*Something Is About to Happen*
_______________________________🌹✍️
jikin shi da kasala Ya juyo Yana duban Benazir dake tunkaro shi ga dukkan alamu bata ga Zeenatu ba.
"Yayana nakaina, me kake yi anan"? Tana murmushi tayi mashi maganar
Sam ya kasa buɗe baki Ya bata amsa, sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi.
"Lafiya? Ya akai naga idanunka sun yi ja"? Aruɗe ta jefa mashi tambayar tana duban shi.
Shafa sumar kanshi yai da hannu ɗaya kafin ya furta"bakomai, Yanzu na tashi daga bacci,"
"Amma dai daga gani baccin bai isheka ba, cos gaba ɗaya kamar ma baka a hayyacinka"
Ƙaƙaro murmushi yayi akan fuskarshi batare dayace mata komai ba.
"Yayana, Maganar zuwa gidan su Aneeleeh ne Ya kawo ni, wallahi duk na damu da rashin samun layin Abie din su, har number dinsa na kar6a awurin daddy na jaraba kiran layin da wayar mom amma shiru ba'a ɗagawa" muryarta tamkar zata fashe da kuka tayi maganar.
"Bana so mubar abuja batare da mun je gidan su ba"
"In sha Allah zamu je, Zanyi maki ƙoƙarin hakan, abun da yakamata mu yi shine mu tura mashi da text message, may be layin nashi baya akan waya duk ranar da ya sanya shi zai ga sakon mu ne"
"Hakane, tun da akwai layin awayarka ka tura mashi da sakon"
Ba tare da 6ata lokaci ba, Dr. Shureim Ya zaro wayarshi, ya soma daddanata
"Me zan rubuta mashi"? Ya tambaya yana kallonta.
"Ka faɗa mashi Benazir ce Ƙawar Aneelerh, Matar Tajuddeen" Ya furta Okey, bayan ya gama rubutu text din Ya turama masa, Kafin daga bisani ya ɗago da ido, Ganin takura mashi ido yasa shi yi mata gyaran murya"lafiya kike kallona"? murmushi tasaki tare da fadin"yayana fada min gaskiya, meya jefa ka cikin yanayin nan" ta fada tana ɗage mashi gira, nan take ya fahimci jikin shi ya nuna halin da yake aciki, shafa kirjin shi yai da hannu tamkar zai gyara ma6allin gaban jallabiyarsa Duk yabi ya dabarbace wata irin kunya ce ta kama shi.
"ina Zeenatu"? Ta jefa mashi tambayar tana bin shi da kallon ƙurulla.
Galla mata harara yayi"Bansani ba, Ƴar sa Ido, Kije dakinta ki neme ta, wato dai bazaki canza halinki ba, Har yanzu kina nan da rashin jin maganarki, ' kafin ta kara furta mashi magana yayi saurin wuce ta Ya nufi bedroom dinshi, Yana shiga ya jefar da wayarshi kan gado da wata irin kasala Ya faɗa saman gadon Yana fuskantar ceilling, wani irin yanayi yake jin kanshi mara misaltuwa.
Lumshe idanunshi yayi yayin da acan cikin zuciyarshi yake tariyo wani abu daya ta6a faruwa arayuwarshi
Har abada bazai ta6a mantawa da wannan daren ba, wanda yake yi mashi laƙabi da DESTINED NIGHT, abun da ya faru a daren Ya tsaya mashi aranshi Ya kafa tarihin da har abada bazai ta6a gogewa aranshi ba.
Ƙoƙarin canza akalar tunanin nashi yayi gudun kada ya fama raunin dake a zuciyarshi.
Sunan Allah yaci gaba da ambato har saida yaji zuciyarshi tayi mashi sanyi tukunna Ya samu damar miƙewa Ya nufi toilet don Ya tsarkake jikin shi.
__________________Boss Bature
A hankali dankareriyar Motarsu Ta kunno kai ta cikin Katafaren Gate din shiga gidan dake a tsare da Security Officers, motace Yar Ubansu mai numfashi tsadaddiyar Gaske, Su biyune a back seat Na motar, Alhaji musa dake a hakimce Ya kishingiɗa saman seat din ta motar, Wankan boyal ne a jikin shi launin milk sun zauna mashi, daga gefen shi Alhaji Ubaid ne Cikin shiga ta shadda fara, dawowarsu kenan daga taron da suka halarta wanda akayi a head quarter na party din su.
Tun kafin Security guard din dake driving dinsu yayi parking, idanun Alhaji musa masu dauke da bacci suka hango mashi Hajiya sarah da layla dake a gaban Swimming pool suna fira, ta cikin window din motar Yake dubansu, Ranshi yayi mugun 6aci, dama fuskar babu annuri ko miskala zarratin.
Bayan motar tasu tayi parking a harabar Ajiye motocinsu, Bai jira Security guard din Ya buɗe mashi mota ba, da kanshi Ya buɗe murfin Ya fito Yana faman haɗe rai, fitowa daga cikin motar Alhaji Ubaid Yai, idanunsa akan Musa yace"wai meke damunka ne? Tun dazu da muka fita taron jam'iya babu annuri akan fuskarka, mutane sai rububinka sukeyi amma kai ko kaɗan basu agaban ka, Ka haɗe rai kamar wanda aka aiko ma sakon mutuwarsa... " kafin Alhaji Ubaid Ya ƙare maganar, Alhaji musa Ya ɗaga mashi hannu babu mutunci Ya furta"Ya isa haka! Bana son jin maganar nan," da sauri Alhaji ubaid Yaja baki yayi shiru, Cikin Takun Isa da izza Alhaji musa Ya haura ƙafa Ya nufi Cikin gidan.
Hajiya Layla dake hangen su Alhaji ubaid tun da suka fito daga mota, da zolaya tace ma mom sarah"Matar so Ga mijin So can Ya dawo, Naga kamar ranshi a6ace Yake yakamata kije ki lallashe shi"
sai data furta maganar Hankalin Sarah Ya kakarta akan su, A lokacin Har Alhaji musa Ya shige Ciki, miƙewa tayi da sauri tana fadin"Nasan bai wuci gajiya bace ta dameshi, dama da safe kafin ya fita Ya faɗa min baya jin dadin jikin shi, " tana ƙare fadan hakan Tabi bayan Alhaji musa.
Bayan tafiyarta, Hajiya layla bata motsa daga inda take a zaune ba, Alhaji ubaid take Jira Ya ƙaraso inda take ganin Yana tunkarota sai faman sakar mata murmushi Yake Yi, Ita ko ta haɗe mashi fuska, don ba ƙaramin haushin shi take ji ba tunda yaƙi amincewa da zancen Komawarsu Joss.
Kujerarar dake fuskantarta Yaja ya zauna.
Fuskarshi da fara'a yace"uwargida ran gida, fatan na sameki Lafiya"
Banza tayi da shi batace komai ba, sai ma cup da ta dauka tana shan sauran coffee dinta
"Layla kina ji ina magana kinyi banza kin ƙyaleni, Ko sannu da dawowa babu"
Ta6e baki tayi tare da hararar shi tace"hmmmm, me kakeso nace"? Shiru yayi baice mata komai ba, sai dai binta da idanu da yakeyi.
"Ka bani mamaki, nayi tunanin mijina Namiji ne, ashe ba haka bane nayi kuskure, Ka nuna min kai ba komai bane wai ƙaninka shike juya ka son ranshi, baka jin maganar kowa In ba ta shi ba, kamar wani ubanka" rai a6ace tayi maganar.
Tuni yanayin fuskar Alhaji ubaid ya canza zuwa matsananciyar damuwa, baya son mitar da Hajiya layla take yi mashi kullum haka ya ke fama da ita.
"Layla bai kamata Kina gaya min magana ba, Har yanzu ni mijinki ne matsayina agareki bazai ta6a canzawa ba... "
Murmushin takaici tasaki tana dubanshi tace"Ubaid! Duk abunda na faɗa maka Kaine kaja, wallahi ka 6ata min rai, bana jin daɗin ƙasƙantar damu da ka ke yi awurin musa, baya ganin girman kowa daga kai har ni, burinshi mu zama tamkar bayinshi shi kuma uban gidan mu, na rasa gane da wani yare zanyi maka magana yadda zaka fahimce ni...." muryarta na rawa ta ƙare maganar, hawaye tuni sun cicciko idanunta.
Girgiza kai yai cikin sanyin murya yace"bani da amsar da zan baki, duk abunda kika faɗi gaskiya ne layla, bawai bana fahimtar ki bane, sai dai bani da yadda zaniyi, yakamata kiyi min uziri, Ni ina girmama musa ne saboda halaccin shi agareni, yayi min abubuwa da dama waɗanda bazan ta6a mantawa ba, duk wani cigaba da kika ga na samu arayuwata musa shine sila....." kasa ƙarasa maganar yayi sakamakon dariyar da layla ta saki tamkar wata zararra, jikinta har jijjiga yake yi.
da mamaki akan fuskarshi yace"meyasa kike min dariya? Kin maidani mahaukaci ko"?
Tsagaitawa tayi da yin dariyar ta soma yin magana.
"Mijina Ina tausayin rayuwarka, Sannan Ina jiye maka ranar da zaka yi danasanin yarda da kayi da ƙaninka musa, saboda ya riga daya gama dakai! tarkon daya ɗana maka Yayi tasiri a zuciyarka, Wai kai baka amfani da ƙwaƙwalwarka ne? Idan har don Allah yake kyautata maka meyasa baya yi maka biyayya amatsayin shi na ƙaninka"!? A faɗace tayi maganar, Alhaji ubaid Yayi shiru Yana sauraronta, kalamanta sun yi mashi tsauri suna neman ruguza mashi lissafin ƙwalwarsa.
"Kasan ni bana 6oye ta cikina! Idan abu yana damuna kai tsaye nake faɗi ma mutun koda kuwa bazata yi mashi daɗi ba" Ta faɗa tana mai ƙara jaddada kalamanta.
"Yakamata ka farka daga baccin da ka ke yi, tunkafin lokaci Ya ƙure maka, Ni dai zan faɗamaka gaskiya koda kuwa zaka ji haushina ne, Alhaji musa ƙaninka ba ƙaunarka yake yi ba dakai da iyalanka, Baya sonmu ba don Allah Yake kyautata mana ba face sai don saboda wata manufa tashi, na faɗa maka hakanne bawai don ina zargin shi da wani abu ba, sai don saboda babu gaskiya a lamarin shi!"
