Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 4

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 4

 ~TAKUN ƘARSHE~ 






_______________________Boss Bature✍️







 Rubutun dake a ƙasan hoto na ƙarshe ta karanta kamar haka

 

  _"If you had the chance to choose between them, which one would you like?"_


A ruɗe zahra take kallon screen din wayar, a ƙalla ta maimaita karanta sakon yafi sau a ƙirga, duk tabi ta ruɗe ga wani farin ciki daya lullu6eta duk da bata gane me hajiya saratu take nufi ba.


 Miƙewa tayi jiki na rawa ta fito ta nufi dakin Aneelerh.


 Tana shiga ta taras da su suna Cin cake, Ita da baby junaid.


  Jin motsin shigowarta yasa duk suka ɗago suna kallonta.


  "Zahra, meye faru naga kina murmushi"?


 "Aunty na, duba ki gani abun da hajiya saratu ta rubuta min" miƙa ma Aneelerh wayar tayi, bayan ta kar6a ta soma duba hotunan, Baby junaid dake cin cake Ya ce"Aunty Zahra, Kin iya cake, Yayi daɗi, Idan Angel dina ta dawo gida, zaki hada mata kalarshi"


 ɗaga mashi kai zahra tayi"me zai hana my baby boy, ai dole baby Angel taci cake" Murmushi yasaki"thank u sis zahra"


 Ɗagowa Aneelerh tayi ta ɗaura idonta kan zahra dake atsaye tana kallonta.


  "Na taya ki murna, wata'kil burinki ne zai cika, a fahimtana, Hajiya saratu tana son haɗa ki da ɗaya daga cikin ƴa'ƴan ta shiyasa ta baki za6i"


   Cike da kokwanton maganarta Zahra tace "Anya aunty Aneelerh? Gaskiya bana tunanin hakan, tayaya ma zata hada ni da ɗanta? Ni da ba yar kowa ba, nifa nasan masu kudin nan basa auran bare sai dai yasu yasu jinin arziƙi" cikin sanyin murya ta furta maganar"kuma ni waɗannan sunfi karfina wallahi, ko lokacin da muke zuwa gidan yi masu hidima basu yi ma mutane magana suna da girman kai, idan muka gaishe dasu da hannu suke amsawa, ko kallo ba mu ishe su ba"


 Dariya Aneeleeh tayi"kin bani mamaki zahra, sai kace bake bace kike da burin auran Chief owais, sai gashi yanzu kina maganar ƙannansa sun fi ƙarfin ki"


 Dariya zahra tayi"ki gane mana, Chief Yafi ƙarfina nesa ba kusa ba, Haukana kawai nake Yi, daga baya kuma na zauna nayi ma kaina karatun tanatsu, Na lallashi zuciyata na haƙura na barma Allah za6i"


Aneelerh na murmushi tace"Yanzu dai zoki zauna daga gefe na, In taya ki za6an wanda Ya dace dake, duk da naga kamannin su ɗaya ban iya banbanta su"


 Zama zahra tayi daga gefenta, hankalin baby junaid baya akansu, Ya samu cake sai ci yake yi duk ya 6ata bakin shi.


  Ƙura ma hotunan ido su ka yi"zahra idan hasashena ya zama gaskiya wani irin farin ciki za ki yi?


 "Mara misaltuwa" amsar da zahra ta bata kenan.


 "Za ki zama ɗaya daga cikin surukan Baba Obie, Uwa Uba ɗan gidan Hajiya saratu minister of health, gashi itace autarsu, gaskiya zaki more wlh gata ta ko'ina zaki samu idan familyn suka kar6e ki hannu biyu" da fara'a akan fuskarta ta yi magana.


Zahra bata ce komai ba, Ita dai gani ta ke kamar hakan ba mai yiwuwa bane


"A cikin su wanene ne yafi kwanta maki a rai"?


 Aneelerh ta jefa mata tambayar


"Aunty aneelerh nabar maki za6i dan Allah, Ni kaina bana iya banbanta su, amma kamar wannan shine Zayn idan kika kalli fuskarshi da kyau zaki fahimci yana da masifa" ta faɗa tana ɗaura yatsanta kan face din Zayn.


 Shi kuma wannan shine zaid a hasashena, Yafi zayn saukin kai.


  Aneelerh tace ƙwara mai saukin kan, akan mai masifar, amma fa kamar yafi kyawun sura.


Zahra tace"Eh, hakane, zayn yafi zaid.


 "Nidai nafi yi maki sha'awar zaid, indai yana da kyakkyawar zuciya"


 Shiru zahra ta ɗan yi kafin tace"An ta6a faɗamin basa jin magana, kamar suna kula mata, Har page dinsu na insta na ta6a shiga, suna yawan ɗaura hotunansu da matan banza masu bayyana tsiraicin su"


 Yanayin fuskar Aneelerh ne Ya canza zuwa damuwa.


 "Zahra kin tabbatar basu jin magana"?

 Ɗaga mata kai zahra tayi alamar eh

 Kwa6e fuska Aneelerh tayi"akwai matsala, but mommynsu tasan da hakan"?


 "Bana tunanin ta sani, saboda mutane suna jin shakkar yi mata magana kinga kuwa babu wanda zai Iya tunkararta da wannan maganar mara dadin ji"


 "Banji dadi ba zahra, Har na fara yi maki murna amma yanzu sai naji abun ya fara fita raina, bazan hana ki za6ar wanda kikeso ba acikinsu, Idan Allah yasa sanadin shiriyarshi ce sai kiga ya shiryu ta silarki, babbar matsalar shine ace baya sonki, da ace idan ta haɗa kun zaku son juna har ma son shi ya rinja yi naki tabbas zai Iya canza kanshi, amma idan ke ki ke son shi baya sonki baki Isa ki iya tanƙwarashi ba sai dai wani iko Na Allah"


Jinjina kai zahra tayi ta gamsu da bayanin Aneelerh sai dai bata Jin zata Iya haƙura da damar da take da ita, Allah na gani ta jima tana son Hajiya saratu da ya'yanta duk wani abu da zai hadasu son shi ta ke yi.


  Cikin sanyin murya tace"Auntyna, addu'arki nake buƙata nima zan dage da addu'a, Idan Har dagaske zata hadani da daya daga cikinsu toh Allah yasa ya zama alkhairi agare ni da kuma shi kanshi wanda zata haɗani dashi din, Idan yana da kyan hali zanyi farin ciki, imma akasin hakan zan dauki hakan amatsayin ƙaddarar rayuwata, Allah na gani Ni bazan Iya janye tayin da tayi min ba"


Dafa kafaɗarta Aneelerh tayi"Zahra, bana so ki jefa rayuwarki inda zaki ƙuntata, babban kuskure ne ki auri miji mai neman mata, Ni nafison kiyi aure inda bazaki ta6a yin danasani ba, ko dan saboda Ƴa'ƴan da zaki haifa yakamata kiyi nazari kafin ki yanke hukunci"


  Damuwace ƙarara akan fuskar zahra, Ga samu ga rashi.


 "Nagode da shawararki auntyna, but ni yanzu bansan wani amsa zan bata ba, gashi na riga da na bude sakon zata ga alamar nagani"


  Shiru Aneeleerh tayi naɗan wani lokaci kafin Ta furta"Ki bata amsa da sunan wanda ya birgeki, zamu jira muga martanin da zata mayar mana"


 Amsa mata tayi da toh, ta kar6i wayar daga hannun Aneelerh, sunan zaid ta rubuta ba tare data ankare ba keyboard Ya canza mata sunan ya koma zayn, ahaka ta tura message din.


Bayan ta kammala ta soma daukarsu hotuna tare da baby junaid, sun dauki lokaci a dakin kafin suka fito falo don ay fira dasu, Hajiya adama da uncle abdallah sun ji dadin tarbar da akayi masu, An mutuntasu an kuma karramasu kamar kada su tafi, ga lafiyayyan abincin da su zahra suka girka masu, sunci sun ƙoshi sun kuma sha fira, wuraren marece suka bar gidan.


*Shin Meke Faruwa A Obie Estate 🔥🔥🔥*


Bayan fitowar Chief owais da Prime minister Tare da Boss man, jami'ai suka yi gaggawar bude masu motar da za su shiga.


  Ta ƙofar baya suka bi wadda zata 6ular dasu zuwa cikin Obie estate, kasancewar Gidan Owais shine ƙarshen ginin dake acan bayan estate din, Gate dinsa Biyu, akwai gate na gaba wanda zai fitar dakai titi, Gate din baya kuma zai shigar dakai Cikin estate.


 Prime minister Ne Ya buƙaci Yana son su fara zuwa gidanshi don su taho da sheikh imam kafin su wuce gidan baba Obie.


Da matsakaicin gudu motocin suka ƙaraso babban katafaren entry na gidan prime minister dake a tsare da jibga jibgan canadian polices da sojoji.


