Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe episode 3

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe episode 3

 _~*✊💋BOSS LADIES WRITERS✊💋✊*~_
        _🔥💫THE PRISONERS🔥💫_            ~TAKUN ƘARSHE~ Daga Alƙalamin Boss Bature                  Dedicated To Aunty Kubra💋

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty❤._
_______________________✍️Shessheƙar kukan Khadeeja ne Ya fara cika kunnanta, Zaro ido waje turai tayi muryarta da alamun ruɗani ta furta"Wacece ke kuka"?


  "Khadeeja ce, Ina Jazz ɗina Yake" kafin Turai ta bata amsa kiran Ya katse, abun ya ɗaure mata kai, Ya akai wayar Jazz taje hannun mace? Maimaita sunan khadeeja tayi aranta kafin da sauri ta fito daga dakin ta nufi bedroom dinsa.


A lokacin suna daga zaune gefen gadon shi, Shi da Ibad dake bashi abinci abaki, hannun ibad ruƙe da plate with spoon, har yayi wanka ya sanya jallabiya a jikin shi.


 Shigowa mom Turai tayi dakin gaba daya suka dago suna kallonta.


  Ajiyar zuciya ta sauke fuskarta da fara'a ta ce"My son, how's your body? I hope you're getting better now."


 In a cool voice yace"Mom da sauki, ina samun kulawa a wurin ƴan uwana, yaya Zaki ma bai jima da fita ba"


 Murmushi tasaki tana kallon Ibad tace"our last born, Sannu da ƙoƙari,  kana Ji da ɗan uwan nan naka"


  Ta6e baki yayi kafin yace"to ya zanyi mommy, daddy ya 6allo mana aikin Jinya, Yana can kwance Kinyi mashi wanka Yana bacci, Ya ya Zaki kuma ya gudu ya barni da aikin bashi abinci abaki"


Tuntsirewa tayi da dariya, shima jazz ɗin dariyar yake Yi, shi kuwa ko ajikin shi bilhakki dagaske Yake Yin maganarshi.


  Tsagaiwata tayi da yin dariyar tace"Ibad na fahimci maganata ta tsaya maka aranka, Nifa ba daddynku nayi ma wanka ba, Taimaka mashi nayi ya rage kayan jikin shi, idan ba haka ba ni taya zan Iya yi ma shi wanka ƙato dashi, Kallarni ka gani Ƴar ƙarama dani" hura mata hanci yayi batare da yace komai ba


 "Jazz where's your phone"? Ta faɗa tana kallon shi.


He was silent for a while, Yana ƙoƙarin tuna inda Yabarta.


 "Mom, kamar nabarta a gidan Yaran da nake Kula da lafiyarsu"


 Miƙa mashi wayar tayi"Duba ka gani, wata yarinya ta kira da layinka, tana kuka, wai jazz dinta take nema"


  Da mamaki akan fuskarshi Ya kar6i wayar, Yana duban Kiran da akayi da layinshi, tunkafin Ya danna kiran ranshi ya bashi cewar Khadeeja ce.


  Da sauri Ya kira layin, ringing uku ta ɗauko tana fadin"Ni ku ƙyale ni tun da ba zaku bani muyi magana da Ya jazz ba, kun wani isheni da kira,"


  Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarsa, jin muryar deejan sa, mom turai da Ibad sun tsareshi da ido suna kallon fuskarshi.


  "Khadeeja ni ne fa" a kwance take kan gado Jin muryarshi Yasa Ta yi zumbur ta miƙe zaune tana fadin"Ya Jazz dama baka mutu ba"? da wani irin farin ciki ta furta maganar.


  Murmushi ya saki tamkar yana a gabanta yace'ban mutu ba My deeja, lafiyata qalou, Yanzu haka ina agida, wannan layin da kika kira, Na mom ɗina ne"


 Shagwa6a ta sanya mashi" I hate U ya jazz, Shine ka manta dani, duk nabi na tashi hankalina akanka ashema kana gida"


"No, it's not like that, Khadeeja. I miss you. I've been thinking about you tun time din dana dawo hayyaci na"


 Kallon juna mom Turai da Ibad su ka yi alokaci ɗaya, kafin suka maida dubansu gare shi.


  "Faɗamin Kin yi breakast da safe kuma kin sha maganinki"?


"Ni ban sha uban komai ba, babu wanda ya bani, waɗancan ƙattan da aka bar mana agida jiya suka cinye mana abincin mu, yau kuma na sanya su dole su girka mana, aiko suka shiga kitchen suna yi, basu sani ba na ɗauki bindigarsu nadinga tsoratar dasu hawwa......." hankalinta kwance take kora mashi jawabi, a firgice ya ɗago da ido yana kallon Mommyn su, ga dukkan alamu suna jin maganar da deeja take Yi mashi,"


  Muryarshi a ruɗe ya furta"Dagaske kike ko wasa"?


 Dariya tasaki kafin tace"Wallahi dagaske nake maka, don ma sun min wayau sun kulleni a ɗaki, ai da tuni na kakkashe su"


Zaro Ido Ibad Yayi, Mom Turai tayi dariya, gani su ke yi kamar zolaya ne abun da yarinyar take faɗa ma jazz, shi kuwa yasan zata aika, Fiye da haka ma shiyasa ya ɗauki maganar ta serious.


  "Khadeeja, Ina fata baki raunata kowa acikinsu ba"


 "Wlh ban kashe kowa ba, ai na faɗa maka sun ƙwace bindigar"


 Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke

"Dan Allah My baby girl kada ki ƙara yunƙuri ɗaukar bindiga kinji ko?


 "Toh,"


 "Yawwa ai nasan kina jin magana ta, idan har kina so na zo gidan karki ƙara rashin ji," muryarta a ladab ce tace"In sha Allah" kamar wata mai hankali


 "Good Girl, Kafin nazo kiyi wanka, Kici abinci ki ƙoshi," tace "Toh"


 "Namanta ban tambaye ki ba, Where did you find my phone?"


  "Aɗaki kabarta saman kayanka, nan na ɗauke ta"


 "Okey, pls Ki ajiye min inta, kada kice zaki yi wasa da ita"


 "Toh, Idan kazo gida zaka gyara min gashin kaina kuma kayi min kalar kitson kalaban nan da ka ta6a yin min"


 Da sauri ya ɗago suka hada ido da mom Turai.


 Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Eyyeh, Lallai ashe Jazz har kitso ka Iya yi ma mace, gama wayar ka bani labari"


da zolaya ibad yace "mommy kin huta, da zuwa saloon, daga yanzu Jazz zai dinga yi maki gyaran gashi" miƙa mashi hannu tayi suka tafa kamar wasu abokai.


  Duƙar da kai Jazz yai"Khadeeja sai anjima, please take care of your self for me"

"You too,"  sallama su ka yi da ita.


 Kunya duk ta kama shi, sai faman sunnar dakai ƙasa Yake Yi.


"Jazz kai muke sauraro ni da mommy" ibad ne yai maganar.


 Fuskarshi a yamutse ya furta "Khadeeja ce yarinyar da daddy ya baku labarin ta, She's mentally ill. There's no love between us. ina kula da ita ne saboda rashin lafiyarta"


mom turai da raha tace "Don't lie to me. I'm your mom and I understand you. Yarinyar  nan dai sonta kake Yi" shiru yayi bai ce komai ba, don yasan da wuya ta fahince shi, zolayar shi suka dinga yi tun yana ɗaure fuska har yakai ga sakin dariya.


______________________✍️A hankali Motar su Ta shigo gidan, bayan jami'in yayi parking, Salsabeel Ya fito daga ciki Yayi mashi sallama kafin ya nufi ƙofar shiga falo.Yana shiga falon ya hango su Hawwa zazzaune kan carpet, An jera masu kayan abinci saman Tray, komai da Khadeeja ta ba sojojin Umarnin su girka masu saida suka girka shi, tun daga kan Chicken pepper soup, fried fish, Chips, wainar kwai, Doya da kwai.

     

Gyaran murya yayi masu tare da buɗe baki Yayi sallama, A hanzarce suka ɗago suna kallonshi, aiko da sauri suka miƙe da sauri hada gudu suka nufeshi, ɗaya bayan ɗaya yake rungumarsu a jikinshi.


 "Ya salsabeel Ina kaje tun jiya baka dawo ba, Ka tafi kabar mu da kewarka"

Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Eyyah am sorry, nima nayi kewarku, ay min afwa wani uziri ne Ya ruƙe ni, amma tunda na dawo yanzu komai ya wuce"

  Yayi maganar idanuwanshi akan fuskokinsu

  "Ina Khadeeja"?

Nan fa suka haɗa baki suna bashi Labarin Ta'asar da Khadeeja tayi ma sojojin da aka bar masu.


 Hankalin shi ya ɗan tashi sai dai baiyi mamakin abun da Khadeeja ta aikata masu ba, ya riga daya san halin kayanshi.


Jin motsin tafiyar mutane yasa shi saurin kai idonshi inda suke.


 Fitowarsu kenan daga kitchen, wanke wanke Suka tsaya yi a kitchen din sun gyara komai da suka 6ata, har sun maida suturarsu.


   Wani ɗan iskan kallo suka watsa ma Salsabeel, Hakan Ya tabbatar mashi da ransu Ya 6aci sun harzuƙa.


  Tamkar mai jin shakkarsu ya furta"Am...dan Allah Kuyi haƙuri, Yanzu na shigo gidan su Hawwa suke bani labarin abun da khadeeja ta aikata maku, banji dadi ba, Yalla6ai ne bai bani damar dawowa da wuri ba, da duk hakan bata faru ba....."


  Fuskokin su babu annuri ko miskala zarratin

  Tiger yace"malam bamu buƙatar Jin komai daga bakin ka, tun da ka dawo gidan falillahil hamdu, Ka ci gaba da kula da ƴa'ƴanka, Mu kaga tafiyar mu sannan duk abun da ka gani badai dai ba kada ka tuhumi kowa, Khadeeja ce sila" Rai a6ace Ya ƙare maganar, Ya nufi Dining table Ya duƙa ya dauko masu bindigoginsu.


  Army boy yace"Zan baka shawara, Yarinyar nan ku gaggauta kai ta Gidan Mahaukata, can ne Yafi dacewa da ita, Idan ba haka ba wata rana zaku kuka da kanku, don wannan tafi bomb bala'e" 


 Army na kammala yin maganar suka nufi ƙofar fita daga falon, da sauri salsabeel Yabi bayansu yana basu haƙuri.


  "Dan Allah Ku tsaya, bai kamata muyi irin wannan rabuwar ba, nasan ban kyauta maku ba, amma dan Allah kuyi hakuri kada ku ruƙe mu aranku"


 Ta6e baki su ka yi, Tiger yace"hmmm bakasan masifar da yarinyar can taso taja mana ba, shiyasa har kake da ƙwarin gwiwar Yi mana magana, Badan Allah Ya kawo mana mafita ba, da yau mu dukan mu zamu baƙunci lahira"


 Jiki asanyaye Salsabeel Yace"ina ƙara baku hakuri, Allah Ya huci zuciyarku"


  "Dama ahuce take, bamu hanya mu wuce" matsa masu hanya yayi, duk bai ji ɗadin abun da ya faru da su ba. har suka fuce bai daina bin bayansu da kallo ba.


   Sai da yajiyo tashin motarsu, tukunna ya sauke ajiyar zuciya, Ya juya ya kalle su Hawwa.


 "Awani ɗaki suka Kulle ta"? Sarah ce Ta nuna mashi kofar dakin, Azafafe Ya nufi upstairs, Yana isa bakin ƙofar Ya sanya hannu ya murɗa key din.


 Tsabar 6acin rai ko sallama baiyi ba ya faɗa ɗakin, a gaban mirror ya taras da ita zaune, ta sanya undy ta jashi har saman kirjinta, ga dukkan alamu wanka tayi shine ta zauna tana gyara jikinta kamar wata mai hankali.


  Gyaran murya yayi mata, zumbur ta miƙe tana faman ƙyafƙyafta idanuwanta, hannayenta biyu ta ɗaura asaman kanta kafin tace "sun faɗa maka abunda na aikata"?


Takaici ne Ya ishe shi wato har tasan ta aikata badai badai ba.


