"Nima tunkafin naji muryarta har naji ta kwanta min araina, idan muka dawo gida ki kira min ita mu gaisa pls" a ƙagare tay maganar
"Kamar kinsani, farko da muka fara waya da ita sai da tace min idan ina da ƙanwa kamarta in haɗata da ita, kinga shikenan sai ku ƙulla ƙawance" wani irin daɗi ne Ya lullu6e Zeenatu har ta fara imagining haɗuwarta da yarinyar tunkafin ma su fara magana a waya abunka ga me son ƙawaye,
Gaba ɗaya firar da suke Yi akan kunnan Dr shureim, wanda Hankalinsa ke akan driving din da Yake yi,
Basu sha wahalar gane gidan ba, ta hanyar amfani da address da Aneelerh ta basu har bakin gate din gidan suka iso, da sauri mai gadin gidan Ya buɗe masu gate motar su ta kunna kai ciki,
Tunkafin Dr shureim Yayi parking Aneelerh ta fito da sauri ta nufi motar su tsabar son takai garesu har tuntube takusa yi, kafin ta ƙaraso Benazir tai saurin fitowa da gudun gaske ta nufi Aneelerh suka rungume juna kamar za su koma mutun ɗaya,
Fuskar Dr shureim ɗauke da murmushi ya fito tare da zagayawa other side ɗin motar Ya buɗe ma Zeenatu, fitowa tay daga ciki ta soma bin ko'ina na gidan da kallo kafin ta sauke idanunta kan su Benazir dake a rungume da juna,
"Yaya Shureim wannan itace ƙawar Aunty Benazir ɗin?"
ɗaga mata kai yai alamar eh,
Tsawon mintuna kafin suka raba jikin su daga na juna, fuskokin su sharkaf da hawaye saboda kukan da suka sha,
Cikin shesshekar kuka Benazir tace"A.. Aneelerh! Ashe da rabon zamu ƙara ganawa da junan mu?
Itama Aneelern da muryar kuka tace "Benazir kinga yadda kika koma? Nayi maraicin ganinki, nayi kewarki aminiyata sosae, wlh bakiji dadin da nake ji ba..." daƙyar suke magana saboda kukan da suke yi har lokacin,
Zeenatu sarkin tausayi har ta fara matsar ƙwalla, shi kanshi Dr shureim dauriya ce kawai Yake Yi, amma ba ƙaramin tausayi suka bashi ba, bazai ta6a manta shaƙuwar da ke atsakaninsu ba,
Fitowa Zahra tayi daga gidan karaf idanunta suka sauka akan su Dr shureim da Zeenatu Har saida taji gabanta Ya faɗi ganin irin kyawun mutumin da kamalarsa daƙyar ta janye idanunta daga kansu ta mayar da dubanta ga su Aneelerh,
Murmushi Zarah ta saki saboda taji daɗin ganin aminnan atare,
"Ki daina kuka bana son ganin hawayen ki," Aneelerh ce tai maganar idanunta jawur Benazir tace "Idan kinaso In daina kema ki daina, taya bazanyi kuka ba Aneelerh? Nayi babban rashin da har abada bazan Iya ta6a yafewa kaina ba, laifina ne gani nake kamar nice silar da zumuncinmu ya tarwatse..." da sauri Aneelerh ta sanya hannu ta toshe mata bakinta "ki daina ɗaurawa kanki laifi, saboda bayin kanki bane tafiyar da kikai, kema bada son ranki aka raba ki da danginki damu kanmu ba...." lallashinta taci gaba da yi Zeenatu har ta fara gajiya da tsayuwa dama ita bata saba da wahala ba,
Tana faman jan ajiyar zuciya ta juya ta dubi su Shureim cikin sanyin murya tace"Aneelerh ga Yaya Shureim da Zeenatu ɗiyar Uncle ɗina" da sauri Aneelerh ta nufe su fuskarta da fara'a ta gaishe da Yaya shureim "sannunku da zuwa Yaya shureim ku shigo daga ciki" tay maganar tare da hugging ɗin Zeenatu tace "Yan mata sannunki kuyi haƙuri mun barku atsaye"
Kamar bata son haɗa ido da shureim saboda girman shi da take gani, tun fil azal tana matuƙar jin nauyinshi kuma tana girmama shi,
"Yawwa anaeelerh mun same ku lafiya",
"Lafiyalou Yayanmu" tay maganar tare da ruƙo hannun Zeenatu suka yi gaba Shureim Yabi bayansu tare da Benazir da sauri Zahra ta koma falo tana jiran su shigo don su gaisa,
Lokacin da suka shigo falon Mami da Ummi suna atsaye suna jiran shigowarsu don su tarbesu, koda Benazir tayi arba da Mami wani irin nauyinta da kunyarta ne suka kamata, Mami kuwa fara'a tasaki da sauri ta janyo Benazir ta rungumeta tana ɗan bubbuga bayanta "marhabun lale ƴata, tsawon lokaci munyi kewar rashin ki" lokaci ɗaya Benazir taji hawaye sun sake wanke mata fuska
Muryarta da shessheka ta furta"Ma..mi " sam takasa ƙarasa maganar,
"na fahimce ki basai kinyi min bayani ba, Aneelerh ta sanar dani komai, ki kwantar da hankalinki ba kuka yakamata kiyi ba, godiya yakamata mu yiwa Allah daya dawo mana dake cikin ƙoshin lafiya" Mamin ta faɗa tare da raba jikinsu ta sa tafin hannunta tana share mata hawaye
Kafin ta ɗago ta dubi Dr shureim wanda tun da ya shigo ya sunnar da kanshi ƙasa saboda nauyin Mami da yaji gani yake kamar har yanzu tabon da yai ma kansa zaisa su guje shi,
Daƙyar ya motsa labbansa zai gaishe da ita Mami tayi saurin katseshi da cewa "Allah sarki Shureim kaine ka koma haka? Gaba ɗaya kun canzamin, Shureim Ka yada zumunci ƙiri ƙiri Ka guje mu ka koma Egypt ban ta6a zaton zakai mana haka ba"
Cikin sanyin murya yace"Mami ay min afuwa nima bada son raina ba nayi nesa daku, zaman ƙasar ne Ya gagareni saboda abun da Ya faru, amma wallahi ko bayan da na tafi kuna araina..." bai ƙare maganar ba Mami ta katse shi da cewa "bakomai Shureim, duk abun da Ya faru mukaddari ne daga Allah, bawa bai isa Ya guje ma ƙaddararsa ba, naji dadin ganin ku cikin koshin lafiya sosae..."
