Hamratul Yazeeda Page 2 by Alkamawa

Hamratul Yazeeda Page 2 by Alkamawa

Novels to read English

 HAMRATU'L    YAZEEDA

Page two

 STORY AND WRITTEN

          By 

 NUSAIBA ALKAMAWA✍️

Dedicated to yazeeda and HAMRAT

 HAMRAT

________Kiran sallar da ake ne yasa hamrat dakatawa dayin rubutu SBD muhimmancin sallah inba lalura ba batason rashin ƙinyin sallah akan lokaci,bata haɗa sallah da komai kome take ,domin kuwa sai sallarka tayi kyau sannan aikin ka zaiyi kyau.kafin afara duba aikinka sai anfara duba sallahrka Allah yasa mudace .rufe littafin tayi tasaka a drowerta ta garƙame da wasu key me madannai .

Azuwan idan ta idar zatazo ta karasa labarin iya inda take so yau ta tsaya.

" dauko sallayar ta, tayi ta shinfiɗa sannan "ta tada  sallah,cike da nutsuwa take sallar ta."

" bayan ta idar ta daga hannu tana rokan Allah tana xubar da hawaye shafa addu'ar tayi,SBD kukan dayaci karfinta.

",kuka take kamar zata shiɗe Amman wani abun mamaki,da nagani shine bai wuce dariya danaga tanayi ba alokaci guda wanda yasanya, nayi mata ƙuri da ido ina mamaki.

" cen naji tace Allah yabani Sa'a awanann karon,tashi tayi cike da farin ciki tana fatan yau ƙudurinta yacika.

" toilet tafaɗa tayi wanka sannan tafito ta nufi dressing mirror tashafa mai da hoda sannan tasanya kwalli da iya lips stick domin kwalliya, ba damunta tayi ba.

_________" bayan tagama tasaka ƙananun kayanta riga da skart ne skit ɗin irin me bin jikin nan,domin hamrat takware a irin shigar ƙananun kaya.

" dauko baƙin glass ɗinta tayi tasanya Sannan tadauko takalmi da jaka tafashe jikinta da turare.

" aikuwa baƙaramin kyau tayi ba, fitowa tayi tana taku,ɗai_ɗai ,duk da taga Dady da aunty a dining area Dady yanacin abinci aunty na kokarin zuba nata, Amman hakan besa ta nufi wajansu  domin su gaisa ba.


",aranta  Murmushi take wanda nakasa gane ma'anarsa, karo suka kusaci da atine me aikinsu."


 "yahkuri hajiya HAMRAT."


 "ban kula dake bane ba.


" cikin zakaƙƙiyar muryarta tace la babu komai mama atine fatan kintashi Lpy?


"Lfy  klau Hajiya karama kema ya kika tashi?


" Lp....aumu laifin me mukayi da baza agaishe muba iyih, my only daughter? 


"Dady yakatse mata maganar da takewa atine.


",wani irin turnuƙin bacin rai ne yakara turniketa Amman afili ,fuskarta bai nuna komai ba .


"Dady,cike da son ƴar tasa kwalli daya kaɗai aduniya yakara cewa daughter HAMRAT,"Yakamata kixo kici abinci kafin kitaf....."tarine ya turnikeshi wanda yasa yakasa karasa maganar.


"tarin nasa yayi ƙarfi aunty kuwa sai sannu take masa haba abu kamar wasa sai yazama gaske, dan Dady warwas yayi aƙasa tamkar babu rai.


*********

 altine da aunty sai salati suke aunty tace innalillahi wainnailahi rajiun Alhaji meyasa meka ?"dan Allah katashi.


" plz HAMRAT ki zo mutaimaka mishi mukaishi asibiti.


"cikin halin ko inkula hamrat tayi wuce warta

cike da murna tana fatan haƙan ta yau ya cimma ruwa .Mai gadi ne yashigo SBD ihun Aunty da atine da yaji da sauri yadagashi wanda Dady tuni babu rai wata farar kumfa tafito abakinshi.