A zafafe Ta ƙarasa maganar, tare da kai hannu ta daki gaban table din, Bata jira amsar da zai bata ba tayi saurin miƙewa zuciyarta na tafarfasa ta nufi cikin gidan ta shige.
Gaba ɗaya Alhaji Ubaid Ya rasa meke yi mashi daɗi a duniyar nan, Har cikin ranshi bayason 6acin ran layla, A cikin ƴan kwanakin nan kusan kullum sai sun samu sa6ani da ita saboda Alhaji musa, baisan ya zai yi da ita ba, a ganin shi itace ta tsani Alhaji musa shiyasa take neman 6ata mashi suna a wurinshi duk don su bar gidansa.
Ya jima zaune kan kujera Hannin shi ɗaya dafe da kanshi sai daga bisani Ya miƙe Ya nufi cikin gidan.
*ALHAJI MUSA💪*
Bayan shigarshi bedroom dinsa, rage kayan Jikin shi yayi, ya rage saura farar shirt da short, Sai faman Cika ya ke yi yana batsewa, zuciyarshi Ta kai maƙura awurin 6aci.
Hajiya sarah tana ƙoƙarin shigowa bedroom din nashi, ba zato ba tsammani taji Ya furta"Kada ki kuskura ki shigo min nan!" Ras taji gabanta Ya faɗi, abakin kofar ta tsaya tana dubanshi Yana daga tsaye Ya dafe sofa din dakin da hannayenshi.
"Meyasa zaka hanani shigowa"? Cikin kwantar da murya tayi mashi maganar
Tamkar bazai tanka mata ba yace"zonan"! Kamar wata ƙaramar yarinya haka ya kirata, bayan ta shiga dakin daga gaban sofa din ta tsaya tana kallon shi.
Zagayowa yayi ta gabanta, ya sassauta fushin fuskarshi.
"Meya hana ki zuwa wurin Aiki yau"?
Cike da jin shakkar shi tace "Namanta ne ban faɗa maka ba, Jiya na ɗauki hutu saboda Hajiya layla inaso muna samun lokacin da zamu dinga zama muna fira harma mu dinga fita" daƙyar ta ƙare maganar ganin irin kallon da yake jefa mata, tuni tasha jinin jikinta.
"Saboda ita kawai kika ɗauki hutun aiki? Kin fara shaye shaye ne"? A ruɗe take kallon
"Kin ci sa'a bani da ɗabi'ar ta6a lafiyar mace, da kuwa yau saikin yaba ma aya zaƙinta, " mamakin maganarshi ne yasa ta zaro idanunta waje har saida ta maimaita kalmar sai kin yaba ma aya zakinta.
Adabarbace ta furta"bangane me kake nufi ba"?
"Bani da lokacin Yi maki bayani, amma Inaso in ja maki kunne akan matar can, bana son ganin kina sakar mata jiki kuna yin fira, wannan umarni ne daga gare ni, ban amince ki rinka ke6ance kanki da ita ba"!
ɗaure mashi fuska hajiya Sarah tayi"akan me zaka hana ni yin fira da ita? Haramunne yin hakan? Ko tayi maka laifi ne? Ina buƙatar hujja.
Da kakkausar Murya Ya furta"Umarni nake baki ba shawara ba, ki koma aiki gobe sannan kada in ƙara ganin kin ke6ance da ita" Ya faɗa yana furzar da huci ta hancin sa.
Ta fahimci bayason hajiya layla, ta daɗe da sanin rashin jituwarsu sai dai batayi tsammanin abun yakai haka ba.
Ƙwara tabi Umarnin shi ta zauna lafiya idan ba haka ba, Ita zata jama kanta"
Yana ƙoƙarin juyawa tayi saurin ruƙo hannun shi acikin nata, kallo ya jefa mata mai kama da harara.
"Ka yi hakuri idan ranka ya 6aci, in sha Allah zanyi maka biyayya bazan ƙara zama yin fira da ita ba"
Lumshe idanunshi yayi kafin ya buɗe su Ahankali Ya furta"me kuke tattaunawa ne da ita"?
Tayi mamakin tambayar daya jefa mata, saboda tasan halin shi, mutunne da bai Iya shiga shirgin mutane ba, idan yana zaune a wuri baka isa ka yi mashi gulmar wani ba, amma sai gashi yau yana neman ta fada mashi abun da suke tattaunawa da Hajiya Layla.
Bayan ta kammala faɗa mashi calmly ya furta"bansan meyasa ta sanya min ido ba, bata son ganina kamar na kashe mata wani"
Matsawa Sarah tayi dab da shi ta ɗaura hannayenta saman fadadan kafaɗunsa
"Kada hakan ya dame ka, ni dai shawarar da zan baka, dan Allah ka basu damar da zasu koma Joss, saboda ta nuna batason zama a gidan nan" ta faɗa tana mai tausasa kalamanta.
Jinjina kanshi yayi"zanyi tunani akan hakan,"
Ya faɗa tare da juyawa Ya nufi Katafaren gadonsa, Ya haye ya kwanta idanunsa suna fuskantar ceilling.
Duk sai taji ba daɗi, ganin yanayin shi da damuwa akan fuskarshi, tasan bai wuci ƙiyayyar da hajiya layla take nuna mashi bace tasa shi shiga yanayin.
"Babe, kana buƙatar wani abu ne In kawo maka"?
Batare daya kalleta ba Ya furta"Bana buƙatar komai, ki zo ki kwanta a gefe na" taji dadin maganar daya furta mata da sauri ta nufi gadon tare da hayewa ta zauna kan mattress din, sai da tafara zage zip din rigarta, ta cireta kafin ta kwanta saman kirjin shi, ya ruƙo waist dinta da hannun shi ɗaya, ɗagowa tayi da blue eyes dinta tana kallon sajan fuskarshi.
"Bana gajiya dakai, banƙi mu kasance har Iya ƙarshen rayuwarmu atare da kai ba, Idanunsa dake a lumshe yaɗan buɗe su A hankali yana duban fuskarta ba tare daya ware su ba.
Sumbatar cheek dinsa tayi, tamkar zaiyi murmushi sai dai bai bari Ya bayyana ba, ta fahimci yaji dadin abunda tayi masa, kallon juna suka cigaba da yi, tunawa tayi da layin dake akan wayar Zeenatu, har ta buɗe baki zata fada mashi kiran da akayi da bakuwar mumber da sauri ya ɗaura mata yatsa sama lips dinta.
"Ina buƙatar hutu!" murmushi tasakar mashi, tare da rungumo shi suka ƙanƙame juna, cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awon gaba da shi.
Idan muka koma 6angaren Zeenatu tun da ta watsa da gudu ta nufi bedroom dinta, tana shiga ta haye saman gado ta kwanta tare da rungumo pillow a ƙirjinta, fuskarta ɗauke da murmushi, wani irin so da ƙaunar yaya shureim take ji, taso ace Benazir bata katse mashi hanzarin shi ba, da yau ta kar6i first kiss dinta a wurin hubbinta, wani irin nishaɗi take ji kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, sai faman juyi take yi a tsakiyar gadon kamar me fama da ciwon ciki.
Jefar da pillown hannun tayi tare da saukowa daga kan gadon ta shiga toilet, after some mins ta fito fuskarta da alamun lemar ruwa ta nufi glass wardrobe dinta, suturar jikinta ta canza zuwa riga da skirt launin dark brown, ta dawo gaban mirror ta zauna tana kiciniyar ɗaure gashin kanta da ribbom.
Jin motsin shigowar mutun ɗakinta ne yasa tayi sauri juyowa don ganin wanene
Benazir ce a tsaye ta goya hannayenta saman kirjinta,
Kamar mara gaskiya haka zeenatu take kallonta, duk tabi ta kame kanta wata irin kunyar Benazir ce ta kamata gani take yi kamar taga abunda suke yi ita da dr. shureim.
Muryarta da in'ina ta furta"am.. um.. aunty Benazir kece" dariya Benazir tayi tare da shiga ciki tana fadin"Zeenatu kenan, dole ki ruɗe babyn shureim"
Waro ido waje tayi jin ta kira ta da sunan babyn shureim hakan na nufin tagansu ɗazu, da sauri ta miƙe daga kan mirror chair din tana faman duƙar dakai ƙasa
"Kin bani mamaki zeenatu, Ki rasa dawa zakiyi soyayya sai yaya shureim! Kamar kin makance, May be bakisan shekarun shi ba, Ki daina ganin shi kyakkyawa kamar matashin saurayi, ya kusa sa'an daddynki... " har saida gabanta ya fadi jin abunda Benazir ta faɗa mata.
Muryarta na rawa ta furta"am... aunty Benazir kina nufin yaya shureim da daddyna sa'annin juna ne"?
"Eh mana, kema in banda abunki taya zaki yi soyayya da wanda Ya girme maki? yafa haife ki" Da biyu Benazir take fada matan hakan duk don tacanza mata ra'ayinta na son ya shureim, don ita aganinta bai kamata yaso ƴar cikinsa ba, badan bata son shi da zeenatun ba, sai dai bata jin zata iya bari ya auri mace mai ƙaramin shekaru amatsayinshi na tazurun daya daɗe baiyi aure ba, zaifi dacewa Ya auri babbar mace wadda takai shekara talatin.
Bubbuga ƙafafu zeenatu tayi akan floor, voice dinta da shagwa6a tace.
"Aunty Benazir ai ba haramun bane, cos The Prophet Muhammad, peace be upon him, married Aisha when she was very young," ta faɗa tare da sanya hannu ta rufe fuskarta cike da jin kunyarta.
Dariya Benazir tayi tana dubanta da mamaki wato bazata kar6i shawararta ba tafi son Sugar daddy irin Ya shureim.
"Zeenatu Ki fahimce ni, Kinfi buƙatar saurayi wanda baifi shakara ashirin da bakwai ba, Ina zaki kai Ya shureim"?
"Aunty benazir dan Allah kidaina fadin haka, wallahi bana so, Inason Ya shureim ɗina, koda tsohone shi" tamkar zata fashe da kuka tayi maganar.
Gyaɗa kai benazir tayi"its Okey, babyn shureim, Naji nayi shiru bazan ƙara magana ba, hakan yayi maki"
Tana faman zumbura baki tace Eh, dariya Benazir tayi da zolaya take fadin"lallai ya shureim yayi kasuwa, Irin wannan So haka? Ta fada tare da samun wuri gefen gadon zeenatu ta zauna.
"Ina wayarki take"?
"Nabarta A cikin wandon jean dina dana cire, Bari na dauko maki" da sauri ta juya ta nufi inda ta rataya kayan.
