*ANEELERH❤🔥*
Tun bayan da ta shiga toilet tabar Zahra atsaye tana kallon hoton su, lokacin da ta fito daga wanka bata taras da zahra a dakinta ba, shaf shaf ta shirya kanta cikin shiga ta abaya maroon colour, ta yafa mayafi akanta, fitowa tayi daga dakin a dining room ta taras da su gaba ɗaya sun hallara kan dining chairs, tun daga kan abie dinta, uncle ɗan iya, mami da ummi da kuma mahboob, sai zahra kaf dinsu ne, kowa ya kimtsa domin yin ɗa’amin, Ana ce take yin serving dinsu tana daga tsaye hannunta ruƙe da serving spoon.
Sautin takun takalmantane Yaja hankulansu ga dubanta, fuskarta da fara ta ƙarasa cikin girmamawa ta soma gaishe da iyayenta
“Barka da safiya, ina kwananku, kun tashi lafiya”
Fuskokinsu asake suka amsa mata.
Mahboob Yace”Gm Auntyna, bismillah zoki zauna gefena” ya faɗa yana nuna mata empty chair din dake gefenshi
Zahra dake kallonsu, murmushi tasaki ganin yadda mahboob Yake yima Aneelerh fadanci abunda bai saba Yi ba.
Bayan Aneelerh ta zauna, Ana ta gaishe da ita, a mutunce ta amsa mata”two days bana ganin ki, kin 6oye min sai kace ba gida ɗaya muke a zaune ba, sai dai idan ni na matsu da son ganinki in shiga kitchen time da kike Yin girki ko”? Sunnar dakai ƙasa Ana tayi yanayin fuskarta babu walwala,
Mami tace”Ai ba tun yauba na lura halinta ne batasan sakewa cikin mutane, kullum kina ƙumshe daga kitchen sai ɗaki, yakamata kina fitowa falo muna yin fira dake” cikin kulawa mami tayi maganar.
Cikin sanyin murya ta furta”ay min afwa zan dinga futowa daga yanzu”
Mami tace”haka nakeson ji, ki daina daukar kanki a matsayin ƴar aiki, damu dake duk abu ɗayane awurin Allah, so please adaina kuntata kai adaki” murmushi Ana tadan saki har cikin ranta taji dadin maganar mami, zahra tace”idan ma bata fitoba ni dakaina zan dinga zuwa dakinta ina takura mata da surutu” dariya Ana tasaki,
ummi tace”dako ta shiga uku dake, har bacci sai kin hanata saboda zafin ɗuminki” tur6une fuska zahra tayi, jin abun da ummi tace, harara ummi ta jafa mata”lafiya kike kallona, ko nayi maki ƙaryane? Kafin zahra tayi magana mahboob yace”wallahi ummi gaskiya kika faɗi” yai maganar yana kokarin tura chips abakin shi”Zahra badai ɗumiba, kamar aku, inta fara zuba kamar radio mai jini, ga tambayar tsiya kamar tsohuwar ƴar jarida” gaba ɗayansu suka sanya dariya, ran zahra ya 6aci a ƙule tace”hmmm mahboob ai ƙwarani, wai talla zaiwa audi gori, idan ni surutu gare ni kai fa? Saboda shegen maƙonka ko kuɗi zaka ƙirga sai ka shiga toilet don kada wani ya gani” dariya su ka yi, Abie Da uncle ɗan Iya sun kasa kunne suna sauraran su, ganin surutun nasu bame ƙarewa bane yasa uncle dan Iya yi masu gyaran murya hankalinsu ya dawo kanshi”surutun Ya isa haka, kun cika mana kunne, Yakamata ku maida hankalinku akan abun da ku ke ci, kun riga da kunsan babu kyau ana cin abinci ana surutu” tunda ya ambaci hakan kowan nan su yaja baki yayi shiru, baka jin sautin komai saina cokulansu kwas kwas tamkar zasu fasa plates din abincinsu, gaba daya hankalin Mahboob dana Aneelerh yana akan Ana, ga dukkan alamu sun fahimci babu lafiya atattare da ita, tun daga kan yadda take faman zazzare idanuwanta.