  A harabar Ajiye motoci su ka Yi parking, A hanzarce Sojoji suka nufo motar, Tare da buɗe masu ƙofa.


 Kusan atare suka fito, ba tare da bata lokaci ba, su ka ɗunguma zuwa babban falon gidan.


  A lokacin Nazli tana zaune saman Sofa ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, Hankalinta na akan laptop dinta, Yayin da Yazrin Take zaune a gefenta hannunta ruƙe da tsadaddiyar Wayarta.


 Ba zato ba tsammani, sallamar su prime minister ta ratsa kunnuwansu.


 Yazrin ce tayi saurin ɗagowa da idonta  yayin da ita Nazli tayi tamkar bata ji sallamar su ba, dama halintane idan tana aiki a laptop ba ƙaramin abu ke Iya dakatar da ita ba.


  Tsantsar farin ciki ne akan fuskar Yazrin, da mamaki ta furta"Big Bro"! da sauri Ta miƙe ta nufe shi, tunkafin ta ƙaraso Chief ya buɗe mata hannu alamar tazo gare shi, hartana tuntu6e garin sauri duk zumuɗin ganin shi ne, prime minister Yace"bi a hankali daughter ba guduwa zaiyi ba" sai faman washe mashi baki take Yi, hugging dinsa tayi, ya ɗaura hannayenshi biyu asaman Bayanta Yana ɗan bubbugashi ahankali Ya furta"Long time no see, I missed You so much"


  Ɗagowa tayi da kanta tana fadin"I miss you too, rabin raina You forgot about us, and you stopped coming to Canada, ko kiran wayarka akayi baka picking" voice dinta tamkar zata fashe mashi da kuka Ta ƙare maganar.


 Ɗaura hannunsa yayi kan mayafinta"Am sorry, Kuna araina, aiki ne Ya 6oye ni, amma hakan ba yana nufin aikina yafi ku mahimmanci ba, Ina fata kin fahimce ni" jinjina mashi kai tayi alamar eh.


 Boss man Dake atsaye Yana kallonsu yayi mamakin yadda owais Yake Yi mata magana, bai ta6a ganin yana sakar ma mace fuska haka ba sai Yau da Allah Ya kawo su gidan Prime minister, Hakiƙa Ya yaba da Haɗuwar daular, sai yaji tamkar Yabar Nigeria ne, ga wani ni'imtaccen sanyin A.c mai ratsa hudojin fatar mutun, ya yaba da kyawun Yazrin, Jefi jefi yakan dan saci kallon falon, badan Ya fito daga gidan chief Owais ba, da Allah kadai Yasan ƙauyancin da taj zaiyi agidan prime minister.


  "Mu shiga daga Ciki mutumina" Muryar prime minister ce ta fargar dashi daga tunanin da yake saƙawa aranshi, Murmushi ya saki, Hateem Ya ruko hannunshi suka nufi jigunannun royal sofas din Falon masu numfashi Ƴan ubansu afagen haɗuwa.


 Yazrin ta ruƙe hannun chief Owais acikin nata, Har suka samu wuri suka zauna saman sofa, Lokacin da Taj yai tozali da Nazli Har saida gabanshi Yadan fadi, aruɗe Yake kallonta sai ya dinga ganin fuskar Danish akan fuskarta, Prime Minister ya lura da rudanin dake akan fuskarshi, gyaran muryar da yayi mashi ne yasa shi yin saurin kallon shi, da ido yai mashi alamar ya yaganta, jinjina mashi kai Taj yayi, suka sakar ma juna murmushi.


"Nazli" Prime minister ne Ya kira sunanta, A hankali Ta dago da fararen idanuwanta ta daurasu akan fuskarshi.


 "Dad, welcome back" ta fada ba tare da ta kau da idonta daka kallon shi ba.


"Yawwa, Baki ga mutanan da nazo da su ba" sai lokaci ta kalli Boss man tamkar bata son yin maganar ta furta"Hey, How are you"


 Fuskarshi da fara'a yace"lafiya lou fatan na same ki lafiya"

 Amsa mashi tayi, harzata dukar da kanta Yazrin tayi saurin cewa"Sister, baki gaishe da big bro ba" ba tare data kalle shi ba tace"Okey" Iya abunda ta furta kenan.


Tsantsar mamaki ne akan fuskar Boss man, ko a mafarki bai ta6a ganin mace mai izza irinta ba, bai ta6a tunanin za'a Iya samun macen da zata kau da idonta daga kallon chief owais, sai akan Nazli.


Chief owais tamkar shima baisan da zamanta ba, hankalinshi na akan wayar hannunshi daya ruƙe Yana daddanawa


"Nazli, ki gaishe da Yayanki" babu wasa akan fuskar Hateem Yayi mata maganar, tun daga kan Yanayin yadda ya furta mata maganar zaka fahimci ranshi ya sosu da abunda Nazli tayi


Batare data dago ta kalli chief owais ba ta furta"ya kake"


Banza yayi da ita, har saida prime minister Ya ambaci sunanshi tukunna Yace"Uncle kada hakan Ya dame ka, ka bar ni da ita, dai dai nake da ita" cikin nuna isa Yayi maganar.


Daure fuska Yazrin tayi, ranta ya 6aci bata ji dadin abunda Nazli tayiwa Chief fa, Kodan saboda baƙon da suka zo dashi aganinta bai kamata tayi hakan ba.


 Miƙewa tayi tare dakai hannu ta dauki laptop dinta, ko sallama babu ta nufi upstairs, sautin takalmanta har cikin kunnuwan su.


Bayan tafiyar Nazli, Gimbiya Mujeedat ta sauko down cikin shiga ta alfarma, tunkafin ta ƙaraso take sakar masu murmushi.


  "Marhaban bika, My Son In-law, Long time bamu haɗu ba, dama kana a kasar," ta jefe mashi tambayar tare da samun wuri ta zauna tana fuskatar su.

 Ɗagowa chief Owais Yai tare da kallonta, da murmushin gefen fuska ya furta"ban jima da dawowa ƙasar ba, nayi laifi ban leƙo mun gaisa ba, sai yau Allah Ya nufa" taj dake kallon gimbiya mujeedat afakaice Ya jinjinawa haduwarta, mace kamar kanta aka fara tsara kyau ta haɗu ga Iya dattako.


  "Sannu da dawowa Mijina, Ina fata anyi nasara"cikin kulawa tayi maganar tana kallon Hateem, lumshe mata ido yai tare da ɗan jinjina mata kai alamar eh

  Dauke idonta tayi daga kan fuskarshi ta dubi Taj, baiyi tsammani zata kula shi ba, amma sai yaga ta sakar mashi murmushi tana fadin"barka da zuwa" yace mata yawwa.


 "Mijina baka fadamin wanene wannan ba"?

 "Sunanshi tajudeen, abokin aikin Owais ne"

 "Masha Allah, malam Taj, naji dadin haduwa dakai, Ya aiki"?

Yace mata lafiyalou," sun ɗan ɗauki lokaci suna tattaunawa kafin daga bisani,

  Prime minister Yace da ita"Sheikh Imam Yana aciki"?

 "Eh, tun ɗazu daya zo, na kaishi masaukin da aka tanadar masa,"


"Okey, bari na shiga wurinshi" ya fada tare da miƙewa ya nufi Hanyar zuwa part din da shiekh Imam Yake.


Kafin dawowarshi, Biyu daga cikin masuyi masu hidima suka shigo falon, Hannayensu ruƙe da ƙayatattun trays, daga saman an jera kayan abinci kala kala da drinks" 


  Cikin girmamawa suka gaishe da su tajudeen, kafin suka sauke farantan kan lallausan carpet din dake awurin.


   "Big bro, fadamin me kake son ci, zan zuba maka da kaina" yazrin ce tayi mashi maganar, girgiza mata kai yai alamar a'a, zuciyarta ajagule tace"Pls, kada abunda sis nazli tayi maka Ya 6ata maka rai, kariga da kasan halinta" calmly ya furta"okey" daga haka bata ƙara yi mashi magana ba, zuƙunna tayi batare da girman kai ba tace da masu hidiman da suka kawo abincin ku tafi ni zan yi serving dinsu, tafiya sukayi, Ita kuma ta zauna ta dauki lemu me sanyi ta tsiyaya shi a cup ta zuba ma Taj ta miƙa mashi.


 Har cikin ranshi yaji dadin hakan, kuma ya yaba da hankalinta, tun anan Ya fahinci tafi sauƙin kai Akan Ƴar uwarta Nazli, nan take Ya tuna da Halin Danish miskilancinshi sak kalar Na nazli ne, Aranshi yace Komai nasu kala daya kamar ɗan uwanta" 


  "ya owais, zan je na dawo" yazrin ta fada Tana kallonshi, amsa mata yai da ok, da sauri ta nufi upstairs.


  Bayan taj Ya kammala shan lemun, ya fara shan fresh fruit din da aka kawo masu.


