Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 28

Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 28


Page 28

Dr.shureim Tun bayan daya dawo daga sallar asuba Yake ta faman shirye shiryen tafiya jos, tuni Yayi wanka ya kimtsa cikin shigar shi ta larabawa Yabi ko'ina na jikin shi Ya feshe da turare, Hannun shi ɗaya ruke da wayar shi ɗayan hannun Yana ruƙe da car key dinsa, takalmasa Ya zura a ƙafa Jiki Na rawa ya nufi ƙofar fita daga ɗakin bayan ya fito bai nifo ko'ina ba sai part din Alhaji musa don Ya sanar mashi da zancen bayyanar benazir da kuma tafiyar da zaiyi zuwa jos, abakin ƙofar ɗakin ya dai daita natsuwarshi, ya ɗaga murya yayi mashi Sallama, kusan sau uku kafin muryar Alhaji musa ta amsa mashi

  "Wa'alaikum salam shureim shigo ciki mana" ajiyar zuciya ya sauke, tare da sanya hannu Ya ture ƙofar ta buɗe, baiyi tsammanin zai ganshi tare da wani ba, ashe bashi kaɗai bane, su biyune shi da Hajiya Sarah suna zaune saman Sofa ɗin ɗakinshi, An jera masu kayan breakfast a saman sofa table din gabansu, mutumin babu annuri akan fuskarshi, Jallabiyace a jikin shi hajiyar tashi kuwa ta ca6a uban adon lace a jikinta, ta kashe ɗaurin kallabinta, wutsiyar gashin kanta ya sauka har saman wuyanta

  Fuskarta da fara'a take kallon shureim"barka da safiya My son, fatan ka wayi gari lafiya" shureim na murmushi yace"yawwa mommy, ina kwananku' ta amsa mashi da Lafiya lou, tare da nuna mashi wuri saman armchair ta ɗakin tace"bismillah ka zauna mana" tun da ya shigo Alhaji musa bai ɗago Ya kalli fuskarshi ba, Hankalin shi na akan abincin da Yake ci, plate ne agabanshi shaƙe da farfesun nama Yaji ƙayan hadi sai ƙamshi Yake Yi, a tsanake Yake cin abun shi.

  Kasa zama shureim yayi idanuwanshi akan fuskar Alhaji musa Yace"uncle barka da safiya" kamar bazai amsa mashi ba ya furta"lafiya" da ido Hajiya sarah tayi alamar yayi haƙuri da halin uncle din nashi, murmushi shureim ya sakar mata yaɗan jinjina mata kai

  "Ko zaka Bari idan Ya gama cin abinci sai ku yi magana, don bai cika son yana cin abinci ana yi mashi magana ba" hajiya sarah ce ta fada,

  Kafin dr shureim ya bata amsa muryar Alhaji musa ta katse mashi hanzarinshi"Shureim ina jin ka, faɗi abunda ya kawo ka"

    Ba ƙaramin daɗi Yaji ba, da fara'arshi ya fara magana"uncle bansani ba, ko daddy ya kira ka awaya ya sanar dakai abun farin cikin daya faru a daren Jiya" sai da ya ambacin hakan tukunna alhaji musa Ya ɗago da ido yana dubanshi alamar yana son jin ƙarashen zancen

  "Ƴar uwata Benazir ta dawo gida a daren Jiya ƙarfe goma sha biyu na dare!!!"

  Tsantsar mamaki da al'ajabi ne Ya bayyana akan fuskar alhaji musa, sai dai babu alamun zai furta magana sai faman jinjina kanshi yake yi.

 Hajiya sarah kuwa Tsabar farin ciki mikewa tayi tsaye tare da ɗaga hannyenta sama tana ambaton"ALHAMDULILLAH!! wayyo Allah shureim Allah Yasa ba wasa kake Yi min, dagaske Benazir ta dawo gida da ƙafafuwanta ko kawota akayi"?

  Shureim na murmushi yace"da kanta ta dawo gida, kuma abun mamaki tana ta sambatu tana ambaton sunan daddy da mommy da mijinta da ƴarta, kuma muna hasashen kurciya ne akayi mata da har ta gudu tsawon shekaru bata dawo gida ba, shiyasa nake so inje jos din Yanzu......." 

 Hawayene suka wanke fuskar Hajiya sarah, Muryarta na rawa ta furta"shureim nima zan bika muje jos din, nasan shima uncle din naka zai je sai mu tafi atare..." kafin ta ƙare maganar Alhaji musa ya dakatar da ita ta hanyar cewa"Ya isa haka? Kinsan bana son shouting" shiru suka yi gaba ɗayansu, duk suka sha jinin jikinsu.

  Kallon shureim yayi"ina zaka je da safen nan, naga ka shirya ga key din mota a hannu"?

  Cikin sanyin murya yace"jos zan tafi, Inason ganin benazir"


  Ta6e baki Alhaji musa yayi, tsawon mintuna ɗakin yai tsita, saida ya mula yasha iska tukunna yace"zanyi waya da yaya ubaid din, basai kaje jos din ba, zansa su zo nan abuja..." har saida gaban shureim Ya faɗi jin abinda Yace, bashi ba hatta Hajiya sarah arude take duban fuskarshi, kallon mara hankali take binshi da shi don wanna Yafi ƙarfin a kira shi da izzah, Tayaya zai nuna ƙarfin iko akan Yayanshi? Waye ya dace yazo gidan wani? Almost 16years yarinya ta 6ace sai Jiya ta dawo ƙarfe sha biyu na dare ko kaɗan bai nuna danuwarshi ba, kuma babu alamun zai je ya taya yayanshi murnar ganin yarsu da suka yi?

  Muryarta na rawa ta furta"am..amma hakan bai dace ba, nayi mamaki daka furta wannan maganar, kodai baka ji abunda shureim Yake faɗi bane? Ƴar wurin Yayanka benazir ce data 6ace tsawon shekaru ta dawo gida a daren jiya ƙarfe goma sha biyu na dare Yakama ka tashi ka shirya mu tafi" da buɗar bakinshi sai cewa yai"Umarni kike bani"? Da ƙarfin hali Ta furta"A'a kawai ina ƙoƙarin faɗa maka abunda Ya dace ne" tamkar zaki Haka ya yunƙura ya miƙe Ya dubi fuskar shureim da mamaki Ya gama kamashi

   "Nace bazaka je jos ba, ka koma ɗaki ka zauna, zansa Iyayen naka su zo tare da ƴar uwar taka abuja" gyaɗa kai dr shureim yayi jiki amace yace"toh uncle, na hakura, zan jira su zo ɗin" ƙwalla ce ta ciko idanuwanshi da sauri Ya juya ya fuce daga dakin.

