Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 25

Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 25


 BossLadiesWriters           💋KURKUKUN ƘADDARA💋Middle step  


          سجن القدر❤🤍❤              THE PRISONERS E25🔥💫
Daga alƙalamin Boss Bature
Confusion of the heart💫  Jami'in dake gefen wanda yai maganar ne ya daura da cewa"Ni kaina na girgiza da ganin matashin saurayin nan, Gaba ɗaya ma na rikice, na tabbata ko shi Boss Owais din Yai arba da wannan Yaron sai yayi mamakin  shi.


Amenity Ward Ya ruɗe da sambatun mutane akan kyawun Garkuwa, shi ko Dan tahalikin Duk yabi ya rikice A rayuwarshi ya tsani kallo saboda Yana affecting din natsuwarsa, Yana Hayaƙa shi, idanuwanshi sun makance neman Angel Yake yi, Gata akusa dashi amma ya kasa ganewa, sai ƴan  waige waige yake yi a ƙoƙarinsa naya gano ta, An rasa me Iya buɗe baki yayi mashi magana acikin ƴan uwan nashi, baisan cewa shine ya ruɗe su ba, Ya canza masu sosai cikin sabuwar shigarshi.


      Sai da Haris Ya ɗaga murya Ya furta"Danish gamu anan" tukunna ya wurga reddish eye balls dinsa akan fuskokinsu, cikin takun sauri Ya nufe su yana ƙarasawa ba yi ƙasa a gwiwa ba Ya rungume Angel a saman broad chest dinsa, Ya cusa fuskarshi saman kafaɗarta Yana faman sauke ajiyar zuciya, lumshe idanuwanta tayi lokacin da ƙamshin turarensa Ya daki hancinta, gaba ɗaya taji ta a wata duniya tacan sama jannati, in a throaty voice ya furta mata"bana son kallo, Ki faɗa masu su daina kallo na, suna cutar dani"


  Sam takasa yin magana, saboda yayi tighting dinta a kirjinshi, ya zagayo da arms dinsa saman bayanta, mutanan dake awurin sai faman sakin murmushi suke yi kamar zautattu, bakomai ne ya burgesu ba face hugging din da Danish yai ma Angel, sunyi tamkar ma'aurata, kayan jikinsu sun yi fitting dinsu black and red, kamar furanni.


  Gyaran Murya ɗaya daga cikin Jami'an isod Yai masu, muryarshi a bubbuɗe ya furta"Zamu Iya tafiya, amma kafin nan Shi wannan Yaron Ina face mask dinsa Yake"? Ya yi tambayar Yana nuna Danish da indext finger.


  Da sauri Dr Mark, ya tura hannu cikin front pocket din coat dinsa, Ya zaro face mask, Ya nufi Danish, yana fadin


  "Handsome man, namanta ban sanya maka mask dinka ba, Kar6i ka sanya" kamar yayi magana da gunki, Ko motsi Baiyi ba, tunda ya ƙanƙame Angel dinsa yayi shiru kamar maiyin bacci.


  Numfasawa dr laura tayi sai lokacin ta samu damar buɗe baki tace"Danish yana yi maka magana, kaga sauran ƴan uwanka duk sun sanya nasu face mask din, Kaima ya kamata ka kar6a ka sanya, jami'an isod suna jiran ku zasu ɗauke ku zuwa Airport ne" Lamarin Ya ɗaure masu kai, Babu alamun zai motsa, Ga Angel tana so ta raba jikinta daga nashi don ta lallashe shi, yaƙi bari tayi hakan saboda matsetan da yayi a chest dinsa, hatta numfashinta daƙyar take Iya fitar dashi"  Cikin ƙagara Haris Yace"dan Allah Danish ka sake ta, Ka kar6i abun fuskar kai ma ka sanya ko mun samu mu tafi" 


Magiya suka dinga yi mashi akan ya saki Angel Amma Yaƙiya ko kallo basu ishe shi ba"


  Ɗaya daga Cikin Jami'an Isod Ne yai nazari akan Yaron, kasancewar suna da kaifin basira, nan take Ya fahimci wani abu dangane da shi, ɗaya bayan ɗaya ya kalli nurses din dake a ward din da likitocin da suka tsaya suna kallon su, Muryarshi a kausashe Ya furta"Idan ba damuwa kowa Ya koma bakin aikinsa"! 


 Jin hakan yasa kowan nan su Juyawa suna tafiya suna waiwayon prisoners, Mutun Biyar ne suka rage, dr laura da mark da brown sai nurse jessica da nurse rebecca.