Elevator Yazrin Ta hau, ta sauke ta a second floor, moving quickly Ta nufi ɗakin Nazli, a buɗe ta samu ƙofar, zura ƙafarta keda Wuya ta fara Cin karo da takalman Nazli a tsakar daki, Ga mayafinta kan floor, Da sauri takai idonta kan katafaren gadonta, tana daga kwance doguwar sumar kanta ta lullu6e mata bayanta.


   Cikin sanyin murya Yazrin ta soma Yin magana tana tunkararta.


  "Sister, Meyasa kika za6i ki ƙuntatawa zuciyarki? kina sonshi amma meyasa kike ja mashi aji"? Shiru Nazli bata tanka mata ba, babu lamun zata motsa.


"Ni banga amfanin 6ata mashi rai da ki ke yi ba, da hankalinki da tunaninki, gaban baƙon daddy, kike nuna ba'a isa dake ba, wannan ba ɗa'a bace, shi kanshi daddy ranshi ya 6aci da abunda kikayi," dakatawa ta danyi da yin maganar tana kallon Nazli dake kwance tamkar maiyin bacci.


  "Nasan kina jina, ban damu ba dan kin share ni, Nidai shawara nake baki a matsayina na ƴar uwarki mai son farin cikinki, kada kiyi wasa da damarki, mata dayawa suna hauka akan son Ya owais, basu ta6a samun damar yin tozali dashi ba, amma ke cikin sauƙi Kin same shi, Kina ƙoƙarin Yin watsi da damarki, bana son kiyi danasani sister," har cikin zuciyarta take furta kalaman.


"I thought when you saw him, you would rush to hug him and tell him how much you missed him, but sai naga akasin hakan, wai yaya owais kika share kamar wani tsaran wasan ki, ki daina ganinshi kamar wani tsaranki, kafin a haife ki shi aka fara haihuwa" 


 Shiru Nazli bata motsa ba, Yazrin taci gaba da cewa"Ki cigaba da ja mashi aji, wata rana zakiyi danasani, Allah yasa Ya auri wata bake ba...." kafin Ta ƙare maganar A fusace Nazli Ta yunƙura ta miƙe zaune Ta rarumi laptop dinta dake agefenta, daga Inda take ta daddage ta wurga ma Yazrin ita, da sauri Yazrin Ta tarbe laptop din da hannu biyu, fuskarta dauke da murmushi tace"kinji haushin magana ta ne"? Kaɗan kika gani, sai ma ranar da za'a shafa fatihar auranshi, Haukan da za ki yi sai yafi wannan" wurga mata laptop din Yazrin tayi kafin ta juya da gudu ta fuce daga dakin ganin yadda Nazli take huci.


 A hankali ta ɗaura kanta saman pillow, haɗi da lumshe idanuwanta, red lips dinta sun ciza launinsu, ita kadai tasan irin radadin da take ji aduk lokacin da tayi ma owais haka, ita aganinta batayi laifi ba, shi yakamata yazo inda take don ya nemi afwarta akan tsawon lokacin daya ɗauka ba tare daya je canada ba, Alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta idan har baizo wurinta Ya wanke kanshi ba ita kuma har abada bazata ta6a kula shi ba, koda an shafa fatihar auran su!!!

Don ita ba irin matan da namiji Yake juyawa bace, macace mai aji, mai kuma Ji da kanta, zata iya haƙura da komai akan izzarta.


Idan muka koma Falo, Bayan ƴan mintuna, Prime Minister Ya shigo falon tare da Shieikh Imam, sai kuma gimbiya Mujeedat, miƙewa Chief Owais Yai shima Taj Ya miƙe, suka yima Gimbiya mujeedat sallama kafin suka dunguma zuwa harabar ajiye motocin gida, jami'ae suka buɗe masu ƙofa suka shiga, Ajere motocin suka nufi gidan baba Obie.



*BABA OBIE*



Bai jima da farkawa daga bacci ba, jikin shi yayi tsauri, wani irin azababben zazza6i ne Ya lullube shi, har sai da Senator Lateef ya kira family doctors din su, domin duba lafiyar mahaifinsu, a ƙalla likitocin sun ɗauki tsawon mintuna talatin akan shi suna ƴan bincike binciken su, kafin daga bisani suka tabbatar masu da cewa Firgici ne da tsoro ke damun shi, Idan Har ba'ayi gaggawar kawar mashi da abunda ke razanar da shi ba, zuciyarshi zata Iya bugawa, Jin wannan maganar daga bakin likitocin yayi matuƙar ƙara ɗaga hankulansu, musamman Hajiya saratu duk tabi ta ruɗe, hannayenta biyu asaman kanta take ambaton Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, mun shiga Uku, Ƙiri kiri ana so aga bayan uban mu.


Bayan tafiyar Likitocin, gaba ɗayansu suna adakin Obinna, zuciyoyinsu cike da jimamin sakamakon ciwon shi, ya kasa ta6uka komai, duk ya yamutse tsufanshi Ya ƙara bayyana, Senate lateef ne ya taimaka mashi ya shiga bathroom yai wanka, ya fito ya canza suturar jikinshi, Kafin Ya shimfiɗa mashi darduma, acikin dakin yai sallar da bai samu damar yi ba, sam babu natsuwa atattare da shi, bayan Ya kammala Yin sallar ne, senate Ya ruƙo hannunshi, Ya zaunar dashi kan lallausan carpet, da sauri His excellency abdul razak Ya miƙe daga kan arm chair din da Yake azaune Ya nufi Kayan abincin da Hajjaty ta kawo mashi, Ya sanya hannu biyu ya ɗauko su yaje ya ajiye farantin gaban Baba obie.


 Saukowa Hajiya saratu tayi daga gefen gadonshi, ta zauna gefenshi idanuwanta acike tab da hawaye take yi mashi sannu.


  "Babana Allah Ya baka Lafiya, Ka daure ka ci abinci, sai kasha maganin zazza6in da likita Ya bada abaka" cikin kulawa tayi mashi maganar, a raunace ya ɗago da idanuwanshi waɗanda suka kaɗa jawur dasu Ya ɗaura su akan fuskar Saratu na tsawon mintuna biyu, kafin ya kau da idon Ya dubi Senate Lateef da ke ƙoƙarin zama gefen gadonshi, A hankali Ya maida idonshi akan fuskar His excellency deen da Pravin waɗanda ke A zaune kan carpet.


  Lumshe idanuwanshi ya ɗanyi, kafin ya ware su kan fuskar Twins dake zaune kan carpet kamar wasu mutanan kirki, sun yi zaman cin tuwo kowa da abun da Yake saƙawa aranshi.


  "Sannu baba, Allah Yabaka Lafiya," su twins ne sukayi mashi ya jiki, kafin sauran mutanan dake adakin suma sukayi mashi Ya jiki, bai samu damar amsa masu ba, Sai dai bin dakin da yake yi da kallo.


 Muryarshi adisashe Yace"Hateem baizo bane ko baku fada mashi halin da nake aciki ba"?


  Shiru su ka yi jin, kowa yana jin fargaban fada mashi abunda Prime minister Yayi.


  "Kunyi shiru bakuce komai ba! ina Owais? Yace min zaizo yau ya akai ban gan shi ba"? fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa Ya furta maganar.


 Hajiya saratu ce tayi ƙarfin halin buɗe baki, ta labarta mashi abunda Pravin Ya fada mata dangane da tura jirgi da hateem yayi zuwa Sudan dan adauko Sheikh imam Ya duba jikin Yaron daya rikiɗa Ya koma maciji.


Tsabar 6acin raine tsantsa akan fuskar Obie, 


Senate Lateef yace"tun safe babu wanda ya kira awaya cikin su don ya tambayi ya ka kwana, Gaba ɗaya sun ɗaura burin duniya akan Yaron da muke zargin Abokan hammayar mu ne suka turo shi donsu tarwatsa zuri'armu" afaɗace senate Lateef Yayi maganar

 His excellency deen Yace"gaskiya bamu ji daɗi ba, Hateem bai kyauta mana ba, yayi abu gamon kanshi batare daya nemi sha'awar mu ba, ni narasa gane meke damunsu daga shi har Owais din idanuwansu sun makance basa ji basa gani indai akan taimako ne, toh gashinan dai suna ƙoƙarin jefa rayuwar mahaifinmu cikin matsala, Fisabilillahi Ina amfanin hakan"? Ya ƙare maganar tare da jan dogon tsoki.


Tun da suka fara magana, Pravin Yake ta tsuma, tsabar zumuɗun su ƙare maganarsu don ya samu damar tunzura su, ganin Deen Ya dasa aya a maganarshine ya samu ƙwarin gwiwar cewa

  "Yakamata ayi gaggawar ɗaukar mataki akan Yaya Hateem, Shina fi ji, duk da ba fata nake Yi ba, amma idan wani abu Ya same shi, Ba iya family din mu Ya shafa ba, Nigeria gaba daya ya shafa, ƙasar da yake mulka bazasu ta6a sassauta mana ba idan wani abu ya samu shugabansu, koda kuwa kwarzane ne Ya fito akan fatarshi sai sunji ba'asi" maganar pravin ta ƙara ɗaga masu hankulansu, babu wanda yai wannan tunanin saida Ya furta tukunna suka ankara da gangancin da suka Yi.


