ƙasanta bazace daga ta jujjuya rigar take bubbuɗewa kamar ana hura mata iska, bayan ta kammala shiryawa nurse ta feshe mata jikinta da turaren desired destiny, fragrance din turaren mai daɗin shaƙa a hanci.


    Face mask din da ta sanya black colour ne launin takalmanta, har saman karan hancinta mask din ya haura, Gray eyes dinta ne kaɗai suka Bayyana.


  Ɗaura Mayafin rigar tayi asaman kanta tayi rolling dinsa, gyalen yana da tsayi ba laifi, Har saman gwiwar hannayenta yakai mata, shima launin takalmanta ne.


  "Kin yi kyau masoyiya Angel, sai ki ka yi mini kama da Cinderella saboda rashin ƙibarki," Ƙayataccen murmushine kwance saman fuskarta,


  "Na lura kin ƙosa ki bar ƙasar nan, Ni kuma gashi bana son ki tafi, saboda na saba da ke masoyiya Angel," cikin sanyin murya Nurse jessy tayi maganar tana duban fuskarta.


  "Dr. laura ta bani kyautar waya, kuma ta faɗa min akwai phone numbers din ku aciki, zan dinga kiranku akai akai muna gaisawa saboda ni kaina bana son mu rabu don ya zamar mana dole ne mu tafi" Sai da tayi maganar Nurse jessica ta wurga eye balls dinta kan kwalin wayar, zaro ido ta ɗanyi haɗi da cewa"wow, gaskiya dr. Laura tana Ji da ke shalelenta, wannan waya haka mai kyau da tsada, Ina taya ki murna masoyiya Angel, Kuma naji dadi da ta baki wayar, Kinga zamu dinga kiran juna muna gaisawa, harma muyi video call" fuskarta dauke da matsanancin farin ciki, ta nufi gefen gadon ta ɗauki kwalin wayar a hannunta, tana ƙare mashi kallo, Angel dai sai murmushi take saki, bakinta yaƙi rufuwa kamar ta fasa ihu Haka take ji tsabar murnar yau zasu Bar america zuwa ƙasarta ta gado.


  "Yakamata mu tafi masoyiya Angel, Ƴan uwanki suna Jiranki a waje" cike da ƙagara Angel ta amsa mata da toh, shaf shaf ta zura takalman a ƙafarta masha Allah, wankan Angel yabi jiki.


   A hannu ta ruƙe wayar bayan ta curo ta daga kwalin, atare suka fito daga ɗakin.


   Tun kafin ta ɗago da idonta, Muryar Jemimah ta katse mata hanzarinta"Genie gamu nan ki dube mu da kyau, mun yi kyau" Da sauri ta wurga idonta kansu, masha Allah har saida gabanta Ya faɗi tsabar kiɗima da ganin Kyawun da suka Yi acikin sabbin kayansu, jemimah da azeeza launin gown dinsu Royal blue ne, hannah da parveen launin punch pink, Ita kuma Batul launi ɗayane dana Angel, red colour, kowaccensu akwai Face mask a fuskarta, Anyi masu rolling Veil a saman kawunansu, takalman kafarsu flat ne ba kalar nata ba, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallon mamakin Kyawun da suka Yi, mutun ɗaya ne ke babu a cikinsu, Mazan su huɗune, kowannansu ya kimtsa cikin shiga ta mutunci ta kece raini wato shigar hadaddun Slim fit suit, sun manna mask a fuskokinsu, kwantacciyar sumar kawunansu ta kwanta luf, ƙafafuwansu na sanye cikin tsadaddun takalman fata, ta ko'ina ƙamshin turarensu ne ya karaɗe ward din da suke.


   Ganin tayi tsaye tana kallonsu bata motsa ba, yasa kowan nan su sanya hannu a lokaci ɗaya suka Zame mask din dake a saman fuskokin su, sai faman washe mata baki suke yi, wani irin farin ciki ne Mara misaltuwa ya kamata, tun daga kan yadda suke shaƙar iskar ƴan ci zaka tabbatar da kwanciyar hankali da natsuwa atattare da su, su kansu sun yaba da kyawunsu, sai faman shafa kayan jikinsu suke Kamar zasu lashesu.


