Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 2 complete


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 2 complete

 _~*BOSS LADIES WRITERS*~_



KE GABATAR MA KU👇



        _🔥💫THE PRISONERS🔥💫_

            ~TAKUN🔥🔥🔥ƘARSHE~ 

Daga Alƙalamin Boss Bature

                  Dedicated To Aunty Kubra😍

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty❤._

_______________________✍️


Bayan ƴan mintuna Pravin ya fito daga toilet fuskarshi a jiƙe da ruwa kamar wanda ya ɗauro alwala, maimakon taga 6acin rai akan fuskarshi sai taga akasin hakan, wani irin shu'umin murmushi yake sakar mata, hakan ba ƙaramin 6ata mata rai ba, ɗaure mashi fuska tayi haɗi da kau da idonta daga kan shi, taci gaba da cin abincinta.



  Gefen ta ya zauna"idan akwai wani punishment din daya fi wanda kika bani a yanzu, A shirye nake dana kar6e shi, Ni dai buri na ki yafe min mu shirya tsakanin mu, My Sarah bazan juri fushin ki ba" daɗin baki Pravin yaci gaba dayi mata, tun da ya fara magana Hajiya Saratu bata dube shi ba.


 Abincin ta take ci, hannu takai zata ɗauki apple ciki Jerin kayan marmarin dake shaƙe a plate da sauri Pravin ya ruƙe hannunta yana faɗin"Bai kamata kina share ni ba, tun ɗazu nake yi maki magana kinyi banza kin ƙyaleni inata zuba kamar aku," a marairaice ya ƙare maganar, ranta ya 6aci ta tsani tana cin abinci a takura mata, a harzuƙe ta fuskance shi da niyar ta 6al6aleshi da masifa sai dai kafin tayi hakan yai saurin shammatarta ya haɗe bakinshi da nata, kafin tayi yunƙurin janye bakinta yayi saurin zagaye hannayenshi ya ruƙe qugunta ruƙo bana wasa ba, still bata daina kiciniyar raba kanta dashi ba sai dai yaci ƙarfinta, lokaci ɗaya ta soma jinta a yanayin da bata shirya kar6arshi ba, kissing ɗinta ya fara yi cikin ƙwarewa yake sarrafa ta, har yayi nasarar zuge zip din rigarta slowly ya zame wuyan rigar har zuwa kan flat stomach dinta, abunda ya jima bai samu damar yi da ita ba, numfashinshi har wani hauhawa ya ke yi kamar mayunwacin zakin da yaga nama, zame tonge dinsa yai daga cikin bakinta ya shiga manna mana mayataccen kiss tun daga kan wuyanta har izuwa saman big boobs dinta da suke acike fam, ƙoƙarin 6alle hannun bra din yayi asusuce yakai hannu zai yi grabbing dinsu kamar daga saman Yaji ta bangaje shi da ƙarfin gaske har sai da Ya faɗa kan mattress din, da sauri ta maida bra din ta gyara wuyan rigarta daya kwale mata, idanuwanta sun kaɗa jawur sun ƙanƙance fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin sai faman huci take yi alamun 6acin rai.


  Lumshe idanuwansa yayi tsabar takaici da ƙululun baƙin cikin da yaji na katse mashi enjoyment dinsa da ta yi ne yasa shi fitar da ruwan hawaye suka soma gangarowa saman kuncinsa, muryarshi ƙasa ƙasa ya furta


"Meyasa za ki yi min haka? Kin hana ni jin daɗin rayuwata sai kace ba mijin ki ba, gaba ɗaya kin juya min baya ta 6angaren bani hakkina, Saratu ba ki yi min adalci sai naci wahala kafin nake samu ki bani haɗin kai, ada ba haka ki ke yi min ba kin canza, Idan laifi nayi maki ki faɗamin mana" zuciyarshi na tafarfasa ya ƙare maganar.


        Gaba ɗaya abincin Ya fita aranta, yunƙurin amai ta soma yi da gudu ta nufi toilet ta shiga, ranshi ya 6aci gani yake kamar don saboda kiss din da yayi matane yasa take yin amai saboda tana ƙyamar shi.


  Daƙyar Ya iya miƙewa zaune ya jingina bayanshi da headboard idanuwanshi sun kaɗa jawur, Ya rasa gane dalilin da yasa ya gaza haƙura da ita duk irin wulaƙancin da take yi mashi, ga dukkan alamu ya manta da abun da ya kawo shi ɗakin.


 Kusan mintuna biyar kafin Hajiya Saratu ta fito daga toilet, hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta, Cak ta tsaya da tafiya ta ɗaura idonta akanshi, kamar yadda take kallonshi haka shima ya ke kallonta, ba ta yi mamakin ganin hawayen dake akan fuskarshi ba, aranta ta furta"jarababbe kawai" a fili kuma tace"dama ka shigo ɗakin ne donka takura min da jarabarka ne"? Meyasa ita wadda ta taya ka kwana adaren jiya bata biya maka buƙatarka ba? Kai ne fa da kanka ka faɗamin cewa tafi ni Iya tarairayar miji ko ba haka ba"? Ta faɗa tana jifar da shi da harara.



 Dafe kanshi yayi da hannu ɗaya, sai yanzu ya gane dalilin dayasa tayi mashi wulaƙancin nan, Kishi ne ke damunta, duk da yasan bata gasgata abun da ya faɗa mata ba.


  Cikin sanyin murya yace"kin 6ata min rai jiya shiyasa na faɗa maki hakan saboda kiji abunda naji, amma ba dagaske nake ba, duk da baki ƙaunata ni bazan iya haɗaki da wata ƴa mace ba, saboda ke kaɗaice acikin zuciyata har abada, shiyasa nake haƙuri dake duk wulakancin da zakiyi min bazan iya cin amanarki ba......." Yana magana hawaye na cigaba da wanke fuskarshi.



  Duk irin zafin da ta ɗauka sai taji jikinta yayi sanyi, lokaci ɗaya tafara sassauta fushin fuskarta, koda Pravin Ya fahimci raunin da zuciyarta tayi sai yai amfani da wannan damar ya ƙara sanyaya muryar shi haɗi da marairai ce mata fuska Yaci daga da cewa"bansan meyasa ki ke son 6ata min rai ba, burinki ki ƙuntata min, bayan ba haka mu ka yi wa juna alƙawari ba, kada ki manta Saratu, ƙaunar da nake yi maki itace tasa nabar dangina saboda kin nuna baki ra'ayin zama a india ahaka na amince na biyoki Nigeria, kuma na zauna a family house dinku saboda kin buƙaci kinfi son zama tare da ƴan uwanki, babu irin gorin da ba'ayi min ba akan ina zama gidan surukaina amma saboda son da nake yi maki yasa na jure duk wani wulaƙancin da nake fuskanta, naci gaba da zamana, har muka tara zuri'a, ban ta6a buɗe baki na faɗa ma wani cewa bada son raina nake zaune gidan surukaina, ke ce ki ka nuna kina so ni kuma saboda ƙaunar da nake yi maki yasa nake yi maki biyayya" dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yana binta da kallo, tsantsar nadama yake gani akan fuskarta.



  "Idan naga dama zan Iya sakin ki, In kama gabana saboda ni ban dogara dake ba, da Allah na dogara ki daina tunanin dukiyarki take sanyawa ina atare dake ba haka bane ko ɗaya, Ni ƙaunarki nake yi don Allah ba don wani ba in ba haka ba ai da tuni na koma ƙasarmu".


 Ƙafafuwanta ne suka Gaza ɗaukarta, a daddafe ta nufi mirror chair ta zauna akai tana fuskantar shi.


  "Saratu ki faɗamin kin daina sona ne"? Yanayin yadda yayi mata maganar, ba ƙaramin karya mata zuciya yayi ba.


 Runtse idanunta ta yi, ita kanta ta rasa gane meyasa take yi mashi haka? kuma a yadda ta ke jin shi babu abun da ya canza na daga ƙaunar da take mashi.



  Jin motsin shi yasa tayi saurin buɗe idanuwanta, saukowa yayi daga kan gadon ya nufi ƙofar fita daga ɗakin Yana share hawayen shi da hanky.