  Tun kafin Jami'in Ya tambayi lafiya su basu tafi ba? Dr laura tace"Muna so muyi masu rakiya har zuwa airport, nasan suma Yaran zasu so hakan" 


Jinjina kai yai tare da ɗaura eye balls dinsa kan Bayan Danish.


   "Danish, likitocin da suka duba lafiyar ku ne su ka rage sai kuma mu jam'an da muka zo domin tafiya da ku, babu kowa bayan mu, muna jiranka please kada ka 6ata mana lokaci"! Cikin kwantar da murya yai mashi magana.


 Sai da Ya ambaci hakan tukunna daƙyar Ya raba jikinshi daga na Angel, numfashinta da sauri sauri Yake fita, hada tarinta saboda mugun shaƙar da tayima turarensa ya sarƙeta.


  Dr mark ne Ya sanya mashi mask din saman fuskarshi, da zolaya jami'in yace"ka tabbatar ka rufe mashi hada idonshi, don wannan idan mutane suna kallon shi tsab zai haɗa mana traffic jam a saman titi" 


Gaba ɗayan su suka sanya dariya, ban da Danish, sam babu kwanciyar hankali atattare da shi, Hakanan Yake jin haushin mutane babu gaira babu dalili, ji yake kamar ya rufe su da bugu har sai sun mutu. Su Batul kuwa duk sun sha jinin jikin su, ganin Jami'an Isod suke Yi tamkar mutanan prison, tun da suka shigo ko motsin kirki sun gaza yi, Sai faman binsu da ido suke yi, ko magana jami'an su ka yi sai sun razana babu wanda Ya lura da hakan. Bayan Dr. mark ya kammala sanya mashi mask din, ya juya ya ruƙo hannun Angel acikin nashi, a jere suka nufi Hanyar fita daga ward din Yayin da dr laura da mark da brown suke Abayansu, su kuma jami'in Isod suna a kewaye da su, domin basu tsaro, duk inda suka gifta a sibitin ido na akansu, ba marasa lafiyan ba, ba ƴan zuwa dubiyan ba, ba Ma'aikatan cikinsu ba, kowa hankalin shi na akan su, Danish sai ƙara matse mata hannunta yake yi a cikin nashi, hankalin ta ba akwance ya ke ba don ta fahimci akwai wani abu dake damun shi.  Kaitsaye suka nufi parking space na asibitin, wasu danƙara danƙaran motoci ne masu numfashi jigunannun gaske, a killace a harabar, da su akazo ɗaukarsu, hankalin su Batul Ba ƙaramin tashi yai ba, Basu ta6a ganin abu irin wannan ba, Motocin dake a killace aharabar suke ta faman bi da ido, Angel ce tayi amfani da harshen hausa wurin yi masu magana akan su natsu kada su tsorata, abun hawa ne da akeyin anfani dasu wurin tafiya mai tsayi wadda ƙafa bazata Iya yinta ba, sai da tayi masu bayani cikin kwantar da murya tukunna suka fara sakin jikinsu.


  Kafin su shiga motar sai da aka fara sanya kayan su a boot, akwatuna ne  da duffle bags kusan guda biyar, Suturar da dr laura ta siya masu ce, tare da Takalmansu da magungunan da zasu dinga sha, da sauran care product da zasu yi amfani da su. Bayan an kammala shigar da kayan cikin motocin ɗaya bayan ɗaya jami'an suka bude masu car doors din, motar farko Danish ne da Angel sai Batul suka zauna a mazaunin Baya, Mota ta biyu Gabriel ne tare da Haris da Hanna, Mota ta uku Naufal ne da parveen sai Javed.


Dr. laura ta nemi alfarmar jami'an akan tana son su bata damar ɗaukar jemimah da Azeeza a motarta, Jami'an suka ce mata zata Iya ɗaukarsu ba wani abu, A back seat na motarta, Azeeza da Jemimah suka shiga, Ita kuma ta zauna A driver seat domin Yin driving dinsu, Dr mark da dr bown suma hada su za a tafi kaisu airpot din, A cikin motocinsu zasu tafi tare da Nurse jessica da rebecca.


  Tun da prisoners suka shiga cikin mota, suke ta ƴan kalle kalle wa yaga baƙauye yazo birni, duk sun sha jinin jikinsu, Fargaba suke Yi kada a cutar dasu, badan Angel ta kwantar masu da hankalinsu ba, da kuwa Anga hauka, kusan A lokaci ɗaya masu tuƙa motocin suka tada su, Jemimah ta rungume Azeeza jin sautin tashin motarsu, Jikin su ya hau yin kerma kamar waɗanda sanyi ya kama, Dr laura dake kallonsu ta madubin motar, fuskarta ɗauke da murmushi ganin yadda suka ƙanƙame tace masu su kwantar da hankalin su, babu abunda zai same su.