Cup din lemu Aneelerh ta dauka takai baki tana kur6arshi, bayan ta kammala sha tace”ki koma ɗaki ki zauna ki hutu” ta fada tana duban Ana
“Inaso ne ku kammala cin abinci in kwashe kayan, akwai sauran aiki da zanyi wanke wanke da gyaran kitchen idan na kammala sai in huta”
Aneelerh tace”kada ki damu zanyi maki aikin, just ki tafi ɗaki ki huta”
Harta buɗe baki zata kuma yin magana mahboob ya tari numfashinta da cewa”Sis Ana, kiyi abunda aunty Aneelerh ta fada maki, nima zan tayata yin aikin”
Gyaɗa kai Ana tayi cikin sanyin murya ta furta”nagode madam, Mahboob thank u” ta fada tare da juyawa ta nufi bedroom dinta da sauri, hatta yanayin tafiyarta babu natsuwa.
Kallon juna Aneeelerh da mahboob sukayi, da ido tayi mashi nuni dayabi bayan Ana yaji masu meke damunta.
Jinjina mata kai yai alamar toh, miƙewa yayi daga kan kujerarsa yakai hannu ya yago tissue Ya goge bakinsa.
“mahboob harka kammala cin abincin”? Uncle ɗan Iya ne ya jefa mashi tambayar.
“Ban ƙoshi ba daddy, ina son zan shiga toilet ne uziri gare ni” uncle ya amsa mashi da okey.
Da sauri Ya juya yabar dining area din,
Kasancewar Bedroom dinsa dana ana a 6angare daya suke shiyasa yai ƙaryar cewa toilet zai shiga.
Tunkafin mahboob Ya shiga ɗakinta ya soma jiyo shessheƙar kukanta, Hankalinshi yayi mugun tashi, koda ya ruƙo handle din ƙofar room din nata adatse ya Ji ta, muryarshi ƙasa ƙasa Ya ambaci sunanta shiru bata amsa mashi ba, knocking kofar yayi”sis ana ki buɗe min ƙofa dan Allah, Inason yin magana dake, Aunty Aneelerh ce ta aiko ni”
Jin ya ambaci sunan aunty aneelerh yasa tayi saurin shiga toilet ta wanko fuskarta, jiki na rawa tazo gaban ƙofar ta buɗe mashi ita.
Ajiyar zuciya ya sauke yana bin fuskarta da kallo, idanuwanta sun kaɗa jawur da su.
Ruƙo hannunta yai acikin nashi kamar wani babban mutun Yajata zuwa cikin dakin, Ya kulle ƙofar.
Tare da goya hannayensa saman ƙirjinsa Yana kallon fuskarta
Ganin ya tsareta da ido yaƙi yin magana ne yasa tace”mahboob lafiya kake kallona? Me aunty Aneelerh tace ka fada min”
Numfashi yaja kafin ya soma yi mata magana
“Meke damunki? daga ni har aunty Aneelerh mun fahimci bakya jin daɗi kamar akwai wani abu dake damunki”
Adabarbarce ta furta”babu komai mahboob lafiyata qalou....”
“Bazai yiwu ba Ana, saboda kafin na shigo ɗakin ki na jiyo sautin shessheƙar kukanki, taya zakice min bakomai? Bayan ga alamu nan nagani akan fuskarki, dan Allah Ana kada ki 6oye mana abunda ke damunki, kinga mun damu dake ni da aunty aneelerh dama sauran mutanan gidan”? A marairaice mahboob yayi mata maganar
Baiwar Allah tayi zuru da ido, komai nata ya canza.
Ƙoƙarin danne damuwarta tayi hawayen da suka taru acikin idonta tayi saurin mayar da su.
Can ƙasan makoshi sound din muryarta ke fita
“Dagaske nake yi maka mahboob, babu abun da ke damuna, idan ma saboda shessheƙar kukan da kaji ina yi ne to ka kwantar da hankalinka, sister dina ce janet ta kirani awaya tana fadin halin da take aciki Na rashin kuɗin da zatayi amfani dasu, gashi bata da koshin lafiya ko aikin da take zuwa yi a hotel yanzu komai ya ta6ar6are mata, idan ba zaka mantaba na ta6a baka labarin ƴan uwana Janet da esther, har na fada maka cewa mu marayune bamu da kowa neman na kanmu muke Yi, A halin yanzu dai nice nake taimaka masu da kuɗin da suke siyan abinci da suturar sanyawarsu, nima idan natara kudin albashina ne nake samun wanda nake tura masu.....
tunda tafara magana jikin mahboob yai sanyi, tausayinta duk ya kama shi, har cikin ranshi ya yarda da abunda ta faɗa mashi.
“kinsan da abun da ke faruwa da ƴan uwanki shine baki faɗa mana ba? Meyasa? Meya amfanin zaman taren Ana”?
