Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 27

Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 27

 


✊💋BossLadiesWriters💋✊

The return of Benazir  

        سجن القدر❤🤍❤Bayan fitar Hajjaty daga ɗakin Hajiya saratu, zafafan hawaye ne su ka wanke fuskarta, taji ɗacin maganganun da saratu ta faɗa mata, ita har ga Allah bada nufin komai taje kai mata abincin ba, dama Pravin ne ya bata shawarar ta rinƙa kyautata mata, wata'ƙil ta fara ƙaunarta, saboda ta faɗa mashi tana son su dinga shiri da matarshi.


Kafin tabar ƙofar ɗakin sai da ta ajiye tray din ƙasa, ta share ƙwallar fuskarta, tukunna ta ɗauka ta nufi ɗakin twins da niyar ta kai masu abincin wata'kil su ci.


   A lokacin Zayn yana zaune saman gado Ya tasa laptop dinsa agaba Yana operating dinta, zaid kuma Yana a kwance gefenshi hannun shi ruƙe da Wayar shi Yana daddanna ta.


    Sallamar hajjaty ce ta janyo hankulan su ga duban ƙofar ɗakin.


    Zayn tamkar bai ji ba yai shiru yaƙi amsawa sai zaid Ne ya amsa mata tare da bata Iznin shigowa ciki, A hankali ta shigo da tray muryarta asanyaya tace"barkan ku da hutawa, fatan kun wuni lafiya" da fara'a akan fuskar zaid ya ce"lafiya lou auntyn mu, yau ke ce da kan ki ki ka zo kawo mana abinci"? Ya yi maganar tare da ajiye wayar shi ya sauko daga saman gadon Ya nufe ta, zayn ko kallo bata ishe shi ba, baiwar Allah taji daɗin sakar fuska da zaid ya yi har cikin ranta taji ta ƙara ƙaunar shi.


  "Abincin ƙasar mu ne, ni na girka shi da kaina, na kawo maku ne don ku ɗanɗana" hannu biyu zaid yasa ya kar6i tray din Daga hannunta yana fadin"gaskiya kina ji da ƴa'ƴan nan naki, wallahi munji daɗi, kamar kinsan kuwa yunwa muke ji, Yanzu nake shirin kira akawo mana abinci mu ci"


    Asaman table ya ɗaura tray din, sai faman sakin murmushi take Yi yayin da take kallon fuskar zaid, buɗe warmer ya fara yi, ƙamshin Abincin ya daki hancinsa, Jinjina kai yai tare da ɗago da ido Ya kalle ta"Aunty, Ya sunan wannan haɗin"? 


 "Chicken tikka masala" ta faɗa still da murmushi kan face dinta.


  "Daga jin ƙamshin abincin zai yi daɗi, balle ma daya kasance hannu mai albarkane Ya girka sa" ya fada yana nade hannun rigarsa.


  "Zaid! Kada ka kuskura ka ci abincin nan! Kai baka da hankaline"? Ras taji gabanta ya fadi jin abun da zayn yace.


  Fuskar zaid a ɗaure ya dube shi"kaga bana son zancen banza, babu ruwanka dani, Kaja baki kayi shiru idan bazaka ci ba"


  Ya ƙare maganar tare da maida dubansa ga hajjaty "mun gode Aunty, Idan nagama cin abincin zaki ji feed back dina" jiki asanyaye ta amsa mashi da toh, da sauri ta fuce daga ɗakin tana faman sauke ajiyar zuciya.


  Ƙamshin Abincin da Zaid ke ci duk Ya cika mashi hanci da maƙoshi, dauriya ce kawai Yake yi, Yana danna laptop Haɗi da satar kallon Zaid, da gangan yake cuko spoon da abincin Yana turawa abaki, hada sambatun shi"wannan abinci kamar a aljanna aka dafa shi? Kai ka ji wani ɗanɗano mai daɗi, gaskiya duk wanda baici abincin nan ba an barshi a baya" Harara Zayn ya watsa mashi sam bai lura ba, saboda Ya bashi Baya.


  Ajiye spoon din ya yi cikin abincin, ya tsiyaya lemu mai sanyi acikin glass, Ya ɗauka Yasha rabi, Ya ajiye.


  "bari na ɗan shiga toilet" ya faɗa hadi da miƙewa da sauri Ya nufi toilet door ya shige, shigar shi ke da wuya Zayn ya janye laptop dinsa, cikin sanɗa Ya rarrafa saman mattress din zuwa gaban table din, Yana faman yamutsa fuska Ya ɗauki spoon Ya zura a plate din abincin aranshi yana fadin ba lallai ma abincin yai daɗi ba, mutuminka tun da yayi one spoon abaki, Tsabar daɗi kunnanshi har motsi suke yi, Yana ci yana satar kallon ƙofar toilet gudun kada Zaid Ya riske shi Yana cin abincin Hajjaty, a ƙarshe Ya ajiye spoon din Ya duma hannu ya ɗauko cinyar kaza Yadinga cizga Yana ci, Kusan Rabin abincin plate din ya cinye, ya ɗauki lemu Ya kur6a, Jin motsin za'a buɗe ƙofar toilet Yasa shi yin saurin sauke glass din lemun saman table, ko hannun shi bai goge ba, Da sauri Ya koma can saman gadon Ya jingina bayanshi jikin headboard ya ɗauki laptop dinsa Ya cigaba da operating dinta.


  Fitowa zaid Yai daga toilet, Yana faman yarfa hannun shi, Satar kallon fuskar zayn yayi, mutumin Ya haɗe rai babu annuri, Sai dai Ya manta bai goge bakinshi ba, yayi dama dama da maiƙon abincin da ya ci.


  Ƙayataccen murmushi zaid ya saki aranshi ya ayyana"babyn mommy ai nasan zaka aika, shiyasa na shiga toilet don na baka damar ka ci, ɗan rainin wayau anaso ana kaiwa kasuwa" Ya faɗa Yana zama bakin gadon, da zolaya yace"Zayn ya akai naga abincin dana rage an ci shi"?


  Muryar zayn ba wasa yace"ka tambayi wanda kaba ajiya, Ni meye ruwana aciki"? Gumtse dariya Zaid yai"amma dai da kunya wallahi, Ni dai nasan babu 6era agidan nan" rai a6ace zayn yace"ban san iya shege zaid, Uban waye 6eran"? 


  "Ai ni ban kama suna ba, kawai nayi maganata ne" dogon tsoki Zayn yaja yana faman hura hanci, Aranshi ya ayyana Ina ma zaid Ya rage abincin da kuwa ya cinye shi duka, don ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba.