______ wani pravet asibitin aka kaishi cikin gaggawa aka karbeshi aka shiga dashi emagency aunty tana addu'ar Allah yasa ba mutuwa yayi ba .
 *HAMRAT* 


___________ darect ma aikatar su ta wuce tashiga office ɗinta.


 "cike da nishaɗi take aikinta,kamar wani abu bai faru da ita ba.


 __________ringtone ɗin wayarta taji,Saida takusa katsewa sannan tadaga.


" shuru tayi daga ɗaya ɓangaren akace "Assalamu alaiki."


 "wslm alaika,tafaɗa kawai tayi shuru.


"Barka da warhaka ranki yadaɗe, sunana Halifa r_k mawaki kuma darector a kannywood.


 ohk ,kawai tace tayi shuru,  ,am ina bibiyar rubutunki ne, shine nace idan babu damuwa inaso nazo muyi Magana.


" ohk to, zanturo maka da address ɗina tana gama faɗan haka kawai takashe wayar Sbd tana so abata dama tayi tunani.


"shikuwa Halifa Rk cikin Rashin jin daɗin abinda tayi masa mekama da wulaƙanci yayi shuru.


" aminu dake kusa dashi yace dama Halifa nafaɗa maka yarinyar nan yar girman kaice kama ci Sa'a ta amince maka ,"hmmn aminu kenan dan ina ganin alfanun da zan samu acikin al'amarin ne kawai yasa xanjure k....baikai ga ƙarasa maganar ba ƙarar massage yashigo wayar tasa.   


*******

da sauri ya duba yanawa Allah Godiya daya bashi wannan babbar damar. *ASIBITI* 


___________Asibiti kuwa Saida likitoci sukai dagaske sannan aka samu, aka shawo kan matsalar, cike da jimami likita yafito.


" da sauri aunty tatare shi tana tambayar lpyr me gidan nata.


" am biyoni office nayi miki bayani.


" babu mutsu ta bishi, kallonta likita yayi yace ya akayi alhaji yasha guba?


",cikin mamaki aunty tace guba kuma likita?


" eh guba me karfi kuwa, wanda da ba'a kawo shi da wuri ba, da tuni yarasa rayuwarshi.


" innalillahi gaskiya banace alhaji da sanin kansa, xaisha guba ba abincin shi nakarshe kuma agida yaci, Amman nidai bansamu naci ba.


______ Amman Kodai menene zan bincika.


" yakamata dai  ko kuma asa hukuma aciki Allah yabashi Lpy, zaki iya tafiya .


_______tashi tayi cike da rashin kwarin jiki ta nufi dakin da  Dady yake taxauna tana kallonshi, cike da tunani kala _kala.
*******


Kishingiɗa tayi sbd  typing din datayi tagaji sosai.


" knocking akayi ta bada izinin shigowa.


________shigowa yayi bakinshi dauke da sallama," amsawa tayi, tayi masa kallon daya ta kauda kai,zama yayi suka gaisa yace sunana Halifa R_k nine wanda mukai waya dake ɗazu.


" ayya nagane ya akayi? tafada cike da kosawa domin tana bukatar abata guri tayi tunani.


"Dama wani littafin ki nagani shine nakeso inba damuwa a mallaka minshi SBD inaso al'umma su amfana da darasin dake cikin labarin inaso ayi Film dashi.


Ayya aikuwa dai yau kaxo asa'a sbd  akwai wani abu da yafaru dani na farin ciki shiyasa xanbaka littafin amma Akwai mutanen da dama da suka nuna sunaso Allah bainufa zasu samu ba , wanda har makudan kudade suka saka Amma naki SBD wani dalili na .*****

Gaskiya ne ngd sosai da karamcinki to ya maganar price din ?


Badamuwa ko nawa xaka iya bayarwa nabakane tamkar sadaka.


Ayi haka? amma dai da kinfada ,ranki yadade.


" bakomai bayar kawai,cike da jindadi yaciro check yabata na 30million godiya yayi mata yace sai sunkara haɗuwa.


",yafita cike da farin cikin sa'ar dayasamu SBD zaisamu riba fiye da abunda yabata ga kuma daukaka da zai kara SBD marubuciyar ba kowa take bawa rubutun taba sai wanda ya cencenta tana aikine da basira da ilmi haɗe da fasaha .______Yana fita ta kalli check din ta yamutsa face, azuciyarta take aiyanawa da siyar da labarin tayi .


