Document: Kurkukun Kaddara Book 2 Complete

Document: Kurkukun Kaddara Book 2 Complete

Novels Elite English

 BOSS LADIES WRITERS*

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

            The Prisoners🔥💫

Middle step

A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty.

Episode 1

Zaro ido su Parveen su ka yi bakunansu a sake, yayin da su ke kallon ƙofar, Wani irin farin Ciki ne Mara misaltuwa ya bayyana akan fuskokinsu Har sun wage baki zasu Fasa ihu Angel Tai saurin Dakatar da su ta hanyar cewa"Kun manta abunda na faɗa ma ku? Komi za ku gani ku ja Baki ku yi shiru idan ba haka ba asirin mu zai tonu har su gane abunda mu ke ƙoƙarin yi' Fuskokinsu Haris da alamun ruɗu donsu basu son kan me ta ke magana ba, sun dai ga murfin ƙarfe jikin bango, bayan haka sunji batul tace ƙofar da su ke nema.

Naufal ne yai ƙoƙarin buɗe baki Yace"Angel Kun bar mu a duhu, bamu san kan me ku ke magana ba" ya ƙarasa maganar idanunshi akan fuskarta, har lokacin bata daina sakin murmushi ba, Haka zalika su parveen Bakin su awashe ya ke Kamar Gonar audugu Ji su ke kamar ma Har sun fuce daga Cikin kurkukun.

"Ki yi mana bayani mana, Wannan murfin ƙarfen na menene a jikin bango"? javed ne yai maganar, sautin Muryoyin su daƙyar ya ke fita saboda rashin ƙarfin jikin su, har ƙwara sauran mazan akan mubeen ko da su ka shigo toilet ɗin kan shi na asaman Kafaɗar Hannah, Sam babu kuzari a jikin shi.

"Na ruɗe Angel Ki fada mana mun ƙosa Mu ji," acewar Gabriel.

duk wanda yai magana acikin su idanuwanta na akan la66ansa, Sai bin su ta ke yi da kallo, farin Ciki Ya hana ta yi magana.

"Idan ba zata Iya yi mana Bayani Ba, Deeja Ku faɗa mana Meke faruwa ne'? Haris ne yai maganar idon shi akan su Deeja dake a tsaitsaye Cirko Cirko. 

Ganin sun fara fusata Yasa ta haɗiyi yawu tare da sauke nauyayyar Ajiyar zuciya, Cikin sanyin murya ta soma kora masu jawabi sannu a hankali ta fayyace masu komai dangane da ƙofar sai dai ta 6oye masu Game da tattaunawar da su ka yi  Ita da Salsabeel.Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post