  Jemimah ce ta ruƙo hannun Azeeza suka watso da gudu zuwa gabanta, Atare suka fada saman jikinta, Hugging dinta su ka yi suna tiƙar dariyar murna, tuni idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla, ko a mafarki bata ta6a tsammanin zata ga wannan ranar ba, yau gata ga ƴan uwanta cikin shiga ta alfarma ba uniform din kurkuku ƙaddara ba.


  A hankali Batul da sauran ƴan uwan nasu suka nufo wurin Angel, ɗaya bayan daya take rungumo su saman chest dinta, suna matuƙar ƙaunar junansu, nurses da likitocin dake tsaitsaye cirko curko sai kallonsu suke yi gwanin ban sha'awa.


  "Angel, Kinga yadda ki kayi kyau? Rigar nan tayi maki kyau, wlh duk munyi kyau," Batul ce tayi maganar tana shafa gaban rigarta da hannunta.


   "Nayi tunanin abinci kaɗaine abu mafi kyau a duniyar nan, ashe sutura ma abu ne mai ƙayatarwa, gaskiya bazan iya misalta farin cikin da nake a ciki ba, Daɗi Nake ji kamar In buga tsalle sama in dira ƙasa," Parveen ce tayi maganar, sautin dariyarsu yacika ko'ina, kasancewar suna Yin firar cikin harshen hausa babu wanda ya fahimci abunda suke tattaunawa a tsakaninsu, sai dai Abi la66ansu da kallo.


  "Ban ta6a ganin kalar kayan nan ba, Mun saba da Uniform kala daya na prison, Yau sai gashi mun tsinci kanmu acikin sutura mai kyan gaske, godiya ta tabbata ga Allah, domin kuwa shine silar komai, dama kin ta6a fada mana cewa mahaƙurci mawadaci, sannan duk tsanani Yana tare da sauƙi, kuma babu yanayi na rayuwa da yake kasancewa Na dundundun, Yau mun shaida hakan Angel" tun da Haris Ya fara magana Suka natsu suna kallonshi, tamkar ba mara lafiyan nan ba, Jikinshi Yayi kyau ɗan black beauty da shi, Kalamanshi sun tunama Angel deeja, Yarinyar akwai tawakkali duk da bata da zurfin ilmin addinin musulci tayi imani da Allah, fiye da wani musulmin daya taso acikin musulunci, tunawa da deeja ne yasa ƙwallar idonta suka soma gangarowa saman kuncinta, a fakaice ta sanya hannu ta share su, haƙiƙa taji zafin mutuwarsu, ga salsabeel daya tsaya mata aranta, bawan Allah ko awani hali yake ayanzu? Ya rayu ko ya mutu? Allah masani!.


  "Angel, Ina fata Yanzu hankalinki ya kwanta, babu sauran damuwa tun da yau zamu koma Nigeria" Gabriel ne yai mata maganar Haɗi da ɗaga mata gira ɗaya, hakan ba ƙaramin dariya yaso ya bata ba, Javed yace"ni fa duk atakure nake jin kaina, mutanan nan sai kallon mu suke Yi,"


  Naufal Yace"ka gode ma Allah tun da ba Giants din kurkukun ƙaddara bane suke kallon ka," gaba daya suka sanya dariya cikin nishaɗi.


Gabriel yace "kyau suke kallo, wankan da muka ɗauka ne Ya burgesu, mu kanmu mun burge kanmu balle kuma su"

 Hanna tace"Wannan abun da aka sanya mana a fuska yafi komai 6ata min rai, Duk ya toshe mun ƙofofin hancina, wai ba yadda za'ai mu tafi batare da mun sanya shi ba"? Tana faman yamutsa fuska tayi tambayar tana kallon Fuskar Angel.