"Ku mu zauna" ta faɗa tare da nuna masu sofas, Bayan kowa Ya zauna Ummi da Zahra suka yi masu barka da zuwa
"Muyiwa Annabi salati" acewar Mami gaba ɗaya suka yi atare kafin daga bisani Mami ta dubi Zeenatu dake ta faman zare blue eyes ɗinta, gaba daya tarasa sukuni saboda bata saba shiga mutane ba kamar tana jin tsoron su,
"Tabarakallahu ahsanul khaliqin, Ƴata wacece wannan bakuyi min bayani ba, gata dai masha Allah daga gani ba jinsin ƙasar mu bane" murmushi Zeenatu tayi,
Ummi tace"kin riga ni faɗa, tun da suka shigo ta tsole min ido, kamar in sace ta" dariya sukai cikin raha,
"Sunanta Zeenatu, ɗiyar Uncle ɗina ce" waro idanu Mami tayi haɗi da jinjina kai,
"Masha Allah, sannu Zeenatu" amsa mata tay da "yawwa"
"Dan Allah ki saki jikinki, ki ɗauka kamar kina agidanku ne, don na fahimci kamar kin takura"
Murmushi Zeenatu tayi har dimples dinta suka lotsa,
"Ina su Maminku ina fata duk suna lafiya" cikin kulawa tayi Maganar tana kallon benazir"
"Suna nan lafiya, sunce mu gaishe daku, taso mu zo tare amma tace sai zuwa na gaba",
Murmushi Mami tayi "Allah Ya kawo ta Lafiya in ma batazo ba ni na fidda lokaci inje gidan naku"
Shiru sukayi na wani lokaci, kowa da abunda Yake saƙawa aranshi, Benazir ta ƙosa su ke6e da Aneelerh don su ƙara jajantama junansu.
Fitowa daga kitchen Ana tayi hannunta ɗauke da tray na kayan abincin da suka shirya masu har zata gifta ta ɗan dakata tare da kallon baƙin nasu karaf idanunta suka sauka akan fuskar benazir, tsabar kiɗima da ganin Benazir Ƙiris Ya rage ta saki kayan abincin hannunta Jikinta Ya hau bari da sauri takai abincin Dining ta nufo su, gaba ɗaya ta zube kan carpet tana ambaton sunan Benazir,
Kusan atare suka ɗago suna kallonta duk tabi ta ruɗe muryarta na rawa take faɗin "Aunty Benazir! Kece? Ko dai makuwa nayi ne?"
Hawaye ne suka ciko idon benazir bakomai Ya faɗo mata aranta ba face Irin azabtarwar da tayi ma yar'uwar Ana mai aikin gidanta Janet taci azaba a hannunta in tai mata laifi hada duka take haɗa mata,
Cike da jin kunyar Ana tace"Ni ce Ana, ba makuwa kikai ba, fatan na same ki lafiya? Ina yar uwarki janet"
Matse ƙwalla Ana tayi "Allah Sarki Aunty Benazir Ina nan lafiyalou, Janet tana a Jos tare da Esther ni kaɗai ce anan, Aunty Benazir Ina kika shiga tsawon lokaci bamu ji ɗuriyarki ba..."
Kafin benazir ta bata amsa Aneelerh tayi saurin tarar numfashinta da cewa "Ana kije ki ƙarasa shirya masu abincin, zanyi maki bayanin komai" ta faɗi hakanne saboda bata son ana tayi maganar 6acewar su Angel gudun kada Benazir taji hankalinta Ya tashi,
"Kada ki damu, zuwa anjima kafin mu tafi zan nemeki..." amsawa Ana tayi da toh, Jiki asanyaye ta miƙe tana tafiya tana waiwayon su Benazir tana mamakin Matashiyar da suka zo da ita, aranta ta ayyana watakil itace Yar uncle ɗinsu da taji ance zasu zo da ita...har sai da ta shige kitchen tukunna ta daina kallon su,
Miƙewa Aneelerh tayi tare da kallon Benazir tace "mu shiga daga ciki",
Mami tace "kuyi me? Ba zaki bari su ci abinci ba, salon ki cika ta da surutu"
"Ba daɗewa zamu yi ba Yanzu zamu fito"
Ummi tace"ke ko an daɗe ba'a haɗu ba, tana son su ɗan ke6e ne ay firar yaushe rabo",
miƙewa Benazir tayi suka nufi bedroom ɗinta hannunsu cikin na juna,
"Shureim ya'yanka nawa Yanzu" sunnar dakai ƙasa yai jin tambayar da Mami tayi masa,
Dariya tayi "dan Allah kada kace min bakai aureba"
Cike da jin kunyarta Yace "banyi ba Mami, amma nakusa in sha Allah" tayi mamakin jin maganarsa gashi har ya fara manyanta baiyi aureba koda Yake komai sai Allah Ya nufa,
"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa" amsa mata su kai da ameen,
Shigowa Ana tayi "Mami na gama shirya abincin"
Mami tace"toh, ku tashi mu ƙarasa Ciki" Dr Shureim Yace"Alhamdulillah, bana Jin yunwa sai dai ko Zeenatu in zata ci"
Maƙe kafaɗa Zeenatu tayi "nima bana jin yunwar ay naci abinci agida" yadda tai maganar yaso basu dariya har sun gane shagwa6a66iyace
"Haƙuri zukuyi ku tashi muje, Nasan baza'a rasa space a cikin ku ba ko ruwan zumunci ne ku sha" lalla6a su Ummi tayi har dai suka miƙe suka bi su Mami zuwa dining..
