Kurkukun Kaddara Book 2 Page 43 Last Page

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 43 Last Page


OBIE ESTATE🌃

Idan muka koma 6angaren dattijon arziƙi, tunda garin Allah ya waye Hankalinshi ba akwance Yake ba, gaba ɗaya yabi ya furgice masu sun rasa gane kanshi, ko jiya da dare bai runtsa ba, sambatu yadinga yi masu yana firgita yana fadin ga macijij nan zai sare shi, Ina owais dinshi  Yana gani za’a cutar da shi bazai kashe macijin ba, mutun biyu da suka taya shi kwana a ɗaki his excellency Deen ne tare da His excellency abdul razak, su kansu basu yi bacciba jiya saboda halin da baban nasu yake aciki, hatta sallar asuba agida sukayi ta yaƙi fita daga ɗaki, kuma ya hana su tafi subarshi, bawan Allah ba ƙaramin jiki yaji ba, hada ruɗun tsufa ke damun shi, daƙyar suka samu nasarar sanya shi yin baccin dole.


A yanzu haka Yana daga kwance saman gadonshi Ya ɗaura kanshi kan pillow, deen da Abdul razak suna a zaune saman arm chairs din dakin idanuwansu akan fuskar baba obie. 

Jin motsin buɗe kofane Yaja hankalinsu ga kallon mai shigowa

   Senate lateef ne, fuskarshi babu walwala.

  Daren jiya da damuwar abunda ya faru ya kwana

  Miƙa masu hannu yai suka gaisa da ƴan uwan nashi

 Kafin ya dubi baban nasu dake kwance kan gado yace”Bacci yake yi ko idon shi biyu”?

 His excellency Deen ne yace”bacci yake yi, daƙyar muka samu Ya runtsa” ajiyar zuciya senate lateef ya sauke kafin yace”banji dadin abunda ya faru jiya ba, gashi har yana neman zautar mana da mahaifinmu, wai taya ma akai har maciji ya shigo part din nan”? Rai amatuƙar 6ace yayi maganar 

 His excellency Abdul razak Yace”abun da yafi ɗaura min kai shi Owais din Yace ba maciji bane mutunne ya rikiɗa....”tunkan Ya ƙare maganar Senate lateef yace”inko dagaske ne wannan maganar to kuwa ba mutun bane dama, Aljani ne sannan ita wannan ifritun yarinyar mai kasada dana gani atare da shi wacece ita!”? Kafin wani ya bashi amsa sallamar Pravin ta katse masu hanzarinsu,

  Shigowa yai cikin shiga ta black suit.


   Cikin girmamawa pravin ya gaishe da su, bayan sun amsa masu fuskokinsu babu walwala, pravin ya soma yin magana

  “Baba bashi da lafiya ne? naga da asuba bai halarcin masallaci ba”

   “Baka ga abun da ya faru jiya bane”? Acewar senate lateef.


   “Nagani, kar dai ace shi ne ya hana shi sukuni”? Cikin nuna kulawa yayi maganar.


  His excellency abdul razak Yace”ai kuwa dai shine, don jiya ko bacci baiyi ba tsabar firgici, yanzu haka ma da kake ganin shi a kwance daƙyar muka samu yayi bacci’

    “Abu baiyi daɗi ba” pravin ya faɗa yana ɗan girgiza kanshi”ubangiji Allah ya bashi lafiya” atare suka amsa mashi da Ameen.

  Senate lateef ya ɗaura da cewa”ni yanzu so nake naji daga bakin shi Owais, ya faɗa min wanene macijin menene alaƙar shi dashi”

    “Bari na kira shi awaya, ai jiya yace zai shigo yai mana bayani amma shiru kake ji wai malam yaci shiru” Deen ne yai maganar tare da curo wayarshi daga aljihu ya danna ma Chif Owais Kira, kusan sau uku tana yin ringing bai yi picking ba.


