Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe episode 1


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe episode 1

 ~TAKUN ƘARSHE~

_______________________Boss Bature✍️

*😈PRAVIN😈*

A kwance Yake saman gadon Hajjaty, Idanuwanshi suna fuskantar Ceilling, tsantsar 6acin raine akan fuskarshi, ranshi ya 6aci da korar karan da Chief Owais yayi mashi agaban su senate lateef, bakomai yafi ƙona mashi rai ba face yadda suka gaza dakatar da shi, hakan ya ƙara tabbatar mashi da cewa shi bakowa bane A family din, Kwandon shara yafi shi amfani, tsawon lokacin da yake akwance babu sallah babu salati, Yana ji anata kiraye kirayen sallar magrib har aka fara na isha'i bai motsaba, yaci alwashin sai Ya tarwatsa zuciyar owais, yajima yana da wannan burin Allah bai bashi ikon yin hakan ba, amma yanzu yafara tukfa da warwara akan ta wace hanya zai 6ullo don ganin ya karya mashi zuciya"?


    Miƙewa yayi daga kwancen da yake, ya jingina bayanshi da pillow, fuskarshi babu annuri ko misƙala zarratin, tunani yaci gaba dayi akan ta wace hanya zai ta6a zuciyar chief owais ta yadda zai azabtar da rayuwarshi, yayi zurfi acikin tunanin shi motsin buɗe ƙofar toilet ya fargar da shi, hajjaty ce ta fito sanye cikin jallabiya ta ɗaure kanta da mayafi, alwala ta ɗauro, ganin shi azaune ne yasa tayi saurin furta"Pravin! Me kake yi har yanzu baka tafi masallaci ba? Ai nayi tunanin zan fito na taras babu kai aɗakin" shiru yayi bai tanka mata ba sai dai binta da yayi da idanu kamar wani mazuru.


>

 "Magana nake yi maka, ko akwai wani abu ne dake damunka? Naga 6acin rai akan fuskarka"


      Saukowa yayi daga saman gadon Ya nufe ta yana huci ya soma magana"Ni da wancan Uban ƴan Ji da kan ne, Harni zai kora daga ɗaki agaban Iyayenshi ba tare da sun tsawatar mashi ba"? Adabarbarce ta furta"bangane akan wa kake magana ba"

Dogon tsoki Yaja kafin Ya kwashe duk abunda Ya faru Ya sanar da ita....


Cikin sanyin murya tace"Owais bai kyauta ba, amma kaima da laifin ka pravin, meyasa kake son shisshige masu ne? Tun da sun nuna basu so to ka daina mana, Ka tsaya A iya matsayinka na surukinsu......" wata irin gigitacciyar tsawa Ya daka mata, Har saida taji gabanta ya fadi, ta shiga zazzare idanuwanta akan fuskarshi Ya canza mata tamkar ba shi ba.


   Nuna ta yayi da yatsan hannun shi"Idan ba zaki kwantar min da hankalina ba, toh kada ki kuskura Ki yi abunda zai ƙara harzuƙa Ni" Muryarta Na rawa tace"Naji amma dole na fada maka gaskiya pravin, mu dukan mu muna fuskantar wulakanci daga wurin waɗanda basa ƙaunar mu a family din nan, kuma ba komai ya jawo hakan ba face zaman da kake Yi agidansu...." Idanuwanta acike tab da ƙwalla ta ƙare maganar.


Lumshe idanuwanshi ya ɗanyi na wani lokaci ba tare daya furta mata komai ba, har saida ta fidda rai da zaiyi mata magana tukunna Taji Yace"Naji zanyi tunani akan maganar, Yanzu akwai wani taimako da nake son Kiyi mini My wife," natsuwa tayi tana sauraron shi don jin me zaice mata.


   "Kinga ni bani da halin da zan Iya shiga cikin su don jin me zasu tattauna atsakanin su tunda owais yana nan bazai bari naje ba, Inaso kiyi min recording duk abun da zasu tattauna tun daga farko har ƙarshe" tsantsar ruɗanine akan fuskarta.


  "Akan wani dalili? Meye naka aciki da kake son jin sirrinsu"! Idanunta azare ta furta maganar.


 Matsawa yayi dab da ita, da yake ɗan duniyane sai ya sassauta muryarshi ta yadda zai shawo kanta.


  "My wife, mutanan sunyi mana halacci daga ni har ke, ba zamu so wani abu da zai cutar da su ba, ai kinga abun da Ya faru Jiya" daga mashi kai tayi alamar eh.


 "Maƙiyane suke ƙoƙarin halaka Baba Obinna, shiyasa suka Turo da macijin nan don Ya hakalar da shi" waro idanuwa waje tayi tamkar kwayar zata faɗo ƙasa.


   "Bashi kaɗai ba, Kowa Na family din nan zata shafa, abunda baki sani ba, Macijin Mutunne fa" dafe ƙirji tayi da hannu ɗaya amatuƙar ruɗe take kallon shi.


  Komai daya faru saida pravin Ya sanar da ita, hada maganar zuwan sheikh imam da canza halittar Danish, baiwar Allah duk tabi ta ruɗe tasha jinin jikinta.


   Muryarta na rawa ta furta"Inna lillahi Wa'inna Ilaihirraji'un,


Afakaice Pravin Yasaki shu'umin murmushi, ganin Ya fara Yin nasara akanta, Yaci gaba da cewa"abun da nakeso na fahimtar dake, Ni ƙoƙari nake yi don ganin na taimaki rayuwar Ahlin nan, wallahi bana son abun da zai cutar da su, shiyasa nake shisshige masu don jin meke faruwa a tsakaninsu ta hanyar hakan nake taimaka masu wurin shawo matsalar dake addabarsu, ɗazu dana shiga dakin owais Ya hankaɗoni waje, zan wuce ta falo naga sheikh imam da wani mutum ban kulasu ba, saboda shi kanshi sheikh Imam din Ina zargin hada shi cikin masu shirya maƙarƙashiya a cikin family din nan"


 Girgiza kai hajjaty tayi"a'a pravin, bana tunanin hakan, Ina kyautata mashi zato, saboda shi aminin obinna ne, kuma yajima yanayi ma family din nan hidima, gaskiya Imam malik bazai iya yarda ahaɗa baki da shi don cutar da familyn obinna ba"


Ta6e baki pravin yai kafin yace"hmm bakisan halin malaman nan ba, yawancin su fuska biyune dasu, A fili musa a zuci fir'auna, duk wanda fa kika ga ya ra6i familyn obinna ba alkhairi bane ya kawo shi"


 "Kana nufin hada mu kenan?" Hajjaty ta jefa mashi tambayar

 da buɗar bakinsa sai cewa yai"ai mu mun riga da mun zama jini ɗaya da su, ina magana ne akan  ire irensu Imam malik masu zuwa kar6ar zakka"


Shiru hajjaty tayi tana nazarin maganar shi, kafin tace"yanzu shi yaron yana agidan owais, tare da sauran yaran daka fada min"?


"Ƙwarai kuwa, Ya kawo mugun abu ya ajiye agidansa, babu fa wanda yasan yazo ƙasar nan, shigowar sirri yayi, kedai kawai Allah ya shiga tsakanin mugu dana gari amma fa akwai matsala idan har basuyi gaggawar ɗaukar mataki ba......" ya faɗa yana mai nuna damuwarshi.


  Ruƙo hannayenta yai acikin nashi"My wife, Ki bani haɗin kai don ganin mun taimaki ahlin nan kodan saboda halaccin da su ka yi mana, Inaso muyi masu gwanintar da zasu yi alfahari da mu wata rana" wasa wasa pravin yadinga tunzurata har yasamu nasarar shawo kanta.


Cikin sanyin murya tace"In sha Allah, zan baka haɗin kai mijina, zamu haɗa hannu don ganin mun yaƙi duk wani mugu dake da mummunar manufa akan zuri'ar baba Obie" da ƙwarin gwiwa ta furta maganar, babu wasa a kalamanta.


Wani irin daɗine Ya ziyarci zuciyar pravin yayin da yake kallonta.


