Yadda ake tsaftace Hammata

Yadda ake tsaftace Hammata

 Body Hygiene


YADDA ZA A TSAFTACE HAMMATA:

Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan filin namu na kwalliya. A yau na kawo muku yadda ake da hammata. Idan an gyara jiki kada a manta cewa akwai inda ya fi muhimmanci da a kula da shi. Musamman ma bayan an aske gashin gurin, akwai hanyoyi da za a bi don hana wajen yin baki. Ababe da dama ne suke kawo hammata ta yi baki koda an aske gashin gurin. Yawan zufa da amfani da man cire gashi gashin hammata da yawan kiba da kuma amfani da turare masu karfi a hammata.

GA HANYOYIN KAMAR HAKA

AMFANI DA MAN KWA-KWA:

Babban abin da ake amfani da shi a wajen hada man zamani shi ne man kwa-kwa domin yana dauke ne da sinadarin kara haske kuma yana da vitamin E. 

A shafa man kwa-kwa a hammata a kullum a yi minti goma kafin a yi wanka. Bayan an yi haka, sai a wanke da sabulu mara karfi (wanda sinadaran da akan hada shi ba mai zafi ba ne) da ruwan dumi.


AMFANI DA GURJI DA LEMON TSAMI:

Kamar yadda aka sani cewa ruwan lemon tsami na dada hasken fata, haka kuma gurji shi ma na dauke da sinadarin kara wa fata haske da kuma sanya ta laushi da sulbi. A hada ruwan lemon tsami da markadaddiyar gurji a guri daya sannan a shafa a hammata. A bari ya jima na tsawon mintuna goma sannan a wanke da ruwan dumi.


GARIN KURKUM DA KWAI: 

Kurkum ma na dada wa fata haske, za a iya kwaba garin garin kurkum da ruwan kwai sannan a shafa a hammata bayan mintuna goma zuwa sha biyar sai a wanke da ruwan dumi. A kullum kafin a yi wanka. 

Aski; a daina barin hammata da gashi a yi kokarin aske shi a lokacin da ya fito. Domin idan da akwai gashi a hammata, zai hana gumi bushewa zai fara tara shi yayi ta ba da wani irin wari. Sai a ga koda an fesa turare, sai a ji kamshin turaren daban, warin hammata kuma daban.

Yin amfani da wadannan ababen wajen gyaran hammata zai rage warin jiki da kuma hana fesowar kuraje da fitowar bakar kala a karkashin hammata da kuma rage gumin hammata.


HANYOYI GOMA (10) WANDA ZA A BI DON GYARAN JIKI:

Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan fili namu na kwalliya. A yau na kawo muku hanyoyi goma wanda za a bi don gyaran jiki ba tare da an kashe kudi a shagon kayan kwalliya ba. Ya kamata mata su koyi dabaru da dama domin taimaka wa maigida. Idan maigida ya saba ba da kudin sayan kayan kwalliya, ranar da babu kuma sai a hakura a gwada daya daga cikin ababen da muke kawo muku na gyaran jiki. A sha karatu lafiya.

  1.  Idan ana so a gyara gashi za a iya hada ayaba da kwai sai a kwaba su sosai sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar (15) zuwa talatin (30) sannan a wanke.
  2.  Domin gyara farce, za a iya tsoma hannu a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar (5) sannan sai a cire a kullum. Farce zai yi matukar kyau sosai.
  3.  Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai santsi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar (15) zuwa ashirin (20) sannan a wanke da ruwan dumi. A gwada wannan hadin sau daya ma a sati za a ga canji.
  4.  Ana amfani da ruwan amfuna da ruwa ana wanke kai. Yin hakan na cire dattin da ke makale a gefen gashin kai.
  5. 5⃣- Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rika shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka bakin da ya bayyana a wasu gabbai ko sassan fata.
  6.  Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaba sai a rika dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.
  7. Man kwa-kwa na matukar gyaran zubewar gashin ka. Za a iya shafa man kwa-kwa a fatar ka, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa daya sannan a wanke.
  8. Maza masu son man gyaran gemu, za su iya amfani da man kwa-kwa.
  9. A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai. Sannan a rika shafawa a kan kurajen fuska. Yin hakan na kashe su sosai.
  10.  Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata

Sai kuma kula da tsaftar zahiri da ta shafi jiki, tufafi, gida da duk bangarorinsa har da ban daki, kayan gida, kayan abinci, rariyar ruwa. Sai miji da mata su taimaka wa juna tun a matakin farko na tsafta da ya hada taimaka wa wurin wanka, cudanya bayan juna, busar da jiki da tawul, sanya tufafi, shafa mai, sanya turare.