Fashe mashi tayi da kuka tana fadin”bana so ne na takura maku, shiyasa ban fada maku ba”
Dafe kai mahboob yayi dahannu ɗaya ranshi ya 6aci afadace yace”kin ban mamaki yanzu ko aunty aneelerh baki Iya faɗama damuwarki ita da ta dauke ki tamkar jininta, gaskiya ni baki kyauta min ba Ana, banyi zaton hakan daga gare ki ba, ashe baki daukemu kamar yadda muka dauke ki ba”
Ruƙo hannayenshi tayi acikin nata yayin da hawaye ke fita akan fuskarta tace”mahboob am sorry, idan ranka ya 6aci”
Ta6e mata baki yayi”Ni zanje na fada ma aunty aneelerh halin da ƴar uwarki take aciki, nasan zata taimaka maki, Nima zanyi kokarin baki wani abu, ki cika, itama zahra zan mata magana, sai mu haɗa maki kudin da zaki tura masu ......”
Godiya ta soma yi mashi
“Nagode mahboob, naji dadin taimakon da zaka yi min”
Sakin fuskarshi yadanyi”dan Allah daga yau ki daina sanya damuwa aranki, ni nafiso in ganki cikin kwanciyar hankali, fuskarki da annuri, idan ma wani abu na damunki, please ki runƙa sanar dani, zan taimaka maki da abun nake dashi, ga kuma aunty aneelerh itama ki dinga fada mata damuwarki”
“Zanyi hakan mahboob nagode da kulawarku agareni”
Sai da mahboob ya tabbatar ya sanyata farin ciki, kafin Ya fito daga dakin Ya nufi dining area Koda ya ƙarasa bai taras da Aneeleerh da zahra ba, Har sun kammala yin breakfast dinsu, daga can falo Ya hango mami da ummi, zaune suna fira tare da Uncle ɗan Iya da abie.
Hatta kayan abincin an kwashe su daga dinning, harya juya zai nufi dakin Aneelerh ta wutsiyar idonshi Ya hango gifcinta a kitchen, da sauri Ya nufi kitchen tun kafin Ya ƙarasa ya jiyo muryar zahra ta zaƙe tana ba Aneelerh labarin shagalin birthday din obie da akayi, maimakon Ya shiga sai ya la6e gefe daya ya kasa kunne Yana sauraronsu.
Babu wanda ya lura dashi acikinsu saboda sun bashi baya.
Aneelerh tana gaban Sink Ta tattara kwanukan da suka 6ata tana wankesu, zahra tana agefenta
“Aunty Aneelerh ina baki labari, wallahi Anyi 6arin dollar a wurin nan, dangin obie sun gaji arziƙi gaba da baya, wai kinga manya manyan mutanan da suka halarta? Attajiran masu kuɗi masu manyan muƙamai, kowa kika gani a filin taron da matsayinsa, daga governor sai president, ga sanatoci da ministoci......”
Murmushi Aneelerh tasaki tana fadin”Gaskiya naji takaici da ban biki munje taron nan ba, da nima na kashe kwarkwatar idanuwana”
“Aunty Aneelerh duk yadda zan baki labari bazan iya fada maki kwatankwacin abun da idanuwana suka gane min ba, nifa lokacin da ƴa’ƴan baba obie suka fito tsakiyar fili sunayi mashi liƙi Yana taka rawa wallahi ji nayi kamar inyi wuff in shiga filin in tattara kuɗin in saƙe a hammata”
Tuntsirewa aneelerh tayi da dariya tana duban zahra, hada kwatanta mata yadda zata kwashe kudin ta saƙe ahammata.
Mahboob dake a la6e yana sauraron su dariya ce kumshe abakinshi.
“Ni abun da yafi burge ni, haɗuwar ƴa’ƴan baba obie da jikokinsa, da surukansa sun ɗauki wanka na mutunci na kece raini kai komai ma sun haɗa, waɗanda suka fi burgeni kinga prime minister Hateem, da president dinmu Sharafudeen sun iya dattako, komai nasu da aji suke yin shi, matayensu sunfi kowa haduwa gimbiya mujeedat da Hajiya malikat sarauta, sai kuma mutuniyata Hajiya saratu inayin matarnan saboda tana ƙaunata mutane suna fadin masifarta ni wallahi bata ta6a yi min koda tsawa ba kamar ƴar cikinta haka take yi min magana....” da farin ciki akan fuskarta tayi maganar.
