Kurkukun Kaddara Book 2 Page 41

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 41

 


Wani irin mugun bugu zuciyar ummi tayi lokacin da idanuwanta su ka yi tozali da fuskar sheikh imam, tsabar firgita har wayar hannunta sai da ta kubce mata, sheikh imam kuwa tunda ya tsayar da kwayar idanuwansa akan fuskarta bai ko ƙyafta ba, wani irin kallo yake binta dashi mai wuyar fassaruwa, lamarin ya ɗaurewa boss man kai, shi da big guy tare da Unaisah gaba ɗaya Hankalinsu na akansu babu wanda yayi yunƙurin dakatar dasu daga kallon da suke jefawa junansu tsawon mintuna ganin abun nasu ba mai ƙarewa bane yasa Boss man yin gyaran murya, adabarbarce ummi ta soma ƙoƙarin tattara natsuwarta duk tabi ta ruɗe kamar wadda taga wani mugun abu.

  Da sauri ta zuƙunna tare dakai yatsun hannunta dake kerma da niyar ta ɗauki wayarta data faɗi kan floor, sai dai kafin ta kai ga yin hakan sheikh imam ya rigata ɗaukar wayartata, lokaci ɗaya ta miƙe ta juya da gudu ta nufi cikin falon sai da tafara taka stairs sautin shessheƙar kukanta ya karaɗe falon.....


Hankalinsu Batool ba ƙaramin tashi yayi ba, Jin sautin kukan aunty umminsu ya jefa su cikin yanayi na damuwa.


  da mamaki akan fuskar Boss man Ya furta”Sheikh meke faruwa? Ko kasan ta ne”?


Shiru ya ɗanyi jim yana jujjuya wayar ummi dake a hannunshi na tsawon sakanni, kafin ya soma magana da karyayyar murya”bansanta ba, Yau na fara ganinta” ya faɗa tare da juyowa yana fuskantarsu

 Da alamun ruɗu akan fuskar big guy yace”amma meyasa kuka dauki lokaci kuna kallon juna kai da ita? Sannan meyasa ta watsa da gudu tana kuka”?

  Fuskar sheikh imam babu walwala Yace”dan Allah kubar maganar nan, kasan dai bazanyi maka ƙarya ba geme geme dani, nima abun da yasa nake kallonta saboda kallon da take yi min, kuka kuma da take yi wata’ƙil nayi mata kama da wani ne da ta rasa a rayuwarta”


  Jinjina kai big guy yayi badan Ya gamsu da bayanin shi ba.


  “Ga wayarta ku ruƙe mata” ya faɗa yana miƙa ma Boss man, wanda yayi zugudum yana kallon yadda jikin sheikh imam ke tsuma sun fahimci da akwai wani abu da ya 6oye masu wanda baison su sani dangane da ganin ummin america da yayi.


  Cikin sanyin murya Unaisah tace”Ni zan kai mata wayar,” ta fada tare dakai hannu ta kar6e phone din daga hannun sheikh imam, ta nufi cikin falon da sauri.


Bayan tafiyarta, sheikh imam Ya mayar da dubanshi kansu Sajeed da suke a tsaye cirko cirko suna kallon shi.


  “Allah ya yi maku albarka, ubangiji Allah ya kareku daga sharrin duk wani abun cutarwa, Allah ya daukaka rayuwarku......” addu’o’i ya dinga karanto masu suna amsa mashi da ameen ameen

 Bayan ya kammala yi masu addu’o’i, yace dasu”Ku faɗamin sunayenku ina son ji” hatta maganarshi da ƙarfin hali yake yinta duk ya rasa kuzarinsa.


>

  Sajeed ne ya fara cewa”Ni sunana sajeed, wannan kuma Azeeza’ ya faɗa yana nuna Azeeza, kafin Ya ɗaura yatsan shi kan Naufal”Sunanshi naufal ta gefenshi Parvin, ga kuma Jemimah da Hanna, sai Javid and Haris, da Batool, ƴar uwarmu data tafi kaima aunty ummi waya sunanta Unaisah”


 duk wanda ya nuna sai ya fadi sunanshi bayan ya kammala sheikh imam yace”sannu da ƙoƙari Sajeed, nagode daka faɗamin sunayen ku” murmushi Sajeed yayi ba tare da ya ce komai ba.


  A hankali Sheikh Imam Ya dubi boss man da big guy, bai yi mamakin ganin kallon da su ke yi mashi ba, yasan dole suyi tunanin wani abun daban, launin idanuwanshi har sun canza zuwa ja, kau da idonshi yayi daga kansu ya kalli su Haris muryarshi asanyaye yace”ku zauna muyi fira ƴan jikokina” zazzaunawa su ka yi kan carpet shi kuma ya zauna kan sofa, su boss ma suka zauna suna fuskantar shi. 