Zata samu  linkin baninkin wannan kuɗin .


" Amman SBD farin cikin dana ke ɗauke dashi yau yasa nabayar haka kamar sadaka,tana fatan Allah yasa ma Dadyn yau ya mutu kowama yahuta.


*******

 *DADDY* 


Alhaji ya akayi kaci guba abinci nifa gaskiya abun nan yafara bani tsoro haba so ai ba hauka bane ba kisan kai fa taso tayi Kuma kasan ba wanann karo nafarko ba da tataɓayin abu makamancin haka ba aunty takarasa maganar cike da jin takaici.Murmushin ƙarfin hali Dady yayi yace" akan ƴata zan iya bada tawa rayuwar kuma idan aka taɓata tamkar Ni aka taɓa duk duniyar nan bani da kamarta kuma ina fatan kiyayyar da take min wataran ta koma soyayya ,Amman lefin da nayi mata nacenceni fiye ma da haka Galala aunty tayi tana kallon shi wato duk da abinda tasoyi Amman baiga laifin taba mako?" tace gaskiya alhaji ai so ba hauka bane ba kuma danme da police sukazo kayi musu karya kace cikin kane yaɓaci to indai ina raye saina tonawa wannan mara mutumci ƴar taka da bata ganin kowa da gashi asiri,saina kamata da hujja.Da kuwa kin raina kanki zanfito miki A Alhaji Ibrahim Khalil ɗina kuwa yayi kwafa yajuya mata baya tsananin bacin ran dayake ciki zai iya mata abinda bashine ba . *HAMRAT* 


Auntyna !auntyna !auntyna ruhina bazai samu sallama ba harsai kinganar da wanda yayi kuskuren nan kuskurenshi ,kitashi kicikamin burina,muryar take mata amsakuwa a kunnen ta  aikuwa firgigit hamra tayi tafarka daga ɗan barcin daya kwasheta batare da shirya mai zuwa ba yazo.


"Kiyahkuri ƙanwata SBD ke bana iya bacci bana iya walwala nashiga damuwa da kunci na tsani kowa SBD ke ciki harda duniyar ma me hade da ruɗu nikaina baxan taɓa samun nutsuwa ba harsai na cika miki kudurinki kanwata.


Tafaɗa haka tana goge kwallar da ta zubo mata.Daukan litttafin tayi domin tacigaba daga inda ta tsaya tafara rubutawa.........


******* *HAMRA'U* 


________Abangaren mai gyad'a kuwa tashi yayi da kyar yakade rigarsa yanufi gida  yana ɗingishi sbd turewar da akayi masa bata wasa bace yabugu,yana shiga mamanshi yafaɗawa abinda yafaru daman itama tasan halin su Hamra'u,babu shiri tadau mayafinta ta nufi gidansu haule daman tare da Dan suke tana zuwa ko sallama babu tafaɗa gidansu haule tafara kwada kira, goggo tafito daga kitchen tana cewa me haulen tayi kike kwada mata kira haka ?


" talatu  tace karar 'yarki nakawo sun samu ɗana sunkarbi gyad'anshi basu bashi kudin ba sannan suka dakeshi suka tafi.


"Yanzu talatu akan

 gyad'an kika zaro mayafi kikazo amsar kudi harkinamin kumfar baki?


" talatu tafarayin masifa nan goggo ta hayayyako mata datagadai goggon tafita iya masifa  sai talatu ta wayince tace nidai zuwa nai kija mata kunne,ki musu tsakani da ɗana tana gama faɗan haka  tafita.