Aneelerh tace”Jinin ku Ya haɗune dana juna, Allah yasa ta zama surukarki kinga shikenan kema zaki samu matsugunni a obie estate” wani irin ihun farin ciki zahra tasaki hada jujjuya qugu tana fadin”Amen Ya Allah, Aunty Aneelerh Allah ya kar6i addu’arki”
Dariya Aneelerh tasaki yayin da take ɗauraye plates din da take wanke wa da ruwan dake fita a faucet.
“Zahra baki faɗamin haduwarki da mutumin ba”?
Kwa6e fuska zahra tayi annurin fuskarta ya ragu.
“Bai zo taron ba, duk irin burin dana ci nason ganinshi bai halarta ba, banji dadi ba dama nasan zai yi wuya yaje saboda mutunne shi da baisan hayaniya”
“Eyyah zahra najiye maki baƙin ciki, in sha Allah wata rana zaku haɗu da shi”
Ta6e baki tayi”Ni yanzu ba wannan ba auntyna, Inataso in baki labarin Nazli da Yazrin Ƴa’ƴan Prime minister da ƙanwar Chief Owais hindu, kinga waɗannan dana lissafa maki ƙarshene su afagen kyau da aji, cikin maza kuwa in ka cire chief owais sai wani ɗan uwansu menene ma sunanshi.....” ta faɗa tana cizon yatsa takasa tuna sunan.
“Namanta, shima a canada yake zaune, mutumin ya iya ɗaukar wanka, ga kyau da aji bayan shi sai twins sun haɗuwa sunyi kyau kamar dollars.
Dariya Aneelerh tayi, jin yadda zahra ta haƙiƙance tana bata labari ko gajiya batayi.
“Yanzu faɗa min alherin da sukayi maki naji ɗazu kince zaki fada min”
Gyara tsayuwa zahra tayi kafin tace
“Kinga da farko Hajiya saratu tayi min kyautar tsadadden leshi guda biyu, da hand bag, hada set na agogo da zobe, da turarurruka......” jinjina kai Aneelerh ta yi tana fadin”masha Allah, zahra najiye maki daɗi, kin samu na sallah”
“Bangama fada maki ba, bayan kuɗin aikin decoration da hajiya saratu ta biyamu, prime minsiter yayi mana kyautar kuɗi duk mutun ɗaya 1.5 million” waro ido waje Aneelerh tayi mahboob dake la6e jin an ambaci kuɗi sai gashi ya dawo gefen zahra Yana raira waƙa.
“In rabo ya tsago dakai kuma abun ya tabbatar saida kai to rabbine yace sai da kai in sai da kai kawai sai da kai, don haka nima Allah ne ya tsaga da rabona ashe arziƙine ke kirana......” gaba ɗaya suka sanya dariya, Aneelerh tace”mahboob yaushe ka shigo kitchen din nan”
Da murmushi akan fuskarshi yace”tun ɗazu ina la6e bakin ƙofa na kasa kunne ina sauraron aku sarkin ɗumi, yau surutun zahra yayi min rana wannan arziƙi haka, wato saboda baƙin ciki zahra ƙiri ƙiri kika hana in rakaki obie estate da yanzu hadani za’ayi rabon kuɗin nan....”
Dariya zara tayi tana fadin”ai baka ji komai ba, bayan kuɗin da prime minister yabamu, president Ya ƙara mana, duk mutun ɗaya dubu ɗari takwas” dafe ƙirji mahboob yayi kamar wanda yaji wani mugun abun
“Sannan Abokin Baba Obie, Jan kunne ya raba mana dubu ɗari biyar biyar da dollar ya bamu su”
Kallon juna mahboob da Aneelerh su kayi.
“Anya zahra dagaske kike kuwa? Wannan kuɗi haka kamar akan bishiya ake tsunkosu”
Hararar shi zahra tayi”an gaya maka kowa mai maƙone irinka, ai su a wurinsu kuɗin da suka bamu bakomai bane”
Jinjina kai mahboob yayi”Allahumma arzuƙni, Sister Yanzu ina kuɗin suke? inaso zan tayaki ƙirgawa”
Dariyar shaƙiyanci zahra tayi kafin tace”suna kwance cikin account bank dina suna bacci, dollar din da aka ba mu ne kaɗai suke a dakina kuma na 6oye su saboda nasan halinka sarai, tsaf zaka Iya zuwa ɗaki yi min halin 6era”
Dariya Aneelerh tasaki, a lokacin ta kammala yin wanke wanken, ta mayar da hankali akan fuskar zahra
Mahboob Yace”kar dai kice zakiyi min rashin mutunci wallahi sai inyi zuciya inje in nemi auran ɗaya daga cikin jikokin baba obie”
Dariya suka saki gaba dayansu bayan sun tsagaita Aneelerh ta dubi mahboob”Ya ake ciki? Kunyi magana da Ana”?