    A motar su Parveen Ta ƙanƙame naufal saboda tsoron da taji, hada javed sun haɗu sun mannewa juna kamar kifayen gwangwani.


A motar su Gabriel kuwa, Hannah da Haris sun ƙanƙame shi, sai faman tiƙar dariya yake yi, shi dama wayayye ne bakomai ne Ya manta na memory dinsa ba, Hannayen shi biyu ya sanya saman bayansu Ya ƙara tighting dinsu ajikinshi yana kwantar masu da hankalinsu.


Danish kuwa tun da suka shiga motar, ya kwantar da kanshi saman kafaɗar Angel, ko motsi baiyi, Yana zaunea left hand dinta, yayin da Batul take a zaune saman seat din dake a right hand dinta, Ganin yadda Batul ta ruɗe jin tashin mota, Hannayenta biyu ta ɗaura saman kanta, kamar zata fasa ihu da sauri Angel ta damƙo hannunta tare kwantar mata da kanta saman laps dinta, ƙanƙameta tayi sosai tana faman sauke ajiyar zuciya, abun ne yazo masu wani iri basu saba ba.


 Slowly motocin suka nufi hanyar babban gate din asibitin, gaba da bayansu motocin Jami'an isod ne, Sun sanya motocin da aka ɗauko su dana su dr. laura a tsakiyar nasu motocin domin basu tsaro.  Da matsakaicin gudu motocin suka haura saman titi, prisoners sun ga abunda yafi ƙarfin idanuwansu, Ta glass din window su ke Hangen danƙara danƙara gine ginen birnin san antoni, masu ƙayatarwa, ga wuraren shaƙawata da kuma mutanan dake zarya ta ko'ina, sun natsu suna kallon ikon Allah abun ya ɗaure masu kai.


 "My man, bacci zaka yi"? angel ce tayi mashi magana tana duban fuskarshi, tayi mamakin ganin zufa na tsastsafo mashi saman forehead dinsa, duk da sanyayyan Sanyin A.c na motar, Batool tuni ta miƙe daga saman laps din Angel, ta koma bakin windown motar tana kallon Ikon Allah.

  In a low voice ya furta mata"Am not feeling well, ina jin wani iri a jikina kamar wani abu zai faru dani" shafa sumar kanshi tayi da hannunta"In sha Allah ba abunda zai faru da kai My Man, Ina atare dakai, so ka kwantar da hankalin ka, bari nayi maka addu'a" ta faɗa haɗi da manna la66anta saman lallausar sumar kanshi, addu'o'i ta soma karantowa tana tottafa mashi asaman kanshi.


 Muryar Batul ce ta katse mata hanzarinta"Angel wai su mutanan duniya dama haka suke da gudu kamar zasu tashi sama"?

  Dariya ce ta kubcewa Angel, ta wurga idonta kan batul data mannewa glass din tagar motar, ta ƙura ido tana kallon al'amurra.


  "Batul ba mutane bane suke Yin gudu, Abun hawan da muka hau ne ya ke yin gudu damu"


  Ba tare da batul ta juyo ta kalle ta ba tace"Oh, yanzu na fahimta" daga haka bata ƙara cewa komai ba.UMMIN AMERICA💋


A hankali motar su take tafiya saman shantalelen titi, tana a zaune saman front seat, ta ɗauki wankan pant suit sunyi bala'en yi mata kyau, dogon wandone fari da sexy vest fara ta matse ta kirjinta Ya fito sosai, don ma ta ɗaura Blue coat daga sama, ta canza launin sumar kanta zuwa blue, light make up ne asaman face dinta , fararen idanuwanta suna a manne da farin glass hakan ba ƙaramin ƙara mata kyau ba, Matar dake driving dinta, ƙawarta ce NATASHA baturiyar England, Aminnan junane, sai dai daga ganinta babu digon imani a zuciyarta, fitsararrace ta bugawa a jariga. Kayan dake a jikinta da su da babu duk ɗayane, doguwar rigarta tamkar net take shara shara kana Iya hangen inners din ta, A yayin da take zaune saman driver's seat, Cigrette ce a hannunta na hagu, ɗayan hannun kuma da shi take juya sitiyarin motar daga gani ta ƙware a iya driving, Tsabar Iya shan taba harta hanci ta baki take huro hayakinta.

