Kurkukun Kaddara Book 2 Page 37

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 37

Nayi danasanin abunda na akaita mata, har yau idan na tuna cewa da hannuna nayi hakan sai inji gaba ɗaya na tsani kaina...." cikin jin ƙunar yai ya ƙare maganar.

 Tsananin tausayinshi ne ya kama Benazir, idanuwansu sun kada jawur

 Harta bude baki zatayi magana, Motsin buɗe kofar toilet Ya dakatar da ita, sam ta manta da zeenatu a toilet, da sauri ta goge hawayenta, dr shureim ma ya share hawayen shi muryarshi adisashe yace"wanene a toilet"?

 Kafin ta bashi amsa, zeenatu ta fito, fuskarta da alamun lemar ruwa, tamkar batasan me suke tattaunawa ba, Har kuka tayi masu saboda sun bata tausayi duk da bata fahimci kan zancen nasu ba, ita a tunaninta Yaya shureim dinta ya ta6a son wata, sannan hoton daya ta6a nuna mata awayarshi amatsayin nata yake kallo yanzu ta gane ba ita bace, ya 6oye matane, har cikin ranta ba ta ji dadin hakan ba, jikinta yai sanyi tamkar wadda ka zarewa laka.  Sun ƙura mata ido suna kallonta, fatansu Allah yasa bata ji me suke tattaunawa ba"


  "Zeeentu dama kina acikin toilet tsawon lokacin dana shigo ɗakin"?


 Jinjina mashi kai tayi"eh yaya shureim bansan ka shigo dakin ba, Uziri ne Ya ruƙe ni a toilet"


  Ajiyar zuciya ya sauke jin tace batasan ya shigo ba.


 "Ina kwana, ka tashi lafiya" muryarshi araunace ya amsa mata"lafiyalou" duban benazir tayi wadda tayi shiru tana kallonta, daga ita har dr. shureim din fuskokinsu sunyi jawur saboda kukan da suka sha, a hake suke ƙoƙarin 6oye mata damuwarsu bayan ga alama nan ta gani.


  "Aunty Benazir, bari naje daki in yi sallar acan, namanta jiya ban ɗauko hijabina ba" ta fadi hakanne don ta basu damar cigaba da tattaunawarsu


  Benazir tace"A'a basai kinje daki ba, Ga hijab dina kiyi da ita" ta fada tare da cire hijabin ta miƙa mata, da sauri zeenatu tace"a'a, Kibarshi, nafison naje daki nayi acan, naga kamar kuna yin magana ne keda ya shureim"


 Murmushin yaƙe Benazir tasakar mata"kada ki damu ƙanwata, bawani abu muke tattaunawaba, kema zamu Iya yin firar dake" 


  "Assalamu alaikum!" Mom layla ce ta doko sallama, gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta, doguwar rigace a jikinta milk colour, ta yafa mayafi akanta, fuskarta dauke da fara'a take dubansu

 Har suna haɗa baki wurin gaishe da ita"ina kwana mommy? Kin tashi lafiya"?


Cikin kulawa ta amsa masu da cewa"lafiyalou Alhamdulillah, fatan na same ku lafiya, zeenatu ya akai naganki atsaye"?


 Washe baki zeenatu tayi tana fadin"yanzu na fito daga toilet, nayi alwala ne zanyi sallah" 

Mom layla tace"okey, yakamata kiyi kada ki makara" amsa mata tayi da toh, da sauri ta nufi kofar fita dakin ta fuce cike da fargaban kada Aunty Benazir ta dakatar da ita, bayan ta fita daga dakin ajiyar zuciya ta shiga saukewa, haƙiƙa taji takaicin halin da taga dr shureim dinta da aunty benazir, ta shiga damuwa tabbas tana ji aranta wani mummunan abunne ya ta6a faruwa da su, a ƙagare ta ke da son jin wacece Yarinyar benazir dinta? Sannan kuma wacece matar da taji yaya shureim dinta yana magana akai har yake fadin bazai samu madadinta ba koda ace yayi aure, burinta ayanzu shine taga hoton matar da ya shureim yake nunawa benazir a wayarsa.Da wannan tunanin ta nufi dakinta dake acan upstairs.Bayan fitar zeenatu, dr shureim da Benazir suka miƙe tsaye suna fuskantar mahaifiyarsu dake binsu da kallon mai tattare da alamar tambaya.


  "Meke damunkune? Ya akai naga fuskokinsu sun yi ja kamar wadanda suka yi kuka"! Tambayar data fara jefa masu kenan 


 Benazir ce tayi kokarin cewa"Ni da ya shureim ne muke yin firar yaushe rabo, mun tuna da rayuwar mu ta bayane kafin mu rabu"


 "Hmm, yakamata ku manta da abunda ya wuce, tuna bayan nan baida amfani, tun da ba abun arziƙi bane ya faru"


 Dr shureim yace"hakane mommy, zamuyi kokarin yin hakan"

 Shiru tadanyi na wani lokaci tana kallonsu.