 “Bai ɗaga ba, may be baya akusane da wayar” ya fada yana kokarin maida wayar cikin aljihun, kwatsam kiran owais ya shigo wayar tafara ruri, ajiyar zuciya ya sauke tare da duban su yace”shi ne ke kira,” ya fada tare da yin picking din kiran Ya kara wayar a kunnanshi, bayan sun gaisa deen yace”muna ta tsammanin zuwanka gida shiru baka shigo ba, ga babanku nan kwance ba lafiya saboda abun da ya faru jiya ko runtsawa baiyi ba sai firgita yake yi”.


  On the other hand chief Owais ya furta”I will come later, insha’Allah,”


“Okay, we’ll be waiting for you, sannan inason sanin Ina macijin nan yake? Naji kace mutunne”

  Muryar chief owais tamkar bai son furta maganar yace”please uncle can i text you” deen yace okey ba damuwa”, rejecting call din yayi, kafin wani ya furta magana ƙarar shigowar saƙo Ya dakatar da su.


   Karanta sakon Deen ya soma yi duk sun ƙura mashi ido suna jiran jin me zaice masu, musamman pravin har wani zoƙa kai yake yi yana leƙen wayar Deen.


  Ɗagowa yai da alamun mamaki akan fuskarshi yace”tabɗijancan, wallahi dagaske macijin mutunne wai shaidanun aljanune a jikinshi, yanzu haka ya rikiɗa ya koma mutun acan gidanshi yake zaune,........” aruɗe suke kallon shi.


  “Wai ko kunsan Prime minister namu shine ya tura da jet din da zai ɗauko sheikh imam daga sudan saboda kawai ya taimaka ma macijin ya dawo halittarsa”?

Jin wannan maganar ba ƙaramin firgita senate lateef yayi ba ranshi a6ace ya furta”what? Bangane me kake nufi ba! Yaushe akayi hakan?batare da sanin mu ba!” a kausashe ya furta maganar,, a sukwane his excellency abdul Razak Ya miƙe Yana fadin”Anya ka karanta saƙon nan dai dai, bani wayar na duba, ya furta hakan tare da kar6ar wayar Deen Yana duba sakon, bayan ya gama yace”ba shakka, kuwa owais dinne ya rubuta da kanshi, magana ta tabbata prime minister namu shi ya tura da jet din daya dauko sheikh imam daga sudan don kawai a duba yaron, muna nan zaune muna jinyar ubanmu shi yana can wajen taimakon yaron da bamusan wanene shi ba, bamu haɗa alaƙar komai da shiba, bansan meke damun prime minister ba, daga shi har owais din shegen son taimakonsu shi zaija su jefa family dinmu cikin matsala ......” kafin Deen Ya ƙare magana senate lateef daya gama fusata yana huci yace”Wallahi basu isa ba, ni bani buƙatarma jin wani ƙarin bayani daga garesu, Yaron nan bazai zauna a estate dinmu ba, tunkafin aje ko’ina harya fara mallake zuciyar ɗan uwanmu hakan na nufin da wata manufa ya shigo family dinmu, zai iya yiyuwa wasu mugayen ne daga maƙiyan jam’iyarmu sukayi amfani da shi don su tarwatsa family dinmu, ku duba kuga fa duk gidajen dake a estate dinmu bai shiga kowanne ba, Ya tsallake nasu Ya faɗo gidan babanmu saboda shine target dinsa.....” a harzuƙe senate lateef Ya ƙare maganar.

  Kanwa uban Ƴan Zigi Pravin Ya haɗe girar ƙasa da sama yace”Ni dama tun Jiya hankalina bai kwanta da shigowar macijin nan ba, Ai daga jin yadda abun ya faru zaka shaida makircine aka shiryama baba, so suke kawai su kashe shi, in ba haka ba taya za’ai ace wai mutun ya koma maciji ai sai dai idan sihirine da shi, munafuki kawai wallahi bazamu yarda ba, Yaron nan bazai zauna mana a estate dinmu ba, dole ne owais Ya kore shi daga estate dinmu, sannan A yanke alaƙarshi da kowa na family dinmu idan ba haka ba zaija mana masifar da bazamu Iya shawo kanta ba” Rai a6ace pravin yayi maganar Yana kallon fuskokinsu.