  Bayan fitarshi Alhaji musa Ya nuna Hajiya sarah da Yatsan hannunshi"koda gigin wasa kada ki kuskura ki ƙara shiga tsakanina da shureim idan muna magana, abune da  ya shafeni da dangina banaki ba, don haka ki kiyaye" yana gama fadin hakan a fusace yakai hannu ya yago tissue ya goge bakinsa ya nufi cikin dakin.

  Jiki asanyaye hajiya sarah ta zauna saman sofa din, lamarin Ya ɗaure mata kai, wannan rashin adalcin har ina? Meyasa zai dinga iko da yayanshi? Ko dan Yana da dukiya ne? girgiza kai tayi ahankali ta furta"wannan ba adalci bane" ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi hanyar fita daga ɗakin.

  Bawan Allah dr shureim abun duniya ya isheshi, Uncle musa Ya bashi mamaki, bai ta6a jin haushinshi ba sai yau daya nuna ƙarfin iko akan iyayenshi, Ya fahimci ma bai damu da dawowar benazir ba saboda babu annuri akan fuskarshi duk da yasan halin shi ne hakan, amma yaji ɗaci aranshi, don me zai dinga juya mahaifinshi son ranshi bayan shine agaba dashi, ko a shekaru Alhaji ubaid Ya zarce Alhaji musa nesa ba kusa ba saboda shi ba wasu shekaru gare shi ba, shiyasa ko a jam'iyarsu ake kiranshi da ƙaraminsu babbansu. Abun ya ɗaurewa Dr. Shureim kai, har ya fara tunani kodan Yana da dukiyane shiyasa yake sarrafa kowa yadda yake so? In banda rashin ta ido har zai Iya buɗe baki yace zai kira iyayan nashi suzo abuja maimakon shi ya tattara iyalansa suje can jos din su tayasu murnar dawowar ƴar su, Anya kuwa Uncle musa bai fara shan ƙwaya ba"? Saƙe saƙe zuciyar shureim take Yi mashi hakanan ya samu kanshi da kokwanton uncle din nasa.

  "Shureim dan Allah ka yi hakuri da abunda uncle dinka Ya faɗa maka, wallahi banji daɗi ba, bai kyauta ba, wannan ai ba adalci bane, bansan meyasa yake yin haka ba"

  Muryar Hajiya sarah ce ta katse mashi zancen zucin nashi, har ya kusa shiga ɗakin shi Ya ci burki tare da Juyowa baya yana dubanta

  Damuwace ƙarara akan fuskarta, kamar yadda shima tashi fuskar damuwarce

  Murmushin yaƙe ya ƙaƙalo akan fuskarshi da karyayyar murya ya furta"kada hakan ya dame ki mommy, da ace bansan halin uncle din nawa bane, amma nasani, shiyasa nake yi mashi uziri, bakomai zan jira su zo din kamar yadda ya fada"

  Gyaɗa kai hajiya sarah tayi har cikin ranta bataji daɗin abin daya faru ba

 "Bari na kira maka zeenatu, nasan zata ɗebe maka kewa, kafin isowarsu" still da murmushi akan fuskarshi Yace toh, zan jirata

   Bayan tafiyarta, Ya shiga dakin shi, asaman gado ya jefar da key din hannun shi, Ya tu6e arab tur6an dinsa Ya jefar saman gado, Ya zauna daga gefe hannu bibbiyu ya zabga uban ta gumi takaici Ya ishe shi, mahaifinshi Yafi 6ata mashi rai saboda shine silar komai, da ace tun farko bai bari uncle musa ya raina shi ba da duk hakan bata faru ba.

  Yayi zurfi acikin tunanin shi muryar Zeenatu ta katse shi

    "Yaya shureim ɗina" a hanzarce ya ɗago da ido yana dubanta, ta zumbula dogon hajibi har ƙasa Yake ja, ta ruƙo round plate mai ɗauke da mug, sai faman sakar mashi murmushi take yi, kwata kwata babu natsuwa atattare da ita, kafin shigowarta ɗakin mommynta ta faɗa mata  xancen ganin benazir shiyasa take ta yin farin ciki, ita fa tun da take bata ta6a ganin benazir ba a hoto kaɗai tasanta saboda kafin guduwar benazir tana ƴar jinjirarta.

  Ganin yadda take tafiya babu natsuwa yasa shin saurin motsa la66ansa da niyar ya dakata da ita, sai dai ina kafin yai yunƙurin yin hakan tuni tayi tuntu6e da takalmanshi daya cire a tsakar ɗakin, Mugs din data dauko yai tsalle sama Ya dira daman ƙafarta ruwan coffee mai zafi Ya ɗalli ƙafarta, zafin da tajine yasa ta jefar da plate din hannunta, ta duƙe saman floor tana kuka, da sauri Ya miƙe ya ƙarasa gabanta, ya zuƙunna tare da kai hannu ya damƙi ƙafafuwanta Ya soma tottofe su da addu'o'i, ta dage sai kuka take yi mashi, abunka ga farar fata wurin da ruwan coffeen Ya ta6a yayi jawur kamar zai fashe.

  Kukanta duk Ya cika mashi kunnuwanshi, a hankali ya ɗago Yana dubanta, hawaye sun wanke fuskarta, lokaci ɗaya ya soma tariyo sambatun benazir tuni yaji jikinshi yai sanyi, haƙiƙa Yana matuƙar tausayin rayuwar ƴa mace, fuskar benazir ce ta dinga yi mashi gizo akan fuskar zeenatu, har baisan sa'adda Ya rungume ta a kirjinshi Ya zagoya da hannanyeshi saman bayanta, Yana ɗan bubbuga shi cikin sigar lallashi, ƙanƙameshi zeenatu tayi kamar zata koma cikin cikinsa, daddaɗan ƙamshin turarenshi ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba, tuni ta haɗiye kukan da take yi, tayi kwance abunta sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, dr. Shureim sam ya manta dawa ya rungume a jikinshi, kewar benazir duk ta addabe shi, Ya jefa zeenatu cikin yanayi najin shauƙin shi, yayin da shi hankalinshi nacan wani wurin daban...............