    Har ya ruƙo handle din ƙofar Aranshi yana Allah Allah ta dakatar dashi yaji ta ambaci sunanshi"Pravin" shu'umin murmushine ya bayyana akan fuskarshi, a hankali take tafiya tana tunkararshi, da sauri ya 6oye murmushin fuskarshi Ya juyo yana dubanta tamkar mai fama da ciwon ido, unexpected tayi hugging dinshi ta zagayo da hannayenta saman bayanshi, muryarta ƙasa ƙasa ta furta"I'm really sorry, my hubby. I've realized my mistake, and I won't hurt you any more"


 Kwantar da kanshi yai kan kafaɗarta Ya zagayo da hands dinsa ya ruƙo waist dinta, yaushe rabon da yaji ɗumin jikinta haka harya manta sosai yayi tighting ɗinta, Yana shaƙar ƙamshin turaren jikinta, bai ta6a tsammanin zaiyi nasara akanta ba, sai gashi cikin sauƙi ya yaudareta da kalamansa.


   "Ki yi min alƙawarin ba zaki ƙara 6ata min rai ba? sannan zaki dinga bani haƙƙina akai akai, duk time dana buƙace ki" ya faɗa batare daya raba jikinshi daga nata ba.


  "Bazan iya yi maka alƙawari ba, kasan ɗan adam ajizine, dole wata rana mu samu sa6ani bawai fatan hakan nake yi mana ba, but in sha Allah zanyi ƙoƙarin ganin na kawar da duk wani abu da zai 6ata maka rai"


 Ƙara ƙanƙameta yayi, hada manna mata kiss kan kafaɗarta.


   Tsawon mintuna kafin ya raba jikin shi daga nata, Ya ruƙo hannunta acikin nashi, fuskokinsu ɗauke da murmushi.


      "Ina fata kanka bai yi maka ciwo, naga idanunka sun kaɗa jawur"

 "Kada ki damu, dama kece damuwata kuma Alhamdulillah yanzu komai ya wuce tun da kika kar6i laifin ki, fatana shine Allah Ya dawwamar da zaman lafiya a tsakanin mu"


"Ameen my husband" daɗi yake wai yau shi hajiya saratu take kira da hubby da kuma sunan mijinta, Ya manta when last yaji hakan daga gare ta.


     Janyo hannunshi tayi"ka dawo mu zauna mu ci abinci a tare, nasan kana jin yunwa" 


 Girgiza mata kai yayi"no bana jin yunwa my wife" ya faɗi hakanne saboda cikinshi acike yake, Hajjaty ta bata shi lafiyayyan abinci yaci ya ƙoshi babu yunwa atare dashi.


  "Namanta ban faɗa maki ba" a hanzarce ta kalle shi tana jiran jin ƙarashen zancen

 "Game da abun da ya faru jiya, dangane da shigowar maciji gidan nan........" a tsanake Pravin Ya labarta mata komai, hatta ƙaryar da yayi masu Senate Lateef bai 6oye mata ba, a ƙarshe yace"na faɗi masu hakanne donsu ɗauki abun serious, saboda bana son abunda zai cutar min dake da kuma ahlinki, shiyasa nayi masu ƙaryar cewa kin kwana idonki biyu"


 Tun da ya fara maganar, Yanayin fuskarta ya canza zuwa 6acin rai, a ruɗe ta furta"Wai kana nufin yaya Hateem shi ya tura da jet aka dauko sheikh imam from sudan to Nigeria? Sannan shi macijin dama mutun ne!? Kuma a gidan Owais dake acikin estate din nan Yake zaune....." Hankali amatuƙar tashe ta furta maganar.


 Jinjina kai pravin Yayi"ƙwarai kuwa duk abunda kika ji na faɗa maki dagaske ne, yakamata mu ɗauki tsastsauran mataki idan ba haka ba owais da prime minister zasu ja mana bala'e garin son taimakonsu, In ba haka ba taya zasu taimaki Yaron dake canza halitta Ya koma Maciji? Ni dai nafi tunanin wasu miyagunne daga cikin abokan hamayyar Jam'iyar su baba Obie suka shirya maƙarƙashiya donsu kashe baba, shiyasa macijin Ya faɗo gidan nan maimakon sauran gine ginen dake akusa da gidan owais din......" a firgice hajiya Saratu take faman zazzare idanunta duk tabi ta ruɗe, maganganun da Pravin Ya faɗa mata sun yi matuƙar yin tasiri Acikin Zuciyarta, Jiki na 6ari ta nufi ƙofa zata fuce don taje ɗakin baba obie, Ko mayafi babu akanta, da sauri pravin ya ruƙo hannunta a haushine ta juyo tana kallonshi.


  "Bari in ɗauko maki mayafi," ya faɗa tare da sakin hannunta, Ya juya cikin takun sauri ya nufi closet dinsu, jim kaɗan Ya dawo hannunshi ruƙe da mayafinta Ya lullu6a mata shi akanta, da sauri ta fice daga ɗakin.


 Fitarta keda wuya Pravin Ya tuntsire da wata irin mahaukaciyar dariya mai matuƙar razanarwa sautinta tamkar ba daga bakin shi take fitowa ba.


    Lokaci ɗaya ya haɗe fuskarshi tamkar bai ta6a yin dariya ba, Ya juya cikin ɗakin Ya nufi gaban mirror Ya tsaya yana kallon fuskarshi, kafin Ya zura hannu ya zaro wayarshi daga aljihun suit dinsa.


   Pressing dinta ya soma yi, kafin Ya kara wayar a kunne.


  da kakkausar Murya Ya furta"mugun Bawa komai yana tafiya yadda muka tsara!!!


  Yana ƙarasa faɗar hakan, Bai Jira amsar da mutumin zai bashi ba yai rejecting call din, akan mirror Ya ɗaura wayar, ya juya da sauri ya fuce daga dakin yabi bayan hajiya Saratu. 



*💋UNAISAH❤*



Idan muka koma 6angaren Unaisah tamkar mai gadi haka ta tsare Danish, duk wani motsinshi akan idanunta, a yanzu haka tana daga kwance gefenshi ta ɗaura kanta saman chest dinshi, ta aza hannunta saman flat stomach dinsa ta natsu tana shaƙar ƙamshinsa, sai faman lumshe idanunta take yi wani irin bacci ne ke ƙoƙarin fisgarta, lokaci yana ta tafiya ba tare data ankare ba ko sallah bata yi ba, gaba ɗaya ta shagala ta saki jikinta, ba zato ba tsammani tajiyo muryar babban mutun Yana faɗin"Allah Yasa ya farka" rass taji gabanta ya faɗi, da ƙarfi ta ware manyan idanuwanta tare da yin wuff ta miƙe zaune tana kallon glass door din a hankali ƙofar ta soma zugewa, a hanzarce ta rarrafa ta faɗo daga saman gadon ta shige cikin labulan ɗakin ta la6e kamar wata 6arauniya, jikinta sai kerma yake yi kamar wadda tayi ma sarki ƙarya.



Gaba ɗayan su ne suka shigo ɗakin tun daga kan Prime minister, sheikh Imam, chief owais, Big guy da salsabeel sai Boss Man, a bakin gadon nashi suka dakata da yin tafiyar idanuwansu akan Danish dake a kwance.


  Unaisah dake a la6e bayan labule zuciyarta ce ta soma bugawa tunawa da ma6allin rigarshi data bari a buɗe, tasan zasu iya gani kuma zasu gane wani ya shigo ɗakin, sai faman cizon yatsanta take yi, tayi danasanin shigowa ɗakin.


     "Har yanzu bai farka ba ko"? Prime minister ne yayi maganar Yana duban fuskar salsabeel.


  "Eh Yalla6ai, amma idan kana buƙatar Ya farka sai atada maka shi, Inyaso daga baya sai ya koma baccin"


  "A'a banaso na takura mashi, zan jira har zuwa lokacin da zai farka"


    da mamaki akan fuskar Boss man yace"ya akai ma6allin rigarshi suka cire"? Sai da ya ambaci hakan su ka yi saurin kai idanuwansu kan Ƙirjinshi dake a buɗe, lamarin Ya ɗaure masu kai.



 "Ko Shi ya buɗe da kanshi? Ko wani ne Ya shigo" Prime minister ne yayi tambayar da alamun ruɗu akan fuskarshi.


 Sheikh Imam Yace"bana tunanin shi ya buɗe da kanshi, sai dai wani iko na Allah ko kuma wanine Ya shigo ɗakin bayan fitar mu"


 "Wanene zai shigo? Yaran gaba ɗaya na tattarasu a ɗakinsu Unaisah, Ummi tana aɗakinta, babu yadda za'ai ma ta Iya ƙetare Iyakarta, Ƴan uwansu maza kuma tare dasu muka tafi masallaci balle ace ko sune suka shigo" big guy ne ya kora jawabin.


 Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba Chief owais da baice komai ba, A hankali yake bin ɗakin da kallo kafin Ya sauke idanuwanshi kan bedsheet din gadon dake a yamutse alamar wani ya hau gadon.


"His bedsheet is squeezed. which means someone came into the room after we left," chief ne ya furta maganar, nan take suka kai dubansu ga zanin gadon, Ya yamutse sosai.


   "Amma wanene Ya shigo" Acewar Boss,"Karfa ace wani mugun abunne"

 Damuwace ƙarara akan fuskar Prime minister,  ya dubi Shiekh Imam dake a gefenshi"Ni dama hankalina bai kwanta ba tun da muka tafi masallaci muka barshi shi kaɗai a ɗakin"


 Cikin kwantar da murya sheikh Imam Yace"In sha Allah babu abunda ya faru dashi, Ina da tabbacin hakan"


 Shiekh Na rufe baki Big guy yace"Sir, please give me a chance to check the CCTV footage, that way we'll be able to find out if someone else entered the room.( Ka bani dama in bincika cctv footage, ta hakan zamu Iya gane wanda ya shigo ɗakin idan har mutunne")


Shiru Chief Owais Ya ɗanyi har Ya buɗe baki zai bashi amsa karaf idanuwanshi suka sauka akan labulan dake lilo Yana mutsi nan take Ya fahimci mutunne Ya la6e aciki



"There's no need to check the CCTV."


Ya faɗa tare da ɗaga Voice dinsa Ya furta"Come Out!"


 Rass taji gabanta Ya faɗi, duk da ranta bai bata da ita Yake yin maganar ba.


  

"I'm commanding you to come out from behind the curtains. Don't make me repeat myself," babu wasa akalamansa.


  Jin wannan maganar yasa gaba ɗayansu su ka kalli direction din da chief owais Yake kallo, Tsantsar mamaki ne akan fuskokinsu ganin labule Yana motsi.


 "Amma koma wanene wannan jikinshi zai gaya mashi, kayi kuskuran shigowa ɗakin nan" big guy ne ya furta maganar.


Prime minister kuwa Ya ƙura ido Yana jiran ganin wani me ƙarar kwanan ne.


  Tsawa Boss man Ya daka da karfi tare da fadin"zaka fito ko sai mun harbe ka da harsashin bindiga" 


  Ƙiris Ya rage ta saki fitsari a wando, tuni ta haɗa uban gumi, jikinta ya hau yin kerma, ita da ba mai laifi ba amma ta firgita kanta, hakanan ta tsinci kanta da jin faɗuwar gaba, gani take kamar in suka kamata a ɗakin zasu zargi wani abu, kodan saboda ma6allin jallabiyarta data cire masa, zasu iya tsammanin da wata manufar tayi hakan.


   "Bawan Allah ka fito salin alin ka bayyana kanka tunkafin mu fusata" acewar big guy, shiru babu alamun na cikin labulan zai motsa.


 Moving quickly Chief Owais Ya nufi labulen yayin da yake nannaɗe hannun Rigar shi, har ya miƙa hannu zai damƙi wuyan mutumin ta cikin labulen muryar Boss man ta dakatar da shi.


  "Sir, Unaisah ce," cak Ya tsaya tare da juyawa yana kallon Boss, gaba ɗaya mutanan dake a ɗakin shi suke kallon cike da mamakin taya akai yasan wanene.


  "Raina ne ya bani itace, kuma ita kaɗaice zata Iya shigowa ɗakin nan don ta duba ɗan uwanta" Ya faɗa tare da ɗaga muryarshi ya furta"Unaisah come out" A hankali kowan nan su Ya ɗaura idanuwanshi kan labulen.


  Janye labulen tayi ta fito tana faman zare gray eyes dinta, nauyin haɗa ido dasu taji da sauri ta duƙar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.


    "Jari mai kasada, da ace kinbari chief ya shaƙi wuyanki sai dai ki ganki a Emmergency room" Big guy ne yai maganar da zolaya, gaba ɗayansu suka saki murmushi, prime minister yace"idan na fahimta wannan itace Yarinyar nan ko" Ya faɗa idanuwanshi akan fuskarta, Boss Man yace"itace My daughter"


 Sheikh Imam Yace"Tabarakallahu ahsanul khaliqin, zonan ƴata mu gaisah" yai maganar tare da miƙa mata hannu.


      ɗagowa ta ɗanyi ta kalli chief dake a gefenta, face mask din fuskarshi Ya hana ta ganshi da kyau, sai dai kyawawan idanuwanshi.


   Tana faman zazzare idanuwanta haɗi da ƙyafƙyaftasu ta nufi sheikh iman, ta ɗaura hannunta asaman nashi daya miƙa mata.


  "Unaisah ko"? Ɗaga mashi kai tayi alamar Eh.


  "Meyasa kina ji muna magana ki ka yi shiru baki tanka mana ba kamar wata mai laifi, ai ba wani abu bane don kinzo duba ɗan uwanki"


   Shiru tayi bata ce komai ba, duk ta kama kanta kamar wadda tayiwa sarki ƙarya.


  "Zonan surukata" prime minister ne ya kirata, da sauri ta wurga eye balls dinta kan fuskarshi rass taji gabanta Yai mugun faɗuwa, har saida ta zaro ido waje ta saki baki tana kallon ikon Allah, duk sun fahimci dalilin ruɗawarta.


   da sauri ta kalli Boss man ta kuma kalli Salsabeel dake atsaye fuskarshi ɗauke da murmushi

  "Baki ji Yana magana ba? Kije ku gaisah" acewar Salsabeel

    Zuwa tayi gaban prime minister ta tsaya muryarta adabarbarce ta furta"Ina kwana,"


 Murmushi yasakar mata Ya ɗaura tafin hannunshi saman sumar kanta

   "Ba ki yi breakfast bane? Ko baki duba time ba, Naji kina fadin Ina kwana bayan rana tayi" cikin kulawa yayi mata maganar.


  Muryarta kamar ta salihar baiwa ta furta"mantawa nayi,'


 "Okey, surukata Ina fata kina lafiya"?


 "Lafiyalou"


"Naji dadin haɗuwa dake, ke fa"?


 Ɗaga mashi kai tayi"nima"


  "Unaisah" Boss ne ya kira sunanta, ta juya tana kallonshi.


  "Sunan shi prime minister, uncle na chief namu, kuma shine ya kira sheikh Imam don Ya duba lafiyar ɗan uwanki"


  Da sauri ta maida kallonta ga prime minister, farin cikin yasa taji hawaye sun cika mata idanuwanta, miryarta na rawa ta furta.


  "Mun.... gode, Ubangiji Allah yasaka maka da gidan Aljanna, kamar yadda ka sanya mu farin ciki kaima Allah Ya faranta maka, In sha Allah duk idan nayi sallah zanyi maka addu'a'.


 Murmushi kowan nan su yasaki, musamman prime minister har cikin ranshi yaji daɗin kalamanta.


  "Nagode surukata,"

Juyawa tayi da sauri ta dubi sheikh imam.


  "Baba mungode, Allah ya saka maka da mafificin Alkhairinsa" addu'o'i ta dinga yiwa sheikh imam, Fuskarshi ɗauke da murmushi Ya shafa sumarta da hannun shi tare da cewa"Nagode da addu'arki agare ni, kina da kaifin basira, kuma kina da hankali, Iyayenki sun baki Tarbiya, Allah yayi maki albarka tare da sauran ƴan uwanki" amsa mashi tayi da ameen, haƙiƙa taji daɗin kalaman sheikh imam, ƴan hawayen da take 6oyewa cikin idanuwanta tuni sun fara gangarowa kan kuncinta.


   "Unaisah, saura chief namu, yakamata kiyi mashi godiya" Boss Man ne ya faɗa yana nuna mata shi, tamkar mai jin shakkar shi ta juya tare da ɗaura idanuwanta kanshi, Yana daga tsaye ya goya hannayenshi on his broad chest, harta ɗaga ƙafa zata nufe shi Big guy yai hanzarin dakatar da ita ta hanyar yi mata Magana.


   Nufota yayi adai dai bayan ta ya dakata tare da duƙo da kanshi saitin kafaɗarta Yayi mata raɗa.


  "You don't need to thank him, saboda baya so, but be kind to him. If you give me the chance, I'll guide you.


   Cikin sanyin murya ta amsa amshi da toh.

  "Good Girl," Ya ambaci hakan tare da ɗago da kanshi, babu wanda yaji me suke tattaunawa.