A 6angarensu Benazir bayan sun shiga ɗaki da Aneelerh, cike da zumuɗi suka zauna daga gefen gado
Sai faman bin juna da kallo suke yi kamar yau suka fada haɗuwa
"Kinga yadda kika canza? Kin ƙara girma kinyi kyau abunki, bani labari bayan kin tafi ina kika faɗa"?
Numfasawa tay kafin tace"Wani bawan Allah ne Ya taimaki Rayuwata, Mutumin kirki, ɗan family ɗin Obinna nasan ba zaki rasa saninsa ba, sunan shi Zaki Mubarak Obinna A ƙasar Canada Yake..." gaba ɗaya Benazir ta bata labarin Yadda suka haɗu da zaki a Abuja bayan ta gudu daga jos da yadda harya taimaketa suka bar kasar atare..
Jinjina kai Aneelerh tayi har cikin ranta taji dadi da rayuwar benazir bata wulaƙanta ba,
"Koma wanene Yayi miki wannan aika aikar in sha Allah sai yaga sakayya, tun agidan duniya, anso a cutar da rayuwarki, da yake Allah ba azzalumin bawansa bane cikin ikonsa kin faɗa hannu nagari",
"Ni inda nagode ma Allah, ban tafi da tsohon ciki na ba, da bansan a Ina zan haife shi ba, ba rabon ƴata tasha wahala wlh banyi zaton zata rayu ba, inaji ina gani nabarta a kwamin wanka tana kuka tana kallona..." kuka ne Ya ci karfinta da sauri Aneelerh ta fara lallashinta
"Ni damuwana wanene yake kokarin ganin ya rabani da dangina? Me na masa Aneelerh? Nasan bana jin magana tun a ƙuruciyata inada jan faɗa da masifa, mutane da dama na sanya su ciwon kai har da masuyi min mummunan fata amma wallahi ban ta6a zaton za'a samu wanda zaiyi min asiri, to waini me nayi masu haka??" idanunta jawur ta faɗa.
Dafa kafadarta Aneelerh tayi"in sha Allah duk wani mai nemanki da sharri kanshi zai koma, ubangiji Allah Ya tona asirin su"
"Ameen Aneelerh nagode sosai da kulawarki agareni, ni wlh banyi zaton zaku kar6e ni hannu biyu idan na dawo ba, ko gida da zan dawo nayi fargaban haɗuwa da su Daddy amma saina ga kowa Yana murnar gani na ba ƙaramin daɗi naji ba, yanzu damuwana ɗaya shine mijina da ƴata ina matuƙar jin shakkarsu saboda nasan da wuya su kar6eni hannu biyu kamar yadda kukai min..."
"Meyasa zaki ce haka? ay su sai sun fi kowa murnar ganinki"
Girgiza kai tay"ba zaki gane ba Aneelerh, bayan tafiyata lokacin ina agidan zaki, kwatsam wata rana saiga saƙon saki daga Taj hakan Ya tabbatarmin da yaji haushin abun da na masa" da mamaki Aneelerh tace"kina nufin bake kika nemi saki daga wurinsa ba?"
Ɗaga mata kai tay alamar eh, shiru Aneelerh tayi jikinta Ya ƙara mutuwa lakwas saboda taj da kanshi Ya ta6a faɗa mata Benazir ta tura masa text message tana neman ya saketa, to kenan wanene Ya shirya wannan tuggun?" Ta jafe ma kanta tambayar da bata da amsarta,
Ruƙo hannayenta Benazir tayi a cikin nata ta damƙe su sosai cikin sanyin murya tace "Dan Allah Aneelerh ki taimaka min Inason yin magana da tajuddeen, naji kince baki da layin da Yake amfani da shi, tun da suna a tare da mijinki dan Allah ki kira Uzair ɗin sai mu yi magana da shi..." Rass Aneelerh taji gabanta Ya faɗi, tuni ta nemi nutsuwarta ta rasa, batasan taya zata shawo kan Benazir ba sam ta manta da jiya ta faɗa mata hada mijinta suna a South Korea,
"Kinyi shiru baki ce min komai" ta faɗa idanunta acikin na Aneelerh, farat ɗaya ta fahimci wani abu daga yanayin da ta nuna, Wani irin kwarjini Benazir tayi mata muryarta da inda inda ta shiga faɗin "am..umm..bani da layin shima uzair...au wayarshi ta lalace zan ce....." bata ƙare maganar ba ta katse ta da cewa "Kada kiyi min karya Aneelerh ba halinki bane, dan Allah ki faɗamin gaskiya ni dama najima ina kokwanton maganar mami, daga baya sai da raina ya bani akwai wani abu da take boyemin don itama lokacin dana tambayeta lambar Taj tunda nasan bata rasata ba kamar da suka bayyana man cewa suke kula da yarinyata lokacin dana dawo amman sai ta nuna man basu da lambarshi ta inda yake, tun nan na fara shakkun maganar ta tunda ko don saboda yarinyar tawa ai ya kamata ace suna da lambar tashi da suke magana, kawai ki faɗamin in da akwae wani abu nayi maki alkawarin bazan tada hankalina ba, boyemin bashi da amfani tunda duk min daren daɗewa zanji ne kuma bazan ji daɗin ƙin sanar man da kuka yi ba...."