 "Zan tayasu da addu'a, ubangiji Allah Ya kare su daga sharrin maƙiya da mahassada, Ya Allah duk wani mai mugun nufi akan zuri'ar baba Obie, Ya Allah Ka toni asirinsa, ka hana shi zama Lafiya, Bayin Allahn nan ni ban ta6a ganin mutane masu kyakkyawar zuciya irinsu ba, amma ahaka wasu bakin ciki su ke yi da ci gabansu......" har cikin zuciyarta take furta maganar, don ita harga Allah tana ƙaunar familyn baba Obie, tana matuƙar sonsu bata son duk wani abu da zai cutar dasu koda kuwa Hajiya saratu ce.


"Yanzu abunda za'ae, kiyi sauri Ki yi sallar, Idan Kika Kammala ki ɗauki wayarki ki tafi second falo, ina da tabbacin acan zasu zauna suyi tattaunawar, ki riga su zuwa ki saƙa wayar inda ba zasu gani ba, bayan kin danna recording, Inyaso daga baya idan suka tafi saiki koma falon ki ɗaukota ki kawo min, yaya sharafuddeen ma Yazo gidan, naji  jiniyar shigowar motocinsu, Har leƙawa nayi ta window naganshi"


Amsa mashi tayi da toh, ta nufi closet din kayanta ta dauko Hijab ta tura a jikinta, saida ta kabbara sallah tukunna Pravin ya shiga toilet domin yin alwala, a ɗakin yai sallar magrib da isha'i kafin Ya gama sallar, tuni hajjaty ta fuce daga ɗakin, zama yayi kan darduma yana ta yin saƙe saƙe acikin zuciyarshi,


Kamar yadda ya tsara mata haka ta aiwatar,  tun kafin su shiga falon hajjaty ta riga su zuwa ta kunna recording da dabara ta shiga falon kamar tana gyara shi, a hankali ta ajiye wayar a karkashin sofa table, kafin ta fito daga falon ta nufi kitchen domin shirya masu abun da zasu sha.


Bayan tafiyar hajjaty, da ƴan mintuna Gaba ɗayan su suka shigo Second  Falo din wanda ya kasance na musamman dake A gidan Baba Obie, an wadata shi da Luxury Furniture ba kasafai suke amfani da shi ba, sai Idan za su yi zaman tattaunawa tukunna ake buɗe shi, wani irin ni'imtaccen sanyin A.c ne ka ratsa cikinsa, dare ne tamkar da rana saboda wadatattun Chandeliers masu haska ko'ina sako da Lungu, Idan ba agogo Ka kalla ba ko sararin samaniya ba zaka ta6a gane dare ne ba a gidan baba Obie.


 Bayan kowan nan su ya samu wuri ya zauna saman sofa, Sheikh Imam ya fara buɗe masu taron da addu'a, kafin daga bisani, baba Obie yaba Owais damar yi masu bayani dangane da Yaran da yake ruƙo a hannun shi.


  A tsanake Ya labarta masu tun daga farkon zancen har zuwa karshe kamar yadda Ya fada masu ɗazu.


  Mutum ɗaya ne baisan da zancen ba, Lokacin da abun ya faru baya agidan sai yanzu yake ji daga bakin Owais.


"Owais dama bayan yaran dake acan gidan da Jazz yake Aiki Akwai wasu A gidan ka" Fuskar Sir mubarak da alamun ruɗu ya furta maganar.


Jinjina mashi kai Owais Yai alamar Eh, nan take ya yanke shawarar sanar dasu dangane da abun da ya faru tsakanin shi da jazz jin cewa sun san da zancen yaran, bayan ya labarta masu, kowan nan su ya jinjina ma lamarin sai dai har yanzu mutun uku basu Goyi bayan zaman Yaran a estate din ba.


Sheikh Imam ya ɗaura da cewa"naji daɗin taruwar da mu ka yi anan kuma ina fata zamu samu maslaha, da farko dai Yaran ba masu cutarwa bane, ba abun da ku ke tsammani bane, Ni shaida ne akan hakan, Mutane ne su kamar kowa, hatta shi kan shi Yaron da yake rikiɗa cikakken mutunne, kamar yadda Owais ya faɗa maku Ni da kaina na duba shi, kuma nayi magana da shaiɗanun jikin shi, wataƙil ko dan baku ta6a ganin mutun ya rikiɗa bane akan idon ku, shiyasa abun Ya ruɗar daku, Amma Ni nasha gani akan idona mutun ya rikiɗa Koya 6ace Idan muka ja mashi ayar Allah....." ya ɗan dakata da yin jawabin yana kallon su, Senate Lateef ya haɗe fuskarshi babu annuri ko misƙala zarratin shi fa yana akan bakan shi.


 Duk sun natsu suna sauraran sheikh Imam sai da yakai Aya tukunna Senate Ya fara magana rai a 6ace"Ni bazan ta6a goyan bayan tsintattun Yaran su  zauna a family din mu !! Bazai yiwu ba wallahi, Saboda Shi jiya mahaifin mu ya kusa zaucewa adaren jiya bai runtsa ba, Da firgici Ya kwana, sannan itama saratu bata runtsa ba a zaune ta kwana saboda gizan da macijin keyi mata, A haka akeson a Ƙaƙaba mana su a family? ya jefa tambayar yana kallo su sheikh imam babu wanda yai yunƙurin dakatar da shi "Ai daga ji babu Alkhairi Atattare da su yakamata aduba maganar“ ya faɗa yana mai ƙara jaddada maganar shi.


   Gaba ɗaya idanuwansu akan shi, sai da ya ƙare maganar, His excellency abdul Razak Yace"Ni ban hana ataimake su ba, Amma bazai yiwu su zauna mana a estate dinmu ba, tun da yaran basu da asali, me zai hana a ɗauke su akaisu Orphanage home dinmu dake anan garin Abuja, In yaso sai mu dinga tallafa masu, amma fa ban da wannan yaron mai fama da aljanu ba zamu lamunta da zaman shi agidan marayu ba, zai iya cutar da mutane, kawai aware shi shi kaɗai yayi rayuwarshi har zuwa lokacin da zai samu warakar lalurar shi"


Tun da suka fara magana Shiekh Imam da chief owais suke bin su da kallo, Shi dai Prime minister ya rasa ta cewa ganin yadda suka haƙiƙance akan ƙin amincewa da zaman yaron, Mai girman sharafuddeen ma yana sauraransu sai dai hankalin shi yafi karkata akan ɗan uwanshi, ya fahimci hankalin shi ba a kwance yake ba dama shi tul fil azal bai cika son rikici ba mutunne ma'aboci son zaman lafiya bayason hayaniya.


  Gyaran murya baba Obie Yai masu, hankalinsu ya dawo kanshi.


   "Kun gama magana"? his excellency deen yace"Eh baba, mu kawai Yaron ke bamu son zaman shi acikin estate dinmu, su sauran Yaran ni bani da ja akansu, tun da su lafiyarsu ƙalau suyi zamansu agidan owais din ko akai su gidan marayun mu...." kafin Deen ya ƙare maganarshi, senate lateef yai hanzarin tarar numfashinshi da cewa"bazai yiwu ba, Nifa ban lamunta da su zauna a estate din nan ba, sannan dole ayanke alaƙar su da danginmu, idan taimakon nasu ya zama dole zamu haɗa masu kuɗin da zasu ishesu suyi rayuwarsu, shi kuma Prime minister Hateem satin da zamu shiga ya hanzarta barin ƙasar nan, zaifi mana kwanciyar hankali, tun da na fahimci idanuwanshi sun makance akan yaron da bai hada alaƙa da shi ba"


 ya faɗa fuskarshi aɗaure, yayin da yake kallon Prime minister Yaci gaba da cewa"Sarai kaga abunda ya faru adaren jiya, amma ka kau da idonka, damuwarka akan yaron ce ba akan mahaifinmu ba, maimakon tun da asussuba ka kamo hanya kazo gida donka duba shi ka ga ya yakwana jiya sai ba ka yi hakan ba duk kabi ka zauce akan yaron da bakasan asalin shi ba...."