   Kafin tayi yunƙurin bata amsa Gabriel ya riga ta cewa"saboda tsaro, shiyasa aka bamu shi don mu sanya, sunanshi face mask," Javed Yace"ai na gane shi, kalar wanda tsohuwa zafreen take sanyawa ne" harara parveen ta ɗan jefa mashi"Ni bana so kuna maganar matar nan, na tsaneta kamar mutuwa ta"



  "Ina danish yake ne? Shi bai fito ba ne"? Angel tayi tambayar tana leƙen ƙofar room dinsa.


  Haris yace"Suna can ɗakin shi suna ta fama dashi akan ya sanya kayanshi yaƙiya, kinsan mutumin da taurin kai kamar ƙashin nama, bansan Ya suka ƙare da shi ba, Har lalla6a shi nayi na nuna mashi kayan dake a jikina amma yasa kafiya akan bazai sanya ba"


  Mai hali bazai ta6a canzawa ba, aranta ta ayyana hakan,  Kallon su azeeza tayi"our twins ku sakar min rigata, zanje ɗakin danish"

 Azeeza tace"toh, mu tafi atare zamu biki" Ruƙo hannayensu tayi a cikin nata, suka nufi ɗakin Danish, Su Haris ma suka bi Bayansu, har sun kusa shiga Muryar dr laura ta katse masu hanzarinsu.


 Cikin harshen turanci take yi masu magana "Duk inda na kalla kyawawan ƴan mata ne da samari nake gani, kunyi kyau sosai, Kamar in sace ku" gaba ɗaya suka sanya dariya, Miƙa ma Haris hannu tayi"zonan My baby boy, Ya jikin naka"? Zuwa yai gabanta ta sanya hannu biyu ta rungume shi a ƙirjinta kamar yaron cikinta


  "Allah ya ƙara maka lafiya Haris, zamu yi kewarku sosai, Ku kula mana da kanku, zamu dinga kira akai akai don mu gaisa da ku" cikin karyayyar murya ta ƙare maganar, tare da raba shi daga jikinta, idanuwansu duk sun ciko da ƙwalla.


 Voice dinshi na rawa ya furta"mun gode sosai da kulawarku agare mu, Kune mutune na farko da kuka fara jan mu a jiki kuka bamu kulawa ta musamman, akanku muka fara yarda cewa akwai mutanan kirki a duniya ba duka aka taru aka zama ɗaya ba" murmushi tasakar mashi tare da kai hannu ta shafa sumar kanshi"nayi magana da Angel, Nasan zata baka kulawar daya dace, duk wani abu da kakeso kayi mata magana" amsa mata yai da toh.


 Angel da su jemimah duk suna a tsaye da sauran nurses da doctors dake kallonsu.


  Miƙa ma Su hannu tayi"ku zonan my twins, Inason jin ɗuminku a jikina, gaskiya zanyi kewarku" da sauri jemimah da Azeeza suka isa gareta hannu biyu ta sanya ta rungume su tighly.


  Bayan ta raba jikinta daga nasu ta kalli parveen da zolaya tace "Oh, Ji ra kike saina ce kizo ki rungumeni? Ko dan baki ga abinci a hannu na ba"?


 Tuntsirewa su ka yi da dariya gaba ɗayansu da gudu parveen ta ƙarasa ta rungumeta, shafa kanta dr laura tayi'ki kula mun da kanki, a duk lokacin da kika ji yunwa, kiyi ma Angel magana zata baki abinci, kada ki zauna da yunwa" lumshe ido parveen tayi ji take kamar karsu rabu da juna, don ba ƙaramun so suke Yima matar ba.

 "Pure heart, my beautiful daughter zo ki rungume mommynki" ta faɗa tana kallon Batul, da ɗan sauri ta je gabanta ta faɗa saman chest dinta sosai ta rungumeta.


