Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 34 Complete
Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 34 Complete

Takun Ƙarshe

 ✍️

EPISODE 33

Kwance take tana sharar bacci cikin kwanciyar hankali, cikin bacci ta yi kwakkwaran juyi zata gyara kwanciyarta kwatsam tayi arba da fuskar mutun wani irin firgita tayi a haukace ta zabura zata mike da sauri Benazir ta cafko hannun ta ta ruƙe shi gam, suka ƙurawa juna ido batare da ƙyaftawa ba, Hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yayi ba, ta rasa gane meyasa cikin ƴan kwanakin nan matarke tsareta da ido kamar zata lashe ta, aranta ta ayyana kodai ta6in hankalin nata ne Ya motsa? Kada fa ta hau ta da bugu tun ba hankaline da ita ba..tuni tasha jinin jikin ta, tana faman haɗiyar yawu kutt murya na rawa ta furta"am..um.. mamana! Tun yaushe kika farka"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda Benazir tayi mata rumfa kamar zata danne ta, babu alamun zata tanka mata tayi shiru tanata kallon ta...babban tashin hankalin unaisah hajiya layla bacci takeyi balle ta kawo mata ɗauki, tuni ido ya raina fata.  

"Dan Allah na roƙe ki, ki daina kallona haka, babaynki ce fa, ki na bani tsoro. .." sai da tay wannan maganar, Benazir ta saki murmushin gefen fuska har dimple

dinta ya lotsa...

"Babyna ne"? La66an unaisah na kerma tace"ni ce, dan Allah kada kiyi min komai..." ƴar dariya benazir tayi, wani irin nishadi take ji..

Shafa sumar kanta tayi har wani kyafkyafta idanu take Yi kamar wata mara gaskiya

Unexpected ta ji ta manna mata sumbata kan kuncinta, kafin tayi wani yunkuri ta kara mata wani kan la66anta, runtse idanu tayi kamar zata fasa ihu ta furta"na shiga uku, tawa ta same ni"! dariya benazir tayi kafin ta janye jikinta daga na unaisah ta koma kan gadonta ta kwanta idanunta na fuskantar ceilling..." wasu zafafan hawayene suka wanke fuskarta da sauri ta cusa kanta jikin pillow,

Satar kallon ta unaisah tayi, ta rasa gane meke damun matar, ta fara tsorata da lamarinta, kwanakin nan ta canza mata, ba kamar farkon da tafara jinyarta ba, ko meyasa❓


Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta sauko daga kan gadon, ta lalla6a cikin sanɗa take tafiya, backpack dinta ta buɗe ta curo wayarta ta nufi toilet ta shige ciki,


Text message ta tura ma daddynta


"Daddy, barka da dare, daddy ni dai nagaji da zaman asibiti, gida nakeso in dawo" tana tura mashi text din jim kaɗan saiga kiran shi, tayi mamaki saboda batasa rai zai bata amsa ba kusan karfe shabiyu na dare, tayi zaton yayi bacci.


Picking call din tayi tare da kara wayar a kunne"My daughter! Me kike yi har yanzu baki kwanta bacci ba? Wani abu ya faru ne"?


Cikin muryar raɗa ta furta"ba abun da ya faru, kawai bana jin dadin yawan kallona da matar takeyi, duk in na farka tsakar dare saina ganta akaina ta tsare ni da idanunta" 


Sautin dariyar shi ce ta ratsa kunnanta  aiko ta haɗe fuska kamar tana agabanshi tace


"Daddy dariya kake yi min?


"Sorry daughter, maganarki ce ta bani dariya, but ki ƙara hakuri Anila ta fada min next tomorror za'a sallame ta"


Shagwa6e fuska tayi, ko tsoro bata ji ita kadai a toilet



"daddy ina yan uwana? Yau banji muryoyin su ba"


"Suna nan cikin koshin lafiya, basu da wata damuwa"


Shiru sukayi na wani lokaci, zuciyar ta sai azalzalarta takeyi akan ta tambaye shi ina Danish amma ina takasa furtawa...


Kamar taj ya karanci abunda ke zuciyarta sai taji yace"Daughter, labari me dadi, dan uwanki Danish ya fara koyon rubutu da karatu a wurin chief, abun saiya baki mamaki yana da kaifin basira, kamar ke lokacin da kina ƙarama, kwakwalwarsa tana ja, abun burgewa sun shaku sosai da chief in kika gansu kamar ƴan uwan juna, tare sukeyin komai......." batasan ya akai ta tsinci kanta da sakin murmushin gefen fuska ba, har cikin ranta taji dadin jin labarin nan da daddynta ya bata..