Idan muka koma 6angaren zahra, tun wuraren ƙarfe shidda Mahboob Ya shigo mata da jakar kuɗin motarta da wayar da aka saida mata, shaf shaf ta shirya cikin jallabiya ta yafa mayafi akanta, tace da mahboob ya taimaka ya kaita gidan Hajiya falmata, yace zai kaita amma bisa sharadin zata bashi nashi kason, tunda ai yayi mata ƙokari, a lokacin taƙagara da taje tace mashi ta amince su tafi kawai, kafin su bar gidan saida ta fara cire miliyan ɗaya ta ajiye su cikin drawer, ya rage saura 3m dai dai kuɗin da zata bata.

  Tana zaune a back seat na motar mahboob, yayin da shi kuma yake zaune a mazaunin driver, a tsanake yake yin driving har Allah Ya kawo su gidan Hajiya falmata.

  A parking space mahboob yai parking din motar yace da ita ta shiga yana jiranta, ta amsa mashi da toh, ta buɗe motar ta fito ta nufi ƙofar shiga babban falon gidan"

    Murmushin gefen fuska Mahboob ya dan saki yayin da yake bin Bayan zahra da kallo, ya zuro ƙafarshi daga cikin motar daya bar murfinta abuɗe

  Wayarshi ce tayi ringing daga cikin aljihu da sauri Ya zura hannu ya duba mai kiranshi sunan Aunty Aneelerh ne Ya bayyana

  Picking call din yai ya kara wayar a kunne"Babbar yayanmu, mun karaso gidan fa, Yau zahra zata sha mamaki, wallahi bakiga yadda take ta zubda uban gumi ba, kamar wadda tayi ma sarki ƙarya fadawa suka kamo ta" tuntsirewa yayi da dariya,

 Muryar Aneelerh da sautin dariya tace"baiwar Allah, ina fata yau hankalinta zai kwanta, naji daɗi da nasarar da muka samu, ubangiji Allah Ya ƙara tsare mata ita" ya amsa mata da ameen


  Ta kuma cewa"Idan kuka dawo gida, ka faɗa mata cewa motarta da wayarta jingina ka bada su, idan tanaso ta baka kuɗin za'a dawo mata da su, sannan please bana so tasan cewa jiya munje gidan hajiya falmata, ya amsa mata da toh, daga haka sukayi sallamar.


  Tun da zahra ta shiga gidan, takasa zama, tana a tsaye tana jiran fitowar hajiya falmata don ta miƙa mata kuɗinta, mai aikin gidan ce ta fito daga part din dakin nata ta dubi zahra"ki zauna mana gatanan fitowa" galla mata harara zahra tayi'ba zama nazo yi ba" murmushi mai aikin tasaki kafin ta wuce ta nufi kitchen

  Jim kaɗan, Hajiya falmata ta sauko down stairs, sleeping dress ne a jikinta riga da wando ta yafa mayafi akanta.

   Fuskarta babu walwala ta dubi zahra"zauna mana" tayi maganar tana nuna mata sofa

  Harara zahra ta watsa mata"ba zama nazo yi ba, kuɗinki na kawo maki" tayi maganar a fadace ta ajiye mata jakar gaban kujerar da take a zaune

  Har ta juya zata fita muryar hajiya falmata ta katse mata hanzarinta

  "Zahra! Dan Allah ki zauna inaso muyi magana badan halina ba"

 Batayi mata gardama ba tace"dan kin haɗani da Allah, shiyasa zan zauna badan haka ba wallahi ko kallo baki ishe ni ba" murmushi hajiya falmata tasaki.

   Bayan zahra ta zauna tana faman haɗe rai tace"ina sauraronki sauri nake yi in tafi"

  "Nasan zakiyi mamaki zahra, kuma ba lallai ki yarda da abunda zan faɗa maki ba, abunda Ya faru a tsakanina dake badagaske bane, jarabaki nayi saboda wani dalili nawa...." da mamaki zahra take dubanta, jinjina kai hajiya falmata tayi"tabbas ba halina bane, nayi ƙoƙarin jan ra'ayinki ne don insan dawa ƴata take tarayya"

 Tunkan ta kare maganar zahra tasaki dariyar rainin wayau tana fadin"dallah malama dakata! Banason zancen banza, harni zaki raina ma wayau? Ki gama zubda mutuncinki agabana kuma ki dawo kina fadin jarabani kikayi akan me kenan? A tsiwace ta furta hakan

  Numfasawa hajiya falmata tayi"zahra dalilin dayasa nayi maki hakan, Mun samu sabani nida wata aminiyata hajiya naja'at akan ƴarta dake bin mata, ta laƙafa mun sharrin cewa ƴata fatima ce ta koya mata, saboda ita kaɗaice suke tarayya, sannan ita taba yarta tarbiya tasan bazata ta6a aikata hakan ba, faɗa sosai mukayi da ita, ta zageni taci mutuncina, damuwar duniya ta isheni, lokacin dana dawo gida narasa ya zanyi in tuhumi fatima saboda nima ina tsoron ace ƴata tana aikata kalar abunda Yarinyar aminiyartawa take yi, nasan zaiyi wuya fatima ta faɗa min gaskiya, kinji dalilin dayasa na yanke shawarar yi maki hakan saboda nasan ke kaɗaice aminiyar fatima, duk wani abu da zatayi saida shawararki, atare kuke yin komai, Ni a tunanina ta hanyar dana 6ullo maki zan samu abunda nake nema na gano abunda ƴata take aikawata ashe ba haka bane nayi babban kuskure zahra, dan Allah Ki yafe min" fashewa tayi da kuka hawaye nabin fuskarta, baiwar Allah zahra tuni zuciyarta ta karya, sam bata kawo komai aranta ba, ta yadda da kalaman hajiya falmata, cikin shessheƙar kuka tace"Amma meyasa zaki yi jarabawar dani? Kin hanani bacci kin hanani cin abinci, kin jefa rayuwata cikin matsanancin tashin hankali, babban abun takaicina shine karya min zuciya da kikayi saboda na ɗauke ki tamkar mahaifiyata ina ganin girmanki, ashe dama duk plan ne kika shirya min"?