   Ganin yadda suka ɗaga hankalinsune Yasa shi ƙara samun kwarin gwiwar cigaba dayin magana.


  "Ga kuma mahaifinmu babu ƙoshin lafiya, ba zamu zuba ido muna ganin wani bakon abu na neman yi mashi illa ba, dole mu dauki mataki, wallahi indai akan baba ne sai inda ƙarfin mu Ya ƙare, dole Yaron Yabar estate din nan, ai nan ba gidan marayu bane" ya faɗa yana mai nuna 6acin ranshi

Senate Lateef Yace"Sannan, shi kanshi Owais din zamu Yanke alaƙarshi da Yaran! Babu shi babu su, shi kuma Hateem tunkan Aje ko'ina, acikin satin da zamu shiga Ya tattara Ya koma canada, don ba zamu bari Yaja mana bala'e ba, Idan muna son ganinshi koda duk weekend ne zamu iya zuwa canada wannan ba damuwarmu bace, awurinmu tamkar zuwa kano ne"


Duk maganar da sukeyi akan kunnan Baba Obie, yayi shiru Yana sauraronsu, abincin ma Yagaza cin shi, hajiya saratu sai lalla6a shi takeyi akan yaci amma Yaƙi Ya, Ranshi Ya 6aci matuƙa, bakomai yafi ƙona mashi rai ba face rashin zuwan Hateem da Owais, bayan sunga halin daya shiga adaren Jiya, maimakon su mayar da hankali wurin kwantar mashi da hankalinshi, sai suka  ta'allaƙa wurin Kula da abun da Ya cutar da rayuwarshi, me hakan Yake nufi? 


"Baba dan Allah kaci abincin idan ba haka ba Hankalina bazai kwanta ba" hajiya saratu ce tayi mashi maganar yayin da take miƙa mashi abincin data ɗebo a cokali, kawar da kanshi gefe ɗaya yai batare daya furta mata magaba ba.


  "Grandfa, please kaci abinci, gaba ɗaya mun damu da halin da kake aciki"  zaid ne yayi maganar.

 Kafin wani Ya kuma furta magana, Suka soma Jiyo dirar motoci acikin Estate din 

  "May be sune suka ƙaraso" Acewar His excellency abduk razak.


  "Anya kuwa sune? Naji ɗazu Yaya deen ya kira Yaya sharafuddeen nafi tunanin shine Yazo" Pravin ne yai maganar, dakatawa su ka yi da yin magana, gaba ɗaya hankalin su ya koma akan ƙofar dakin, sunyi matuƙar ƙagara da son ganin wanene zai shigo.


Knocking ƙofar dakin Akayi, Pravin Ya ɗaga murya tare da cewa"ku shigo daga ciki"


Lokacin da ƙofar ɗakin ta buɗe, Prime Minister Hateem Ne Ya fara shigowa yana maiyi masu sallama, Chief Owais Yana abiye da bayanshi, su kadai suka shigo, Boss man da sheikh Imam suna acan babban falon gidan suka zauna saman sofa.


Tun da suka shigo dakin kowa yayi shiru yana binsu da kallo, su kansu sun  fuskanci babu Lafiya, cikin girmamawa Hateem yabi ƴan uwanshi ɗaya bayan ɗaya ya gaishe da su, fuskokinsu babu walwala suka amsa mashi, chief Owais ma Haka yabi kowan nan su ya gaishe da shi, banda Pravin, baya acikin jerin mutanan da suka kai matsayin da zai iya gaishe da su, tunfil azal basu jituwa, shiyasa hajiya saratu take matuƙar jin haushin Owais, saboda ƙiyayyar da yake nunawa mijinta, ko yanzu daya gaishe da ita daƙyar ta amsa mashi tana faman yamutsa fuska.


  A hankali ya zauna daga gaban farantin kayan abincin baba Obie, wanda tun da suka shigo ɗakin idanuwanshi suke akan fuskokinsu, Idan ya kalli prime minister sai Ya kalli Owais, har gaishe da shi su kayi bai amsa masu ba, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin prime minister yayi ba, don wannan alama ce dake nuna cewa mahaifinshi yana fushi da shi.


da sauri Zayn da zayn suka haɗa baki wurin gaishe da Prime minister, bayan ya amsa masu suka gaishe da chief Owais, shima ya amsa masu fuskarshi babu walwala, daga haka babu wanda ya ƙara furta magana, munafuki pravin a fakaice yake sakin shu'umin mirmushi, wato haƙarsa ta cimma ruwa


Baba Obie, Ya tsayar da idanuwanshi akan fuskar Owais, kamar yadda yake kallon shi shima haka yake kallon shi


"Hateem, meyasa tun safe bakazo gida ka duba ni ba"? Baba obie ne Ya jefa mashi tambayar.


Daƙyar Ya iya buɗe baki Yace"Kana araina baba, nasan ban kyauta ba na rashin zuwana, ka gafarce ni"


"Baka fada min me ya dakatar dakai daga zuwa ba? Shi nake son ji"


Da sauri Zayn da zaid suka miƙe ganin irin kallon da hajiya saratu tayi masu alamar su tashi su tafi, salin Alin suka fuce daga dakin


A tsanake Prime minister Ya labarta mashi abun da Ya faru.


"Saboda wa kazo ƙasar nan"? 


Jim ya ɗanyi kafin Ya furta"saboda kai babana"


"Taya za'ai nayarda da maganar ka  Hateem? Abun da Ya cutar dani daren Jiya shi ka tsaya taimako, tun safe kana can kana yi mashi hidima, yayin da ni kuma nake kwance ba lafiya"


Tuni prime minister Yasha jinin jikinshi, duk sai yaji ba dadi, zuciyarshi ta karaya

 "Baba bansan baka da lafiya ba, dan Allah kayi hakuri idan na 6ata maka rai, amma ka riga da kasan halina kuma kaine kake ƙarfafa min gwiwa akan yin taimako, ka sha fada mana tun muna yara idan muka ga mutun na buƙatar taimako to mu taimaka masa da abun da muke dashi, kada mubarshi hakanan, Yaran nan bayin kanshi bane, ƙaddarace ta afka mashi, baida kowa marayane, Yana buƙatar waɗanda zasu tallafi rayuwarshi....   "Kafin Ya ƙare maganar, Pravin yayi kuskuran  katse shi da cewa "yaya kai ne baka fahimta ba, Yaron nan maƙiya ne suka turo shi don su tarwatsa zuri'armu, idan ba haka ba ta ina mutun zai Iya rikiɗa ya zama maciji? Sannan ya rasa inda zai faɗo duk gine ginen dake a estate din nan na kusa da gidan Owais din bai shiga cikin su ba sai nan zai faɗo"? Daƙyar Ya ƙare maganar, ganin wani mugun kallo da chief owais Ya watsa mashi, nan take Ya haɗiye yawu ya soma ƴan kame kame

  Rai amatuƙar 6ace yace"malam, fuce kabar ɗakin nan, meye alaƙarka damu da har zaka katse Prime minister Yana magana, wannan abune daya shafi dangin mu bana ka ba" Tsabar mamakin kalaman Owais Yasa kowan nan su Ya dube shi, musamman Hajiya saratu ta muzanta da jin cin mutuncin da Owais Yayima mijinta.


  Babu kunya Pravin Yace"Owais kai har yanzu yarone, duk abunda zaka fada min ba zan ji haushi ba, Ina yi maka uziri, kuma magana da kaga Inayi don in kare dangin ku ne saboda halaccin da kuka Yi min....."  Azafafe Owais Ya yunƙura Ya miƙe tsaye, Yana naɗe hannun rigarshi tamkar Mayun wacin zaki haka Ya tunkari Pravin, An rasa wa zai dakatar dashi, kafin Owais ya ƙaraso Pravin yayi saurin nufar ƙofa ya buɗe ya fuce yana huci Ya maida ƙofa Ya datse.


  Juyawa owais yayi ya koma inda ya tashi ya zauna.


  Da buɗar bakin Prime minister sai cewa yayi"My son ka yi abunda Ya dace" wannan maganar Ta hateem ta ta6a zuciyar Hajiya saratu

 Ranta a6ace tace"yaya hateem, kana goya mashi baya saboda Yaci mutuncin mijina"?


  Prime minister bai tanka mata ba, bai kuma ɗago da ido Ya kalle ta ba. Hakan Ya ƙara 6ata mata rai, harara tadinga jefawa Owais Ko kallo bata ishe shi ba, baima san tana yi ba.


Shi dai baba Obie, Ya zubawa sarautar Allah ido, don wannan fadan Yafi ƙarfin shi.