 

fira suke ɗan ta6awa a tsakaninsu cikin harshen turanci.


  "Zanyi kewarki ummi, yanzu idan kika tafi yaushe zaki dawo? Natasha ce ta jefa mata tambayar.


 Numfasawa tayi kafin calmy ta furta "bazan daɗe ba, temporary guardianship ne ba permanent ba, da zarar na kammala yi masu aiki zan dawo America"


 Dariyar shaƙiyanci Natasha ta saki, tana mai cigaba da hura hayakin tabarta.


 "idan ki ka yi wata ɗaya baki dawo ba, zan biyoki Nigeria don bazan Iya jure rashin ki ba" ta fada tana duban fuskar Ummi. 


  "Zaki tafi ki barni da mutananki, don nasan ba zasu ƙyaleni ba, da zarar sunji ki shiru ni zasu tuntu6a," Ummi tace"Zaifi ki canza layin wayar ki, kafin in dawo, don bana so kowa yasan da zancen barina ƙasar nan ko kuma inda zanje, Yana daga cikin sharuɗɗan da sojoji suka gindaya mini."


  "Ai nayi mamaki da kika amince zaki kar6i jagorancin kula da yara har goma sha ɗaya, idan nice bazan Iya ba, kema nasan ba hakanan kika kar6i aikin ba. akwai wata manufa a ƙasa" ta ƙare maganar tana dariya.


 Ummi tace"kamar kin shiga zuciyata, tabbas inaso naje Nigeria ne don karan kaina bawai don aikin da sojoji suka bani ba, nima akwai abun da zai kai ni, da ba don haka babu abun da zai sa in bar America.


 Natasha tace"yayi kyau mutuniyata, ina fata zaki cigaba da sheƙe ayarki, bana so silar zuwan ki ƙasarki ki shiryu nafison ki ƙara lalacewa ki 6ata masu mazajen auransu," dariya suka sanya gaba ɗayansu.


 Ummi tace"Yaran fa da aka bani in jagoranta kyawawane fa akwai wani zazzafan Yaro acikinsu, yana da kyawun sura" lumshe ido natasha tayi muryarta tamkar ta mashayin giya tace"kice yaron babbar harka ne, tun kafin ma in ganshi na ƙyasa"


  Ummi na dariya tace"yadda kike shaiɗaniyar nan nayi imanin idan kika ganshi daƙyar zaki Iya runtsawa, kallon shi kaɗai zai tada maki da maitarki, Natasha nayi mu'amala da maza kala daban daban amma shi wannan Yaron na musamman ne, Kamar dai Chief Owais, kinsan shima Yana da zazzafar sura.


 Natasha tace"Har yau ban daina kallon hotonshi ba saboda bana gajiya, aduk lokacin dana rasa abokin harka hoton shi nake kallo in rage zafi, gayen ya haɗu duniyace shi" cikin jin shauƙi Tayi maganar"


Ta ƙara da cewa"ƙawata zan baki shawara, matasan Yaran da za'a baki rainon su, kada ki raga masu, idan jarabarki ta motsa kibiya buƙatarki da su, ai ke wannan Aikin da sojoji suka baki gaba ta kai ki, in banda abunsu sun ta6a ganin inda aka ba kura ajiyar nama"? Da shaƙiyanci ta faɗa tana sakin shu'umin murmushi na tantiran ƴan duniya.


 Ummi ta ɗan zaro ido haɗi da cewa"ba zai yiwu ba natasha, ke kin san wanene Chief owais, yafi bomb bala'i, akan shi na fara jin tsoron namiji a duniyar nan, Mutumin bai da fara'a Yana  da kamun kai, sannan bai da imani idan ya damƙi Mara gaskiya, idan har na kuskura na ƙetare Iyakata akan Yaran wlh tsaf zai Iya kasheni har lahira, ni ko dai ban shirya mutuwa ba, akwai sauran bururrukan da nakeson cimmawa.


  Fashewa Natasha tayi da dariya fararen haƙoranta a jere kamar gonar auduga, sam firar su bata ɗauke mata hankali ga yin driving din da take Yi ba, har ta zuƙe tabar hannun ta duka.


 "Dole kiyi mini dariya ƴar rainin wayau" ta fada tana hararar ta.