   Jinjina kai kowan nan su yayi alamar gamsuwa da bayanin pravin,

  His excellency abdul razak Yace”Ai bazamu ta6a yin gangancin nan ba, mu jira owais din ya shigo anjima, shima hateem din Zanyi waya da shi”

  Pravin yace “yamakata atara kowa har shi kanshi yaya sharafuddeen din yazo yaji abun da owais ke shirin janyo mana a family, wallahi jiya Saratu batayi bacci ba, saboda fargabar macijin nan, sambatu ta dinga yi min tana kuka tana fadin gashi nan zai sareta, duk tabi ta haukace ta rikice min aɗaki, daƙyar nashawo kanta da ayar Allah”

Aruɗe Senate lateef yace”kunji ko? Tun yanzu ana kokarin ganin bayan ahlinmu”

 Damuwa ƙarara akan fuskar Deen yace”Pravin kana nufin saratu batayi bacci ba jiya saboda macijin”? Batare da ɗar ba yace”bata yi ba yaya, yadda taga rana haka taga dare, ni na zauna ina yi mata fifita saboda zufar dake tsastsafo mata gafa ac a daki amma haka ta dinga zubda gumi”

  Hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, gaba ɗaya sunyi amanna da maganar pravin

  Murya na rawa his excellency abdul razak Yace”Yanzu awani hali take ciki? Tayi bacci da safe?

 Girgiza kai pravin yai fuskarshi da alamun jimami yace”batayi ba idonta biyu ko abinci takasa ci,”

  “Inason ganinta pravin” acewar abdul razak”

   Pravin yace toh, bari naje nazo da ita ya juya jiki na 6ari ya fuce daga ɗakin.


 Yana fitowa daga dakin su ka yi kici6us da Hajjaty, ta ɗauki wankan bubu gown ta lace a jikinta, ta ca6a uban ado, ƙamshin turarenta ya buɗe ko’ina, mayafin rigar asaman kafaɗa ta daurashi, doguwar suman kanta ta zubo har gadon bayanta, Hannayenta biyu ruƙe da faffaɗan tray daga saman shi an ɗaura jerin kayan abinci.

 Wani mugun kallo da pravin ya watsa mata saida gabanta Ya faɗi, duk tabi tasha jinin jikinta, sarai tasan ya hanata    yin kwalliya idan har bashi zatayi mawa ba amma taƙi jin maganarshi.

  Sai faman ƙyafƙyafta idanuwanta take yi, tayi mashi kyau sai dai yaji haushin adon data ca6a.

  “Kin manta gargaɗin da nayi maki? Baki jin maganata ko”? muryarta na rawa ta furta”am sorry dear, na saba ne” guntun tsoki Yaja “yanzu ahaka zaki shiga dakin obie, bayan kinsan bashi kaɗai bane aɗakin, Balagaggun ƴa’ƴansa duk suna aciki, duk kamun kansu bazasu iya jure shaƙar ƙamshin turaren jikinki ba batare da kin jefa su yanayi ba, ko kallon ki su ka yi  sai sun ayyana wani abun aransu....” shiru tayi mashi ba tare da tace komai ba, numfasawa yayi kafin ya ɗaura da cewa”bazan bari ki shiga ɗakin ahaka ba, sai dai ki haƙura da kai masu abincin ki koma ɗaki ni sai in kai masu”


muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”dan Allah dear ka barni in kai masu, Jiya fa bansamu damar gaishe dasu ba”da shagwa6a tayi mashi maganar, nan take  kasala tafara kama shi, matsawa yayi dab da ita, ya ruƙo mayafinta data ɗaura kan kafaɗarta, ya janyoshi zuwa saman kanta ya lullu6e mata sumar kanta da kirjinta saboda yana jin kishin agane mashi majiyar dadin shi, ƙoƙarin manna mata kiss yayi saman red lips dinta, kamar daga sama yaji ance”Daddy!” A firgice pravin ya ɗago yana faman zazzare idanuwanshi Jin muryar zayn, su biyune hannayensu ruƙe cikin na juna shida Zaid, fuskokinsu da alamun ruɗani, kafin ƙarasowarsu pravin yayi saurin ɗaukar juice dake acikin jerin drinks din tray din hannun hajjaty ya buɗe murfin ya watsa mata ruwan lemun gefen galenta, baiwar Allah jikinta sai kerma yake yi, mugun tsoron Zayn take yi, tasan muddin ya gane abun da pravin ke ƙoƙarin yi mata sai ta yaba ma aya zaƙinta, ajiya juice din pravin yayi, ya dai daita natsuwarshi, ya nufesu fuskarshi dauke da murmushi ya ware masu hannayensu da niyar yayi hugginsu dinsu,