  His excellency abdul Razak ne Yace"Owais, Kai muke sauraro muna son jin ƙarin bayani dangane da Yaron daya rikiɗa da kuma Yarinyar dake atare da shi"


     Kusan mintuna da Yin maganar abdul Razak Kafin Ya furta"Marayune su goma sha ɗaya nake ruƙo a hannuna, dukansu agidana suke da zama, a ƙarƙashin kulawata," Iya abunda Ya furta mashi kenan

  "A ina ka tsince su"? Shiru yayi bai bashi amsa ba Har saida His excellency abdul Razak Ya maimaita mashi maganar a tunaninshi kobai ji mai yace bane

   "Sojojin america ne suka tsince su A daji, shine suka damƙa case dinsu a hukumarmu, saboda Yaran sun faɗi cewa Su Ƴan Nigeria ne, ɗaya daga cikin Yaran ma akwai mahaifinta mun same shi, muna zargin masuyin garkuwa ne suka sace su daga Ahlin su, shi kuma yaron aljanune suka shige shi a dajin sune suke canza mashi halitta, wannan shine Iya abunda nasani dangane da su" atakaice Ya ƙare bayanin.

      Gyaran murya senate Lafeef Yayi kafin Ya soma magana

   "Mun riga da mun Yanke hukunci, Bamu buƙatar Yaran su ci gaba da zama a estate dinmu! Saboda Lafiyar mahaifinmu, sannan mun yanke alaƙarka da su, shi kuma prime minister zai koma canada adai dai date din da aka bashi umarnin komawa, don ba zamu lamunci gangancinku na son taimako Ya jefa rayuwar Ahlinmu cikin matsala ba, don ni har Yanzu ban yarda da Yaran ba, tunkafin ma in gansu Hankalina bai kwanta da su ba, tayaya za'a tsinci Yara adaji sannan akawo su estate dinmu? Meyasa su sojojin american basu ruƙe su ba a hannunsu ba? Saboda sunsan ba alkhairi bane shiyasa suka manna maku su" fuskar shi babu annuri yayi maganar.

 Hankalin prime Minister Ba ƙaramin tashi yayi ba Jin abunda suka ce, kasancewar shi mutunne mai biyayya ga yayyan sa ko kara suka ajiye mashi bai iya ƙetare wa, mutun ɗaya ne zai Iya dakatar dasu wato mahaifinsu sai dai ga dukkan alamu shima Yana goyan bayan hukuncin da suka Yanke,

Muryarshi asanyaye ya furta"kada kuyi min haka, saboda ku nazo ƙasar nan a ƙalla nakusa shekara ban samu damar zuwa gida ba, Yanzu Idan na koma bansan ranar dawowa ba, Baba ka sanya baki a maganar nan"


His excellency Deen dake zaune Yace"Idan saboda mu kazo ƙasar nan, kada ka damu, ka tafi kawai mu zamu zo inda kake, idan ma takama duk sati zamu Iya shigowa Canada kasan bamu da matsalar abun hawa" ya faɗa yana ƙara jaddada mashi"zamu Iya barin aikinmu mu ɗauki hutu saboda kai, munyi maka alƙawarin hakan, zamanka a ƙasartamu ne bamu yarda da shi ba, don ba zamu yi gangancin da zaka cutu ba har wani abun Ya same ka, Idan ka manta wanene kai bari in tuna maka, prime minister na ƙasar canada" duƙar da kanshi ƙasa yai hawaye tuni sun cika idanuwanshi, bakomai yake jimawa ba face Yaron daya ƙwallafa ran shi, yasan idan harya haura ƙafa yabar ƙasar nan da wuya su sake haɗuwa, watakil ma daya daga cikinsu yabar duniyar batare da sun yi tozali da juna ba.


Jikin Chief owais yayi sanyi laƙwas, hankalinshi na akan prime minister, shi kadai Yasan damuwarshi 


His excellency abdul Razak ya numfasa kafin ya ɗaura da cewa"kai kuma Owais, ba zamu hana Ka Yin aikin ka ba, sai dai babu zancen Yara su cigaba da zama agidan nan, ka kaisu gidan marayu ka haɗa su da wadanda zasu cigaba da rainonsu"


Takaici Ya hana Chief Owais furta masu komai, gaba ɗayansu hankalinsu ba akwance Yake ba.


    A hankali Baba Obie Yake kallon fuskar Prime minister data Chief owais, ga dukkan alamu Ya fahince su sai dai Yana jin tsoron wani abu Ya same su ta silar taimakon da suke Yi, shiyasa bai dakatar dasu senate lateef ba.


   "Baba, dan Allah kace wani abu, nasan zaka fahimce ni, wallahi Ina  ƙaunar Yaron, baka ganshi ba Yana kama dani da Nazli, komai namu iri ɗaya kamar ni na haife shi" muryarshi tamkar zai fashe da kuka yayi maganar, basu ta6a ganin raunin prime minister ba sai Yau da Allah Ya jarabce shi da ƙaunar wani bare


"Hateem! Wannan bai shafe mu ba, kowani ɗan adam yana da masu kama dashi a duniyarnan, shi kuma mugun mutun ba'a gane shi a suffar shi yakan  shiga cikin mutanan da yake hari yayi rayuwa dasu na tsawon lokaci Yana kyautata masu rana ɗaya yake tarwatsa su da makircin shi, na fadi wannan maganar ne don ni har yanzu ban yarda da yaron ba, dashi da sauran ƴan uwanshi, mutanan da aka tsinta a daji, wama yasani ko ƴa'ƴan aljanu ne kuka dauko mana" senate Lateef ne ya faɗa Yana watsa hannayen shi.


A hankali prime minister Ya zura hannu cikin aljihu ya ɗauko wayarshi, wadda tun safe rabon shi da ita, a gida yabarta gudun kada atakura mashi da kiraye kirayen waya, sai ɗazu da suka shiga gidan Ya kar6eta daga hannun gimbiya mujeedat.

  Layin Sharufudeen Ya dannawa Kira, bugu uku Yai picking,

     "Ina agida, dan Allah kazo, idan ba haka ba komai zai Iya faruwa"

 On the other hand muryar sharafuddeen Ta amsa mashi da toh, gani nan zuwa, ka kula min da kanka" amsa mashi yai da toh kafin yai rejecting kiran

   "Meye amfanin Kiran Sharafudden da kayi? Dakai dashi duka a ƙarƙashin ikon mu kuke, mune agaba daku" cikin nuna isa senate lateef Ya furta maganar

  Cikin sanyin murya Hateem Yace"nasan da hakan Yaya, amma shi zai Iya fahimtar zuciyata fiye da kowa, kuma zai kwantar min da hankalina"


 "Kana nufin mu bamu Iya kwantar maka da hankalinka? Kodan saboda shine shaƙiƙinka"? A harzuƙe senate Lateef Ya furta maganar

  Da sauri Baba Obie Yai masu gyaran murya gudun kada su fara Yi mashi ƴan ubanci abun da Ya tsana arayuwarshi.


 Gaba ɗaya Hankalinsu ya dawo kanshi"Ya Isa Haka! ya Isa, bana son nasake Jin wani Ya furta magana acikin ku" Shiru sukayi batare da wani ya kuma cewa Uffan ba

     "Baba abincin fa Yana hucewa, Yakamata Kaci" hajiya saratu ce tayi maganar cikin nuna damuwarta

    Kallon Owais yayi nan take Ya fahimci me Yake nufi

   Hannu owais Ya sanya cikin plate din da hajiya saratu ta zuba mashi abinci


   Ya soma ɗebowa Yana bashi abaki Yana ci,

  Hakan Ya ƙara 6ata mata rai, wato ita ta bashi abinci da hannunta Yaƙi Ci sai Owais daya fi ƙauna, shi ya za6a ya bashi abinci

 Bazata juri kallon su ba, miƙewa tayi tana fadin"Baba Allah Ya ƙara Lafiya, Ni zan wuce ɗaki" bata jira amsar da zai bata ba tayi saurin fucewa daga ɗakin.

   Senate latef ma ranshi ya sosu, duk irin rashin ɗa'ar da Owais Yayi ma Pravin baba obie bai dakatar da shi ba, after that Ya sanya shi bashi abinci abaki, bayan Hajiya saratu itace tafara Yunƙurin bashi amma Yaƙi kar6a, ba tun yau ba ya saba nuna banbanci akan Sauran Jikokinshi da Owais, Hatta Ya'yan Hateem Yafi Ji da su akan nasu me hakan ke nufi"? Aranshi ya saƙa maganar


      (Nidai nace na shiga uku, Kada afara Ƴan uba A family Obinna, Rikicin zai haɗe mana)


  Yayin da chief Owais Yake ba baba Obie abinci abaki, Ya tsare shi da ido Yana bin shi da kallon so da ƙauna kamar zai haɗiye shi, Lemu mai sanyi ya zuba mashi a cup Ya miƙa mashi, Ya sanya hannu Ya kar6a Yana sha, har cikin ranshi Yaji dadin hakan aduk lokacin da ranshi ya 6aci indai Owais Yana atare dashi wani irin sanyi ne yake ratsa zuciyarshi tuni yake neman damuwar Ya rasata.