   

SIR MUBARAK🤍A Hankali Yake tafiya Yana tunkarar ɗakin Dr. Jazz, Daga shi sai short A jikin shi da singlet, Tura ƙofar Yayi baiga kowa a ɗakin Ba, shiga Ciki Yai Yana bin ko'ina da Kallo zanin gadonshi a hargitse Takalman shi Yashe saman floor, tunani ya shiga yi aranshi ko ina ya shiga? Ko dai yana a toilet ne Ko ya shiga Garden, Yanke shawarar zuwa garden ɗin ya yi don Ya dubo shi, Ahanzar ce Ya juya da niyar ya fuce kwatsam Muryar Jazz ta katse mashi hanzarin shi.


   "Oh tsayawa za ka yi Kana kallonta? Babu abun da zaka Iya yi mata? Sai kace ba ka san Hanyar da zaka kashe ta ba idan haukanta Ya motsa"! wani irin bugu zuciyar Sir Mubarak Tayi Jin Kalmar Kisa, A firgice ya juya baya Yana bin toilet door ɗin ɗakin da kallo, don Ya fahimci acikin toilet yake Yin wayar, Cikin tafiyar sanɗa Sir Mubarak Ya nufi ƙofar toilet Ɗin Ya kanga kunnan shi Yana sauraron shi.


  "Ai ba dole Saina zo ba, Kaima zaka Iya sarrafata, Idan taƙiya Kawai ka bi Hanyar da nace maka, ka kashe ta kowa Ya huta," shiru Ya ɗanyi can kuma yaji yaci gaba da cewa"ba yadda za'ai inzo, Ina tsoron asirina Ya toni, hmm bakasan halin da nake aciki ba, ko jiya saida na kamo Hanya zanzo gidan, ganin ana bin motata yasa na karya kwana na nufi asibiti, saboda raina ya bani akwai wanda ke bin diddigina dole Inyi takatsantsan" 


   Hankalin Sir Mubarak Ba ƙaramin tashi yai ba, sai faman jinjina kanshi yake Yi, Bai ta6a tsammanin Jazz Yana da wayau ba sai Yau, Har yasan Ana bibiyarshi wato shine Ya canza Hanya, Hakan ya ƙara tabbatar mashi da zargin shi akanshi.


    

"What are you doing here, baby?"


Muryar Turai ce ta ratsa kunnanshi, Hatta dr Jazz dake a toilet, Sai da Ya ji sautin muryar mutun a ɗakin shi, a yayin da yake atsaye gaban sink, wandon crazy jeans ne da shirt a jikin shi, da sauri Yai rejecting call din Ya tura wayar cikin aljihun wandon shi, Jikinshi Ya hau Yin kerma, Tsananin fargabane Ya kama shi, A hankali Yake tafiya yana nufar ƙofar fita, Kafin fitowarshi da sauri Sir Mubarak Yai wuff Ya nufi Turai dake kallonshi da mamaki akan face dinta ganin Yadda ya ke yima Jazz la6e a ɗaki, Harta buɗe baki zata ƙara yin magana ya yi saurin sanya faffaɗan tafin hannunsa Ya toshe mata bakinta, tare da janta zuwa wajen ɗakin.


  Lokacin da Jazz ya fito daga toilet din zufa na bin fuskarshi, ya dubi ko'ina baiga mutun ba, Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, har wajen ɗakin Ya leƙa bai ga kowa ba, Hakan yasa shi kokwanton wata'ƙil Kunnuwanshi ne suka jiyo mashi ba dai dai ba, hankalinshi ya kwanta, komawa ya yi cikin ɗakin Ya kwanta saman gadonshi, yayin da idanuwanshi ke fuskantar ceilling, ga dukkan alamu wani abu yake tunanowa wanda yasa shi fitar da ƙwalla a idon shi.A bedroom Sir mubarak Ya shigar da turai suna tsaye suna kallon juna, kallon tuhuma take bin shi da shi.


"Nayi mamakin ganinka a ɗakin Jazz kana yi mashi la6e, meyasa"? 


 Fuskarshi a murtuke babu annuri yace"laifi ne don uba ya shiga ɗakin ɗanshi"? Aruɗe tace"ba laifi bane, amma meyasa kake yi mashi la6e"? Shiru ya yi yana duban fuskarta, A yadda suke atsaye suna fuskantar juna, Ko kafaɗarshi bata kai ba, saboda ƙarantarta, doguwar rigace a jikinta ta shan iska, ta tufke blonde hair dinta da ribbom.


  "Ka tsare ni da ido kana kallona, Baka bani amsar Tambayata ba"! a ƙagare ta faɗa, Ya rasa ya zaiyi ya kawar da hankalinta daga tambayar da take yi masa.


 Dubara ce ta faɗo masa, da sauri Ya sanya Hannu biyu ya ruƙe waist dinta, sama ya ɗaga ta kamar ɗiyar roba Ya kwantar da ita saman gadon shi Rumfa ya yi mata da faffaɗan kirjin shi, tuni tasha jinin jikinta.


  "Kin tsareni da tambaya ke ga mai ɗa ko? Ni da ke waye yafi wani iko da shi? Yawu ta haɗiya muryarta na ɗan rawa ta furta"kai"


  "Kinsan da hakan shine kike yi min tambayoyi kamar ƴar jarida"? Shiru tayi mashi tana faman zazzare green eyes dinta. 

  "Jibarki ƴar mitsila dake kamar in matseki nake ji" dariya ce ta kubce mata, natsuwa yai yana kallon fararen haƙoranta.


  "Yanzu dai faɗamin me kike shiryawa a birthday din Baba? Ba za kiyi kitso da ƙunshi ba"?


"Idan zaka kai ni inda za'ai min kitson da ƙunshin inaso, sai dai anko din da zasu sanya nasan hajiya saratu bazata barni in shiga cikinsu ba ko da na siya" a marairaice ta ƙare mashi maganar.


  Jan hancin ta ya yi da hannun shi"Ina ruwanki da ita? Ai ba dole sai kin shiga cikinsu ba, babban tarone fa za'ayi akwai manyan baƙi da zasu zo, kema zaki samu ƙawaye acikin su"


 Da shagwa6e ta furta"baby ba zaka gane ba, hajiya saratu bata son ganina, ita fa haryan zu kallon ƴar aiki take Yi mini, hada faɗa min wai ba ata6a canzawa tuwo suna, ni dai inajin fargabar ta disgani acikin su, ƙwara Inyi zamana acikin gida zai fiye min kwanciyar hankali" daƙyar ta ƙare maganar ganin yadda ya tsare ta da ido, kallon so da ƙauna ya ke yi mata.  "Meyasa kike kira na baby? Ko kunya bakya ji? Nayi maki kama da ƙaramin Yaro ne?" fuskar shi a ɗaure yai mata maganar.