  Hajiya falmata na matsar ƙwalla tace"kiyi hakuri zahra nasan ban kyauta maki ba, dan Allah ki rufe min asiri kada kowa Yaji maganar nan, saboda banaso ayi tsammanin nima ina aikatawa ne sannan, maganar kuɗin da nake binku ni tuntuni na yafe maku, wallahi na bar maku su babu abunda zanyi dasu, sannan maganar yin order na kaya daga dubai in sha Allah gobe zasu iso Nigeria, inaso kuci gaba da gudanar da aikinku a companyna ke da fatima, don bazanso in rasa mace mai nagarta da tawakkali irinki ba, komai kuke so zanyi maku zahra, ni dai fatana ki manta da duk wani abu daya faru a tsakanina dake, Ki cigaba da daukata tamkar mahaifiyarki"

  Rushewa zahra tayi da kuka, kamar ranta zai fita, bata ta6a tsammanin komai zai zo mata da sauƙi ba, harta fidda ran cigaba da aiki a companynsu da kuma damar zuwa obie estate ashe da rabon mafarkin ta ya zama gaskiya.

   Cikin shessheƙar kuka tace"In sha Allah mommy babu wanda zaiji maganar nan, komai Ya wuce amma dan Allah kada ki ƙara yi min wasan nan, ni kaɗai nasan raɗaɗin da naji acikin zuciyata"

  Jinjina kai hajiya falmata tayi da karyayyar murya tace"bazan ƙaraba zahra, nima nayi danasani, dan Allah ki tsaya mu yi breakfast atare kada kice zaki tafiya"

 Zahra tace"sauri nake yi wata rana zan dawo, Ina fatima take"? Hajiya falmata tace"bata nan, jiya ta tafi gidan uncle dinta amma yau zata dawo saboda aikin da zakuyi tare" murmushin farin cikine Ya bayyana akan fuskar Zahra, sai faman washe bake takeyi harta fara tunanin irin rashin mutuncin da zatayi ma Aneelerh idan ta koma gida,

  Godiya sosai hajiya falmata tayi mata, itama zahra tayi mata godiya da fara'a suka rabu.

   Ta ruƙo jakar kuɗinta a hannu, tana fitowa daga falon da gudu ta nufi motar mahboob tana dariya haɗi da yin rawa tana jujjuya,

  Mahboob tamkar baisan komai yace"zahra kin haukace ne? Lafiya kike dariya kamar wadda ta zauce ga hawaye akan fuskarki" da sauri ta share hawayen da gyalen jallabiyarta

 Tace dashi"bro ka tayani murna yau ina cikin farin ciki, amma fa kada ka tambayeni meyasani shiga yanayin nan"

  Mahboob na murmushi yace"shakuruminki aini ba ɗan jarida bane da zan tsareki da tambaya, Yanzu dai shiga mota muje gida muyi magana akan haƙƙina,"

 Da farin ciki tace"ai mahboob kamar yadda Allah Ya rufa min asiri kaima zan rufa maka asiri, kai dai muje gidan" ta faɗa haɗi da shiga motar, ya tada suka nufi Hanyar komawa gida.
EX-PRISONERS🥳


At abuja Nigeria🛬Alhamdulillah Matafiya sun samu damar sauka Lafiya basu wayi gari ba sai acikin Katafaren Luxury Villa Mallakin Chief Owais sharafuddeen Obinna! haɗaɗɗiyar Daular arzƙi ce wadda zamu Iya kiranta da Aljannar duniya saboda Kayan alatun dake acikin ta, Katafaren gini ne mai girman gaske ta 6angaren tsayi da faɗi Yana ɗauke da Sassa Uku acikinsa, a ɗaya daga cikin Part din gidan aka yima Prisoners masaukinsu, A hankali nake bin ginin da kallo domin in ƙarasa ga cikinsa, ta ko'ina na kalla ƙyalƙyalin gilassai ne suke kashe min idona da kyawunsu, wasu irin haɗaɗɗun floor-to-ceiling Glass windows ne masu mamaye bango, daga ƙasa har sama glass ne, Kana Iya hangen Katafaren Main falo din dake acikin sashen ta glass windows din, Ga wasu sliding doors ƙofofi masu zuge kansu da zarar sun gama tantance mutun saboda gidan Yana da mugun tsaro ba iya mutane ba hada na'urori ke sarrafa shi, ba za ka ta6a Iya ƙetare Gingirimeman entry way din gidan ba tare da An tantance ka ba, daga ƙasa har sama, bana tunanin ko aljani zai Iya shiga salin alin ba tare da na'ura ta haska shi ba, salon kuma ace nayi karya (😂)