Sai gata ta dawo hannunta ruƙe da wayar ta miƙa ma Benazir, bayan ta kar6a, zeenatu ta zauna agefenta.
Screen din wayar ta ƙurama ido hoton Fatiman shureim ne, nan take yanayin fuskarta ya canza, da sauri ta furta"Zeenatu! Meyasa kika daura hoton nan a wallpaper dinki"?
"Saboda inason hoton ne, yaya shureim ne ya tura mun hotunanta"
Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, aranta ta ayyana bazai yiwu ba, dole in sa zeenatu ta sauke hoton fateema daga wallpaper dinta.
"Aunty Benazir, Ɗazu An kirani da wata baƙuwar number lokacin na shiga toilet, bansan wanene ba, har mommy nakaima wayar tace ita batasan ma da layi akan wayarba, Nima kuma bansan da layin ba"
Cikin kulawa Benazir tace"waye ya siya maki wayar ne"?
"Daddy ne Ya siya min, amma bani yaba ma ita ba, saboda bayason ina yawan amfani da waya zata Iya ɗauke min hankali daga yin ibada, shine yaba mommy wayar, ita kuma ta ajiye min ita, dama ni ban damu da ita ba, sai da naga hotunan fatiman ya shureim awayarsa shine naje nace ma mommy ta bani wayata zan yi amfani da ita" tunda tafara yin maganar Benazir bata kau da ido daga kallon ta ba, tayi mamakin da har shureim ya iya faɗama Zeenatu sirrin shi, hakan ya ƙara tabbatar mata da irin Ƙaunar da yake yima zeenatu.
A hankali ta kau da idanunta daga kan Zeenatu, ta ɗaurasu kan screen din wayar, Call logs ta shiga, nan take tayi tozali da bakuwar number da aka kira zeenatu da ita kusan 2 missed calls, Aranta ta ayyana Uncle musa ne ya siya mata layin awaya ko kuwa tare da sim din aka siya mata wayar? Tayaya ma haka zata yiwu? Idan shine ya sanya mata sim din meyasa bai sanarma mom sarah ko ita zeenatun da akwai sim a wayar ba? Sannan babu yadda za'ai companyn da aka sayi waya su bada ita tare da sim"
Zeenatu dake kallonta ganin ta ƙurama screen din ido babu alamun zatayi magana ne yasa tace"ko dai in kaima daddy wayar ya duba min mommy ma tace idan ta shigo gidan zata bibiyi layin"!
"A'a zeenatu, Kada ki kai mashi wayar, nafi tunanin shine ya sanya maki sim din aciki ba tare dasanin ki ba may be ya manta bai faɗa maki ba, sannan layin da aka kira ki da shi ina da tabbacin wrong number ne suka kira"
"Nima raina ya bani hakan, to ki goge min layin daga kan wayata"
Benazir tace"A'a, kada mu yi saurin goge number, Mu jaraba kira don mu faɗa ma mai layin wrong number ne ya kira, Kinga ta hakanne zai iya gyara number din ya kira wanda yake son yin magana da shi"
Jinjina kai zeenatu tayi alamar gamsuwa da bayaninta.
"Yaushe zamu kira su"?
"Yanzu zan jaraba"
Danna kira Benazir tayi, duk sun ƙagara da son jin me layin ya ɗaga sai dai kash Kiran yaƙi shiga"
"Ki bar min wayar a hannuna, tunda ba amfani kikeyi da ita ba, Zuwa anjima zan jaraba kiran layin"
Amsa mata tayi da toh
"Amma idan mommy ta tambayeni ina wayar ya zan fada mata"?
"Sai kice mata ni na kar6a, ina wani amfani ne da ita" amsa mata tayi da toh.
"Namanta wayata a hannun mutumin da na zauna awurinshi can ƙasar Canada" benazir ce tayi maganar
Zeenatu tace"aunty dama a canada kika zauna? Ya sunan mutumin da kika zauna a wurin shi"?
Shiru ta yi tamkar bazata tanka mata ba tace"hakane a canada na zauna, mutumin daya ruƙe ni sunan shi Zaki Mubarak Obinna, ɗan gidan chief of army staff bansan ko kin san shi ba"
Murmushi zeenatu tayi tare da cewa"nasan ƴan family din obinna sosai, tun kafin in mallaki hankali na muna yawan zuwa estate dinsu nida mommy na, da yake suna mutunci da Hajiya saratu daga bayane daddy ya hanata zuwa Yawo dani, tun da na kammala secondry school Ya garƙameni agida, bai bari tana fita dani, har sai da Ya shureim Ya dawo da zama gidanmu sannan Ya kyaleni ina fita tare da shi.
Murmushi benazir tayi"Allah sarki, kada ki damu ai yanzu tunda ina nan zamu dinga zuwa yawo sosai, Harma estate din nasu zamu Iya zuwa duk da bansan su ba amma indai na tuntu6i zaki mukayi magana da shi nasan zai gayyace ni zuwa gidansu, ya jima yana da burin inje gidansu saboda ya nuna ma Iyayen shi ni, Amma naƙi amince mashi saboda bana son zuwa nigeria a lokacin"
"Idan ma zaki gidansu ƙawarki Aneeleeh dan Allah ki tafi dani, nima inason zuwa, Naji kuna magana da su mom layla akan zaku je gidan"
"In sha Allah, atare zamu tafi," taji dadin maganar Benazir fatan ta Allah yasa ta samu ƙawaye agidan kawar Benazir, tana da burin ganin ta tara friends sai dai daddynta Ya hanata Yin kawaye, baison kowa ya rabeta.
*❤EX-PRISONERS🌹*
Shigowa ɗakin Naufal Yayi, fuskar shi babu walwala, shima babu suturar a jikinshi sai gajeran wando, sumar kanshi duk ta yamutse har saman wuyan shi, Kunsan atare Unaisah Da Sajeed suka juyo suna kallon shi
Harara ya watsa ma sajeed tare da cewa"Ɗan rainin wayau, ashe nan ka shigo, kasa inata nemanka, Hankalina Yaƙi kwanciya ganin Halin da ka farka daga bacci"
Murmushi Sajeed Ya sakar mashi, tare da saukowa daga saman gadon unaisah bayan ya miƙa mata wayarta ya nufi Naufal Ya rungumo shi Yana fadin"Sorry My baby Boy, Na tayar maka da hankali, ashe ka damu dani har haka? Halan ma kuka kayi saboda rashin ganina da baka yi ba" ya fada da zolaya yana shafa mashi fuskarshi.
Tsoki Naufal Yaja ba tare daya tanka mashi ba Ya dubi Unaisah
"Sister barka sannunki"
Murmushi tayi dimple dinta biyu suka lotsa
"Yawwa rabin raina, halan Sajeed ne Ya 6ata maka rai"?
Yamutsa fuska yayi kafin yace"eh mana, kawai Ina kwance Ina bacci na jiyo shessheƙar kukan shi ya cika min kunne na, ba arziƙi na farka Hankali atashe na tada shi daga bacci ina tambayarshi lafiya yake kuka, Bai tanka min ba kamar wani shashasha haka yabarni ya fito daga dakin, Ina ta neman shi ashe nan ya shigo" Ya faɗa yana jifar Sajeed da harara"don yaga na damu da shi ne, Allah nan gaba idan Ya ƙara yi min haka, Bulala zan sanya mashi"
Dariya su ka yi gaba ɗayansu, Sajeed yace"na fi ƙarfinka Naufal, mai buguna sai ruwan sama da rana," ya fada yana nuna mashi faffadan kirjinshi da damtsen hannunshi.
Nannaɗe hannun riga Naufal yayi yana fadin"ba kai kaɗai Allah Yaba kirar karfin ba, Nima ina da ita, babu abunda zaka nuna min in banda girman jiki"
Unaisah dake kallonsu kamar ta samu tv, Wayarta dake a hannunta ta danna ta shiga Camera, Ta saita su tana ɗaukarsu Video batare da sanin su ba, saboda sunyi mata kyau, sai taji inama ace hada Danish dinta da kuwa shi zai kar6i kambun faɗan nasu, domin kuwa Danish Yafi su tsayi da kuma kyawun Sura duk da suma ɗin ba daga baya ba musamman Gabriel Namiji ne.
A yayin da take ɗaukarsu video, bakomai take tunawa ba face garkuwarsu, lokacin da ta risƙe shi a ɗakin Gidan kurkukun ƙaddara Kwance Yana bacci da red shirt a jikin shi, yayi mata kyau fiye da tunanin mai tunani, duk da a lokacin a matsayin giant yake saima ya ƙara yi mata kyau, tana matuƙar ƙaunar komai nashi ta ƙosa ya dawo normal mutun kodan suci gaba da bama junansu kulawa.
Tayi zurfi acikin tunaninta, Shessheƙar kukan Azeeza Ya fargar da ita, da sauri ta janye wayar daga saitin fuskarta, su Sajeed dake atsaye suna kokoyi shida Naufal jin kukun Azeeza ne Yasa suka dakata kusan atare suka kalli ƙofar shigowa dakin.
Kamar Mahaukaciya Haka ta shigo sanye da ƴar gown wadda bata rufe gwiwar ƙafarta ba, fuskarta sharkaf da hawaye tayi jawur da ita, rigar jikinta ta jiƙe da ruwa
daga bayanta Jamimah ce atsaye ta ruƙe rugu tana faman sakin murmushin mugunta.
da sauri Unaisah ta sauko daga saman gason, ta nufi Azeeza ta ruƙo hannunta tare da rungumeta tana tambayar ta lafiya take kuka
Muryarta da shessheƙar kuka tace"jamimah ce ina bacci ta watsa min ruwa ajikina, shine wai take cewa nayi fitsarin kwance bayan itane ta kwarara mun ruwa a kasan rigata.... " tunkafin Azeeza ta ƙarasa maganar, Jemimah tayi saurin cewa"wallahi ƙarya take yi min, Fitsarin kwance ne tayi mana a ɗakin mu, Ni bani na zuba mata ruwa ba" Ta faɗa tana faman gumtse dariya.
Cikin muryar Raɗa Naufal Yace da Sajeed"babynka tayi fitsarin kwance, Yakamata kaje ka wanke mata" harara Sajeed Ya watsa mashi tare da ingije shi, Ya nufi Jemimah, ganin Yana tunkarota Yasa ta juya da niyar ta gudu sai dai kafin ta fuce daga ɗakin, Yayi hanzarin cafkota da hannu biyu ya ɗaga ta sama yana fadin"Mugunta ko? Ai ba ke kaɗai kika iyaba kowa ma Ya iya ta, rasa kunya 6eran tanka, da wasu kunnuwanki kamar na zomanya, Jibi kumatunki duk kin shanye ma mutane madara da bonbita, Yau zanyi maganinki" Ya fada tare da Juyawa ya nufi Toilet da ita, Kuka tadinga yi mashi tana kokarin kwacewa, da gudu naufal yabi bayan shi yana fadin"please bro, Ka kyaleta yarinya ce bata da wayau" ko sauraron shi baiyi ba yaja kofa Ya datse.
