Hamratul Yazeeda Page 1 by Alkamawa

Hamratul Yazeeda Page 1 by Alkamawa

Novels to read

*HAMRATU'L YAZEEDA** 

           Na

 *NUSAIBA ALKAMAWA* 

      ( *AUNTY NUSY* )

 *PART* 1

 *TSOKACI!!* 

_________________________

Littafi mai cike da abubuwan ban mamaki  faɗakarwa nishaɗantarwa.

No 07036162215

Bismillah rahmanir rahim 

________________________"HAMRA'U!! HAMRA'U!!

Dattijuwar matar take kwala mata kira tana kallon kofar ɗakin da HAMRA'U take ciki, da sauri yarinyar ta fito tana karasowa kusa da matar tana turo baki gaba irin na shagwababbun yaran nan.


     "Inna wai kiran mai kike ta kwala min ne tun dazu?"


   "Dama so nake kije tuƙa_tuƙa  ki debo mana ruwa, Kinga babu ko na ɗora sanwa wanda kike debo ɗazu ya kare."


   Bubbuga ƙafa ta fara yi cike da sakalci tana matsar kwalla.


    "Haba Inna ɗazu fa na ɗebo ruwan nan yanzu kuma kice harya ƙare, Kuma ni yanzu wallahi na gaji." Ta karasa maganar tana son fashewa da kuka.


     Tafa hannuwa Inna ta fara yi tana kallon ta. "Sallallahu-alaihiwa sallam. Yanzu Hamra'u idan baki ɗebo mana ruwan nan ba da mai kikeso na Dora abinci?

 To gwamma ma kizo ki ɗebo mana tun wuri tunda dai ba zamu zauna da yunwa ba, kuma kinfi kowa fara cewa yunwa kike ji."


     Bokitin ta dauka tana gyara ɗamaran da tayi tana fadin. "Inna Dan dai kin matsa ne wallahi Amma na gaji kuma bana son in zauna da yunwa."


     "Yawwa 'yar Albarka kiyi maza ki dawo Amma don Allah kada ki janyo min magana babu ruwanki da kowa."


   Turo d'an mitsitsin bakinta tayi gaba, rai a bace ta fara magana. "To ai sune suke takalata da faɗa, idan basu takaleni ba babu ruwana dasu, Amma idan yarinya ta kawo min rainin hankali dole ne na lakaɗa mata na jaki idan ma na kyaleta ai sai nayi zazzabi."


    "Naji ni dai maza jeki ki dawo."


  Bata sake magana ba tasa kai ta fice daga giɗan tana wulla bokitin dake hannunta, tana fitowa maimakon ta wuce tuƙa_tuƙa ta debo ruwan kawai sai ta wuce gidan su Haule, tun daga zaure take rangaɗa sallama harta shiga cikin gidan.


_______ Goggo ta gani zaune tana tankaɗen gari, kamar abin arziki tace.


   "Goggo Ina wuni?" Washe jajayan haƙoranta tayi tana fadin. 


   "Lahiya lau Hamra'u, yasu Innar taki?"


"Tana nan lahiya, wai Goggo Haule tana nan kuwa?"


    "Wallahi Kinga bata nan tun dazu na aiketa nasan yanzu haka tana kan hanyar dawo..." Bata karasa rufe Baki ba sukaji sallamar ta.


" washe Baki Hamra'u tayi.


   "ƴar halak kinki ambato yanzun nan muke zanchan ki, sai gashi kin shigo."


   "Wallahi kuwa, dama nasan zakizo naimana shi ya sa nake ta sauri."

 Ta karasa maganar tana ajjiye iccen dake kanta, ta ɗauki bokitinta itama suka yi wa Goggo sallama suka ɗauki hanyar zuwa rafi. Suna tafe suna 'yan tsalle-tsallen su tana hira har suka iso wajan Hadi mai rake, da hannu Hamra'u ta yafito Haule tana fad'in.


   "Ni fa gaskiya sha'awar rake nakeyi, Kuma gashi banda kud'i."


  "To ai wannan ba matsala bane ba, muje kawai mu karɓi bashi idan muka samu kudin sai mu biyasa, dama yana binmu bashin wanchan karon da muka karɓa."


"    Dariya Hamra'u tayi sosai saida tayi mai isarta sannan tace. "Daɗina dake kin iya Bada shawara mai ma'ana." Suna zuwa wajan sa suka gaishe sa cike da ladabi kamar mutanen kirki.