Jinjina kai Aneelerh tayi tuni taji ƙwalla ta cika idanunta don har yanzu zuciyarta da ciwon abun,
Numfashi taja kafin ta fara bata labarin abun da Ya faru na 6acewar su Tajudeen,
Tsabar tashin hankali Yasa Benazir saukowa daga zaunan da take a gefen gadon ta dawo kan floor dirshan ta ɗaura hannayenta biyu asaman kanta muryarta cike da tashin hankali take faɗin "INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN! INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN......" Misalta tashin hankalin da zuciyarta ta fuskanta ba abune mai sauƙi ba, Idanunta sun kaɗa jawur facial muscle dinta har kerma take gaba ɗaya jikinta ya ɗau wani irin mahaukacin zafi kamar mai fama da zazza6i sai kerma take,
Dafa kafaɗarta Aneelerh tayi muryarta a raunace ta furta "Innallaha ma'assabirin Iya abun da zan iya furta maki kenan, abun da Ya faru Ya riga daya faru Benazir, illa iyaka mu cigaba dayi masu addu'a ubangiji Allah Ya bayyanar mana da su tunda har Yanzu babu labarin suna araye ko sun mutu,
Cikin shesshekar kuka Benazir take faɗin "nashiga uku Aneelerh! Meke faruwa da rayuwata ne? Da farko An rabani da dangina hakan bai isa ba sai da akayi silar da ƴata da mijina suka 6ace! Wai wanene ke bibiyar rayuwarmu ne? Uban me muka masa...." jin Yadda take ɗaga Murya Yasa Aneelerh saurin toshe mata baki da tafin hannunta gudun kada su Mami su jiyota....
A ƙarshe ma sai ta rungumeta saboda ta samu relief ɗin abunda ke damunta
Allah kaɗai Yasan tafarfasar da zuciyarta keyi mata kamar numfashinta zai ɗauke bakomai take tunawa ba face fuskar Taj dana yarta Unaisah yanzu shikenan ta rasa su?
Gunjin kuka taci gaba da yi, kwantar mata da hankali Aneelerh ta shiga yi, suna haka Mami ta shigo ganin halin da suke ciki yasa ta nufosu da sauri tana tambayar lafiya mike faruwa ne ta gan su haka da alamun tashin hankali, zama tayi a bakin gadon ta dafa kafaɗar Benazir tana faɗin "mike faruwa ne na gan ki cikin wannan halin??" Aneelerh ce dake ƙwalla ta faɗi mata dalilin shigarta halin, yanayin damuwa ne ya bayyana akan fuskar Mami tace ma Aneelerh tunda bata sani ba ai da bata sanar mata ba, shiru Aneelerh tayi cikin kuka Benazir tace "Mami nice na matsa mata ta sanar man, 6oye mani baida amfani don koda yaushe ina sa ran haɗuwa dasu ashe ba rabo, an raba ni da mijina da kuma ƴata, Mami suwaye waɗannan azzaluman da suka tarwatsa kan iyalin mu, mi mukai masu ne don Allah" gaba ɗaya ta gama karya masu da zukatansu itama Mami har idanunta sun ciko da ƙwallan, rarrashinta ta shiga yi tana karfafa mata gwuiwa kan inda rabo sai suga sun bayyana tunda har yanzu ba'a da tabbacin ko sun mutu har ta bata misali da ita yadda ta 6ace 6at ba'asan ina take ba tsawon lokaci gashi yanzu Allah ya bayyanar masu da ita don haka ba abunda zasu yi sai suci gaba da yin Addu'a, a tare suka cigaba da rarrashinta har saida suka ga ta ɗan samu nutsuwa Mami tace ta taso suje taci abinci dama shi ta shigo tayi mata magana, idanunta sunyi jawur ta girgiza mata kai kafin cikin disashshiyar murya tace bazata iya cin wani abu ba a yanzu, dole Mami ta ƙyaleta Benazir ɗin ta buƙaci shiga toilet da sauri Aneelerh ta miƙe tana nuna mata toilet ɗin ta miƙe jiki ba ƙwari ta shiga, bayan shigarta Mami ta miƙe cike da tausayinsu ta fita, wanko fuskarta tayi bayan ta fito akan gadon aneelerh ta kwanta kamar ba laka a jikin ta, tsananin tausayinta duk Ya kama Aneelerh tana ta kallonta, bayan wani lokaci ta miƙe taje ta kawo mata abinci da juice don tasha tace mata bazata iya cin komai ba, lalla6ata tay dakyar ta samu tasha juice ɗin, shiru sukai can Benazir din tace "Ina yaronki? Naga bangan shi ba? Ina abie?"
