Kurkukun Kaddara Book 2 Page 40

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 40

Something Unexpected*

*WAIWAYE🌹

*A Obie International Hospital*

Emergency room

Abun da ya faru daren Jiya da Sir mubarak Ya dauki Dr jazz zuwa asibiti, tunkafin su ƙarasa Ya kira Dr fawan awaya ya sanar dashi game da zuwansu, tuni nurses sun fito da stretcher bed din da zasu dauke shi, motarsu nayin parking a harabar ajiye motocin asibitin, Sir mubarak Ya fito jiki na 6ari ya cuccu6i dr jazz ya daura shi kan gadon, A gaggauce nurses suka gungurashi zuwa Emmergency room.


  Fitowa Major yai daga front seat na motar, Yabi bayan Sir mubarak dake tafiya yana nufar inda nurses din zasu kai Dr jazz, duk inda ya gifta manyan likitocin dake zarya cikin girmamawa suke gaishe da shi, a bakin ƙofar emmergency room din suka dakata da yin tafiyar, damuwar duniya ta isheshi, ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daɗi, haƙika yaji takaicin bugun da yayi ma jazz bisa rashin sani.

   "Yalla6ai, ka zauna" Major ne yai mashi maganar yana nuna mashi waiting seat dake jingine da bango

 Girgiza kai Sir mubarak yai"bazan iya zama ba, Idan har jazz bai farfaɗo ba, Ni kadai nasan halin da nake aciki, Major ka tayani da addu'a Allah yasa yarona ya farka bana so wani abu ya same shi"

   Cikin kwantar da murya major yace"Sir in sha Allah babu abunda zai same shi, zai ji sauƙi, ubangiji Allah ya bashi lafiya"

  "Ameen" ya amsa mashi.

 Tunda aka shiga da jazz cikin emmergency room, likitoci suka taru akanshi, yadda kasan zasu hana shi mutuwa idan tazo daukar shi. 

After some minutes, Dr fawan Ya fito daga medical room din, sanye cikin shiga ta likitoci, fuskarshi da face mask, tunkan ya ƙaraso wurin su sir mubarak yai hanzarin nufarshi yana fadin"fawan ya farfado? Ko hanyar yanzu"? 

Calmly dr fawan yace"daddy ka kwantar da hankalinka, har yanzu bamuyi nasarar farfaɗo dashi ba, jazz ya bugu sosai, yanzu dai muna ƙoƙarin ganin munyi mashi treatment din raunukan dake akan goshinsa, In sha Allah nan badajimawa ba zai farfaɗo, ina da tabbacin hakan" ya ƙare maganar yana duban fuskar sir mubarak, babu alamun zai kwantar da hankalinsa, fuskarshi duk ta yamutse.

 Dr fawan baiyi mamakin ganin hakan ba, yasan da irin shaƙuwar dake atsakaninshi da jazz, dole ya damu.

  Duk da yana jin shakkar shi saida yai ƙoƙarin jaraba tambayarshi ya akai jazz yaji mummunan rauni saman goshinsa.

  Kasancewar baya acikin natsuwarshi, da kanshi ya labarta ma dr fawan abunda ya faru.

 Dafe kai fawan yai da hannu ɗaya tunawa da ranar da sukazo asibitin suka tirkeshi kan ya fada masu abunda jazz yake aikatawa shi kanshi yayi tsammanin wani mugun abun Jazz yake kullawa ashe ba haka bane sun yi mashi mummunan zato.

   Ruƙo hannun shi sir mubarak Yai"fawan ka taimaka min, bansan ya zanyi ba, ina jin fargabar jazz ya farfado ya juya min baya saboda bugun da nayi mashi nasan daƙyar zai fahimce ni, nayi kuskure fawan na yanke mashi hukuncin cikin fushi batare dana saurare shi ba" cikin rauni na murya ya ƙare maganar, tsananin tausayinshi ne Ya kama dr fawan, hatta major ya tausaya ma shi.


  "Daddy, har abada bana tunanin jazz zai Iya juya maka baya, Saboda ni shaidane akan ƙaunar da yake yi maka,  balle kuma baka da laifi, laifin shine dabai sanar dakai ba a matsayinka na mahaifinsa, sannan duk abun da kayi mashi daddy kayi ne saboda ba ka son ya jefa rayuwarshi cikin hatsari, ni aganina kayi abunda ya dace kowani uba na gari yayi, shine ya tsaya tsayin daka don ganin yaronshi bai 6ace hanya ba....." tunda dr fawan ya fara magana sir mubarak ya natsu yana sauraronshi, major sai faman jinjina kanshi yake yi alamar gamsuwa da bayanin Dr fawan

  Sai da ya kai aya a maganarshi kafin major ya daura da cewa"yalla6ai gaskiya ne abun da dr fawan ya ke gaya maka, kuskuren da mukayi bisa rashin sani ne, tun da kake da jazz baka ta6a nuna mashi wariya ko acikin ƴa'ƴanka ba sannan baka ta6a yi mashi koda tsawa bane don yayi maka badai dai ba, don haka bana tunanin jazz zai juya maka baya saboda abunda ya faru, zai fahimce ka kuma zai gane kuskuren shi"


 Nauyayyar ajiyar zuciya sir mubarak ya sauke, fatanshi Allah yasa maganar su dr fawan ya tabbata, don bayason jazz ya guje shi saboda ƙaunar da yake yi mashi. 


   "Major ka kira layin Zaki ka faɗa mashi muna atare da jazz sai zuwa gobe zamu dawo gida" 


 "Okey Sir" Major ya faɗa tare da zaro wayarshi daga aljihu, Ya danna ma Zaki Kira, Bugu Uku kafin Yai picking, bayan sun gaisa Ya isar mashi da sakon Mahaifinsu kafin daga bisani su ka yi sallama.


  "Daddy ku zauna mana, ko zamu shiga daga cikine ka kwanta a resting room dinmu"


Girgiza kai Sir mubarak Yai alamar a'a, 


 "Bazan Iya runtsawa ba, Nafi buƙatar farfaɗowar Jazz hankalina sai yafi kwanciya"


   Gyaɗa kai Dr fawan yai"bari na koma ciki daddy" juyawa yai da sauri ya shiga medical room din, Sir mubarak Yana atsaye ya dan jingina bayanshi da bango, major yana daga gefenshi, idanuwansu sunyi masu nauyi, ga gajiyar hidimar shagalin da akayi ga bacci da damuwar halin da jazz yake aciki. 

 A ƙalla sun kwashe awanni a tsaye, dare ya nutsa sosai, a lokacin da basuyi tsammani ba, sautin muryar jazz ya karaɗe kunnuwansu, da ƙarfi yake fadin"daddy zanyi maka bayani ka daina buguna, wayyo Allah kaina zai fashe zafi yake yi min"


 A gigice Sir mubarak Ya nufi dakin da aka kwantar da shi da sauri major Ya take mashi baya suna shiga suka tarar da Dr Jazz zaune tsakiyar gadon hannayenshi biyu tallabe da kanshi dake a nannaɗe da bandage, gefen gadon dr fawan ne atsaye Yana lallashinshi, gaba ɗaya ya birkice sai sambatu yake yi masu.