      Boss Man Yace"Unaisah zoki wuce ki tafi ɗaki ki yi sallah, Yanzu za'a kawo maku lunch ɗinku" amsa mashi tayi da toh, kafin ta nufi ƙofar room ɗin ta fuce da sauri.


    Kafin wani ya kuma yin magana acikinsu, Danish dake akwance Yaja dogon Numfashi, Yatsun ƙafarshi suka soma yin kerma da na hannayensa nan take suka fahimci ya farka daga bacci, wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskar prime minister.


  Salsabeel Yace"Ya farka, Yakamata akawo mashi abincin Yanzun"


      "Wani kalar abinci zai Iya ci"? big guy ne ya tambaya.

   


"Abinci mai ruwa zaifi yi mashi sauƙin wuce wa ta maƙoshi, don bazai Iya tauna abu mai tauri ba" 


  "Okey, bari naje na kawo mashi" big guy ya faɗa tare da juyawa a hanzarce ya fuce daga ɗakin.


   Fitarshi keda wuya, Wayar Chief ta fara Ringing, gaba ɗaya suka ɗago suna kallon shi

 Prime minister yace"Wanene ke kiranka"

  Curo wayar yayi daga aljihu Ya duba screen din kafin Ya bashi amsa da cewa"Dad Lateef ne"


  "Okey, idan kana buƙatar ka shirya kafin mu tafi can gidan ka tafi ɗaki, in sha Allah kafin ka dawo na kammala bashi abincin mu sai mu fara zuwa gida" 


Chief ya furta"okey," kafin ya juya ya nufi room door din, bayan fitarsa


 Sheikh Imam Yace"atare zamu tafi gidan baban naku, Inason in gaishe da aminina da sauran mutanan gidan"


 Prime minister Yace"Toh,"


Shigowa ɗakin Big guy yai hannayen  shi a ruƙe da tray madaidaici, kan carpet din gefen gadon Ya daurashi, kafin Ya haye saman gadon Yayi ma salsabeel alamar yazo Ya taimaka mashi, atare suka ɗaɗɗago da Danish suka jinginar da bayanshi jikin headboard din gadon bayan sun sanya mashi pillow, Yalwatacciyar sumar kanshi ta sauko kan shoulders dinshi.


  "Baba, ko zaku je gidana ka huta, kafin in kammala bashi abinci, in yaso daga baya zamu zo tare da Chief owais, sai mu wuce gidan baban"


Jinjina kai Sheikh Imam Yayi, Hakan yayi nima inaso in canza kayan jikina, Wa zai kai ni gidan"?


  Big guy yace"Aikina ne wannan" ya faɗa tare da saukowa daga kan gadon, Yace da sheikh su tafi Ya sauke shi a mota, Sallama sheikh Yayi ma Prime minister kafin fitarshi saida Ya faɗa cewa idan sunga wani abu badai dai ba dangane da Danish su kira shi awaya su sanar da shi.


 Prime minister Ya amsa mashi da toh haɗi da yi mashi godiya, bayan fitarsu, wayar boss tayi ringing, da sauri ya zaro daga aljihu, sunan chief ne ya bayyana akan screen din da sauri yai Ya kara wayar a kunnanshi.

 

 Bayan sun kammala yin wayar Ya dubi Salsabeel.


 "Chief Yace ka koma gida wurinsu khadeeja" Amsa mashi yayi da toh,

 "Yalla6ai zan wuce, In sha zuwa gobe zan shigo in ƙara duba jikinshi" cikin girmamawa yayi maganar Yana duban Prime minister

 Fuskarshi asake yace"Allah yakaimu Lafiya, Amma nayi tunanin kaima agidan nan kake zaune"

 Salsabeel Yace"a'a, gidanmu daban, Ina kula da sauran Ƴan uwanmu ne"

 "Akwai sauran Yaran kenan bayan wanda ke acikin gidan nan"?

 "Eh yalla6ai"

"Allah ya tayaku ruƙo, Sai Allah Yakaimu"


 "Ameen" ya fada tare da kallon boss yayi mashi sallama.


 "chief yayi magana da Jami'in da zai yi driving dinka, Yana awaje Yana jiranka"

 Amsa yayi da toh, kafin Yasakai Ya fuce daga ɗakin.


Ya rage saura prime minister da Boss man sai Danish da ke asaman gadon.


  "Yalla6ai zan taimaka maka mu bashi abincin"

 Prime minister yace"Okey," 

Boss man ne ya ɗauki tray din abincin Ya ɗaura shi daga gefen gadon, Ya ɗauki robar madara Ya cire murfin a cup ya tsiyaya madarar, kafin Ya miƙa ma prime minister yasa hannu ya kar6a haɗi da furta mashi thanks.


    Abaki ya kanga ma Danish sai dai yaƙi buɗe bakin ya rufe shi gam.


    Ajiye robar milk din boss yayi, tare dakai hannu ya ruƙo la66ansa ya buɗe mashi baki daƙyar, a hankali milk din take shiga bakinshi hankalin prime minister ya kwanta ganin yana swallowing dinta, duka ya shanye, murmushi yasaki yana kallon boss man yace"naji dadi daya sha, ka ƙara mashi da yogurt" 


Martanin murmushin Boss yayi mashi kafin ya kar6i cup din ya zuba mashi yogurt ya miƙa ma hateem, cikin ikon Allah danish ya shanye, sai da ya tabbatar daya cika mashi cikin shi tukunna yace.


 "Bari nabarshi haka, kada naci ka mashi ciki," Hateem ne ya faɗi hakan idanunsa akan fuskar Danish wani irin kallon so da ƙauna yake jefa mashi.


 Sauke tray din boss yayi kan carpet, kafin ya ɗago yana kallon hateem daya ƙurawa danish ido kamar mai karanto wani abu akan fuskarshi, tun ɗazu yake ta son ya tambayeshi wani abu sai dai ya kasa, gani yake kamar raini ne yayi magana da mutun mai babban muƙami irin Hateem.


Daurewa yayi muryarshi da alamun jin shakkar furta maganar yace"yalla6ai..." kallon da prime minister yayi mashi ne yasa shi saurin haɗiyar maganar.


 Murmushi ya sakar mashi tare da cewa "I'm listening to you, and I heard you mention my name. Why did you go silent? Is there something you want to tell me?"


Sunnar dakai ƙasa Tajo yayi"bakomai subul da baka nayi wurin furta sunan"


 "Ban yarda ba, please tell me what you want to talk to me about. Kada kaji nauyin yi min magana, I'm a human being like everyone else." 


Da sauri boss ya ɗago da ido ya kalleshi, haƙiƙa yana matuƙar mamakin sauƙin kan prime minister Hateem, tun da yake arayuwarshi bai ta6a tsammanin akwai wata rana wadda zato zo har ya sami damar ganawa da shugaban ƙasar Nigeria sai gashi cikin ikon Allah ya haɗu da mutun bai ruƙe da babban muƙami na shugaban ƙasar canada ƙasar da tana ɗaya cikin Manyan ƙasashen duniya da suke da tarin jama'a da wadatar arziƙi...


  Yayi zurfi acikin tunaninshi muryar prime minister ta katse shi"kayi shiru baka ce komai ba,"

Sosa ƙeya ya ɗanyi da hannunshi kafin ya furta"am....dama yalla6ai tambayace nakeso nayi maka idan ka bani dama, amma dan Allah kada ka ɗauka da wata manufa"

Da fara'a akan fuskar Hateem Yace"kada hakan ya dame ka, Nifa ɗan siyasane, tambayoyi har marasa kan gado ƴan jarida sunayi min kuma in basu amsa dai dai dasu, ballanta kuma kai dana yaba da hankalin ka, duk mutumin da Owais ya yarda dashi toh nima na yarda dashi, don haka kada kaji komai na baka damar yi min kowace irin tambaya ce"


Ajiyar zuciya boss man ya sauke, har cikin ranshi yaji dadin kalaman prime minister, kuma ya ƙara jin ƙaunar mutumin aranshi.

Sai dai duk da haka nauyin shi yake yi, daƙyar ya iya buɗe baki yace"yalla6ai, naji kamar ance baka ta6a haihuwar ɗa namiji ba, ƴa'ƴan biyu duka mata ne shin dagaske ne"? Boss Na ƙare maganar yayi saurin kau da idonshi gefe ɗaya saboda kunyar tambayar da yayi mashi 


 Shiru prime minister ya ɗanyi, na ƴan mintuna yana maimaita maganar taj acikin zuciyarshi, yayin da yake kallon fuskar danish


 "Am sorry Sir, idan tambayata ta 6ata maka rai" acewar Tajj.