 Har dai Benazir ta fahimci kamar akwai wani abu dake akasan zuciyar mahaifiyar tasu

 "Mommy, kina son yin magana damu ne"?

  Girgiza kai tadanyi kafin tace"tausayin rayuwarku nake ji, ina jin fargaban ranar da zan mutu in barku a duniyar nan mai cike da ruɗani, saboda mahaifinku bazai iya tsaya maku ba, shi kanshi juya shi akeyi....." jikinsu ne yai sanyi jin abunda tace, tamkar tana basu wasiyya ne, matsawa tayi kusada su tare da ruƙo hannayensu acikin nata.


  "Bazan 6oye maku ba, ji nake kamar wani abu zai faru"


   "Mommy ki daina fadin hakan, Ki kwantar da hankalinki, Allah yana atare damu, ni bana so naji kina zancen mutuwa" dr shureim ne yai maganar.


 "Addu'arki kadai muke buƙata mama, kidaina sanya damuwa aranki" benazir ce ta fadi hakan.


 Gyaɗa kai Mom layla tayi"shikenan nadaina, Benazir yaushe zaki je gidansu Aneelerh?

Murmurshi benazir tasaki kafin ta bata amsar tambayarta dr shureim ya riga ta fadi "zuwa jibi in sha Allah, zan kaita gidan dakaina"


 Mom layla tace"naji dadin jin hakan, zanyi magana da mahaifinku shi yake da layin mahaifin Aneelerh, in yaso saiya fada mashi game da zuwanku, tun da babu wanda yasan gidan nasu, sai sun tura mana da adress dinsu.


   Benazir tace"hakan yayi mun gode mommy, ki kwantar da hankalinki, don na lura kamar bakya jin dadi"


 Murmushi mom layla tasakar masu, lokaci ɗaya kuma yanayin fuskarta ya canza ganin wani abu ajikin benazir, harta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta fasa tana kokwanto acikin zuciyarta.


 "Mommy lafiya"? Benazir ce ta fargar da ita, ganin ta ƙura ido tana kallon wuyanta"

 Girgiza kai tayi'bakomai, bari na koma daki, namanta banyi azhkar ba, Ina fata kuma kunyi naku, koda yake nasan ma shureim yayi ke fa"? Ta fada tana kallon benazir hankalinta yafi karkata akan jan ta6on da tagani gefen wuyan benazir kamar Yakushinta akayi fatar wurin duk ta karkarce.


 "Nayi mommy, bayan na kammala sallar asuba"

 Jim ta danyi kafin tace"okey, ku cigaba da firar ku, amma dan Allah adaina tuna bayan nan"

 Murmushi kowan nan su yasaki, insha Allah mommy" 


 Juyawa tayi ta nufi kofar fita dakin, zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, ta rude da abunda tagani, tambayoyi ta shiga jefa ma kanta me yakawo jan tabo da sahun yakushi saman wuyan benazir? 

  Da wannan tunanin ta nufi dakinta.

  

(Abunda ya faru bayan Big guy ya fita neman hannah)


Cikin takun sauri Big guy ya nufi bedroom dinsu dake a down stairs, wata'ƙil aci sa'a ya ganta, hankalin shi ba akwance yake ba, saboda ya bincika ko'ina na part dinsu saƙo da lungu babu cikon yarinyar da yake nema, ba ƙaramin ruɗewa yai ba, fargabanshi kada ace wani wajen taje ta faɗa takasa fita, ɗaya bayan ɗaya ya ke shiga dakunan matan babu kowa, yabi hanyar da zata kaishi bedrooms din mazan, A bakin ƙofar dakin su Naufal Yaci burki, Ya dafe  jikin glass door din, slowly kofar ta zuge, leƙawa ciki yai, a kwakkwance ya same su saman shimfiɗeɗan gadonsu, sun cunkushe kamar kinfin gwangwani, gaba ɗaya sun lullu6e jikinsu da bargo, buga ƙofar yai ranshi a jagule Ya juya zai fuce daga ɗakin ganin mazane zalla kuma gaba ɗayansu suke aɗakinsu naufal, Cak Ya tsaya da tafiya kwakwalwarsa ta soma tariyo masa abunda ya gani, da sauri Ya koma dakin ya tsaya daga bakin gadon yana kallon ƙafafuwansu da suka leƙo daga cikin bargon, a hankali ya ɗaura eye balls dinsa kan kafar da yake hasashen ta macace bata namiji ba, shape dinta ya banbanta data mazan kuma tafi kafafuwansu ƙaranta, hannu ya miƙa ya damƙi kasar bargon ya yaye shi, lokaci ɗaya big guy yasauke nannauyar ajiyar zuciya, hankalin shi ya kwanta ya samu natsuwa, Hanna ce a tsakiyar mazan ta ƙanƙame gabriel kamar zata koma cikinsa, Yayi mamakin ganinta tsumu tsumu acikinsu, gefenta na dama naufal ne da haris, daga 6angaren hagun katifar gabriel ne da javed, sunyi nisa acikin baccinsu.