 *UNAISAH❤*  


   

Koda Unaisah ta ƙarasa ƙofar ɗakin ummi dafe glass door din ƙofar tayi a hankali ta zugeta, bata sameta a adakin ba, sai dai ta jiyo shessheƙar kukanta acikin toilet.


   Ɗaga murya tayi tare da cewa”Aunty Ummi, ga wayarki na kawo maki” shiru ummi bata tanka mata ba, kusan sau biyar tana maimaita maganar babu alamun za’a amsa mata.

      Saman gado ta ajiye mata wayar,  kafin ta nufi ƙofar toilet din ta sanya hannu tayi mata knocking,

  “Aunty Ummi dan Allah ki daina yin kuka, bamu jin daɗi, idan wani ne ya 6ata maki rai, ki yi haƙuri” lallashinta Unaisah taci gaba da yi tun tana jin shessheƙar kukan ummi, har tadaina jiyo sautin kukanta, hankalinta ya ɗan kwanta juyawa tayi da sauri ta fuce daga ɗakin, maimakon ta sauka down ta koma falo sai ta kalla6a ta nufi ɗakin Danish, dama abun take yima zumuɗi kenan shiyasa ta kar6i wayar ummi da sunan zata kai mata.


Idan muka koma 6angaren Danish tsawon mintuna da suka shiga da shi bathroom, kafin su fara yi mashi wankan saida prime minister ya tofe ruwan da addu’o’i kamar yadda sheikh imam yace adinga yi mashi, batare daya cire mashi short din jikinshi ba yayi mashi wanka da ruwa mai ɗumi, tamkar ya samu jinjirin yaro, saƙo da lungu na jikinshi sai da prime minister ya cuccuɗa shi, bayan ya kammala ya ɗauko farin towel cikin jerin waɗanda ke sagale jikin hanger, ya ɗaure mashi a waist dinshi da dabara ya zame short din daya jiƙe duk don kada yaga tsiraicin shi, shanya short din yayi kafin salsabeel Ya taimaka mashi suka fiddo da shi daga cikin kwamin wankan.


Kafin fitowarsu Chief Owais kadai ya rage a ɗakin, Cikin takun sauri ya nufi faskekiyar closet din Danish ya buɗe yana bin jerin tsadaddun suturunsa da kallo A hankali ya tsayar da idanuwanshi wurin jerin jallabiyoyi yana da tabbacin zaifi samun walwala acikin jallabiya, launin fara ya ɗauko mashi, ya dawo ya ɗaura kan gado.


   Jin motsin buɗe toilet door ne yaja hankalinshi ga kallon su

  A daddafe suka fito da danish hannayensu tallabe da shi, da sauri chief Ya ƙarasa gabansu Ya tallabo masu shi a saman shimfiɗeɗan gadonshi suka kwantar da shi.

  “Sannu da ƙoƙari Uncle,” acewar chief

Prime minister yace”yawwa my son, kaima sannunka da ƙoƙari, tun jiya mun hana ka runtsa”


 “Bakomai uncle kada hakan ya dame ka aikina ne”


  Murmushi prime minister yasaki haɗi da bubbuga kafaɗar chief owais alamar jinjina.


  “Uncle yakamata ka koma gida, za’a iya nemanka, ni zan cigaba da kula maka shi”


 Girgiza kai Prime minister yayi”No, ba yanzu zan koma gida ba, sai zuwa anjima” Chief bai musa mashi ba don ya fahimci baison tafiya yabar Danish.


  “Sabeel, bring me some body lotion and perfume” cikin girmamawa salsabeel ya amsa mashi da toh sir.


>

  Ya juya da sauri ya nufi dressing mirror ya ɗauko body lotion tare da turare yazo ya ajiye su kan gadon.


   prime minster ne ya soma bin ko’ina na jikin danish yana shafe shi da mai haɗi da yi mashi tausa don yaji dadin jikin shi, chief ne ya taimaka mashi wurin burkito mashi da danish Ya juya mashi bayanshi, Ya shafa mashi man kafin yabi da turare ya feshe shi.


    da taimakon chief suka sanya mashi jallabiyar, masha Allah, tayi bala’en yi mashi kyau, a karo na farko kenan don bai ta6a sanya jallabiyaba, tabi shape jikinshi ta bayyana kyakkyawar surar jikin shi, musamman broad chest dinsa da strong arms nasa sun fito ruɗu ruɗu ta jikin jallabiyar.


  Ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, ganin sunci nasarar gyara mashi jikin shi, hatta sumar kanshi saida prime minister ya sharceta ya shafe mashi ita da mayukan gyaran gashi, ƙamshin turaren danish ya cika ɗakin kamar wanda akayi ma wanka da ruwan turare.