   

   "Rake za'a bamu na Dari."

    "Tom Hamra'un inna."


  Leda ya dauko ya zuba musu da yawa harda gyara ya mika musu, karba suka yi cike da Murna suna shirin juyawa ba tare da sun basa kudin ba. 


"Saurin Shan gaban su Hadi yayi Yana bata rai Hadi merake yayi saurin matsawa gabansu yace "yakuma zaku tafi baku bani kudina ba daman INA binku kudin rannan ,haule ce tayi charab tace mufa daman bashi mukaxo karɓa, kabari lokacin da mukayi kudi xamu baka kudinka,tafada tana harararsa,alqur'an yau bazan yarda ba saikun ban kudina billahill azim Baku isa ba,kallon juna sukayi sukayi mgn ta ido gani yayi suna JA baya,saida suka jingina da teburin raken, ai hadi me rake bai ankaraba yaga rakenshi akasa sunzubarmai sunkara diban wasu raken sunfalfala aguje,shima baiyi wata _wata ba yatake musu baya suna gudu yana binsu suna zuwa hanyar dazasu rabu kowa yayi hanyar gidansu.


", ,shikuma hadi bin bayan Hamra'u yayi burmawa gidansu tayi aguje yarda bokitin tayi Allah yasa bokitin karfene da yafashe, fad'awa daki tayi tasaka sakata,inna tana bandaki saijin karar kofa taji gamm anbuga kofa, saurin fitowa tayi taga hadi atsaye sai haki yake yana hura hanci alaman yasha gudu.


",hadi meya kawoka gidana harda shigowa saikace wanda akama babban sata ka,biyo 'barawo? Hadi cikin hura hanci tare da nishin wahalar gudu yace alqur'an yau sai anbani kudin rakena bazan yarda ba kullum sai sunxo sunkarbi bashin rakena yauma tazo takarba yaudai bazan hakura ba abani kudina.______Sallallahu alaihiwa sallam yanzu hadi akan kudin rake shine zaka shigomin har cikin gida,toma nawane kudin raken naka dakake gudu akanshi?


" cikin hura hanci irin ankaishi bango yace nad'ari suka siya rannan ma sunsai nadari kinga 'Dari biyu kenan, 

Da ita da kawarta haule 'yar gidan malam tanimu.


" Rike da haɓa inna tace yanzu hadi akan nera d'ari biyun kashi gomin gidana kai tsaye saikace ba musulmi ba.Lekowa HAMRA'U tayi tace wllh inna karya yakeyi d'ari da hamsin ne kudinsa  ni karma kibashi kudin munsha abanza,tafaɗa tana me kifkifta ido.


"kinga HAMRA'U kiyi shiru Dan wannan Ɗan banzan yaron sai yazo yaɓalla kofarnan yadukan minke abanza dankuwa wllh yasake yatabaminke wllh sai munje gaban megari yamana tsakani mudashi,tanayi tana kunce zaninta taciro wani yamushashshiyar d'ari biyu tamiƙamai, fizgar kudin yayi , wllh inka yaga bazan baka wani kudin ba cewar inna, shidai fita yayi yace yadaifi muku sauki da kuka bani kudina.


________ yana fita HAMRA'U tafito, inna ta kalleta tace watakam Hamra'u bazaki daina tsokanar hadi me rake ba ko?"cikin turo baki tace,nifa ba tsokanarshi nayiba

Ai yanzu saiki nemo yaro yad'ebo mana ruwan,tunda ke indai kika fita bazasu barminke ba sai sunsaki agaba suna takuramin ke kamar kekad'aice ƴa mace akauyannan,nidai naga alama duk mutanan kauyennan basa sonki, yanzu jeki nemomin yaro koda kanin haulene yazo yad'ebomin ruwan.'To' inna fita tayi tanufi gidansu haule sallama tayi haulece tafito daga d'aki suna had'a ido suka tuntsire da dariya,harsuna dukawa tsabar dariya saida sukayi iya yinsu sannan suka lafa da dariyar ,haule  tace ke kinga Dana shigo da gudu gidannan daman goggo tana zaune atsakar gida, INA shigowa da gudu ai kawai ganin goggo nayi ta Burma d'aki nida aka biyo amma ita tarigani shiga daki,hartana rigani saka sakata.