  Acikin zuciyarshi ya furta"Kin tayarmin da hankalina" ya ambaci hakan tare da sakin bargon Ya juya ya fuce daga ɗakin nasu.

*Unaisah Angel💋❤*
Fitowa tayi daga cikin toilet, fuskarta da alamun lemar ruwa, Salsabeel yana daga zaune saman gadon Ya jingina bayanshi jikin headboard yayin da Giant snake din yake a kwance gefenshi ya daura kanshi saman laps dinsa.


 Jin motsin fitowarta ne ya janyo hankalin salsabeel ga kallonta, baiwar Allah ba ƙaramin tausayi take bashi ba, ƴar ƙarama da ita ta ɗaurama kanta damuwar da ko wani babban bazai Iya jurarta ba, ganin yana kallontane yasa ta dan sakin fuskarta data kumbura suntum.


  "Fuskarki kika wanko"? 


Girgiza mashi kai tai"a'a alwala nayi"

 "Amma ba'a fara kiran sallar asuba ba"

 "Nafila nake so nafara Yi, kafin a kira sallar asuba, Inaso zanyi ma danish ɗina addu'a ne"

  Murmushi salsabeel yasakar mata, dama saida ya ayyana hakan aranshi

 "Kina kaunar ɗan uwan nan naki"

"Fiye da yadda nake ƙaunar kaina" ta furta hakan tare da juyawa ta nufi kofar fita dakin don taje nasu ɗakin ta ɗauko Hijabin da zatayi sallah, har ta kusa fita daga dakin kamar ance ta waiwayo ta kalli gadon


  Ba zato ba tsammani macijin Ya girgiza Yana kokarin tashi

 Da sauri ta furta"yanzu zan dawo my Man, kada ka biyoni, Nima bazan Iya yin nesa dakai ba, Hijabin sallah zan ɗauko a ɗaki" komawa macijin yai tare da daura kansa saman laps din salsabeel.


Ajiyar zuciya ta sauke haɗi da yin ƙayataccen murmushi, salsabeel dake kallonta shima murmushin yake yi, lamarin Danish na matuƙar bashi mamaki.


  Juyawa tayi da sauri ta fuce daga dakin.


    Moving quickly take tattaka matakalar benan, kasancewar ko'ina na part din da haske tamkar da rana baka ta6a gane lokaci saika kalli agogo, a tsanake take bin ginin da kallo Yayin da take saukowa down, zuciyarta tayi mata nauyi, zazza6in jikinta sai ƙara nunkuwa yake yi, Ita kadai tasan halin da take aciki, da ace zata Iya dauke ma danish abunda ke damunshi da kuwa tayi hakan, zaifi mata sauƙi akan taganshi a wuyanci hali.


  Tana gab da zata dira ƙafarta kan floor din falo, ranta ya bata cewar akwai mutun awurin, wurga eye balls dinta tayi akan first floor bataga kowa ba, A hankali ta mayar da eyes din nata kan Second floor, rass taji gabanta Ya faɗi ganin mutumin nan da ta ta6a gani a gym room yana motsa jiki, Ya juya mata baya, bata Iya ganin fuskarshi da kyau, batasan ya akai ta tsinci kanta da yi mashi kallon kurulla ba, bakomai take son gani ba face fuskarshi, sai dai kash takasa ganinta, faffaɗan bayanshi kadai take kallo, Ba ƙaramin jikine da shi ba, murdadden damtsen hannayensa take kallo, da alama Ya ruƙe wani abu yana sha a cup, duba da yadda hannun shi na dama ke motsi, yayin da ɗayan hannun nashi ya zura shi a shorts pocket dinsa.


  Aranta ta ayyana ko wanene wannan mutumin? daga gani yana da ƙarfi da tarin dukiya, komai nashi cikin ƙasaita yake yin shi, dai dai da yanayin tsayuwarshi abun kallo ce, yaɗan jingina bayanshi jikin benan.


Hankalinta ya karkata akanshi, ta manta da hijabin da zata je daukowa, ta tafi wani tunanin daban, ita so take taga wanene shi? Ranta yafi bata  cewar Chief din da taji ana fadi ne, 


"Unaisah" firgigit ta ɗauke idonta daga kallon chief da take Yi, Jin muryar Boss, da sauri yake tunkarota shigowarshi kenan part din, jallabiya ce a jikin shi, Ya sanya face mask a fuskarshi, tayi mamakin ganinshi a irin wannan lokacin, abunda bata sani lokacin da boss Ya ambaci sunanta, Chief owais Ya juya don ganin wanene ke magana, dai dai sa'adda ita kuma ta kawar da kanta, Natsuwa yai yana dubansu daga can saman second floor.