   “Yanzu me ya rage mana”? Acewar chief, prime minister yace”nasan yana jin yunwa, Yana buƙatar abincin da zai ci”


Salsabeel yace “Yayi bacci yanzu, naga lokacin sallah yakusa cika, may be kafin mu kammala yin sallah ya farka sai mu bashi abincin” 


 “Kana nufin har muka yi mashi wanka bacci yake yi”? Prime minister ne ya faɗa yana duban salsabeel.


 “A’a yalla6ai, idonshi biyu, tun lokacin da muka shiga dashi bathroom, Yanzu nan yayi bacci”


 “Taya akai ka gane yayi bacci” da mamaki yayi mashi tambayar, chief dai yana atsaye yana sauraronsu.


  “Yatsun hannun shi dana ƙafarshi, suna kerma yanzu kuma sun daina gaba ɗaya sun tsaya yadda su ke”

Fuskar prime minister dauke da murmushi yace”ka karanci ɗan uwan nan naka sosai, naji dadin jin hakan, may be wankan da mu ka yi mashi ne yasa shi jin daɗi har yayi bacci”

 Saldabeel yace”ƙwarai kuwa yalla6ai, ay kayi ƙoƙari, Allah yasaka maka da mafificin alkhairinsa kamar yadda ka faranta mashi rai ka gatanta shi kaima inayi maka fatan Allah ya faranta maka ya ƙara ɗaukaka ka” Har cikin ranshi yaji daɗin kalaman salsabeel, 

  “Yalla6ai kaima ban barka abayaba, domin kuwa kayi namijin ƙoƙari wurin ganin ɗan uwana ya samu lafiya, Allah ne kaɗai zai Iya biyanka” ya faɗa yana duban chief owais.

 Jinjina mashi kai yayi batare daya furta komai ba.

  Kiraye kirayen sallar Azhar da aka farayi ne Yaja hankalinsu

    da sauri chief ya zaro agogon azurfar hateem tare da Zobensa daga aljihu Ya miƙa mashi.

>

  Bayan ya saka a hannun shi, ɗaya bayan ɗaya su kayo alwala, kafin fitarsu daga dakin saida prime minister yaje har gaban gadon danish ya ɗan duka tare da kai small lips dinsa saman forehead din danish Ya manna mashi peck, ji yake kamar karya tafi yabar shi, ganin abun nashi bamai ƙarewa bane ga time ɗin salla na tafiya ya kafe danish da ido babu ƙyaftawa da sauri chief yaje ya ruƙo hannun shi ya janyo shi a hankali suka nufi ƙofar fita ɗakin.


 Adai dai lokacin Unaisah dake la6e bakin ƙofar ɗakin tana sauraron su, jin motsin tafiyarsune yasa tayi saurin watsawa da gudu ta la6e a wata ƴar corner.

 Akan Idonta, Chief Owais Ya fito hannun shi ruƙe dana prime minister, still bata samu damar ganin fuskokinsu ba, sai dai salsabeel daya biyo bayansu shi tagani da kyau, tunani ta somayi aranta ko wanene wannan babban mutumin, taso ace taga fuskarshi shida chief, Allah bai bata sa’a ba, Har saida suka 6ace ma ganinta tukunna cikin sanɗa take bin bango tana nifar ɗakin danish cikin sa’a ta buɗe ƙofar ta shige, daddaɗan ƙamshin turarenshi ne ya daki hancinta har saida ta lumshe idanuwanta tana shaƙar shi ......


Cikin takun sanɗa ta nufi gadon, yayin da idanuwanta suke hango mata Man dinta, hayewa saman gadon tayi daga gefenshi ta dakata tana bin body dinsa da kallo, from head to toe, wani irin farin cikine ya lullu6eta ganin shi cikin shiga ta farar jallabiya yayi mata kyau, aranta ta ayyana nasan waɗannan mutanan ne suka taimaka mashi wurin gyara jikinshi saboda boss ya faɗamin cewa ko yatsanshi bai iya ɗagawa, idan kuwa hasashena gaskiya ne naji daɗi ubangiji Allah ya saka masu da gidan Aljanna, ta ƙare zancen zucin fuskarta ɗauke da murmushin farin ciki.


>

   Ta rasa gane bacci yake yi ko idonshi biyu, amma dai tayi missing dinshi na tsawon awannin daya ɗauka tun jiya a halittar maciji, ashe dai da rabon zata sake ganinshi da ainihin suffarshi, yayin da take kallonshi karaf idanuwanta suka sauka akan jan tabonnin dake akan farar fatar dogon wuyansa, harzuwa saman fatar hannunsa.