    Calmly Hateem Ya soma magana ba tare da ya kau idon shi daga kan fuskar Danish ba.


     "Ka fama min raunin da yake kwance acikin zuciyata, tsawon shekaru da suka gabata, bana son tuna haukan da nayi, da hawayen dana zubar, da kuma ƙunci da raɗaɗin dana fuskanta saboda rashin da nayi na abun da na ƙwallafawa rai........" tuni yanayin fuskarshi ya canza zuwa matsananciyar damuwa, yayin da yake yin maganar farin ruwane kwance acikin fararen idanuwanshi.

 Hatta tajj dake sauraronshi, Jikinshi yayi mugun yin sanyi tunkafin Ya ƙarasa jin zancen nashi

Numfasawa prime minister yayi before saying"I've lost so much that I still haven't forgotten him. I loved him more than I love my children now, and I've never stopped missing him. I know if I tell you that, you'll think it's crazy." He said it with a smile on his face.


("nayi babban rashi da har yau bana manta shi, inason shi fiye da ƴa'ƴan da nake dasu a yanzu, kuma har yau ban ta6a cire shi araina ba, nasan idan na faɗa maka zaka ji abun wani iri" ya faɗa fuskarshi da murmushi.)



"Bayan gimbiya mujeedat ta yi haihuwa ta biyu ta haifi Yazrin, a ƙalla ta ɗauki shekaru bata sake haihuwa ba, tunda Allah ya bani ƴan mata har biyu, sai na ƙwallafa rai ga son samun ɗa Namiji  har tsakar dare inayin nafilfili akan Allah ya bani ɗa namiji, cikin ikon Allah a lokacin da banyi tsammani ba, Allah ya kar6i addu'ata, Matata ta samu ciki a daren ranar ko runtsawa banyi ba.. though I wasn't sure if it was a girl or a boy, nidai kawai nasanyawa raina namiji ne.." dakatawa yaɗan yi da yin maganar, tajj ya natsu yana sauraronshi, tun yana daga tsaye har dai yakai ga janyo kujerar gaban mirror ya ajiyeta daga gefen gadon ya zauna yana kallon prime minister.

 Cigaba da magana yayi"tun kafin a haife shi na fidda mashi suna, na tsara mashi kalar rayuwar jin daɗin da zaiyi, hatta makarantar da zan sanya shi da komai ma na rayuwarshi sai da na rubuta a diary din dana ajiye domin shi kawai, ita kanta gimbiyata mamaki ta dinga yi ganin yadda na haukace akan son abunda ke acikinta, har fadi take yi na fahimci kafi sonshi akan sauran yaran dana haifa maka, idan ta fadi hakan sai dai nayi murmushi, ba ita kadai ba hatta family dina na Canada dana Nigeria sai da suka shaida ƙaunar dana ke yi mashi, duk rana ta Allah saina kirasu awaya nace su tayani da addu'a Allah ya sauki matana lafiya, saida na addabi kowa da zancen cikinta, mahaifina har tsakar dare nake tada shi daga bacci ince mashi ya tashi yayi nafila ya taya matana da addu'a......" shiru ya ɗanyi idanuwanshi akan agogon hannunshi.


 Tajj duk ya ƙagara da sonjin ƙarashen zancen.


  "Ban ta6a kawowa raina cewa yaron zaizo duniya amace ko zai mutu bayan an haife shi, kana Naka Allah Yana nashi, sai gashi an haife shi babu rai, wallahi bazan iya misalta haukan da nayi ba a asibitin da ta haihu, likitan daya fara furta mun zancen an haifi yarona babu rai da hannu biyu na cakumi wuyan rigarshi na shaƙe shi tamkar zan kashe shi daƙyar dangina suka raba ni dashi, na dinga yi masu sambatu ina fadin karya sukeyi min ni yarona bai mutu ba da ranshi, daga ni har mahaifiyarshi ba'a bari munganshi ba, ita bata acikin hayyacinta bacci takeyi, ni kuma an hana in ganshi gudun kada in haukace masu saboda sun fahimci na mutu akan ƙaunarsa, tun bayan 2 weeks da faruwar lamarin, Ina kwance gadon asibiti Ina jinyar zuciyata, duk na fita hayyacina sai sambatu nake yi ina fadin ina yarona baba kana gani za'a raba ni dashi, ni nasan ɗana bai mutu ba, baba ina jin bugun zuciyarshi acikin zuciyata, ire iren kalaman da nake fadi masu ba ƙaramin raunata masu zuciya nayi ba, babu wanda bai zubar min da kwalla ba, haka suka dinga lallashina sunayi min nasiha, daƙyar suka shawo kaina har suka samu na haƙura nabarma Allah komai sai gashi yanzu tamkar ba'ayi ba" Prime minister Hateem ya ƙare maganar yayin da hawaye ke ƙoƙarin gangarowa saman kuncinshi, da sauri boss man yayi saurin share mashi hawayen don bazai juri ganin babban mutun kamar prime minister yana zubar da hawayensa akan idonsa.


"Nayi kuskure dana yi maka tambayar nan, ka gafarceni yalla6ai, ni kaina jikina yayi sanyi kuma banji daɗin yanayin da na jefa ka ba, da ace nasan maganata zata fama maka raunin dake acikin zuciyarka wallahi daban furtata ba" cikin sanyin murya murya Boss man Yayi maganar. 


  Cikin karyayyar murya yace"kada ka damu, ay yanzu komai ya riga daya wuce,"


Ƙarfin hali taj yayi wurin furta"yalla6ai ko zan Iya sanin sunan baby boy din da ka rasa"


He smiled a little before saying, "Sunanshi *OMAIR BIN HATEEM OBINNA* wannan shine sunan da nayi niyar sanya mashi, Allah bai nufa ba"


Maimaita sunan taj yayi"suna mai daɗi, ubangiji Allah ya baka mafiyin abunda ka rasa, In sha Allah zan tayaka da addu'a"

"Nagode sosai"


"Yalla6ai, zan fada maka wani abu, ni tunda nake arayuwata ban ta6a ganin mutun mai babban muƙami mara girman kai irin ka, A yanzu haka da muke yin magana sai nake jin tamkar a mafarki ne


Murmushin gefen fuska prime minister ya saki jin abunda taj yace.


"Ba kai kaɗai ba, mutane dayawa suna mamakin halina, ni ta inda na banbanta da sauran, bani da girman kai, kuma bana ɗaukar kaina wani, duk idan na tuna cewa mu dukkanmu bayin Allah ne, kuma babu wanda yafi wani awurinshi sai wanda yafi jin tsoronshi sai in ƙara jin ni ba wani bane, idan na shiga cikin takalawa sai in manta wanene ni, zan saki jiki dasu muyi mu'amala tamkar bani da ko sisi, haka zalika idan na shiga cikin masu kuɗi sai inji dai dai nake da su, yanzu haka da nake atare dakai, kallon aboki nake yi maka" zaro ido taj yayi fuskar shi da alamun mamaki.


  "Ni kuma yalla6ai"


Ɗaga mashi kai hateem yayi alamar eh, wani irin farin cikine ya lullu6e Taj sai faman sakin murmushi yake yi jin prime minister ya kira shi da sunan aboki.

  A hankali Hateem Ya mayar da idanuwanshi kan fuskar Danish, ya miƙa hannu ya shafi gefen fuskarshi.


  "Allah ya jarabceni da ƙaunarka, Ina fata ka zama alkhairi arayuwata, zan cigaba da yi maka addu'a Allah Ya baka lafiya, bana so in koma ƙasar canada batare da ka buɗe idanuwanka kayi tozali dani ba" cikin sanyin mirya ya ƙare maganar, ba zato ba tsammani yaji saukar yatsun hannun danish acikin nashi wata irin cakuma yayi ma hannun prime minister ya ƙanƙame shi, hankalin Taj ba ƙaramin tashi yayi ba, har ya yunƙura zai raba hannun Danish daga ruƙon da yayi ma Hateem, da sauri ya girgiza mashi kai alamar a'a, komawa yayi ya zauna still hankalin shi bai kwanta ba, idanun shi akan hannayensu dake harɗe cikin na juna, lamarin yayi mugun ɗaure mashi kai ganin mutumin da ko yatsan shi bai iya ɗagawa amma yayi ƙarfin halin ruƙe hannun mai girma Hateem.