"Ba ki yi bacci ba"? Tambayar da boss ya jefa mata kenan a yayin daya ƙaraso gabanta yaci burki ya tsaya yana kallon fuskarta.


  "Banjima da farkawa ba, amma meya hana ka bacci" ta tambaya tana kallon rinannun idanuwanshi masu dauke da tsantsar damuwa

 "Taya zan Iya yin bacci? Bayan kema bakiyi ba"

 Matashin murmushin ta ɗan saki, har cikin ranta taji dadin maganarsa, shi kuwa ji yake kamar ya rungumeta ko dan yaji sanyi aranshi, ya damu da halin da suke aciki ita da ɗan uwanta, tausayinsu ya hanashi sukuni har ya gaza runtsawa shiyasa ya fito don yazo ganin su.


 "Yakamata ka kwanta ka huta boss, na fahimci ka damu dani, meyasa"?

  "Taya bazan damu dake ba? Kefa jinina ce, jinin dake yawo ajikina shi yake yawo ajikin ki....." da sauri Ya katse maganar, Jin su6ul da bakan da yai, murmushin gefen fuska tayi mashi, ga dukkan alamu taji dadin maganarshi


 "Boss kayi shiri baka ƙarasa zancen ba? Ni wallahi idan kana Yi min magana sai inji kamar mahaifina"


"Meyasa kikace haka"?


 "Saboda Yana ƙaunata fiye da yadda yake kaunar kansa, ya sadaukar da farin cikinshi saboda ni, nayi rashin ji aƙuruciyata, na azabtar da daddyna amma duk idan na tuna ayanzu sai inji haushin kaina......" sambatu take yi mashi sam batasan me take furtawa ba, abune ya haɗe mata ga radadin da zuciyar ta keyi mata shiyasa take yi mashi zuba, tana magana hawaye na taruwa acikin idanuwanta.


  "Amma meyasa kike jin haushin kanki ayanzu"? Muryarshi araunace ya furta mata maganar.


  Shesshekar kuka ta soma yi mashi tana fadin"saboda nagane cewa bani da masoyi a duniyar nan daya wuce shi, bani da tamkar shi har abada, Har yau idan na tuna cewa shine silar duk wani abu dana koya aduniyarnan ba ƙaramin dadi nake ji ba....." kasa ƙarasa maganar tayi, sakamakon janyota da yai zuwa jikinshi ya rungumeta sosai, haɗi da daura hannayenshi saman bayanta yana lallashinta, bata kawo komai aranta ba, sai dai bugun zuciyarta da taji ya ƙaru, tajima tana mamakin yanayin da take tsintar kanta idan Boss yana akusa da ita, sakankancewa takeyi taji kamar daddyn ta ne ya dawo.


  "Ya isa haka, ki daina kuka Unaisah, In sha Allah, daddynki zai bayyana, bama ke kadai ba da sauran ƴan uwanki duk zamu binciko maku danginku"


  Ajiyar zuciya ta shiga saukewa, takasa raba jikinta daga nashi, tamkar zata koma cikinshi.


Duk wannan abun dake faru atsakanin Boss Man da Unaisah, akan idon chief owais, yayin da yake kur6ar coffee dinsa.


     Tunawa da Hijabin da zata daukone yasa tayi saurin furta"boss namanta, alwala nayi zanje daki na dauko hijabi da prayer mat, yakamata na tafi idan danish yaji na dade zai Iya biyoni, yanzuma da ƙyar ya bari na fito"  ta fada tana raba jikinta daga nashi.

  "Nagode da kulawarka agaremu,"

"Kada ki damu, muje na rakaki ɗakin,"

"Banaso na takura maka, naga idanuwanka sun kaɗa jawur, baccine a idonka yakamata kaje ka kwanta" ta fada tana kokarin kakaro murmushi 

 Ruƙo hannunta yai acikin nashi da zolaya yace"saifa na biki Allah, ai tunda baki runtsa ba nima bazan yi bacciba, zan zauna atare daku har sainaga abunda ya turema buzu naɗi"

 Dariya tadan saki jin maganarshi ta ƙarshe, atare suka jera zuwa bedroom din nasu.

     Koda suka ƙarasa dakin, arude ta furta"Boss babu batool fa"! Ta fadi tana faman zare ido akan gadonsu.


  "Calm down ur mind, nasan inda suke, ba sace su akayi ba, abunda ya farune dazu ya tayar masu da hankulansu, shine na rakasu dakin Ummi, nasan yanzu haka sunyi nisa acikin baccinsu" ajiyar zuciya ta sauke, har taji sanyi aranta.


"bayin Allah, nasan daƙyar suka Iya runtsawa, musamman Azeeza tafi kowa tsoro a cikinsu" ta furta hakan tare da kama hanyar closet dinsu, bin bayanta yai da kallo harta 6ace ma ganin shi.