Ras taji gabanta ya faɗi, ta zazzaro idanuwanta waje tana fadin”My man meke damunka? Jan tabon menene nake gani a jikinka”? Ta ƙare maganar fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa, hawaye tuni sun jiƙe gashin idonta.


Ziraran yatsun hannunta ta ɗaura saman wuyanshi ta soma shafa tabonnin slowly ta zame fingers din daga neck dinsa zuwa kan broad chest dinsa, a hankali take 6alle links din gaban jallabiyar don ta samu damar ganin sauran tabonnin da ke akan fatarshi, da ta buɗe faffadan kirjin nashi, hankalinta yayi matuƙar tashi da ganin tabonnin ta ko’ina, ji tayi tamkar zuciyarshi bata bugawa da sauri ta kanga Kunnanta na dama saitin zuciyarshi, natsuwa tayi tana sauraran yadda take harbawa cikin kwanciyar hankali, tsawon mintuna bata ɗago da kanta ba saboda dadin sauraran heart beat dinsa da take ji, A hankali ta ɗago da kanta karaf idanuwanta suka sauka akan soft lips dinsa batasan ya akai ta tsinci kanta dayi masu kallon ƙurulla ba sun ɗan kumbura, zuciya ce ta soma tunzurata akansu, unaisah da kasada ta ɗaura yatsun hannunta na dama kan la66ansa tayi squeezing ɗin su, ba zato ba tsammani taji yaja dogon numfashi da ƙarfin gaske, tsabar kiɗima jiki na rawa ta rarrafa ta ta wulkita can ƙasan gadon ta faɗo ta labe zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi jikinta ya hauyin kerma duk tabi ta ruɗe gani take yi kamar ta fama mashi ciwon shi... Runtse idanuwanta tayi hadi da matse pink lips dinta wani irin yanayi take ji mara misaltuwa atattare da ita, Jin shiru ya daina jan numfashin ne yasa ta lalla6a ta ɗago da kanta tana leƙenshi, babu abun da ya canza yaci gaba da yin baccin nashi.

Ƙasa ƙasa da murya ta furta”I’m sorry to disturb you, I’ve missed you so much. I can’t take my eyes off you.”Lalla6awa tayi a hankali ta haura saman gadon da rarrafe ta nufe shi, rumfa tayi mashi da sumar kanta ta natsu tana shaƙar ƙamshin turaren jikinsa, tabi ta addabi rayuwarshi da sunan tayi kewarshi tahana mashi sukuni abaccinsa, don taga babu kowa aɗakin shiyasa take yi mashi iya shege....


>

Lokacin da Chief da prime minister tare da salsabeel suka sauko down, kaitsaye suka nufi babban falon, tunkafin su ƙaraso takun takalmansu Ya isar da saƙon zuwansu, A hanzarce Sheikh imam da su Boss man suka mimmiƙe tsaye suna jiran ƙarasowar su, su sajeed dake zazzaune kan carpet suna kallonsu, lokaci ɗaya suka shiga ruɗanin ganin fuskar prime minister Hateem data chief Owais, duk da shi chief ya sanya face mask a fuskarshi, a matuƙar ruɗe suke kallonshi bakunansu asake babu alamun zasu motsa.


  “Sannu da fitowa Yalla6ai” Boss man ne yayi maganar, Big guy yace”barka da fitowa” amsa masu yayi fuskarshi asake,

Sheikh Imam yace”ya jikin yaron? 

Prime minister yace”Yayi bacci shiyasa muka ƙyale shi zuwa time da zai farka”

“Alhamdulillah, naji dadin jin hakan, baccin nan da yayi hutu ne agare shi”


“Babana, muna ƙara yi maka godiya bisa ƙoƙarin da kayi mana, mun hana ka sakat mun kuma hana ka huta, Allah ne kadai zai iya biyanka.....” fuskar sheikh imam dauke da murmushi ya furta”bakomai Hateem, kada kaji komai, ai indai akan aikin lada ne bazani ta6a gajiyawaba, koda zan shekara inayi ne, ni dai fata na shine Allah ya dubi kyakkyawar niyarmu akan yaron nan ya bamu nasara akan ƙudirin da muke dashi na ganin mun raba shi da miyagun dake bibiyar rayuwarshi” jinjina kai kowan nan su yayi, shiekh imam ya daura da cewa”idan na samu natsuwa kafin zuwa dare, Zan turama shi Awaisun addu’o’in daya kamata arunƙa mashi akan komai da zaiyi amfani dashi, kada a kuskura abarshi ya yi gamon kan shi, tun da shi ba musulmi bane bai yi imani da Allah ba, shaidanun dake ajikinsa bazasu ta6a bari ya ambaci sunan Allah, ko ruwan addu’a zaku bashi ku tabbatar yasha akan idonku idan bahaka ba shaidanun zasu iya zubar dashi ko su canza mashi ruwan batare da kun ankareba, tun da su ba ganinsu akeyi”


  “Insha Allah malam zamuyi ƙokarin yin hakan” acewar Boss man.