 "Meyasa"! Aɗan tsawace Ya jefa mata tambayar, Ta6e mashi baki tafara yi alamar zata fashe mashi da kuka da sauri Ya zare mata ido haɗi da cewa"Yi min shiru! kar in kuskura Inji kukan ki," da buɗar bakinta sai cewa tayi"ai dama ba ka so na, Kafi son su hawwa, shiyasa kake min fada" sassauta fushin fuskarshi yayi tunawa da karancin hankalinta 


 "Am sorry, raina ne Ya 6aci, bawai bana sonki ba, pls ki daina rashin ji dan Allah"


Washe mashi baki tayi "Nadaina, bari na ɗauko maka wayar Ya jazz, na kira shi har mun gaisa ashe bai mutu ba Yana nan da ranshi" ta faɗa tana dariya ta juya ta nufi gado ta dauko wayar taje ta miƙa mashi Yasa hannu Ya kar6a.


da mamaki yace "Taya akai ki ka yi waya dashi"? Watsa hannu tayi"nima bansani ba, na daddana saina kira,"

 Call log Ya shiga, numbar farko data bayyana ta Mom turai, Ya danna ma Kira, Bayan ta ɗaga wayar cikin girmamawa salsabeel Ya gaishe da ita, daga bisani Ya tambayeta Ya jikin jazz, tace mashi da sauki, bata tambayi wanene shi ba sai ta ba Jazz wayar suka cigaba da yin magana,


Hankalin shi ya kwanta Jin muryarshi raɗau tamkar bai ta6a yin ciwo ba, sun jima suna yin wayar har jazz ya tuna mashi da maganin khadeeja kafin suka yi sallama Ya adana mashi wayar a hannun shi

  Tattara Yaran yayi a falo, hada shi suka zauna suna kwasar girkin da Su Tiger suka Yi masu, dama da yunwar shi Ya dawo, aikuwa dai sunyi kullu wash rabu hani'an, su mama Tiger An Iya girki, sai santi su ke yi, musamman khadeeja, bakinta dama dama da maiƙo.


 

 *🌹ZEENATU🌹*Baiwar Allah, Ta hana zuciyarta sukuni, tun lokacin da tayi masu Benazir la6e a toilet, kunnuwanta suka jiyo mata maganganun da suka tsaya mata aranta, haƙiƙa tayi danasanin sauraransu, don tun safe take faman jinyar zuciyarta, kiri kiri taki cin breakfast dinta, har lunch bata ci ba, yini tayi a cikin bedroom dinta da raɗaɗin abun azuciyarta, Tani tayi ƙoƙarin shawo kanta donta faɗa mata meke damunta taƙi ta sanar da ita, ba irin lallashin da ba ta yi mata ba amma taƙi sakin jikinta.


A yanzu haka tana daga kwance saman prayer mat, ta lullu6e jikin ta da dogon hijabinta launin milk, daga gaban dardumar qur'anic stand ne an bude shi alamar karatu take cikin yi bacci yayi awon gaba da ita.


Damuwar halin da take aciki Ya hana Tani samun sukuni, fargabanta kada ace wani abunne ke shirin faruwa da ita shiyasa ta canza mata.


Shigowa ɗakin tayi domin gyara mata bedroom din, karaf idanuwanta suka sauka akan zeenatu dake ƙudundune tana bacci.


   Cikin takun sauri Tani ta nufi dardumar, aranta tana fadin'baiwar Allah, daɗina da ita duk halin da zata shiga bata mantawa da yin ibadarta"


  Zuƙunnawa tayi agaban prayer mat din, muryarta ƙasa kasa ta ambaci sunanta.


 "Zeenatu! Zeenatu! Ki tashi ki koma kan gado ki kwanta, kwanciya kan prayer mat, bai da amfani jibi yadda ki ka ƙudundune kanki duk kin takure kanki"


 Tani sai zuba takeyi babu alamun zeenatu zata farka,

  "Oh Oh ni wannan baccin naki bame ƙarewa bane da alama, dan Allah ki tashi" still bata tanka mata ba.


  Hannu ta ɗaura saman jikin zeenatu ta bubbugata, nan ma taƙi farkawa, lokaci ɗaya Tani ta fara Jin fargaba acikin zuciyarta, hankalinta yayi mugun tashi, a ruɗe ta ɗaga murya tana ƙwala mata kira da sauti mai karfi"Zeenatu! Zeenatu! Nashiga uku, Wayyo Allahna, meke faruwa dake ne, Zeenatu dan Allah ki tashi" jikinta na rawa ta soma kiciniyar tu6e mata hijabin data ƙudundu ne kanta aciki daƙyar ta samu ta yakice hijabin ta nannaɗeta gefe daya kan darduma, koda Tani ta ɗaura idanuwanta akan jikin zeenatu saida gabanta Ya faɗi, ganin wata irin zufa dake tsastsafo mata ta ko'ina, Rigar jikinta ta manne ma fatarta, sumar kanta kuwa duk ta yamutse babu gyara, shafa wuyanta Tani tayi nan fa taji yaɗauki zafi sosai.A gigice ta miƙe ta watso da gudu ta nufi babban falon gidan, a lokacin Dr shureim Yana daga zaune kan Sofa, Benazir tana a gefenshi, fuskarta ɗauke da murmushi take kallon shureim dake bata labarin ƙuruciyarta.


Kamar mahaukaci haka Tani ta nufo su ta zagayo ta gaban Sofas din, kusan atare suka dago suna kallonta da alamun ruɗani akan faces dinsu

 Dr shureim Yace"Tani! Lafiya? Meke faruwa"?


  Sai faman yarfa hannu take yi duk tabi ta ruɗe.


 "Pls ki buɗe baki kiyi mana magana" acewar Benazir, daƙyar ta iya tattara natsuwarta wuri guda, da karfin hali ta furta"Zeenatu ba lafiya! Tana acan daki rai hannun Allah, kwata kwata bata motsi..." kafin ta ƙare maganar, da gudu Dr shureim da Benazir suka nufi part dinta, tsabar sauri mayafin jallabiyar Benazir har faɗuwa yake yi kan kafaɗarta da sauri take sanya hannu ta gyarashi, Tani tana abiye da bayansu.


 Suna shiga ɗakin idanuwansu suka sauka akan zeenatu dake a kwance magashiyan tamkar bata numfashi.


  Slowly dr shureim ya zube agabanta kan gwiwowinsa, ya sanya hannayenshi biyu ya tallabo da kanta ya ɗaura saman laps dinsa, Benazir ta zuƙunna gefenshi, fuskokinsu da alamun ruɗu suk soma ambaton sunanta"Zeenatu! Zeenatu"!