Tsabar yadda senate ke magana har wani gumi yake fitarta, duk da sanyin A.c na falon, Lamarin yayi mugun ɗaurewa Sheikh Imam kai sai faman jinjina kai yake yi, maganganun senate ba ƙaramin fusata Chief owais su ka yi ba, tun da ya duƙar da kanshi ƙasa bai ɗago da shi ba, ƙoƙari yake yi don ya lallashin zuciyarshi idan ba haka ba komai zai Iya faruwa!!.


Senate yaci gaba da cewa"kai kuma Owais," ya faɗa yana nuna shi da hannu"ka 6ata min rai! Meyasa ka ke yin komai gamon kan ka? ba tare da ka nemi shawarar mu ba? ko dawowarka Nigeria Yakamata ka sanar damu, amma sai ba ka yi hakan ba kamar kai ke da kan ka, sannan ka kwaso mana wasu tarkace acikin family batare da ka sanar damu ba, me hakan ke nufi? Bamu da amfani ne ko bamu isa dakai  ba ne?" a zafafe Senate Lateef yayi maganar yana duban chief owais, wanda yayi shiru yana sauraron shi batare daya yi yunƙurin tanka ma shi ba.


"Allah Ya huci zuciyarku, Na fahimci gaba ɗaya ranku Ya 6aci dangane da abunda ya faru Jiya Ina mai baku hakuri amadadin Owais" mai girma sharafuddeen ne yayi maganar yana mai tausasa harshen shi.

 

 "Bai kamata kan wannan maganar mu ɗaga hankulanmu ba, Owais dai muke iko dashi, Sannan Kune manyan Family duk abunda kuka zartar dolen mu ne muyi biyayya akai, ko munaso ko bamu so," Jin maganar sharafuddeen yasa senate yafara sassauta fushin fuskarshi, hatta sauran sun ɗan samu natsuwa.


 "Baba, Hukunci ya rage naka, Kai muke sauraro duk abunda ka zartar dangane da yaran nan wallahi zamuyi maka biyayya" in a calm voice sharafuddeen ya faɗa yana duban baba obie.


 Gaba ɗaya hankali ya dawo kan Baba Obinna, dake zaune kan sofa, sandar shi tana a jingine da sofa hand.


 sun ƙagara da son jin amsarshi, saboda shi kaɗaine mai faɗa Aji.


"Mubarak!" da sauri sir Mubarak ya ɗago ya kalleshi cikin girmamawa ya amsa mashi da na'am baba.


  "Banji kace komai ba"


Murmushin gefen fuska Sir mubarak ya yi kafin yace"Baba, ni bani da matsala wallahi, yaran nan ba akaina zasu zauna ba, owais ne ke kula dasu akan me zan damu? Na yarda da shi kuma nasan bazai ta6a kawo abunda zai cutar da zuri'armu ba, Ni dai inayi mashi fatan Alkhairi duk shawarar da ka yanke zamuyi biyayya"


  Chief yaji daɗin maganar sir mubarak, dama yasan bazai bashi matsala ba.


  "Aminina, naji kayi shiru, inaso naji daga gare ka" baba obie ne ya faɗa yana duban Imam malik.


    Murmushi ya saki, Yana mai fara'a yace"wannan abu na ku ne na Ƴan siyasa, Kun san yanda ake jefa ƙuri'a waɗanda suka fi rinjayi, maganarsu yakamata aɗauka, Nidai anawa ganin kenan, Yaro dai bame cutarwa bane, jarabtace ta ubangiji babu wanda yafi ƙarfin Allah ya jarabce shi acikin mu, shi kuma owais Jinin ku ne Ku kan ku kun yaba da hankalinsa, ni banga wani abu da zaisa ace za'a yanke alaƙarshi da yaran ba yakamata aduba maganar nan" cikin Hikma Imam malik yake yi masu magana, har cikin ranshi baison yaji suna maganar korar yaran daga familyn Obie.

  

Jinjina kai Baba Obie yayi kafin ya kai dubanshi ga sharafuddeen.


  "Meye ra'ayinka dangane da yaran"?


"Baba, Ni bani da matsala, kamar yadda  yaya Mubarak Ya faɗi, Nima haka, Kafin mu yanke hukunci yakamata mu yi wa kan mu adalci dasu kansu Yaran, Abun da Ya faru da ɗan uwansu bayin kanshi bane, Allah ne yake jarabtarsa, gaba ɗayanmu musulmai ne kuma munyi imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, so yakamata mu kar6i yaran nan hannu biyu mu rungume su, Sannan Yaran nan fa ba muke ɗaukar ɗawainiyarsu ba, ba agidan mu suke zaune ba, Agidan owais suke zaune shi ne ke kula dasu kuma shine ke da alhakin duk wani abu da zai faru, babu yadda za'ai araba owais da yaran nan! Saboda Bincike su ke yi a kansu, Hukumar Sojin america suna da sanya hannu akan case dinsu, bazai yiwu owais ya rabu da su ba...." jin wannan maganar ta sharafudeen yasa senate ɗaure fuska, gani ya ke yi kamar hada baƙar magana sharafudeen ya gaya mashi daya faɗi cewa agidan owais suke zaune kuma shi ke ɗaukar ɗawainiyar shi, maganar ta sosa ran shi, Deen da abdul razak sun fara aminta da kalaman sharafudeen akan zaman yaran.


  Bayan Sharafuddeen Ya kammala maganarshi, Baba Obie Ya ambaci sunan Hateem, A hankali ya ɗago da idanunsa waɗanda suka kaɗa jawur da su, Muryarshi adisashe ya furta"Bani da abin cewa, duk hukuncin da aka yanke baba zanyi biyayya"


Shiru su ka yi na wani lokaci babu wanda ya ƙara furta magana acikinsu  falon yayi tsit kamar mutuwa ta gifta.


Shigowa falon hajjaty tayi da sallama a bakinta, hannunta biyu ruƙe da faranti daga saman shi Tea pot ce tare da cups, daga bayanta Abla ce tare da Sophia kowan nan su ya ruko tray na kayan abinci, Amsa masu sallamar sukayi cikin girmamawa suka sauke trays din kafin suka gaishe da su sheikh Imam da sauran mutanan falon, da fara'a suka amsa masu, kafin daga bisani suka fuce daga ɗakin.


      Babu wanda yai yunƙurin ta6a kayan abincin, kowa kanshi ya ɗauki zafi.


  "Aminina, bismillah" Obie ne ya furta hakan harya yunƙura da niyar ya zuba mashi Tea a cup da sauri Imam malik yace"Alhamdulillah, kafin na baro gidan Hateem na cika cikina babu yunwa atare dani,"


Cikin kulawa obie yace"Ban yarda ba, amma tun da kace haka, Bari na zuba maka tea din kasha, nasan zaka ji dadin shi, Hajjaty ce ta haɗa shi"


 Sheikh Imam na murmushi yace"na fahimci ba ƙaramin ji kake da matar nan ba"

Murmushi obie yai batare dayace komai ba.

 Owais ne ya miƙe ya nufi tray din ya dauki tea pot ya tsiyaya masu tea a cups din yabi kowan nan su Ya miƙa mashi, ba tare da ya zuba nashi ba ya koma ya zauna.


  "Ba za ka sha ba"? Hateem ne yai mashi maganar, Calmly ya furta"bani buƙata" 

 Bayan kowan nan su ya kur6i tea din, baba obie ya soma magana yana duban fuskokin su.


"Na yanke shawara....." bai ƙarasa maganar ba, ganin yadda suka ɗago suna kallonshi Ya fahimci sun ƙagara da son jin mai zai ce ne.


"Dangane da abun da ya faru jiya, na ruɗe ne shiyasa harna firgice, amma yau da Owais ɗina yayi min bayani na fahimce shi, na yarda yaron mutunne kuma ba mai cutarwa bane, tun time da abun ya faru har ya shigo gida na, ya samu damar da zai iya cutar da mu amma bai yi hakan ba, sannan naga ƴar uwarshi taje gare shi ta lullu6e shi da rigarta tana kuka tana rokon shi akan ya canza halittar shi ya zama mutun, nayi mamaki ƙaramar yarinya bata ji tsoron tunkarar shi ba a suffar maciji, sannan baiyi yunƙurin sarar ta ba, hakan ya ƙara tabbatar min da cewa mutunne da gaske......" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Owais da Hateem da sauran masu goyan bayan zaman su, In ka cire Senate lateef donshi har ga Allah bai yarda da yaran ba.