"Daddy, na taya shi murna, kuma naji dadi wlh, Allah ne kadai zai iya biyan chief, yayi mana hallacci arayuwar mu, ina jin dadin kyautatawarshi agare mu, Allah yasaka mashi da mafificin Alkhairinsa....." addu'o'i ta cigaba da yi mashi daddynta yana amsa mata da ameen


Kafin daga bisani yace"daughter, ki koma bacci, bana so ki makara sallar asuba, kiyi addu'a kafin ki kwanta sannan ki kula min da kanki" 


"Toh daddy, kaima ka kwanta kayi bacci, ka kula min da kanka" bayan sunyi sallama da juna, kasa motsawa tayi daga cikin toilet din, wani irin yanayi take jin kanta mara misaltuwa, tanaji aranta kamar tayi missing din wani abu da zuciyarta take muradin son gani, ta wani bangaren taji dadin labarin cigaban da danish ya samu sosai har wani dan murmushi ta saki


Lumshe idanu tayi tare da jingina bayanta jikin wall na tsawon mintuna kafin ta juya ta buɗe kofar, cikin sanda take tafiya tana satar kallon gadon benazir, ta lullu6e jikinta da bargo da alama ta koma bacci, hakan ba karamin dadi yayi ma unaisah ba..

Kan gado ta haye ta kwanta tare da jan duvet tayi covering  jikin ta wani baccin ne ya kuma daukarta...


_________________________________✍️


*Hajjaty*


Tun da sanyin safiya bugun kofa Ya farkar da ita, tana tsaka da jin dadin baccin ta, da wata irin kasala ta miƙe ta sauko daga kan gadon tayi miƙa haɗi da yin hamma, Ƴar rigar bacci ce a jikin ta, sai da ta fara daukar hula ta lullu6e kanta kafin ta nufi kofar tana tambayar wanene"?


Daga waje tajiyo muryar sofia cikin tashin hankali tace"Aunty ni ce sofia, ki buɗe min kofa" da sauri hajjaty ta buɗe kofar ta leƙa kai tana kallon sofia wadda gaba ɗaya babu kwanciyar hankali atare da ita ..tunkafin taji me zata faɗa mata gabanta ya fara faɗuwa.


"Sofia! Meke faruwa ne? naganki kamar ba lafiya"? Yarfa hannu safiya tayi murya na rawa tace"marwa! Aunty mun shiga uku, kizo kiga abunda ke faru ! Marwa ta kuturce. .." aruɗe hajjaty ta ce"bangane me kike nufi ba? Meya faru da ita? Wata irin kuturta . "? Bata jira hajjaty ta kare maganar ba, taja hannunta da sauri suka nufi dakin marwa dake anan corridor din da ɗakunan house maids din gidan su ke..


Shigarsu ke da wuya hajjaty tayi arba da ƴan aikin gidan gaba dayansu, sun hallara, fuskar kowan nansu sharkaf da hawaye cikin tashin hankali suke sallallami idanunsu akan marwa.


Suna ganin hajjaty suka buɗe mata hanya don taga abun tashin hankalin da suke kallo,

Lokacin da ta sauke idonta kan marwa dake nannaɗe kan katifarta rass taji gabanta yayi mata wani irin mahaukacin bugu na tashin hankali, ta waro idanu waje, agigice ta daura hannayenta biyu saman kanta, ta zabga salati tana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'u!!


 la66anta na kerma ta furta"Mar..marwa! Meya faru dake? Ya akai kika koma haka? ta faɗa tana kallon yatsun marwa da suka dunkule irin na kutare ga wani ruwa mai yauƙi dake gangarowa ta tsakaninsu,, la66anta sun shafe babu hudar baki kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba, wani irin nishi take saki, idanunta sun kaɗa jawur ga zufa data wanke jikin ta baiwar Allah ita kadai tasan azabar da take ji, sai faman zare na mujiya takeyi jikin ta nata kerma.


Fashewa hajjaty tayi da kuka, gaba daya sautin koke koken su Ya cika dakin

"Wayyo Allah! Na shkga uku! Dan Allah ku fadamun meya faru da ita?  kaina ya kulle nagaza yarda da abunda idanuna suke nuna min! Jiya jiyan nan mukayi aikin dinner tare da ita lafiya lou muka rabu da ita...taya akai ta samu wannan lalurar ta kuturta? Ina bakinta yake"? Cikin shesshekar kuka tayi maganar

Abla tace"Aunty bamusan meya faru da ita ba, yau da safe mun tashi zamu fara aikin breakfast, mun ga bata fito daga daki ba, shine nace ma sofia taje tayi mata magana kada mu makara, bayan tafiyar sofia har mun fara aiki muka jiyo sautin ƙararta daga dakin marwa shine muka taho da gudu mu duka dan muga mike faruwa a nan muka tarar da marwa cikin wannan halin.. ." ta ƙare maganar tana kuka

Sofia tace"wlh bansan meya faru da ita ba, Nima haka na sameta, ina shigowa dakin na isketa a nannaɗe kan kafita, har ina zolayarta nace mata bana son iya shege kina ji inata ƙwala maki kira kinyi shiru baki ce min komai, wlh aunty dana zo gaban katifar naga hawaye idonta gashi babu hudar baki, yatsun hannunta sun kuturce bansan sa'adda na fasa ihu ba, ni ban ta6a ganin tashin hankali irin wannan ba, Allah daga gani Aljanune suka shafe ta . ..." gaba daya duk sunbi sun ruɗe, hankalin su Ya tashi, jikin hajjaty na 6ari tace"ba kallonta yakamata mu tsaya munayi ba, bari inje in sanar da mutanan gidan..." da sauri ta fuce daga dakin...  .