  Kashe mashi ido ɗaya tayi"I call you baby because you're like a baby to me, and I still take care of you kuma ina feeding dinka" ɗan zaro mata ido ya yi da sauri ta rufe baki tana faman zazzare mashi ido.


  Da zolaya ya furta"raini ya fara shiga tsakanina dake, saboda ina tu6e kaya agabanki ko"? Runtse mashi ido tayi tana faman tiƙar dariya.


  Jinjina kanshi yai"ki saurare dakyau, daga yanzu idan saratu ta faɗa maki magana ki dinga mayar mata da martani, ki daina nuna kina jin tsoronta shiyasa ta rainaki, Kina jina ko"? Tana faman zumbura mashi pink lips dinta tace"ni bazan Iyaba, saboda ta girmeni ko a shekaru kuma ƙanwarka ce,"


  "Umarni nake baki ba shawara ba, kada na kuskura na ƙara ganin kin dawo gidan nan kinayi min jan ido akan saratu tayi maki wani abu, idan ba haka ba zaki kar6i horo mai tsanani daga gareni," muryar shi a kausace yake yi mata maganar

  Kama kunnanta ya yi da yatsan hannun shi"Idan kunne Ya tsira"? Da sauri ta ƙarasa mashi karin maganar"Jiki Ya tsira My baby" murmushi yasaki tare da manna mata kiss saman soft lips dinta.


GIDAN ƊAN IYA


Zahra ce zaune saman prayer mat, ta zumbula dogon Hijabi, fuskarta sharkaf da hawaye, tun da ta kammala sallar Magrib bata motsa ba, hannunta ruƙe da cazba sai faman janta take Yi, damuwar duniya ta isheta, tun ɗazu data farka daga bacci ta kasa Yin wanka ko abinci bata ci ba, babu kuma wanda yai tunanin ya leƙo ta, tayi trying kiran layin mahboob yaƙi picking call din, har yanzu bai leƙo cikin gidan ba, ga lokaci yana ta tafiya gani take yi kamar ana ƙara gudun agogon ɗakinta, hannayenta biyu ta ɗaga sama tana jera addu'o'i akan Allah Ya kawo mata mafita.


   Muryar Aneelerh ce ta ratsa kunnanta"Yar uwata rabin raina, tun safe baki ci komai ba, Ga abinci na kawo maki" Shafa tafin hannunta tayi saman fuskarta, Rai amatuƙar 6ace ta yunƙura ta mike haɗi da fuskantar Aneelerh, dake tunkarota, hannunta ruƙe da madaidaicin tray, mai ɗauke da plate din shinkara da ƙaramar warmer ta miya, tare da lemu mai sanyi.


   Kafin ta ƙaraso zahra ta dakatar da ita ta hanyar yi mata magana"Aunty Aneeleeh idan kin kawo abincin nan domin in ci ne to ki maida shi kitchen! Bana buƙata" a faɗace ta furta.


  "Haba zahra, kashe kanki ki ke so Ki yi ne? Tun safe baki ci komai ba, Ni kaɗai na damu dake, dan Allah ki kar6a ki ci"


 Harara zahra ta wurga mata cikin 6acin rai tace"Ai ni kingama zubda girmanki a idona, tun da har kika iya bani shawarar In amince wurin aikata sa6on Allah, Kin ban mamaki aunty aneelerh, bansan haka kike ba" tana magana tana jan majina.


 Jinjina kai Aneelerh tayi"Laifina ne zahra, Ni da na damu dake shiyasa kike gaya min magana son ranki, daga taimako? Daga yau ka da ki kuma tsammanin zan ƙara baki shawara idan har baki kar6i abincin nan ba" wani ɗan iskan kallo Zahra ta watsa mata, har saida ta dasa aya amaganarta tukunna zahra ta ruƙe qugu kamar ana tunzurata tace"Idan har kin damu dani, meyasa ba zaki taimaka mu nemi mafita atare? Saima ƙoƙarin da ki ka yi don ganin kin sanya ni a gur6atacciyar hanyar da zan lalata duniyata da lahirata, ke ba mai ƙaunata bace aunty Aneeleeh, bana sonki kuma bana son ganin ki!, Yakamata ki nisanta kan ki dani, Idan ba haka ba zan yi maki rashin mutuncin da baki ta6a tsammani ba!!" 


A kausashe Ta furta maganar tana nuna Aneelerh da cazbahar hannunta kamar zata rufe ta da bugu.


 Gyaɗa kai Aneelerh tayi tama rasa bakin magana, kalaman zahra sun bata mamaki, bata ta6a tunanin zahra zata Ya furta mata su ba.


  Juyawa ta yi da sauri ta nufi ƙofar fita, adai dai lokacin Mahboob yana ƙoƙarin shigowa ɗakin suka ci karo da Aneelerh, har gaishe ta ya yi amma ko kallon shi ba ta yi ba, hakan yasa shi tsammanin ko wani abu Ya faru ne.


 Zahra na jin sallamar shi da sauri ta sanya hannu biyu ta share hawayen dake akan fuskarta, komawa tayi daga gefen gadonta ta zauna tana dubanshi.


  Riga da wandon shadda ne ajikinshi, hannun shi ruƙe da key din motar shi.


  "Zahra Lafiya ki ke yi mini kiran talauci? Ina akan hanyar dawowa gida naga miss calls dinki, Allah dai yasa lafiya"

 

 Cikin sanyin murya tace da shi"ka zauna mahboob mu yi magana" zama yai da ɗan mamaki akan face dinsa yace"meyasa ki kuka? Naga idanuwanki sun kumbura wanene Ya ta6a ki? Ko ke da aunty Aneelerh ne"?


 A hanzarce ta girgiza mashi kai tana faɗin"bakomai, banajin daɗi ne kaina ke ciwo"


  "Kin sha magani" cikin kulawa yake yi mata magana, ɗaga mashi kai tayi alamar eh ta ƙara da cewa"Aunty Aneelerh ce ta bani maganin"


  Gyaɗa kai yai"okey, Allah ya sawaƙe sister yanzu dai faɗamin me kike buƙata ne Kin dai san ban da ko sisi"


 Murmushin takaici tasa kar mashi jin abinda yace


  "Mahboob ba kuɗi zan roƙe ka ba, taimako nakeso kayi min dan Allah, bana son ka tambayeni dalili kawai ka yi abun da nace maka, kuma bana son kowa Ya sani daga ni sai kai"


  "Kada ki damu, Ina jin ki" a ƙagare Ya furta mata hakan

  "Inason zan siyar da motata ne da wayata, saboda ina buƙatar kuɗi ko akwai wanda ka sani da zai Iya siya a yau din nan'? Ta jefa mashi tambayar tana duban fuskarshi.