Yana da muhimmanci matukar gaske mu kula da tsaftar jikinmu, ma fi muhimmancin tsaftar da ya kamata mu kula kanta ita ce wacce a matakin farko muke iya cutar da mutane idan ba mu kiyaye ta ba, da farko zamu ga warin baki da na hammata sun fi damun mutane, kuma suna nuna mana kimar mutum da darajarsa a matakin farko.

Idan ma’aurata suna son samar da gida mai nishadi da zama abin koyi a cikin al’umma to sai su kiyaye wannan tsaftar hatta a cikin gidajensu, su kiyaye wanke bakinsu da burash da makilin, su goge hakoransu da harshensu kowace safiya, su shafa body spray a hammata bayan wanka, idan akwai hali sai su hada da turare a tufafinsu. Su kula da yankan farshe, aske gashin gaba, gyara fuska, kawar da fason kafa, gyaran gashi ko kitso ga mace, kayan shafe-shafe da jan baki ko farce ga mace, da sauran abubuwan da zasu ba ta ado ga mijinta.

Ma’aurata suna iya yi wa junansu askin duk wani bangare na jikinsu da ya hada da gabansu da hammatarsu da yanke wa juna farce da makamantan hakan. Tsaftar jiki ita ce asasin farko na nishadin rayuwar mutum shi kansa balle kuma idan yana tare da mutane, ballantana kuma abokan taraiya a rayuwar duniya kamar miji da mata. Duk wani wari da yake fita daga jikin mutum yana da matukar gudummuwa da yake bayarwa wurin dasashe kaifin tunanin mutum da hazakarsa, sau tari mutanen da suka rayu suna shakar wari ya kasance sakamakon dakelewar tunaninsu. Hada da cewa wari yana haifar da cututtukan da suke halakar da mutum ko yada cututtuka wasu ma masu wuyar magani, ko kuma ya haifar da cutar da ba a san maganinta ba.

Gashi wuri ne da yake boye cututtuka don haka ne shari’a ta yi umarni da aske gashi musamman gaba da hammata a duk sati, haka ma farce wuri ne da cututtuka suke labewa don haka yanke shi yake da muhimmanci ta wannan fuskar. Gashin namiji yana bukatar tajewa lokaci-lokaci, haka ma gashin mace yana bukatar gyara ko kitso a lokaci-lokaci, gashi wuri ne da duk wata dauda take labewa, don haka gyara shi ya ke nuna darajar

Haka ma tsaftar sauran gabobin mutum take da muhimmanci; warin kunne, ko hanci, ko baki, mutuwa ke nan. Wari ne da suke misalta jahannamar duniya kafin barzahu, idan mutum yana da warin kunne ko hanci ko baki ya yi gaugawar samun likita don kawar da wannan bala’in da yake kawar da duk ni’imomin rayuwa. Rayuwar mutum ta yi ban kwana da nishadin rayuwarsa da ta abokin zaman rayuwarsa matukar yana da warin kunne, baki, hanci, da sauransu, kuma ya yi ban kwana da samun sukuni a cikin al’umma. Idan dai akwai adalci ga kai ko ga abokin ko abokiyar rayuwar tare to mai wannan cutar zai gaugauta koma wa likitoci don kawar da wannan cutar.

Wanke duk wani abu da yake iya yin wari idan ba a wanke shi ba yake da muhimmanci, sai a goge baki sosai da hakora da harshe kafin da bayan bacci ko cin abinci. A wanke bayan kunne yayin wanka, a goge cikinsa da auduga a cire duk wata daudar kunne. A kula da hanci ka da a bar shi da majina ko tasono ko wani abu da zai sanya shi wari. A yayin wanka a kiyaye sosai a wanke wasu bangarori masu rike dauda da boye ta, sai a kula da wanke tsakanin cinyoyi, kasan nono ga mace, hammata, wuya, kafafu, tsakanin ‘yan yatsu, wurin faso, da sauransu.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post