Kafin wani lokaci gaba ɗaya mutanan gidan suka hallara a dakin marwa, da sauri maids din suka basu hanya don su shuga ciki, baba obie ne kan gaba jikin shi sai 6ari yakeyi, Pravin da twins suna abiye da shi, har sunyi shirin zuwa office wannan abun tashin hankalin Ya risƙe su, hada Hajiya saratu ta shigo ta zumbula buba ajikinta, sai faman raba idanu takeyi tun kafin ma taga meya faru da marwan!!


lokacin da sukayi arba da marwa gaba ɗaya hankulansu suka tashi, sunyi matuƙar razana da ganin yadda halittar marwa ta canza, kowa sai tambayar ba'asi yakeyi,  Tafa hannu hajiya saratu tayi"La'haula walakuwata illa billahil azim! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni filmusibati.. Gaba ɗaya tabi ta rikice, "Ya akai Haka ta faru? Wata irin lalura ce wannan"? Ta faɗa tana zare na majuya

Masu aikin suka hada bakin wurin fadin wlh bamu sani ba, haka muka same ta,

Idan  hankalin su twins yayi dubu toh ya tashi, wani irin ƙyanƙyami da ƙyamar marwa ne Ya kama su, babu wanda Ya lura suka sa6e daga dakin suka yi tafiyar su don bazasu juri ganin tashin hankalin nan ba. 

Tsabar tashin hankali da kiɗima Ya hana baba Obie furta kalma, dama da ƴar cazbahar shi a hannu sai faman jan ta yakeyi yana ambaton sunan Allah

Pravin dake a ruƙe da kofa fuskar shi a hautsine Yana ta faman zazzare idanu kamar na kwarton muzuru har wani gumi Ya haɗa muryarsa na rawa yace"yarinyar nan ba ta rasa iskokai akanta, daga gani aikin aljanune, taya za'ace farat ɗaya mutun ya tashi ba baki? yatsu kuma sun kuturce"? 


Jin wannan maganar Ta pravin Yasa hankalin hajiya saratu yayi mugun tashi, nan fa ido ya raina fata, dama a tsorace take da lamarin, baban tashin hankalinta kada itama abun ya shafeta, tunda kwana nan suna mutunci da marwa saboda aikin leƙen asirin da take yi mata, batare da kowa Ya lura ba, ta lalla6a ta fuce daga dakin marwa, jiki na kerma ta koma bedroom dinta, ta yi shirin zuwa office don ta bar gidan, saboda rashin tausayi maimakon ta tsaya su nema mata mafita tunda dai ita takeyiwa aiki

Baiwar Allah marwa ba halin Yin magana, kukan zuci take mai ɗacin gaske, ga abu tana so ta fada amma takasa sai kallon hajjaty da pravin takeyi hankalin ta yafi kakarta akansu


Dakyar baba obie Ya haɗiye tashin hankalin shi, Ya dubi maids din dake kuka cikin sanyin murya yace"kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, ba kuka yakamata kuyi mata ba, addu'arku take buƙata..." ya fada tare da kallon Hajjaty"ku taimaka ku dauko ta, muje asibiti aduba lafiyarta. " da sauri hajjaty da Abla suka haɗa karfi wurin cuccu6ar marwa suka fito daga dakin sauran masu aikin suka bi bayansu, tunkafin su fito baba obie yayi waya da ɗaya daga cikin jami'an gidan, Aka fiddo da mota mai kama da bus, aciki suka shigar da ita, kowan nan su Ya samu wurin zama, motarsu baba obie da pravin tana abiye da tasu a jere motocin suka fuce kaitsaye suka nufi asibiti💔 tunkafin sukai asibitin marwa take ta kallon hajjaty kamar zata hadiyeta ita kanta hajjatyn dake aruke da ita tayi matuƙar tsorata da kallon da marwa keyi mata ga wani nishi da gurnani da takeyi😢


(Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana❓❗)


__________________________________✍️


A zaune take kan dinning chair, ta sanya abaya dogo ajikinta, table din gabanta cike Yake da kayan breakfast  ita kadai ta rage a dining, tana cikin shan tea a cup, ƙamshin turaren dr shureim Ya daki hancin ta, da sauri ta ɗago tare da kallon inda take jiyo sautin tafiyarshi, a tsanake Yake tafiya cikin kamala, Ya sanya shadda a jikin shi ta zauna mashi yayi wani fresh da shi hannun shi ruƙe da car key,

Tunda ta kafe shi da ido sam ta kasa daina kallon shi, saboda yayi mata kyau

Karasowa yayi gaban dining din, fuskarshi dauke da murmushi Ya furta"sanyin idaniya, ina fata kin tashi lafiya"? Farfari tayi mashi da ido hadi da sakar mashi murmushi kafin tace"hubbyna na tashi lafiya, ina fata kaima haka"

Yace Alhamdulillah,

"Yaya shurem, Ka zauna mu yi breakfast, ko ka riga da kaci ne? Yau ni kaɗai na rage a dining, ban iske kowa ba .." 