"Tani, bata da lafiya ne"? Benazir ce ta jefa mata tambayar

Muryar Tani tamkar zata fashe da kuka tace"wallahi ban sani ba nima, yanzu nashigo ɗakin na taras da ita a kwance, nayi tsammanin ko bacci ta ke yi, amma dana kira sunanta na bubbuga jikinta taƙi farkawa nan fa na gane babu lafiya atare da ita"

A faɗa ce Benazir tace

"Tayaya za ki ce bakisan meke damunta ba? Bayan ke ce kike kula da bedroom dinta"

Tani dake kallon Benazir duk tasha jinin jikinta

 "Bansan ya zanyi maki bayani ba, ba laifi na bane, tun safe nake fama da ita akan ta fadamin meke damunta taƙi ta sanar dani, na rasa gane kanta ta ƙuntata kanta aɗaki, ta hana kanta sukuni yinin yau" hawaye har sun fara sauka kan fuskar Tani.


  Jiki asanyaye Benazir tace"bari naje na faɗa ma su Mommy abinda ke faruwa" A firgice Tani tayi hanzarin dakatar da ita ta hanyar shan gabanta muryarta na rawa ta ke ambaton" inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, dan Allah ki rufa min asiri kada ki faɗa masu abunda ke faruwa, wlh zasu Iya korata daga gidan nan, ba lallai su fahimce ni ba, Alhaji musa baya raga mana akan Zeenatu, Idan yaji wannan maganar babu makawa zai kore ni ne"


Cikin rashin fahimtar kalaman Tani, Benazir tace"dan Allah malama ki bani hanya in wuce, kina ganin yarinya babu numfashi sannan ki hana in fadama Iyayenta, hakan bazai yiwu ba dole suji ko dan akira likitan ya duba ta" a tsiwace Benazir tayi maganar, tare da bi ta gefen Tani ta nufi ƙofar fita dakin.


  Zubewa Tani tayi saman gwiwowinta hannayenta biyu asaman kanta, yayin da hawaye ke yin sintiri akan kuncinta.


 "Dr shureim nasan kai zaka fahimce ni, dan Allah ka hanata fita daga dakin nan, wallahi idan ta faɗa masu halin da ake ciki, bani kadai zata ja ma bala'e ba, duka ma'aikatan gidan nan zata shafa"


  Ɗagowa dr shureim yayi, launin idanuwanshi har sun canza kala, muryarshi adidashe Ya ambaci sunan benazir, Harta ɗaga ƙafa zata ƙetare kofar ɗakin tayi saurin cin burki jin kiran shureim.


  Juyowa tayi miryarta da faɗa tace"yaya shurem kada ka biyewa matar nan, akan me zata hana afada masu halin da ƴarsu take aciki, so kike mu rufa maki asiri, mu zuba ido muna ganin yarinya bata motsi har wani abin da ba'a fata ya faru da ita ko"?


 Fashewa Tani tayi da kuka, abun duniya ya isheta.


 Cikin sanyin murya dr shureim yace"Sister calm down ur mind, Zeenatu suma tayi ki miƙo mun ruwa in yayyafa mata, sannan kada ki sanar da kowa, mu jira muga awani yanayi zata farka, Idan ba lafiya dole mu sanar da mutanan gidan don akira mata doctor" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta nufi ƙaramin fridge dake a dakin ta buɗe ta ɗauko bottle water taje ta miƙa ma shureim yasa hannu ya kar6a.

 Kowan nan su fargaba ce azuciyarsa, musamman Tani jikinta yaƙi daina yin kakarwa 

  Kusan sau uku dr shureim Yana yayyafa mata ruwa a fuskarta batare da ta motsa ba, Har sun fara fidda rai  a lokacin da ba su yi tsammani ba suka ga Taja dogon numfashi tare da sauke shi, da wata irin kasalalliyar murya ta firta"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"


Atare suka hada baki suna ambaton sunanta"Zeenatu! Zeenat"

Firgigit ta ware blue eyes dinta akan fuskokinsu, launin farin idon ya canza sosai

Wata irin nauyayyar Ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke

 "Zeenatu, fada min meke damunki"? Tani ce tayi maganar

 Cikin kwantar da mirya Benazir tace"Sister ɗina, baki da lafiya"? Da ƙyar zeenatu take buɗe idanuwanta sunyi mata nauyi saboda kukan da tasha, fuskarta tayi jawur.


  "My zeenat" jin miryar dr shureim yasa tayi saurin wurga eye balls dinta akan fuskarshi, wani sabon kukan ne ya kufce mata tamkar ranta zai fita, duk tabi ta rikitar da su.


   Hada baki su ka yi wuri lallashinta da kwantar mata da hankali daƙyar su ka shawo kanta, tayi shiru tana faman ƙyafƙyafta masu idanuwanta waɗanda ke ajiƙe sharkaf da ruwan hawaye.


  "Please faɗa min meke maki ciwo"? Dr shureim ne yai maganar, 

   Duk sun tsareta da ido

 Daƙyar ta iya buɗe baki ta furta"Yunwa nake ji" sunyi mamakin jin abunda ta fada masu badan sun yarda da maganarta ba,

 "Tani, dama zeenatu bata ci abinci ba?  Shiru tani tayi tana faman zare idanuwanta, banezir ta jefa mata kallon tuhuma kafin tace" Ɗazu da safe ke kika ce tace akai mata breakfast dinta a ɗaki Kenan baki kai mata ba "?

 Girgiza kai tayi Tani tayi"Na kawo mata abincin, Itace taƙi ci, ba yau ta fara yi min hakan ba, Idan wani abu na damunta bata cin abinci, kona tursasa mata akan dole taci, sai tace min in tafi zata ci, da zarar nabar ɗakin take daukar abincin ta shiga toilet da shi tayi flushing dinshi" har saida Dr shureim ya ɗan zaro ido jin abunda Tani tace, Zeenatu ta haɗe fuska ga dukkan alamu bata da gaskiya, Miƙewa benazir tayi da sauri ta nufi toilet jim kaɗan sai gata ta fito daga ciki fuskarta adaure babu walwala tace"Zeenatu baki kyauta mana ba, Fisabilillah haka ake rayuwa? Don wani abu na damunka sai kaƙi cin abinci? Maimakon ma in ba ci zakiyi ba ki bata ta mayar a kitchen sai ki zubda lafiyayyan abinci, kinsan fa ba kyau Almubazzaranci"


  Rufe ido zeenatu tayi, har lokacin bata ɗago da kanta daga kan laps din dr shureim ba.