Azeeza dake kwance Jikin Unaisah sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, Taji daɗi Sajeed zai rama mata abunda Jemimah tayi mata, ba tun yau ba kusan kullum sai jamimah tayi mata mugunta don taga suna kwana a ɗaki ɗaya.
"Ki yi haƙuri da sister dinki, nasan halinta bata jin magana, Kunnan ƙashi ne da ita, amma please ki daina bari tana ganin kukanki, shiyasa take ƙara rainaki saboda tasaba sanyaki kuka... "
Cikin sanyin murya Azeeza tace"Toh, amma kiyi mata magana tadaina jana fada, har fadi takeyi wai ni ban isa da ita Ba, maganarki kaɗai take Ji"
Murmushi unaisah tayi"zan yi mata magana idan ma bata daina ba zamu fara koya mata hankali ne"
Fitowa Sajeed Yayi daga cikin toilet Yana faman sauke ajiyar zuciya, fuskarshi ɗauke da murmushin mugunta.
Naufal dake kallonshi yace"Mugu Ina ka baro mana jamimah"?
Harararshi yayi" ka shiga ka ɗaukota, wata'ƙil ƙafafuwanta baza su iya daukarta ba shiyasa ta kasa fitowa"
Ya faɗa tare da wucewa Ya nufi Azeeza, Ruƙo hannunta yayi Acikin nashi ya rabata daga jikin Unaisah
Ya zauna daga gefen gadon Yana fadin"Har nagaji da yi maki magana akan ki daina bari Waccan Ƙaramar halittar tana sanyaki kuka, serious idan baki daina ba zamu 6ata" ya faɗa yana daure mata fuska.
Muryarta ƙasa ƙasa tace"zan daina"
Harara ya watsa mata"haka kullim kike fadamin, last warning zan baki daga yau idan na ƙara ganin hawaye akan fuskarki da sunan jamimah ne tasa ki kuka Jikin kine zai gaya maki" yai maganar tare da kama kunnanta yace"Idan kunne Yaji"? da sauri tace mashi Jiki Ya tsira"
Dariya ce ta kubce ma unaisah da naufal, shima sajeed din dariyarce tazo mashi sai dai Yaƙi barin ta kubce mashi don baison raini ya fara shiga tsakanin shi da Azeezarsa, Yafi son tana jin shakkarshi.
"Jemimah!" Jamimah ta"! Naufal Ne ya kira sunanta, Shiru taki ta amsa mashi, Sajeed Yace"zuciyar ce ta motsa, tana jin ka ƴar rainin wayau"
Miƙewa unaisah tayi da sauri ta nufi toilet din, tana shiga ta taras da jemimah zaune cikin kwamin wanka da sajeed Ya cika da ruwan mai uban yawa, Rigar jikinta duk ta manne ma fatarta, ta ɗaure fuska sai shessheƙar kuka take Yi kamar zata haɗiyi zuciya tsabar 6acin rai.
Ganin Unaisah yasa ta fashe da kuka rai a6ace ta dinga bugun ruwan da hannayenta tana fadin"wayyo Allahna Anci mutuncina, Zuciyata tafarfasa take Yi min, Genie kinga abunda Sajeed Yayi min ko? Kina gani baki hana shi ba, Saboda rashin mutunci ya jefa ni acikin ruwa"
Hatta su Sajeed dake adakin saida suka jiyo maganganun da Jemimah takeyi a toilet, gaba ɗayansu suka sanya dariya hada Azeeza.
"Am sorry My Little sister, Sajeed bai kyau ta miki ba, Amma kiyi hakuri dan Allah" unaisah ce ta fada Cikin lallashi da lallami Ta nufi jemimah, ta sanya hannu ta ɗaukota daga cikin ruwan,
"Kinyi wanka"? Idanunta na fitar da hawaye tace"a'a ni ban yi ba"
"Okey, Bari nayi maki wanka, Sai in ɗauko maki wasu kayan ki canza"
Ta fada tare da cire mata rigar, shaf shaf tayi mata wanka ta daure mata jikinta da towel, Asaman bayanta ta goyo jemimah, suka fito daga toilet din, sai faman zumbura baki take Yi, Hada jifarsu Sajeed da harara.
"Azeeza mu tafi dakinku, Inaso Ku shirya in yi mana hotuna da wayata" amsa mata tayi da toh,
Sajeed yace"Mu ma bari muje mu shirya ayi mana hotunan, Ko mun samu na ajiyewa saboda tarihi"
Yayi maganar tare da miƙewa Ya dafa kafaɗar Naufal, suka fuce daga dakin.
*❤BATOOL🌹*
Kusan mintuna da tafiyar Unaisah, Chief Ya shigo dakin sanye cikin shiga ta white thobe launin Sky blue, tabi shape din jikin shi, Hannun shi ɗaya ruke da wayar shi, Ya karata a kunnanshi ga dukkan alamu waya yake yi.
"Yanzu na shigo gidan, In sha Allah Uncle Idan na shiga bedroom dinsa zan kira ka video call kaga fuskarshi, nasan hakan zai kwantar maka da hankalin ka"
On the other hand, Prime minister yace"nagode my Son, bansan meyasa nakasa cire shi arai na ba, Na ƙwallafa rai akan shi"
"Kada ka damu uncle, Nafi so ka kwantar da hankalin ka, baifi awanni daka dawo daga tafiya ba, nasan kana bukatar hutu, Idan rabon ka ne shi watarana zaku gana"
"Ina fatan hakan, nagode da kulawarka, sai naji ka".
"Okey" ya ambaci hakan tare da zame wayar daga kan ear dinsa.
Yayin da yake tafiya A hankali yake bin ko'ina na room din shi da kallo, Kafin Ya sauke idon shi akan Glass table din dake dauke da breakfast dinsa.
Ƙarasa shiga ciki Yayi, batare da 6ata lokaci ba, Ya zame jallabiyar jikin shi, Daga shi sai short Ya nufi toilet Ya shiga domin yin wanka.
After 15 mins Ya fito Waist dinsa daure da white towel, a gaban dressing mirror ya tsaya da niyar ya gyara jikin shi, kwatsam A lokacin da baiyi tsammani ba kunnuwansa suka jiyo mashi sautin motsin mutun a bedroom dinsa.
A hanzarce ya ɗaura idanunsa kan madubin, ta ciki ya hangota ta fito daga hanyar zuwa Gym Room dinsa kamar Aljanna, Hannunta ɗaya ruƙe da mayafinta, Ga wannan Uban gashin kan nata data ta saki saman bayanta yayi mata tamkar hijabi, Lamarin ya ɗaure mashi kai ganin matashiyar mace a ɗakin kwanansa, Wacece ita? Tayaya akai ta shigo mashi bedroom din sa? Da iznin wa"? Acikin zuciyarsa ya furta hakan ba tare daya kau da ido daga kallon ta ba, ƙarfin halin ta yayi matuƙar bashi mamaki, tsawon lokacin daya shigo dakin har ya shiga bathroom yayi wanka duk tana a ciki ko me take yi!?
Gaba ɗaya Hankalinta ba akanshi yake ba, batasan ma da zaman shi a dakin ba, har ta ƙaraso tsakiyar dakin bata lura da chief Owais ba, idanunta ba su hango mata shi ba, Sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi kamar wadda tasha gudu.
Ganin bata da alamun motsawa tabar mashi room dinsa ne yasa shi juyowa A hankali Ya nufe ta, sam bata ji motsin takun shi ba, saboda Ta juya mashi baya sai ƴan waige waige take Yi, duk kallon da tayima dakin nashi bai isheta ba.
A lokacin da batayi tsammani ba, Taji saukar hannun mutun saman sumar kanta, Kafin tayi wani yunƙuri Ya damƙi gashinta, wata irin firgita Batool tayi, A gigice Ta fasa ƙara Sautin Ya cika kunnuwanshi dasauri ya sakar mata gashi, hakan ya bata damar juyowa don ganin wanene.
Wani irin bugu zuciyarta tayi lokacin da idanunta suka sauka akan faffaɗan ƙirjinshi, da waɗannan Strong arms din nashi, ta zazzaro mashi ido waje la66anta na kerma take ambaton"INNAHU MIN SULAIMAN WAINNAHU BISMILLAH" adabarbarce ta furta hakan, kamar wadda taga wani mugun abu, Kallo ɗaya da tayi ma fuskarshi har suka haɗa ido ba ƙaramin gigitar da ita yayi ba, duk tabi ta ruɗe, Mayafin hannunta tuni ya jima da zamewa saman floor, juyawa tayi da gudu tana neman hanyar fita daga dakin sai dai takasa gane ta ina ƙofar da suka shigo take, sai faman bin bango take yi, Jikinta ya hau yin kerma kamar wadda Sanyi ya kama.
Chief dake atsaye yana dubanta, Kallon mahaukaciya Yake Yi mata saboda kalmar data furta mashi da kuma firgitar da tayi kamar taga wani mugun abu, Ya rasa gane me ya ruɗar da itane, ta6e la66ansa yayi kafin Ya juya ya nufi cikin ɗakin,
Batool dake ta neman kofar fita, tuni zufa ta jiƙeta yadda kasan babu A.c a dakin, Mugun tsoron shine Ya kamata hada ƙarin babu sutura a jikin shi shiyasa ta rikice da ganin al'amurransa, towel din daya ɗaure waist da shi ko gwiwarshi bai rufe ba.
Jin takun tafiyar Shi abayantane Yasa ta ƙara ruɗewa, A gigice Ta juyo tana duban shi, sumar kanta ta rufe mata gefe da gefen fuskarta, har Ya sanya Short a jikin shi tare da singlet fara ƙal.
Fashe mashi tayi da kuka tana fadin"nashiga uku, dan Allah ka buɗe mun ƙofa in tafi ɗakin mu, wallahi ni ba 6arawo bane, bada niyar wani abu na shigo maka ɗakinka ba.
Fuskarta sharkaf da hawaye tayi maganar tana faman jan majina.
Bai tanka mata ba, yama rasa bakin magana, mamakin ta ya gama kama shi, sai yanzu ya gane fuskarta a cikin Yaran da suke kula da su.