In a respectful voice Chief Ya soma yi mashi magana, ta yadda babu mai iya jin su.


   "Kai kadai ne zaka Iya fahimtata, saboda kai ka raine ni tun ina ƙaramina, aduk lokacin da na sanya buri akan abunda nakeson cimmawa kaine kake ƙarfafa min gwiwa don ganin nakai ga matakin nasara, babana kada ka bari wannan karan in faɗi ƙasa, yakamata ka sanya baki awannan maganar, kasan bazan ta6a kawo wani abu da zai cutar dakai ba, Haƙƙina ne in kareka daga dukkan wani abun farmaki, yaran nan mutanene kamar kowa, basu da niyar cutar da kowa, saida na zurfafa bincike akansu na tabbatar da hakan tukunna na kawosu cikin gidana, bazan Iya yin nesa da su ba, Kuma bazan Iya dakatar da hukuncin da iyayena suka zartarba, amma kai zaka Iya dakatar da su,' cikin tausasa harshe Ya ƙare maganar tare da ruƙo hannayen baba obie acikin nashi, Ya ruƙe su sosai.

  

"Baba, Yaran nan basu da kowa, suna buƙatar wadanda zasu tallafi rayuwar su, nasani ba dole saini zan taimake su ba amma na riga dana daukarwa kaina alƙawarin bazan ta6a rabuwa dasu ba, A yau ina so ka nuna min ƙaunar da kake Yi min, da goyan bayan da kake bani, baba kada ka bari arabani da yaran nan ko a tursasamin akan in fitar da su daga gidana......." yanayin yadda owais yake yi mashi maganar yayi matuƙar karya mashi zuciya, tuni jikinshi yayi sanyi laƙwas, launin idanuwanshi har sun ɗan canza kala.


  Shi kadai Yake jin me owais Yake Fadi mashi, sauran saidai su bi da ido, prime minister dai tunda ya dukar da kanshi kasa bai ƙara dagowa ba, shi kadai Yasan abunda ke damun shi, zuciyarshi tafarfasa take yi tamkar ana rurata da garwashin wuta, Aranshi ya ayyana koda zai bar ƙasar bazai daina bin diddigin rayuwar yaron ba, bazai ta6a bari Ya wulakanta ba.


Lumshe ido Obie Yai a hankali ya ware su kan fuskar Owais

      "Zanyi tunani akai" atakaice Ya furta mashi maganar, ajiyar zuciya chief owais ya sauke, ya riga dayasan ƙaunar da yake mashi bazai Iya jurar 6acin ranshi ba

  "Allah ya ƙara maka lafiya kakana, da anjima kafin ka kwanta bacci zanyi maka tausarnan dana saba yi maka duk idan nazo nigeria, nasan zaka ji daɗi"

 Dariya baba Obie Yai har hakoransa suka bayyana fafare ƙyal da su

  "Owais ka iya fadanci, kasan duk wata hanya da zaka faranta min, Allah yabarmin kai jikana" amsa mashi yai da Ameen.


  daga haka basu ƙara Yin magana ba, sai dai kallon juna da sukeyi jefi jefi, su sanate lateef sun zama Ƴan kallo, kamar hotuna haka suka zauna zugudun suna kallon su.


Bayan wani lokaci Jiniyar Motoci ta karaɗe Estate din, nan take ransu Ya basu cewar Mai girma sharafudeen ne Ya ƙaraso gidan, tun abakin entry hall din shiga falo, Security details dinshi suka dakata da take mashi baya kamar yadda ya basu umarni, shi kadai Ya shiga Gidan Cikin shiga ta alfarma tsadaddiyar shaddace a jikinshi launin kore, duk Inda Ya gifta masu aikin gidan a gaggauce suke russinawa su gaishe dashi kamar zasuyi mashi sujjada, A main falo din gidan Yaci karo da sheikh Imam tare da Taj zaune saman Royal sofa, Hankalinsu kwance suke tattauna fira atsakaninsu, sunyi jiran ganin mutanan gidan shiru basu fito ba har sun fara tunanin kodai babu lafiyane? Musamman lokacin da pravin ya fito daga dakin baba obie ko kallo basu ishe shi ba, har kallonsu yayi amma yaƙi tanka masu, hakan ya sosa zucuyarsu, haka itama hajiya saratu tazo ta wuce ta falon bata bi takansu ba, har ƙwara su twins sun gaishe da sheikh Imam, suka kuma gaida Taj kafin suka wuce.


 Zuwan sharafudeen Obinna, Ya faranta masu rai, tunkafin Ya ƙaraso garesu Yake Fadin"wa nake gani kamar babana Imam malik," miƙewa Imam yayi ya nufe shi suka rungume juna kafin suka raba jikinsu

  "Ashe rai kanga Rai? Baba Imam sai yau zansa ka a idona? Gaskiya nayi fushi" Ya faɗa Yana haɗe fuskarshi

  Dafe kafaɗarshi sheikh Imam Yayi"Masha Allah, Sharafuddeen Bana ƙasar, shiyasa baka ganina akai kai, amma yanzu tunda nazo in sha Allah zan dinga shigowa Villa muna gaisawa'

   Sharafudeen na murmushi Yace"Idan ma bakazo ba, Ni zanzo har inda kake, wallahi nayi farin cikin ganinka, tun yaushe kazo ƙasar"

 Shiekh Imam Yace"Yau da sassafe Nayi sammakon shigowa ƙasar, saboda kiran da ɗan uwanka yayi min"


"Masha Allah, Ina fata komai lafiya"

 Sheikh Imam Yace"lafiyalou, Ga abokin Aikin Owais Ku gaisa da shi" Ya faɗa Yana nuna mashi tajudeen dake azaune, kamar ya sanshi haka Ya nufe shi da fara'a, da sauri Taj Ya miƙe suka rungume juna, haƙiƙa yasha ruwan mamaki, bai ta6a ganin mutane masu ruƙe da babban muƙami da suke da sauƙin kai irin Hateem da ɗan uwansa sharafuddeen, yajima yana mamaki da al'ajabinsu, kowa nasu ne basu ɗauki duniya da zafi ba.


  Raba jikinsu yayi daga na juna"yalla6ai sannu da zuwa, Ina wuni, Ya hidima da jama'a, ubangiji Allah ya taimaka"

 "ameen mutumina, Ina fata na same ka Lafiya"da mamaki Taj yake kallonshi jin ya kira shi da sunan mutumina kamar yadda yaji ɗazu Hateem Ya kira shi da sunan 

 Ganin alamun ruɗu akan fuskarshi yasa mai girman sharafudeen cewa"Owais Ya fada min komai dangane dakai, ganinka ne kawai ban ta6a yi ba, nasan zakayi mamaki dana gane ka ba tare dana tambaya ba" ya faɗa yana sakar mashi murmushi, shima taj din murmushin yayi har cikin ranshi ya ƙara ƙaunar Chief owais.

  "Babu isasshen lokaci, In sha Allah zan samu time din da zamu tattauna dakai" ya fada Yana bubbuga kafaɗar taj da hannunshi.

 "Toh Yalla6ai, nagode sosai" kallon shiekh Imam yai"baba mu shiga daga Ciki" yai maganar tare da ruƙo hannunshi suka nufi part din baba obie,


Zama taj yayi akan sofa, fuskarshi ɗauke da murmushi, Ji yake tamkar ya zuba ruwa a kasa yasha, acikin ranshi ya furta"Allah nagode maka da haɗani da mutanan kirki acikin rayuwata"

  Wayarshi Ya zaro daga aljihu ya soma tunanin Kiran Big guy don Yaji awani hali su Unaisah suke aciki sun ci abinci ko kuwa.

   Kiran na shiga big guy yayi picking

 "Ya mutumina kana Ina ne? Na dawo gidan na taras baku nan"

  "Mun shigo gidan baba Obie ne mu dukanmu muna anan"

  "Okey, Ina fata komai na tafiya yadda yakamata"

 "Taya zan sani, nifa ka ganni nan a falo, Ina zaman jiran fitowarsu, Allah yasa dai mu ji alkhairi, don kuwa naga wannan ba'indiyan da kake bani labari sai mazurai yake yi, ko gaishe mu bai yi ba"

  Sautin dariyar big guy ne Ya karaɗe kunnuwanshi

 "Itama wannan matar, mai kama da su chief owais ta fito tagan mu bata gaishe damu ba"

 "Dama ya za'ae ta gaishe dakai, taga baƙuwar fuska, matar da bata sakar ma bare fuska, sai dai shi sheikh Imam din ne dai bata kyautaba tun da aminin baban su ne, wata'ƙilma bata ganku bane shiyasa bata gaishe da shi ba"

 Boss yace"nima nayi tunanin hakan"

 "Shi kuma wannan gabjejen ƙaton dangin su kirishna, kabarshi kawai, mutumin banza, baida mutunci, shi da yazo cin arziƙi yayi kane kane a dangi" da zolaya big guy yayi maganar, taj yayi dariya cike da nishaɗi yake sauraron shi.