  "Tani ki ci gaba da yin haƙuri da ita, In sha Allah zata daina very soon yanzu ki koma kitchen ki haɗa mata wani abincin ni zan bata da kaina"


  Muryar Tani asanyaye tace"To" kafin ta juya da sauri tabar dakin

  "Sister, nabar wayata daki ko zaki dauko min"

   Benazir ta amsa mashi da toh, kafin ta fuce daga dakin, Ya rage da ga shi sai zeenatu, dama da biyu ya aiki benazir ta ɗauke mashi waya.


  A hankali ya tallabo kanta ya ɗaura shi kan ƙirjin shi, tamkar ƴar baby haka ya ruƙe ta.


Wata irin kunyarshi ce ta kamata, taƙi bari su haɗa ido.


  "My zeenat, haka za mu yi aure kina yin min rigima? Ya kikeso inyi da rayuwata idan baki gyara halin nan naki ba"?


 Turo mashi pink lips dinta tayi batare da tace komai ba, murmushi yasaki yana mai mamakin ƙuruciyar zeenatu.


 "Faɗa min waya ta6a min ke"? Daƙyar ta ɗan iya buɗe ido ta harare shi kafin tayi sauri kau da idonta gefe, nan take ya fahimci wani abu.


 "Hakan na nufin ni na 6ata maki rai? Ko kinji maganganun da muka tattauna nida sister benazir ɗazu da safe"?


 Muryarta da shagwa6a tace" I heard everything, ya Shuraim! I won't marry you, because you lied to me. You told me that you had never been in love, bayan ba haka ba ne, sannan ka nuna min hotona amatsayin hoton da ka ke yawan kallo a phone din ka, ashe ba haka bane hoton wata ne daban, Why ya shureim? What did I do to deserve that?' she said, giving him a suspicious look.


 Aranshi ya ayyana zeenatu matsala, tun yanzu ya fara jin shakkar kishinta .


  "Ka tsare ni da ido baka ce komai ba Sannan har fadi kake yi wai ba zaka ta6a samun madadinta ba even if u get married" ranta a6ace ta ƙare maganar hawaye nabin fuskarta, hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta.


  Tun da take yin magana ya natsu yana bin fuskarta da kallo har saida ta gaji don kanta ta dakata da yin maganar tukunna ya samu damar bata amsa

  Calmly ya furta"My zeenat, baki fahimci kan zancen namu ba, shiyasa babu kyau yiwa mutun la6e, kalli yadda kika takura kanki akan abunda baki da tabbaci kansa" harara ta jefa masa"yaya shureim ni fa ba kurma bane, Ina ji ai," ta faɗa tana nuna mashi kunnanta da hannu.


 Murmushi yayi mata, ita ko sai ƙara haɗe mashi fuska take yi.


 "Bana son 6acin ranki zeenatu, don haka zan faɗa maki gaskiyar abunda na 6oye maki, saboda ina burin na aureki duk wani sirrina ya kamata ki sani, amma bana so ki faɗa ma kowa"


  Jinjina mashi kai tayi alamar Toh, shiru yai yana yanke shawara da zuciyarshi, ƙwara ya faɗa mata gaskiya idan ba haka ba zata ci gaba da yi mashi kallon maƙaryaci kuma ba sonta ya ke yi ba tun da yana da wadda yake kallon hotonta kullum bayan haka zata cigaba da yin jinyar zuciyartane tun da ita haka Allah ya halicce ta da kishin tsiya.


  "Dangane da hoton dana nuna maki naki, tabbas bashi nake kallo ba, hoton ƴata ne nake kallo....." tsabar firgita da jin maganarshi yasa zeenatu ta zabura ta sauka daga jikinshi ta koma tana fuskantar shi, idanuwanta azazzare, maganar  ta daki kunnanta tamkar a mafarki taji ta.


  "Yaya shurem na shiga uku, ƴa fa kace, dama ka ta6a yin aure hada baby"

  Girgiza mata kai yayi"a'a, Ni ban ta6a yin aure ba, na samu yarinyar bata hanyar aure ba...." bai kai ga ƙare maganar ba yaga ta ɗaura hannayenta biyu saman kanta alamar ta shiga uku.


 "Ya shureim dama kai ɗan iskane" dafe kanshi yai da hannu ɗaya


 "Idan ba zaki natsu ki saurare ni ba, zan tashi nabar ɗakin nan" da sauri taja baki tayi shiru.


Tuni yanayin fuskarshi ya canza sam baya son tuna abunda ya faru a rayuwar shi, tamkar yana faman raunin dake a zuciyar shi ne


Numfasawa yai kafin ya ɗaura da cewa "Bayin kai na bane, zan Iya cewa ƙaddarace ta afka min har hakan ya faru, a yanzu haka da nake baki labari, Yarinyar bata araye tun tana jaririya ta rasu, Tsakanina da mahaifiyarta bamu ta6a yin soyayya ba, daga ni har ita ba mu ta6a tsammanin zamu yi mu'amala da junan mu har takai mu ga aikata sa6on Allah, mun fuskanci matsanancin tashin hankali, abun da ya faru zeenatu shine silar ƙuncin rayuwar da na shiga.....   '


  Duƙar da kanshi ƙasa yayi tamkar mai neman gafara, hawaye tuni sun cika idanuwanshi, sam bayason tuna baya saboda tsohon raunin dake acikin zuciyarshi.


 Jikin zeenatu yayi mugun yin sanyi, har cikin ranta ta yarda da maganar shi, ta kuma ji tausayin shi.


  "Yaya shureim na yarda da kai, please forgive me for what I said. Rashin sani ne kuma nayi danasani, dan Allah ka daina zubar da hawayen ka, I know it's hurting your heart, amma kayi haƙuri"


  Matsawa tayi kusa dashi ta sanya tafin hannayenta biyu ta share mashi hawayen dake akan fuskarshi, wani irin tausayinshi ne ya kamata, da sauri ta rungumoshi ya ɗaura kanshi saman kafaɗarta itama ta ɗaura nata kan asaman tashi kafaɗar.


 "Yaya shureim ita babyn taka an riga haihuwarta kafin Ni"?


 Cikin rauni na murya ya furta"da ace tana araye da yanzu ta girmeki" cikin sigar lallashi take ɗan bubbuga bayanshi da hannayenta, ba tare da sun raba jikinsu ba taci gaba da tambayarshi Ya sunanta"?


  "*FATIMA*" atakaice Ya bata amsa

 "Allah sarki Ƴar uwata fatima, Allah yajiƙanta"

 "Ameen"

 "Ita maman babyn naka, meye sunanta" shiru yayi don baison furta sunan.