  Mamakine ƙarara akan fuskarshi, Har saida Yaɗan saki baki da ido Yana dubanta Kafin yace"ke kuwa me zai ja ki siyar da motarki da wayarki? Runtse ido ta dan yi hawaye na ƙoƙarin cin ƙarfinta tace dashi"Mahboob banason tambaya! Kawai ka taimaka mun in zaka Iya in kuma ba za ka yi ba to ka tashi ka tafi kaban wuri"


  "Shikenan Naji, nayi shirun, amma dai kinsan kowa zai saye su sai kin faɗi ko? Ba lallai asamu wanda zai siya da mutunci ba"


  Ɗaga mashi kai tayi "Ni wannan ba damuwata bace, indai kuɗin zasu kai 4m Ya wadatar"


  "Okey, amma ni shawarar da zan baki mai zai hana ki bada motar da wayar taki jingina? Idan kika samu halin biyan kuɗin sai ki Kar6o Kayan ki, zahra kinsan babu mai siya maki su idan kika rasa na hannunki kuma ni bazan juri ara maki motata ba" Ya faɗa Yana yamutsa fuskarsa, Harara ta watsa mashi da rinannun idanuwanta"kai fa banza ne wlh, Ni ina ruwana da motarka? Koda zan rasa abun hawa mahboob bazan ta6a aron kayanka ba"


 Murmushi ya ɗan saki tare da miƙewa yace"to Aunty zahra, Ni zan tafi, in sha Allah zan samu wanda zai siya, amma ki sani zamu kasa kuɗin gida uku, Ki kwashi kaso biyu ni kuma ɗaya...."


 Tunkan ya ƙare maganar zahra ta rarumi pillow aguje tabi shi da gudu ya fuce daga ɗakin Yana tiƙar dariya muryarta ashaƙe take fadin"wallahi mahboob ka fita idona, Ni ba tsarar wasanka bace, kuɗin nan da gumina na tarasu bada gumin wani ba' rai a6ace take yin maganar, bayan ta gama zazzaga mashi masifar ta juya ta koma cikin ɗakinta tana faman tallabe cikinta dake yi mata kukan yunwa.


  Safa da marwa ta soma Yi A tsakar dakin duk ta ƙagara da jiran kiran mahboob, Fatanta Allah yasa asamu wanda zai sayi motar.


  Wuraren ƙarfe 8 na dare, Kiran mahboob Ya shigo wayarta jiki na rawa ta ɗaga ta kara a kunnanta, Anan yake sanar da ita cewa abokinsa Ya ce yana so harma sunyi cinikin motar akan miliyan uku da rabi zai siyeta, ita kuma wayar zai siyeta dubu ɗari biyar idan ta bari ahakan zuwa gobe da safe zai kai mashi Motar da wayar, daga nan zai  tura mashi kuɗin, tsabar farin Ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha, duk da tayi asara ba kaɗan, saboda an karya kuɗin motar da wayar, amma hakan bai dameta, burinta ta sauke nauyin dake akanta, Bayan sun gama wayar, ta zuƙunna takai goshi ƙasa tana godiya da Allah, daga bisani ta mike tana tiƙar rawa, da gudu ta fito daga ɗaki ta nufi kitchen, ta ciko plate da abinci, ta buɗe frigde ta dauko lemu mai sanyi kafin ta dawo ɗakinta, ita kadai ta zauna tsakiyar gado tana ci tana sakin murmushi, baƙin cikinta ɗaya ta rasa damar da take da ita na zuwa Obie estate, tunawa da wannan yasata rushewa da kuka ga abinci cike abakinta.


JOS CITY


Dare ya tsala sosai, Gari yayi duhu, a lokacin da kowani mahaluƙi yake a makwancinsa domin runtsawa, baka jin sautin komai saina kukan tsuntsaye dana karnukan Layi dake Hargowa.


  A hankali take tafiya Hannunta ruƙe da trolley, doguwa ce a halitta, siririya bata da ƙiba sai dai tana da hips, doguwar jallabiyace a jikinta, ta sanya niƙab ta rufe fuskarta, abun da zai baka mamaki ita kaɗai take Bin santar babu alamun tsoro atattare da ita, da taimakon street light ta ke samun damar ganin ko'ina, Har Allah Ya nuna mata gidan da take nema, Katafaren Villa ne Mai gingirimeman gate.


    da sassarfa ta nufi gate din, tana zuwa gabanshi, Takai hannu ta soma ƙwanƙwasa ƙofar, tun tana yi a hankali har takai ga tsunto dutse ta cigaba da bugun ƙofar da shi kamar zata 6alle gate din'


 Security officers din dake tsaron gidan guda Biyu ne cikin kakinsu suka fito daga ɗakunansu jiki na rawa suka ƙara so gaban gate din, da alamun mamaki akan fuskokinsu suka haɗa bakin wurin furta Wanene ke buga mana ƙofa a dai dai irin wannan lokacin"! Da fargaba suka furta maganar.


  Cikin shessheƙar kuka da muryarta mai tsiwa ta furta"BENAZIR CE"


 kallon Juna Officers din suka Yi, ɗaya yace"Wanene kuma haka? Mutun ko aljan? Wa ki ka zo nema agidan ko dai kin yi 6atan Hanya ne"


   Tamkar zata fashe da kuka tace"dan Allah ku buɗe mun gate in shigo, ni ce benazir ɗiyar Alhaji ubaid"!


  Ba ƙaramin ɗaure masu kai lamarin yayi ba, kasancewar su tsoffin masu gadin gidan, sunsan wacece benazir Yarinyar uban gidansu data 6ace tsawon shekara goma sha shidda, kokwanto suka soma Yi anya kuwa itace?


  Officer mai gemu yace"kai, Da wuya ya zama gaskiya yarinyar da babu tabbacin tana araye kota mutu"!


 Ɗayan kuma yace"Ai ni banma yarda ba gaskiya, Kusan shekara goma sha shidda da 6atanta sai Yau ƙarfe sha biyu na dare zata dawo! anya kuwa ba tarko bane aka ɗana mana"?


 Mai gemu yace"amma kuma muryarta sak kalarta hajiya layla, Har tsiwar iri ɗaya da tayi maganar" 


 Jin sunƙi buɗe mata kofa yasa ta rushe masu da kuka mai sautin gaske a faɗa ce ta ke fadin"wai baza ku buɗe mun gate ba, na gaji da tsayuwa wallahi idan baku buɗe ba na shigo cikin gidan saina Sa an kore ku"


 Yawu suka haɗiya atare mai gemu yace"Ke baiwar Allah, ba yadda za'ai mu buɗe maki gate ba tare da mun sanar da masu gidan ba, dan haka ki ƙara haƙuri mu faɗa masu"


 Kafin suyi yunƙurin zuwa cikin gidan su sanar masu, ba zato ba tsammani suka ji ta bangaje ƙofar jikin gate din dake a kulle, nan take ƙofar ta buɗe, hankalin su ba ƙaramin tashi Yai ba, A firgice suke dubanta yayin da take shigowa ciki da akwatinta, Ko kallo basu isheta ba, da sauri ta nufi cikin gidan.