  A hanzarce Sir mubarak Ya zauna gefenshi, Muryarshi a raunace ya ambaci sunanshi"Jazz My son"


 Har saida ya firgita jin muryar sir mubarak, adabarbarce yake dubanshi da rinannun idanuwanshi waɗanda suka kaɗa jawur, abunka ga farar fata fuskarshi tayi ja la66ansa sunyi suntum bawan Allah Ya bugu ba kaɗan ba.

   Ido cikin ido suke kallon juna,

"Am sorry jazz, na gane kuskurena na bugunka da nayi ba tare da nayi bincike ba, Dan Allah ka yafe min" a hankali ya ruƙo hannun jazz acikin nashi ya ruƙe shi sosai.


  Babu alamun zai furta mashi kalma, sai faman jan numfashi yake yi haɗi da lumshe idanuwanshi har yanzu allurar da dr fawan yai mashi bata sake shi ba.


  Daƙyar ya iya buɗe baki ya furta"meyasa ka buge ni daddy? Dama kaine kake bibiyata daddy? Laifin me nayi maka? Kai da kanka ka faɗamin ba zaka iya ta6a lafiyar jikina ba, kuma bazaka bari wani ya cutar dani na, Ko a mafarki ban ta6a tunanin zaka yi min haka ba, sai gashi yau ka nemi ka raba ni da rayuwata....." a wahalce ya ƙare maganar yana fitar da huci.


 Girgiza kai sir mubarak yai hawaye tuni sun taru cikin idanuwanshi.

  Muryarshi asanyaye ya ce"Jazz ba laifina bane abun da ya faru, rashin sani ne, Jazz kaine tun farko baka sanar dani game da aikin sirrin da kake yi ba, a tunanina ka ɗauke ni kamar mahaifinka wanda yai silar zuwanka duniya but why kake 6oye min abunda ya shafe ka? jazz kamanta alƙawarin da muka ɗaukarwa junanmu'? Runtse ido jazz yai hawaye suka soma wanke fuskarshi.

 Cikin shessheƙar kuka ya furta"ban manta ba daddy, kayi hakuri, yaya Owais ne Yahana in faɗa maka, shiyasa ban gaya maka ba, nayi ƙoƙarin fahimtar dashi kuskuren yin hakan amma sai yace min kaima kasan da case din Yaran......." jin wannan maganar yasa hankalin sir mubarak ya ƙara tashi aruɗe yake kallon fuskar jazz tamkar yana karanto wani abu, Major da dr fawan suka kalli juna, da alama sunyi mamakin jin abunda jazz ya furta, dafe kai sir mubarak yayi da hannu ɗaya tunawa da zancen case din yaran da sojojin ƙasar ghana suka nemi hukumar sojin nigeria data kar6i case din daga hannun su, a lokacin basu kar6i case dinba sai suka nemi hukumar Isod da su shiga lamarin yaran, bai ta6a ganinsu ba ko a hoto yadaisan da zancen, sannan baida masaniya akan aikin da owais ya ɗauki Jazz Na kula da lafiyar yaran shiyasa aka samu matsala.


    Jinjina kai sir mubarak yayi, cike da danasanin hukuncin daya yanke mashi, 


  "Jazz ina ƙara baka haƙuri, dan Allah kada ka ruƙeni a zuciyarka, da ace bana sonka wallahi bazan damu da rayuwarka ba, amma saboda ƙaunar da nake yimaka ne yasa harna yi maka shisshigi......" a tsanake sir mubarak ya labarta mashi duk abunda ya faru tundaga rana ta farka daya fara jin shi yana waya a garden kan maganar kaji har zuwa ranar daya yi mashi la6e a toilet yajiyo shi yana fadin akasheta...

  "Jazz kasan ba mummunan abu kake aikatawa ba, amma meyasa kake amfani da kalamai masu hatsarin gaske kamar kalmar kisa da naji kana faɗi"?

  Numfashi jazz yaja kafin ya bashi amsa da cewa"saboda yaya Owais ya gargaɗeni akan kada na kuskura wani ya san aikin da nake yi, koda kuwa mommyna ne shiyasa nake yin amfani da waɗannan kalaman, lokacin da kaji nace bayasan hanyar da zai kashe ta ba, Ina nufin yasan hanyar da zai magance matsalarta, a lokacin Salsabeel ne ya kirani a waya, ya fada min haukan khadeeja ya motsa, shine nake fada mashi maganganun da kaji inayi"

  "Wanene salsabeel"? 

"Shine babban cikinsu, atare da yaran yake, ba ƙaramin mutun bane ya girmi yaya owais"

   Shiru Sir mubarak yayi, still bai kawar da idanuwanshi daga kan fuskar jazz ba.

  "Ya jikin naka? Ina fata babu inda keyi maka ciwo"?

 Ɗaga mashi kai jazz yai alamar Eh.

 "Yunwa fa"? 

"Bana jin yunwa, ina son yin magana da mommyna"

 "Ba zamu iya kirantaba a yanzu, tayi bacci, sai zuwa gobe zamu tafi gida"

 Don dole jazz ya haƙura da sonyin magana da mommynsa.

  A daren ranar major a resting room din dr jazz Ya zauna, shi kuma sir mubarak ya kasa tafiya yabar jazz, kan kafaɗarshi jazz ya ɗaura kanshi, anan bacci yai awon gaba da su manne da juna.


  Ataƙaice kenan abunda Ya faru daren Jiya dangane da sir mubarak. 

*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✍️*


Idan muka koma 6angaren Sheikh Imam tun bayan da Chief Ya buɗe ƙofar dakin Danish, Kowa fargaban Abunda idanuwanshi zasu gane mashi yake yi, ƙarfin hali chief owais yayi wajen zura ƙafarshi cikin ɗakin, rass yaji gabanshi yai mugun faɗuwa ganin hular sheikh imam da arab turban dinsa yashe kan floor kamar an wurgo dasu sun tarwatse, ga takalmansa ware ɗaya bakin gadon ware ɗaya kan carpet, a ruɗe chief Ya wurga eye balls dinsa kan katafaren gadon Danish, lamarin yayi matuƙar ɗaure mashi kai, ganin bargo lullu6e da mutun, ƙafafuwansa sun leƙo waje, farare sol da su, Iya neck dinsa bargon Ya lullu6e hakan ya bayyana lallausar sumar kanshi data tarwatse saman wuyanshi hatta gefen fuskarshi ta lullu6e, Chief Ya fahimci yaron ya dawo suffarshi ta mutane sai dai abunda bai gane ba Ina sheikh imam yake? Saboda kwata kwata babu shi a ɗakin babu alamar shi.


"Yalla6ai lafiya"? Salsabeel ne Ya ambaci haka yayin da yake shigowa ɗakin daga bayanshi boss man ne da prime minister hateem suka shigo ɗakin suna ƙarema ko'ina kallo.