 "Very soon zamu yi mashi korar kare daga family din, tun da ba gidan ubansa bane" acewar big guy gaba ɗayansu suka tuntsire da dariya

  Bayan sun tsagaita Boss man Yace"dama na kirane don inji lafiyar ƴa'ƴana"

 "Kai dai fadi gaskiya, Ko dai ka Kira Kaji Lafiyar Jarin ka, Ifrituwar Yarinya wlh ɗazu data la6e a bayan labule, naso ace ka bari chief Ya shaƙi wuyanta, Yasin sai tayi jinya a gadon asibiti, Yarinya sai ƙiriniya kamar ansanya mata battery" fashewa taj yayi da dariya

 "Cin mutuncin Ya isa haka, Na lura baƙin ciki kake Yi da ita shiyasa ka sanya mata ido, Ni dai yanzu fada min suna ina.


  Sai da Ya Mula Yasha Iska tukunna Yace"Sun ci sun ƙoshi, kowannansu Ya koma dakinsa, harma sunyi wanka sun canza sutura, Na rakasu dakin Danish sun ganshi, Yanzu haka kowan nan su Ya koma dakin shi,"


Ajiyar zuciya Boss man ya sauke"Alhamdulillah, Naji dadin jin hakan, inataso in tambaye ka ka tuntu6i 6angarensu Salsabeel"?


  "Bakasan meya faru ba" nan fa big guy ya kwashe duk abunda Ya faru Ya sanar dashi, hankalinshi Ya dan tashi

  "Bawan Allah jazz, abu baiyi dadi ba, Allah ya bashi Lafiya, In sha Allah zamu fidda lokaci muje duba shi, Har Yanzu suna a asibitin ne"?


 " Na kira Major Waya Ya fada min cewa An sallame su, Jikinshi yayi kyau da sauki, naso na kira jazz din awaya ashe ya mantata acan gidan Yaran, sai dai muka gaisa da shi ta wayar Major har nayi mashi Ya jiki"

 Boss Yace"ka kyauta, Nima zan kirashi zuwa anjima kafin muje gidan nasu, amma fa yakamata Yaran nan a ƙara masu tsaro"

 Big guy yace"Nima nayi tunanin hakan, Jira nake komai ya lafa Yaron nan Danish Yaji sauƙi kafin mu tattauna akan yaran idan za'a haɗesu gida ɗayane ko kuma za abarsu acan din, but Yanzu zan tura da jami'an da zasu basu tsaro in sha Allah"

    Sunjima suna tattaunawa atsakaninsu daga bisani sukayi sallama da junansu.


________________________✍️


Gaba ɗaya Sun hallara, Bayan Shigar Mai girma sharafudeen da Sheikh Imam, Cikin girmamawa da karramawa suka Yi mashi Kyakkyawar Tarba sanin matsayin shi awurin mahaifinsu Obie, kusan aminine shi, Ya jima Yana yi masu hidima da ta shafi 6angaren addinin islama, shiyasa suke girmama shi suna ganin ƙimar shi da darajar shi acikin idanuwansu, Baba Obie Yayi farin Cikin Ganin shiekh Imam har Yana fadin Ya akai Prime minister bai shigo da shi ba, shiekh Imam Yace shi ne Ya buƙaci Zama a falo, Obie Duk da bai jin dadin jikinshi sai da Ya miƙe adaddafe da taimakon chief owais  daya ruƙo shi, ya samu damar rungume imam malik, fuskokinsu ɗauke da matsanancin farin ciki sunyi matuƙar yin kewar Junansu, Mai girma Sharufudden tuni ya nufi ƴan uwanshi tun daga kan senate lateef, duk wanda Ya miƙa ma hannu suka gaisa daga bisani sai Ya yi hugging dinshi, Har yazo kan Hateem wata irin runguma yayi mashi tamkar zai maida shi ciki, Hateem yayi murnar ganin ɗan uwan nashi yasan shi kadaine zai fahimci zuciyarshi ya kuma share mashi hawayen shi, bayan sun kammala Ƴan gaishe gaishen nasu, Sheikh Imam malik ya fara Yi masu addu'o'i kamar yadda yake yi masu duk inyazo gidan, hakan ba ƙaramin daɗi yake yi masu ba, amsa mashi suka dinga yi da ameen ameen, har ya gama yin addu'o'in nashi, baba obie yace yaji dadin zuwanshi yana da tabbacin zai taimaka mashi wurin warware matsalar data ke ƙoƙarin kunno kai a zuri'arshi, Imam Malik yace shima yaji dadin zuwa Gidan kuma in sha Allah komai zai tafi dai dai, bi'iznillah, amma kafin su fara zaman tattaunawar, duba da gabatowar sallar Magrib Yana ga su bari su yi salla, harma da Isha'i kafin su dawo ayi zama na musamman don asamu maslaha, gaba ɗaya sunyi amanna da maganar Imam malik, ba tare da 6ata lokaci ba, kowannansu ya dauro alwala, suka fito atare suka ɗunguma zuwa harabar ajiye motocin gidan, sojojine suka take masu baya har zuwa masallaci, acan masallaci suka haɗu da Sir Mubarak tare da Zaki sunji dadin ganin shi tun daren Jiya daya tafi suna tsaka da yin firar yaushe rabo sai yanzu Allah Ya haɗa su dashi, bayan sun fito daga masallaci suka tsaya suna ƙara gaisawa, anan Sir mubarak Ya sanar da su uzurinshi na rashin zuwa gidan, sai dai bai sanar dasu game da zargin jazz da yai har takai shi ga bugunshi yadai ce masu Jazz Ba lafiya sun kwana asibiti Jiya sai Yau suka dawo, Hankalin baba Obie Ya tashi jin cewa Jazz din shi baida lafiya, duk yabi ya rude, har saida Sir mubarak Ya kira mashi jazz a waya yaji muryarshi da sauƙi har yana zolayar shi yayi missing din ganin gemun shi, shifa lafiyarshi qalou jinyace tadan lokaci, kada yai tunanin zai riga shi mutuwane shima sai yaci zamaninshi ya tara ya'ya da jikoki, dariya baba obie yayi sosai, sun ɗan jima suna yin wayar kafin Ya miƙa ma su hateem wayar duk suka yi mashi ya jiki ya amsa masu da sauƙi, hatta imam malik saida yayi waya da jazz hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Jazz ba ganin yadda suka nuna damuwarsu akanshi, bayan sun kammala yin wayar ne sir mubarak Ya amshi phone dinsa Ya tura aljahu, ɗaya bayan ɗaya suka shiga motocinsu, a jere suka nufi Estate dinsu......✍️



*❤UMMIN AMERICA❤*



Moving quickly yake tattaka stairs, tun kafin ya ƙarasa ƙofar room dinta, sautin daddaɗar Muryarta dake yin qira'ar karatun alƙur'ni mai girma ya ratsa kunnuwanshi, har saida ya lumshe idanuwamshi saboda yadda karatun nata ya ratsa zuciyarshi, sautun tamkar ana busa sarewa tsabar daɗinta, daƙyar ya samu damar tattara natsuwarshi da kamalarshi ya nufi ƙofar, ya sanya hannu yaɗan yi knocking dinta, shiru babu alamun zata dakata da yin karatun balle harya ya sanya ran zata bashi permission din shiga ciki, kusan sau biyar yanayin knocking shiru taƙi tanka mashi, A ƙarshe ya yanke shawarar buɗe ƙofar da kanshi, A hankali Ya zuge ta, tana ƙarasa buɗewa Ya haura ƙafarshi cikin ɗakin bakinshi ɗauke da sallama, yayin da idanuwanshi ke kallonta, tana daga zaune saman darduma, dogon hijabin dake ajikinta launin maroon yayi mata kyau, ya bayyana ainihin wacece Ita, bakomai ne ya karya mashi zuciyarshi ba face ruwan hawayen da suka wanke fuskarta sharkaf, Eye lashes dinta sun cukurkuɗe dakyar take Iya kallon Qur'anin data buɗe tana karantawa, duk da sanyin A.c na ɗakin hakan bai hana ta zubda gumi ba......


Ya fahimci batasan da shigowarshi ɗakin ba, hakan yasa shi ɗaga murya ya furta sunanta"UMMI!" Ras Taji gabanta ya faɗi don sai taji tamkar muryar Sheikh Imam ce Ta ambaci sunanta, a wani irin firgice ta yunƙura ta miƙe tare da yin saurin kai idanuwanta da suka kaɗa jawur kan fuskar shi, wata irin nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke ganin Big Guy ne , fuskarshi sanye da face mask.


Ganin irin kallon da yake yi matane yasa tayi saurin share hawayen fuskarta.