 Tsagaitawa Natasha tayi da yin dariyar ta dubi fuskar Ummin america"mutuniyata, Kina ta zumuɗin zuwa Nigeria, banji kina maganar mutumin ki ba" cikin rashin fahimtar kalamanta ta furta"Wa? Kashe mata ido ɗaya Natasha tayi"Boss Man, ko kina nufin har kin manta da shi? ta faɗa tana duban hanya.


Yamutsa fuska Ummin america tayi"Allah ya raba ni da alaƙaƙai, bana fata wani abu ya ƙara hada ni dashi, jarababbe kawai"


 Natasha na dariya tace"haba ummi, mutumin fa ya mutu akan ƙaunarki,  nayi ƙoƙarin ganin na maye gurbinki acikin zuciyarshi sai dai Ya nuna mun cewa ke kaɗai ce za ki Iya sarrafa shi yadda ki ke so, kuma yana nan akan bakansa na cewa ba zai ta6a barinki ba har abada ke tashi ce"


  Mood din fuskarta ne ya canza zuwa 6acin rai.

 "Natasha, I don't even want to hear his name, bawai don bana son shi ba, kawai ni bana son mutumin da zai nuna ƙarfin iko akaina, kamar wani ubana, yaushe rabona da shi tun lokacin dana ɗauki cikinsa na zubar ba tare da saninshi ba, muka samu sa6ani dashi ban ƙara ganin ƙeyarsa ba, Kin san fa mutumin akwai zuciya ga girman kai, nasan zai neme ni ne tun da baya gajiya dani"


 Natasha tace"kina wasa da damarki ummi, da Ace nice na samu matsayin da kika samu acikin zuciyarshi, bana tunanin zan iya bijire mashi, biyayya zanyi mashi sau da ƙafa""


  Ta6e baki ummi tayi"nima ba gudunshi nake yi ba, Ciki ke bana so, saboda zai 6ata min shape din jikina, kuma ni tun kafin mu ƙulla alaƙa dashi sai da na faɗa mashi sharuɗɗana, nace mashi bana ra'ayin yin aure kuma bana son ciki, ban damuwa ba idan zamu shekara munayin sharholiyarmu da shi in dai zaiyi min biyayya"


  Murmushin gefe fuska Natasha tasaki"Ummi kenan, Yanzu mu ajiye zacenshi a gefe, ni dai shawarar da zan baki shine idan kika koma ƙasarku, kada ki kuskura ki kula ƙasƙantattun mutanan da su ka yi silar barin ki Nigeria, bana so ki nuna kin san su, inaso ki nuna masu cewa kwandon shara yafi su mahimmanci a awurin ki"


 Maganar Natasha ta ta6a zuciyarta ummi, tuni ta ɗaure fuskarta, tunawa da wani abu da ya faru a rayuwarta.


 "Please, stop talking about them, i don't wanna hear it" rai a6ace ta furta hakan, jinjina kai Natasha tayi"shikenan nadaina mutuniyar saboda bana son 6acin ranki" mood din fuskar Ummi Ya canza sosai, abubuwan da suka faru arayuwarta take tariyowa, masu daɗi da marasa daɗi.


  "Mutum biyu masu mahimmanci arayuwata, ina fata na sake haɗuwa da su, Yarinyar dana bari inason na ganta duk da bani da tabbacin tana araye ko ta mutu, ba dan bana son ta ba, na tafi na barta, tun tana jaririya, shi kaɗai ne danasanin da zanyi arayuwata"


 A cikin zuciyarta ta furta hakan ba tare da sautin muryarta ya fita ba, tuni idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla. Afakaice ta zaro hanky daga hand bag dinta ta share ƙwallar idonta.


  Sun jima suna tattaunawa da ƙawarta Natasha, A lokaci ɗaya motar su, da motocin jami'an da suka ɗauko su Angel suka ƙaraso katafaren Airport din, slowly Ummi ta zuge glass din motar don ta samu damar ƙare ma Yaran kallo ita da Natasha, kafin fitowarsu daga mota, suka soma Jin jiniyar motar sojoji, kusan guda uku suka nufi wurin da sukayi parking din nasu motocin, bayan sunyi parking din motocinsu, Commender ya fito daga motarshi, tare da Major da captain da sauran sojojin da su ka zo da su. kowan nan su yana sanye cikin kakinsa, ga dukkan alamu sunzo Yi masu bankwana ne.