Idanuwan mai girma prime minister basu sauka akan kowa ba sai akan matashin dake lullu6e da bargo, tun daga kan shantala shantalan ƙafafuwanshi yasoma kallo har izuwa kan brown hair dinsa, aruɗe ya furta"dama yaron macace ba Namiji ba"? ya jefa tambayar yana dubansu.


"ba maca bace, Namijine Yana da sumar kai ne" acewar Boss man


  "Ni abunda bangane ba, Ina sheikh Imam"? Chief ne ya faɗa yana bin ko'ina na room din da kallo.


    "Allah dai yasa ba wani abunne ya faru da shi ba" acewar Boss man.


   Sunyi tsaitsaye cirko cirko bakin gadon fuskokinsu da alamun ruɗanin rashin ganin sheikh imam.


   Prime minister ya kasa kau da idonshi daga kallon sumar kan Danish da yake yi, Ya ƙagara da son ganin fuskarshi.


A lokacin da ba su yi tsammani ba, suka soma jiyo motsin buɗe toilet door, kusan atare suka kai idanuwansu ga kallon ƙofar, bakowa bane yake fitowa face sheikh imam malik, hannun shi ruƙe da cazbaharshi, hankalin shi kwance sai dai da alamun damuwa akan fuskarshi.


  Nauyayyar ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, har suna haɗa baki wurin ambaton sunan shi"Sheikh Imam! Muna fata babu abunda ya same ka"?

  Jinjina masu kai yayi batare da yace komai ba, har saida ya dawo gefen gadon ya zauna tare da ɗaura idanuwanshi kan bargon dake lullu6e da danish tukunna

   A hankali Ya furta"Alhamdulillah, cikin Ikon Allah nayi nasara, Yaron ya canza halittarshi........"ya faɗa fuskarshi da matsakaicin annuri.


  Har cikin ransu sunji daɗin jin hakan, musamman prime minister, atare suka haɗa baki suna ambaton Alhamdulillah sannu da ƙoƙari malam.


 Girgiza kai sheikh imam yai kafin ya ɗaura da cewa"sai dai ina mai baƙin cikin sanar daku cewa Har yanzu baƙaƙen shaidanun dake atare da shi suna nan daram daƙam, babu alamun zamu yi nasarar raba shi da su.........."


  Kallon juna su ka yi kafin suka maida dubansu ga sheikh imam

 Cigaba da yin magana yayi"Ina buƙatar neman ƙarin bayani dangane da abunda ke faruwa da yaron? Shin Menene Yajaza mashi faɗawa tarkon miyagun matsafa? da har suka samu ƙarfin ikon Juya shi son ransu'?


  Kallon salsabeel Boss man yayi"kai kaɗaine kasan komai Ya kamata ka sanar da Sheikh Imam, kada ka 6oye mashi komai dangane da rayuwar yaran ta hakanne kaɗai zai Iya shawo kan matsalar.


 Jinjina kai salsabeel yayi alamar ya gamsu da bayaninshi.

    "Labarine mai tsayi, zai ɗauki tsawon lokaci," acewar salsabeel.


 Sheikh Imam Yace"tun da kace labarine mai tsayi, inaga mubarshi zuwa lokacin da yaron zai wartsake, Yanzu Yana buƙatar kulawarmu"


    Prime minister yace"Ni kaina zanso naji tarihin kyakkyawan matashin saurayin nan, In sha Allah saboda shi zan nemi iznin ƙara kwanakin tafiyata, but abunda nake son sani, Yaron idonshi biyu? Ko bacci yake yi"? ya tambaya yana kallon sheikh imam.


  "Ba bacci yake yi ba, idonshi biyu, sai dai bazai iya ɗaga ko yatsan hannunsa ba, shaiɗanun sun sakar mashi da kasala Ya jigata sosai, Bayan haka akwai tabonni saman fatar bayanshi" sheikh Ya faɗa tare da miƙa hannu ya ruƙo bargon tare da janshi Ya yaye shi gefe ɗaya, faffaɗan bayan danish ne Ya bayyana, Fari sol sai dai ko'ina da tabon ja.


  "Wannan tabon na bayanshi, sahun harsashin bindigar da jami'an isod suka harba mashi ne, dama ya faɗa min sunyi mashi illah" acewar salsabeel.


  Tsananin tausayinshi ne ya kama prime minister, ji yake tamkar ya rungumoshi, baisan ya akai ya tsinci kanshi da son ganin fuskar yaron ba, shi dai ya kwanta mashi arai, 

  "Nayi mamakin ganin suffarshi, naji kace min yarone amma surar jikinshi bata yara bace" prime minister ne yai magnar yana duban owais

    Chief dake atsaye ya goya hannayensa kan kirjinsa ya furta"wata'kil halittarsace haka, Girman jiki da ƙananun shekaru"

     Jinjina kai prime minister yayi kafin ya kuma cewa"baba Yanzu me yakamata muyi mashi don mu taimakashi ya dawo normal? Ko dai zamu kira likitane Ya duba shi"?

   Sheikh Imam Yace"kada ayi haka, saboda bakowa bane zai Iya tunkararshi a wannan yanayin ya zauna lafiya, kawai kubi shi da addu'a in sha Allah zai warware"

  "Akwai ruwan zam zam na addu'a da na ta6a jaraba bashi, inaga da za'a same shi wata'kil Ya taimaka mashi wajen samun lafiyarshi, Kafin rasuwar mahaifina Yana yin amfani da ruwan zam zam din wurin yin treatment din mutanan dake fama da irin lalurarshi.

  Salsabeel ne ya kora masu jawabin, sheikh Imam Yace"ƙwarai kuwa zam zam Yana da amfani, idan akwai inda za'a same shi kuyi ƙoƙarin samun shi"

  Prime minister yace"in sha Allah zamuyi ƙoƙarin samun zam zam din, baba mun gode da ƙoƙarin da kayi mana, Allah ne kaɗai zai Iya biyanka"

    Boss man yace"ya sheikh ya akai rawaninka da hular suka faɗo ƙasa? Allah yasa dai ba wani abun bane ya faru" Ya furta maganar tare da juyawa ya nufi bakin ƙofar, Ya dauko mashi rawanin da hular.

 Murmushi sheikh imam yasaki kafin yace"kai dai bari, sha'ani da baƙaƙen shaidanu ba abune mai sauƙi ba, ai dambe muka yi dasu, suna bugu ina bugu na haɗasu da ayar Allah, Ni ban ma lura babu rawanin akaina ba sai da ka yi magana" murmushi kowannansu yakeyi, maganarshi ta basu nishaɗi.

  "Yaron nan fa sai mun dage da yi masa addu'a, Yana buƙatarta, domin kuwa shaiɗanun dake atare dashi mugayen shu'umaine suna da hatsarin gaske, ba'a ta6a su a zauna lafiya, amma da yake mu da Allah muka dogara kuma munyi imanin cewa shi kadaine gatanmu in sha Allah babu wani mahaluƙi daya isa Ya karya mu sai dai mu muga bayanshi, Na tausaya ma rayuwar yaron kuma ashirye nake da in bada gudummuwata don ganin mun raba shi da su" da kakkausar murya sheikh imam yayi maganar, gaba ɗaya sun natsu suna sauraronshi, har ya kai ƙarshen maganarshi kafin chief owais ya soma yin magana a tsanake"sheikh zamu iya sanin me yaron yake buƙata a yanzu"?