Numfasawa baba obie yai, kafin yaci gaba da yin maganar sai da ya fara kur6ar tea din hannun shi.


  "Na amince su cigaba da zama a estate din mu"! A matuƙar ruɗe Senate lateef ke kallonshi da tsantsar mamakin yadda ya amince da zaman tsintattu a zuri'ar su, zuciyar shi ta sosu sai dai bai yi kuskuran katse mashi maganar shi ba, wani irin annurin farin ciki ne ya bayyana akan fuskar Hateem da sauran magoya bayan zaman yaran a estate din.


 "Amma abu ɗaya ne ban yarda da shi ba"!! ya faɗa Yana Shafa gemunshi da hannu ɗaya, yayin da idanuwanshi ke akan fuskar Hateem da chief Owais, kamar yadda yake kallonsu haka suma suke kallon shi.


  "Hateem, bana so wani abu Ya ƙara shiga tsakaninka da Yaron, babu kai babu shi, ban amince ka taka inda yake ba Har ka koma Canada," Ras yaji gabanshi yai mugun faɗuwa, baisan sa'adda ya sauko daga saman sofa ya dawo kan carpet ya zauna, motsa la66ansa ya soma yi da niyar yin magana da sauri sharafuddeen Yai mashi gyaran murya nan take Ya fahimci me yake nufi, ƙoƙarin haɗiye damuwarshi yayi, In a cool Voice yace"Shikenan baba, Na amince, amma dan Allah Ina neman alfarma awurinka" a marairai ce yayi mashi maganar.


 "Ina sauraronka"


"Nayi ma Gimbiya mujeedat alƙawarin zan kawo yaron gidana don ta ganshi....." da sauri senate ya katse shi"mugun abun zaka kai gidanka? Inda iyalanka suke?  Wannan wani irin gangancine"?


Deen yace"yakamata aduba lamarin nan fa, gaskiya ba zamu lamunta ba hauka kake yi da zaka ɗauki mutun mai hatsari ka kai gidanka? What if something happens?" he said in a tense voice.


"In sha Allah Ba abun da zai Faru, Nidai kawai ay min alfarmar dana nema"  ranshi aƙuntatace yayi maganar.


"Hateem Kayi haƙuri, tunda Yaron baida lafiya, ba yadda za'ai ma ya Iya taka ƙafarshi balle har Yaje gidanka, sai dai Idan Yaji sauki kafin lokacin da zaka koma canada" Imam Malik ne Yayi maganar yana dubanshi


Jinjina kanshi ya ɗanyi, ba tare da ya ce komai ba.


Baba obie dake kallon shi ya fahimci babu nutsuwa atare dashi, cikin kwantar da murya yace"Hateem, kada hakan ya dame ka, kasan ina son farin cikin kowan nan ku, ba zanso abun da zai 6ata maka rai ba, dalilin dayasa na raba ka da yaron saboda lalurar dake atare da shi, bana so wani abu ya cutar min dakai...." gyaɗa kai yai"bakomai baba nagode" cikin sanyin murya ya faɗi hakan.


 Murmushi sheikh imam ya saki yana fadin"aminina yakamata kaga yaron nan da Hateem ya ƙwallafa rai akai, dama sauran yaran, zaku sha mamakin kamanninshi da Hateem, daku kanku" ya faɗa yana nuna su Deen, ba yabo ba fallasa suka dube shi batare da sun ce ƙala ba.

Baba obie ya ɗan yi jim na wani lokaci kafin yace"aminina, acigaba da bashi kulawa ta musamman, Idan yaji sauƙi Allah ya raba shi da abun dake damun shi, in sha Allah zamu je mu duba shi, zamu taya shi da addu'a, Allah ya yaye mashi abunda ke damun shi"


 Sheikh imam ya amsa mashi da ameen aranshi yayi mamaki yadda suka nuna basu buƙatar ganin yaran duk da ya fahimci kamar suna gudun  haɗuwa da danish ne saboda lalurar shi.


Duba agogo sharafuddeen yayi"dare yana ƙara yi, Ina so zan wuce"


Baba obie ya dube shi"zaka iya tafiya tun da inada madadinka," ya faɗa yana nuna chief Owais da cup din hannun shi

 Murmushi sharafudeen yasaki tare da kallon Owais a fakai ce ya kashe mashi ido ɗaya, murmushin gefen fuska chief ya saki ganin abunda daddynsa yayi masa, ba tun yau ba ya saba yi mashi hakan sometimes tamkar aboki yake ɗaukar shi.


Gyaran murya Senate lateef yai hankalinsu ya dawo kanshi, fuskarshi babu walwala ya furta.


  "Hateem, kada ka manta, akwai taron da zamuyi a National Assembly, domin gabatar da jawabi da kuma ganawa da kakakin majalissar wakilai" 


 "Ina sane da wannan" atakaice Hateem ya furta hakan.


Sharafuddeen yace"bayan haka zamu ziyarci national Mosque, da kuma National Christian Centre, akwai kuma ganawa ta musamman da zaka yi da sarakunan gargajiya daga sassan kasar mu, after that zaka halarci State Dinner (Liyafar cin abincin dare) tare Ni  A Villa"


  Sheikah Imam yace"babu hutu kenan Hateem zai fara yawo, ko da yake haka ya dace tun da ba kowani lokaci ake samun damar zuwa ƙasar ba, ƙwara ka za gaya gari nima dai hadani za'a je villa wurin liyafar ko ba agayyace ni ba sai na je don nasan za'aci kaji" da zolaya sheikh imam ya fada yana murmushi 


maganar shi ta ba su nishaɗi, gaba ɗayansu suka sanya dariya.


 Sharafudeen yace"aikune kan gaba baba, kai zaka buɗe mana taro da addu'a" sheikh imam yace masha Allah nagode da karramawarnan"

 Baba obie yace"Idan da hali ma, yakamata ku leƙa masarautar yarbawa ku gaishe da dangin mariganya ƙudirat, da kuma masarautar kano suma yakamata aje masu da Hateem, sannan zaka ziyarci National museum dake a lagos, da kuma Yankari Game reserve....  "Tunkan baba obie ya ƙare maganar, Hateem ya furta"baba duk ni zan halarci waɗannan wuraren daka lissafa? Bani da isasshen lokaci, On saturday next week zan koma canada, ina buƙatar hutu" fuskarshi a yamutse yayi maganar.


 Senate yace"dole ne kaje ko kana so ko baka so, mu zamu jagorance ka, Tun da ka shigo ƙasar tamu, dole ka zaga dangi, ka kuma ziyarci wuraren buɗe ido,"


 gyaɗa kanshi yai har cikin ranshi baison yawace yawacen nan badan komai ba sai don saboda Danish baisan yayi nisa da estate din, duk da an yanke alakarshi da yaron zaifi mashi kwanciyar hankali idan har yana akusa da inda yake rayuwa.


  "On friday zamu shirya maka family dinner, na bankwana" acewar Deen.


 Muryarshi asanyaye ya furta "Allah yakaimu lafiya" suka amsa mashi da ameen.

  

  

Sun dauki tsawon lokaci suna tattaunawa a tsakaninsu har wuraren ƙarfe sha ɗaya Na dare, Kafin daga bisani sheikh Imam ya rufe masu taron da addu'a, daga nan su ka yi wa junansu sallama, Har bakin entry Hall, Baba obie yayi masu rakiya, Hateem Ya shiga mota tare da sharafuddeen, Sheikh Imam tare da Boss man suka shiga mota ɗaya, suma sauran kowa Ya nufi Gidan shi dake a estate din, banda chief Owais, baba obie Ya ruƙe shi, yace shi zai taya shi kwana yau tunda shi yakawo abunda ya tsoratar da shi babu musu owais ya amince mashi domin shima yayi kewar kakan nashi.