Gently Ya juya Ya nufi gaban side drawer din shi, ya buɗe Ya dauko jotter da pen asaman drawer din Ya ɗaura jotter, rubutu yayi mata bayan ya kammala ya cire paper din ya tunkari Batool Ya miƙa mata takardar, gabanta na faduwa ta sanya hannunta dake kerma ta kar6a tana kallon abun da ya rubuta mata.
Muryarta da shessheƙar kuka Ta furta"ai..ai.. Ni Ban Iya karatu ba, sai dai in kaima Unaisah ta karanta min"
Wannan maganar da ta furta mashi ta ta6a zuciyar shi, har sai da ya ɗaura reddish eyes dinsa akan soft brownish lips ɗinta da suka jike da ruwan hawayen ta, ga wani uban gumi da ta haɗa a jikin ta, shi abun da ya ɗaure mashi kai ruɗewar da tayi kamar taga wani mugun abu, ita kanta Batool din tunfarko taso idan suka haɗu ta natsu ta yi mashi bayanin abunda ya kawota dakinsa, sai dai dalilin shaƙar da yayi ma sumar kanta ne, Yasa ta firgice mashi ta kuma fahimci bai san da maganar zuwan ta ɗakin shi yi mashi aiki ba!.
Taƙi Yarda ta ɗago su haɗa ido saboda ƙwarjinin da yayi mata, gani take yi kamar zai rufeta da bugune yadda yayi mata rumfa da kirjinsa.
"Dan Allah ka buɗe min ƙofa in tafi daki, zan kai mata ta karanta min"
ba tare daya furta mata komai ba, Ya dafe Glass door din dakin nan take ƙofar ta soma zugewa a hankali, Jikinta har rawa yake Yi wurin yin saurin fucewa daga dakin kamar za tayi tuntu6e.
Ta tafi tabar mashi Mayafinta akan floor, komawa yayi gefen gadonshi Ya zauna da sanyin jiki, wata irin yunwa ce ke addabar shi, bazai juri jiran wani yayi serving na shi ba,
Da kanshi Yayi serving abunda zaici, Kakkauran tea ya zuba a cup Ya soma kur6an shi atsanake, Yayin da brain dinshi ke tariyo mashi kalaman Batool
Ai ni ban Iya karatu ba, zan kaima unaisah ta karanta min, Abun Ya tsaya mashi aranshi, Duk da bai kalleta dakyau ba, zai Iya bata shekaru goma sha bakwai zuwa sha takwas, a wannan shekarun bata Iya karatu ba? Bai yi tsammanin abun yakai haka ba.
Bayan fitar batool daga dakin chief, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, tana tafiya idanunta akan paper ɗin daya bata, Har ta sauko down ta nufi dakin su.
Lokacin da ta shiga bata taras da kowa ba, yanke shawarar shiga toilet tayi don ta wanko fuskarta, asaman gadon su ta ɗaura paper din, da sauri ta shiga toilet ta wanke fuskarta, fitowa tayi tareda nufar gado nasu, isarta keda wuya ƙafarta dake sanye cikin wandon pakistan ta harba hotunan da suke yashe kan floor ba tare data lura da su ba, nan take hotunan suka gangara ƙarƙashin gadon suka shiga ta yadda babu mai iya ganin su.
Miƙa hannu Batool tayi ta ɗauki Paper din Ta juya da sauri ta fito daga dakin tana neman su Unaisah.
Sautin Muryoyin su Tajiyo A falo suna surutu cikin takun sauri ta nufe su, tun kafin ta ƙarasa ta hango su tsaitsaye sun yima Unaisah rumfa hannunta ruƙe da waya tana yi masu hotuna, tun daga kan Haris, Naufal, Javed, Sajeed, da su Azeeza jamimah, parveen and Hannah kowannansu ya sanya sutura mai kyau ajikin shi, Unaisah ce tasa suka ɗauki wanka, don tayi masu hoto.
Babu wanda Ya lura da Batool acikin su, Camera taja hankulansu, har saida Ta furta Sunan Unaisah tukunna suka ɗago da idanunsu akanta.
Kallo ɗaya da Unaisah tayi mata saida taji gabanta ya fadi ganin yadda kumatunta suka yi ja alamar tayi kuka
Gaba ɗaya sun lura da yanayin Batool babu walwala,
Ruƙo hannunta Haris yai acikin nashi"Sister baki da lafiya ne"?
Shiru tayi batace mashi komai ba, Hankalinta na akan Unaisah
"Me akayi maki? Kuka ki ka yi"? parveen ce tayi mata tambayar, girgiza mata kai tayi alamar a'a.
hannah ta ruƙo hannunta tana fadin"Sis Batul ki zo ay mana hoto atare dake"
Fahimtar halin da take aciki ne Yasa Unaisah miƙa ma Sajeed wayar hannunta, bayan ya kar6a tace"ka cigaba da yi maku hotunan, yanzu zan dawo"
Ta faɗa tare da ruƙe hannun batool, suka juya atare suka nufi ƙarshen falon inda babu mai jin su
Shafa gefen fuskarta tayi da hannu tana fadin"meya faru? Chief ɗin Ya dawo"?
Batare da batool ta furta kalma ba ta miƙa mata Paper din hannunta
da sauri Unaisah ta sanya hannu ta kar6a, A fili ta karanta.
"How did you get into my room? And why are you crying at me like I'm a monster? nayi maki wani abu ne"?
Murmushin gefen fuska unaisah tayi"meyasa ki kuka? Faɗamin?
Tana faman jan numfashi tace"tsoro ya bani, ya damƙi gashin kaina da hannun shi kuma babu kaya a jikinshi, short towel ya ɗaure a qugunsa.... " tun kafin ta ƙare maganar Unaisah ta tuntsire da dariya
Batool dake kallonta ganin tana yi mata dariyane yasa ta ji jikinta yayi sanyi laƙwas, in cool voice tace"Nayi ƙauyanci"? tambayar da tasaba yi mata kenan a duk lokacin da take tunanin ta aikata ba dai dai
Dafa kafaɗarta Unaisah tayi fuskarta da murmushi tace"My own sis ba ki yi ƙauyanci ba,
"To meyasa kike min dariya"?
"Saboda kin bani dariya, meye nayi mashi kuka? Ba bugu ba zagi kin fashe da kuka kamar wata ƙaramar yarinya ni danake so ki zama big girl, matar manya.
"Ni dai bazan ƙara komawa ɗakinsa ba, Tsoronsa nake ji sai dai ke ki je" ta faɗa tana nuna ta da hannu.
Maƙe kafaɗa Unaisah tayi"Batool ki fahimta ni bazan iya shiga dakin sa ba, bayason ana sharing aiki a part dinsa, idan mutun ɗaya ya fara shi zai cigaba da yi har sai in shi yace ya gaji baya so, nima big guy ne ya gaya min hakan.
Fuskarta ayamutse ta ƙare maganar tana dubanta, itama batool din kallon ta take yi, taƙi gane cewa wayau Unaisah take yi mata.
"Ya zanyi? Ni wallahi tsoron shi nake ji, baki ga launin idanuwanshi ba kalar na danish ɗinmu, kuma ma suna kama sosai don dai shi launin fatarshi chocolate ne"
ta fahimci Batool ta tsorata da chief, idan tana magana yatsun hannunta har kerma su ke Yi.
"A hankali zaki saba da shi, dan Allah ki daure Sister, za ki ji dadin yi mashi aiki" da wayau da dabara Unaisah ta shawo kanta, har ta amince zata cigaba da zuwa.
"Yanzu idan kika koma ki fada mashi cewa, Big guy ne ya baki aikin kula da part dinsa, ke zaki cigaba da daukar ɗawainiyarsa kina gyara mashi daki da kuma kai mashi abinci, haka zaki faɗa mashi,"
Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"amma ba yanzu zan koma ba ko"?
"Idan baki koma ba kayan abincin da kika bar mashi a ɗaki wazai kwashe su? Na fada maki bayason kazanta, sannan bai saba da wahala ba komai yi mashi akeyi"
tana ƙarasa fadan hakan Taja hannun Batool suka nufi Hanyar zuwa Part dinsa, A bakin ƙofar shiga unaisah ta saki hannunta.
Jiki na rawa Batool ta sanya hannu ta kwankwasa ƙofar,
A hankali Ta zuge, saida ta fara dadaita natsuwarta tukunna ta yi mashi sallama, shiru bai amsa mata ba, a tsananin tsoro ce ta zura kafarta, a lokacin Harya kammala Yin breakfast dinsa, yana daga kwance saman lallausar mattress dinsa, Ya ɗaura kanshi bisa pillow, Yayin da idanunsa ke akan Laptop dinsa da yake operating
Yawu ta haɗiya Muryarta na rawa ta furta"am.. dama Big guy ne yace in dinga zuwa inayi maka aiki a part dinka, kuka kuma da nayi kaine ka bani tsoro daka kama min gashin kaina"
Dakyar ta ƙare maganar, batare da ta motsa daga bakin ƙofar ɗakin ba, tamkar baisan tanayi ba, yayi shiru yana sauraronta, babu alamun zai kalleta
Jin shiru bai tanka mata ba, yasa ta yanke shawarar shiga dakin donta kawar mashi da kayan abincin da ya gama amfani da su.
Cikin sanɗa take yin tafiya kamar 6arauniya, duk a tunaninta bacci yake yi saboda idanunsa dake a lumshe batasan cewa idonshi biyu ba kuma yana kallonta, yayi mata hakanne saboda baison Ya ƙara firgitar da ita, tunda ya fahimci ruɗaɗɗiyace ita.
Tana ƙarasawa gaban table din tayi saurin kwashe kayan abincin, sam bata yi tunanin ɗaukar mayafinta data gani akan pillow ba saboda saurin da take Yi, bayan ta fita abakin bene ta tarass da unaisah tana jiranta.
Murmushi ta saki tare da nufarta tana fadin"Sister, nayi mashi bayani amma kamar bacci ma yake yi, ga tray din abincin na dauko Ina zamu kai shi"?
"Nikaina bansan ina ne kitchen dinsu ba," unaisah ta fada tare da kar6ar tray din"bari naje na nemo kitchen din, Ki tafi falo," amsa mata tayi da toh, da sauri Batool ta sauka daga kan benan ta nufi falo.
Unaisah tana cikin tafiya, Tajiyo motsin buɗe kofar Falon, su biyu suka shigo Boss man tare da Big guy, wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta, Allah Ya taimaketa, Ta kar6i tray din daga hannun Batul da kuwa Big guy saiya gane ba ita taje yima chief aiki ba.