 Ga dukkan alamu Prime minister Hateem bai lura dasu Batool ba, hatta shi kanshi chief owais din, wani iko na Allah salsabeel dake kallonsu har kallonshi sukayi babu alamun sun gane shi, nan take ya fahimci basu ruƙe kamanninshi ba, saboda sau ɗaya suka ta6a ganinshi kuma a lokacin basu acikin hayyacinsu, jamimah da Azeeza da parveen su dama basu ta6a ganinshi ba, asume aka fitar dasu daga kurkukun.


 “Lahh! Ji wani mai kama da Danish dinmu” muryar Jemimah ce ta fargar dasu, kusan atare suka daura idanuwansu akan yaran

 Zumbur jemimah ta miƙe taje gaban prime minister ta tsaya hada ruƙe qugu tana ƙare mashi kallon mamaki da al’ajabi 


>

  Ɗaya bayan ɗaya yake bin yaran da kallon, Ya fahimci kallon mamaki suke yi mashi, Boss man ne yai masu gyaran murya tare da cewa”Sajeed, kuzo ku gaishe da Kawun Chief dinmu Owais sunanshi prime minister Hateem, wannan kuma shine chief dinmu Owais” ya faɗa yana nuna masu chief da hannun shi.

 Atare suka miƙe tsaye suka nufi prime minister cikin girmamawa suka gaishe da shi, kafin suka gaishe da Chief Owais.

 Murmushi prime minister yasakar masu har dimple dinshi ya lotsa, da mamaki suka kalli juna ganin yadda kamanninsa da danish suke ƙara bayyana.

  “Masha Allah, Naji dadin haduwa daku, My Son ina kuka samu kyawawan ƴan mata da samari masu kama da jinin family dinmu? Ai ni nayi tsammanin Danish ne kadai yake kama damu amma sai nake ganin fuskokin ƴan uwana akan faces dinsu kodai idanuwana ne suke nuna min badai ba”?

 Sheikh imam na murmushi yace”ba kai kadai ba Hateem, ni kaina tun da nayi tozali da yaran nan nake ta mamakin kamannin ku dasu”


  “Uncle, waɗannan sune sauran yaran da muke kula dasu, Ƴan uwan danish ne” chief owais Ne ya faɗa yana nuna su da hannun shi.

  “My son Allah Ya tayaku ruƙo, Ina ƙara yaba maka da jinjina maka akan ƙoƙarinka” calmly chief ya furta mashi thanks”

   “Sajeed, mu tafi masallaci, Batool kija sauran ƴan uwan naki ku tafi ɗaki ku yi sallah, Boss man ne yayi masu maganar,

   Cikin sanyin murya batool tace”Idan muka kammala yin sallah zamu Iya zuwa ɗakin ɗan uwanmu Danish mu duba shi” da ta furta maganar har chief owais saida ya kalleta kafin ya kau da idon shi.

>

Salsabeel ne yace”ku ƙara hakuri yanzu bacci yake yi, sai dai zuwa anjima idan sun farka” amsa mashi tayi da toh, tayi mamakin ganin yana sakar mata murmushi, yayi tsammanin idan sukaji muryarshi zasu gane shi amma still babu alamun zasu gane ɗin.

“Ina ƴar uwarku Unaisah”? Ya jefa mata tambaya, kafin ta bashi amsa boss man ya rigata cewa”taje ɗakin ummi ne” 

Prime minister yace”In sha Allah zuwa anjima idan na dawo gidan zanyi magana daku” ya faɗa yana nuna su batool,’ amsa mashi sukayi da toh, hadi da yi masu godiya.


 Bayan tafiyarsu Batool taja sauran ƴan uwanta mata suka nufi ɗakin su.


*SIR MUBARAK✊*
Tun wuraren ƙarfe takwas na safe suka baro asibitin kafin tafiyarsu saida Sir mubarak yayima Dr fawan Alheri saboda yaji daɗin Yadda ya taimaka mashi wurin ganin Jazz Ya samu lafiya, da matsakaicin gudu motarsu ta haura saman titi, Major ne yake yin driving dinsu, yayin da sir mubarak da jazz suke zaune a back seat na motar.