  Kasa motsi suka yi Kamar an dasa masu Aya, tuni zufa ta wanke fuskokinsu, Mamakin su Taya akai ta Iya bugun ƙofa da ƙarfi Har jamlock mai ƙarko Ya zame kanshi! Tabbas suna hasashen ba mutun bace aljana ce, tuni suka sha jinin jikinsu.


     Tana tafiya tana bin ko'ina na gidan da kallo, abubuwa da dama sun canza mata ba kamar yadda ta tafi tabarshi ba.


  Adai dai lokacin Zainab mai aikin gidan tana a palour hannunta ruƙe da floor wiper tana goge tiles, ta saba ba tun Yau idan bata son aiki Yayi mata yawa takan fito har tsakar dare Tana aikace aikacen ta don ta rage wasu ayyukan na safe duk idan taji ƙarfi a jikinta.


    Tamkar da rana saboda hasken Ƙaton kwan dake a falon Ya gauraye ko'ina, Hankalinta kwance ta duƙufa tana gudanar da aikinta ba zato ba tsammani taji an banko ƙofar falon.


   A firgice Zainab ta ɗago tana kallon matar da ta fado cikin falon afujajen, tsabar firgitar da ta yi har batasan sa'adda ta jefar da wiper din hannun ta ba, tun daga ƙasa har sama take kallonta, Hankalin ta ba ƙaramin tashi yai ba, tsananin tsoro Ya kamata, Jikinta ya hau yin kerma, Muryarta na rawa ta furta"baiwar Allah wacece ke? taya ya akai kika shigo gidan nan? Ƙarfe sha biyu na dare"? Aruɗe take jefa mata tambayar.


  Shessheƙar Kukan matar ne Ya ƙara firgitar da ita, ta soma Ja da baya tana ƙoƙarin guduwa cikin gidan don ta faɗo ma Hajiya layla abun da ke faruwa sai dai kafin Ta juya muryar Matar ya ratsa kunnanta cikin harshen larabcin take faɗin.


  "AUNTY ZAINAB NI CE BENAZIR!! INA ABBANA! INA UMMI NA! INA MIJINA DA ƳA TA!!! A jere ta jefa mata tambayoyin.


Har abada ba zata ta6a mantawa da muryar nan ba, koda kuwa amafarkine Ta jita tabbas zata shaida mamallakiyarta.


   A hargitse Ta juya Tana dubanta, A hankali benazir ta ɗaura ziraran yatsun hannun ta farare tas ta ruƙo ƙasan niƙab ɗin fuskarta ta ɗage shi sama" tsabar kiɗima da ganin fuskar da tayi kimanin shekaru sha shidda ba ta yi tozali da ita bane yasa Jikinta ya hau yin kerma, tsantsar mamaki da al'ajabi ne akan fuskarta, ta zazzare idonta akan kyakkyawar fuskar benazir, sam takasa yarda da abun da idanuwanta ke nuna mana gani take yi tamkar mafarki ne take Yi!!

 

Tayi wani irin haske Kamar ka ta6a jini ya ɗigo, Fuskarta sharkaf take da hawaye ta ko'ina, ga zufa dake tsastsafo mata sam babu kwanciyar hankali atattare da ita.


  Tsantsar tashi hankaline Akan fuskar zainab, Muryarta adabarbarce ta furta"be..be..nazir! Dagaske ke ce ko dai idanuwana ne suke nuna min ba dai dai ba"?


  Da ƙarfi ta furta"Ni ce Aunty zainab! Ki amsa min tambayoyin da nayi maki"!


Tana faɗin hakan Nan take Ta yanke jiki Ta faɗi ƙasa a sume, akwatin hannunta ya kife saman floor.


  Juyawa Zainab tayi da gudun gaske ta nufi ɗakin hajiya layla, Hada yin tuntu6e tsabar sauri, tunkafin ta ƙarasa ta soma ƙwala mata kira na fitar hayyaci tamkar maƙoshin ta zai 6allo waje.


  "Hajiya layla! hajiya layla"


 Kaitsaye kiran ya daki dodon kunnuwan su daga ita har Alhaji ubaid dake kwance saman katafaren gadonsu, A firgice suka farka a lokaci ɗaya suka miƙe zaune suna ambaton Sunan zainab.


  Doguwar jallabiya ce a jikin alhaji ubaid wuyan rigar ya karkace, Hajiya layla kuwa Rigar Bacci ce a jikinta, da sauri Alhaji ubaid ya kunna bedside lamp din ɗakin.


    Sam babu kwanciyar hankali atattare da su, duk sun ƙura ido suna jiran ganin ta inda zainab zata 6ullo.


   Kamar daga sama suka ji ta banko ƙofar ɗakin tana faman Yin haki.

 Da mamaki Akan fuskar Layla tace"Zainab baki da hankali ne? Ko kin makance ne? Taya zaki faɗo mana ɗaki a irin wannan lokacin ba tare da kin nemi iznin shigowa ciki ba"!


  Kafin zainab ta bata amsa Alhaji ubaid Ya katse mata hanzarinta da cewa"Zainab Lafiya kike ƙwala mana kifa? Kowani abun ne Ya faru"?


  Cikin rawar murya ta furta"dan Allah kuyi haƙuri ku yafe ni, bana acikin kwanciyar hankalina ne shiyasa na faɗo maku ɗaki ba sallama nasan bai dace ba" dogon tsoki Layla Taja"Ba dogon bayani na tambaye ki ba, Ki faɗi min uban mi Ya kawo ki ɗakin mu? 


Bata kai ga ƙarasa maganar ba, Alhaji ubaid Yai saurin katse ta da cewa"Ya isa haka, Haba kin cikata da faɗa, Kin ƙi bari tayi mana bayani dangane da abunda ke faruwa" tsuke fuska Layla Tayi.


  Cikin sanyin murya zainab tace"dama BENAZIR ce ta dawo!"


 Kallon juna Alhaji ubaid da layla suka Yi lokaci ɗaya, kafin suka dawo da dubansu ga zainab, Har suna haɗa baki wurin tambayar wacece Benazir!! Tsabar ruɗanin da suka shiga

 Zainab tace"benazir ƙanwar dr shureim Ƴar wurinku itace ta dawo, Yanzu haka tana acikin palour ta yanke jiki ta faɗi a sume.