 Dafa ƙofar glass din Nayi da hannuna ɗaya, Na'ura ta tantance ni aka bani iznin shiga ciki, Slowly glass din Ya soma zugewa, Na baza ido ina kallon tsaruwar Falon da kallon shi kaɗai zai Iya faranta zuciya, launukan painting cikinsa black, gold and white, An ƙawata shi da manya manyan sectional Chersterfield sofas, saiti biyu ne a palourn, Ƴan ubansu masu numfashi masu tafshi da daɗin zama ga jerin Throw pillows launuka daban daban saman kowace sofa, daga tsakiyar Katafaren falon wani faffaɗan Glass table ne daga saman shi an ɗaura flowers Vase, Furannin har ƙyalli suke Yi masu launi daban daban, bayan haka a kowani sofa hand din akwai Round glass table, mai dauke da kayan ƙyale-ƙyale na ado, daga saman jigunan ceilling din falon wasu ƙayatattun Crystal chandeliers ne masu girman gaske, An ƙawatasu da ado, kusan guda Uku ne a saman silin din, Haskensu Ya mamaye ko'ina tamkar da rana, Idan ka kalle su sai ka yi tsammanin zasu rubzo maka saman kai, sobada girman su, ga wata faskekiyar flat screen tv wadda idan kana kallo da ita sai ka yi tsammanin mutanan ciki zasu fito waje saboda girmanta, Bayan sofas din falon akwai hamshaƙan armchairs har guda biyu, hatta saman floor din falon Kayan adone aka ɗaura samansu, sparkling floor lamps ne ajiye a kasa suna bada nasu hasken mai ƙyalƙyali, akwai Kayan jin sauti, Ga Dogayen labulaye dake kewaye da falon an zuge su, A ƙalla Part din Yana ɗauke da Faluka sun kai Uku, bayan wanda na zayyana ma ku, daga cikin falon farko kana Iya hangen furniture din da ke a cikin falo na biyu ta hanyar Glass window, komai zaka Iya gani, Gidan fa Ya haɗu Ga glass elevator gefen twins stairs din dake a falon, ta ko'ina sanyayyan sanyin A.c ne ke ratsa fatar jikin bil'adama mai ni'imar gaske, bayan haka ta cikin glass din falon zaka Iya hango Sashen da tanƙameman swimming pool din gidan Yake, ruwan dake acikinsa launin sky blue ne, da wasu kujerun shaƙatawa a gefenshi, da sauran ababen more rayuwa, Idan muka koma Dining room wato ɗakin cin abincin gidan abun ba'a magana, shima a kewaye yake da floor-to-ceilling glass windows, kana Iya hangen abubuwan dake wakana daga wajen ɗakin cin abincin, An ƙawata shi da haɗaɗɗun dining tables, na farko zungureren table ne mai mazaunin mutun goma sha biyu, da me mazaunin mutun shidda, da kuma tabur mai mazaunin mutun uku, kowan nan su saman shi an ƙerashi da zallar glass, ƙafafuwansu kuma wooden legs ne, wasu haɗaɗun gujerune kewaye da tables din, daga saman ceilling din ɗakin cin abincin ƙaton kwan fitila ne ke haskaka cikinsa, ga kuma Zungureriyar floor lamp, Itama nata hasken Daban Yake, agurguje zamu leƙa Cikin Bedrooms din dake a part din, A ƙalla ɗakunan kwanan dake a cikin part din sun kai goma sha biyar, Just for one part, ƙofar shigar kowani ɗaki ta glass ce sai dai baka Iya hangen abunda ke ciki idan har na  cikin ɗakin ya zuge curtain dinsa ba, ƙofar da kanta take zugewa da zarar mutun Ya kusance ta take sliding a hankali, Idan ka shiga ɗakin idanuwanka zasu fara Yin Arba da wallpaper ta bango mai matuƙar jan hankali, kowani room Yana ɗauke da hamshaƙan king-side beds masu tausasan Katifu kalar wanda ko mutun bai jin bacci idan Ya hau su sai dai aji sautin minsharin shi, saman gadon shimfiɗe yake da tausasan bedsheet, da jibgegen bargon lullu6a kafi mage laushi, ga jerin matassan kai daga gaban gadon.


Gefe da gefen gadon nightstands ne, wadanda ke ɗauke da bedside lamps, daga bakin gadon faffaɗan wooden table ne mai ɗauke da drawer chest a jikin shi, ga wani haɗaɗɗen rag carpet shimfiɗe ƙasa mai dumbujejen gashi gashi ajikinshi tsaf mutun zai Iya kwanciya saman shi saboda laushinshi, ga wani ƙayataccen dressing mirror gabanshi haɗaɗɗiyar kujerace, daga can cikin ɗakin akwai dressing room, aljannar duniya kamar ka shiga company saboda haɗuwar Large walk in closet din daya mamaye kowani bango na dakin sanya suturar, suturun sanyawa ne an jera su, daga waje zaka Iya ganin kayan dake a cikin closet din, 6angaren Kayan bacci, dana Dogayen riguna, 6angaren english wears dana atamfofi ga laces, da jerin coat, ga 6angaren takalma kala kala, dana jakkuna, kai komai fa an zuba shi babu ce kaɗai ke babu, shima ɗakin Yana da nashi dressing table, mai ɗauke da oval-shaped mirror, Mai Kyan gaske.


 Ataƙaice Idan fa nace zan tsaya zayyana daular Owais sharafudden tabbas zamu ƙare littafin akan bayyana kyawunsa, sai dai mun shiga cikin labarin sannu a hankali zan ƙarasa zayyana maku haɗuwar wasu 6angarorin na gidan.CHIEF OWAIS✊Gajiyar tafiya ta hana shi ta6uka komai, ga6o6in jikinsa sunyi mashi nauyi, tun da ya fito daga bathroom yake a kwance saman katafaren king bed dinsa, ya lullu6e surar jikinshi da Cashmere robe launin dark navy, Iya gwiwarsa rigar ta tsaya mashi, ya ɗaure igiyarta daga saiting flat waist dinsa, mutumin fa akwai ƙirar ƙarfi, Kyawawan idanuwanshi A lumshe suke tamkar maiyin bacci, Yalwatattun eye lashes dinsa sun kwanta luf, a hankali Yake motsa soft thin lips dinsa tausasa launin pink, dogon hancinsa Yayi tsaye babu lanƙwasa Yayin da yake fitar da numfashi cikin kwanciyar hankali, ya zagayo da hannun shi ɗaya ta saman yalwatacciyar sumar kanshi, ba za ka ta6a gane a wani yanayi yake aciki ba, ya tada kansa asaman tattausan pillow.


Alert ne ya shigo wayarshi, tamkar baisan motsawa A hankali ya miƙa ziraran yatsun hannunsa na dama ya janyo wayar dake ajiye saman nightstand, daƙyar yake iya buɗe eyes dinshi akan screen din wayar, Doorbell alert ya gani alamar wani yana son shigowa room dinsa, unclock button ya danna, a hankali ƙofar room ɗin ta zuge, mutun biyu ne sanye cikin kakinsu, baƙaƙen kaya, dogon wando tare da black shirt, daga sama sun ɗaura long coat, kowannansu ya 6oye fuskarshi da face mask, idanuwansu ne kaɗai zaka Iya gani, suna da faffaɗan ƙirji, agaban gadon shi suka dakata da yin tafiya, cikin girmamawa suka haɗa baki wurin furta 


"Barka da safiya Yalla6ai, fatan ka tashi lafiya, Ya gajiyar tafiya" tun da suka fara magana basu ɗago da ido sun kalle shi ba, saboda a ƙa'ida shi ba'ayi mashi magana ana kallon cikin idon shi, hakan babban laifi ne.