   Sai dai sunƙi bashi haɗin kai, wani irin matsiyacin kallon zayn yake watsama hajjaty data juya masu baya.


 Adabarbace pravin yace”kun ganmu atsaye ko? na fito daga ɗakin baba ne na bankaɗeta batare dana ankara ba” kallon tuhuma Zayn yayi mashi kafin yace”daddy mayafinta fa naga ka ruƙe a hannunka akan wani dalili” 

  “Baka ji mena ce ba, bugeta nayi har tray din hannunta ya girgiza lemu ya 6arar mata jikin gyalenta shine fa na ruko gyalen ina ƙoƙarin goge mata” yayi maganar tare da juyawa ya ruƙo bakin gyalen hajjaty yana nuna masu,

Ajiyar zuciya zayn ya sauke, zaid yace”daddy barka da safiya, ya gajiyar jiya” ya faɗa tare da yin huggin dinsa, pravin yadan bubbuga bayanshi”Alhamdulillah My son, Ina fata kun tashi lafiya, Yau ba zaku shiga office bane” cikin kulawa yayi maganar, hankalinshi na kan zayn, ya lura yafi ɗaukar zafi halinsa ɗaya dana jatumarsa wurin iya masifa.


  Ɗago da kai zaid yayi daga kan shoulder din daddyn nasu yace”mun tashi lafiya daddy, ba zamu je aiki yau ba sai zuwa next week, mun ɗauki hutu saboda zuwan Ƴan uwanmu” jinjina kai pravin yayi”hakan yayi, kunyi tunani,” ya faɗa still idonshi akan fuskar zayn daurewa yayi tare da ce mashi”Son ba magana? Ka tsareni da ido kana kallona ko akwai wani abune”

 Ta6e baki zayn yayi, kafin yace”bakomai, daddy ni me zance? Tun da ga zaid nan yana yi maka magana dani dashi duk abu ɗayane”

   Hajjaty tuni ta shige ɗakin Obie, batare da sun ankara ba.

   Dafa kafaɗar shi pravin yayi”kaima ina buƙatar yin magana dakai, bai kamata kana faɗamin haka ba, Ni mahaifinka ne yakamata kana tuna wannan” ya faɗa tare da janyoshi yayi huggin dinsa, zayn fa ji yake kamar ya haɗa jikinsa da allon bango, shifa sam mahaifinsu baya burgeshi baisan dalilin dayasa yake jin haka ba, kamar bashi ya haife shi ba” bayan sun raba jikinsu zayn yai ƙoƙarin furta”am sorry daddy, idan na 6ata maka rai,” murmushin gefen fuska pravin ya sakar mashi”kada ka damu, inayi maka uziri saboda har yanzu kallon ƙaramin yaro nake yi maka, akwai sauran kuruciya atattare dakai,” dan zaro ido zayn yayi”dady nine ƙarami”? Pravin yace ƙwarai kuwa, ko ka manta shekarunkane? Idan ka manta bari na tuna maka you’re just 2O something  years, wata’ƙil don kana ruƙe da muƙami a company shiyasa kake jin kanka wani babba”

 Dafe kai zayn yayi da hannunshi, arayuwarshi ya tsani ana fada mashi shekarunshi, haushi yake ji, zaid dai sai faman murmushi yake saki, yana jin dadin tsokanar da daddynsu yake yima  zayn.

  “Jiya a ina kuka kwana ne”? 