   Ya ruƙe hannun jazz acikin nashi, kamar ance za’a ƙwace mashi shi, Jazz sai faman lumshe idanuwanshi yake yi kamar mai jin bacci,

  “Jazz me kake tunani naji kayi shiru tun da muka fito daga asibitin baka ce komai ba,” cikin kulawa Sir mubarak yayi mashi magana yana dubanshi

>

   In a cool voice ya furta”Ina tunanin khadija, bata sha maganinta na safe ba bansani ba ko salsabeel Ya bata”

  Murmushin gefen fuska Sir mubarak yayi”idan na fahimceka kana magana ne akan Yarinyar nan mai ta6in hankali ta gidan kajin da kuke kiwo ko ba haka ba” ya fada da zolaya yana ɗaga mashi gira, tuntsirewa sukayi da dariya gaba ɗayansu hatta major dake driving dariyar yake yi.

    “Daddy dan Allah mu daina tuna abun da ya wuce” sir mubarak ya ce”okey na daina my son, tun da baka so”

  Gyaran murya Major yayi sir mubarak ya dago yana kallon fuskarshi ta cikin mirror.


  “Sir, ina zamu nufa? gidanka ko can gidan da Yaran suke?”

 

   Shiru sir mubarak ya danyi kafin yace”mu wuce gida, jazz yana son ganin mommynsa, nasan tayi kewarshi, in yaso daga baya sai muje can gidan” Amsa mashi yayi da toh.


  “Idan mun isa gida please ka kira tiger A waya ka tambaye shi awani hali yaran suke aciki, inason sani”

  Cikin girmamawa Major Ya ce”in sha Allah Yalla6ai zan tuntu6e shi’

  Ajiyar zuciya sir mubarak Ya sauke tare dakai dubanshi ga Dr jazz,

  “My son, ya zamuyi? Bansan ta yadda zanyima mommynka bayani ba, gashi ni ban iya ƙaryaba, nasan dole ta shiga damuwa idan ta kalli fuskarka,” fuskarshi a yamutse yayi maganar, har cikin ranshi baison 6acin ran turai duk da yasan zata fahimce shi amma dole taji ba daɗi.

   “Daddy kada ka damu, idan mukayi mata bayani zata fahimce mu in sha Allah” 

>

     “Allah yasa my son” daga haka babu wanda ya ƙara yin magana acikinsu, har suka shigo estate, Motarsu bata nufi ko’ina ba sai katafaren gate din Gidansa

 A harabar ajiye motocinsa sukayi parking, babu wanda yasan da zuwansu, da sauri Major ya fito ya zagaya ta baya ya buɗe masu mota, sir mubarak ne ya fara fitowa kafin Ya taimaka ma Dr jazz shima Ya fito, hannunshi ɗaya dafe da waist din shi. saboda baya iya tafiya dai dai, tun lokacin da sir mubarak ya cakumi rigarshi ya buga shi da ƙasa ƙafarshi ɗaya ta lanƙwashe daƙyar yake iya takata a yanzu.


 A haka suka nufi cikin gidan, banda Major wanda tuni Ya nufi sauran ƴan uwanshi sojoji dake kai komo a cikin gidan.

    A zaune yake saman Sofa, ya ɗauki wankan dark jeans and white V-neck shirt kayan sun bi shape din jikinsa, hankalinshi a kwance yake operating laptop din gabansa dake ajiye kan table,

 Fitowa mom turai tayi daga cikin kitchen hannunta ruƙe da mugs guda biyu na coffee, ta nufi cikin falon fuskarta asake taje gaban table din Zaki ta ɗaura cup ɗaya

  “Ga wannan My son, Nasan zaka buƙace shi” ɗagowa yayi fuskarshi ɗauke da murmushi ya furta”mom nagode da kulawarki agareni, kina ji da ɗan nan naki”

        Kafin ta kuma cewa wani abu muryar ibad ta janyo hankulansu ga dubanshi, fitowarshi kenan daga cikin ɗaki Sai faman yin miƙa yake yi haɗi da yin hamma, daga shi sai short a jikin shi

  Muryarshi da shagwa6a ya furta”mommy nifa”?

 Zaki ne ya bashi amsa da cewa”Na ƙarfi ne zoka ƙwata, ɗan rainin wayau sai yanzu ka ga damar tashi daga baccin”

 Tur6une fuska yayi”babban yaya jiya fa bamuyi wani isasshen bacci ba, shine nake yin ramuwar na jiyan”

  Dariya mom turai tayi shagwa6ar ibad har mamaki take bata, duk da shima jazz idan abun ya motsa yana yi mata shagwa6a

  “Ranka zai 6aci ne idan ka ci gaba dayi min shagwa6a kamar wani ƙaramin yaro,”

  Bubbuga ƙafafuwanshi yayi hada ruƙe qugunsa wato yayi sai dai ayanka shi

  Mom turai tace”sai fa kana haƙuri da shi, kasan autane kuma kai ka rainesa duk abun da yayi kai ne ka sangartar da shi”

>

 Ta6e baki Zaki yayi tare da kau da idonshi daga kan fuskar Ibad Ya miƙa hannu ya ɗauki mug Ya soma kur6ar coffee..