Tunkararsu tayi fuskarta dauke da fara'a tace"Yalla6ai nagama yi mashi aikin, A ina zan ajiye tray din"
Big guy yaji dadin Jin hakan daga gareta, alamar jinjina yayi mata da yatsan hannun shi kafin Yace"ai tunda naga kina yin fara'a raina ya bani cewar Kin samu kar6uwa awurin chief, bani labari daya ganki meya ce maki"? boss man dake sauraronsu murmushi ne dauke akan fuskarshi dake asanye da facemask.
"Bayan na gaishe dashi Ya amsa min, sai nace mashi me yakeson ci in zuba mashi, to daya fada min saina zuba mashi na tsaya har ya cinye na ƙara mashi wani, kusan fa plate uku ya cinye ya kuma sha Tea" da mamaki Big guy ya maimaita kalmar plate uku!
"Kina nufin chief shi yaci abinci har plate uku"?
Ɗaga mashi kai tayi alamar Eh, saboda karfin hali irin nata ko tsoron yace zai buɗe warmer din batayi ba
Boss man yace"wow, My daughter kin ciri tuta, ai ni tunda nake da chief bai ta6a yarda wata mace tayi mashi aiki a part dinsa ba saboda bayaso"
Sai faman washe masu baki take Yi,
"Ga tray din abincin, Yanzu saura aikin kai mashi lunch ko"? Ta tambaya tana kallon big guy
Boss man yace"a'a, Sai kuma dinner, idan yakai Rana bai ci breakfast dinsa da wuriba to baya cin lunch na safen daya ci ya ishe shi sai kuma Dinner dinsa.
Wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta"Allah Yakaimu daren Lafiya" suka amsa mata da ameen, daga bisani big guy Ya kar6i tray din hannunta Yace tabiyo bayanshi zai nuna mata kitchen dinsu.
Atare suka tafi shi kuma boss Ya wuce dakin chief, Bayan Ya bashi iznin shiga, Yana zura kafarshi karaf idanunsa suka sauka aka Mayafin dake yashe kan pillow, farat ɗaya ranshi ya bashi cewar Na unaisah ne da ta shigo kawo mashi abincin, zuciyarshi ta musa da cewar ba mayafinta bane, saboda ita yaganta da mayafi tayi rolling,! Kenan na wanene wannan"!
A hankali Yakai hannu Ya ruƙo mayafin Yana dubanshi Kafin Ya kalli chief dake a kwance Ya lumshe idanunsa
"Yalla6ai barka da hutawa"
In a calm voice Ya amsa mashi yawwa
"Naga missed call dinka awayata ina fata lafiya"?
"Alright. I'm just reminding you about the plan we have for Hateem's farewell dinner tomorrow.
Murmushi Boss man Ya saki"Ina sane da komai Yalla6ai, Kuma in sha Allah babu wanda zaisan da zancen zuwanmu tare da Yaran, ba zata zamuyi masu, Sai dai yalla6ai naso ace hada Danish zamuje, ko dan saboda Prime minister Hateem, Ina so su gana da junansu, har magana nayi ma sheikh imam akan ko zamu iya kaishi asibiti aduba lafiyarshi sai yace min babu abunda likitoci zasu Iya yi mashi a halin da yake aciki" cikin sanyin murya ya kare maganar
A hankali chief Yaɗan ware idanunsa tare da cewa"nima nayi fatan hakan sai dai har yanzu babu wani cigaba a lafiyarshi, Allah Ya bashi lafiya"
Boss ya amsa mashi da amen, kafin Ya fuce daga dakin hannun shi ruƙe da mayafin daya tsinta.
..shigar shi falo keda wuya, Idanunsa suka sauka akan Batool, dake sanye da Pakistan launin Mayafin hannun shi, girgiza kai yayi don ya riga da ya gane itace taje dakin Chief Yi mashi aiki ba Unaisah ba, baiyi mamakin hakan ba saboda Ya riga daya san halin kayansa, idan bata son yin abu babu wanda Ya isa ya tursasa mata akan tayi shi, shiyasa da big guy ya bata aikin kula da part din chief sai ta tura Batool don tayi a matsayin itane taje, dole ya ɗauki matakin akan hakan don bayason ya samu tangarɗa akan alƙawarin daya daukarwa kanshi.
Batare da Batool Ta luraba, Ya daura mata mayafinta saman kanta, Kafin Ya nufi su sajeed dake ta faman daukar hotuna Daya bayan ɗaya ya rungume su sai dadi suke Ji yazo, Nan fa suka fara daukar hoto tare da shi.
*🌹ANEELARH❤*
A kwance take saman gado tana sharar baccinta, tun da ta sallami baby junaid ya tafi school ta koma kan gado ta kwanta bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,
Can cikin baccinta ta soma jin ana ƙwanƙwasa ƙofar dakinta, da wata irin kasala ta farka tana yin miƙa, doguwar rigar jikinta duk ta yamutse, saukowa tayi daga saman gadon ta nufi ƙofar tana tanbayar wanene
Daga waje muryar Ana ta amsa mata da cewa"Aunty ni ce"
Buɗe ƙofar tayi tare da bata iznin shigowa daga ciki.
A hankali ta zuro kafarta Jikinta sam babu kuzari ta rame tayi duhu, v-neck shirt da pencil skirt ne ajikinta black and white, ta daure guntun gashin kanta da ribbom.
"Aunty barka da safiya, Ina fata ban takura maki ba, Na katse maki baccin ki" ta fada tana faman duƙar da kanta ƙasa
"Babu komai, Ina fata dai lafiya kike ko"? Cikin kulawa tayi maganar
"Lafiylou, dama nazo ne in ƙara yi maki godiya...." kafin ta ƙare maganar Aneelerh ta ɗaure mata fuska tare da cewa"Ana bana son abunda kikeyi min, na fada maki bana son godiyar da kike yi min amma kinƙi ki daina, "
Cikin sanyin Murya tace"kiyi hakuri Aunty idan na 6ata maki rai," dakyar ta ƙare maganar saboda kukan daya ciyota nan take ta fashe mata da kuka.....
Lamarin ya ɗaurema Aneelerh kai Daga maganar batason godiya sai kuka? Anya kuwa ba wani abunne na daban ke damun Ana ba?
Dafa kafaɗarta tayi da hannu daya"ya Isa haka, bana son kukan nan, Idan wani abu ke damunki dan Allah ki fadamin kada ki ji komai, In sha Allah zan yi ƙoƙarin ganin na taimaka maki mun magance koma menene".
Yayin da Ana ke kallonta idanunta sun kaɗa jawur, fuskarta ta jiƙe sharkaf da hawaye,
Muryarta na rawa ta furta"Aunty Aneelerh bakomai"
Girgiza kai Aneelerh tayi"wallahi ban yarda dake ba Ana! Nifa ba haihuwar yau bace, Duk wanda Ya kalleki sai ya gane baki da koshin lafiya, kuma da akwai wani abu dake damunki, Don haka ki fada min kawai! Rashin. fadamin shi zaija maki yin danasani"!
Su6ul da baka tayi wurin furta"kona faɗima babu wanda zai yarda dani, zai yi wuya afahimce ni"!! Rass Aneelerh taji gabanta ya fadi, muryarta da alamun ruɗu ta furta"Meke nan"?
A firgice ta zare ido tare da yin saurin cewa"babu komai, babu komai! Na tafi sai anjima" juyawa tayi da sauri ta nufi ƙofar dakin zata fuce, sai dai kafin ta haura kafarta Aneeleeh tayi saurin ruko hannunta ta juyo da ita suna fuskantar juna
Wani irin kallon kallo suke jefa ma juna batare da sanin ma'anar hakan ba
"Ana! Ki faɗamin meke damunki? Menene kike son fadamin wanda kike tunanin babu wanda zai yarda dake?dan Allah kada ki 6oye min, idan ma sirri ne nayi maki alƙawarin bazan fada ma kowa ba"
Numfashi Ana taja, gaba dayanta a tsoroce take babu kwanciyar hankali atare da ita
"Babu komai!Nabar Girkin dana daura a kitchen zanje na duba" tana karasa fadan hakan ta zame hannunta daga ruƙon da Aneelerh tayi mata, da sauri ta fuce daga ɗakin.
Bayan fitarta, Hankalin Aneelerh Yaƙi kwanciya, Ta jefata a ruɗani, ga wani bugun zuciya da take ji a kirjinta.
kalmar Da ana ta fadi ta tsaya mata aranta, da tace kota fadi babu wanda zai yarda da ita meke nan"?!
Tayi zurfi acikin tunaninta Wayarta dake ajiye kan side drawer ta soma ruri, a hanzarce ta juya ta nufi drawer ta dauki wayar, sunan zahra ne ya bayyana akan screen din wayar,
Bayan ta ɗaga kiran ta kara a kunne
kafin tayi sallama Muryar Zahra ta katse mata hanzarinta
"Auntyna ya ki ke ya gida"?
"Lafiyalou Sister, Bakya a gidan ne"?
"Na tafi wurin aiki, har dakin ki na shigo don inyi maki sallama sai na tarar kina bacci, bana so na takura maki shiyasa ban tada ki ba"
Shiru Aneelerh tayi tana sauraronta har ta ƙare maganar babu alamun zata tanka mata, Jin shiru yasa zahra cewa"auntyna kodai baccin bai ishe ki bane? Naji kinyi shiru?
Numfasawa tayi tare da samun wuri gefen gado ta zauna tukunna ta samun natsuwar yi mata magana
"Ban jima da farkawa ba, Har yanzu kasalar baccin bata sake ni ba, shiyasa zaki ji ni wani iri"
"Kiyi wanka zaki ji dadin jikin ki" acewar zahra
"Zanyi in sha Allah, yanzu dai fada min meya faru ne kika kirani awaya? Naji muryarki kamar akwai farin ciki atattare dake"? Ta fada tana murmushi tamkar suna atare da juna
"Kamar kin sani auntyna, shiyasa nake ƙara ƙaunarki saboda kina fahimtata fiye da kowa, abunda Ya faru Ina awurin aiki, Hajiya sarah ta kirani awaya.... " a ƙagare Aneelerh tace"me tace maki"?