Tun acikin mota, Sharafuddeen yake tausar Hateem akan yayi haƙuri dangane da hukuncin da baba Obie ya yanke mashi na raba shi da yaron, sannan ya kwantar da hankalin shi, ya yi mashi alƙawarin ko bayan baya ƙasar zasu kula da rayuwar yaron, ba zasu ta6a bari ya wulaƙanta ba, kalamanshi sun tausasa zuciyar Hateem, shi abinda yafi damunshi raba shi da akayi da yaron, yanzu shikenan bazai sake zuwa inda yake ba, har ya koma canada , abun ya ta6a zuciyarshi baiso haka ba, har cikin gidanshi sharafuddeen ya shiga, suka gaisa da gimbiya mujeedat, ita kadaice bata runtsa ba saboda rashin dawowar mijinta, Su Yazrin tuni sun nutsa a baccin su, bayan sharafuddeen yayi masu sallama ya fito daga gidan security detail dinshi suka buɗe mashi mota ya shiga, batare da 6ata lokaci ba, suka nufi Aso Villa domin komawa ga muhallinsa.


Bayan barin su gidan da kusan mintuna talatin, Hajjaty ta lalla6a taje ta ɗauko wayarta data ajiye ƙasan table, jiki na rawa ta nufi dakin don ta kaima pravin, tana shiga ta taras da shi yanata faman yin zarya adaki kamar mai fama da ɗan kanoma da basir, duk ya ƙagara da son jin abunda suke tattaunawa, jin sallamarta yasa shi yin saurin tambayarta ina wayar, da sauri ta miƙa mashi, yasa hannu ya kar6a tare da kunna recording din, ya soma sauraron tattaunarsu, hajjaty dake kallon shi, ganin yadda yake tsuma zufa ta wanke fuskarshi yasa tace mashi lafiya, rai a6ace ya jefar da wayar saman gado yana fadin wannan wace irin masiface? Wato dole dai sai yaran nan sun zauna a estate din nan, wallahi bazai yiwu ba, duk yadda zanyi saina yi silar barin su, nasan owais ne ya tunzura obie har ya amince da zaman su, saboda ya makance akan ƙaunar shi, Idan sunsan wata basu san wata ba....." yana huci yai maganar, hajjaty dake kallon shi, tsantsar mamaki ne akan fuskanta, harta fara kokwanton anya pravin baida wata manufa akan yaran? Meyasa ya tada hankalin shi akansu? Tayi zurfi a tunaninta taji ya buɗe kofar ɗakin Ya fuce waje, Jiki asanyaye ta nufi gefen gadonta ta zauna tare da kwantar da kanta, tayi tsammanin zai dawo dakin amma sai taji shiru, ranta ne ya bata cewar ko ya tafi dakin hajiya saratu ne hakan yasa ta ja bargo ta lullu6e jikinta....




*❤EX-PRISONERS❤*




Bayan Sun kammala Cin dinner dinsu, sam sun kasa runtsawa saboda tunanin ɗan uwan su Danish, ɗazu da marece sun je duba shi, Yanzu ma kuma Bayan sun sanya kayan bacci a jikin su sun yi shirin kwanciya, ɗakin shi suka nufa, gaba ɗayan su ne a kawaye da gadon shi, sun yi tsaitsaye cirko cirko suna kallon shi.


Unaisah da Batool sun sanya kayan bacci kala ɗaya Riga da wando launin black gray, rigar tana da hula duk sun lullu6e kawunansu da ita, Jemimah da Azeeza ma kalar nasu sleep dress din  iri ɗaya ne Yar gown ce dai dai gwiwa ta tsaya masu launin pink colour, sun daure kawunansu da head scarf, Praveen da Hanna launin nasu farare ne riga da wando masu zanen flowers ajikinsu.


Hala zalika Mazan ma kowan nan su yana sanye da kayan baccin sa.


Tun suna daga tsaye har dai suka kaiga samun wuri gefe da gefen gadonshi suka zazzauna, banda Gabriel dake atsaye ya goya Azeeza a bayan shi saboda makantar daren ta, duk da lalurar ta fara sauki yanzu, tana gani ba laifi saboda hasken dake gauraye da gidan tamkar da rana, yana ƙara ƙarfafa mata ganinta sai dai babu clear amma takan iya shaida fuskokin su, shiyasa bata damuwa yanzu bama kowa yasan tana da lalurar ba sai ƴan uwanta.....


Fuskokinsu babu walwala, yayin da suke kallon shi, musamman Haris hawaye tuni sun jiƙe fuskarshi.


"Allah ya baka lafiya ɗan uwana rabin raina, Danish na tausaya maka, Ina jin raɗaɗin da ka ke ji acikin zuciyarka, In sha Allah ƙarshen wahalarka ne Yazo"


 murya arauna ce Haris Ya furta maganar, idanunsa akan fuskar Danish dake akwance tsakiyar gadon kamar matacce.


"Danish, ban sani ba ko kana ji na, dan Allah ka kwantar da hankalinka, kada ka ta6a sanya damuwa akan abunda ke faruwa dakai, ko jiya da muka guje ka don ba mu san kai bane, amma Yanzu mun riga da mun sani, kuma in sha Allah, a kowani hali na rayuwa duk runtsi duk wuya muna a tare dakai, har ƙarshen rayuwar mu" Batool na ƙarasa faɗar maganar ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, da sauri ta kifa kanta saman mattress din daga gefen hannun shi, ta ɗaura nata hannun akan nashi.


 "Batool ki daina yin kuka, zaki ƙara karya mashi zuciyarshi, saboda Ina ji araina yana sauraron mu ba bacci yake yi ba" cikin kwantar da murya Unaisah ta furta maganar, idanuwanta akan Batool cikin shesshekar kuka tace"ya wahala sosai, ko motsi bai iyayi, mu kallon shi kawai mu ke yi, shi ka ɗai yasan raɗaɗin da yake ji acikin zuciyar shi, sai yaushe ne zaiji dadin rayuwarshi"? Cikin jin ƙunar rai ta furta maganar tare da dago da kanta idanuwanta sun kaɗa jawur..


Fashewa da kuka Azeeza da jemimah su ka yi, sautin su ya karaɗe ɗakin, Naufal Yace"Dallah meye haka? Kuka shi zai mana maganin damuwar ɗan uwan mu ne? Ku bar mu muji da abunda ke damunmu mana" zuciyarshi a jagule yayi maganar,


Muryar Jemimah da shessheƙar kuka tace"Ni wallahi tausayinshi nake ji, bawan Allah, lokacin da muna a daji bamu lafiya shi ya rinƙa ɗawainiya damu har muka ji sauƙi....." kafin ta ƙare maganar, parveen cikin raunin murya ta katse ta da cewa"Idan muna jin yunwa shi yake sama mana abinci, sannan Ya hana idonshi bacci duk don saboda mu, amma meyasa mu muka kasa taimaka mashi awannan halin"? Muryarta na rawa ta jefa masu tambayar.


  "Saboda bamu da yadda zamuyi Parveeen, addu'a ce kadai zamu Iya taimaka mashi da ita," acewar Javed shima fuskarshi ayamutse take.


  "Ba iya addu'a ba javed, Idan muka tona asirin miyagun mutanan can da suka ƙasƙantar da rayuwarmu, Ina da tabbacin zamu Yi nasarar kawo ƙarshen matsalar Danish damu kan mu, don kuwa nasan har Yanzu suna nan suna bibiyar rayuwarmu bazasu ta6a ƙyalemu ba kodan saboda kada mu tona masu asiri dole subi diddiginmu" sajeed ne Yai maganar..


Unaisah ta natsu tana kallonsu, ba tare data tsoma baki ba, saboda ita a halin yanzu ta fahimci wani abu, tun da har jami'an isod suka gano salsabeel to kuwa tana da tabbacin sun san komai game da rayuwarsu!! Kallonsu kawai su ke yi.