"Bana jin yunwa, Inason zan fita ne" yanayin fuskarta ne Ya canza, kamar zata fashe mashi da kuka tace"dan Allah ya shureim kada ka tafi kabarni agida ni kadai, kaga mommy ta tafi office, daddy da uncle sun je party meeting, kullum sai ni kadai kuke bari agida bana aikin kome" ta faɗa da shagwaba...

Shiru yayi yana tunanin meya kamata yayi? Shi ma baison suna tafiya su barta agida ita kadai baisan ya zaiyi da ita bane tunda bata son zuwa asibiti wurin Benazir, gashi har benazir ta fara tambayar shi ina zeenatu, itama hajiya layla abun ya fara damunta duk in yaje sai tace wai meya hana zeenatu zuwa. 

Wata dabarace ta fado mashi aranshi, da sauri ya dubeta ta kura mashi blue eyes dinta masu walwali

"Zaki rakani mu tafi atare inda zanje"? 

"Ina zamuje"?

"Wani wuri ne..." shiru tayi jim kafin tace"ni dai saika fadamin ina ne"

"Yawon buɗe Ido" waro ido tayi kafin tace"dagaske"? Jinjina mata kai yayi alamar eh, da sauri ta mike tana fadin"yaya shureim bari naje na canza kaya"

"Okey, ki same ni a mota, but karfa ki dade" amsa mashi tayi da toh, jikinta na rawa tsabar zumudi ta nufi part dinta

Murmushin gefen fuska shureim ya saki aranshi ya furta"yau zanga meke akanki my zeenati"! Ya faɗa tare da juyawa ya fuce daga falon


After some mins, Yana zaune a driver's seat, Ya dan jingina kanshi jikin headseat, har ya lumshe idanun shi Yaji motsin buɗe car door, A hankali Ya kalli zeenatu dake kokarin shigowa ciki, wani irin sanyayyan kamshin turarentane Ya ratsa hancin sa, kamar wadda zataje gasar miss world, wata hadaddiyar emirati abaya ce ta sanya launin yellow, abunka ga jinsin turai ta fito fara fess rigar tayi mata kyau, ga wani veil da tayo rolling, hannunta ruƙe da wayarta, kafarta kuwa wasu highhills ne masu tsini, harta zauna dr shurem bai daina kallon ta ba...

Farfari tayi mashi da ido voice dinta da shagwa6a tace"yaya shureim wannan kallon fa" kayataccen murmushi ya sakar mata, tare da kai hannu ya shafa sajen shi, key yai wa motar, ya ɗanyi reverse kafin Ya fara driving slowly Ya nufi katafaren gate din gidan, tunkafin Ya karaso waɗannan Samudawan security office din suka yunkuro kamar zasu rufe motarshi da bugu ba don komai ba sai don saboda Ya dauko zeenatu...

Ba arziki yayi parking motar, ya sauke glass din Yana kallon su

da kakkausar murya daya daga cikin su Yace"da iznin wa zaka fita da ita.. " saboda karfin hali na dr shureim Ya wani hade fuska Yace"daddyn ta ne Ya bani izni" arude zeenatu ta kalle shi wato taji ya shureim yayi karya agabanta

"Amma mu bai fada mana ba"!

"Ku kira shi awaya sai kuji" ya fada yana ƙara tamke fuskar shi

Kiran alhaji musa sukayi wayar tayi ta yin ringing ba'ayi picking ba, dr shureim Allah Allah Yake kada Alhaji musa ya ɗaga, kai hada addu'a yayi a zuciyar shi, cikin sa'a bai ɗaga ba..

Muryar zeenatu na kerma tace"ku kira mommy ku tambayeta, ay itama tasan da zancen fitarmu, daddyne ma yace ya tafi dani..." ba suyi ƙasa a gwiwa ba suka kira hajiya saratu bugu uku kafin suka samu ta ɗaga...

"Ranki ya dade, da izninki dr shueim zai fita da zeenatu"? Kallon juna zeenatu da dr shureim sukayi duk suka sha jinin jikin su, fargabansu kada hajiya sarah ta kwafsa masu


"To amma shi yalla6ai yasan da fitar su? 

Hajiya sarah tace"eh ya sani, kawai ku barsu su tafi"..kusan atare dr shueim da zeenatu suka sauke ajiyar zuciya.. munafukan gate officers din ba don sunso ba suka basu hanya, dr shurem Ya ƙara wa motar gudu Ya fuce daga gidan....