________ tunda haule take bawa hamra'u lbr take dariya hartana rike ciki.goggo ce tafito daga d'aki sai haki take kamar Wanda tayi gasar tsere ,gawajan goshinta akumɓure  gashi tahada zufa, 

Suna kallonta suka kwashe da dariya, wai nikuwa haule me akai kike wannan  gudun? Hmmm ai goggo hadi merake

ne yabiyomu wllh shine fa mukai wannan gudun,salati goggo tafarayi,aini

Nazata wani katon zakine yabiyoku,

gashi kunsani nabige goshina cewar goggo,amma gskia yarannan kun iya rashin mutunci,Allah dai yashirya munku.


______ yauwa goggo sule yana nan yad'ebo mana ruwa mudora girki Hamra'u takatse goggo "wllh sule bayanan yatafi makarantar allo amma bara nasan muku nawa tunda ni inadashi,sai kusamu kuɗora girkin,bokiti tadebo ta d'ibanmata gashi kikai mata tajuye kidawomin da bokitin,

*to goggo mungode* fita tayi tanufi gidansu tana shiga tace inna ga ruwan goggon haule tabaki ,karba inna tayi tace aikuwa nagode juye ruwan tayi tamika mata fita tayi tana shiga gidan 

Tamikawa goggo bokitin,haule zomuje gidansu abuwa,mikewa haule tayi da sauri dayake itama akwai sanyawo dama zanice tatarar da mujemu.
Fitowa sukai suka nufi gidansu abuwa suna tafe suna hirarsu irinta kawaye 

Suna cikin tafiyane suka hadu da wani yaro yanasai da gyad'a kiransa sukayi yaro yazo da saurinsa yana murna za amai ciniki,tambayarsa sukayi nawa nawane gyad'an da murnanshi yace musu ishirin_ ishirin,d'aukan d'aid'ai sukayi sukace bara suji da dadi gyad'an nashi indai babu dadi bazasu siyaba shidai yaro tunda yaji haka jikinshi yayi sanyi,saida suka cinye gyad'an tsaf tukunna sukace gaskia gyad'an nan batai dadi bazasu siya ba tayi wani bauri gashi kuma ta kone da yawa ɗaci ma.


******

  ammafa azahirin gskia yayi musu dadi amma dayake sunsan basuda kudi shiyasa sukace mai haka.


" take yaro yafara kuka yana cewa shifa sai anbashi kudin gyad'an shi rike rigar haule yayi yana kuka,hankad'eshi tayi yafadi kasa sukuma sukayi tafiyarsu suna shiga gidansu abuwa sukaga ummansu abuwa azaune tana tsince shinkafa,gaidata sukayi ta amsa fuska babu yabo babu fallasa SBD ita batason mu'amalarsu da su Hamra'u SBD yaran basajin mgn duk sun addabi gari.


",umma abuwa tananan kuwa haule takatse mata tunani daure fuska takarayi na'aiketa tabasu amsa atakaice, fita sukayi daga gidan ahanya suke gulmar umman abuwa haule take cewa nifa naga duk lokacin da mukazo gidansu abuwa sai taita daure mana fuska, Hamra'u  tace, hmm  kyaleta darajar abuwa kawai takeci amma wllh da saimun Nuna mata asalin halinmu.________Suna cikin maganar ne suka hango tahowar abuwa shiru sukayi da zanchan tana karasowa suka gaisa Hamra'u tace yanzunnan mukaje gidanku akace bakyanan .


Wllh ummace ta aikeni daman fada miki zamuyi Dan anjima zamuje dandali .


"To" Allah yakaimu sai anjima zanbiyo ta gidansu haule sai muzo gidan Ku.


" to shikenan sai mun haɗu,tafiya tayi gidansu suma kowa Yakama hanyar gidans

 *HAMRAT* 


________Kiran sallar da ake ne yasa hamrat dakatawa dayin rubutu SBD muhimmancin sallah inba lalura ba batason rashin ƙinyin sallah akan lokaci,bata haɗa sallah da komai kome take ,domin kuwa sai sallarka tayi kyau sannann aikin ka zaiyi kyau kafin a fara duba aikin ka sai anfara duba sallahr ka Allah yasa mudace.rufe littafin tayi tasaka a drowerta ta garƙame da wasu key me madannai .

Azuwan idan ta idar zatazo ta ƙarasa labarin iya inda take so yau ta tsaya.

Daga taskar NUSAIBA ALKAMAWA ✍️

Comments and share fisabilillah

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post