Jami'in dake tuƙa motarsu Angel ne ya fito da sauri Ya zagaya Ya buɗe masu kofa, Angel ce ta fito hannunta ruƙe dana Danish, duk da face mask din dake akan fuskokinsu hakan bai 6oye tsantsar kyawun idanuwansu ba, Hankalin Natasha ba ƙaramin tashi yai ba lokacin da idanuwanta su ka yi tozli da kyakkyawar surar Danish, tun kan ummi ta faɗa mata wanene shi tayi saurin cewa"kamar Yaron da kika faɗa min ko"? Ummi na murmushin shaƙiyanci tace"may be shine, ai ni fuskar shi na gani a hoto, naga wannan ya sanya face mask, amma dai ina da tabbacin shi ɗin ne, masha Allah ƙaramin mutum da babbar harka, Ni ma ban ta6a ganin shi ido da ido ba sai yau, Nayi tsammanin jin shi yafi ganinshi, ashe ganin shi yafi jinshi," lashe baki Natasha tayi da harshenta kamar wata mayya tace"Ya tafi da imanina, Ya za'ai ummi? Anya bazan biyo ku Nigeria ba? Kinga ke sai ki dinga rainon su ni kuma Ina biyan buƙatata da su"


Ummi tace"bismillah zaki Iya bin mu amma ki sani komai ya faru dake kada ki nemi ni, Chief owais sai yayi jajjagen namanki, idan kika ta6a mashi ƴa'ƴanshi"


 Har ta ƙarasa maganar, Natasha batasan me take cewa ba, idonta akan Danish, Bayan fitowarshi da Angel, Batul ta fito, Sauran Jami'an suka fito tare da bubbuɗe masu motocin. Gabriel ya fito tare da Haris da hannah, Naufal ya fito da parveen da javeed, dr laura ta fito daga motarta, ta bude masu Azeeza, suka fito suma, Nurses din dake atare da su da dr mark da brown kowan nan su Ya fito waje. Prisoners sun baza ido suna kallon inda suke, tun kafin su shiga cikin Airport din.


Ummi America da natasha sun tsaresu da ido

  "Yaran Fa akwai kyau, Yanzu ummi har kina Iya zama wuri ɗaya dasu ba tare da kin rage zafi ba"? Shiru ummi tayi mata ba tare data tanka mata ba, hankalinta na akan prisoners, ta ƙura masu ido, hakanan ta dinga jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, ba tare da sanin dalilin daya haifar mata da hakan ba, jikinta yai wani irin sanyi, ɗaya bayan ɗaya take bin su da kallo, yayin da suke gaisawa da sojojin cikin raha suke amsa masu.


 Sai daga bisani Ummin America ta buɗe murfin motarsu, atare suka fito ita da Natasha, Hankalin su Angel Ya dawo kansu, Kallo ɗaya tayi mata sai da gabanta ya faɗi, kuma nan take ta gane wacece ita, tun da taga uban hips dinta da boobs dinta da suka cika ƙirjinta, ranta ya bata cewar tabbas itace matar da aka damƙa ma amanarsu, tun da ta fito hankalin kowa ya dawo kanta, taku ɗaya girgiza goma, wankan suit din jikinta ya tafi da imanin kowa dake awurin.


 Kallon kallo suka soma bin juna da shi, tsakanin prisoners da ummin america, da kuma dr. Laura, da jami'an isod, da sojojin da suka halarta, sama sama suka soma gaisawa da ita, Dr laura ta haɗe rai kamar yadda itama ummin american ta ɗaure mata fuska, bayan sun gama gaisawa da juna, jami'an suka buɗe boot na motocin da suka zo da su suka ɗauko suitcases dinsu tare da jakunkunan kayansu, gaba ɗayansu suka ɗunguma zuwa cikin departure gate din Airport, ta inda suka samu sauƙi, Jirgin da zai ɗauke su privet jet ne mallakin Jami'an isod, babu buƙatar jira ko wasu shaidu, An riga An shirya masu komai su kawai ake jira domin tafiya, duk inda suka bi darewa akeyi abasu hanya saboda sojojin dake atare da su, prisoners sai ƴan kalle kalle suke Yi, sunga wuri mai kyan gaske ga mutane launi daban daban suna ta yin zarya acikin wurin, Yankin da jirginsu zai tashi  fili ne na musamman aka ware shi domin tashi da safkar jirage masu zaman kansu.


Tanƙamemen Privet jet ne Aka tanadar masu, Mallakin Chief of isod, Aljannar duniyace ƴar ubansu a wurin haɗuwa, tun daga wajen jirgin zaka fara cin karo da sunan ISOD da aka rubuta da manyan haruffa ajikinsa.