" , gidansu Hamra'u tanufa sallama tayi  inna ta amsa sannu dazuwa talatu ga guri zauna,aa nifa bazamane yakawoniba karar Hamra'u nakawo naxone da  kija mata kunne  karta kuma shiga harkar ɗana , mekuma Hamra'u tayi cewar inna, gyada suka cinyemin suda haule kawarta,  tafaɗa tana dokawa inna harara "Dan Allah talatu kiyi hakuri kinsan yaran yanzu sai ahankali , hmm ai wllh darajarki kawai takeci wllh amma shikenan babu komai ." tana fita sukaci karo da Hamra'u kallon sama da kasa tayi musu tanayi tana murguda baki da fari da ido,sannan ta kalli ɗan tace watakam ƙarata ka kawo shine kadauko wannan matar mekama da fuskar biri , aikuwa ran talatu inyayi dubu yabaci ai batasan lokacin da tadamki hannun HAMRA'U ba ita kuma Hamra'u jin andamki hannunta harya farai mata zafi yasa ta gantsarawa talatu cizo saurin sakin hannunta tayi cikin jin zafin cizo, ita kuma hamratu aguje tafada gida hartana bige inna tafada daki tasaka sakata,itama matar tabi bayanta .Itakuma inna salati tafarayi tana cewa waya tabamin ke shikenan daga fita baza abarki kisha iska ba ,komawaye anyi asararre,bata gama rufe bakiba talatu itama tafado gidan  

Tana cewa wllh yau sainaga me cetonki anan gidan Dan ubanki "kul kul karki kara zagin ubanta Dan wllh kika kara zagin baban ta saina miki rashin mutunci, toma mekika tsayayi baki tafiba bayan minyi sallama dake?

 

"Ina fita nahadu da wannan shedaniyar yarinyar  dakata! karki kara kiran jikata da shedaniya meyasa dakika ganta kika tsaya biye mata kina matsayin babba masifa talatu tafara tana cewa daman  bakyasan lefin Hamra'u shiyasa take abinda ranta yakeso , eh naji amanace agurin iyayenta suka bani tayaya zanso lefinta indan kudin gyadane ungo nabakima nera d'ari 

Kece matsiyaciya mika mata kudin tayi takarbi kuwa kudin babu kunya sannan tafita daga gidan suda yaranta .Fitowa tayi tana turo bakinta gaba tace ni wllh inna duk nagaji da wannan garin 

Duk suntsaneni ni wllh naga Dama saina koma gidan dady nazauna achan ."Kekyalesu duk yan bakin cikine SBD sunganki kyakykyawa shiyasa suke bakin ciki kuma duk bakin cikin da suke miki sai sunga mijin dazaki aura insha allah.


" , dariya Hamra'u tayi tace wllh inna na auri irin Dan gidan dadyn birni da namore miji da kullum saina zauna NATA kallanshi SBD kyanshi, gashi kamar Dan India gakuma kuɗi,dariya inna tayi tace inma mufeen ( mufeed ) 

din kikace zaki aura saikin aureshi , rike haba Hamra'u tayi tace rufan asiri inna yaushe zanyarda na aureshi kullum yayita jibgata sarkin mugunta Chan wllh badaniba gashi dai ina da wayo sodaya yataba dukana bazan taba mantawaba kuma Allah ya isana.


Nidai bawai wannan zancen ba angama abincine?gashinan jeki d'iba yana tukunya zubo abinchin tayi taci tana gamawa taje tayi sallah sannan tadauki

Allonta tanufi makatantar allo, sai wajan la'asar aka tashesu, tana dawowa tayi sallar la'asar wajan magrib bayan tayi sallar tadauko sabbin kayanta,tasa Riga da skart ,dadyn birnine ya d'inka mata gashi d'inkin yazauna mata  kamar Wanda aka gwadata shape dinta yafito sosai

SBD Hamra'u gashidai yarinyace amma akwaita da diri Dan wandama yaganta saiyace takai shekaru shabakwai saidai yarintarta kana gani kasan yarinyace  shagwab .


Hamra'u chocolate colour CE gata da hancinta daidai misali shiba dogo sosaiba shiba gajere ba , gatada manyan idanu dara _dara kuma idanunta kamar Wanda takejin bacci alumshe gata da tsayinta daidai misali amma yanzu indai kaganta saikazata kamar bakace SBD ruwan kauye Daya rinar da ita.