  Girgiza kai layla tayi haɗi da cewa"baki da hankali zainab, dama na fara zargin kin fara shan ƙwaya, In ba haka ba, ta ya ya benazir da ta gudu da ƙafafuwanta zata dawo gida! bazai yiwu ba.


 Alhaji ubaid Yace"ko dai mafarki ki ka yi ne zainab? Girgiza mashi kai tayi hada hawaye akan fuskarta tace"wallahi dagaske nake yi zaku Iya zuwa palourn ku duba benazir ce da kanta ta dawo"


  Kusan atare suka sauko daga saman gadon, da sauri zainab ta basu hanya suka fuce har suna bange juna tsabar sauri.


  Tunkafin su ƙarasa falon suka soma hango mutun kwance saman floor da baƙaƙen Kaya ga trolley dinta a gefe ɗaya, kasancewar ta yaye niqab din fuskarta hakan ya basu damar ganin fuskarta, wani irin mahaukacin bugu zuciyarsu tayi A matuƙar gigice suka furta sunanta"BENAZIR" adai dai lokacin gate security officers din gidan suka shigo falon da sallama sam babu kwanciyar hankali akan fuskokinsu ganin Yanayin mutanan gidan yasa suma suka ƙame suna faman zare ido.


   Muryar Hajiya layla Na rawa ta furta"wallahi itace Benazir ɗina ce, Yarinya tace data 6ata, itace ta dawo da kanta" ta ƙare maganar jiki na 6ari ta nufi gaban Benazir dake kwance ta zube saman gwiwowinta tare da kai hannu ta ruƙo niƙab din fuskarta ta ƙarasa cire mata shi, Kowa dake a falon saida yai matuƙar Al'ajabin ganin Benazir, yalwataccen gashin kanta har gadon bayanta Ya nannaɗe kamar taliyar indomie, babu alamun wahala atare da ita, sai ma hutun dake kwance saman farar fatarta, wani iko na Allah, gaba ɗaya Jikinta Ya jiƙe da ruwan zufar dake tsastsafo mata, hatta baƙar jallabiyar jikinta ta manne ma fatarta saboda zufar data wanketa, ga wata zufar dake kurɗaɗowa ta cikin sumar kanta ta jiƙe sharkaf duk da sanyin A.c din falon.


  Rushewa da kuka Hajiya layla tayi haɗi da ɗaura Hannayenta biyu saman kanta tana fadin"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Dan Allah kuyi wani abu akai mana kun tsaya kuna kallonta, sai kace baku gane ta ba, ɗiyata ce benazir Allah Ya dawo mun da ita da ranta" Sautin kukan ta ya cika ɗakin, Zainab ma tuni ta fashe da kukan farin ciki, security officers dake tsaye Jikinsu ya yi mugun yin sanyi, da farko sunyi tsammanin ba mutun bace amma daga bisani Bayan ta shigo cikin gidan suka dudduba ƙofar donsu tabbatar mutun ce ba aljana ba, ashe Jamlock ɗin ƙofar gate dinne basu kulle shi ba sun manta, shiyasa har ta samu damar sanya ƙarfi ta bangaje ƙofar ta shigo ciki.


  Mamaki da al'jabi sun Hana Alhaji ubaid motsawa Ya kafe fuskar Ƴar tashi da ido Yana kallonta, ruwan hawaye ne kwance acikin idanuwanshi haƙiƙa ya yi farin ciki mara misaltuwa kusan shekara goma sha shidda Yau rana ɗaya Allah Ya kaɗo masu da hankalinta ta dawo wurinsu, Allah ne kaɗai Yasan uwa duniyar data shiga.


  Cikin shessheƙar kuka zainab tace"yakamata muyi wani abu akai, Benazir tana buƙatar taimakon gaggawa, ga dukkan alamu wani abunne Ya faru da ita wanda Ya haifar mata da fitar da gumi a jikinta"


   Da sauri Alhaji Ubaid Ya sanya Hannayenshi biyu, Ya cuccu6eta Ya juya ya nufi sofa mai mazaunin mutun uku Ya kwantar da ita, kallon zainab yai"je ki ɗauko min wayata a ɗaki" ta amsa mashi da toh, da ɗan gudunta ta nufi bedroom dinsu.


   Jiki amace layla ta miƙe ta koma saman sofa hand din da benazir ke akwance ta zauna tana duban fuskar ƴartata Kamar Ta haɗiyeta haka take ji.


  "Alhaji kun tabbata benazir ɗinmu ce ta dawo"! Mai gemu ne Yai mashi Maganar, Jinjina masu kai Yai"babu shakka itace Allah ya dawo mana da ita" Ajiyar zuciya kowan nan su Ya sauke tsantsar farin ciki Ne Ya kamasu.


  "Muna tayaku murna, ita kuma muna yi mata fatan Allah Ya bata lafiya, Ubangiji Allah yasa ƙarshen wahalarta kenan, sannan Alhaji Muna baku shawarar a kira malamin da zai dubata don yanayinta dana gani a matsayina na wanda yake da sani a 6angaren sihiri, Yarinyar ka ba likita take buƙata ba, Malami take buƙata saboda duk wasu alamomi na jikinta sun nuna kamar sihirine daya daɗe a jikinta ya kwance !!! A firgice Alhaji Ubaid Da Hajiya layla suka ɗago suna duban mai gemu da yayi maganar, jinjina masu kai yayi"ba yau na fara ganin irin hakan ba, ina da tabbacin Yarinyar nan kurciya aka yi mata, amma idan kunaso ku gasgata zance na ku kira babban malamin da zai dubata" sam sun kasa magana sai bin shi da kallo da su ke Yi.


 Daƙyar Hajiya layla Ta iya buɗe bakinta la66anta na kerma tace"amma benazir da ƙafafuwanta ta gudu tabar gidan tajudden Bayan ta haihu tabar mashi jinjira a cikin kwamin wanka, tayaya hakan zai yiwu? Wanene zai yi mana hakan? 


 Girgiza kai mai gemu yai"haka zakuyi tunani saboda bakusan dalilin tafiyarta ba, amma abun duba anan tayaya Uwa zata gudu tabar jinjirin ɗan da ta haifa ta hanyar raya sunna!! Duk irin soyayyar dake tsakanin uwa da ɗanta? Sannan idan har dagaske benazir ta gudu don son ranta tsawon shekara goma sha ɗaya meyasa zata dawo da ƙafafuwanta ba'a cikin Hayyacin ta? Ga zufa duk ta wanke suturar jikinta, Nidai shawarar da zan baku shine a tuntu6i malamin da zai dubata"


   Jinjina kai Alhaji ubaid ya yi shi kanshi jikin shi ya yi sanyi da zancen Mai gemu, saboda akwai ƙamshin gaskiya a kalamanshi.


 Shigowa falon Zainab tayi hannunta ruke da wayar Alhaji ubaid Ta miƙa mashi, Yasa hannu Ya kar6a.