  Idan ka shiga cikin jirgin kamar ka shiga haɗaɗɗen villa ne saboda haɗuwar kayan alatun dake acikin sa,  akwai Falour wanda yaji hadaddun leather seats masu numfashi, tare da ƙayatattun tables, ga fine carpet shimfiɗe saman floor na jirgin, bayan shi akwai large flat-screen TV, ga Conference table domin yin meeting, a kewaye yake da kujeru, ga kitchen da bathroom, and privet bedroom da kuma dining area, Komai fa akwai shi acikin jirgin babu ce kaɗai ke babu, ta ko'ina sanyin A.c ka ratsa cikinsa.


  Bayan sun sauka abakin jirgin, Hankalin su Batul Yaƙi kwanciya tun da su ka yi arba da jibgegen jirgin dake agabansu, ko a mafarki basu ta6a yin tozali da abu kamar wannan ba, duk sun bi sun rude, sai faman zazzare idanuwa suke yi, badan Angel na atare da su ba, da tuni wasu daga cikinsu sun zauce saboda tsabar kiɗima, bankwana suka somayi da sojojin da suka rako su, Dr laura hada hawayenta na rabuwa da su, ɗaya bayan ɗaya saida ta rungume su, tana yi masu fatan alkhairi, Jemimah da Azeeza sunji ɗacin rabuwa da ita, sun sha kuka  hawaye duk Ya 6ata fuskokinsu, lallashinsu ta dinga yi tana kwantar masu da hankali, tace kada su damu zata iya zuwa har Nigeria tagan su, babu wanda bai ji kewar rabuwa da su ba, Dr mark da brown suma sun matse ƙwallarsu, hatta nurse jessica da Rebecce sai da su kayi kukan rabuwa da su, musamman masoyiya Angel kowa ya saba da ita, suna sonta sosai, ummin america tuni tayi sallama da ƙawarta Natasha, bayan sun gama ƴan rungume rungume, sojojin da ke atare dasu sunyi masu fatan sauka lafiya, lokacin da zasu hau matakalar jirgin daƙyar suke taka staircases din, har  dai suka samu damar shiga ciki, al'ajabi ya kama su ganin haɗuwar jirgin, kowan nan su Ya samu wuri saman tausasan leather seats din suka zazzauna, tun da suka shiga jirgin ummin america bata tanka masu ba, sai dai kallon kallon da suke Yi a tsakanin su, ita dai Angel damuwarta Danish ɗinta, Ya ƙanƙameta, babu alamun lafiya atattare da shi, jikin shi yai zafi rau.


 Lokacin da jirgin Ya soma tafiya Yana bin hanya kafin Ya ɗaga sama, Hankalinsu Azeeza ba ƙaramin tashi yai ba, jami'an Sunyi ƙoƙarin kwantar masu da hankali, ganin yadda su ka ruɗe jikin su ya hau yin kerma, sun fahimci mugun tsoro ne da su, Angel ce ta tunasar dasu akan suyi addu'a, aiko atare suka hada baki suna karanta addu'o'in data koya masu.


  Cikin ƙanƙanin lokacin jirgin Ya ɗaga sama Ya keta hazo can cikin sararin samaniya, Ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke kamar an yaye masu tsoron da suke Ji, hankalin kowan nan su ya kwanta tun da aka kunna masu kallo a tv, ban da na Angel, Yanayin fuskarta ya canza, sakamakon maganganun da taji Danish yana furta mata acikin kunnanta, muryarshi arauna ce yake fadin baya son mutane, haushin su yake ji, yana ji kamar ya kashe su, jinin su yake sha" ƴan hanjin cikin ta ba ƙaramin kaɗawa su ka yi ba, sai faman zazzare ido take yi, babu wanda ya lura da halin da take a ciki, sauƙin ma acikin kunne yake yi mata raɗa, sautin muryar baya fita, kuma akwai tazara tsakanin seats dinsu dana sauran ƴan uwansu, ɗaya daga cikin jami'an isod ne Ya ɗauko mashi eye mask ya miƙa ma Angel don ta sanya mashi a tunanin shi hasken jirgin ke bayaso shiyasa ya cusa kanshi saman kafadar Angel may be ko yana son ya runtsa ne.


Tun da ta sanya mashi eye mask taji yayi shiru ya daina magana alamar bacci ya dauke shi, a ƙalla ta sauke ajiyar zuciya yafi a ƙirga, addu'o'i taci gaba da karanto mashi tana tottofa mashi saman sumar kanshi, fatanta Allah yasa ba wani mugun abun bane zai faru da shi, gashi ta manta bata nemi takardar dake ɗauke da address din gidansu salsabeel, duk da bata tunanin ma ko sunje zasu samu abunda suke so.