 Fahimtar hakan yasa tayi saurin canza akalar zancen nata


 "Yaya shureim idan aunty benazir ta kawo maka wayarka zaka nuna min hotonta dan Allah"

 "Zan nuna maki"

  A hankali ta ɗago da fuskarta, haɗi da daura idanuwanta akan fuskarshi, ta dafe kafadunsa da hannayenta

Ido cikin ido suke kallon juna

  "Idan mukayi aure nima zan haifa maka ɗiya, bama ɗaya ba Ƴan biyu zan haifa maka, sai mu sanya masu sunan Fatimarka" tunkan ta ƙare maganar tayi saurin dukar da idonta ƙasa

 Shi kanshi yayi mamakin maganar data furta mashi, saboda kunyar dake gareta amma ya fahimci tausayin shi ne Ya kamata.


 Shafa sumar kanta yai da hannun shi ɗaya"nagode da kulawarki agare ni,"

da buɗar bakinta sai cewa tayi"ya shureim pls ka sanar da daddyna da daddynka maganar auranmu, suyi sauri su daura mana aure, don in haifa maka fatima"


Dariyace ta kubce mashi, cikin jin kunyarshi Zeenatu ta yi saurin miƙewa ta nufi gado ta haye ta kwantar da kanta

Abun da basu sani ba, benazir tana la6e tana sauraronsu, hannayenta biyu ruƙe da Tray din abincin zeenatu data kar6a a hannun Tani

 Hankalinta idan yai dubu toh ya tashi, har sai da gabanta ya fadi, Jin zeenatu nayiwa shureim zancen aure, aranta tace"taya ma haka zata yiwu? Soyayya tsakanin Ya shureim da zeenatu ƴar cikinsa? Anya kuwa zeenatu tasan ainihin shekarun dr shureim? Lamarin ya ɗaure mata head.

 Shiga dakin tayi da sallama abakinta, dr shurem ne ya amsa mata sallamar, ta ƙarasa kan carpet din gefen gadon ta ɗaura mata tray din

 Idanuwanta akan fuskar Dr shureim, ya lura da kallon da take yi mashi sai dai bai kawo komai aranshi ba

 "Ina wayar"

Cikin aljihun jallabiyar jikinta ta zaro wayar ta miƙa mashi, Ya kar6a yana fadin"nagode sister,"

"Yayana, wani abu ya farune bayan fitana? Naga zeenatu a kwance kan gado"

"Taji sauƙin abunda ke damunta, dama ba wani ciwo bane" gyaɗa kai benazir tayi"Okey, mu taimaka mata taci abincin"

  Atare suka zauna da zeenatu suna bata abinci abaki, Hankalin benazir yaki kwanciya sai satar kallon dr shureim da zeenatu takeyi afakaice batare da sun ankara ba, har wani kallon ƙauna taga suna jefawa junansu, ita dai abun ya tsaya mata aranta, ya girmi tunaninta.......

  


*❤HAJIYA ADAMA🤍*A zaune take kan mirror chair, ta ɗauki wankan riga da zane na zallar leshi launin ruwan toka rigar tayi matuƙar yi mata kyau, ta ca6a adon zabba da awarwaro a hannunta, head dinta kala ɗayane da takalman ƙafarta black colour, Hand bag ɗinta tana ajiye saman gadonta itama launin takalmanta ce.


  A tsanake take shirya kanta, bayan ta gama shafe shafenta, ta kai hannu ta ɗauki turare tabi ko'ina na jikinta ta feshe, miƙewa tayi ta nufi gadon inda ta ajiye mayafinta, ta ɗauka ta yafa shi a kafaɗa, kafin ta ruƙo handbag din.

       Tana ƙoƙarin juyawa Uncle abdallah Ya doko sallama hannunshi ɗauke da baby junaid sunyi shiga kala ɗaya ta shadda blue sky.

    Murmushi tasakar mashi, da fara'a akan fuskar uncle abdalla yace"madam shanyar da ki ka yi ta bushe tun ɗazu ba ki je kin dubo ta ba"


   Farfari tayi mashi da ido"am sorry my husband, nabarku kunata jirana awaje"

     From head to toe yake binta da kallo har zuwa kan head din data ɗaura, komai nata burgeshi yake yi, Hajiya adama ta Iya ɗaukar wanka.


  Baby junaid sai faman lumshe idanunsa yakeyi sam baya fahintar komai biji biji yake ganinsu baccine ke neman yaci ƙarfinsa

  "Kullum ƙara kyau kike yi, faɗamin menene sirrin"?

 Still fuskarta da murmushi tace"bani da wani sirri daya wuce kai, Mijina, saboda kulawar da kake bani da tarairayata da kakeyi sune suke ƙaramin kwanciyar hankali da natsuwar da nake samu har kake ganin ina ƙara kyau"


Lumshe idanuwanshi yayi tare da waresu kan fuskarta.


 "Shiyasa nake ƙara ƙaunarki acikin zuciyata, samun mace irinki abune mai wuya a duniyar nan, kin haɗa komai hajiyata, kyau, nasaba, ilmi, abu mafi jan hankali agare ki, tsaftarki, da Iya girkinki, idan nace zan lissafa maki kyawawan ɗabi'unki da halayanki to kuwa zamu kwana batare dana kammala karanto maki ba"

 Tsabar jin dadin maganarshi ce tasata yin dariyar farin ciki

 "Kana ƙara huramin kaina fa,"

 "Ba hura maki kai nakeyi ba, Kin cancantane my wife" 

  "Thank u dear, for loving me and for everything" har cikin zuciyarta take fada mashi kalaman

   "Yakamata mu tafi, baby junaid fushi yake yi damu, munƙi kai shi wurin mommynsa" ya fada yana dariya

  Kallon fuskar baby junaid hajiya adama tayi, tuni bacci yai awon gaba dashi, Ya langwa6e kansa saman chest din uncle abdallah.


  "We will miss him. I love my grandson  bana son rabuwa dashi sai dai ba yadda zanyi dole na maida ma mamansa" yanayin fuskarta ne ya canza zuwa damuwa,

  " jin kaina nakeyi tamkar ban ta6a haihuwa ba saboda rashin Uzair, abun yana ta6a min zuciyata, shi kaɗai nake gani inji dadi, da kuma ɗan uwansa tajuddeen da baby angel dinmu Yanzu duk babu su ..." cikin jin ƙunar rai ta furta maganar, jikin uncle abdallah yayi sanyi, Shi kanshi abun yana damunshi.