  Maganar amininshi ce ta fado mashi aranshi, a ranar daya kira shi video call yana daga kwance saman gado shida Angel dinsa.


  Tuni idanuwanshi suka cicciko tab da ƙwalla, haƙiƙa yayi babban rashin da bazai ta6a samun mai maye mashi gurbinshi ba"

A hankali Ya furta"Allah Yajiƙanka aminina"

 "Boss mu tafi" muryar unaisa ce fargar da shi ga kallonta, Harta zura hijabin ajikinta launin milk, Iya gwiwa ta tsaya mata, hannunta a ruƙe da prayer mat.

  Lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke, dama ranta babu daɗi, dauriya kawai take Yi,

 "Meyasa kika 6ata fuska"?

 Zumbura mashi baki tai kafin tace"kaine mana, kaƙi jin maganata ni nasan baccine ke addabarka, amma kaƙi zuwa ka kwanta, kalli idanuwanta har sun canza launi sun yi jawur da su..." cikin kulawa tayi maganar

 In a cool voice ya furta"karki damu dani, babu bacci atare dani, idona ne keyi min ciwo, kafin na fito daga gida saida na ɗiga magani"

Unaisa sarkin tausayi, duk sai taji ba dadi, jin baida lafiya.

 "Allah yabaka lafiya boss, amma dan Allah kaje ka kwanta kayi bacci"

Bakomai ya tuna ba face maganarta lokacin da tana yarintarta, Idan baida lafiya ya kwanta don yai bacci, saman jikinshi take hayewa tana fadin ai wallahi bazan bari kayi bacci ba, ka jira sai lokacin da nima zanyi sai muyi atare, idan ta fadi hakan to bai isa yai bacci ba, dole yajira har zuwa time da zata gama wahalar dashi tukunna suyi bacci, yayi zurfi acikin tunanin shi muryarta ta dawo dashi

"Ka ƙura min ido kana kallona, ko nayi maka kama da wanine"? mamaki take bashi idan tana magana.

Adabarbarce ya furta"um...bakomai mu tafi kawai"

Ya ruƙo hannunta acikin nashi, Suka nufi ƙofar fita daga dakin.

 

Kafin dawowarsu dakin danish, Tuni Big guy ya kawo mashi fresh fruit, a faffadan tray ya ajiye mashi saman mattress, abunka ga maciji, ɗai ɗai yake ɗauka da baki Yana lunkuma shi, Cikin ƙanƙanin lokaci Ya shanye kayan marmarin, bayan Ya kammala ci, Big guy ya tambayi Salsabeel Ina Unaisah take? Yaga babu ita adakin salsabeel Yace ta fita dauko hijabin sallah ne, amsa mashi yai da okey, kafin Ya dauki tray din Ya juya yabar dakin. 


Adai dai lokacin daya sauko down hannunshi ruƙe da tray, Unaisah da Boss man suna kokarin nufar benan, 

Da mamaki big guy ya furta"wa nake gani kamar Boss namu? Me ye hana ka runtsawa"?

 Fuska asake Boss Ya nufe shi yana fadin"abunda ya hanaka runtsawa nima shi yahana in runtsa"


 Dariya big ya saki"kai dai fadi gaskiya mutumina, nasan me ya hanaka yin bacci, damuwace ta isheka da fargabar kada maciji ya sari ƴarka, koba haka ba"? Ya faɗa yana ɗage mashi gira da zolaya.

"Baka da dama Big guy, ai dole na damu, ita kaɗaice fa ƙwallin ƙwal, bugun zuciyar,"ya fada idanuwanshi akan unaisah wadda tuni Ta haura saman bene don ta isa ga dakin danish

"Na fahimci ba ƙaramin so ka ke yi ma yarinyarnan taka ba, nima kuma inasonta, me zai hana ka bani auranta?da zolaya yai maganar

Harara Boss Ya watsa mashi shima da zolayar yace"ka dai bi a hankali, kada mamallakinta Yaji ka, kaima kasan me zai biyo baya,"

Da sauri Big guy ya toshe baki yana fadin"au namanta, ashefa ka bayar da ita, balle ma nasan koda  baka bada ita ba da wuya ka bani ita, don na fahimci kafison inda zata huta" dariya boss yasaki yana fadin"kamar ka sani, kaima din ai ba daga baya ba, sai dai kayi mata tsufa, ina laifin ka nemi ummi mana zata dace dakai....." tunkan ya ƙare maganar, Big guy ya galla mashi harara"Allah Ya kiyaye, in rasa wazan nema sai karuwa"

Boss yace"abar dai kaza cikin gashinta, kaima din ai tubabbe ne, nima labari naji"

"Ina ganin girmanka man, mu bar maganar, bana son tuna baya, Ni bansan ma wani munafukinne yabaka labari ba, wallahi da zan sani saina takaita jin dadinsa"

 Dariya Boss yai ganin yadda ya 6ata fuska.