Ɗaga mata kai yai alamar eh, zahra tace me ya faru ne ko bata da lafiya”
Nan mahboob Ya kwashe komai Ya sanar dasu dangane da halin da Ana take aciki.
Shiru sukayi jikin kowa yayi sanyi, musamman Aneelerh, ranta Ya dan 6aci bata ji dadin ƙin gaya matan da tayi ba.
“Idan kuwa hakana Ana bata kyauta min ba,Yanzu har akwai abunda zata 6oye min duk irin shaƙuwar dake atsakanin mu?”
“Aunty Aneelerh please kada ranki ya 6aci, na riga da nayi mata faɗa, abun da ya dace ku harhaɗa mata kudin da zata turama ƴan uwan nata”
Zahra sarkin tausayi tace”nida da halima wallahi da sun dawo gidan nan da zama.....” wata uwar harara Mahboob Ya watsa mata”saboda ke zaki ciyar dasu ko”? Fashewa sukayi da dariya.
Aneelerh tace’baka da dama mahboob, yanzu fa ka gama fadin a harhada mata kudi aturawa ƴan uwanta shine kuma don tace su dawo nan da zama kake tada jijiyoyin wuya daga maganar taimako”
Yamutsa fuska mahboob yayi”abun da nake nufi Aunty Aneelerh, ɗan adam ba abun yarda bane, muna iya mu taimake su su kuma su butulce mana shine abunda nake jiye mana, kawai dai ƙwara in taimakon zamuyi masu mu tura masu can su ƙarata”
“Ka faɗi gaskiya mahboob, nima nayi wannan tunanin, Yanzu me yakamata muyi”? Acewar Aneelerh.
Zahra tayi karaf ta kar6e dacewa”kowa ya kawo abunda yake dashi hada kai mahboob nakama sai yafi yawa tunda kaine jagaba atafiyar”
Harararta yayi”zahra ki daina wannan maganar, ni bawai bazan bada ba, idan na bada ai ba faduwa nayi ba, duk wanda ya taimaki wani shima Allah zai ji ƙansa, ga lada da mutun zai samu, kawai dai ni bani da kuɗinne Yanzu.....” ya fada yana soso keyarshi.
da zolaya zahra tace”hmmm, Ana fa ba musulma bace, ta ina zamu samu lada idan muka taimake ta”?
Banza yayi da ita baice komai ba, Aneelerh tace”babu ruwanmu da wannan, don Allah zamuyi da kyakkyawar niya, kidaina wannan tunanin” gyaɗa kai zahra tayi”shikenan naji, zan bata wani abu cikin kuɗin dana samu, Mahboob Idan kana da acct number dinta ka tura min” Aneelerh tace”Ina da ita, Idan muka koma ɗaki zan tura maki, Nima zan sanya nawa kudin”
Farin ciki ne tsantsa akan fuskar mahboob, Yaji daɗi zasu taimaki Ana batare da ko sisin shi ba.
“Allah yabarmun ku sisters dina, zahra Allah ya baki miji nagari mai sonki mai ƙaunarki, and aunty Aneelerh ubangiji Allah ya bayyanar mana da mijinki da ƴan uwansa , Allah ya raya mana baby junaid dinmu....” addu’o’i yadinga yi masu suna amsa mashi da ameen, kafin Ya juya zai fuce daga kitchen din
“Mahboob” kiran sunanshi da Aneelerh tayine ya dakatar da shi daga yin tafiyar ya waiwayo yana kallonta
“Please idan ka fita ka faɗama su mami, zuwa anjima Hajiya adama zata zo kawo mana baby junaid nasan bata sanar da ita ba”
“Aunty Aneelerh ashe yau muna da babban baƙo agidan namu, mutumina zai dawo, zamu dasa daga inda muka tsaya”
Murmushi Aneelerh tasaki, zahra tace”wallahi har na kosa in ganshi,Yau zaisha daƙuna duk saina sale mashi fatarshi” Aneelerh na murmushi tace”inaso zamu shirya masu abincin da zasu ci, tun da Ana bata jin dadin zuciyarta mubarta ta huta sai muyi aikin atare”
Zahra tace”Lafiyalou, dama na kwana biyu banyi girki ba, har cake zan haɗama baby junaid dina”
Sun jima suna yin fira a kitchen kafin daga bisani suka fuce zuwa ɗakin domin yin sallar azhar da aka fara kira.