 "Tunda na haifi uzair ban sake samun damar da zan haihu ba, saboda matsalar dana samu, mijina meyasa ba zaka kar6i shawarata ba? Nifa inason ganin jininka" idanuwanta sun cika tab da ƙwalla.


  Ɗaure fuska uncle abdalla yayi, tamkar bai ta6a yin dariya ba


 "That's enough! Bana so kina min maganar nan! Stop trying to pressure me into getting married. I have no intention of doing it, ke kaɗai kin ishe ni, kada na kuskura naji kin sake tada maganar," Yana ƙarasa maganar ya juya da sauri ya fuce daga falon, Bin bayanshi tayi, a harabar ajiye motocinsu, ta same shi tsaye ya jingina bayanshi jikin motar, harya kwantar da baby junaid, a back seat.


  Agabanshi ta tsaya tana ƙoƙarin shanye damuwarta tace"am sorry, idan ranka ya 6aci, bazan ƙarayi maka maganar ba,"

 Batare dayace mata komai ba ya nuna mata murfin motar, buɗewa tayi ta zauna a front seat, Ya zagaya ta other side ya zauna a driver's seat, key yayi ma motar, a hankali yayi reverse ya karya kwana ya fitar dasu daga cikin gidan, tunda suka haura kan titi babu wanda yayima wani magana acikinsu,    kowa da abunda yake saƙawa aran shi, idanuwan hajiya adama sun kaɗa jawur dasu, jefi jefi takan kai idonta ta cikin mirror din motar ta kalli baby junaid dake akwance yana sharar baccinsa, mutuwar son yaron takeyi, sam batason rabuwa dashi sai dai ba yadda zatayi.


  A hankali motarsu ta ƙaraso bakin gate din gidan Uncle ɗan Iya, Horn su ka yi Baba mai gadi Ya buɗe masu ƙofar su ka shiga daga ciki, bayan uncle abdallah yayi parking din motar, cikin kulawa ya dubi fuskar Hajiya adama

 "My wife," kallon shi tayi fuskarta a yamutse babu walwala

 "Kinsan ina sonki, and bana son 6acin ranki, zan Iya yin komai danganin na faranta maki rai, dalilin dayasa bazan dauki shawararki ba saboda gudun in jefa rayuwarmu cikin hatsari, ke kanki kinsani samun mace tagari wahala ne dashi a duniyar nan, ina jin tsoron in auro wadda zata yi silar tarwatsewar farin cikin mu, ko in auro maki Yarinya da zata raina ki, Ina fata kin fahimce ni"?

 Ajiyar zuciya ta ɗan sauke fuskarta  ɗauke da murmushi tace"na fahimce ka, mu shiga daga ciki" ta fada tare da buɗe murfin motar ta fito ta buɗe mazaunin baya ta ɗauko baby junaid ta rungume shi a kirjinta, ta rufe kofar, atare da uncle abdallah suka nufi entry hall na shiga gidan Uncle abdallah


Tunkafin su ƙarasa Aneelerh da zahra suka fito fuskokinsu dauke da fara'a sun dauki wankan Atamfa riga da skirt,  ɗaurin ɗan kwalinsu kala ɗaya, Aneelerh ta yafa Mayafi akanta, yayin da zahra ta daura nata mayafin kan kafaɗarta,

  "sannunku da zuwa, Ina wuninku," zahra ce tayi maganar, Uncle abdallah Ya amsa mata da Lafiyalou, Fatan mun same ku lafiya" ya faɗa yana kallonta tace"Lafiyalou,"

Kafin ta kar6i baby junaid daga hannun Hajiya adama, rungume juna sukayi ita da Aneelerh

 "Mommy sannu da zuwa, nayi murnar ganinku," Aneelerh ta fada tana murmushi ta dago da kanta, Itama hajiya adaman murmushin ta sakar mata

"Surukar arzuƙi, kullum ƙara kyau kike yi," cikin jin kunyarta ta dan dukar da kanta tana fadin"daddy Ina wuni Ya gida Ya aiki"

 Uncle Abdallah Yace"lafiyalou daughter, fushi nake yi dake, kinƙi zuwa kiga gidan mu"

 "Naso zuwa mommy adama ce tace nabari zata zo kawo shi, badan haka ba ai dani zan zo dauko shi daga nan ma har inga gidan, amma ay min afwa in sha Allah zan fidda lokaci ni da zahra mu shigo gidan" yaji daɗin maganarta

 Zahra tace"mu shiga daga ciki," ta fada tare da basu hanya suka nufi ciki, 

    A lokacin Mami tana cikin jera masu abinci a dining, Ummi kuma ta fito daga daki jikin ta sanye da hijabi, tana ganinsu ta nufesu fuskarta dauke da annurin farin ciki, Itama mami ta ajiye jeran abincin da take yi ta nufesu da fara'a suka gaisa da junansu, kafin suka zazzauna saman sofa, fira suka fara ta6awa a tsakaninsu, Zahra da Aneelerh suka basu wuri, Ɗaki suka shiga a saman gado Zahra ta kwantar da baby junaid tana fadin"Baby boy dinmu Yaji hutu, sati biyu kacal har ƙiba ya ƙara, fatarshi tayi kyau"

 Aneelerh tace"ni kaina na lura da canzawar da yayi, gaskiya mommy adama ta iya raino, kalli kumatunsa sunyi 6ul6ul da su" gaba daya suka sanya dariya

"nasan baby junaid ba ƙaramin ta'asa yayi masu ba, Allah kadai yasan adadin madarar da ya shanye masu" cike da shakiyanci zahra tayi maganar tana jan kumatunsa da hannunta

Aneelerh tace"kamar wanda yasha ƙwaya sai bacci yake yi yaƙi farkawa duk surutun da muke yi, Allah na gani nayi kewar babyna" daga gefen gadon suka zauna suna kallonshi kamar zasu hadiyeshi, farin cikin ganin shi ne Ya cika su

 "Auntyna bari naje kitchen in dauko mashi Cake dinsa nasan zai yi farin ciki idan Ya ganshi" Miƙewa zahra tayi jiki na rawa ta fuce daga dakin.