"Bayanan sun tafi unguwa tare da Mahboob ƙanin Zahra, su abie suma basa nan amma nasan zuwa anjima kaɗan zasu dawo gidan"
"Allah Ya dawo da su lafiya" amsa mata tayi da Ameen daga haka bata ƙara magana ba har bacci Ya ɗan dauke ta a ɗakin.
____________________Chief
Around 5 na marece Ya fito daga Gym room ɗinsa, daga shi sai short baƙi a jikinsa, Ya haɗa uban gumi zufa ta ko'ina take tsatstsafo masa, Hannunsa ɗaya ruƙe da short towel da yake goge gumin jikinsa,
Bathroom Ya shiga, within 15 mins Ya fito daga wanka ya nufi walk-in closet dinsa cikin kankanin lokaci Ya kimtsa cikin suit navy blue sunyi bala'en Yi mashi kyau da alama zai fita wani wuri ne, hadaddiyar agogon hannunsa sai salki take, kafafunsa na sanye da hadaddun leather shoe ta ko'ina kamshin turarensa Ya karaɗe ɗakin,
Wayarsa ce ta fara ruri ya ɗauko tare da duba sunan mai kiran sa, hidding number ce nan take Ya gane mutumin nan ne daya saba yi mashi kiran sirri,
Picking call din Yayi tare da kara wayar a kunne,
"Naji daɗi da ka fara yadda da maganata, Yanzu Ya rage naka Owais kai kokari wurin gano su wanene miyagun dake a family ɗinka tunkafin lokaci Ya ƙure maka"
"Sai yaushe ne zaka bayyana min kanka? Ina son sanin Wanene kai?And how did you know everything that's happening with my fam?
Sautin dariyar mutumince ta cika masa kunnansa "sanin wanene ni bai da amfani, idan kuma ka damu da son sanin wanene to ka fara kawo ƙarshen miyagun dake a cikin zuri'arku" runtse ido Chief Owais yai har cikin ranshi bai son jin Ya ambaci miyagu a family dinsa zuciyarsa karaya ta ke yi kalmar bata masa dadi,
Rai a6ace yace "babu miyagu a family dina, ka kiyaye kalamanka," dariya mutumin yayi "shiyasa nake jin tausayin ka Owais saboda ka yarda da kowa na family ɗinka, me zai faru a ranar da ka gane gaskiyar da nake kokarin ganar da kai" a fusace Ya daka masa tsawa baima tsaya ya ƙarasa jin zancen mutumin ba Ya wurgar da wayar kan Gadonsa, Yana faman fitar da huci Ya furta "bazai ta6a yiwuwa ba, na yarda da family dina, babu bata gari a cikin su...." Yana a cikin wannan Halin Wayarsa ta sake Yin ringing, Ko kallonta baiyi ba a zaton shi mutuminne Ya ƙara Kiransa shiyasa bai kulata ba,
Jiki amace Ya zauna kan couch gaba ɗaya Ya rasa sukuninsa zuciyarsa sam bata masa dadi,
Wayarsa sai faman ringing take da zarar kiran Ya katse wani Yake shigowa,
Runtse idanunsa yayi bakomai Yake hangowa ba face fuskar Daddynsa data Uncles dinsa kai harma da Kakansa mutanan kirki masu Daraja a idon duniya, abune mawuyaci ya gasgata maganar mutumin in har ba gani yayi a zahirance ba, to wai wa akeso Ya zarga a cikin su? hakan ma bazai ta6a yiwuwa ba, wannan rashin imanin badai a family ɗinsa ba, sai dai wani baren dake a cikin su,
Knocking kofarsa akai, nan take alert ya shigo masa, kamar bazai tashi ba, a kasalance Ya miƙe Ya nufi wayar Ya danna unclock slowly ƙofar ta buɗe, bai kai idonsa ga mai shigowa ba hankalinsa na akan missed calls din da akai masa daga delivery man na Companynsu, tunawa da saƙon Hateem yasa shi saurin dannawa mutumin kiran bayan yai picking suka gaisa ya sanar dashi saƙone Ya kawo masa tun ɗazu Ya shigo jami'ae sun hana shi ƙarasowa ciki,
"Okey, Gani nan zuwa" ya furta,
Sauke wayar yayi daga kunnansa
Juyawar da zaiyi ke da wuya karaf idanunsa suka sauka akan ƙafafunta dake asanye cikin highhill, sam ya manta da izni daya bada na ashigo dakinsa,
Tun daga ƙasa Ya fara kallonta har Ya sauke idanunsa kan fuskarta, ganin kallon da yake yi mata ne yasa tai saurin cewa "naga kana waya shiyasa ban yi magana ba" muryarta ba ƙaramin sanyaya masa zuciya tayi ba sai yaji kamar yasha pain reliever ne,
Kallo ɗaya da unaisah tayi masa sai da ta fahimci wani abu na damunsa,
"Ina wuni,"
Lumshe idanunsa yai muryarsa da sanyi ya furta "lafiyalou,"
"Idan akwai wani aiki da zan maka ka faɗa min"
"Okey" ya faɗa tare da kallon bedroom dinsa "ki gyara min ɗakin but karki takura kanki" amsa mashi tayi da toh, Fucewa yai daga ɗakin Ya barta ita kadai wani irin dadi taji, sai da ta 6ata lokaci wurin shaƙar kamshin turarensa daya cika dakin kafin ta fara gyara mashi gadon shi,