  “last born zoka kar6i wannan” girgiza mata kai yayi”no mommy, na hannun shi nakeso yasha ya rage min, wannan nakine ki sha” a sukwane Zaki ya dakata da shan coffeen Ya waiwayo yana dubanshi, Ya rasa gane dalilin dayasa Ibad yake yi mashi haka, aduk lokacin da zai ci abu saiya sa rigima akan yaci ya rage mashi kamar wani tsaran wasan shi

  “Kada ka damu zan shiga kitchen in haɗa nawa, kai dai kar6i kasha” mom turai ce tayi maganar

 Ibad ya maƙe mata kafaɗa”mom ni ai nafison yasha ya rage min”

 Girgiza kai Zaki yayi tare da kallon mom turai yace”zan rage mashi”

“Amma ai baida yawa taya zai isheku ku biyu abunda baifi rabin cup ba”

  “Idan bai ishe mu ba, zan turo shi ya ƙaro mana wani a kitchen”

 Gyaɗa kai tayi okey, Har ta nufi sofa zata zauna, sallamar sir mubarak ta katse mata hanzarinta,

  Kusan atare suka kai idanuwansu ga duban ƙofar falon

  Shigowa Sir mubarak yayi hannunshi dafe da dr jazz, tsabar firgice Yasa mom turai ta saki mug din hannunta gaba ɗaya ruwan coffeen Ya zube kan floor, Jikinta na 6ari ta nufe su, Hankalin kowan nan su ya tashi, zaki tuni ya dakata da shan coffeen a hanzarce ya miƙe ya nufi sir mubarak, Ibad kuwa hannayenshi biyu ya ɗaura saman kanshi yana ambaton”mun shiga uku, ɗan uwa Jazz meya same ka? Kayi hatsarin mota ne?


 Muryar turai na rawa take fadin”innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, babe meya faru da jazz ɗina? idanuwanta har sun fara fitar da ƙwalla,

  Sir mubarak bai sauraresu ba, Ya nufi sofa da sauri zaki Ya taimaka mashi suka zaunar da jazz.

 A Hankali Ya ɗago Yana dubansu ɗaya bayan ɗaya kafin ya tsayar da idanuwanshi kan mom turai da tafara sharar ƙwalla, Jikinta asanyaye ta nufo su ta zauna gefen jazz ta ruƙo hannun shi acikin nata,

  “Kayi shiru bakace komai ba? Meya faru da jazz”?

>

 “Daddy kai muke sauraro,” acewar Ibad wanda tuni ya dawo gefen ɗan uwanshi zaki ya tsaya hadi da ruƙe qugunshi

  A tsanake ya soma yi masu magana”ku kwantar da hankalinku.....” tunkafin ya ƙarasa maganar, mom turai ta katse shi ta hanyar yi mashi tsawa tana fadin”taya zakace mu kwantar da hankalin mu? Yaro ya fita gida lafiyarshi qalau yanzu kuma ka dawo dashi goshi ɗaure da bandage ga tabonni akan fuskarshi, sannan babu kayan da ya fita da su a jikin shi, ni dama tun jiya hankalina bai kwanta da fitar jazz ba, babe ka faɗamin meya faru da yarona”!! idanuwanta azazzare tayi mashi maganar.


 Tun da yake da turai bata ta6a gigin katse shi yana cikin yin magana ba sai yau, hakan ya ƙara tabbatar mashi da cewa ranta yakai maƙura a wurin 6aci,

  “Mommy, yaya zaki, Ibad” dr jazz ne ya ambaci sunayensu, a hanzarce suka kai dubansu gare shi.


  “Zanyi maku bayanin komai” 

 “A’a jazz shi nake so yayi min bayani, gaba daya a raunace kake, ka daina yin magana zaka fama ciwonka” ta faɗa tare da kallon sir mubarak wanda yayi shiru yana kallon fuskarta...

  “Meyasa ka tsareni da ido? Ba zaka yi min bayani ba”?

   Bai tanka mata ba har saida ya samu wuri saman sofa dake fuskantar su, Ya zauna, tukunna ya samu natsuwar yin masu bayanin komai daya faru.......