"Ta faɗamin suna buƙatar za'ayi masu decoration gobe friday, Za suyi Farewall dinner, Na bankwana da prime minister Hateem, Jibi zai bar ƙasar tare da Iyalansa zasu koma Canada"
Wani irin farin cikine Ya bayyana akan fuskar Aneelerh"Zahra na tayaki murna, Alkhairi ne ke bibiyarki, hajiya sarah bata manta dake ba, Ashe kina aranta"
Sautin murya zahra da annushuwa tace"bana tunanin zan iya runtsawa a daren yau, saboda farin cikin zan halarci family dinner dinsu, wallahi aunty naso ace tare dake zamu je amma nasan bamai yiwu bane tunda nima tace daƙyar tayi mana hanyar da zamu samu halartar taron, saboda tsaron da za'a sanyama Estate din a goben"
"Kada ki damu zahra, Nima inason zuwa amma koda nasamu damar da zan biki bazan je ba, idan ma kikaje kamar naje ne, bani da damuwa nasan zaki bani labarin komai daya faru a shagalin, Harma Ki dauko min hotuna da videos don inga Ƴan family din Obinna"
Zahra tace"in sha Allah auntyna, yanzu zan koma bakin aikina, Sai na dawo gidan ki kula min da kanki,"
"Nima ki kula min da kanki sai anjima" baya sunyi sallama Aneelerh ta ajiye wayar saman pillow, ta miƙe da sauri ta nufi toilet ta shiga ciki, after some minutes ta fito daga wanka, shaf shaf ta canza suturar jikinta, ta sanya
Primcess vest tare da wrap skirt, ta ɗaure kanta da mayafi, da sauri ta fito daga dakin ta nufi bedroom din mami.
Tunkafin ta shiga ta soma jiyo muryarta tanayin karatun kur'ani, da sallama ta shiga ciki, a zaune ta taras da mamie saman darduma sanye da hijab, idanunta akan kur'anin da take karantawa, gefen gadonta ta zauna tana jiran ta kai Aya.
"Aneelerh kin tashi daga baccin lalacin"? Mami ce ta faɗa tana dubanta
Murmushi tayi mata"mami bansan baccin ya ɗauke ni ba,"
"Na gaji da ganinki zaune a gida, zan tuna ma Abie dinki maganar aikin da Uncle ɗan Iya yace zai sama maki a asibitin Obinna, Indai dagaske yake zai yi maki hanya"
"Mami nikaina nagaji da zama babu aikin, Dan Allah ki tuna mashi idan Ya dawo su yi magana asama min aikin in fara zuwa"
"In sha Allah zanyi mashi magana, ai nafi son ganin cigaban ki"
Murmushi suka sakar ma juna
" shiru sukayi kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyarshi.
"Dama zuwa kikayi don kiyi ta kallona"? Mami ce tayi maganar fuskarta da murmushi.
"Dangane da Ana ne, mami Yarinyar nan akwai abunda ke damunta, taƙi ta sanar dani, ina ɗaki ta shigo daga yi min godiya akan kudin da muka bata ni da zahra, sai nace mata bana so tana min godiya kawai sai ta fashe mini da kuka.... " gaba ɗaya Aneelerh ta sanar da ita abunda Ya faru.
Mami ta jinjina kai tana dubanta tace"tuntuni fa na lura da canzawarta, tayi baƙi ta rame kamar bata da koshin lafiyar, har tambayarta nayi meke damunta sai ce min tayi babu komai lafiyarta ƙalau Ni bansan ya zamuyi da ita ba" Mami ce ta fada tana mai nuna damuwarta.
"Mami yakamata ki ja ta a jiki kiyi mata magana wata'ƙil ke ta faɗa miki tunda kin haifeta zata ji tamkar mahaifiyarta ce keyi mata magana"
Shiru mami tayi na wani lokaci kafin tace"Toh, zan jaraba yi mata magana mu ji meke damunta"
"Tana a ina ne yanzu"?
"Ta fadamin zata je kitchen duba girkin da ta daura"
Mikewa mamie tayi"muje wurinta Inji" da sauri aneelerh ta miƙe ta dauki kur'anin mami da cazbaharta ta ajiye su a ma'ajiyarsu, Kafin Tabi bayan ta suka fito daga dakin,
Adai dai Lokacin Ummi ta fito daga daki sanye da dogon Hijab taci karo da su atare
Fuskarta da fara'a tace"Uwa da ɗiya ina zuwane haka"
"Wurin Ana zamuje, Yarinya duk ta rame tayi baƙi, Taƙi fada ma mutane abundake damunta ko ke baki Lura bane"?
Jim ummi tayi kafin tace"kamar kun shiga zuciyata, fitowar nan da nayi dakin ki nake shirin zuwa don inyi maki magana game da ita, na jima da lura da hakan, duk ta canza ba kamar yadda nasanta ba farkon zuwanku gidan nan, Yanzu tayi baki ta rame babu ƙugun nan nata da kirjinta duk sun zube kamar mai fama da wata lalura,"
Aneelerh tace"abun da yafi ɗaure min kai da ita ummi, kwata kwata bata da natsuwa, ko magana take yi yatsun hannayenta zaki ga suna kerma kamar wadda sanyi ya kama"
Ummi tace"Muje muji meke damunta," gaba dayansu suka nufi kitchen din gidan, Koda suka shiga basu ganta ba, Har ta kamma aikace aikacen da take Yi, tayi wanke wanke tayi mopping dinsa.
Ummi tace"baiwar Allah gata da ƙoƙarin yin aiki, banji dadin halin da take aciki ba"
Fitowa sukayi daga kitchen din suka nufi bedroom din Ana.
Abakin Door room din Suka dakata da yin tafiyar, Aneelerh ta kwankwasa mata kofa, kusan sau uku Tana buga kofar kafin suka jiyo motsinta ta cikin dakin, buɗe kofar tayi tare da leƙowa tana kallon su
Fuskarta a yamutse, idanunta sun yi jajir da su.
Murmushin yaƙe ta ƙaƙalo akan fuskarta, cikin girmamawa ta gaishe dasu tana ƙoƙarin 6oye damuwarta
"Wurin ki muka zo mu shiga daga ciki" mami ce tayi maganar, da sauri Ana ta matsa masu hanya suka shiga dakin, Daga tsaye suka tsaya tace mashi su zauna saman gadonta
Ummi tace"ba zama ya kawo mu ba, zuwa mukayi don muji meke damunki Ana, meke faruwa dake ne? Duk kin canza mana kin rame kinyi baƙi! Baki da lafiyane"?
La66anta na kerma ta furta"babu komai lafiyana lau madam, wallahi babu abun dake damuna"
Cikin kwantar da Murya mami tace"Kada ki 6oye mana komai, Ki ɗauke mu tamkar iyayenki, dan Allah ki fada mana damuwarki, In sha Allah zamu share maki hawayenki,
Mami na rufe baki Aneelerh tace"Ana please kada ki bani kunya, Saboda mun ɗauke ki da daraja shiyasa muka damu da damuwarki, Kina gani dai mami da ummi da kansu suka zo dakin ki yau duk don saboda sun damu dake, Idan kika ce babu abunda ke damunki, kinyi mana karya saboda babu yadda za'ai ki rame batare da ciwo ko wani abu ba, dole da akwai wani abu da baki son mu sani"
Gaba ɗaya sun ɗaga mata Hankalinta, Cikin kwantar da murya suke yi mata magana amma sai ta dinga ganin kamar suna yi mata faɗane, Dafe kanta tayi da hannu biyu tana ambaton sunan Allah tamkar musulma.
Muryarta na rawa take fadin"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, na roƙe ku ku ƙyaleni, ku tafi kawai, nagode da kulawarku agare ni,nagode"
Hankulansu atashe suke ambaton sunanta haɗi da tambayarta meke damunta.
Gaba ɗaya ta rikice masu, sai sambatu takeyi tana rokonsu akan su tafi subar dakinta, a karshe ta watsa da gudu ta shige toilet taja ƙofa ta datse. 😳
Kallon juna suka somayi da tsantsar mamaki da rudani aka fuskokinsu,
..mami tace"to fa, Anya kuwa lafiya"?
Ummi tace"bafa lafiya, Ni dai inaga kamar hada aljanu ke damunta.
Jikin Aneelerh yayi sanyi, tun datake da ana bata ta6a ɗaga mata murya ba sai yau da ta rikice masu tana korarsu daga dakinta, tabbas babu lafiya!
"Yanzu ya zamu yi da ita"? Mami ce tayi maganar,
Ummi tace"yakamata mu sanar da su Abie, dangane da halin da take aciki"
Sun jima a dakin Ana suna yi mata magiya akan ta fito daga toilet, amma taki fitowa a karshe dole suka hakura suka bar mata dakinta..
*Daular Obie Estate*
Gaba ɗaya Manyan matan Family din sun hallara a gidan Hateem domin yi masu bangajiyar tafiyar da su ka yi, musamman saboda zuwansu akayi masu shimfiɗa ta alfarma a katafaren Garden din gidan hateem, garden ne na alfarma cike ya ke da tsiro da furanni launuka daban daban masu ban sha'awa, ga wata irin ni'imtacciyar iska mai ratsa fatar jikin mutun, daga can cikin garden din akwai wani ƙaramin tafki wanda ke acike da tsaftaccen ruwa launin blue sky, inda fararen agwagi suke shawagi acikin sa, an tsara komai da kyau, a tsakiyar garden din akwai wani katafaren wurin zama, kewaye da ciyawar da aka yi wa ado, Lallausar darduma ce mai wani irin laushi a jikinta irin ta sarakuna, An kewayeta da tuntuye, yayin da suke a zaune kowaccensu ta ɗauki wanka na kece raini na mutunci, mata ne masu duniya, ajin farko, waɗanda suka gaji arziƙi tun kaka da kakanni, wayayyune masu ji da ilmin da Allah ya basu, mace ta farko Gimbiya mujeedat ce a kishingiɗe saman dardumar tayi shiga ta alfarma cikin tsadaddiyar Arab gown launin Ash colour anyi mata adon sparkling stones, masu ɗaukar ido, ta yafa mayafin saman kafaɗarta, baƙar sumar kanta ta sauko har saman dardumar da suke, daga gefenta First Lady ce Hajiya Malikat Sarauta ƴar sarkin Yarbawa jihar Lagos, Mace mai ji da kanta, mahaifiyar Chief Owais, A launin fata chocolate colour ce, taji hutu, bata da yawan fara'a, tana da ƙaramin baki ga dogon hanci, idanunta masu kyan gaske sunyi kama da Asian eyes, kayan jikinta Na yarbawa ne, Wrap around skirt ta sanya tare da farar shirt, anyi mata naɗin head akanta, tun daga kan wuyanta har hannayenta adone na zinarai, bayan Hajiya Malikat sai Hajiya Laurat uwar ji da izza, ƙanwar Alhaji Musa, Idan ka gansu atare da Hajiya malikat baka ta6a gane cewa kishiyoyine saboda kowaccensu bata ɗaukar raini, ita malikat arziki da sarauta ta gada, ita kuma Laurat Arziƙine gare su na fitar shari'a, sai dai daga ganin fuskarta zatayi rashin mutunci idan aka ta6a, daga ka kalli fuskarta zaka shaida ƙanwar Alhaji musa ce, Kamanninsu har sun 6aci da shi, hatta launin fatarsu kala ɗaya ce, Hausa fulani ce, ta ɗauki wankan shadda launin dark brown anyi mata ado, Wuyanta na asanye da sarƙar diamond, haka yatsun hannayenta zabban diamond ne masu kyalkyali da daukar ido.