A sitting room dinshi Yasa aka shigo mashi da ɗan sakon, da sallama Ya shigo hannunsa ruƙe da wata katuwar shopping bag mai ɗauke da logo na Obie tech,
"Barka da warhaka Yalla6ai, fatan na same ka lafiya" yana daga zaune kan sectional sofa Ya amsa mashi da barka da zuwa,
"Yawwa Sir, ga saƙon" da hannu Ya nuna masa gaban sofa ɗin da Yake mutumin Ya ƙarasa Ya sauke jakar kayan Kafin sukai sallama Ya juya ya fuce,
Ko minti biyar ba ayi ba wani senior agent Ya shigo sitting room ɗin hannunsa ruƙe da mug din coffee, cikin girmamawa ya gaishe da shi kafin Ya ɗaura masa cup din kan table din gabansa,
Da hannu ya nuna masa shopping bag din "fito min da kayan dake a ciki"
"Okey sir" zuƙunnawa yayi agaban Jakar Ya fara zaro Apple laptop sabuwa gal, tare da phone box na Iphone 15pro max, A hankali Ya ɗaura su kan rug din gaban sofa din kafin ya ƙarasa curo sauran kayan, Apple ipad da headphone tare da watch box and eyeglass case" bayan ya kammala curo su, chief Ya ɗan jinjina kansa kafin yace da shi ya maida su ciki ya amsa mashi da Okey Sir, mayar da su ciki yay sannan Ya miƙe Ya sarah mashi da hannu yay mashi alamar yaje ya juya ya fuce,
Har cikin ranshi Yaji dadin kyautar da Hateem yayi ma yaron kaya masu kyau da tsada, aransa ya ayyana zaiyi amfani da wannan damar wurin ganin Yaja shi a jiki,
Cup ɗin Ya dauka Ya fara kurbar coffee a halin Yanzu Baya buƙatar kowa a kusa da shi shiyasa Ya ke6e kansa don Ya samu damar Yin nazari,
A 6angaren Unaisah dake gyara masa bedroom dinsa, har ta gama da gadon ta dawo gaban dressing mirror ɗinsa tana jera masa perfumes ɗin yayi amfani dasu,
Tunkafin tagama take Jin kamar faɗuwar gaba, kamar ance ta ɗago ta kalli madubin kwatsam idanunta suka sauka akan shi, Rasss! taji gabanta ya faɗi, a matuƙar firgice ta juyo tana kallon shi ya harɗe hannayensa kan ƙirjinsa fuskarsa kamar wanda aka aiko ma saƙon mutuwa, ko tayaya akai ya shigo ɗakin bayan kofar tana da security? in badai Chief ɗin bai rufeta ba, anya kuwa shi ne? Ko dai iskokan dake ajikinsa ne? Taya akai ma Yasan tana a dakin Chief?,
Yawu ta haɗiya daƙyar zuciyarta na harbawa da matsanancin bugu ta furta"..My man"
Wani kallon tuhuma Ya wurga mata tare da ƙara haɗe girarsa,
Muryarta da inda inda tace "um..ka gane, wai dama ina ɗan gyara masa dakinsa ne kaga ya taimaki rayuwarmu shiyasa nake son kyautata mashi....." kamar mara gaskiya haka ta fara kora masa jawabin da bai tambayeta ba, har wani gumi ta fara haɗawa akan fuskarta duk da sanyin A.c din dakin,
"You don't want peace" da kakkausar murya taji Ya faɗa,
"Me kake nufi?"
"Abunda kunnanki Yajiye maki"
Yai maganar tare da takawa yaje gabanta ya damƙo hannunta ya jata da karfi ya nufi ƙofar, kokarin ƙwacewa ta dinga yi tana fadin "dan Allah ka sake ni, ban kammala Yi masa gyaran ba, Daddyna ne yace na dinga kyautata masa...." ko ta kanta baibi ba har sai da Ya fito da ita daga ɗakin ya nufi bedroom dinsu da ita, A kan gado Ya wurgar da ita ta mirgina tana faman maida numfashi,
"Kada ki kuskura ki ƙara zuwa ɗakin shi idan ba haka ba Kinsan zan iya komai akanki, har Daddyn naki bazan ƙyale sa ba saina ja masa kunne akanki in har yana son zaman lafiya dani" waro idanu waje tayi tare da ɗagowa tana kallon shi, Ya haɗe rai kai kace ba daga bakinsa maganar take fitowa ba,
Harara ya watsa mata kafin ya juya zai bar ɗakin, durowa tayi daga kan gadon jiki na 6ari tayi saurin shan gaban shi Ya tsaya yana kallonta,
Wani irin kwarjini yayi mata a ido, cikin sanyin murya tace"tunda bakaso bazan ƙara ba, amma dan Allah kada ka ta6a min Daddyna wallahi ina son shi bana son wani abu ya same shi, kuma ay shi baisan alaƙar dake a tsakanina dakai ba shiyasa yace haka..." marairaice masa fuska tayi kamar zata sanya mashi kuka
wani irin kallo taga Yana bin ta da shi, tunawa da abunda Ya faru ɗazu ne Yasa tayi saurin matsawa ta bashi hanya don Ya wuce,
Yana fita daga ɗakin ta sauke ajiyar zuciya, tsoki ta dan ja abun na shi ya fara bata takaici, Wannan wani irin kishi ne? "Jarababbe kawai" ta faɗa tare da samun wuri gefen gadonsu ta zauna tana faman haɗe rai, ta ƙudiri aniyar sai ta koma ɗakin chief yi masa aiki ko ba yau ba sai dai Ya haɗiyi zuciya ya mutu, saboda shi bazata ƙi bin umarnin Daddynta ba duk da tana jin tsoron yace zaiyi mashi wani abu don ta fahimci ba kaine da shi na,