"Sorry mutumina, zolayatace kawai, ni bansan komai ba, kaine ka kama kanka,"


"Next time idan ka ƙara min wannan wasan, A jikin ƴarka zaka gani" Ya fada tare da bi ta gefen Boss Ya wuce yana dariya, shima Boss din dariyar yakeyi

"Ai kai ƙaramin ɗan iskane, sai dai ka cika baki indai akan Angel dinane, don kuwa kasan ko kallon banza kayi mata a jikinka zaka gani," 

Big guy bai juyo ya dube shi ba, Yai tafiyarshi.

  

Bayan komawar Unaisah dakin, a kishingiɗe ta samu salsabeel harya gaji da zama, macijin yana nannaɗe gefenshi.


Tayi tunanin bacci yake yi hakan yasa ta soma yin sanɗa tana tafiya duk don kada ta farkar dashi, shimfida dardumar hannunta tayi, kafin ta daidaita natsuwarta, ta kabbara sallah.


Boss na kokarin shigowa dakin aka fara kiraye kirayen sallar asuba, daga bakin kofar ya tsaya yai gyaran murya, salsabeel daya lumshe idanuwanshi jin gyaran muryar da Boss yai mashine yasashi bude idanuwanshi 

  "Sannu da kokari, Mun hana ka bacci," yamutsa fuska salsabeel Yai, bacci yana neman yaci ƙarfin shi

 "Baku kuka hanani bacci ba, ni na hana kaina saboda ɗan uwana" ya fada yana duban macijin.

   Kallon shi Boss Yai, gwanin ban tausayi ya langwa6e kansa, bawan Allah takaicin duniya ya ishe shi.

  Shiga cikin ɗakin Boss Yai, a bakin gadon ya dakata da yin tafiyar yana kallon Giant snake din

  "Bacci yake yi"? Ya jefa ma salsabeel tambayar

"Bazai Iya runtsawaba, idan har ba Ƴar uwarshi tana atare da shi ba, sai kuma idan ya dawo ainihin halittarsa"

Cikin tausayawa boss yace"kayi hakuri, wata rana sai labari, In sha Allah ƙarshen wahalarka ne Yazo, wadanda suka yi silar ƙuntata rayuwarka, bi'iznillahi ajalin su ne yazo, zasu ɗanɗani kuɗarsu har sai sunji dama ba a halitto su a duniyar nan ba, sai sunyi danasanin rayuwarsu....." kalamai masu dadi da kwantar da hankali Boss yake fada ma giant snake din, yayi lamo yana sauraronshi.


      "Naji an fara kiran sallar asuba, Bari nashiga toilet inyi alwala, idan na fito kaima saika shiga ka yi mu tafi masallaci," yai magabar yana duban salsabeel.

Batare da 6ara lokaci ba, Boss ya shiga toilet ya dauro alwala, bayan ya futo salsabeel Ya shiga shima yai alwalar,, sallama sukayi ma Unaisah dake zaune saman darduma, kafin suka tafi.


Kamar jira take Yi, subar ɗakin, jiki na 6ari ta miƙe ta nufi gadon ta haye gefen shi tana kallonshi, ta fahimci bacci yake ji, hakan yasa ta janyo bargo ta lullu6asu don ta taimaka mashi yai bacci.


*EX-PRISONERS❤*


Lokacin da Batul ta farka daga bacci, jikinta duk ba daɗi, tamkar mai fama da zazza6i, mura tayi mata mugun kamu, muryarta daƙyar take fita, fitowa tayi daga cikin bargon idanuwanta sunyi luhu luhu, ƙoƙari take tabar dakin duk don kada ta ƙara haɗa ido da ummi, tayi tsammanin zata ganta asaman gadon sai ganinta tay kwance saman carpet, ta lullu6e half body dinta da bargo, tafi ƙarfin ta haɗa shimfiɗa da su shine ta dawo kan carpet ta kwanta.

 Muryar batul kasa kasa ta ke ambaton sunan parveen,

  Daƙyar ta samu parveen ta farka daga bacci, tana faman yin miƙa haɗi da yin hamma, juyawa tayi 6angaren su Jemimah ta soma tada su daga bacci ɗaya bayan ɗaya suka farka suna faman mutsustsuke idonsu.


  Cikin muryar rada take yi masu magana"ku tashi mu tafi ɗaki, lokacin sallar asuba yayi," ruƙo hannun  jemimah tayi ta sauko da ita daga saman gadon, Parveen ta ruƙo hannun Azeeza suka sauko.


 "Bana so ta farka ta ganmu, kada ku yi surutu mu lalla6a mu bar mata ɗakinta" ta faɗa tana dubansu, Jinjina mata kai su ka yi alamar toh.