   "Ƙwara kowa yasan me suke aikatawa, mu faɗa masu kawai, su taimaka su rabamu da su, Su ƙyale ɗan uwanmu yayi rayuwarshi cikin salama" Hanna ce ta faɗa tana faman tada jijiyoyin wuyanta.


  Calmly Unaisah ta furta"ku daina surutu kuna hana shi natsuwa, yakamata mu je mu kwanta, tun da mun ganshi inyaso gobe da safe sai mu dawo mu ƙara duba shi"


       Shiru su ka yi, ba tare da sun motsa ba saboda basu sun yin nesa da shi, da da halima a ɗakin shi za su kwana, yayin da su ke cigaba da kallon shi tamkar zasu haɗiye shi, tsananin tausayin shi suke ji ga wata irin ƙaunarsa da su ke ji.

   

Parveen da Jamimah sai hamma su ke yi, ita jamimah hada gyangyaɗin bacci.


   "Please ku tashi mu tafi ɗakunan mu" Nawfal ne yai maganar, tare da miƙewa ya zagaya ta 6angaren da garkuwa yake akwance ya duƙar da kanshi ya manna mashi sumbata akan forahead dinsa, ganin hakan yasa Jemimah yin sauri rarrafawa tsabar iyayi saman chest dinshi ta haye tukunna ta manna mashi sumbata kan cheek dinsa har sau biyu, murmushi kowan nan su yasaki abun ya ƙayatar da su.


    Ƙarasa hawayewa gadon Batool tayi har zuwa gefen Garkuwa in a cool voice ta furta"ɗan uwana rabin raina, idan kana saurare ni, nayi kewarka sosai, Allah ya baka Lafiya sanyin idaniyata" gefen fuskarshi ta manna ma kiss, kafin ta sauka daga kan gadon, da sauri Haris ya zagaya ta inda su nawfal suke a tsaye daga gaban gadon ya russina tare da ruƙo hannun Danish ya buɗe tafin hannunsa A hankali ya sumbace shi kafin Ya furta"ko ban faɗa maka ba, nasan kasan da irin ƙaunar da nake yi maka jinin jikina, Allah ya tashi kafaɗunka" bayan Haris Ya saki hannun shi, Javed Ya miƙe ya nufi Side da danish yake, Ya manna mashi kiss a forehead nashi.


   "Big bro, our guardian, Allah ya baka lafiya" ya faɗa cikin nuna tausayawarshi.


   Sajeed dake agoye da Azeeza, Ya matsa kusa da Danish,Ya sauketa daga gefen gadon, da rarrafe ta lalubo Danish ta ɗaura fingers dinta saman fuskarshi ta shasshafa shi, duk suna ta kallonta.


 Haris da zolaya yace"kada ki lashe mana ɗan uwa, Kiss ɗaya zaki manna mashi ya wadatar" kusan sau uku ta sumbace shi, biyu kan cheek dinsa, ɗaya kan tsinin hancin shi, bayan ta gama nata, Sajeed ya ruƙo Hannun shi kamar yadda Haris yayi, a hankali Ya sumbace shi gently ya furta"ka kula mana da kanka our super star, zamu kwana da tunaninka, gobe da sassafe zamu zo duba lafiyarka, garkuwar mu"


Murmushi duk suka saki, wani irin daɗi suke ji, mayar da goyan Azeeza Sajeed yayi akan bayan shi.


  Hanna ma ta sumbace shi, Ya rage saura Unaisah, dake zaune tayi zugudun kamar mai tunanin wani abu.

  

  "Genie saura ke" acewar jemimah idanuwanta sunyi luhu luhu saboda baccin da take ji.


   "Unaisah we are waiting for u, ki yi mashi kiss kamar yadda muka Yi mashi kafin mu tafi" Sajeed ne yai maganar, tamkar bata ji me suke cewa ba, tayi kasaƙe tana faman wurwurga eye balls dinta.


  Dafa shoulder dinta Batool tayi"Sister, Kin yi shiru, ki motsa mana, Ko kin manta abun da muka ce zamuyi idan mun fita daga ɗakin Danish"


 Haris Yace"menene za ku yi" da sauri tace"karatu ne zamu yi kafin mu kwanta bacci" Ya furta okey,


  Jiki asanyaye Unaisah ta ƙarasa haurawa kan gadon, crowling slowly ta nufi Danish, koda ta ƙarasa inda yake a kwance, saita sanya hannu ta zame hular kanta, nan take nannaɗaɗɗiyar sumar kanta ta warwaro ta sauko kan kafaɗunta, rumfa tayi mashi da gashinta ta yadda ba zasu Iya ganin sumbatar da za ta yi mashi ba.


Sajeed Ya buga ƙafa yace"ba mu yarda ba wlh, You are trying to be smart Unaisah, dole ki janye sumar kanki mu gani da kyau" Ya faɗa yana sakin murmushi.


Haris yace"kiyi yadda kowa yayi" Batool  da su javed sai murmushi suke saki, shiru tayi bata tanka masu ba.


    Babu Mai Iya ganinta acikinsu, ɗaura tsinin hancinta tayi akan nashi, numfashinsu ya soma kokawa dana juna, hatta bugun zuciyarshi saida ya canza, dogon wuyan shi ta fara manna ma sumbata har zuwa kan chin dinsa ta sumbace shi a hankali kafin slowly ta ɗago da kanta, ta sumbaci forehead dinsa, ta dawo kan eye lids dinsa ɗaya bayan ɗaya ta sumbace su, tana ƙoƙarin kai mashi sumbata kan soft lips dinsa ba zato ba tsammani taji an damƙo sumar kanta, da ƙarfi ya ɗago da ita, A firgice ta juyo don ganin wanene Ya katse ta......


  Rass taji gabanta Ya faɗi ganin Big Guy, wata irin kunya ce ta rufeta, da sauri ta sanya tafukan hannayenta ta rufe face dinta, su Haris dake atsaitsaye sai tiƙar dariya suke yi, ashe tunda ta dukufa tana sumbatar danish suka jiyo motsin buɗe ƙofa, suna kallon shi yai masu alamar suyi shiru da bakinsu, nan fa kowan nan su Yaja baki yai shiru, Lamarin ya ɗaure mashi kai, don bai fahimci me ta ke yi ma danish din ba, yadai ga tayi mashi rumfa da sumar kanta, Cikin sanɗa yaje gaban gadon Ya daddage Ya damƙo gashinta kanta.


 "Ki ji tsoron Allah Jari, Faɗa min kike Aikata ma bawan Allahn nan" fuskar shi ɗauke da murmushi yayi maganar yana bin ta da kallon tuhuma, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"wallahi Ni ba ƴar iska bace, ba abun da kake tunani bane, Ka tambaye su ka ji" ta faɗa tare da ɗago da kanta a lokacin ya sakar mata gashin kanta, duk tabi ta ruɗe, gani ta ke yi kamar kallon ƴar iska yake yi mata, tun akan abun da Ya faru ɗazu da suka kama ta a ɗakin Danish ta cire mashi ma6allin gaban rigarshi, shiyasa take fargaban kada ace kallon yar iska yake yi mata.


  Sunnar da kanta ƙasa tayi, fuskarta a tur6une babu annuri, sai faman ƙyafkyafta idanunta take Yi


"Ƴan uwan Jari, ku fada min me take aikatawa tunda ita bazata fadamin gaskiya ba" Ya fada Yana nuna su Sajeed Da hannun shi

 Har suna hada baki wurin maimaita sunan JARI,

  da shagwa6a66iyar Murya Jemimah tace"Unaisa ɗin mu ce Jari"


 Big guy yace"Yeah, Ita nake nufi, ko bakusan cewa ita ɗin Jari bace"? Da mamaki suka girgiza mashi kai gami da tambayarshi ma'anar jari.


  "Shi Jari wani abu ne da idan ka sanya shi zaka samu riba, yar uwarku jari ce gare mu baki ɗaya, tun da muna ƙaruwa da ita, kamar dai yanzu da take koya mana wani baƙon abu...." tunkan ya ƙare maganar Unaisah tai saurin furta"wlh bani na faraba ai, Naufal ne Ya fara Yi mashi kiss, kowa yayi nice ma ta ƙarshe, Kuma ni bama kiss nake mashi ba, Falaƙi da nasi nake karanta mashi..." a shagwa6e ta ƙare maganar.