_______________Mahboob
Shigowa gidan yayi bayansa a goye da Baby Junaid, tunda yayi sallama idanunsa suka sauka akansu Zeenatu dake a falon har kusan firgita yayi da ganinta saboda kyanta da yaja hankalinsa, Aneelerh na ganinsa ta miƙe tana faɗin "Oyoyo Baby junaid ɗina, mahboob Ina ka kai min shi tun safe sai Yanzu fisabilillah, halan koma abinci baici ba" ta faɗa tare da kar6ar Junaid ta rungume shi a jikinta, sam babu kuzari a jikinshi kamar bacci ma yakeyi ya farka
Muryarsa tamkar zai fashe da kuka Yace"Mommy, Yaya mahboob bai da tausayi sai da nace masa ni ya dawo dani gida amma yaƙi ya dawo dani, kuma wallahi Allah bazan sake binsa unguwa ba" idanunsa aruntse yake masifa, gaba ɗaya mutanan falon Suka kwashe da dariya hada Benazir da bata jima da fitowa ba, Yaron ba ƙaramin burgesu Yayi ba musamman Zeenatu, duk rashin sakewarta jiki na rawa ta miƙe ta nufi su Aneeleeh tace "Aunty ki bani shi in dauke shi"
Murmushi Benazir tayi "Allah yasa ya yarda rigima ne da shi" miƙa mata shi tayi, abun mamaki jikinshi har 6ari Yake wurin Miƙa ma Zeenatu hannu don ta ɗauke shi Ummi na dariya tace "ɗan ƙwal uba yaga farar fata, da mu mukace masa yazo yadda ransa ya 6aci ɗin nan wlh ba zuwa zaiyi ba" dariya sukai baki ɗaya,
Rungumesa Zeenatu tayi har wani ƙara ƙanƙameta yakeyi, komawa tayi kan sofa ta zauna hannunta akan sumar kan shi
daga bisani mahboob Ya gaishe da su Dr shureim fuskokinsu da fara'a suka amsa mashi, gabatar masu da shi Aneelerhtayi kamar yadda ta gabatar masu da Zahra a matsayin ya'yan uncle dinta,
Sunji dadin karramasu da akayi, ko da lokacin salla yayi Mahboob ne Ya raka Dr shureim masallaci sukayi sallah atare,
Har wuraren karfe shida na marece suna agidan, Dr shureim yaso su tafi Mami ce ta tsaida su saboda abie ya kira waya yace in sunzo su jira su dawo gidan don su gaisa, Bayan dawowar su Abie a falo suka zauna wata sabuwar firar suka soma yi cikin raha hada Uncle ɗan Iya Ya dinga basu labaran ban dariya gaba ɗaya suka cika su da farin ciki, baiwar Allah Benazir daurewa kawai takeyi duk don kada su gane halin da take a ciki, Aneelerh ce da Mami kadai suka san meke damunta, da zarar sun haɗa ido da Aneelerh take yi mata alamar tayi haƙuri, har bayan sallar magrib suna gidan
Lokacin da zasu tafi har bakin motarsu suka rako su baki ɗaya Kamar kar su rabu da juna, musamman benazir da Aneelerh, haka itama Zeenatu da Junaid yaron Ya kwanta mata aranta, har hotuna tayi masu da wayar Dr shureim, ko time ɗin da zai ci abinci ita ta bashi abaki, bayan sunyi sallama da junansu suka tafi, su mami basu daina kallon motarsu ba har suka fuce daga gate din gidan kafin suka koma ciki.
______________
Tun cikin mota Zeenatu ta lura da Yanayin Benazir ta haɗe rai sosai fuskarta tayi jawur Ko magana bata son yi, Ita kaɗai tasan raɗadin da take ji ta ƙosa su koma gida saboda taji zafin 6oye mata gaskiya da Mami tayi,
Motarsu na ƙarasa shiga gida Kamar jira take Dr shureim Yayi parking azafafe ta hankaɗe murfin motar ko yar purse dinta bata dauka ba ta nufi falo,
Hankali a tashe Dr shureim Ya fito Yabi bayanta, Itama Zeenatu ta fito hannunta ɗauke da purse ɗin Benazir ta bi bayansu,
Da karfi take ambaton sunan Mami kamar maƙoshinta zai 6allo, ko sallama batayi ba,
Jiki na 6ari Hajiya layla da Hajiya Sarah suka fito daga dakunan su,
Tunkafin ma tayi magana Hajiya layla ta fahimci meke damunta abun da take gudune Ya faru, dama tun ɗazu take zullumin dawowarsu har kiran Benazir ɗin tayi amma batay picking ba balle har ta samu damar Yin magana da Aneelerh don ta dakatar da ita akan kada ta faɗa mata gaskiyar abun da Ya faru,
"Benazir ba saida nace maki idan kin isa gidan ki kira ni ba? Meyasa bakiyi hakan ba...." a rude Mami ta furta hakan, Cikin shesshekar kuka tace "Nagode ma Allah dana manta ban kira ba, abun da kike 6oye min shi aka faɗa min! Mami meyasa zakiyi min ƙarya akan 6atan mijina da ƴata?" rai a matukar 6ace tay maganar tana kallon cikin idonta,
"Wallahi baku kyauta min ba, kinsan kuwa yadda na ƙwallafa raina akan son ganinsu? Mami why? Why kikai min haka..."