 

A Kishingiɗe yake saman shimfiɗeɗan full-sized bed dinsa dake acikin privet room na jirgin, ya ɗaura kansa saman tattausan pillow, Shin wanene wannan kyakkyawan matashin saurayin? A jin farko afagen kyau da ƙasaita, Namijin duniya, A halitta madai-dai ci ne, mai wani irin faffaɗan ƙirji a  buɗe yake, ga wannan six pack din nasa baro baro, Vest din jikinsa tayi tighting dinsa, kana iya ganin zanen ƙirjinsa, Ko ɗan wrestling bazai nuna mashi ƙirar ƙarfi ba, in ka kalli damtsen hannunsa sai ka tsorata, mutun ne mai ji da ƙarfi, Allah yabasa kyawawan idanuwa farare tass ga su so sexy, masu ɗauke da launin ƙwayar ido reddish brown, har shining suke yi, ga wani kwantaccen saje mai shegen kyau, eye brows ɗinsa kuwa tamkar an zana ta, tayi wani irin shape ga gashi cike da ita, kiris ya rage jagirarsa su haɗe da juna saboda Yana da yalwatacciyar suma, lallausar sumar kanshi tasha gyara anyi mashi Military haircut yayi bala'en yi mashi kyau, abun da yafi komai jan hankali a jikin shi tsadaddiyar launin fatar shi, chocolate colour, har wani glowing take yi, hutu ya zauna mashi, jikinshi ya wanku da dollar, duk inda namiji yakai to ya zarce nan, komai nashi na kece raini ne ba wasa a tattare dashi, kuma burin kowace ƴa mace ne shi, a 6angaren wadatar arziki kuwa basai an faɗa maka ba, su kan su kuɗin raina kansu suke yi agabanshi, duk da tarin dukiyarsa baida girman girka, mutum ne shi da bai ɗauki duniya da zafi ba, Allah ya bashi kaifin basira, Yana da ilmin addini dana zamani, ta ko'ina Allah ya hore mashi, yana matuƙar jin ƙan talaka, Yana da tausayi ga son taimako, shi sam abun hannunshi bai rufe mashi ido ba, kyawawan halayansa da ɗabi'unsa abun burgewa ne, shiyasa ya fita daban ko acikin jikokin family ɗinsu, ya shahara aduniya sosai, babu inda ba'a sanshi ba, mutane basa gajiya da yabon shi, burin kowane ya yi tozali da shi, babban abunda ya tsana a duniyar nan shi ne yaga mugun mutun mara imani acikin mutane Yana zalunci, In kuwa ya damƙi irin su, mai ƙwatar su sai Allah, shiyasa mutane masu irin halin suke mugun jin shakkar shi, dai dai da sunan shi aka fada sai gabansu ya fadi, don baya yi masu da kyau, ni nasan bazan Iya misalta ƙasaitaccen Namijin nan ba, Kaɗan ne na Iya faɗa maku sauran ku biyo ni acikin labarin, Yanzu ne wasan Ya fara.


Tun da ya ɗaura lumsassun idanuwanshi akan tsadaddar laptop din gabanshi ƙirar Apple macbook pro bai ƙyafta idon shi ba, Hannun shi na dama na sanye da wrist watch ƙirar Rolex submariner haɗaɗɗar gaske, ya tattara dukkan natsuwar shi akan abun da yake kallo, duk wani motsin prisoners dake acikin jirgin yana kallon su ta cikin laptop dinsa, Ƙayataccen table din dake agaban gadon shi ɗauke ya ke da Mug na cofee ga fresh fruit da aka ajiye mashi, daga gefen shi saman mattress, suit jacket dinsa ce daya cire launin Navy blue, trouser din ta ne a jikin shi, hankali a kwance bai da wata damuwa.


 Awanni da suka ɗauka acikin jirgin ba ƙaramin daɗi suka ji ba, saboda an gatanta su, sunci abinci har sau biyu, sun yi bacci sun tashi, komai suke so yi masu ake yi, Danish ne kaɗai baici komai ba, tun da bacci ya ɗauke shi bai farka ba.   💋ABBAN SOJOJI💋

💋KURKUKUN ƘADDARA💋Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da kuma kurkukun ƙaddara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440  whatsapp din ya samu matsala, ga wadda za'a same ni da ita (08134387050) ayi mini magana ta whatsapp, message from Boss Bature


 ✍ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin
First bank
3196407426, 
Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post