 “Muna agidan daddy deen, munyi fira tare dasu justice, shine yace mu tsaya ayi firar yaushe rabo” zaid ne yayi mashi bayani

 Pravin yace”naji dadin jin haka amma ya akai Justice ya tsaya yin fira da ƙannansa maimakon ya tuntu6i Zaki shi da yake sa’ansa” da biyu yayi maganar yana kallon zayn, haɗe girar sama da ƙasa yayi”daddy, zolayar ta isa haka, nima zan ƙara shekarunne nan bada jimawa ba” dariya zaid da pravin sukayi, bayan sun tsagaita da yin dariyar pravin yace”bakusan abun da ya faru jiya da dare a part din baba”


 A ruɗe suka furt”meya faru daddy”? Nan fa ya labarta masu kaf abunda ya faru tun daga shigowar macijin, da firgicin obinna, Hankalinsu yayi matuƙar tashi.


  “Daddy kana nufin mommy batayi bacci ba saboda macijin? Sannan baba shima bai runtsa ba? Kuma naji kace chief owais ne Ya kau da macijin yaushe yazo ƙasar? Taya akai macijin ya samu damar shigowa estate dinmu dake acike da tsaron sojoji da ƴan sanda”? Zayn ne ya kora jawabin.

 Pravin ya ta6e baki haɗi da cewa”macijin fa mutunne wai ya rikide, acewar shi owais....”tunkan ya ƙare maganar, zayn da zaid suka kalli juna da alamun al’ajabi.


  “Tayaya haka zai yiwu? Kamar dai ashirin film, ko atarihi ni ban ta6a jin mutun ya rikiɗa ya koma dabba ba” acewar zaid.


 Pravin yace”ai shine muma abunda ya ɗaure mana kai, ni dai nafi tunanin yaron aljanine ko kuma wasu miyagunne da suke son cutar da kakanku suka yi amfani da sihiri a jikin yaron donsu kashe shi”

  Hankalinsu zayn ba ƙaramin tashi yayi ba, jikinsu har tsuma yake yi,

  “Ku shiga daga ciki, ku duba jikin baban naku, Sauran uncles dinku suna a cikin dakin, idan kun shiga ku tayasu  jimamin abunda ya samu babanku, sannan please kada ku goyi bayan yaron yaci gaba da zama a estate din nan, tunda shi owais din bai san ciwon kanshi ba, idan ba haka ba taya zai ɗauko mugun abu ya ajiye agidan shi da sunan taimako”? Ranshi amatuƙar 6ace yayi maganar.


 Zayn daya gama harzuƙa yace”wallahi bazai yiwu ba daddy, wannan ai ba maganar da hankali zai ɗauka bace, in banda an rainawa mutane wayau taya za’ace wai mutun ya zama maciji? Kuma ya rasa inda zai farmaka sai gidan baban mu, bayan ga sauran gine ginen dane akusa dana shi owais din duk ya tsallakesu Ya nufo nan so ake kawai akashe mana shi, dama ya lafiyar giwa, ga mahaifiyarmu itama da firgici ta kwana bazan lamuntaba dole mu dauki mataki....” Yana huci ya ƙare maganar.


 Cikin sanyin murya zaid yace”Allah ne kadai yasan dai dai, kada mu yanke hukunci cikin fushi, bayan bamu da masaniya akan wanene yaron? Menene silar canza halittar shi, da son ranshi ko kuwa ƙaddarace ta afka mashi, duk waɗannan amsoshin zamu same su abakin Yayanmu owais tun da shi yasan komai dangane da yaron....”tunkan ya ƙare maganar, Pravin yai hanzarin katse shi da cewa”babu wata hujja da zamu jira zaid, ka duba kaga fa yadda ya siye zuciyar kawunku Hateem, meye alakarshi da yaron da har zai tura da jet din da zai dauko sheikh imam daga sudan, duk irin manyan malaman da muke dasu A nigeria, basuyi mashi ba sai da ya kashe makuɗan kudi don a dauko mashi sheikh, don baku agidan macijin ya kawo farmaki da baka furta maganar da kayi ba ayanzu, badan Allah yasa Owais Ya kau da macijin ba da tuni Ya sari kakanku saboda shi kadai yake kokarin kaima hari” jin wannan maganar yasa zaid shan jinin jikinshi