  "Dare Yayi yanzu, kada mu katse ma wani baccin shi, shawarar da zan bada shine a ɗebo ruwa a yayyafa mata in sha Allah zata farka, zuwa asuba sai a kira malamin da zai dubata" mai gemu ne Yayi maganar, muryar Alhaji ubaid a sanyaye yace"Inaso zan kira Dr shureim ne, saboda a irin wannan lokacin baya runtsawa Idonshi biyu Yana tashi domin Yin nafilfilin dare" ya ambaci hakan tare da Danna wayar hannunshi ya buga ma dr shureim Kira ta soma ringing.


  Kallon zainab Hajiya layla tayi idanuwanta sun kaɗa jawur tace"ɗauko mun ruwa a fridge " amsa mata zainab tayi da toh, da sauri ta nufi hanyar kitchen.


  Dafe kai Hajiya layla tayi da hannu ɗaya, Sumar kanta duk ta tarwatse saman bayanta, ta manta da yanayin jikinta, don ma babu wanda ke acikin natsuwar shi, hankalinsu na akan Benazir.


  Bayan zainab ta dawo, hannunta ruƙe da bottle water me sanyi ta buɗe murfin ta miƙa ma Hajiya layla, Yayyafa mata tayi saman fuskarta, nan take ta sauke nannauyar ajiyar zuciyata muryarta da tsiwa take fadin"ina mahaifiyata Ina mahaifina! Ina mijina da ƴata Ina yayana shureim, suna ina ! Na shiga uku na bani na lalace Na rasa kowa nawa, wayyo Allahna na shiga Uku wallahi gida zan koma Nabar Yarinyata cikin Jini, tajuddeen kai na bama amanar ɗiyata nasan bazaka bari rayuwarta ta wulaƙanta ba. Dan Allah ka bani Ƴata ita nake son gani'


tunda ta fara sambatun nan zainab da hajiya layla suka fashe da kuka suna kallonta, ta runtse idanuwanta sai faman ciccije le6enta take Yi da haƙoranta tuni suka soma faffashewa, jini Ya soma tsastsafowa, dunƙule hannu tayi tana buge buge, da sauri zainab da hajiya layla suke rurruƙeta sosai suna ambaton sunanta

  

DR.SHUREIM❤


Lokacin da Kiran Alhaji Ubaid ya shigo wayarshi, Yana a zaune saman darduma cikin shiga ta larabawa, Yayi nisa acikin karatun qur'nin dayake yi Kiran Ya daki dodon kunnanshi, Hakanan yaji gabanshi Na faduwa, aranshi ya ayyana kowa ne ne ke kiranshi a tsakar daren na! ya salam, Sai da yakai ƙarshen Aya tukunna Ya zabura Ya miƙe Ya nufi wayar dake ajiye saman side drawer ya ɗauke ta yana duban Screen din, Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba ganin sunan Abie dinsa Ya bayyana, kafin Ya ɗaga kiran saida Ya fara kallon agogon bango ƙarfe ɗaya da rabi na dare, picking call ɗin ya yi muryarshi na rawa ya furta"Assalamu alaikum Daddy!!!" muryar Alhaji ubaid Babu natsuwa Ya furta mashi"shureim Ƴar uwarka ta dawo gida daren nan cikin mawuyacin hali"! Da alamun ruɗu akan fuskar dr shureim Yace"bangane wa kake nufi ba daddy" muryar shi da sauti mai ƙarfi Yace"BENAZIR!! nake nufi ta dawo gida cikin daren Nan, Gatanan kwance tana buge buge zufa duk ta wanke jikinta, mun rasa ya zamuyi da ita"


  Zafafan Hawaye ne suka wanke fuskar dr. shureim, tsabar farin ciki baisan sa'adda Ya zube saman gwiwowinsa Yayi sujjada, sosai ya fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, Alhaji Ubaid Yana jiyo sautin kukan dr shureim Kamar ƙaramin Yaro.


  "Shureim ba kuka yakamata kayi ba, dan Allah ka natsu muyi magana, hankalin mu ba'a kwance Yake ba, Ƴar uwarka bata acikin Hayyacinta, Mai gemu ya tabbatar min da cewa Kurciya ne akayi mata, saboda alamomin dake a jikinta na fitar sihirine"


  Jin wannan maganar ta Mahaifin nasa ne yasa shi saurin ɗagowa daga sujjadar, arab turban dinsa tuni ya warware Yabar saman kanshi.


  Manna wayar yai saman kunnanshi da alamun kiɗima ya furta"Sihiri kuma!!

  Alhaji ubaid Yace"to haka dai mai gemu Ya faɗa mana, baka ga yadda jikinta ke fitar da gumi ba kamar wadda aka tsamo daga kogon ruwa, bari na kanga maka wayar kaji haukan da take Yi mana" on the other hand Alhaji Ubaid Ya matsa gaban benazir Ya saita wayar abakinta.


  Muryarya ce ta ratsa kunnuwan dr shureim"Ni ku sake ni, Ku ƙyaleni ku daina ruƙe mun hannuna, wurin Mijina zanje nabar mashi ƴata a gida ita nake son gani, wallahi ku rabu dani dole in tafi" Jikin taƙaura yai la'asar, a sukwane Dr shureim ya miƙe tsaye da waya kare a kunnanshi.


  Muryarshi na rawa Ya furta"daddy najima ina zargin hakan, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wallahi da ina da halin da zan Iya zuwa Jos acikin daren nan da babu abun da zai hana inzo don in cece rayuwar ƴar uwata, amma duk da haka daga nan ɗin ma zan Iya taimakawa, Daddy Idan Aunty zainab  tana akusa ka miƙa mata wayar!"


 Jikin Alhaji ubaid na 6ari ya miƙa ma zainab Wayar yace ta kar6a dr shureim ne ke son Yin magana da ita, da sauri ta sanya hannu ta kar6i wayar tana fadin"dr shureim kaga wani ikon Allah ko? Tsawon shekara goma sha shidda Yau benazir ta dawo gida, wlh tsabar farin ciki bansan inda zan tsoma kaina ba, sai dai na damu da yanayin da take aciki"


 Numfasawa dr shureim Yai tare da cewa a tsanake"Aunty zainab, yanzu bani da natsuwa, zuwa gobe da sassafe zan shigo Jos din, amma kafin nan ki duba ɗakina a cikin drawer chest na bedside drawer gida na uku, akwai robobin ruwan zam zam da wani malamin mu na ƙasar egyp ya bamu su don mu dinga yin amfani da su muna taimakon mutanan da suke fama da matsalar sihiri, ki ɗauki ɗaya Kije ki buɗe bakin benazir Ki matsa mata shi ki tabbar ta shanye shi duka in sha Allah, sauran sihirin dake ajikinta zai barta ne kafin goben mu ƙaraso" amsa mashi tayi da toh, yace ta miƙa ma mahaifiyarshi wayar da sauri ta miƙa mata, yatsun hannun layla na kerma ta kar6i wayar.