    Dariya suka saki gaba ɗayansu, bayan sun lafa, Big guy yace Ku tashi muje in rakaku ɗakunan ku, Dare Yayi sosai, Yakamata kuna bacci da wuri saboda karatun asubahi da ake koya maku" amsa mashi su ka yi da toh, yakai hannu ya ɗauki Jemimah, kafin su bar ɗakin saida Kowan nan su yayi mashi addu'a suka tottofe mashi jikinshi, har sun fita Unaisah ta dawo ɗakin da gudu ta lullu6e garkuwa da lallausar bargonsa, kafin ta kashe switch din dakin yai duhu, ta kunna mashi bedside lamp, tamkar karta bar ɗakin haka take ji, addu'o'i ta tottofa mashi tun daga ƙasa har sama kafin tabi bayan su suka nufi bedrooms din su.


 Sai da big guy ya tabbatar kowan nan su Ya shiga dakin shi, tukunna Ya nufi hanyar da zata kaishi part din da room dinsa Yake agidan.


Fitarshi keda Wuya, Unaisah da Batool, suka fito daga ɗakin su, Hannayen su ruƙe da plates sun rufe su, abincin da suka ajiyema Ummi ne, tun ɗazu suka shirya zuwa dakinta don su kai mata abinci sun kasa saboda fargabar awani hali zasu taras da ita, duba da yanayin da ta shiga ɗazu na ganin sheikh Imam, Batool ce ta bada shawarar su ɗebi abinci su kai mata, tun lokacin da aka kawo masu dinner dinsu, Suka ɗibar mata plate biyu na abinci, A ɗakinsu suke 6oye mata shi sai yanzu su ka samu damar fito da shi.


Cikin sanɗa suke yin tafiya suna ƴan waige waige kamar wasu munafukai, fargaban su kada wani ya gan su, basu san cewa duk wani motsin su akan idon jami'an isod dake kula da CCTV room ɗin gidan.


   A hankali suka haura second floor kaitsaye suka nufi ƙofar dakin ummi, cike da fargaba Batool take zazzare ido, don har yanzu mugun jin tsoron ummi take yi, gashi ta damu da ita kamar yunwar cikinta.


     "Sister, Ni zan jira ki awaje, ke sai ki fara shiga" cikin muryar raɗa batool tayi ma unaisa maganar.


 Harara unaisah ta jefa mata" waye ya kawo shawarar mu kawo mata abincin"? Yamutsa fuska batool tayi"Ni ce,"


 "Don haka ke zaki fara shiga, Ni dama hankalina bai kwanta da mu zo kawo mata abinci ba, wata'ƙil ma taci abincinta tun ɗazu, mu ne ba mu sani ba"


 "Shikenan, Mu koma ɗaki sai mu cinye"


Dariya Unaisah tasaki tana kallon batool tace"ai wallahi yadda kikasa muka ajiye mata abincin nan sai mun kai mata shi, Kuma ke zaki miƙa mata da hannunki" ta faɗa tana nuna ta da girar ta, jikin Batul harya fara kerma tsabar tsoro, idanunta suka ciko da ƙwalla.


  "Nidai mu koma ɗaki, sai in cinye abincin" a tsorace ta faɗa.


  da zolaya Unaisah Tace"You are just a coward, ai na lura shakkar aunty ummi kike ji, gashi duk kin damu da ita, Yinin yau tun bayan data shige daki kika ga bata fito ba shikenan kika addabe ni da tambayar Aunty ummi, bata ci abinci ba, tana adaki, ko awani hali take aciki, ni narasa gane meyasata kuka, yen yen yen haka kika isheni, shine yanzu kuma mun kawo abincin kike kokarin zillewa" murguɗa mata baki batool tayi batare da tace mata ƙala ba.


  Knocking ƙofar Unaisah tayi daga ciki suka jiyo Muryar Ummi ta furta"Come In"


   Tura ƙofar Unaisah tayi kafin ta shiga da sallama abakinta, Batool tana abiye da ita sai fama 6oye kanta take Yi.


Kusan atare suka ɗaura idanunsu akan shimfiɗeɗan gadonta, tana daga kwance ta ɗaura kanta saman pillow, yayin da eyes dinta ke akan apple laptop dinta da ta ajiye saitin inda take fuskanta, wata yar gown ce a jikinta, shara shara kana Iya hangen inners dinta, tsayin rigar bai wuci gwiwar ƙafarta ba, gashin kanta a yamutse yake mai uban yawan gaske, ya cunkushe wuri guda, yanayinta da kasala a jikinta babu kuzari.


     Kamar an danna masu full stop haka suka dakata da yin tafiyar suna faman binta da kallo, jin shiru sunyi mata sallama basu shigo bane yasa taɗan ɗago da idanunta waɗanda suka rikiɗa suka koma launin Ja, Su kansu da su ka yi tozali da idanunta saida suka sha jinin jikinsu, wani ɗan iskan murmushi tasakar masu haɗi da ɗage masu gira ɗaya tace"meyasa ku ke kallona? Ba zaku shigo ciki bane"? Kallon juna su ka yi cike da al'ajabin jin sautin muryarta tamkar ta gardin ƙato wanda yasha ya bugu da giya.


  "Aunty Ummi baki da lafiya ne"? Unaisah ce ta furta maganar, a kasalance ta miƙe zaune haɗi da jingina bayanta kan gadon, kafin ta furta"Lafiyana Lau, menene ku ka kawo min"


  ta tambaya yayin da take kallon Batool data 6oye kanta bayan Unaisah.


 "Abinci ne" buɗe ido ta yi alamar tadan yi mamaki .


 "Wanene Yayi tunanin kawo min abinci acikin ku"? Ta faɗa tana nuna su da yatsanta.


  Cikin muryar raɗa Batool tace"Dan Allah ki ce mata ke ce bani ba"


Murmushin mugunta Unaisah tayi jin abun da ta raɗa mata,


Da gangan tace "Batool ce, tun ɗazu da kika tafi ɗaki kina kuka ta hana kanta sukuni, ta dinga damuna da tambaya akan Aunty ummi shiru bata fito taci abincin ta ba, ta tafi tana kuka bansan awani hali take ba, Pls sister mu ajiye mata abinci mu kai mata"


Lumshe idanu ummi tayi, har cikin ranta taji dadin jin hakan.


 "Ku shigo daga ciki," ta faɗa tana nuna masu gadonta da hannu, Unaisah ce tayi gaba Batool tana abiye da bayanta kamar wata mara gaskiya, taji haushin faɗa matan da unaisah tayi 

   

 "Bani plates din" ta fada tare da mike masu hannu ta kar6i plate din hannun Unaisah, ta ajiye akan gadon, ta kar6i na hannun batul ta ɗaura shi kan side drawer tana fadin"tun da kun kawo min abincin, ku zaku bani a baki in ci" 


duk idan tayi maganar sai sun kalli fuskarta, bakomai ne yake ɗaure masu kai ba, face sautin muryata daya canza kamar na wadda tasha giya, ga idanuwanta sun yi ja.


 "Aunty Ummi sautin voice dinki Ya canza, Idanunki ma suna yi ja sosai, ba ki jin daɗin jikin ki ne"? Cikin kulawa Unaisah tayi mata tambayar, ƙamshin turaren ummi duk Ya buɗe ɗakin.

 

 "Nothing is bothering me. Maybe it was my crying that made my voice change." She said, trying to bring her voice back to normal.


 "Meyasa ki kuka ɗazu da kika ga sheikh Imam"? unaisah ce ta ƙara jefa mata tambayar 


 da zolaya tace"Unaisah kin cika bin ƙwaƙƙwafi, Kina min tambaya kamar Ƴar jarida, Ku zo ku zauna Yau muyi fira" ta faɗa tana nuna masu mattress.