"Dan Allah Kiyi haƙuri Benazir, tayi hakan ne saboda guje ma bacin ranki.." Hajiya Sarah ce ta fara kokarin shawo kanta, Zeenatu dake kuka da gudu ta nufi ɗaki ta shige saboda bata son tashin hankali, Idanunta jawur ta kalli Hajiya Saratu "miye amfanin boyemin da tayi? Bayan dole wata rana zanji awani wuri! Da ace ta faɗamin da yanzu komai ya wuce saboda ba yadda zanyi dole inyi haƙuri ....ni banji daɗi ba Mami wlh baki kyauta min ba...."
Dr shureim Sam Ya kasa magana, tsananin tausayin benazir ne Ya cika sa, baisan Ya akai Aneelerh ta sanar da ita ba,
Kallonshi Benazir tay"Yaya Shureim why? Kaima hada kai aka haɗa baki don 6oye mun gaskiya? Ban ta6a tunanin zakuyi min haka ba..."
"Zanyi maki bayani ki nutsu ki saurare ni...." bai ƙare maganar ba da gudu Benazir ta bar falon ta shige ɗakinta, tana shiga ta maido ƙofa ta datse tabar su atsaye suna kallon kallo,
"Shureim wai wanene Ya faɗa mata? Kuma kana agidan baka dakatar da hakan ba?" cike da damuwa Mami ta faɗa,
"Wallahi Mami bansan komai dangane da wanda Ya faɗa mata ba nasan dai bai wuce Aneelerh, kawai yanzu tun da ta riga ta sani muje mu lallasheta har asamu ashawo kanta,
Babu irin bugun da basuyi ma kofar dakin Benazir ba amma taƙi buɗe masu, tana jiyo sautin muryoyinsu daga waje sunata yi mata magiya akan ta buɗe masu ƙofa,
Tana kuka tace masu dama sun daina wahala saboda bazata bude ba har sai lokacin da ranta yabar gangar jikinta" wannan maganar tay matuƙar ɗaga masu hankali, Mami tun tana lallashinta har takaiga hada mata da ashar amman tayi burus taki buɗewa,
Wuraren ƙarfe tara na dare su Alhaji ubaid suka dawo gidan, nan fa suka tarar da abunda ke faruwa kowa Yayi tsaye kofar ɗakin Benazir in ka cire Alhaji musa wanda tun shigowarsu daya gama sauraran abunda ke faruwa yace su kyaleta in ta gaji zata buɗe kofar, Yana faɗan hakan Ya ƙara gaba abunsa, Babu wanda Yaji dadin maganarsa Hatta Alhaji ubaid yaji zafin Yadda Ya nuna halin ko'in kula akan halin da Benazir ɗin ke ciki, Har wurin ƙarfe 12 na dare ana abu ɗaya don dole suka hakura kowa Ya koma ɗakinshi ransu a jagule ahakan ma babu wanda Ya Iya runtsawa a cikin su..
Dr Shureim Yana Cikin Yin zarya a ɗakinsa kwatsam Ya tuna da shaƙar da ake ma Benazir idan dare Yayi Tabbas Yana ji aranshi za'a Iya kaimata hari duba da halin da take a ciki ba lallai ta iya ta6uka wani abu ba gashi ta datse kofa, Fitowa yai da sauri har Yana tuntu6e garin sauri Ya nufi kofar ɗakin Yay knocking shiru batai magana ba, Cikin sanyin murya yace "Pls idan kina saurarena ki tashi ki kunna karatun alkur'ani kada ki kwana ahaka, Yakamata kiyi hada nafila..." shiru bata tanka masa ba, jikinsa yai mugun sanyi baisan awani hali take a ciki ba, karshe zama yayi a ƙofar ɗakin don baya jin zai iya tafiya yabarta ya ƙwammace ya kwana anan.
____________________________
Sai dare Zahra ta kunna wayarta da Mahboob Ya kawo mata daga wurin gyara, Cike da zumuɗi ta shiga gallery dinta anan taga hotunan da suka ɗauka tare da Unaisah, da sauri ta fito daga ɗakinta ta nufi bedroom ɗin Aneelerh, tana shiga ta sameta a zaune kan prayer mat hannunta ruƙe da cazbaha tana ja yayin da acan ƙasan zuciyarta take tunanin ko ya su Benazir suka isa gida taji shiru bata kirata ba, har kira tay amma ba'ay picking ba,
Jin sallamar Zahra yasa ta ɗago kai ta kalle ta,
"Zahrah me kikeyi har yanzu baki kwanta ba"?
"Taya zan Iya runtsawa bayan ban nuna maki hotunan dinner ba, sai Yanzu na samu damar kunna wayar ma" ta faɗa tare da miƙa mata, Kar6a Aneelerh tayi kafin ta soma bin hotunan da kallo,
Zahra na atsaye tana kallonta, kwatsam taga Aneelerh ta zabura ta miƙe tsaye hannunta na kerma tuni cazbahar ta jima da barin yatsan ta,
A ruɗe ta furta"Zahra wacece wannan Yarinyar da kukai hoto da ita??"
Murmushi Zahra tayi "itace yarinyar da nake baki labari mun haɗu a wurin dinner ɗin, amma ya akai naga kamar hankalinki Ya tashi da ganinta?" Ta faɗa tana kallon fuskarta,
"Zahra taya hankalina bazai tashi ba, ke baki ga fuskarta da kyau ba? wannan yarinyar kamanninta sun 6aci dana Angel ɗinmu...!" Saida Aneelerh tay wannan maganar Zahra tafara tariyo fuskar Yarinyar, haba shiyasa take tayi mata kallon sani,
"Zahra bata fada maki sunanta ba"?
"Tace min sunanta UNAISAH"!