Numfasawa sheikh imam yai yayin da yake bin sumar kan danish da kallo ya furta"Idan zaku Iya taimaka mashi yai wanka, tabbas zaiji daɗin jikin shi, sannan ashirya mashi lafiyayyan abincin da zaici inyaso ko abakine sai abashi tunda bai iya ci da kanshi, Bayan haka daga rana irin ta yau duk wani abu da zai yi amfani dashi kada a kuskura abashi batare da an tofe shi da addu'a ba, tun daga kan ruwan da zaisha, shimfidarshi, ruwan wankan shi da suturar sanyawarshi........"kafin malam ya ƙare jawabin, Boss man yai hanzarin tarar numfashinshi da cewa"Allah yaja da ran malam, yaron ba musulmi bane, hakan zai yiwu kuwa? Yar Uwarshi unaisah ta fada min cewa sunyi fama dashi akan ya musulunta amma yaƙiya, ko kalmar bismillah bai ta6a furtawa ba"


  Har cikin zuciyar prime minister baiji dadin jin cewa Yaron ba musulmi bane,  Sheikh Imam yace"in ba wani iko na Allah ba zaiyi wuya ya musulunta idan har shaidanun jikinshi basu rabu da shi ba, sune suke hana shi ambaton sunan Allah saboda lagwon su ne, In sha Allah zamu magance matsalar nan badajimawa ba"

 Ajiyar zuciya prime minister ya sauke, haɗi da numfasawa yace"Ina son ganin fuskarshi" ya furta hakan Yana duban chief owais, da sauri salsabeel Ya zagaya ta 6angaren daman gadon, Ya haye tare da ruko bargon da hannun shi ya tattare shi gefe ɗaya kan mattress, santala santalan cinyoyinsa farare sol sunyi sambal dasu, sai uban tabonni, kafin komawarshi maciji short ne ajikinshi haka zalika A yanzu haka da yake akwance gajeran wandonne.


  Sanin nauyin jikin Danish yasa salsabeel nannaɗe hannun jallabiyarsa ya daddage Ya ruƙo kafaɗunsa da hannayensa ya juyar dashi ya fuskanci ceilling, still fuskarshi bata bayyana ba saboda yalwatacciyar sumar kanshi data rufeta.

   Cike da zumuɗi prime minister yace da salsabeel"please, ka jinginar dashi kan headbored, Ka nannaɗe min sumar kanshi daga kan fuskarshi inason ganinshi da kyau"

  Cikin girmamawa Salsabeel Ya amsa mashi da toh, Kafin Ya daddage Ya ɗago da Danish Ya jinginar dashi jikin headboard, A hankali Ya soma janye sumar kanshi daga kan fuskarshi,

  Tunkafin Ya ƙarasa kau da sumar, Hankalin prime minsiter yai matuƙar tashi haiƙam, zuciyarshi ta soma harbawa da matsanancin speed, Yayin da idanuwanshi suka zazzaro waje, tamkar eye balls dinsa zasu fado ƙasa, haƙiƙa yayi matuƙar girgiza da ganin abunda idanuwanshi suke nuna mashi, kowa dake a ɗakin saida ya lura da yanayin da prime minister ya shiga na tsantsar mamaki da Al'ajabi, bashi ba hatta sheikh imam da Chief owais al'ajabine akan fuskokinsu.

  Muryar prime minister na rawa ya furta"Sheikh...! Owais Kuna ganin abunda nake gani  kuwa? a ruɗe ya furta maganar yana ƙarema fuskar Danish kallo.

 Sheikh Imam da al'ajabi Ya gama kamashi, Baisan sa'dda ya furta"amma dai wannan yaron Jininka ne ko? don wannan yafi ƙarfin ace kamanceceniyace ta halitta sai dai ta jini, saboda kamanninshi sun 6aci dakai da kuma yarinyar wurinka Nazli, Tamkar kayi kakinsa, komai nashi kalar naka ne, tun da Allah Ya halicceni ban ta6a ganin kama irin wannan ba, gaskiya nayi mamaki....." 

  Boss man yace"ai ba tun yau ba, nasha faɗama chief owais cewa Yaron Yana kama dashi, bani ba hatta abokanan aikin mu sun shaida hakan, sai dai wani abu daya ƙara ɗaure mun kai ayau, Yaron yafi kama da prime minister hateem, bai baro komai nashi ba, tun daga kan shape din bakinsu, dogon hancinsu da idanuwansu, Yalla6ai da zaka ga launin idonshi zaka sha ruwan mamaki, domin kuwa kalar nakune"

 Dafe kai prime minister yayi da hannun shi ɗaya, Hankalinshi Yaƙi kwanciya da kamanninsu da yaron.

   Gyaran murya salsabeel Yayi kafin ya soma yin magana yana duban su

  "Ni kaina na jima ina mamakin kamannin dake a tsakanin Chief owais da Danish, komai nasu kala ɗaya ne banbancinsu launin fata ne da kuma tsayin sumar kai, wani iko na Allah sai gashi Yalla6ai Hateem Yafi kama da Danish"

  Runtse ido prime minister yayi, baisan ya akai yake jin wani irin yanayin atattare dashi ba.


   Muryarshi araunace ya furta"ban haɗa komai dashi ba, bani da alaƙa da shi, Yauce rana tafarko dana fara yin tozali da fuskarshi, amma meyasa nake jin wani abu agame dashi? Dan Allah ku fahimtar dani na shiga ruɗani, ya akai komai nashi kalar nawa"? Yana magana la66ansa na kerma.


   "Owais ka faɗamin wanene Yaron nan? Su wanene Iyayenshi? Meyasa yake kama dani da ƴata Nazli"? Da kakkausar murya ya furta maganar saboda aruɗe yake da lamarin.

  Shi kanshi chief owais din Ya kasa furta komai, Lamarin Ya ruɗar dashi ya rikirkitar mashi da tunaninshi, bai ta6a tsammanin kamanninshi da yaron sun 6aci har haka ba.


  A hankali Ya soma yin taku Izuwa gaban Prime minister hateem dake dubanshi fuskarshi a yamutse.


      Cikin kwantar da murya ya furta"Uncle, bamu da masaniya akan su wanene Iyayen shi, saboda bai dasu a halin Yanzu, da shi da ƴan uwanshi dake ahannunmu bamusan komai nasu ba, tamkar marayu suke a hannunmu, Yarinya ɗayace mukasan Mahaifinta tajuddeen" ya faɗa yana nuna Boss man da hannun shi.

  Girgiza kai yaɗanyi numfashinshi na fita da huci yace"Owais kada ku maidani mahaukaci, nafasan me nake yi, taya za'ace babu danginshi? Kyakkyawan yaro kamar wannan?ni kawai so nake ku faɗamin meyasa muke Kama"!!! Ga dukkan alamu prime minister ya fara zaucewa, wata irin zuface take tsastsafo mashi saman goshin shi.