   Bai da niyar yi masu magana, bai kuma buɗe idanuwanshi ba tun da ya lumshe su, aran su su ka ayyana yau qasaitar tashi ce ta motsa, kamar gumaka Ya shanyasu a tsaye suna jiran amsar shi, sai da ya mula yasha iska kamar baison motsa la66ansa Ya furta"Lafiya" muryarshi tamkar ana busa sarewa.


   Big Guy yace"Sir, is there anything you need?" ya tambaye shi ne don shi a ƙa'ida ba'ayi mashi abun da bai ce yana so ba, ko da kuwa abinci ne ka kawo mashi duk mun yunwar da yake ji in dai bashi yace yana so ba to zai ce maka ka koma dashi inda ka ɗauko shi sai in yaga dama ya ke kar6ar shi"


   Jin yayi shiru yasa Big Guy kuma cewa"yalla6ai zamu Iya yin magana ta waya"? Sai lokacin Ya ɗaga mashi kai alamar eh, ajiyar zuciya Big Guy ya sauke tare da kallon mutumin dake a gefen shi wanda suke kira Boss Man, murmushi su ka sakar ma junan su, sun ƙwammace su yi magana dashi ta text message saboda wahala yake basu in dai a baki zai furta masu magana.


Slowly ya ware reddish brown eyes dinsa akan screen din iphone dinsa, a tsanake yake yin typing.


   Jin ƙarar shigowar message ta wayar  Big Guy ne yasa shi yin saurin curo wayar daga cikin aljihun coat dinsa Ya duba abun da Chief ya rubuta mashi


    I need My breakfast right nowcikin girmamawa big guy yace "I'll bring it to you immediately,"


Ya faɗa tare da Juyawa ya fuce daga ɗakin, Boss Man daya ya rage a tsaye ya natsu yana jiran jin me zai ce.


  A lokacin da bai yi tsammani ba, muryar Chief ta katse shi"Have a seat" wuri ya samu saman doguwar sofa din ɗakin Ya zauna

  "Check your phone, I sent you a message."

Ya bashi umarni.

  Da sauri Boss Man Ya zaro wayarshi daga aljihu ya soma karanta saƙon chief din nasu.


  "Ya kake fatan ka tashi lafiya" murmushi ya saki har saida ya ɗago dakai Ya kalli fuskarshi, Yana matuƙar yin mamakin girmama shi da yake yi duk cikin waɗanda ke aiki a ƙarƙashinsa shi kaɗai Owais Yake gatantawa, suna mutunci da juna.


    "Lafiyalou Alhamdulillah, Ina fata kaima lafiya, don na lura kamar gajiyar tafiya bata sake ka ba" abaki Ya furta mashi maganar, shi kuma Ya bashi amsa ta text message.


  "Nagaji sosai, amma alhamdulillah, lafiyata ƙalou, Ina fata ka leƙa wurin Ƴar taka, "


 Still fuskar Boss man da murmushi yace"ban kaiga zuwa ba, Yanzu nake shirin shiga na duba ta"


  Text ya rubuta mashi"Make sure you give her a big hug. I know you've missed her for a long time."


  Idanuwan shi ne suka cicciko tab da ƙwalla, tuni jikinshi yai sanyi, cikin sanyin murya ya furta"in sha Allah, zanyi hakan, daren jiya ko runtsawa banyi ba saboda jiran ƙarasowarku Nigeria, duk don saboda Inyi tozali da ita, sai dai ban samu damar Yin hakan ba, saboda Bayan nayi sallar asubahi a masallaci bacci Ya dauke ni, saida na shigo gida nake jin labarin ƙarasowar ku......" dakatawa ya ɗanyin da yin maganar, ganin text din da owais Ya tura mashi.

  

"Don't let the tears fall from your eyes, Otherwise, I won't let you see your daughter."  fashewa yayi da dariya jin abunda yace mishi, har saida ya ɗago ya dubi fuskar Owais, Hankali kwance sam idanuwanshi basa akan fuskar Boss Man ɗin.


  "Kana da mutunci, shiyasa muke ƙaunarka, wallahi tunda nake arayuwata ban ta6a ganin matashin saurayi mai wadatar arziƙi, da kyau da asali, mara girman kai irinka ba, saboda kowa naka ne, babu ruwanka ka ji daɗin rayuwarka, bazan ta6a mantawa da alheran da kayi mun ba, nasan bazan Iya biyanka ba amma ina fata Allah Ya wadatani da abunda zan faranta maka da shi"


  Tunda ya fara magana Chief owais Ya natsu yana sauraron shi, idanuwanshi akan screen din wayarshi.


  Tambaya ya jefa mashi"What's her full name?" 


  cikin girmamawa Boss Man yace"UNAISAH ZAHEER TAJUDDEEN" lumshe idanuwanshi yayi, ƙamshin turaren jikinsa yana ƙara daɗaɗa hancinsa.


   "She looks like you" dariya Boss Man ya saki yana duban fuskarshi Yace"tayaya akai ka sani? Kaida baka kallon mutane, Ni nasan baku haɗu da ita ba"


   Kafin Owais Ya furta magana, alert Ya shigo wayar shi, unclock button ya danna, door room din ta zuge, Big Guy ne ya shigo da food trolley, Ya gunguro shi zuwa gaban wooden table din gadon Owais, a saman shi Ya jera mashi kayan Lafiyayyan breakfast dinsa, Bayan ya gama da zolaya Boss man yace"Big Guy, mutumin fa yau baya iya cin abinci da kanshi, ko zaka mashi abaki"? Big Guy na murmushi yace"If he gives me the opportunity to do that, I'll do it har wanka zan dinga yi mashi...."daƙyar Ya ƙare maganar ganin yadda Chief owais Ya ɗago da sexy eyes dinsa akan fuskarshi, cikin jin kunyar maganar daya furta ya sunnar dakai ƙasa Yana faɗin"afwan Sir, su6ul da baka nayi"


  Fuskarshi a ɗaure Ya furta"If you ever repeat this mistake, you'll spend the rest of your life in prison." Dariya Boss Man yayi jin abunda chief yace, Big Guy na murmushi aranshi Yana fadin"Ai bazan ma ƙaraba, Yanzun ma albarkacin boss man naci"


       Ajiye wayarshi yayi saman nightstand, Ya yunƙura Ya miƙe Yana faman Yamutsa fuskarshi, Big guy dake satar kallon damtsen hannun shi sai faman jinjina kanshi Yake Yi, dawowa yayi end bed din Ya zaune gaban glass table din dake shaƙe da abinci.