Lumshe idanu zeenatu tayi tana dariya tace"ya shureim kasan Allah da ace daddy ya ɗaga kiran nan da sukayi mashi wallahi bazai bari ka fita dani ba, ni narasa gane dalilin dayasa yake kullena kamar wata matar aure..."

"Mommynki ta rufa mana asiri wlh, naji dadi my zeenatu, kinga yanzu zamu sakata mu wala..." yai maganar hankalinsa na akan driving din da yakeyi, A hankali ta daura hannunta saman  dayan hannunshi gefe tare da lumshe idanunta, har satar kallon ta sai da yayi kamar wata jinjira komai nata burge shi yakeyi...


________________________________✍️


Gaba ɗayansu sun shirya tsaf, zasu ziyarci gidan uncle abdallah, tun daga kan mami, ummi, zahra, abi, da uncle ɗan iya, kowannansu ya ɗauki wanka na mutunci namu na hausawa, mutun biyu ke babu a cikin su, mahboob wanda tun safe ya tafi kai baby junaid school, har yanzu bai dawo ba..

A tare suka fito daga falon gidan, suka nufi harabar ajiye motocin su, 

Mami tace"yau dai Allah Ya nufa zamu cika mata alkawari, baiwar Allah mun saka mata rai, kullum ayta za'aje za'aja amma shiru.." ummi tace"nasan zatayi farin ciki idan taganmu kwanmu da kwarkwatarmu don ma babu junaid, ay da sai tafi jin dadi munzo mata da ɗan jikallan ta..." .murmushi kowannansu Yasaki,

A bakin motocin suka dakata da yin tafiya, suna jiran Aneelerh da zahra su fito,

Abie Yace"wai zaman me sukeyi agidan? Kwalliyar ce har yanzu ba'a gama ba? 

Uncle ɗan iya yace"da rabon mu tafi mu barsu agidan sun taho daga baya, dama tafiya indai da mata za'ayi ta to fa sai an 6ata lokaci, su komai nasu da nawa babu karsashi..." ya faɗa yana haɗe fuska....


Acan cikin gidan kuwa, fitowa zahra tayi ta dauki wankan atampa, an yafa veil a kafada, hannu ruke da jaka, ta ca6a uban ado, dakin aneelerh ta nufa, kafin takaiga kofar dakin sai ga Aneelerh fito cikin sauri, wata hadaddiyar lafaya ta laga a jikin ta,launin orange mai adon stones, ta fito ɗass abunta, itama ta ruko handbag din ta, zahra na ganinta taci burki tana fadin"Aunty aneeleeh! kinga yadda kikai kyau? Meyasa baki fadamin lafaya zaki sanya ba nima ay saina sanya nawa" ta fada tana hade fuska, murmushi Anila tayi"kai zahra ay kin ma fini kyau, kinga su abie suna jiranmu, mu tafi kada mu 6ata masu lokaci" ta fada tare da ruko hannun zahra suka fara tafiya, har sun kusa fita daga falon muryar Ana ta katse masu hanzarin su


"Aunty Anila, Allah ya kiyaye hanya agaishe min da hajiya adama..." dakatawa sukayi da yin tafiyar, a wani irin yanayi Anila ta dubi fuskar Ana wadda ke acan tsaye kofar kitchen jikinta sanye da riga da mini skirt, ta ɗaure kanta da hula sai faman sakar mata murmushi takeyi . 

Batasan ya akai ta tsinci kanta da jin faduwar gababa, 

"Zahra kunyi kyau sosai, kun burgeni, sai naji dama hada ni zaku tafi" murmushi zahra ta sakar mata"mungode kada ki damu next time idan zamu ƙara zuwa hada ke zamuje, yanzu dai ki koma kitchen, pls kafin mu dawo ki gyara mana bedrooms dinmu sunyi datti..." amsawa tayi da toh, kafin ta sake kallon Anila wadda keta kallon ta ko kyaftawa bata yi murmushi Ana ta sake yi mata

"Aunty anila, adawo lafiya.."

Dakyar ta jinjina mata kai, cikin sanyin murya ta furta"Ana ba lallai mu dawo da wuri ba! Ki kula da gidan, sai anjima" awani slow ta kau da idonta daga na Ana, taja hannun Zahra suka fuce daga gidan...


Ana tana a kitchen tana goge gogen floor da wiper ta jiyo tashin motocin su,


*AGIDAN UNCLE ABDALLA"


Hajiya Adama Yau ba zama, tunda Anila ta sanar da ita zancen zuwan su, ta fara yan gyare gyaren gida, ganin tana ta wahala ita kadai ga girkin da zata yi masu ko farawa batayi ba, hakan yasa Uncle abdalla Ya dauko mata hayar house help wata bayerabiya kakkarfa, atare da ita suka fara girkin cikin kankanin lokaci suka kammala shi, hajiya adama har mamakin matar takeyi kamar inji bata gajiya da aiki, tana da kwazo da ƙwarewa ta bangaren aikace aikacen gida, kafin wani lokaci sun kammala tsaftace gidan.. 


da sauri hajiya adama ta shiga toilet, tayo wanka, ta fara shirya kanta,wani tsadadden leshi ta sanya a jikinta, ta kashe daurin dankwali, ta zauna kan mirror chair tana ƙarasa yin make up ɗin ta...