 A ƙarshe yace”bana buƙatar wani yaji abun nan saboda aikin sirri ne sukeyi, basu buƙatar kowa ya sani, Na faɗa maku ne don na wanke kaina daga zargin da zakuyi min na halin da na jefa jazz”

>

  Cikin sanyin murya turai tace”am sorry dear, nayi maka tsawa bisa rashin sani, kayi hakuri dan Allah, hankalina ne ba akwance ba” 

“Na fahimce ki,” atakaice ya furta hakan

 Mayar da duban ta tayi akan jazz”dan Allah nan gaba kada ka ƙarayin wannan gangancin, duk wani abu da zakayi ka sanar da mahaifinka koda ace ni bazaka sanar min ba,” amsa mata yayi da toh,

Kafin ta juyo da dubanta kan sir mubarak”Babe, babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani dasu wurin yi maka godiya saboda irin kulawar da kake ba jazz.....” kafin ta ƙare maganar sir mubarak yai hanzarin katseta”Kada na sake jin kinyi min godiya saboda nayiwa jazz abu, kinsan banaso” cikin sanyin murya tace”nadaina in sha Allah”

 “Daddy, sannu da dawowa, nayi missing dinka sosai, meyasa jiya baka faɗamin halin da kake aciki ba ai da nazo asibitin na tayaka jinya” zaki ne yayi maganar yayin da yake ƙoƙarin zama gefen jazz

 Murmushi sir mubarak ya sakar mashi”sanyin idaniyata, ina fata na same ku lafiya”?

Mayar mashi da martanin murmushin Zaki yayi”lafiyalou, sai dai jiya dukkanmu bamu runtsa ba saboda rashin ganinku da bamuyi ba”

  Sir mubarak yace”shiyasa naga idanuwanku sun kumbura, ashe bani kadai na kwana azaune ba”

>

     Tun da suka fara magana ibad ya haɗe ranshi, 

 “Daddy ni baka ganni bane”? Ya faɗa yana duban sir mubarak

  Girgiza kai ya ɗanyi kafin yace”naganka ibad, amma nida kai wanene ya dace ya fara gaishe da wani? Yamutsa fuskarshi yayi ƙasa ƙasa da murya ya furta”sannu da dawowa dad” ta6e baki sir mubarak yayi saida na roƙa, bubbuga ƙafa ibad yayi

 Mom turai tace”mu shiga ciki, in taimaka maka kayi wanka” zaro ido Ibad yayi haɗi da furta”Mom wa zaki ma wanka? Jazz  ko daddy”?  Duk da halin da suke aciki na damuwa hakan bai hanasu yin dariya ba, shi kanshi jazz din saida ya murmusa,

  “Daddynku nake magana akai,” hannu biyu yasa ya toshe bakinshi, Idan ya kalli sir mubarak sai ya kalli mom turai

  Ko kaɗan batajin kunyar ƴa’ƴanshi, saboda ita aganinta bawani abu bane donta furta hakan agabansu.

    “My son, zamu shiga” 

Zaki yace”okey, zan tafi da jazz ɗaki, zan taimaka mashi yayi wanka ya canza kayan jikinshi’

 “Hakan yayi,” ta faɗa tare da duban Ibad Har yanzu mamaki bai sake shi ba, sai kace baiyi rayuwa a turai ba.

  “Akwai kayan abinci dana shirya mana a kitchen, ka shiga ka dauko su a dining zaka jera”

    Amsa mata yayi da toh, da sauri ya juya ya nufi hanyar kitchen

   Miƙewa zaki yayi tare da ruƙo jazz ya miƙar dashi,

  “Allah ya baka lafiya my jazz,” amsa mata yayi da ameen, kafin suka nufi ɗakin shi

  Bayan tafiyarsu ta dubi sir mubarak”ina ƙara baka hakuri, kasan ba halina bane”

>

 Murmushi yasakar mata”kada hakan ya dame ki, ni dama fargabana halin da zaki shiga, but Alhamdulillah tun da kin fahince ni, yanzu bani da sauran damuwa” Ya faɗa tare da ruƙo hannunta suka nufi bedroom dinshi 

 “Jiya nayi kewarka, idanuwana sunyi maraicin ganinka, dole na haƙura na rungume pillow amadadinka” tayi maganar ayayin da take taimaka mashi wurin cire Rigar jikinshi

  Daɗaɗan kalamanta ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya sukeyi ba, shiyasa akoda yaushe yake ƙara jin sonta, saboda ƙaunar da take nuna mashi, tun farkon auransu bata ta6a barin ya shiga toilet yin wanka shi kadaiba sai idan wani uzirinne mai ƙarfi ya hanasu shiga atare, sannan ta hana ya ajiye mata masu aiki agida ba yadda baiyi da ita ba akan baison tanayin aikin wahala amma taƙiya saboda kishinshi da take yi, batason wata ta ƙwace mata mijinta, 

 Atare suka shiga toilet..............

NEXT PAGE


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post