  Serving dinshi big guy Ya fara Yi, Ya miƙa mashi mug na coffee, Kafin Ya fara sha sai da Ya fara fadin"Boss bismillah" Man na murmushi Yace"A'a yalla6ai, Ni ina na isa In haɗa Kafaɗa dakai wurin cin abinci, kaima ka sani bamai yiwuwa bane, sannan Ni a ƙoshe nake, Madam ta girka min abinci na cika ciki na" 


  Ta6e baki Chief Owais Yai, ba tare daya ƙara furta komai ba.


  "Yaran fa har Yanzu bacci suke Yi yalla6ai, na lura ba ƙaramin gajiya suka yi ba, musamman Kyakkyawan matashin nan dake acikinsu, mai kama dakai,' yamutsa fuska owais Yai jin ance mai kama da shi.


    Fresh fruit ya soma ɗauka Yan sha, duk wani motsin shi akan idon Boss Man, Yaron ba ƙaramin burgeshi Yake Yi ba, ƙaramin mutun da halin girma, Idan kaji shekarun chief owais zaka sha mamaki, girman jikine kawai dashi da kuma babban matsayi da Allah Ya bashi, uwa uba Ya iya dattako.


  Boss man Yace"An kammala shirya masu breakfast dinsu, masu aiki suna can suna aikin jera masu, Yanzu su kaɗai muke jira su farka don su ci" ya faɗa yana duban fuskar chief, Jinjina kanshi ya ɗanyi batare daya ɗago da idona ba ya furta"hakan Yayi kyau"


   Miƙewa Boss Man Yayi"Ni zan shiga Cikin gidan, Ka ci abinci Lafiya our chief" Ya ambaci hakan tare da Juyawa Ya fuce daga ɗakin, Ya rage saura Big guy dake saving dinshi.

    

🤍EX-PRISONERS❤


Kwance take saman katafaren gadon ɗakin Danish, tun daren Jiya da suka ƙaraso kowannansu aka ware mashi ɗakin shi, mutun biyu ɗaki ɗaya, Danish ne kaɗai Aka mallaka mashi bedroom ɗaya saboda shine babbansu, Angel da Batul ɗakinsu daban, Azeeza da jamima ɗaki ɗaya, Parveen da Hanna suma nasu daban, Gabriel da Naufal room ɗaya, Javed da haris a ɗaki ɗaya.


Saboda Rashin lafiyar danish yasa ta gudo daga ɗakinsu ta dawo nashi tana matuƙar jin tausayinshi batasan wani abu ya same shi, gani take kamar idan tayi nesa dashi wani abu zai faru da shi, gown din Jiyace a jikinta red colour, tayi uban squeezing, hatta sumar kanta a haukece take babu gyara sunsha bacci kamar ba za su farka ba, daɗin lumbutsetsiyar katifar gadonne Ya sanya suka shagala, daga ita har shi garkuwan, ya cire suit jacket din jikinshi Iya farar shirt dince Ya bari, da gajeran wando fararen laps dinshi kamar ka ta6a jini ya ɗago tsabar hasken fatar, ya ɗaura kanshi saman wuyanta, yayin da hannayenshi biyu ke a ruƙe da waist dinta, zafin jikinshi ya daidaita bakamar da suna acikin jirgi ba zazza6i ya lullu6e shi, Yanzu ya samu sauƙi numfashinshi na fita cikin kwanciyar hankali, Sanyin A.c din dakin ya ƙara masu ƙaimi wurin Yin baccin nasu kamar matattu.


     Mutsu mutsu ya soma yi alamar zai farka, wata irin matsiyaciyar yunwace ta addabe shi, tun Jiya baici ko mai ba, ko ruwa bai gifta maƙoshin shi ba, Dogon numfashi yaja idanuwanshi sunyi mashi nauyi Ya gaza buɗe su, da wata irin kasalalliyar murya ya soma ambaton sunanta"My Angel! My Angel" badan la66ansa na akusa da wuyanta ba da kuwa zaiyi wuya ta iya jin muryarshi.


   Kamar an zungureta, a firgice ta farka tana faman zare gray eyes dinta haɗi da ambaton sunanshi"Danish are u okey? Ko jikin ne"?


   Daƙyar Ya iya janye head dinsa daga saman wuyanta Ya daura shi saman tattausan pillow, a hanzarce ta yunƙura Ta miƙe zaune tana faman mutsistsike idanuwanta da hannunta donta samu damar ƙare mashi kallo.


  "My man, yunwa ko"? Tun kafin ma ya faɗa mata abunda Yake Ji ta riga shi faɗi.

  Ɗaga mata gira yai alamar eh, murmushi ta ɗan sakar mashi har dimple dinta Ya lotsa"Danish banga ka yaba kyan ɗakinka ba, ko da yake baka acikin hayyacinka, saboda kana Jin Yunwa, bari naje naga ko zan samo maka abunda zaka ci, kafin in dawo ka shiga toilet kayi wanka, sai ka canza kayan jikinka" kamar ƙaramin yaro haka takeyi mashi magana.


  Wurga eye balls dinshi yayi akan katafaren ɗakin nashi, kamar na ɗan shugaban ƙasa tsabar haɗuwarshi.


  Saukowa Angel tayi daga saman gadon, tana tafiya tana waiwayon shi, daɗi kamar ya kashe ta, haƙika taji daɗin canjin rayuwar da suka samu, har ta fara tsara masu irin rayuwar jin daɗin da zasuyi, sai dai ta ɗan shafa'a da zancen kurkukun ƙaddara.