  “Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un, wannan wace irin masiface daddy? In sha Allah koma su wanene miyagun da ke son ganin bayanshi bazasu ta6a yin nasaraba, sannan Nima na goyi bayan a kori yaron daga estate dinmu” gyaɗa kai pravin yayi”yanzu naji magana my son”ya faɗa tare da dafa kafadar zaid din”ku shiga dakin baban, Ni yanzu zan je nataho da mahaifiyar taku”Amsa mashi sukayi da toh, kafin suka nifi ɗakin baba obie suka shiga da sallama abakunansu.


*HAJIYA SARATU❤*


Fitowa tayi daga bathroom, jikinta sanye cikin bathrobe fara ƙal, wanka ta samu tayi don taji daɗin jikinta, don tun da safe data farka bata motsa daga kan gadoba saboda fargabar abun da ya faru jiya da kuma damuwar da pravin Ya haddasa mata.

    Agaban mirror ta tsaya fuskarta babu walwala, idanuwanta sun ƙanƙance saboda rashin baccin da batayi ba a jiya, hatta kanta ciwo yake yi mata.

   Expensive body lotions dinta ta soma shafama skin dinta, bayan ta kammala ta nufi closet din kayanta, jim kaɗan ta dawo harta cire rigar wankan ta maida doguwar riga bubu ta material, turare ta dauka ta feshe jikinta da shi.

 Kafin ta kammala wayar ta dake ajiye kan pillow ta soma ringing, yamutsa fuska tayi kamar bazata ɗaga kiran ba, ta nufi wayar ta duba sunan me kiranta, ajiyar zuciya ta sauke kafin tayi picking call din

      Ko sallama batayi ba ta furta”daughter, sai yaushe zaki shigo gida”?

 On the other hand muryar faryat ta ratsa kunnanta


   “Mommy, tun jiya nayi niyar shigowa in kwana anan part dinku, Zulaihat ce ta ruƙe ni wai dole saina kwana a gidansu, mom madina ma tace in tsaya in kwanar masu shiyasa kika ji ni shiru kuma ma bani kaɗai bace, hada su Yusra duk muna agidan” 


 Ta6e baki hajiya saratu tayi”okey, duk lokacin da kika ga damar shigowa ina jiranki,” faryat ta amsa mata da toh, kafin sukayi sallama, Landline din kitchen ta danna ma kira, Bugu uku Abla tayi picking call din

  “Jira kuke yi sainace akawo min breakfast dina”? A faɗace tayi masu maganar

 Cikin girmamawa abla tace”Ina bada haƙuri aunty, Yanzu nan zan shirya maki” guntun tsoki taja tare da katse kiran ta wurga wayar kan mattress.


  Bakomai take tariyowa ba face Rashin mutuncin da pravin yayi mata, Ya ƙona mata rai adaren jiyan nan, wai har ita zata kirashi yaƙi zuwa sannan yayi rejecting call dinta? bata motsa daga gaban mirror din ba, ƙarar knocking din ƙofa Ya katse mata zancen zucin nata

  Sai da ta mula tasha iska tukunna ta furta”Come in” muryar abla da ƙarfi ta furta”Aunty ƙofar a kulle take” tunawa tayi da ta datse dakin jiya ta ciki, juyawa tayi taje ta buɗe ƙofar, shigowa abla tayi hannayenta biyu ruƙe da wooden tray daga saman shi kayan breakfast ne.