    Cikin takun sanɗa suka nufi ƙofar fita dakin, sai da suka fita Batul ta tuna da kayan ummi dake a jikinta, dafe kai tayi da hannu ɗaya"nashiga uku ashe ban cire mata kayanta ba, Parveen ki ruƙe hannun Aziza dana jemimah ku tafi ɗakin mu zan biyo ku daga baya"


 Maƙe kafada jemimah tayi"ni tsoro nake ji, idan abun nan ya ganmu fa"? 

"Kada ki damu, babu shi ai, waɗannan mutanan sun kashe shi" daƙyar batul take Yi masu magana

 "Batul baki lafiya? Idanuwanki sun kumbura jawur, muryar ki kamar ba'aji sosai" Azeeza ce tayi magnar.


  Kafin batul ta bata amsa parveen tace"sanyine ya kamata, sai da na hana ta kar6i rigata amma ta kar6a tasaka"


  "Amma ai aunty ummi ta bani kaya na saka, Kawai bana jin daɗine bawani abu ke damuna ba, Ku tafi ɗaki zan biyoki" Ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakin.


 A tsananin tsoroce suke tafiya suna tunkarar benan, parveen tana aruƙe da hannun azeeza dana jemimah, har yanzu basu daina jin fargabar macijin ba.


  Bayan batul ta koma dakin Ummi cikin sanda take tafiya, harta ƙarasa gaban gadonta, ta cire mata kayanta, ta ɗauki doguwar rigar parveen data jefar ƙasa, ta zura a jikinta, Juyawar da zatai keda wuya, taji sautin datse kofar ɗaki, rass taji gabanta ya fadi ganin ummi atsaye bakin kofar ta goya hannayenta kan ƙirjinta, fuskarta a murtuke babu annuri, idanuwanta sun ƙanƙance.


Hankalin batul ya tashi matuƙa, agigice ta furta"aunty ummi ina kwana"

Harara ta galla mata"daban kwana ba kin ganni atsaye? Kilbabba uwar iyayi"


 Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Ai na cire maki kayanki, gasunan kan gado, Ni dakinmu zan tafi, wajen unaisah"


 "Idan kinga na ƙyale ki kin fita daga dakin nan, to kuwa kin gyara sautin muryarki ne, wallahi baki isa kija min bala'e ba, Har kayan sanyi na baki, na kuma kashe sanyin a.c, saboda baƙin hali irin naki saida kika bari mura tayi maki mugun kamu duk don kija min masifa ko"?


Hawayene suka soma wanke fuskar batul, muryarta na rawa tace"ba haka bane aunty ummi, nima bayin kaina bane, bansan mura ta kamani har haka ba, dan Allah kibarni in koma cikin ƴan uwana"


 Shu'umin murmushi ummi tayi mata,

"Zan barki ki tafi, amma kafin nan saina fara kawar maki da murar nan, don haka mu shiga toilet inyi maki wanka da ruwan zafi"


 Zazzare ido batul tayi hadi da girgiza kanta"dan Allah aunty ummi ki ƙyaleni, ai ni ba yarinya bace, da zaki min wanka, ni kawai ki rabu dani nayi maki alƙawarin babu wanda zaisan ina yin mura"


Ɗaure mata fuska ummi tayi zaki wuce mu shiga toilet ko saina 6ata maki rai"?


 Cikin jin ƙunar rai, batul ta maƙe mata kafaɗa"ni bazan shiga ba, Na fada maki banaso, ki ƙyaleni," atakure take Yi mata magana, makoshinta radadi yake yi mata.

   Ganin ummi na tunkarota ne yasa ta soma ja da baya tana kuka, kokarin kubce mata tayi da sauri ummi ta damƙo sumar kanta, tajata ta ƙarfi ta shigar da ita toilet tana fadin"Ke har kin isa ki kufce min, ƙaramar ƴar shila dake, me zan gani a jikinki? da har kike fadamin ke ba yarinya bace" sautin kukan batul ya cika dakin ummi, gigitacciyar tsawar data kwatsa matane yasa tayi saurin jan baki tayi shiru, hawaye na cigaba da bin fuskarta.


 Ummi tafi ƙarfinta, da girmanta da komai, Tayi mata wanka da ruwan zafi, tamkar zata sale mata fatarta, fitowa ummi tayi daga cikin toilet din, ta nufi closet din kayanta, tana faman sakin murmushin mugunta, riga da wando ta dauko masu kyan gaske, na saƙa launin pink, waɗannan kayan tsohuwar ajiyace tuntana ƴar shekara sha bakwai a duniya take 6oyansu, tana matukar son kayan, rigar tana da hula hannunta dogone.


 Komawa toilet din tayi kamar yadda tabar batul haka ta sameta, ta ƙanƙame kanta jikin bango, dan pant ne ajikinta, hannunta biyu tallabe da kirjinta ta kakkare boobs dinta.


 Jefa mata kayan ummi tayi da sauri ta kar6esu.


 "Ina jiranki aɗaki, salon kuma ki daɗe, idan kika ƙara mintuna wani wankan zan sake yi maki" cike da isa ta furta maganar, kafin ta juya ta fuce daga toilet din, abakin ƙofar ta dakata tana jiran fitowar batul.