 Unaisah ce ta fara hawa gadon, Kafin Batool ta haye gadon tana mai jin shakkar haɗa ido da ummi, suna fuskantar juna da ita, Batool tana agefen Unaisah, Ummi tana fuskantarsu.


 ta lura kamar Aunty Ummi batason tambayar da take Yi mata dangane da sheikh Imam hakan yasa taja baki shiru.


da fara'a akan fuskarta tace"Banyi tsammanin kun damu dani ba, har na fidda rai da zanci abinci, gashi wata iri yunwa nake ji kamar inci ƴan hanjin cikina...." ta ƙare maganar tana ya mutsa fuska ta buɗe plate din gabanta, ashaƙe yake da tsiran nama, yanka yanka yaji kayan haɗi sai maiƙo yake yi ga kayan lambun da aka yayyanka mashi, sai ƙamshi yake yi, sun kura mata ido suna kallon ta.


"naji daɗin tsiran nan da ku ka kawo min, wa zai fara bani abaki" da sauri Unaisah tace"Batool" ta faɗa tare da ruƙo hannun batool ta ɗaura shi kan plate din, Hankalin batool ba ƙaramin tashi yai ba, fuskarta duk ta yamutse itafa atakura take jin kanta har yanzu bata manta abunda ya faru tsakaninta da ummi ba a daren Jiya, gani takeyi kamar bata ƙaunarta.


  "Babe, Ki bani tsiren miyau na Ya gwada" ta faɗa tana ɗage mata gira, hada sakar mata murmushin gefen fuska

  Daurewa batool tayi, ta ɗauki tsiran hannunta na kerma takai shi bakin ummi, Unaisah na dariya tace"wlh batool tsoron ki take ji aunty ummi," ruƙo hannun batul ummi tayi ta ƙarasa tura naman abakinta, har wani lumshe ido takeyi, tana taunarshi ta ce.


 "Na lura da hakan, Amma kada ki damu zamu saba ne" Ummi ce tayi maganar, sanya hannu unaisah tayi cikin plate din tsiren ta dauko ta tura ma ummi abaki, Idan batul ta bata ita ma sai ta bata abaki, wani irin ƙaunarsu ce ta ɗarsu acikin zuciyarta, A hankali take satar kallonsu afakaice, don bata son su gane tana kallonsu.


  Bayan sun kammala bata tsiren suka buɗe dayan plate din me ɗauke da chips, shima suka bata har tana tambayarsu sunci nasu abincin ne? Suka ce mata Eh sun ci, duk da haka saida ta ɗebi chips ta tura ma kowan nan su abaki, Cike da nishadi suke tauna.

  bayan sun gama, Unaisah ta ɗauko masu Juice me sanyi suka sha.


     Ganin sun fara yunkurin tafiya ne Yasa tace"why baza ku tayani kwana ba"? Waro ido batul tayi tunawa da abinda Ya faru Jiya, Murmushi Ummi ta sakar mata, Ta fahimci tsoro take ji kada ta ƙara Yi mata irin na jiya hakan yasa tace


 "Asaman gadona zamu kwana, kafin muyi bacci har kallo zan kunna mana a laptop," jin hakan yasa batul taji hankalinta ya kwanta.


  gaba ɗayan su suka haye gadonta, unaisah ta takura ma Ummi akan tana son ta gyara mata gashinta, adole ummi ta ɗauko mata comb, da ita da batool suka kama gashin kanta suka dinga sharce shi bayan sun kammala, ta basu ribbom babba suka ɗaure mata gashin daƙyar saboda yawanshi gashi taurine dashi donma tana gyarashi da mayuka masu sanya laushin gashi.


   Gefe da gefenta suka kwanta, ta kunna masu kallo a laptop, cikin nishadi su ke yi, da zarar anzo wurin da za'ae kiss ko makancin hakan take yin saurin rufe masu idanuwansu da tafukan hannayenta, hakan ba ƙaramin dariya yake basu ba, Saida dare Ya fara nutsawa ta kashe kallon, a lokacin bacci mai nauyi yai awon gaba da su, ta sauko daga kan gadon ta kunna masu bedside lamp kafin taje ta kashe hasken ɗakin ya rage saura na fitilun gefen gadon, ta dawo ta kwanta a tsakiyarsu.


   A jiyar zuciya ta sauke, tare da ɗaura eye balls dinta tana kallon fuskar batool dake ta sharar baccinta, A hankali ta daura hannunta kan hular batul ta zameta, gashin kanta ya bayyana, shafashi taci gaba dayi tana binta da kallon ƙurulla, gani take kamar ta ta6a sanin mai kama da ita, sai dai ta gaza tuna wanene ko wacece ke kamanceceniya da ita cikin mutanan da tayi tarayya da su.


     Lumshe idanuwanta tayi yayin da ƙwalwarta ke tariyo mata wani abu can daya ta6a faruwa a arayuwarta wanda yayi silar tarwatsewar Farin Cikinta, baƙin tarihin da har bada bazata ta6a mantawa da shi ba, Ya lalata darajarta da ƙimarta Ya zubar mata da mutuncinta a idon jama'a, wasu kalmomi ne suka soma yi mata yawo acikin kanta.


_Nayi danasanin kasancewarki Ƴata, wallahi da ace nasan da zuwan wannan ranar da tun kina acikin ciki zanyi silar da za'a 6arar dake_


Tuna wannan maganar yasa ta fashe da wani irin matsanancin kuka tamkar ana zare ranta, sham ta manta da su Unaisah dake bacci.


    Cikin muryar bacci batul ta furta"aunty ummi kuka ki ke yi"? Da sauri ta haɗiye kukanta, Hannunta ɗaya atoshe da bakinta, ta runtse idanuwanta.


  Idanun batul biji biji ta buɗesu, akan fuskar ummi, hankalinta ya tashi matuƙa ganin yadda fuskarta ta jiƙe da hawaye, muryarta na rawa ta furta"aunty.... ummi, baki da lafiya? Meke damunki"?


Daƙyar ta iya buɗe ido ta kalli batool dake kallonta batare da tace mata komai ba.


  Duk da shakkarta da Batool take ji hakan bai hanata jin tausayinta ba, hankalin ta ya tashi matuƙa da ganin yanayin da ummi take aciki.


 Hannunta na kerma ta ɗaura shi saman fuskar ummi a hankali take share mata hawayen dake sintiri kan kuncinta.


 "Aunty ummi ki daina kuka dan Allah, bana son ganin ki cikin damuwa"


Muryarta adisashe ta furta"meyasa kika damu dani? Ko Kin manta abunda nayi maki jiya"?


"A'a ban manta ba, ni kawai ina ƙaunarki kuma bana son ganin kina kuka"


tayi mamakin abunda batul tace mata.


"Don't worry, I'm feeling better. Go back to sleep." ta faɗa tana ƙoƙarin danne damuwarta.


 "Bazan Iya bacci ba, idan bakiyi ba," kalaman batul sun sanyaya mata zuciya.


"Ki sanyani inyi baccin" matsawa batul tayi dab da ita.


Da ƙarfin hali ta rungume ummi sosai tayi tighting dinta, ta daura hannayenta saman bayanta, itama ummi ta daura nata hannun asaman bayan batool ta ƙanƙameta, wani irin yanayi ta soma ji mai wuyar fassaruwa hatta bugun zuciyarta ya canza, ta rasa gane dalilin faruwar hakan, Yau ne karo na farko data fara rungume Batool ajikinta amma wani iko na Allah sai ta dinga jin kamar ta ta6a rungumarta, ita kanta Batool din sai da taji canzawar bugun zuciyarta daurewa kawai take yi amma sai take ji kamar su dawwama ahaka ita da ummi batare da sun raba jikin su daga na juna ba.


   Ƴan addu'o'in da Unaisah ta koya masu, ta soma karantowa tana tottofa ma ummi.


Wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, lokaci ɗaya ta nemi damuwarta tarasa,  Ahaka bacci mai nauyi yayi awon gaba da su rungume da juna kamar zasu koma mutun ɗaya..... 

(Nima kuma na rungumi Alƙalamina)

Mu haɗu Gobe Idan Allah yakaimu da rai da Lafiya🌹

Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura

3196407426

First bank 

Bature Hafsat Muhammad,

 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post