Sallamar uncle abdalla ce ta katse ta, 

"Har yanzu ba su iso ba"? ta cikin mirror ta kalle shi suit ne a jikin shi..

"Nima naji shiru, amma ina ji araina sun kusa karasowa, 

"Kodai basu gane gidan bane"?

"Bana tunanin hakan, ay na tura mata address din gidan tun jiya, bari na kira Anila naji.." ta fada tare da miƙewa ta nufi wayarta dake ajiye kan mattress, kafin ta ɗauko kiran waya ya shigo da sauri ta duba sunan mai kiran nata, murmushi tayi tare da kallon uncle abdalla"Anila ce ke kira" picking call din tayi ta kara wayar a kunne

"Anila kun taho ne"?

On the other hand anila tace"Eh, dama na kirane in fada maki mun kusa shugowa unguwan naku" wani irin farin cikine ya lullu6eta"Allah ya kawo ku lafiya" bayan ta katse kiran ta kalli uncle abdallah"tace min sun kusa isowa, yakamata muje mu taro su" 

Murmushi uncle abdalla yayi"naga kina ta zumudin zuwan su, idan ma don saboda junaid ne kwara ki fidda rai, yau ranar school ne, ba lallai su zo da shi ba" daure mashi fuska tayi"ko baka fada ba, na sani, farin cikin dakaga inayi badan komai ba sai don saboda za'a kawo min ziyara gidana, kasan ba wani ke gareni a garin nan ba..." tay maganar tare da daukar mayafi ta yafa akanta,

Tayi gaba yabi bayanta. daidai lokacin da suka fito daga entry hall, suka hango mai gadin gidan Ya buɗe gate, a jere motocin suka kunno kai cikin gidan,

Bayan sunyi parking, hajiya adama ta nufi motocin da sauri kafin ta karaso anila ta rigata fitowa da sauri ta nufe ta suka rungume juna fuskar kowannansu dauke da annurin farin ciki.


 Abie da Uncle dan iya suka nufi uncle abdalla dake tunkaro su, suka fara yin gaisuwarsu ta manya” Sassannun ku, da zuwa, ku ƙaraso ciki”, Mamie da hajiya adama suka rungume juna fuskar kowan nan su ɗauke da murmushi, bayan sun raba jikinsu, Ummi ta miƙa mata hannu suka gaisa a mutunce,kafin ta janyo zahra tayi hugginta dinta, daga bisani suka haɗu gaba daya suka shiga falon gidan, yau ne karo na farko da su anila suka fara zuwa, zahra sai yan kalle kalle takeyi gidan ya burgeta ginine babba, ita kanta anila tayi mamakin haduwar gidan surukan nata, an wadata gidan da duk wani abu na biyan bukata. 


Bayan kowan nan su Ya zauna kan sofa, Uncle dan Iya yace"masha Allah, kunsan ni bani gani inyi shiru, abdalla kayi kokari wannan dankareran gida haka kamar dubai"? ya fada Yana bin falon da kallo, hakan ba karamin dariya ya basu ba, 

Mami tace"naso ace tuntuni mukazo ganin gida Allah bai nufa ba sai yau, gaskiya bamu kyauta ba.." hajiya adama tace"ay kun goge laifinku, tun da kuka zo  yau gaba dayanku don ma babu jikalle na..."

Mami tace"Allah sarki, Ya tafi school,  abunda yasa ma bamu tsaya jiran shi ba, sai marece suke dawowa.."


Fira ce ta barke tsakaninsu yadda kasan dangi ɗaya, daga bisani bayerabiyar dake a gidan ta shirya masu abinci akan dining, suka hallara gaba daya suka zauna suna ci, uncle dan iya sai santin abincin yakaye yi, ita dai anila hankalinta kamar ba akwance yake ba, ta kasa cin abincin, saboda wani irin faduwar gaba da take ji..  

"Anila meke damunki ne? Naga kamar bakison cin abincin" cikin kulawa hajiya adama tay maganar, cikin sanyin jiki Anila tayi murmushi tace"babu komai mommy, abincin ne yayi min dadi shiyasa nake santin shi" dariya hajiya adama tay"karki damu idan ma baki koshi ba zansa akara maki ne nafi so ku ci ku koshi dama saboda ku akai girkin dayawa" murmushi kowan nan su yayi, zahra ba baka sai kunne Hankalin ta na akan plate din fatan doyan da take ci......