  Jin motsin buɗe toilet door dinne yasa ummi kai idonta ga dubanta, har saida taji gabanta ya fadi, ganin kyan da kayan sukayi ma batul, rigar tayi mata daidai, wandonma haka, kamar don ita aka saƙa kayan, bata sanya hular ba, yalwatacciyar sumar kanta ta sauko har gadon bayanta dark brown.


  Sai faman ƙanƙame jikinta take yi, ganin yadda ummi ke kallontane yasa ta duƙar da idanuwanta ƙasa, duk tasha jinin jikinta.


   Batasan ya akai ta tsinci kanta dayi ma fuskar batul kallon sani, sai dai tarasa tuna dawa take yi mata kama.

 Matsawa tayi kusa da ita, takai hannu ta ruƙo hular rigar ta sanya mata ita, sai taga ta ƙara yi mata kyau.


 "Ki daina ganin ina kallonki, ba kyau kikayi min ba, Munin fuskarki nake kallo" shiru Batul batace mata komai ba, bayan ta kammala gyara mata hular rigar, ta nuna mata gado"ki koma ki kwanta, har zuwa time da muryarki zata dawo dai dai kinji ko"?

 Maƙe mata kafaɗa batul tayi"ni bazan kwanta ba, dan Allah kibarni in tafi daki wajen ƴan uwana, Inason ganin Unaisah" muryarta shaƙe ta furta maganar.

"Wato saboda kinga makwancina shiyasa kika fara rainani ko? Har kina da bakin fadin Bazaki yi abu ba idan nasaka ki, Dalla ni wuce ciki ko inyi ball dake"


 Ƙin matsawa Batul tayi, gani take kamar ummi zata iya kasheta, furucin da tayi mata jiya sun firgitar da ita, sun kuma tsaya mata aranta.


  Zabura tayi da niyar ta nufi kofa don ta gudu, ai kuwa azafafe ummi ta damƙota kamar ɗiyar roba haka ta ɗaga ta sama, ta nufi gado ta jefar da ita, ta kuma janyo bargo ta lullu6eta tana fadin"idan kika kuskura kika leƙo koda kankine saina murƙusheƙi" 

Muryar batul da shessheƙar kuka take fadin"aunty ummi dan Allah kibarni in tafi, banason kwanciyar, ni wajen ƴan uwana zanje" ummi dake tsaye tana kallon bargon tace"idan kina son fita daga dakin nan to ki fara gyara muryarki"


"Ai ni bansan yadda zan gyarata ba, ki bani magani in sha"


  Ta cikin bargo batul take Yi mata magana.


 Tunani ta somayi aranta, ina zata samo mata maganin mura? Tasan ba'a rasa dakin ajiye magani a gidan tun da na jami'ae ne kuma yaran an tanadar masu komai da zasu buƙata saboda rayuwar kullece aka shirya masu. 


Boss man kadai take da contact dinsa, awayarta, daukar wayar tayi dake ajiye on bedside drawer ta danna ma Boss kira, cikin sa'a ya ɗaga kiran.


  Cikin girmamawa ta gaishe da shi"barka da asuba yalla6ai"

On the other hand muryar boss ta amsa mata da cewa"wa'alaikum salam, ummi barka da safiya"

 "Yawwa barka, Allah yasa dai ban katse maka baccinka ba"


 "Kada ki damu, idona biyu yanzu nake shirin zuwa cikin gidan, ko akwai wani abu da kike buƙata"?


   "Taimako nakeso kayi min in ba takura, maganin mura nake buƙata"


  "Wanene ke baida lafiya"? Da sauri tace"nice zan sha, Yaran dake atare dani lafiyarsu ƙalau' amsa mata yai da okey, idan zan shigo gidan zan taho maki da shi"


"Nagode" katse kiran tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, Batul dake a ƙumshe cikin bargo, abun duniya ya isheta.


Muryarta shake tace"aunty ummi banyi sallar asubaba, kuma ina jin yunwa"

  Guntun tsoki ummi taja"kiyi min shiru malama, ni ma ai banyi sallar ba, kuma ina jin yunwar bawai bana ji ba"


 Ta fada Tare da samun wuri daga gefen gadon ta zauna tana gadin Batul, hannunta ruƙe da wayarta, chatting ta kama yi, batul tayi shiru cikin bargo tana faman matse ƙwalla.


*sanarwa, bazan samu damar yin posting a monday ba, fatan za'ayi min uziri, in sha Allah da zarar na dawo za'a cigaba daga inda aka tsaya, game bukatar cigaba da karanta prisoners 500 ne zaku tura ta bank acct dina, ga ta inda za'a tuntu6eni 08103884440*
3196407426


Bature Hafsat Muhammad

First bank 

Idan kin tura zaki bada hoton receipt amatsayin shaida🤗

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post