Wani irin tausayintane Ya kama shi, bai ta6a jin ta burge shi ba irin yau.


Calmy Ya furta"Am sorry, na shigo maki ɗakin without asking for ur permission, na kwankwasa ƙofar shiru baki buɗe ba, shiyasa na yanke shawarar shigowa"


Shiru tayi bata ce mashi komai ba, aranta taɗanyi mamakin tausasa harshen da yayi wurin yi mata magana, don tun ranar da suka fara haɗuwa ta fuskanci baida sauƙin kai, musamman jiya da ta ƙure ma su batul sanyin A.c Ya rufe ta da faɗa kamar ubanta abun ya ƙona mata rai, ta kuma yi mamakin zafin kanshi don tun da take  arayuwarta wani namiji bai ta6a yi mata hakan ba saboda kyawun surarta  da ke jan hankalinsu..


"Kin yi shiru baki ce komai ba"? Muryarshi ce ta fargar da ita, adabarbarce ta furta"badamuwa"


Goya hannayensa yai kan chest dinsa Ya nufe ta har sai da yaje dab da ita tukunna ya dakata

  

"Dama kin iya karatul alƙur'ani? da sanya hijabi"?


   "Kamar yadda ka gani" ta bashi amsa atakaice"


Lumshe idanunshi yadanyi before ya furta"kin kusa tafiya da imanina, inason  mace me ilmin addini"


"Ni bani da ilmi, Idan ma abun da ke aranka kenan to ka daina, Ni karuwa ce, zaifi ka fuce min daga ɗaki tun kafin in rinjayi zuciyarka" fuskarta adaure babu annuri ta furta maganar.


Dariya yai ta cikin face mask dinsa sautin ke fita,

   

"Da ace kinsan wanene Ni, da baki furta wannan maganar ba, domin kuwa ke bakomai bace akaina" yanayin yadda ya furta maganar yaɗan so ya jefa ta aruɗani, sai taji Muryar tamkar ba ta shi ba.


 tafin hannayensa biyu ya daura akan gefe da gefen fuskarta, nan taji wani irin abu ya ziyarci zuciyarta

   "Na damu da halin da kike aciki, shiyasa nazo don na dubaki, ɗazu muna a falo, naga yanayin da kika shiga ganin Imam malik, kin san shi ne"?

 Aharzuƙe Ta janye hannayensa tana girgiza kai tace'bansan shi ba, Yau na fara ganin shi, Ni da ba'a Nigeria nake ba taya zan san shi ma" ta faɗa tana haɗe fuskarta.

  "Hakane, amma meyasa kika gudu kina kuka"?

  Rai a6ace tace"Idan wannan ne ya kawo ka ɗakina, Dan Allah Ka fuce ka bani wuri,"

  Gyaɗa kanshi yai"Shikenan, nadaina, am sorry idan na 6ata maki rai, kamar yadda na fada maki, Na damu dake ne, wunin yau baki ci abinci ba, Kin hana kanki sakat, Ki faɗamin meke damunki"?

  Yamutsa fuskarta tayi kafin tace"babu abun da ke damuna, kawai bana son kowa atare dani, bana son takura, kuma bana jin yunwa shiyasa ban nemi abinci ba" atsiyace ta ƙare maganar, ya natsu yana kallon small lips dinta tamkar na jinjiri

  "Haƙƙin mu ne mu kula da cin ki, dan Haka dole ki ci abinci ko kina so ko bakya so," ya faɗa yana ɗaga mata gira

  Harara ta galla mashi"babu wanda ya isa yayi min dole, ciki dai nawa ne idan naga dama zanci abincin basai an tursasa min ba"

    "Kidaina yi min magana da tsawa, kodan saboda kinga na damu dake ne"?

  Ɗaga mashi kai tayi alamar Eh,

"Da zaka fuce ka barmin ɗakina da hankalina sai yafi kwanciya"

Shiru ya yi jimm tamkar baiji dadin maganarta ba, tayi tunanin zai tafi amma sai ta ga ya sanya hannun shi na dama ya ruƙo face mask din fuskarshi, slowly ya zame shi

 Wata irin furgita tayi lokacin da fuskarshi ta bayyana, Har saida ta ja da baya da baya ta kusa faɗawa mirror chair ta dafe ta da hannu ɗaya, idanunta amatuƙar zazzare take kallon shi tamkar ƙwayar zasu faɗo ƙasa la66anta na rawa ta furta"da.....ma kai ne? tayaya akai ka shigo gidan nan"?


 Wani irin shu'umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, kalar na tantiran ƴan iska, waɗanda suka shahara afagen iya shaidanci

  Lokaci ɗaya suffarshi ta ƙara bayyana, faffadan kirjinshi Ya buɗe sosai.

  Zame rigar jikinshi yayi, wani irin murɗaɗɗen damtsen hannu ne dashi, gaban kirjinshi kuwa da bayanshi zanan tattoo ne 6aro 6aro, kai daga ganin wannan ko acikin shaidanun ibliss ne shi,

  Lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai, ya gigitar da ita, jikinta ya soma yin kakarwa, duk tabi ta ruɗe, asaman gadonta Ya jefar da long coat dinsa


Muryarshi tamkar ta mashayin giya ya furta"Kin tsorata ne"?

Sam takasa furta magana, tamkar an ɗaure maƙoshinta, yanayin yadda numfashinta ke fita da ƙarfi kirjinta har sama da ƙasa yake yi,

   Tuntsirewa ya kuma yi da dariya, haɗi da tausasa harshenshi Ya furta"ba fa yau kika saba gani na ba, ni ne dai naki ɗin nan da kika sani"

  Yawu ta haɗiya Kutt! Sautin Ya fita, daƙyar Ta Iya tattara kalmomin dake akan harshenta ta furta"tayaya akai ka shigo gidan nan dake atsare da Jami'an isod, Bayan haka ko'ina akwai CCTv cameras saƙo da lungu, dan Allah ka faɗamin ta wace ƙofa ka shigo, kuma ya akai ka sanya kalar kakinsu? sannan kayi min suffar big guy" a razane take jefa mashi tambayoyin, abunne yafi karfin kwalwarta, mutun kamar aljani, takasa yadda da cewa shine, gani takeyi kamar mafarkine takeyi

  Cikin Takun Izza Ya nufeta, dab da ita ya tsaya, tare da ɗaura hannayenshi kan bayan kujerar da ta jingina bayanta.


  Can ƙasan maƙoshi Ya furta"Ummi, kinsan wanene ni, akan buƙatata zan iya yin komai, nagaza jurewa ne shiyasa na tako da kaina nakawo kaina inda kike....." da ƙarfi ta furta"baka bani amsar tambayar da nayi maka ba"?

 "Kada ki ƙara yi min magana kina ɗaga min murya" atsorace ta jinjina mashi kai Alamar toh

 Lumshe idonshi yadanyi na wani lokaci kafin ya furta"Idan kin yarda dani ki daina tambayata bana so, duk abun da nayi nayine saboda ke" ajiyar zuciya ta sauke, lokaci ɗaya taji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, kuma nan take taji ta aminta da kalamanshi, ɗaura hannayenta tayi saman kafaɗunshi, tana faman lumshe idanu ta furta"'I'm glad to see you, My controller, saboda a ƙuntace nake, bana Iya fita koda kofar gate ne, sun hana rayuwata sakat saboda aikin da nikeyi masu babu shige babu fuce, tamkar prison haka nake jin kaina" 

  Shu'umin murmushin gefen fuska ya sakar mata, tare da kashe mata ido ɗaya, hakan ba ƙaramin jefa ta yanayi yayi ba, A hankali Ya ruƙo ƙasan hijabin jikinta, ya yaye shi tare da jefar da shi kan gadonta, ruƙo gaban jallabiyar jikinta yai da hannu biyu, tun daga sama ya direta ƙasa, batare daya zuge zip dinta ba, sai da ya rage daga ita sai pant da bra tukunna Ya dakata, yana duban fuskarta, numfashinta harya fara canzawa, da wani irin huci yake fita, baiyi mamakin ganin cukowar kirjinta ba, yana ɗaya daga cikin abunda yake ƙara gigitar dashi akanta, idan zai shekara baya tare da ita, duk ranar da ya dawo gareta, baya ganin ci baya sai dai ci gaba, dirin jikinta natural ne.

    Ɗaura hannayenta tayi saman kafaɗunshi, yai saurin hade bakinsu wuri guda tamkar zasu cinye harsunan junansu,  

  Dungurugum ya ɗauketa da hannayenshi, ya nufi toilet da ita, yana shiga ƙofar ta datse.

  wani irin sautin gurnanine ya soma fitowa mai haɗe da nishinsu tamkar namun dawa suna fafatawa, kafin wani lokaci sautin sambatun ummi ya karaɗe ɗakin haɗi da ƙarar da take saki tamkar zata fasa bango............."





*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✍️*



Mu haɗu Jibi Idan Allah yakaimu da rai da Lafiya🌹



*Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post