_______________________________✍️


A hankali motar dr shureim ta kunno kai cikin entrance gate din asibitin, bayan yayi parking din motar, Ya dan juya ya kalli zeenatu data langwa6e kanta kan shoulder dinshi, kwata kwata batasan inda suka zo ba, ta nutsu tana shakar kamshi turaren shi ta wani lumshe idanunta...

Cikin sanyin murya ya furta"zeenatu mun ƙaraso" buɗe idanunta tayi tare da gyara zamanta, kwata kwata bata lura da inda suka zo ba, kusan atare suka fito daga motar, kamar ance ta kalli saman ginin karaf idanunta suka sauka akan sunan asibitin da aka rubuta da manyan haruffa masu daukar ido, wani irin bugu kirjinta yayi da sauri ta dafe saitin zuciyarta,

"Yaya shureim! Ina ne nan? Kamar asibiti nake gani? Dama nan zaka kawo ni"? Cikin rawar murya tay maganar tana ja da baya

"Zeenat ki kwantar da hankalin ki, kamar yadda kika gani asibiti ne, wurin auntynki benazir na kawo ki, kullum saita tamabayi kina ina meyasa baki zuwa dubata...." bai ƙare maganarba, zeenatu ta juya a firgice ta damƙi murfin motarsu ta kutsa kai zata koma ciki da sauri Ya cafki hannunta ya fiddo da ita yana fadin meya haka zeenatu? Meke damunki ne? Benazir din ke bakison gani" wani irin kakarwa jikinta ya farayi ta ɗaura hannu biyu akai ta fasa wata iri gigitacciyar ƙara wadda tajanyo hankulan visitors din dake zarya a harabar asibitin, gaba daya hankalin mutane ya dawo kansu wasu har sun fara tambayar meya faru? wasu kuwa sunyi tunanin wani mugun abun akai mata...."

Cikin shesshekan kuka da murya mai ƙaraji take fadi "bazan shiga ba Yaya shureim ka maidani gida, wayyo Allahna na shiga uku, na bani ya shureim...." tsantsar tashin hankali ne akan fuskarshi gaba daya tabi ta rikitashi, ga jama'a da suka tasa shi gaba suna tambayar me akai mata...bai san sa'adda ya janyota kan kirjinshi ya rungumeta sosai kamar zai maida ita cikinshi, idanunshi sun kaɗa jawur yai saurin kai la66anshi saitin kunnanta, A hankali ya fara zuba mata kira'ar alqur'ni wohoho zokaga idanu mutane sun nutsu suna ba idonsu abinci, wasu sai santin karatun shi sukeyi, yayin da wasu kuma suka kokwanton watakil aljanu gare ta, wani irin sanyine ya ratsa zuciyar zeenatu, gaba ɗaya ta narke mashi tana faman sauke ajiyar zuciya, tuni ta nemi kukan da takeyi ta rasa shi, tayi shiru sai ƙara nutsa kanta cikin kirjinshi takeyi, mutanan dake kallonsu sunyi masu ƙawanya hada masu daukarsu hotuna da video hakan yasa shi kare fuskarshi ya ƙara ƙanƙame zeenatun shi, ahaka yajata suka nufi cikin asibitin don bayajin zai iya juyawa da ita gida.💔


Duk ta kankame shi, mutane sai kallonsu sukeyi, nurses har tambayar shi suke yi patient ce? Yace masu a'a lafiyarta lou, 

hajiya layla dake tsaye tana waya bakin kofar privet room juyowar da zatayi keda wuya ta hango su, arude take binsu da kallon har suka karaso inda take

"Shureim wacece wannan ka rungumo haka"?  Ta fada tana kallonta sam bata gane wacece ba saboda ya rufe fuskarta.

"Mami zeenatu ce, tazo duba jikin benazir ne"

A ruɗe tace"meke damuntane? Ke zeenatu ya akai? Ko bakison zuwane aka matsa maki? Muryarta kasa kasa ta furta"bana jin dadin jikina..."

"Haba shureim kasan bata da lafiya ka taso ta? Ko likita kukazo gani ne"? 

"A'a mami, lafiyarta qalou, zanyi maki bayanin abunda ke damun ta, mu shiga daga ciki....." 


___________________________________✍️


A lokacin Unaisah tana zaune kan chair din gaban gadon Benazir, hannun ta ruke da glass na ruwa, magani take bata in ta sanya abaki saita bata ruwan ta sha, ta maida kanta kamar ƙaramar yarinya agaban unaisah, har yanzu bata daina binta da kallon kurullan ba...