  


  (Wacece Hamra'u)

Aysha Ibrahim salisu shine cikakken sunanta mlm Salisu shine yahaifi Adam da Ibrahim, adam  ne babba sannan Ibrahim Allah yayiwa mlm salisu rasuwa tun Ibrahim yana karami,matarshi tayi kukan rashin mijinta sosai, mai suna Aisha (inna)


Suma sunyi kukan rashin mahaifinsu jajirtace ahaka dai mahaifiyarsu take Sana'a take samu take ciyar dasu  har Adam yakawo karfin Sana'a yatafi birni Sana'a kuma yaje asa'a , yahadu da wani maikudi yadorashi akan kasuwanci dakuma plaza daya bude Adam ne manager  da haka dai shima yafarayin kudinshi nakanshi Yagina plaza dinshi nakanshi atakaice dai Adam shima yayi kudi Dan yanzu yana daya daga cikin masu kudin kaduna ta harkar kasuwanci, kuma yana taimakawa talakawa, ahakadai yasamu wata budurwa mai suna fateemah , fateemah kyakykyawar yarinyace Dan fulaninesu 

Fulanin Adamawa tazo kadunane wajan wani Dan uwan babanta ahanya yazo hucewa yaganta tashiga gidan baidai mata magana ba saida yayi bincike akanta akace masa bakuwace saida, yaje gidan dan'uwannasu ,shima baiyi musuba SBD yasan alhaji Adam mutumin kirkine baiyi musuba yafadawa Dan uwannashi, dafarko mahaifin yarinyar baiyardaba SBD yafisan yarinyarshi tazauna akusa dashi bayasan tayi auran nesa.Amma daga baya saida d'an uwanshi yasan yadda yayi yanusar dashi har yayarda,  shikuma alhaji Adam yafara zuwa wajan fateemah zance itama ta amince mai suka fara soyayya harya kawo.kudin aure, sannan yadauketa yakaita kauyensu wajan inna itama tayaba da hankalin yarinyar.


_____Andaura aure ankai amarya gidan mijinta bayan wasu watanni amarya ta haifo d'anta namiji kyakykyawan gaske ,

Mekama da mamanshi amma kuma haryafi mamanshi kyau duk kyanta to yanunkata, shekara shida tsakani tasake haihuwar danta namiji mekama da babanshi shima kyakykyawa akasamai Ibrahim Khalil, ananne kuma shima Ibrahim yayi aure ya auri matarshi kyakykyawa,bafulatana anan garin take itama ,saida sukayi shekara d'aya tahaifi yarta mace kyakykyawa gaske kamar ita taikanta , akasa mata sunan inna wato *aysha* ananne babban Dan alhaji Adam mai suna yakub, amma anace mai mufeed Dan alokacinma yana shekara goma shadaya shine yazabawa aysha sunan daza ana faɗa mata wato *hamrat* akauyenne akece mata Hamra'u mufeed yanasan hamrat sosai SBD yarinyar akwai Shiga ran mutane .


 alhaji Adam yabiya musu saudiya gabaki dayansu harda yaran duk suka tafi har inna, inna sai kukan farin ciki takeyi bayan sundawone Adam yace sudawo Kaduna dazama amma fir "inna" taki ahakadai yahakura yakyalesu Dan shima Ibrahim yace bazejeba SBD yafison zama da inna, wajan shekara uku da zuwa aikin hajji dasukayi Ibrahim suka shirya dashi da matarshi, zasujai ziyara wajan Adamu zuwa Kaduna amma hamrat sunbarta awajan inna, suna kanhanya tsautsayi ya ritsa dasu Dan yanfashine suka taresu, suka kashe nacikin motan gabaki dayansu, hardasu Ibrahim da matarshi hajiya hauwa  mutanen kauyen sunji mutuwarsu, alhaji Adam yagirgiza da mutuwar kanin nashi da matarshi." inna kuwa tasha kuka bakadan ba , bayan anyi wata biyu Adam yace su taimaka sudawo kusa dashi yafi samun nutsuwa, 

Sam alokacinma inna tace bazataba.


" dayace kuma abashi hamrat shima tace bazata bashiba, SBD intana ganinta kamar taga fuskar ɗanta ne

Badan yasoba yahakura yakara gyare musu gidansu, yayi kyau yadawo nazamani duk kauyen babu Wanda yakai nasu kyau haryafi na mai gari ma..


No 09030567767

     Or   07036162215

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post