  Tun da ya kafe hannun Danish dake a ruƙe da nashi da ido, bai ko ƙyafta ba, wani irin yanayi yake ji atattare dashi mara misaltuwa, ga wani bugu da zuciyarshi take yi mashi, gaba ɗaya ya shagala da kallon hannayensu na tsawon awa batare daya ankara da gudun da lokaci ke yi ba


Motsin buɗe ƙofar ɗakinne Yaja hankalin boss ga kallon mai shigowa, Chief Owais ne Yake nufo su cikin shiga ta tsadaddun suit launin ash colour, wani irin sanyayyan ƙamshin turarene ke fita daga jikinsa, tunkafin Ya ƙarasa garesu idanuwanshi suka sauka akan hannayen prime minister dake a ruƙe dana Garkuwa, walking gently ya nufi bakin gadon ya ɗan dakata da yin tafiya, miƙewa Boss yayi tare da sarah mashi.


    "Uncle am ready, yakamata mu tafi suna jiran mu, tun ɗazu suke kira awaya" tamkar baisan furta maganar yayi ta.


   Shiru babu alamun prime minister zai amsa mashi.


 Boss man ne yace"Sir, wani abu ne ya faru wanda ya ɗaure mana kai, yanzun nan kafin ka shigo Danish Ya damƙi hannun prime minister Ya ruƙe shi sosai, ina da tabbacin shine dalilin dayasa ya shiga yanayin nan"


 Ɗage girarsa yai alamar yaɗanyi mamaki kafin ya furta"Okey, kayi mashi magana ta yadda zai ji ka"


 Boss ya amsa da toh, sannan ya je daga gefen prime minister yadan russina tare da cewa"Yalla6ai, Chief Ya shigo Yana son yin magana dakai"

Tamakar bazai ɗago ba, A ƙalla sai da ya ƙara mintuna biyar cuf tukunna A hankali Ya dago da fararen idanuwanshi waɗanda suka kaɗa jawur da su tamkar mai fama da ciwon ido.


 Zagayowa chief yayi ta 6angaren da prime minister yake a zaune Ya tsaya yana duban fuskarshi.


  'Uncle are you okey," ya tambayane ganin yadda idanuwanshi suka yi ja.


  Can ƙasan maƙoshi sound din muryarshi ke fita"Owais, kaga yadda ya ruƙe min hannuna? meaning, he feels what I feel about him."


"Uncle, don't let that bother you, zamu dawo ne anjima sai ka ƙara duba shi.


   Jinjina mashi kai yai ba tare daya furta komai ba, shi kanshi chief yana mai al'ajabin ƙaunar da Uncle Hateem ya ke ma Danish.


   

 Ganin yaƙi sakin hannun Danish, yasa shi sake furta"uncle, we ave to go" Magana chief yakeyi mashi amma gaba ɗaya hankalinshi na akan danish, ganin babu alamun zai motsa yasa chief, ruƙo hannunshi cikin kulawa yai mashi alamar ya tashi su tafi, yunƙura prime minister yayi da niyar ya miƙe daga saman gadon sai dai wani iko na Allah Danish Yaƙi bari ya raba hannun shi da nashi.


   Muryar mai girma Hateem na rawa ya furta"My son, Yaron nan Yaƙi sakin hannuna, baison in tafi nabar shi"


       "Uncle, kada hakan ya dame ka" chief ya faɗa, tare dakai hannu ya damƙi hanun danish daƙyar ya 6an6areshi daga ruƙon da yayi ma hannun hateem, shatun akaifun danish  har saman fatar hannun prime minister, wurin yayi ja.

 Hakan ya sosa ran Chief Owais, baiji daɗin yakushin da Danish yayi mashi ba, shi kuwa Hateem ko kaɗan baiji zafi ba, baima lura da yakushin ba.


     Chief da boss ne suka kwantar da Danish, tare da lullu6a mashi bargo har saman ƙirjinshi, kafin suka bar ɗakin, bawan Allah prime minister yana tafiya yana waiwayon ɗakin, gani yake kamar idan ya tafi bazai ƙara ganin shi ba.


 __________________________✍️


BARI MU ƊAN KOMA BAYA MUJI MEKE FARUWA A 6ANGAREN SU ARMY BOY DA TIGER.


Bayan Gari Ya waye suna akwance Saman Sofa, sun saki baki da hanci suna sharar bacci, ba zato ba tsammani Muryar Khadeeja ta farkar da su, Daga can saman bene ta kware murya da ƙarfi tana fadin"Wayyo Allah, Mayu sun kwanar mana agidanmu, wai ku ba zaku tafi gidan ubanku ba" A firgice Suka farka suna faman mutsustsuke idanuwansu, kafin suka kalle ta, a lokacin harta nufi bene tana saukowa down, Sumar kanta a hargitse babu kayan mutunci a jikinta Rigar baccin jiyace bata cire ta ba, dai dai gwiwarta rigar ta tsaya mata, hannunta ɗaya ruƙe da qugunta, ta dambara janbaki saman la66anta har kan kumatunta, ga wani man baki data shafa sai ƙyalli yake yi.


Kallon juna su ka yi fuskarsu babu walwala, Army boy yace"Allah ya wadaran naka Ya lalace wannan masifaffiyar yarinyar Allah Yayi mana maganinta, saboda jaraba baccin ma bazata bari mu ƙarasa shi cikin dadin rai ba, Ni dai harga Allah an takura min, yakamata sir ya bamu iznin komawa gida"


Takaici Ya hana Tiger cewa komai, Jira yake kawai Ta ƙaraso Yaji me zatace masu

 Da gudu ƴan uwanta suka fito daga ɗakunansu, suka biyo bayanta,


A tsakankanin sofas din khadeeja ta dakata da yin tafiyar tana jifarsu da matsiyacin Kallo Tace"mayu masu cinye ma mutane abincinsu, Yanzu sai ku girka mana abunda zamu ci" zaro ido su ka yi suna kallonta.


  Mamaki take basu, A iya sanin su dayawa mata suna jin shakkar sojoji amma ita wannan mai kunnan zoman babu alamun tsoronsu a fuskarta.


 Tsawa Army boy Ya daka mata"ke karki kuskura ki ƙara kiran mu da sunan mayu idan ba haka ba zan harbe ki da bindiga" maimakon taji tsoron maganarshi saita galla mashi harara tana fadin"Ai wallahi sai kun girka mana abun da zamu ci, tunda kuka cinye mana sauran abincinmu na jiya"


  Dafa kafadarta hawwa tayi"dan Allah ki ƙyalesu, Ki zo mu koma ɗaki, ki yi wanka ki canza kayan jikinki," murguɗa mata baki tayi"ni babu inda zanje, wallahi sai sun girka mana abincin da zamu ci, saboda Yunwa nake ji"


  Girgiza kai sojojin sukayi suna kallonta kafin suka kalli sauran ƴan uwan nata,

  "Jiya bamu samu damar Yin magana daku ba, muna fata kun tashi lafiya"

 Atare suka hada baki wurin amsa masu da lafiyalou"

  Tiger Yace"Ku fada mana sunayenku muna son ji"


     Namijin cikinsu ne Ya fara Yin magana.


  "ni sunana MUBEEN" Jinjina kai tiger yayi"Ke fa" Ya nuna Macan dake a gefenshi, Fara ce sol tana da kumatu da ƴar kiba

  "RUBINA"

"Suna mai daɗi, Kefa mai idanuwan ƴan chaina, ya fada da zolaya yana nuna ta gefen rubina

  "YASMIN SUNANA"

 "Good Girl, and You " Da ido Ya nuna Ƴan matan dake ruke da hannun junansu ɗaya Doguwa ɗaya madaidaiciya

 "Ni sunana Hibba ita kuma Sarah"

"Masha Allah, Naji dadin haduwa daku, Allah yayi ma rayuwarku albarka" amsa mashi sukayi da ameen

  Khadeeja masifaffiya tace"ƙwarama da baku tambaye ni sunana ba, don ba fada maku zanyi ba" murmushi suka saki ba tare da sunce mata ƙala ba.


  Bubbuga ƙafafuwanta tayi"ni dai yunwa nake ji, ku tashi ku shiga kitchen ku girka mana abinci"

 Army yace"bamu Iya girki ba, Ko kin ganmu da zannuwane ɗaure a ƙugunmu?

Harara ta watsa mashi

 Tiger yace"Yar uwa khadeeja, baku da maiyi baku girkine a gidan"?