 Hankalin kowan nan su Yana akanshi, owais baisan taya zai fahimtar da uncle din nashi ba, Miƙewa Sheikh Imam yai tare da nufar prime minister Ya tsaya agabanshi, tare da kai hannu ɗaya ya dafa kafaɗarshi, a tsanake Ya soma yi mashi magana

  "Ka kwantar da hankalinka, yakamata ka fahimci abun da Awaisu Yake ƙoƙarin faɗa maka, su kansu basu da masaniya akan yaron, kaɗan daga cikin ikon Allah kenan, kowani ɗan adam yana da masu kama da shi A duniya....." tunkan sheikh Imam Ya ƙare maganar, prime minister yace"baba, wannan yafi ƙarfin ace kamace kawai, ka dubi fuskarshi dakyau, tamkar anyi photocopy dina, kamar dai nina haife shi, Ina jinshi tamkar jini na, ƙaunar da nake yi mashi kaɗai abun dubawace, ta zarce misali, saboda shifa na kasa runtsawa adaren Jiya, na damu da shi fiye da tunaninku........." gaba ɗaya sun rasa taya zasu shawo kan prime minister, a iya sanin su da shi bai ta6a haihuwar ɗa Namiji ba, balle ace yarom shine daya 6ata.


 "Yanzu abun da za'ai, tun da kana ƙaunarsa kuma yaron baida iyaye, mai zai hana ka ɗauki ragamar kula dashi kafin komawarka canada? Wata'ƙil hankalinka zaifi kwanciya" acewar sheikh Imam, ya fadi hakanne donya kwantar masa da hankalinsa ganin irin ruɗun daya shiga.


   "hakan yayi shiekh, Uncle ka ƙaddara cewa jininka ne shi, kana da damar da zaka Iya bashi kyakkyawar kulawa" Chief owais na ya furta hakan.


  Kalamansu sun tausasa mashi zuciyarshi, har cikin ranshi Yaji dadin jin hakan.


  "Inaso na taimaka mashi yayi wankan ya sanya sutura a jikinshi, zan kira ɗan uwana awaya don yazo ya ganshi, nasan shi kadaine zai ƙara tabbatar min da abunda nake gani a idona, sannan Idan yaron yaji sauƙi kafin in koma canada, zan je dashi gidana don in nuna ma gimbiyata shi da ƴa'ƴana nasan zasuyi mamakin kamanninsa dani musamman Nazli, hatta hasken fatarshi kalar nata ne" murmushi ne akan fuskokinsu, sunji daɗin sakewar da prime minister yayi, hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yayi ba.


    Naɗe hannun rigarshi yayi, tare da cire agogon azurfarshi, da zoben hannun shi, Ya miƙa ma owais su, da sauri owais ya sanya hannu ya kar6a, gaba ɗaya kallon shi suke da mamaki akan fuskokinsu.


   Murmushin gefen fuska yasaki har dimple dinsa ya lotsa"kada kuga ina zumuɗi akanshi ƙaunarsa nake Yi" da zolaya ya furta maganar kafin yace" wazai taimaka min mu shiga da shi bathroom room"? da sauri Salsabeel Yace"ni Yalla6ai" 

     "Yawwa, ruƙo min shi mu shiga ciki, ko da ya ke naga yana da girman jiki zaiyi nauyi, bari na kama maka" a hanzarce Ya zagaya ta 6angaren da salsabeel Yake, a lokacin sabeel Yayi koƙarin janyo danish da ƙyar ya kawo shi bakin gadon.

 Kafaɗunshi suka rurruƙe shi da prime minsiter suka miƙar dashi tsaye, wanda badan ƙarfin giant da sabeel yake dashi ba da kuwa babu mai iya ɗaga shi, jikin shi ya saki tamkar wanda baida ƙashi, kanshi ya kalli kasa sumar kanshi ta lullu6e fuskarshi, idanuwanshi suna arufe gam, zufa ta ko'ina take tsasstsafo mashi, a hankali suke tafiya dashi suna nufar toilet, har suka yi nasarar shigar da shi ciki'

   Bayan shigarsu, sheikh imam ya dubi boss man da owais

  "Inason ganin sauran Yaran da kuke ruko a hannunku"

   Da sauri Boss Man Ya amsa mashi da toh, Ya miƙa ma sheikh imam rawanin shi daya ruƙe a hannunshi tare da hularshi, godiya yayi mashi, har ya juya zai fuce muryar chief owais ta dakatar dashi

  "Boss, Ka tara yaran a main falo, Yanzu zamu sauko down"

  Amsa mashi yai da toh, kafin yasa kai ya fuce daga dakin Ya sauka down.


A hanzarce yake tattaka staircases din benan, har ya kusa saukowa down yai tozali da big guy dake tafiya cikin takun sauri, ganin boss yasa shi fadin"Ya ake ciki mutumina?

  Boss yace"Alhamdulillah Danish ya dawo ainihin suffarshi, Sai dai babu kuzari ajikinshi, Ko yatsanshi bai iya ɗagawa, ga tabonnin harbin bindigar da akayi mashi ta ko'ina saman fatar shi"

 Cike da jin alhini Big guy yace"bawan Allah, banji dadin jin hakan ba, wallahi yaron tausayi yake bani, ashe munyi mashi illa da harbin bindigar amma ina fata baiji mugun rauni ba ko"?


 Ɗaga mashi kai boss yayi alamar eh, fuskarshi da damuwa yace"ubangiji Allah yaba shi lafiya, Allah kuma ya kawo mashi ƙarshen wahalar shi"Boss ya amsa mashi da ameen kafin yace"yanzu haka Prime minister da ɗan uwanshi, sun shiga dashi bathroom zasuyi mashi wanka, sheikh imam ne ya bada shawarar yin hakan"

  Zaro ido big guy yai da zolaya yace"Yanzu wannan ƙaton balagaggen zasuyi ma wanka? Yaron fa yakai chief dinmu girman jiki,"

 Harara Boss man ya jefa mashi"laifina ne dana tsaya yin magana da ɗan ƙwaya, sai kace ba ka ji nace maka bai iya ɗaga koda yatsansa ba, lalura ce ko kai kanka akwai ciwon da sai dai adinga yi maka wanka, ba fata nake yi maka ba, ina dai kwatanta maka ne babu wanda yafi ƙarfin ƙaddara"

  Dariya big guy yasaki"Haba mutumina, nima fa wasa nake yi, nadai jinjina lamarin ne, amma baka fadamin ba prime minister baiyi mamakin ganin fuskar yaron ba"?

   Dariya boss yayi kafin yace"daɗina da kai shegen son gulma uwa mace"

 Cike da zumuɗi big guy yace"ni dai ka amsa min tambayata na ƙosa naji"

   Boss man yace"kallo yabarka, hankalin prime minister ba ƙaramin tashi yayi ba, kusan fa hauka yayi mana gaba ɗaya ya rikice tunda yayi tozali da fuskar yaron, daƙyar fa muka shawo kanshi, duk yabi ya ruɗe......" a tsanake Man ya labarta mashi komai.