  Cikin shessheƙar kuka tace"shureim benazir ɗinmu ta dawo gida, sai dai kamar bata acikin hayyacinta, duk ta faffasa la66anta da haƙoranta.


 Cikin kwantar da murya dr shureim Yace"Ki sanya handsfree Inason daddy yaji maganar da zanyi" da sauri layla ta mayar da wayar handsfree, zainab tuni ta shige ɗakin dr shureim neman ruwan zam zam.


   "Mommy daddy, dan Allah ku kwantar da hankalinku, wallahi Allah ne ya taimaki rayuwar baiwar Allah nan Ya Karya sihirin dake a jikinta, kuma ya dawo mana da ita da ranta, wani mugun aka samu mara imani mai zuciya irin ta kafuran farko Yai silar rabata da danginta tsawon shekara goma sha shidda, wallahi tun lokacin dana ji yanayin da benazir ta gudu tabar gida raina ya bani cewar wani abunne Ya faru da ita, haƙiƙa munyi sakaci wurin kula da ita, gaba ɗaya mun ɗaura mata lafin guduwarta babu wanda ya ta6a yi mata kyakkyawan zato akan meyasa ta gudu tabar jinjira acikin kwamin wanka, Kuma bata nemi kowa ba ta kama hanya tayi tafiyarta, anyi amfani da halayanta na rashin jin magana da rashin Kunya da take dashi anyi mata abun da yasa tabar mu saboda ansan kowa zai yi tsammanin ita ta gudu dakanta tunda dama bata jin magana, da ya ke Allah ba azzulumin bawansa bane sai gashi ya dawo mana da ita a lokacin da bamuyi tsammanin ganin ta ba" gaba ɗaya sun natsu suna sauraron muryar dr.shureim, hatta security officers din gidan duk suna sauraron shi ga dukkan alamu suna gamsuwa da bayananshi duba da yadda suke gyaɗa kawunansu.


  "Banaso wani daga cikinku Ya tambayeta meyasa ta tafi, ko kuce zakuyi mata faɗa dan Allah kada kuyi mata hakan, Kuma kada ku faɗa mata abun da ya faru da mijinta da ƴarta, naji tana ambaton sunansu, ku sanar da ita cewa suna nan kuma zaku haɗata da su idan ta kwantar da hankalinta, idan ba haka ba zata Iya zaucewa idan taji cewa babu su"


  Kamar malami da ɗalibansa haka shureim keyi masu magana suna amsa mashi da toh.


  "Zuwa da safe kafin mu ƙaraso, a kira likitan gidanmu Ya duba lafiyarta," suka amsa mashi da toh.


  "Mommy idan zainab ta bata ruwan zam zam din, in dai bacci bai ɗauke ta ba, ki taimaka mata tayi wanka taci abinci, idan kuma tayi bacci ku ƙyale ta kada ku takura mata" layla ta amsa mashi da toh.


  Shigowa falon Zainab tayi hannunta ruƙe da robar zam zam ta ƙara so gaban sofa din da benazir ke akwance tana sambatu, muryarta harta disashe fuskarta ta kumbura suntum.


  Zuƙunnawa tayi agaban sofa din, ta cizge murfin robar, da sauri Alhaji ubaid ya rurruƙe mata hannuwan Benazir, daƙyar ta Iya buɗe bakinta ta kafa mata ruwan zam zam din ya dinga shiga cikin ƙaramin bakinta, gaba ɗaya ta shanye ruwan, ko mintuna biyar ba'ayi ba da bata ruwan bacci mai nauyi ya ɗauketa, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, zufar jikinta tuni ta soma daskarewa, addu'o'i zainab ta dinga karantowa cikin harshen larabci tana tottofa mata saman fuskarta da jikinta, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma iyayenta ba, tuni layla tayi sallama da dr shureim ta miƙa ma Alhaji ubaid wayarshi ya sanya hannu Ya kar6a ya tura a aljihun jallabiyarshi, security office din dake atsaye bakin ƙofar falon suka yi masu sallama da niyar gobe da safe zasu dawo duba jikin benazir, Alhaji ubaid yai masu godiya kafin suka fice daga falon.


  Hajiya layla ta dubi zainab kije ki kwanta mun gode sosai, dan Allah gobe da a suba ki shirya mata lafiyayyan breakfast din da zata ci" amsa mata tayi da toh, ta mike ta nufi room dinta, ya rage saura Alhaji ubaid da Hajiya layla a falon, kallon juna sukayi lamarin Ya girgiza su, abun daya ɗaure masu kai wanene yayi masu wannan muguwar aika aikar!!! 

   Atare suka ɗaura idanuwansu kan benazir tsantsar sonta da ƙaunarta ne Ya kamasu, Har cikin zuciyarsu basu ji daɗin ƙaddarar data afka mata ba, tayi matuƙar basu tausayi ganin irin mayuwacin halin da take aciki, fatansu Allah Ya toni asirin baƙin azzulim daya yi silar barinta gida!!! yadda suka ga Rana haka suka ga dare, babu wanda Ya runtsa acikin zukatan nan guda huɗu, Hajiya layla da Alhaji ubaid, Dr shureim da Zainab, akan kunnuwansu aka fara kiran sallar asubahi!!!! 


EX-PRISONERS🥳


At abuja Nigeria🛬


Alhamdulillah Matafiya sun samu damar sauka Lafiya basu wayi gari ba sai acikin Katafaren Luxury Villa Mallakin Chief Owais sharafuddeen Obinna! Aljannar duniya ce mai zaman kanta, sai dai mun haɗu a next page zamu ji Ya haɗuwar Villa din Yake Ya prisoners suka wayi Gari? Ya Zahra zata ƙare da Hajiya falmata? Me kuke tunani game da dawowar BENAZIR MAHAIFIYAR UNAISAH ZAHEER TAJUDEEN😳YANZU NE ASALIN GAME DIN ZAI FARA!! KOWA YA ƊAURA ƊAMARAR SHI, NI DAMA TAWA A ƊAURE TAKE NA SHIRYA TSAF, NA FEƘE ALƘALAMINA 😂🤣

  

   


  💋ABBAN SOJOJI💋 

💋KURKUKUN ƘADDARA💋Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da kuma kurkukun ƙaddara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440  whatsapp din ya samu matsala, ga wadda za'a same ni da ita (08134387050) ayi mini magana ta whatsapp, message from Boss Bature


 ✍ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin
First bank
3196407426,

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post