  Hawwa ce ta bashi amsa da cewa"yayanmu salsabeel shine yake girka mana abinci"


 Zaro ido Tiger yayi"kina nufin wannan ƙaton mutumin"?


 Ɗaga mashi kai tayi alamar eh

Sarah tace"ba koda yaushe yake girka mana abinci ba, yaya omar yana kawo mana daga gidan su," sun gane wa take nufi, wato Big guy shi ne suke kira da Asalin sunan shi Umar.


  Kallon agogo Army boy yai a lokacin ƙarfe goma sha biyu na safe.


 "Da alama sun manta yau basu kawo maku abincin da wuri ba, Ya za'ai kenan"?


 Da sauri Mubeen Yace'ai akwai yogurt da madara a frigde, hada bread a store, Idan muna jin yunwa kafin akawo mana abinci su muke ɗauka mu ci,"


 Ran khadeeja Ya gama 6aci, Bubbuga ƙafafuwanta tayi hankalinsu ya dawo kanta, idanuwanta rufe ta soma zazzaga masu masifa tana fadin"ni wlh bazansha yogurt da bready ba, ai kune kuka cinye mana sauran abincinmu a kitchen, wlh idan baku je kun girma min abunda nakeso ba zan kira yaya Omar awaya in fada mashi kun ci mana abincin mu"

Aruɗe suka hada baki suna fadin"Me yai zafi, Kinji munce bazamu girka maki ba ne?


 Nuna masu hanyar kitchen tayi da hannunta"ku tashi ku shiga ku dafa min abinci"


 Agajiye suka miƙe tayi gaba suka bi bayanta sune har cikin kitchen.


 Ƴan uwan dake a falo, saman sofa suka zauna, su kansu ba zasu Iya da rigimar khadeeja ba, Sara ce ta ɗauko masu Robobin madara, Ta miƙa ma kowan nan su, suka zauna suna sha

Daga falo suna jiyo sautin muryar khadeeja dake acikin kitchen.


  "wainar kwai zaku soya min" ta fada tare da buɗe kofar store ta dauko masu egg container ta kawo masu shi akan Countertop ta daura shi.


   Cikin kwantar da murya Tiger yace"khadeeja wannan kwan yayi maki yawa ina laifin a soya maki biyar" harara ta galla mashi"ai bani kadai zanci ba, hada Ƴan uwana suma suna jin yunwar" roba ta ɗauko masu inda zasu kaɗa kwan hada abun kaɗawar,

Kafin ta nufi freezer tana fadin"hada Chicken pepper soup zaku yi mana, Sannan Ku soya mana kifi mubeen yana son ci" Bin ta da kallo su ka yi baku nan su a buɗe kamar sakarkaru haka suka bi ta da kallo.


  Kaji ta ɗauko Guda Uku Manya manya masu tsokoki ajikinsu ta ajiye masu


 Tace"chicken peper soup zakuyi mana, akwai kayan miya da kayan ƙamshi duk zan ɗauko maku su" hankalinta kwance takeyi masu magana, har wani ƙyafkyafta masu idanu takeyi.


  Daƙyar tiger ya iya bude baki yace"Yar uwa khadeeja, bakomai muka Iya girkawa ba, Kuma wannan abincin yayi yawa, ga kwai ga kuma kaji"?


 Zum6ura mashi baki tayi"wanda yasa kuka cinye mana abincin mu na jiya," ta faɗa tare da juya masu baya ta nufi cikin store, gabansu har faɗuwa yake yi, Jim kaɗan ta dawo hannunta ruƙe da Manya manyan doyoyi guda uku ta ajiye masu aƙasa tana faman yin nishi tace"idan kun gama girka wadannan saiku fere doyar ku soya mana ita da kwai" Baki abuɗe suke sauraronta

Komawa cikin store tayi sai gata ta kuma dawowa hannunta ɗauke da ƙaramar roba, dankalin turawane acikinta

 "Chips zaku soya mana da shi" ta ajiye robar, har ta juya zata koma Army boy yayi saurin shan gabanta, Muryarshi a tausashe Yace"khadeeja, Ya isa haka, wai ke meke damunki? Mu fa mazane ba mata ba, bamu Iya girki ba, Bindigogi muka Iya ruƙewa, taya zaki kwaso wannan uban kayan abincin kice mu girka maki"?


  Fashe mashi tayi da kuka tana bubbuga ƙafa tace"wallahi idan baku girka ba saina fada ma Yaya omar kun cinye mana abinci, Kuma In ƙala maku sharrin kun ta6ani" Waro ido waje su kayi har saida gabansu Ya fadi jin abunda tace, Ita kanta da tayi maganar bada wata manufa ta furta ta ba.


 Lallashinta suka soma yi"shikenan, Munji zamu girka maki, Yanzu ki koma falo ki zauna, ashagwa6e tace toh, kuma zan dinga leƙowa ina duba ku" amsa mata sukayi da toh

Bayan fitarta daga kitchen din tiger yace"Allahumma ajirni filmusibati wa aklikni khairan min ha, Yarinyar nan ba ƙaramar makira bace"

  Army boy yace'ai duk laifinka ne, kaine jiya kasa na kwaso masu abincinsu da duk hakan bata faru ba, yanzu gashi ta daura mana wannan uban aikin"


 "Idan laifina ne kaima hada laifinka ai, tunda atare muka cinye masu abincinsu"


 Ran kowan nan su Ya 6aci, tamakar zasu rufe juna da bugu


"Faɗa ku ke yi ko"? Muryar Khadeeja ce ta fargar dasu, arude suka hada baki wurin fadin"A'a aunty, Muna yanke shawarane akan meya kamata mu fara girkawa"


 Murmushi ta saki har dimple dinta Ya lotsa, Hannunta ɗaya ruƙe da Robar milk da take sha.


 "Idan ma faɗa ku ke yi ku kuka sani, Nidai ina jiran abinci, kuma wallahi Kafin In shanye madarar nan ku gama min girki na, idan ba haka ba hmmmm kunsan sauran" Ta fada tare da juyawa ta fuce daga kitchen din.


  Army ya ɗaura hannayenshi biyu saman kanshi"mun shiga uku, wannan wata irin bakar rana ce"?


  Tiger yace"Ba surutu Ya kamata mu tsaya muna yi ba, Mu fara mata girkin kada ta shanye madarar"


  Tu6e rigunansu sukayi, Ya rage saura wandunan kakinsu a jikinsu, sham sun manta da bindigogin su da suka ajiye afalo.


 Kamar mata haka suka fara aikace aikace, wanke nama, Fere doya, Gyaran cefane, da yankan kayan lambu suna haɗa uban gumi zufa ta ko'ina, da waya sukeyin amfani wurin yin browsing yadda akeyin chicken paper soup da sauran abunda basu Iyaba, duk bayan ƴan mintuna sai khadeeja ta leƙo kitchen don taga idan suna yin aikin yadda ya kamata, bayin Allah kamar ba sojoji ba, ta takura masu ta addabi rayuwarsu


Yayin da take zaune a falo cikin ƴan uwanta, Hawwa tace"khaeeja baki kyauta masu ba, dan Allah Ki yafe masu aikin yayi masu yawa"

 Gatsina mata hanci tayi batare da ta tanka mata ba

  Sarah taja guntun tsoki tana kallonta tace"kinji haushin rayuwarki, kuma wallahi saina fada ma Yaya Jazz abunda kika yi masu"

  Banza tayi dasu tamkar bata ji me suke fadi ba,

  Yasmin tace"please ku daina yi mata magana, Itama bayin kanta bane, Lalurace Yaya jazz fa yace mu runka hakuri da yar uwarmu"

  Hibba tace"duk da haka halintane, Deeja tafiye rashin jin magana, bata da haƙuri, saina fada ma Yaya salsabeel"

 Duk wanda yayi magana saita kalli la66ansa

  Robar yogurt din dake a hannunta ta ajiye kan carpet, Ta yunƙura ta miƙe tana yin miƙa, duk suka bita da ido, bindigar da ta gani sakon kujera takai hannu ta dauka ta saita su da ita tana fadin"wallahi dukan ku sai kun mutu, banzaye kawai, Har ni zaku dinga yi ma faɗa"


Dariya suka saki gaba ɗayan su, saboda basu san meye amfanin bindigar ba.