 Dariyar shaƙiyanci Big guy yasaki hada tafa hannayensa yana fadin"ni dama nasan za'a rina wallahi, nifa tuntuni nake mamakin kamanninsu da yaron, koda ake maganar yana kama da chief namu saida na raya arainacewa duk ranar da hateem yayi arba da yaron sai ya sha mamaki, donni nafi ganin kamanninshi da nashi, sai gashi maganata ta tabbata" da ƙwarin gwiwa ya ƙare maganar, boss da zolaya yace"sannu malamin duba, aikinka na kyau, ka tsareni da surutu kamar kanyar da bata da daɗi, ka hanani ƙarasawa inda zanje"

  "Ina zakaje ne"? Big guy ya jefa mashi tambayar.

  "Sheikh imam ne Ya buƙaci atara mashi sauran yaran yana son ganinsu"

  Big guy yace"ai ƙwara yagansu domin kuwa suna buƙatarshi kodan saboda wannan jarin taka, ni ina da tabbacin ba'a rasa almatsutsai akanta....."dariyace ta kubce mashi daƙyar ya ƙare maganar, ganin yadda boss man ya haɗe fuskarshi.

  Harara ya jefa mashi"Idan ka isa ka maimaita maganarnan agaban chief"

 Big guy yace"ai ko giyar wake nasha bazanyi wannan gangancin ba,"

  Fuskar boss ɗauke da fara'a Yabi ta gefen big guy Ya yi gaba abunshi

   Ɗaga murya big guy yai tare da cewa"Yaran suna a ɗakin Jarinka gaba ɗayansu na tarasu anan"

  Murmushi taj yasaki, haɗi da girgiza kanshi, bakomai yasa shi yin hakan ba face sunan da big guy yake kiran Babynsa angel, wato JARI, saboda yace mashi chief zaiba auranta yafi son inda zata huta shine fa ya ruƙe abun azuciyarshi har yake tsokanarshi da sunanta.


Idan muka koma 6angaren su unaisah, tuni sun kammala yin breakfast dinsu, kowa yaci ya ƙoshi yayi hani'an, sai dai damuwa ta hanasu sakat, Hankalinsu ba akwance Yake ba, sunyi zugudum saman carpet, kowa ya zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki, jefi jefi sukan buɗe baki suce Allah sarki danish dinmu, ko awani hali yake a yanzu, a lokacin ummin america ta shiga toilet din dakin nasu.


  Batool ta kwantar da kanta kan kafaɗar unaisah, Azeeza ta ɗaura nata kan a shoulder din Sajeed, hannayensu ruƙe cikin na juna, Jemimah ta haye bisa laps din haris idanuwanta alumshe sai faman firgita take Yi tana jan numfashi kamar baccine ke ƙoƙarin yin awon gaba da ita, parveen da naufal sun jingina bayansu jikin gado fuskokinsu babu walwala, hannah kuwa ta ɗaura kanta saman laps din javed, sunyi shiru babu mai magana, daga tsakiyar carpet din tray din kayan abincin da suka kammala ci ne ba akaiga kawar da su ba, wasu daga cikinsu sai faman lumshe idanuwansu sukeyi alamun bacci suke ji.


  Jin motsin buɗe ƙofar toilet yasa Batool yin saurin runtse idanuwanta ta ƙanƙame unaisah, gudun kada ta haɗa ido da aunty ummi, fitowa tayi daga cikin toilet din, sautin takalman ƙafartane ya fargar da masu gyangyadin cikinsu, gaba daya suka ware idanuwansu akan ummi dake tunkarosu.


    Ta fahimci tsantsar damuwace atattare dasu, tun ɗazu da suna cin abinci ta lura da kyar suke cusa abinci abakunansu, tasan bai wuci damuwar halin da ɗan uwansu yake aciki bane"

    "Aunty ummi, Inaso zanje dakin danish in duba jikinshi" unaisah ce tayi maganar 

 Ummi tace"a'a, ba'a bada iznin wani daga cikin ku Ya fita ba"

 Ya mutsa fuska unaisah tayi tamkar zata fashe da kuka ta kuma cewa"aunty ummi batool ta manta doguwar rigarta a ɗakinki jiya da su ka je kwana, zanje na ɗauko mata" 

   Girgiza kai ummi tayi"basai kinje ba, zuwa anjima da kaina zan dauko mata rigarta" zumbura mata baki Unaisah tayi duk yadda taso tayi ma ummi wayau taƙi barinta ta fita.

 A ƙule unaisah tace "To waimu haka zamuyi ta zama a ɗaki kamar an kulle kaji a keji"

 Dariya ummi tasaki har fararen haƙoranta suka bayyana tar dasu kamar gonar auduga

  "Kin gaji ne"? Ɗaga mata gira unaisah tayi alamar eh.

       Gyaɗa kai ummi tayi"okey, bari na taimaka maku ku girgije jikinku," basu fahimci me take nufi ba.

   Zura hannu tayi cikin aljihun doguwar rigar jikinta ta zaro iphone dinta, duk sun ƙura mata ido suna jiran ganin me zatayi da wayar.

   Zira ziran yatsun hannunta ta ɗaura kan screen din wayar ta soma yin pressing dinta, jim kaɗan daddaɗan sautin kiɗa ya soma karaɗe bedroom din nasu, taken waƙar ed shareen mai suna Shape of you.


 Fuskarta ɗauke da shu'umin murmushi take kallonsu, sun ƙura mata ido suna kallonta, ganin ta fara jujjuya qugunta tana taka rawa.


  "Idan kuna ra'ayi ku taso muyi rawa" ɗaure fuska Unaisah tayi ranta a6ace take dubanta har ta buɗe baki zatace mata bazasuyi rawarba, Sajeed Ya miƙe Yana taka rawa ya nufi tsakiyar ɗakin, miƙewa Azeeza tayi da sauri tabi shi Ya ruƙo hannunta Yana jujjuyata, tuntsirewa Ummi tayi da dariya tana kallon su, abu kamar wasa sautin kiɗan yafara kai masu karo, Naufal ya miƙe ya ruƙo hannun Parveen suka nufi tsakiyar ɗakin suma suka fara yin rawa, Aruɗe unaisah take kallonsu kamar waɗanda akayima asiri, lallai ummi ba ƙaramar shaidaniya bace hakanan taja hankalinsu da sautin kiɗa, ruƙo hannun Hanna javed yai suka miƙa suma suka nufi tsakiyar dakin, Haris Ya miƙe Jemimah ta like mashi tana fadin itama zatayi rawar, ya ruko hannunta suka bi sahu, Ya rage saura Unaisah da Batool su kadai ne suka ki tashi.


  "Sanya damuwa aranku bazai ta6a yi maku maganin matsalarku ba, Ni taimakon ku nake sonyi don na fahimci baku san me ake nufi dajin dadin rayuwa ba, kunfi so kuyita ƙuntata kanku bayan kowani ɗan adam yana da damar da zai sanya kanshi farin ciki, If you let me do my job, you'll see the positive results soon."......" muryarta da kwarkwasa take yin magana tana kallon Batool da Unaisah.