  "Ki kula mun da kanki, Allah ya tsare mun ku, zanyi kewarku" Batul tace"muma zamuyi kewarku, idan muka samu dama zamu dinga zuwa muna ganin ku,"dr laura tace"kada ki damu basai kunzo ba, muma zamu Iya zuwa dubaku har ƙasar taku" Batul taji dadin kalamanta, ɗaya bayan ɗaya sai da tabisu ta rungumesu tana mai ƙara jaddada masu akan su kula dakan su.


  Lokacin da tazo kan Angel, Har ta miƙa hannu zata rungumota, Ba zato ba tsammani Garkuwa Ya fito daga room dinsa, adai dai lokacin Jami'an Isod sun shigo ward din, Cikin shiga ta black suits, Hannayensu da ƙafafuwansu sanye cikin baƙaƙen safuna, takalman ƙafarsu leather shoes ne fuskokinsu duk sun sanya face mask, ƙirar su bata da banbanci data jami'an kurkukun ƙaddara, Giants ne wani irin faffaɗan kirjine dasu, na ban mamaki, suna tafiya cikin taku na ƙasaita, kai daga ganinsu zaka shaida ƙarfin da suke dashi damtsen hannunsu tamkar zai fasa rigar jikinsu a murmurɗe suke, azafafe suke yin takunsu tamkar zakuna, Suna tafiya tsokokin jikinsu na motsawa da ƙaƙƙarfan kuzari na majiya ƙarfi. 

 

  Lokaci ɗaya ward din Yai tsit tamkar mutuwa ta gifta, bakomai ne Ya jawo hakan ba face fitowar Danish daga room dinsa, tare da dr brown da dr. Mark jackson, Tabarakallahu ahsanul khalikin, ko a mafarki basu ta6a yin tozali da mutumin da sutura ta raina kanta a jikinsa ba irin Danish !


Wankan daya ɗauka na slim fit suit dinsa sunyi bala'en yi mashi kyau, ya fito a garkuwarsa, Garzon namiji mai jini ajika, sannan kuma mai ji da kyau da ƙarfi, haɗaɗdar sumar kanshi dark brown curly sun gyara mashi ita, sunyi cutting dinta sun ɗaure mashi ita, ta sauko saman dogon wuyan shi, takalman ƙafarsa leather shoe ne launin black suit dinsa.


 Fuskarshi tamkar anyi mashi make up tsabar haɗuwa, ga wani irin zazzafan ƙamshin turare dake kurɗaɗowa saƙo da lungu na jikinsa kamar wanda aka tsamo daga cikin kogon turare, Agogon hannunsa silver ce sai ɗaukar ido take Yi, wani abu da zai baka mamaki duk irin haɗuwar da yai acikin kayan babu annuri akan fuskarshi ko misƙala zarratin Ya haɗe rai kamar wanda aka ɗaura ma aure da mutuwa, Yana tafiya a bubbuɗe kamar wanda zai Yi dambe, Kyawun surar danish yayi matuƙar tafiya da Imanin Nurses din dake a kewaye da wurin da likitoci, all eyes on him ba matan ba mazan ba, kowa kallonshi yake yi kamar zasu haɗiye shi, kai hatta Jami'an isod sai da gabansu ya faɗi sunyi matuƙar girgiza da ganin shi, har dai wani daga cikin su ya gaza jurewa muryarshi ƙasa ƙasa cikin harshen turanci Ya furta"Nayi tsammanin daga Chief din mu angama halittar Namiji mai kyan fuska da sura, ashe ba haka bane nayi kuskure, a yau naci karo da namijin duniya kamar garzonmu OWAIS, wannan Yaron Bai da mararraba da shi, banbancinsu Launin fata" 


 

💋ABBAN SOJOJI💋

💋KURKUKUN ƘADDARA💋


Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da kuma kurkukun ƙaddara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440  whatsapp din ya samu matsala, ga wadda za'a same ni da ita (08134387050) ayi mini magana ta whatsapp, message from Boss Bature


 ✍ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin




First bank




3196407426, 




Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post