"Mommy ki maida hankali kan ruwan  da kike sha, kada ki shake" murmushi taskar mata"bana gajiya da kallon ki ne, Kin sace min zuciyata" da mamaki unaisah take kallonta, kalaman matar suna sanyata kokwanton kamar ta dawo hayyacin ta

 Shigowarsu dr shureim dakinne Yaja hankulansu ga kallon kofar, 

"Benazir yau Allah yayi, zeenatu tazo dubaki, sai dai kamar bata jin dadin jikin ta,..." da wani irin yanayi benazir ke kallon zeenatu wadda ta 6oye fuskarta jikin shureim...cikin sanyin murya ta furta"Zeenatu...."! shiru bata amsa mata ba, Unaisah dai ta zuba ido tana kallon matashiyar dake kankame da shurem, jikinta sai kerma yakeyi kuma taƙi dago da fuskarta...

"Zeenatu bakiga auntyn naki ba"? In a low voice ta furta"bana son ganinta" waro ido waje benazir tayi sam ta manta da pretending din da takeyi saboda ruɗewar da tayi, lamarin ya daure masu kai, arude hajiya layla ta kalli shureim suka hada ido, unaisah dake kallon su abun ya bata mamaki aranta ta ayyana kowacece wannan take ta wani boye fuskarta? Yanzu haka bawani kyan kirki gareta ba, in banda wulakanci hada wani cewa bata son ganin mamanta, yanzu haka yar kishiya ce... Acikin zuciyarta take wannan sambatu

Banezir kuwa jikinta yayi sanyi lakwas zuciyarta ta karaya da jin kalmar da zeenatu ta furta abun Ya girgizata sam takasa magana sai motsa la66anta take

"Pls kada hakan Ya dame ku, bayin kanta bane, Ina tunanin iska ne suka shiga jikin ta..." calmly ya zayyana masu komai dangane da abun da ya faru ranar farko da ya koma gida har yayi mata maganar benazir ta share shi, har zuwa ga abunda ya faru yau, mami ta tafa hannu tana ambaton "inna lillahi wa'inna ilaihirraji'in zeenatu Allah ya baki lafiya, Allah ya yaye maki abunda ke damunki, baiwar Allah ashe shiyasa tadaina zuwa asibitin, sannu zeenatu ta faɗa tana leƙen fuskarta, banza tayi da ita, benazir dai takasa magana kallon su kawai takeyi, ita dai unaisah ta baza kunne tana sauraron su bakomai ya bata haushi ba face Yarinyar da take ta boye fuska.


"Yaya shureim ka maidani gida! Kada daddy ya dawo ya iske bana nan!..."

Cikin kwantar da murya yace"ko ya dawo ba abunda zaiyi maki, ai ni na fito dake, da anjima zan maidaki, mu karasa ciki ki zauna..." yai maganar yana kokarin janyota cikin dakin, aikuwa ta turje tana yan fizge fuzge Hankali atashe mami tace"shureim abun da ban tsorofa kamar ba zeenatu ba, pls ka maida ita gida, tunda ta nuna bata son zama nan din..

Shi dai baison Ya maida ta gida saboda bai shirya komawa ba

"Mami babu kowa gidan, ita da kanta ta nuna batason zama ita kadai shiyasa na taho da ita..." ya fada fuskarshi ayamutse...

Saukowa Benazir tayi daga kan gadon ta tsaya agabansu cikin karyayyar murya ta furta"zeenatu! dagaske bakison gani na"? da wata irin tsiwa ta furta"Bana son ganin ki, ki daina yi min magana...." kafin ta ƙare maganar, Benazir takai hannu ta damƙi shoulder dinta dakyar ta rabata daga jikin dr shureim ta jijjigata da karfi har mayafin daya rufe fuskarta ya zame kan kafaɗarta....


Kamar daga sama sukaji Sautin fashewar glass kusan atare suka kai dubansu ga Unaisah wadda ta miƙe a sukwane tana faman zazzare idanun ta, tsantsar tashin hankali da rudani ne akan fuskarta

"Azeezaty meya faru...." hada baki sukayi wurin tambayar ta, la66anta sai kerma sukeyi gaba ɗaya ta rikice ta kasa magana, gabanta na faduwa ta nufi zeenatu wadda ke ta kerma tana zare blue eyes dinta akan fuskar Unaisah 


Wani irin gumi ne ya wanke fuskar Angel duk da sanyin A.c din dake a dakin, ta sanya tafukanta ta murza idanunta saboda tana kokwanton ko dai gizau takeyi mata ne? In ba haka ba tayaya mutumin daya mutu zai dawo araye? Ta kasa yarda da abunda idanunta ke nuna mata, kusan sau uku tana murza su don su dawo dai dai, Hankulan su dr shureim na akanta, sun rasa gane meke damun ta! Ko dai tasan zeenatu ne? Meyasa ta razana da ganin zeenatu harta fasa water glass din hannun ta! Dukansu kansu ya daure

Agaban zeenatu ta tsaya suka fuskanci juna, ido cikin ido, dafe kai unaisah tayi da hannayenta biyu saboda wani irin sara mata da yayi, zuciyarta ta fara dakan uku uku, Muryarta adabarbace ta furta*"UNAIZA❗❓* 

*Daga Alkamin Boss Bature🔥✍️*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post