 "Idan kunaso mu zauna lafiya daku, to ku bani haɗin kai, Ni kuma zan wayar maku da kanku, zan sanyaku farin cikin da zai kawar maku da damuwarku" da shaƙiyanci take yi masu magana tana ɗage girarta.


   Sunyi shiru babu alamun zasu tanka mata, shu'umar dariya tasaki tare da cewa"Na fahimci unaisah kece mai taurin kai, Saboda ke Batool taƙi tashi ta taka rawa ko"? Murguɗa mata baki unaisah tayi.

   "Idan kika bani hadin kai mukayi rawa zan barki ki fita daga ɗakin nan kije wurin ɗan uwanki danish...."tunkan ummi ta rufe baki unaisah tayi saurin furta"a'a sai dai ki bari in fara zuwa dakin shi, Idan na dawo sai muyi rawar"

  "Zaki rasa damar da kike da ita" acewar ummi, Ta furta maganar tare da miƙa ma batool hannunta alamar ta taso suyi yawa, cike da jin shakkarta Batool take kallonta, fuskar ummi a ɗaure tace da ita"Come to me" sai da batool tafara kallon unaisah jikinta sukuku kafin ta yunƙura ta miƙe tare da ɗaura hannunta na dama saman hannun ummin america, gam ta ruƙe hannun tajata zuwa tsakiyar ɗakin rawa suka soma takawa kamar mace da namiji haka take juya batool tana rungumeta idonta akan unaisah data haɗe fuska tana satar kallonsu.


  Canza masu waƙa tayi ta sanya masu waƙar rema mai taken baby come down, tunda sautin kiɗan Ya fara ratsa mata zuciya takasa jurewa ji tayi kamar ana janta a hankali ta miƙe tsaye tana kallon ƴan uwanta dake ta tiƙar rawa suna dariya, itama sai taji tana buƙatar yin nishaɗin kota ɗebe kewar danish dake damunta.

 Ganin ta miƙe tsaye sototo tana kallonsu yasa ummi miƙa mata hannu ɗaya alamar tazo gareta.

 Maƙe mata kafaɗa tayi alamar bazata zo ba, batool tace"please sister kizo muyi yawa atare dan Allah" harara ta watsa ma batool, muryar sajeed ce ta janyo hankalinta ga dubanshi.

  "Sister zo mu taka mana, muna buƙatarki afilin nan" murguɗa mashi baki tayi.

  "Genie dan Allah kizo muyi rawa, kinga ni banda abokin yi haris baiyi dani" da shagwa6a jemimah tayi mata maganar, hada marairaice mata fuska.

   Magiya suka dinga mata akan tashigo suyi rawar, tun tana maƙe masu kafaɗa, har dai jemimah tazo taja hannunta suka shiga filin, ai tunda tafara taka rawa kamar ɗiyar roba, daɗi ya kamasu ganin unaisah ta saki jiki tana tiƙar rawa, nan fa kowa ya bada himmah, sosai suke jijjiga qugunansu, wani abun ƙayatarwarma sai sun yarfar da sumar kansu kamar indiyawa, sautin kiɗan ba ƙaramin ƙara masu ƙaimi yake yi ba, ummi ce kaɗai take bin waƙar suma tun basu iyaba har suka fara bi saboda harshen turancine tamkar yarensu ne........:

    Dawo da waƙar farko tayi jin sun fara dauka suna bi, aikuwa gaba daya suka kware murya suna bin waƙar 

 

Baby, calm down, calm down

Girl, this your body e put my heart for lockdown

For lockdown, oh, lockdown

Girl, you sweet like Fanta, Fanta

If I tell you say I love you no dey form yanga, oh, yanga

No tell me no, no, no, no, whoa-whoa-whoa-whoa

Oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh

Baby, come gimme your lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-love

You got me like, "Whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa"

Shawty come gimme your lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-love, mm-mm


Cike da nishaɗi suke bin waƙar suna dariya fararen hakoransu kamar gonar auduga, ita kanta ummin america ba ƙaramin burgeta sukayi ba, Kamar sakarya haka tasaki baki tana kallonsu, a ƙarshe saita bar masu filin rawar ta koma gefe ɗaya tamkar dj ta goya hannayenta saman kirjinta tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi, sun bata mamaki, daga kunna masu waƙa har sun haddace ta, aranta ta ayyana lallai yaran suna da kaifin basira, yanayin yadda sukeyin rawar suna jujjuya qugunansu yafi komai tafiya da hankalinta, musamman unaisah da parveen sunfi zaƙewa sai kuma uban gayya Sajeed dama shine yafara koya masu rawa tun agidan kurkukun ƙaddara, salon rawarshi kalar ta ƴan club ce, da aji yake yinta hannun shi ruƙe dana Azeezarshi Sun tsunduma suna tiƙar rawa ko gajiya basayi.

  Da ƙarfi Sajeed Yace Aunty Ummi ki canza mana wata waƙar mai daɗi"

   Da sauri ta ɗauki wayar ta kunna masu waƙar alen walker.

  Unaisah na soma jin taken waƙar tayi saurin kamawa tafara bi  saboda tasanta tun da jimawa, sajeed ma ya iya waƙar, atare suka haɗa baki suna bin waƙar

   Lost in your mind, I wanna know

Am I losin' my mind?

Never let me go

If this night is not forever, at least we are together

I know I'm not alone

I know I'm not alone

Anywhere, whenever

Apart but still together

I know I'm not alone

I know I'm not alone

I know I'm not alone

I know I'm not alone

Unconscious mind, l'm wide awake

Wanna feel one last time

Take my pain away......."


Abun da basu sani ba, tun ɗazu boss man Ya shigo ɗakin, yana daga tsaye bakin kofar Ya goya hannayenshi saman kirjinshi, ɗaya bayan ɗaya yake binsu da kallo kafin ya tsayar da idanuwanshi akan Unaisah da ta zaƙe tanata jujjuya qugu tana bin waƙar, tsabar mamakine Ya hanashi yi masu sallama, bai ta6a tsammanin zata Iya yin rawa har haka ba,Yarinyar da kullum take acikin damuwa.

 Ummin america tana faman wurwurga eye balls dinta akansu karaf idanuwanta suka hango mata boss man dake atsaye yana kalonsu, da sauri ta kashe sautin, ta kama yin ƴan kame kame, su kuwa prisoners koda ta kashe sautin basu lura da shi ba, a shagwa6e Jemimah ta bubbuga ƙafa tana fadin"wayyo Allah aunty ummi, meyasa kika kashe mana abun, ni wallahi bangaji ba, dan Allah ki sake kunna mana muyi rawa mu girgije" ta faɗa tana karkaɗa ƙaramin qugunta, gaba ɗaya suka tuntsire da dariya.


    Banda ummi data kame kanta 


  "Please aunty ummi ki kunna mana mu ƙarasa yin rawar" acewar parveen

   idanuwanta akan fuskar boss dake tsaye yana kallonsu, Sun juya mashi baya shiyasa basusan da zaman shi ba, ita kadaice take Iya ganin shi.