  Hawwa tace"dalla malama Ajiyeta a ƙasa, Kada ki lalata masu abunsu"


  Harara ta watsa mata tana faman cije la66a tace"ta kanki zan fara hawwa Jiya Hada kulleni adaki don kada In futo waje, yau idan na kashe ki bazaki sake Yi min haka ba

 Tana ƙare maganar ta daddage ta ruƙe bindigar dakyau, Tana ƙoƙarin harbawa, Mubeen yayi saurin Janyo Hawwa gefe daya, ba zato ba tsammani harsashin bindigar Ya harbi jikin kujarar inda Hawwa take zaune, Wani irin Hayaƙi ya fita Wurin da bullet din ya shiga nan take ya fashe.(😳)


Nan fa ido Ya raina fata, Gaba ɗayansu sun rude sun gigice, Amatuƙar firgice suka mimmiƙe tsaye suna faman zare idanuwansu

 Dariya tasaki tana fadin"kunyi tunanin bansan yadda akeyin amfani da ita ba ko? To ai na ta6a ganin video a wayar Ya omar, wasu suna kakkashe mugaye da ita, ɗaya bayan ɗaya kuma zan kashe ku yanzun nan" Ta faɗa Tana saita su da ita, fashewa sukayi da kuka suna yi mata magiya, saboda rashin hankali Ta kara sakin wani harsashin kaitsaye ya sauka a tsakankanin ƙafafuwan Rubina, Baiwar Allah Kuka hada majina, sauƙin ma bai ta6a fatar ta ba.


Maza suna a kitchen suna girki, sun bar psycho afalo tana aiki, duk irin girman sautin harbin bindiga basu ji ba, Mubeen Ne ya watso da gudu Ya shigo kitchen din ya ɗaga murya Yace"ga khadeeja can ta daukar maku abunku tana harbin mu" gabansu ne yayi wani irin mugun faduwa, aguje suka fito daga kitchen din adai dai lokaci ta saita kan Sarah jikinta sai kerma yakeyi


   Tsawa Tiger Ya daka Mata, da sauri Ta juyo da bindigar ta saitasu tana dariya tace"Ajalin ku ne ya fito daku daga kitchen, dama haushinku nake ji, Jiya kunkashe min jazz dina"

  Hankalinsu idan yai dubu toh Ya tashi, Khadeeja ta saka su a tsaka Mai wuya, Ga girki sun baro a kitchen Ga wani tashin hankalin dayafi gigitasu

   Dole suka zube kan gwiwowinsu muryoyin su na rawa suke yi mata magiya"dan Allah Anty khadeeja ki rufa mana asiri, wlh bamu kashe maki jazz dinki ba, Yana nan da ranshi, yaji sauƙi raunin jikinshi ya warke, Ki taimaki rayuwarmu ki ajiye bindigarnan aƙasa....." tamkar zasu fashe da kuka haka suka dinga roƙonta, zuciyarta kamar ta kafuran farko babu alamun sassauci tace

  "Nafa san me nake Yi, baku isa ku raina min wayau ba, Idan dagaske Ya jazz bai mutu ba toh Yana ina"?

   Fuska amarairaice Army boy yace"Yana asibiti, likitoci suna duba lafiyarshi,"

  Ƙasa ƙasa da murya Tiger yai mashi raɗa"kai dole fa mu nemi mafita wallahi, Idan ba haka ba zata Iya kashe mu ko ta kashe ƴan uwanta tun da ba hankali gareta ba, ga kuma Abinci mun bari kan gass"


  Army boy yace"to ya zamuyi! Ni wallahi komai ya kwance min,"

  "Gulmata kukeyi koh"? Ta fada tana jifarsu da harara

  Atare suka girgiza mata kai alamar eh, tace"idan ma gulmata kukeyi daga yau Idan na kashe ku bazaku sake yi ba"

    "Ku lallashi yar uwarku, zata Iya ja mana bala'e daga mu har ku" Tiger ne yayi maganar Yana kallonsu Hawwa.


 Duk wanda yayi yunkurin buɗe baki zai bata haƙuri  da bindiga take saita shi,

  Kwatsam Wayar Tiger Ta soma Yin ringing, adabarbarce ya zura hannu ya zarota daga aljihun wandonshi, duk sun rude, ganin sunan Major ya bayyana ne yasa hankalinsu Ya ɗan kwanta,

 Picking call din yayi tare da kara wayar akunne

  Ko sallamar major bai amsa ba, Ya furta"Jazz Ya Jikin Naka"? On the other hand Muryar Major da alamun mamaki yace"Jazz Kuma? Baka ga sunan wanda Ya kira ka bane"?

  Tiger bai kula maganarshi ba yaci gaba da fadin"Kamar ka sani tun safe khadeeja take son Yin magana dakai, Ai saida na fada mata baka mutu ba lafiyarka ƙalou amma taki jin maganata"

 Tun da ya ambaci sunan Jazz khadeeja ta jefar da bindigar kan carpet, ta nufe shi tana fadin"Bani shi muyi magana" jiki na 6ari Army yayi saurin Miƙewa ya damƙi ƙeyarta yana fadin"bashi bane don ubanki, Har mu zakija ma bala'e, masifaffiya kawai, Kin bi kin ƙuntata rayuwurmu kin hanamu sakat, wlh baki isa ba, Aɗaki zan kulle ki," kuka tadinga yi mashi tana zagin shi, ɗaukarta yayi ya nufi saman bene da ita, Daki ya shigar da ita ya kwantar saman gado, Ya fito da sauri yaja ƙofar Ya datse ta da mukullin daya gani ajikin ƙofar, Ajiyar zuciya ya sauke kafin Ya nufi falon, A lokacin Tiger Ya kammala yin wayar da major, Ya miƙe dasauri Yaje ya dauki bindigar ya hada da ɗayar da suka ajiye kan sofa, duka biyun Ya turasu karkashin dining table

  Kallon sauran yaran su ka yi"ku koma ku zauna Yanzu zamu kawo maku abincin" amsa masu sukayi da toh, Jiki asanyaye suka zauna duk basu ji dadin abunda khadeeja ta aikata ma sojojin ba

 "Dan Allah kuyi hakuri Idan mun 6ata maku rai" sarah ce tayi masu maganar

 Murmushin yaƙe suka sakar mata"kada ku damu, ai munyi maganinta yanzu" juyawa sukayi atare suka nufi kitchen, abun da suka daura kan gass harya fara ƙonewa shaf shaf suka ƙarasa Yin girkin.


Khadeeja dake adaki, Sai kuka takeyi tana bubbuga ƙofa da hannunta kamar zata 6alleta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta

  Gajiya tafara Yi da buga ƙofar, Ta Juya zata je ta kwanta karaf idanuwanta suka sauka akan Wayar dr jazz da suka bari kasa, Ga kayanshi daya bari riga da wandon shadda, jiki na 6ari taje ta dauki wayar, duk da bata Iya amfani da ita ba sai da tayi ƙoƙarin kunnata, saboda ta haddace Yadda jazz yake latsawa agabanta, Cikin sa'a ta kunna wayar haskenta Ya kawo,

 Gefen gado ta zauna tana yin shessheƙar kuka

  Ta soma kacaccala mashi wayar, kasancewar babu password a wayar Yasa ta samu damar dannata son ranta, batare da saninta ba ta shigar mashi contact dinsa adai dai kan sunan My Mom ta latsa Kira, Ringin wayar ta fara Yi, Khadeeja ta natsu tana jiran jin wazai Yi magana kamar yadda taga Ana yin amfani da ita ayi communicating


Kiran wayane Ya shigo layin Mom turai, a lokacin tana acikin bedroom dinta ita da sir mubarak akwance saman gado, ita kadai ce idonta biyu, shi Sir mubarak Ramuwar baccin dabaiyi ba jiya yake Yi.

 Jin wayarta na ruri ne Yasa ta sauko daga kan gado, taje gaban mirror ta duba sunan mai kiranta

  Mamakin ƙarara akan fuskarta ganin sunan My Own Son Ya bayyana akan screen din wayarta

    Murmushi tadan saki tana fadin"Allah Sarki My son, Ciwo Ya hana kazo inda nike shiyasa ka kirani awaya, bari Naji me Yake buƙata" ta faɗa tare da ɗaga wayar ta kara a kunnanta, hada ƙoƙarin yin sallama.


  Shessheƙar kukan Khadeeja ne Ya fara cika kunnanta, Zaro ido waje turai tayi muryarta da alamun ruɗani ta furta"Wacece ke kuka"?


*Daga Alƙalamin Boss Bature🫶*



*Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida*

2 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Alsm Don Allah atamakamin da kurkun kaddara book 2

    ReplyDelete
  2. Dan allah ataimakamin da kurkukun kaddara takun karshe

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post