 Fitarta  ɗakin keda wuya Baby junaid Ya fara mutsi mutsin farkawa daga bacci, tunkan Ya buɗe idanuwanshi Ya fara  yin sambatu yana fadin Ni wurin mommyn baby zanje, ni ku kaini gidan mamana"

 Dariya Aneeerh tasaki batare da tace komai ba, ƙarasa buɗe idanuwanshi yayi Biji biji Ya fara ganinta kafin ya ƙara ware idanuwan akan fuskarta, zazzaresu yayi tamkar yau ya fara ganinta, muryarsa da shagwa6a ya furta"Mommyna, bacci nake yi ko mafarki" tuntsirewa tayi da dariya tare da sanya hannayenta biyu ta daukoshi ta daura shi kan laps dinta haɗi da rungume kanshi saman kirjinta

 "Baby mommy ni ce, ba mafarki kake Yi ba, mommy adama ta dawo mun dakai kana bacci"

 Fashe mata yayi da kuka Ya ƙanƙameta da hannayensa biyu, Hankalinta atashe ta ke fadin"My baby boy meyasa keke yin kuka? Maimakon kayi farin cikin ganina, ko ba ka so dawowo gida bane"?

 Cikin shessheƙar kuka yace"mom..my wallahi bazan ƙara zuwa gidansu kwana ba, Ni bazan ƙara tafiya in barki ba, duk inda zamuje sai dai mu tafi atare......" bata bari ya ƙare maganarba tai saurin toshe masa bakinsa da tafin hannunta, gudun kada su Hajiya adama su jiyo sautin kukanshi da maganarshi

"sorry my baby boy, Nima bazan ƙara bari kayi nesa dani ba, kayi hakuri idan hakan ya 6ata maka rai" dakyar ta lallasheshi Yadaina yin kukan

 Shafa sumar kanshi tayi da hannunta"yanzu fada min me ya faru bayan zuwanka gidan" tamkar baison furta maganar yace"Bakomai" dariya ta yi donta fahimce ranshi a6ace yake

 "Tunda bazaka fadamin ba, Ni zan fada maka meya faru bayan tafiyarka" ƙura mata manyan idanuwanshi yayi fuskarshi babu annuri

 "Idan dare yayi bana Iya bacci saboda rashin ka atare dani, nayi maraicinka my baby boy, bani da aikinyi sai tunaninka, dakai nake kwana dakai nake tashi, har mafarkinka nake yi, idan abun ya dame ni sosai, sai in dauki pillow Ina kuka ina Kiran sunanka, wayyo Allah baby junaid dina ka tafi kabarni....." da wasa takeyin maganar tana kwatanta mashi yadda ta ke yin kukan, Murmushi taga ya fara sakar mata hakan ba ƙaramin dadi yai mata ba

"Mommy kema kinyi kuka da bana nan"

Ɗaga mashi gira tayi alamar eh, dariya yasaki har fararen haƙoranshi suka bayyana tar dasu

 "Wallahi naji dadi, ke ma kinji abunda naji," wannan maganar da yayi mata ta bata dariya.


 Shigowa ɗakin zahra tayi hannunta ɗauke da plate daga saman shi chocolate cake ne, an ajiye cake knife daga gefe ɗaya.


 Akan table zahra ta daura mashi cake dinshi, kafin ta zauna daga gefen Aneelerh

 "Ashe Ya farka, rigimamme naga sai haɗe min fuska yakeyi, ko ba ka ji dadin ganina bane"?

 Washe mata baki Yayi idanuwanshi akan cake din data kawo mashi yace"na wanene wannan"?

 Aneelerh na murmushi tace"naka ne, aunty zahra ce ta haɗa maka"

  Wani irin farin cikine ya bayyana akan fuskarshi, da sauri ya sauka daga kan laps din Aneelerh Ya rungume Zahra yana fadin"I miss U sis zahra," dariya suka saki, Zahra tace"yau naci albarkacin cake, Har ana fadin Anyi missing dina, toh nagode Nima nayi kewarka our baby boy," ta fada tana shafa sumar kanshi

  "Ni zan yanka cake din" Ya fada Tare da raba jikinshi daga nata, da zumuɗi yakai hannu zai dauki wukar aneelerh tayi saurin rigashi daukarta"Ni zan Yanka maka" ba musu ya amsa mata da toh

Zahra dake kallonsu gwanin ban sha'awa tace"Aunty Aneelerh ki cigaba da tayani addu'a Allah Ya bani miji nagari inyi aure kafin in mutu, wallahi inason ƴa'ƴa idan ina kallonki ke da baby junaid sai inji dama ni"

Fuskar Aneelerh dauke da murmushi tace"in sha Allah zahra, zan cigaba da tayaki addu'a, very soon kema zakiyi aure har ma ki haifa mana babies"


 "Ameen Ya Allah Auntyna, Bari in dauko wayata Inyi maku hoto" acewar zahra, Ta miƙe da sauri ta fuce daga dakin, har zata gifta ta falo tajiyo sallamar Abie da Uncle dan Iya, da sauri takai idonta kansu, atare suka shigo fuskarsu dauke da fara'a suka nufi su uncle abdallah,

 Kau da idonta tayi da sauri ta nufi bedroom dinta ta shiga, akan gado ta dauko wayarta, ta ɗan dakata tana daddana wayar, wi-fi ta kunna ta shiga whatsapp dinta, messages ne suka fara shigowa ta ko'ina, wasu sakonnin daga abokan aikinta wasu kuma daga mutanan da suke mutunci dasu,

  Shagala tayi da karanta sakonnin mutane, har tazo kan sakon da Hajiya saratu ta tura mata tun jiya da marace bata gani ba sai yanzu, Gajiyar aikin da su ka yi ne ya hanata hawa whatsapp din jiya.


 Tsabar zumuɗi yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin buɗe chat dinsu

 Unexpected Tayi tozali da hotunan da hajiya saratu ta tura mata, Na twins dinta, Sunyi matuƙar yin kyau hotunan a ƙalla sunkai guda biyar, Hoto na farko  a london suka yi shi, Hoto na biyu sunyi shi a ƙasar dubai, sauran hotunan an dauke shi a dakin taron da aka gabatar da shagalin birthday din baba obie, Jiya kenan"

 Abun kallo ya samu, Komawa zahra tayi gefen gadon ta ta zauna tana mai mamakin turo mata hotunansu da hajiya saratu tayi? Takasa gane me take nufi da hakan.

Message ta gani daga ƙasan hoto na ƙarshw da sauri ta soma karanta shi kamar haka 


  

 


*Daga Alƙalamin Boss Bature🫶**Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post