  Wuce wa ciki abla tayi, ta daura tray din kan table, Kafin ta juya tana fuskantar hajiya saratu data ruƙe qugu da hannu ɗaya, har saida taji gabanta ya faɗi ganin 6acin ran dake kwance akan fuskarta, cike da jin shakkarta ta furta”ko akwai wani abu da kike buƙata”? Atsiwace hajiya saratu tace”ke nake buƙatar ki fuce min daga ɗaki, kin wani tsareni da ido kina kallona kamar yau kika fara gani na” Jiki na 6ari Abla ta nufi ƙofar fita daga ɗakin bayan ta fuce hajiya saratu ta nufi gefen gadon ta zauna, ta soma cin breakfast dinta, farawa da bismillah kakkauran tea ta ɗauka ta kur6eshi dukanshi, kafin ta rarumi roasted chicken takai baki tana cizgarta atsiyace, daɗina da hajiya saratu damuwa bata hanata cin abincin, adai dai lokacin da ta ɗauki burger da hannu biyu ta gutsireta da baki, Muryar pravin ta dakatar da ita daka taunar burger din da takeyi, lokaci guda yanayin fuskarta ya canza ta haɗe rai kamar baƙin haɗari.


  shigowa ɗakin yayi fuskarshi ɗauke da murmushi, yasan tsiyar daya tsula mata shiyasa yake jin shakkar tunkararta

  Daga nesa da ita ya tsaya haɗi da goya hannayenshi on his chest cikin muryar lallashi ya furta”My wife, ina neman afwarki, dan Allah ki yafe min nasan ban kyauta maki ba, duk da ba laifina bane, laifin ki ne saboda kece kikaja nayi maki hakan, kin nuna bani da mahimmanci awurinki...” kau da idonta tayi daga kallon fuskarshi, taci gaba da cin burger dinta ta share shi kamar batasan da zaman shi ba.


  “Dan Allah kiyi min magana sanyin idaniyata, kamar yadda na 6ata maki rai nima haka raina ya 6aci, saboda tunanin awani hali kika kwana jiya ko runtsawa banyi ba, nayi kewar rashinki atare dani, da pillow na kwana rungume a kirjina ina jin tamkar kece na rungume” 


fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa yayi mata maganar, duk don ya samu ta yafe mashi, burinshi ta aminta dashi su sasanta tsakanin su, duk don ya tunzurata akan maganar macijin daya tsoratar da ita jiya, yasan muddin saratu ta ƙyamaci zaman yaron a estate dinsu dole kowa ya amince saboda ƙaunar da yayyanta su ke yi mata.


 “Bugun zuciyata, please ki kula ni mana, bana son sharenin da kike yi, wallahi ashirye nake dana kar6i duk wani horo da zaki bani ni kawai so nake mu sasanta tsakaninmu bana so kina fushi dashi” ƙara ɗaure mashi fuska tayi batare data juya ta dube shi ba.

  Zuƙunna pravin yayi, tare da kama kunnansa Ya soma yin tsallan kwaɗi Yana nufar gaban table dinta Yana fadin”Am sorry my wife, nagane kuskurena bazan ƙara ba”

  Tunkafin Ya ƙaraso gabanta, ta tsiyaya ruwan lemu acikin cup mai sanyi, ta ruƙe a hannunta, Yana zuwa dab da table din ta daddage ta watsa mashi ruwan lemun saman fuskarshi, da sauri ya runtse idanuwanshi jin raɗaɗin da ya shigar mashi, burger ta ɗauka ta yunƙura ta kifa mashi ita a fuskarshi, tunda tayi mashi hakan sai taji sauƙi acikin ranta, komawa tayi ta zauna tana dubanshi tace”Ina fata ka tashi lafiya” shiru pravin bai furta komai ba, ƙoƙarin buɗe idanuwanshi yake yi sai dai ya kasa, shu’umin murmushi hajiya saratu tasakar mashi tare da cewa”malam, ka tashi ka shiga toilet ka wanke fuskarka,” babu musu pravin ya miƙe kamar makaho Yana laluban hanya daƙyar ya gano ƙofar toilet......”

    *✊💋ALHAMDULILLAH, END OF MIDDLE STEP, FATA NA SHINE ALLAH YA BANI IKON KAMMALA TAKUN ƘARSHE LAFIYA KAMAR YADDA NA KAMMALA TAKUN FARKO DA TAKUN TSAKITA💋✊*

(Domin neman ƙarin bayani a tuntu6i layukan mu (08103884440 0r 08169856268)

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post