Mace ta gaba, Hajiya Madina ce matar senate Lateef, barumaya ce, tana da hasken fata da tarin sumar kai, hatta gefe da gefen fuskarta akwai tsagensu na rumawa, Tana da kyau iya gargado sutura tanayi mata kyau, daga ganin fuskarta tana da kyakkyawar zuciya ko ba'a faɗa maka ba, Hadaddiyar atampa chiganvy ce a jikinta tabi shape din jikinta, Itama ta dauki nata adon na zinarai.
Bayan Ita sai matar His excellency Deen, Hajiya Jamila, Bafullatanar usili ce, Ƴar sarkin Jihar adamawa state, Fara ce jawur da ita, tsabar kyanta kamar ba'indiya.
Daga ita sai Matar Abdul Razak, Her excellency Muhibbat, Shuwa Arab ce ƴar mai duguri, fara doguwa ga gashi har gadon baya, family dinsu sunyi ƙaurin suna a 6angaren Arziƙi, Mace ce mai ji da kyawu da wadatar arziki, tana sanye cikin shiga ta bubu gown ta lace, ta kashe ɗaurin kallabi, awarwaron dake a hannayenta na zallar zinari ne.
Mace ta karshe basai nayi maku bayaninta ba, Kun riga da kun santa, bakowa bace face Aunty Masifatu Hajiya saratu, mutuniyar, wankan material ta ɗauka, gaba ɗaya ƙamshin turarensu Ya karaɗe iskar garden din hakan ba ƙaramin ƙara ma yanayin ni'ima yayi ba.
Daga tsakiyarsu Katafaren Faranti ne na azurfa, mai girman gaske wanda masu hidima suka kawo masu shi, An cika shi da Soyayyun Kaji jar suya, da kayan marmari nunannu, tare da juice masu sanyi.
Fira su ke yi atsakaninsu cikin harshen turanci tamkar ba su son furta magana.
"Naji daɗin ziyarar da kuka kawo min, kuma naji daɗin ganinku, Sai naji dama A ƙasar nan nake zaune, saboda mu runƙa sada zumunci a tsakaninmu akai akai" gimbiya mujeedat ce tayi maganar tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
"Ni kaina naji dadin haɗuwar da mu ka yi, bazan Iya musalta farin cikin da nake a ciki ba, Allah Ya ƙara Haɗa kawunanmu da zuri'armu" hajiya malika ce ta fada, tare da kai hannu ta ɗauki Yankan Tufa tana sha.
"Canada tamkar gida take awurina ina yawan zuwa saboda business din da nake yi Acan, In sha Allah zan dinga zuwa Ina kawo maku ziyara, Har sai kun gaji da ganina" hajiya Laurat ce ta faɗa tana duban gimbiya mujeedat, murmushin gefen fuska Mujeedat ta sakar mata tare da lumshe idanunta.
Hajiya Jamila tace"naji kamar kuna Bankwana, Tun Kafin jibin tayi ko kun manta da family dinner da zamu Yi a gobe?
Hajiya saratu tace"Kamar kin shiga zuciyata, nima tun ɗazu maganar da nake ta so Inyi masu kenan, ai gobe muna da gagarumin shagali In Allah yakaimu da rai da lafiya, dole kowa ya halarta" ta faɗa tare da kai hannu cikin faranti Ta yago cinyar kaza ta tura abaki tana tauna
Hajiya jamila na dariya tace"daɗina dake saratu baki wasa da cikin ki, Zaman mu anan kin cinye fiye da rabin kaza, shiyasa gaki nan kullim ƙara ƙiba kike yi,"
"Kinsama kanwar nan tawa ido" acewar Gimibiya mujeedat.
"Kibarni da ita aunty, da duk wani mai sanya min ido akan cin abincina, nasan maganinku, zanyima yayyena magana su ƙara maku kishiyoyi, ƙwara ku lalla6ani ku dinga lallashina idan ba haka ba kun san sauran" dariya su ka yi gaba dayansu,
"Meya yayi zafi, nayi shiru bazan ƙara tanka maki ba, Ci ki ƙoshi, Idan ma kina buƙatar ƙari zansa akawo maki" hajiya jamila ce ta faɗa tana tura mata farantin agabanta, Hajiya sarah tayi dariya da zolaya tace"Bari naja bakina nayi shiru, naga wasu sun fara haɗe min fuska saboda nayi maganar kishiya"
Murmushi kowannansu ya saki,
Gimbiya mujeedat tace"ko kaɗan banji fargababa, because I know who my husband is. He doesn't want to remarry; I'm enough for him." She said proudly and gently.
Hajiya laurat tace"ai dama irinku ba'ayi maku kishiya, wane mutun, ballanta kuma mijinki da gaba ɗaya rayuwarsa acikin turawa yayita, ba lallai Yana da wannan ra'ayin ba, tun da suma mace ɗaya su ke aure"
Her excellency Muhibbat ta murmusa tare da cewa"ni dai koban fada maku ba kun riga da kun sani, ba'ayi mana kishiya, Mijina bai ta6a gigin kula wata ƴa mace ba"
Hajiya malikat dake sauraransu tace"nima nan bada jimawaba zansa mijina yayi waje da wata" ta faɗa da zolaya tana kallon Hajiya laurat, dariya suka sanya gaba ɗayansu.
Hajiya Laurat tace"Ni da sharafudden mutu karaba takalmin kaza, badai mutun ba sai Allah, me raba ni da shi sai mutuwa"
Yamutsa fuska Hajiya malikat tayi"alfarma fa nayi mashi ya aure ki, saboda yana jin shakkar tunkarata da zancen auranki yasa shi ƙin sanar dani sai dai naji daga saman an shafa fatihar auranku, wato yanzu kin samu wurin zama shiyasa har kike da bakin fadin mutu karaba takalmin kaza," cikin raha suke Yin firar tasu.
Hajiya Muhubbat tace"ai ni ina mamakin dauriyarku da har kuka Iya haɗa kanku, babu mai jin sirrinku, Gaskiya kun burgeni, amma ni fa wallahi bana tunanin zan Iya zaman lafiya da kishiya, shiyasa tun kafin abdul razak Ya aureni saida muka ƙulla yarjejeniyar bazai yi min kishiya ba, mahaifina ma saida Yaja mashi kunne akan hakan"
Jinjina kai Hajiya madina tayi'lallai abun naki azimin ne, ni kuwa dai bana jin zan Iya hana Mijina Yin aure, tun da Allah ya Halasta masu auren mata har huɗu, Idan Ya nuna yana so zan goyi bayanshi, kuma Idan Ya aurota zamu yi zaman lafiya da ita idan har ba ita bace ta bijirema hakan ba"
Wani kallo her excellency Muhibbat Ta yi mata"babu zuciya a kirjinki, Shiyasa bakya kishin mijinki"
"Bawai don bani da kishi bane, nafiso idan ma kishin zanyi inyi irin na matan manzon Allah SAW, ni fa da ace mijina Yana bin matan banza ƙwara ya auro mata uku a lokaci ɗaya, amma idan nace zan tauye mashi hakkin shi in hana shi auran abunda yake so to fa zan jefa shi ga halaka ne, sannan ban Isa In hana zuciyarshi son wata ƴa mace ba"
Jinjina kai su kayi jin bayanin Hajiya madina badan sun fahimce ta ba.
Hajiya Jamila tace"godiya yakamata muyiwa Allah daya bamu mazaje nagartattu, nagari masu ƙaunarmu tsakani da Allah, Har Yau Ina alfahari da kasancewata ɗaya daga cikin surukan dattijon Arziƙi, Allah Ya saka mashi da gidan Aljanna, Ya haifa mana zaratan maza sadaukai, Tsakaninmu dashi sai son barka" Murmushi hajiya saratu tadinga saki jin ana yabon mahaifinsu, wani irin dadine Ya lullu6eta
Hajiya Muhibbat tace"Ai Zuri'ar Obi komai sun haɗa Allah Ya basu, kyau, nasaba, ilmi, wadatar arziƙi, ƙawayena har tambayata sukeyi wai babu sauran ƴa'ƴan shi da suka rage? Don su aura suma su shigo daga ciki, nace masu sai dai Jikokinsa ƴa'ƴan cikin su in suna so" dariya sukayi gaba ɗayansu.
Bayan sun lafa, kowaccensu Ta sanya hannu a faranti ta dauki abunda take son ci, wasu nama Wasu kayan marmari wasu kuma lemu suke sha.
_______________________🌹✍️
A hankali Motar Sir Mubarak Tashigo Gidan Hateem, A Harabar ajiye motoci yayi parking dinta, fitowa yayi daga front seat ya zagaya ta back seat Ya bude ma mom turai kofa, A hankali ta fito ta sanya atampa riga da skirt sunyi mata kyau, Ta yafa mayafi saman kafadarta, yayin dashi kuma yake asanye da Shadda.
Kallon juna sukayi, da sauri ta kau da idonta gefe, hannunta ruƙe da ƴar handbag dinta
Muryarta ƙasa ƙasa ta furta"dan Allah kabarni in koma gida, bansan meyasa ka tursasa min akan inzo gurinsu ba, na faɗa maka basu ƙaunata, wallahi ci mun mutunci zasuyi"
Ɗaure mata fuska yayi"kar na kuskura nasake jin kin furta maganar nan! bana jin dadin yadda kike ware kanki daga cikinsu! Dame suka fi ki? Tsoron su kike ji? Baki Iya mayar masu da martani in suka gaya maki magana"?
Tuni idanuwanta sun cicciko da ƙwalla muryarta tamkar zata fashe mashi da kuka tace"Ina da banbanci dasu, Har Yau har gobe sunƙi mantawa da matsayina agidanku, Suna yi min kallon ƙasƙantacciya Ƴar aiki, babu abunda Ya canza"
*DAGA ALƘALAMIN HAFSAT BATURE✍️*