  A wayance tace"nifa ba don wani abu na kunna maku sauti ba, kawai na fahimci kuna acikin yanayi na damuwa shiyasa nayi ƙoƙarin don in sanyaku nishaɗi, kuma Alhamdulillah naga canji atare daku...." tunkan ta ƙare maganar, Boss man ya ɗaga hannayenshi yai clapping da ƙarfi haɗi da furta"Sannunku da ƙoƙari" a firgice suka waiwayo baya suna dubanshi kamar wadanda suka ga dodo.

   Unaisah hada dafe ƙirji tana fadin"Boss tun yaushe ka shigo dakin nan"?

 "Tun time da kika fara rawa ina atsaye ina kallonki" wata irin kunyace ta kamata da sauri ta juya ta nufi saman gado ta haye ta kifa kanta jikin pillow tana dariya.


 Hakan da tayi yayi matuƙar bashi dariya.


ɗaura idanuwanshi yayi akan fuskar ummin america sai faman ƙyafƙyafta idanuwanta take yi.


  "Ummi Amanar da muka baki kenan? A matsayinki na mamansu kin tarasu akan idonki suke tiƙar ruwa, ke da kanki kika kunna masu sauti, ƙiri ƙiri so kike ki maida mana ƴa'ƴa ƴan rawa ko"? 


A ruɗe ta furta"I'm sorry Sir if I offended you, but I didn't have any bad intentions. I was just trying to make them happy because I noticed they were worried about their brother's illness. That's why I tried to cheer them up......" aladabce tayi maganar, tana matuƙar girmama boss man saboda karamcin da yake yi mata, yafi sakar mata fuska akan sauran jami'an isod. 


  "Kada ki damu babu komai nima nayi maganarne kawai bawai ina nufin hakan ba, ai nasan ba zaki ta6a yin abunda zai 6ata masu tarbiyaba ba, yau dinma kinyine donki ɗebe masu kewa kuma naji dadin hakan Na yaba da tunaninki, tunda gashi nagani da idona kin taimaka masu da kika sanya su nishaɗi, Na jinjina maki" ya faɗa hadi da yi mata alamar jinjina da yatsanshi.

 Ƙayataccen murmushi tasakar mashi"nagode da ka fahimce ni"

  Mayar da dubanshi yayi akan su sajeed dake tsaye suna kallonsu

  "Ay min afwa na katse maku jin daɗin ku, nima ba laifina bane laifin sheikh imam ne daya buƙaci son ganinku don haka in akwai mai ƙorafi ya tanadi abunsa idan munje gabanshi sai ku faɗa mashi" da zolaya yayi masu maganar, murmushi kowan nan su yasaki.

Unaisah jin an ambaci sunan sheikh Imam da kuma maganar yana son ganinsu yasa tayi sauri saukowa daga saman gadon, 

  A kunyace ta kalli boss man tana faman noƙe kai tace"mu tafi boss"

  Ruƙo hannunta yai acikin nashi, da sauri Batool ta ruƙe ɗayan hannun nashi sukayi gaba su naufal suna abiye da bayansu, gaba ɗayansu suka nufi falon hada Ummin America. 

   

A tsakiyar falon su ka dakata da yin tafiyar Boss Man yace"Ku jira anan bari naje na sanar dashi" harya kama hanya zai tafi Unaisah ta kwala mashi kira, a hanzarce ya juya yana kallonta.


  Sosa kai ta ɗanyi da hannunta kafin tace"am..dama inaso ne na tambayeka awani hali danish dinmu Yake aciki ne"?


  "Ya dawo mutun" wani irin farin cikine Ya lullu6esu, musamman unaisah bakinta yaƙi rufuwa

  "sai dai babu ƙarfi a jikin shi, bai iya yin komai ko yatsan hannun shi bai iya ɗagawa" lokaci ɗaya murna ta koma ciki jin abun da Boss man Yace.

     jikinsu duk yai sanyi, Unaisah tace"baida lafiyane"? Ɗaga mata kai yai alamar eh, ya ƙara da cewa"kada ki sanya damuwa aranku, zaiji sauƙi in sha Allah, addu'arku yake buƙata"

  Cike da zumuɗi tace"zan Iya binka zuwa ɗakin nashi"

  Jim ya danyi kafin yace"No, ki tsaya tare da ƴan uwanki, zuwa anjima za'a baku damar ku ganshi" jiki asanyaye ta amsa mashi da toh.

    juyawa boss man yayi da sauri Ya haye upstairs.

   Ajiyar zuciya kowannansu ya sauke, ummi dake atsaye harta fara gajiya, wuri ta samu saman sofa ta zauna tare da ɗaura ƙafarta ɗaya bisa ɗaya, taci gaba da danna wayar hannunta.

      "Mu zauna kafin malamin Ya ƙaraso acewar Unaisah"

     Amsa mata su ka yi da toh, kowa ya samu wuri Ya zauna, sanyin A.c sai ratsa fatar jikinsu Yake Yi, sunyi shiru babu mai yin magana acikin su, sai faman ƙyafƙyafta idanuwansu suke Yi, duk sun ƙagara da son ganin malamin


Tsawon mintuna ƙalilan, suka soma jiyo takun takalmansu, a hanzarce su unaisah suka kai dubansu gare su.


Sheikh imam ne agaba, daga bayanshi boss man ne tare da Big Guy.


Tunkafin Ya ƙaraso cikin falon Yake binsu da kallo, hannunshi ruƙe da cazbaharshi, a tsakiyar sofa set din suka dakata da yin tafiyar, ummi sam bata lura da su ba, hankalinta na akan wayarta da take dannawa.

   Cikin girmama su unaisah suka sauko daga saman sofa, suka dawo kan carpet, atare suka haɗa baki wurin gaishe da shi, hakan ba ƙaramin burge shi yayi ba, sai faman sakin murmushi yake,

  "Masha Allah, kyawawan ƴan mata da samari, fatan na sameku lafiya" amsa mashi sukayi da lafiyalou.

  "Alhamdulillah, ubangiji Allah ya Albarkaci rayuwarku..." kafin Sheikh Ya ƙare maganar, Boss man Ya kira sunan ummi, a hankali ta ɗago tana kallon shi"bakiga sheikh imam bane"? Adabarbarce ta mamaita sunan malamin da boss Ya kira mata, kasancewar Ya juya mata baya bata samu damar ganin fuskarshi ba, Jin muyarta yasa sheikh imam yin saurin juyowa baya don ganin wacece.........."


(🔥🔥🔥Labari Ya dauko zafi, da zarar kunga na rubuta Takun ƙarshe to kowa ya daure damararsa domin kuwa anan ne badaƙalar take, anan ne mai afkuwa zata aiku🔥🔥🔥😳

*mu haɗu next page monday idan Allah yakaimu da rai da lafiya in sha Allah zan baku double page a haɗe a matsayin bashin da nace zan biya, long page zanyi na ƙarshen book two sannan game bukatar cigaba da karanta prisoners complete book one two and 3  500 ne zaku tura ta bank acct dina, ga ta inda za'a tuntu6eni 08103884440*

3196407426

Bature Hafsat Muhammad

First bank 

Idan kin tura zaki bada hoton receipt amatsayin shaida🤗

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post