Tun da ta fito daga ɗakin take faman ƙwala ido tana kallon haɗuwar katafaren falon, Cikin sanɗa take Yin tafiya kamar 6arauniya, fararen ƙafafuwanta babu takalma, bata nufi ko'ina ba sai ɗakin su Azeeza a hankali ta zuge ƙofar ta faɗa cikinsa, tayi mamakin ganinsu a tsaitsaye saman bed mattress kowacce ta ruƙe pillow a hannunta, sai tsalle suke Yi suna fadin"gamu agidan daddyn Genie" dariyace ta kusa kubce mata da sauri ta toshe bakinta da tafin hannunta, wato su duk a tunaninsu gidan daddyn Genie ne aka kawo. yara sun zama ƴan hutu. Fitowa tayi daga ɗakinsu ta nufi ɗakin Parveen tana shiga ta sameta a zaune tsakiyar gado,  bacci yaƙi sakinta ga yunwa tana ji sai faman yin hamma take Yi, sumar kanta kamar ta mahaukaciya duk ta yamutsata, ta gimtse eyes dinta, hannah na akwance gefenta sai sharar baccinta take Yi.


   Ƙumshe dariya Angel tayi da sauri ta fito ta nufi ɗakin su Haris don ta duba su, lokacin data shiga ɗakin gaba ɗayansu bacci suke yi daga shi har javed duk sun cire suit jacket dinsu sunbar shirt da gajeran wando.


 Fitowa tayi dakinsu ta nufi, ɗakinsu Naufal, adai dai lokacin Gabriel Ya fito daga wanka, daga shi sai short, Ya ruƙe short toilet Yana tsane sumar kanshi, Naufal kuma yana zaune saman mirror chair Ya ƙura ma madubin ido da alama gabriel din Yake jira ya fito daga wankan shima Ya shiga.


 Gaba ɗaya basu lura da Angel ba, da zolaya gabriel Yace"mutumin kyau kake kallo a madubi naga tun ɗazu ka tasa shi agaba ko ƙyafta ido baka Yi"


   Ba tare daya juyo ya dube shi ba yace"Kai nake jira ka fito daga toilet din nima wankan nake son Yi"


  Gabriel Yace"amma dai kasan toilet din nan ba kalar na prison bane, akwai ruwan zafi dana sanyi kada kaje ka ƙona fatarka, kazo in nuna maka Yadda zakayi amfani da shi"


  Harara Naufal Ya watsa mashi"bana buƙata, nima zan Iya dakai na" gabriel na dariya yace"bana so ka yi danasani" miƙewa naufal yai ya nufi toilet din Ya shige, shigar shi ko minti ɗaya ba ai ba sai gashi ya fito Yana haɗe rai Ya kalli gabriel"nifa bangane komai ba" dariya ce ta kufce ma Angel gaba ɗaya suka juya suna kallonta, har ta juya zata gudu Gabriel Yai saurin zuwa ya ruƙo hannunta"Sister yaushe kika shigo? Ba sallama?

"6atan Hanya nayi, ni banma san na faɗo ɗakinku ba"


 Naufal Yace"kindai shigone yi mana leƙen asiri, kuma kinga abunda kikeson gani, gashi har kina dariya" girgiza kai tayi"wallahi ni ba abunda nashigo gani, ba ri ma in tafi" ta faɗa tare da Juyawa da sauri ta fuce daga ɗakin,


  Kallon Naufal Yai"muje ko" sai da ya fara murguɗa mashi baki, kafin Ya Juya suka nufi toilet din, Ya nuna mashi yadda zaiyi amfani da komai, kafin Ya baro shi a cikin toilet din.


   Tana cikin tafiya Muryar Batul ta katse mata hanzarinta"Angel"a firgice ta Juya tana kallonta, buɗe baki tayi haɗi da zare idonta, ganin Batul ta fito tana faman Yin hamma haɗi da Yin miƙa duk a lokaci ɗaya

  "Yaushe kika tashi"?

"Yanzu, na duba ɗakin banganki ba ashe kina anan" tunda ta fara magana idonta ba akan Angel Yake ba, Katafaram Falon take ƙarema kallo, kamar maijin tsoron shi, sai faman ƙyafƙyafta idanuwanta take Yi, bakinta hada Miyan bacci, kwata kwata babu natsuwa atare da ita, musamman sumar kanta tafi komai haukacewa.


 Miƙa mata hannu Angel tayi"idan zaki bini taho mu tafi, Nima kitchen nake nema, danish ne Yake jin yunwa" da sauri batul ta ƙarasa ta nufeta ruƙo hannunta tayi acikin nata, Har sun ɗaga ƙafa zasu motsa kwatsam muryar Ummin america ta katse masu hanzarin su"Where are you all going? Wa ya Baku iznin fitowa daga ɗaki"? Har saida gabansu Ya faɗi, duk suka sha jinin jikinsu, A hankali take saukowa down stairs, kimono robe ce a jikinta har ƙasa rigar takai mata, Tabi shape din jikinta, takalman ƙafarta high hills ne, hair wing din dake akanta launin black ne.


  Tana tafiya Hips dinta na jujjuyawa kamar ana kaɗasu, agabansu ta tsaya haɗi da Goya hannayenta saman tudun kirjinta tana kallonsu, idan ta kalli Angel sai ta kalli Batul, kamar wasu munafukai sunyi wuƙi wuƙi da ido, musamman Batul duk tasha jinin jikinta, saboda mugun jin shakkarta take ji, har ƙwara Angel ashirye take da tayi mata rashin kunya idan har ta ƙetare iyakarta.


  "Ke! Meye sunanki"! Ta jefa ma batul tambayar, muryarta na rawa ta furta"BATUL"! ta6e baki ummi tayi tare da daura idonta kan Angel"ke fa"?

  Ɗaure mata fuska Angel tayi kamar bazata tanka mata ba tace"UNAISAH" 

  "Me kuke nema ne"?


     

  💋ABBAN SOJOJI💋 

💋KURKUKUN ƘADDARA💋Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da kuma kurkukun ƙaddara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440  whatsapp din ya samu matsala, ga wadda za'a same ni da ita (08134387050) ayi mini magana ta whatsapp, message from Boss Bature


 ✍ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post