Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 35 Complete
Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 35 Complete

Takun Ƙarshe

DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✍️💋✊🔥

Agaban Zeenatu ta tsaya suka fuskanci juna, ido cikin ido, dafe kai Unaisah ta yi da hannayenta biyu saboda wani irin sara matan da yayi, zuciyarta ta fara dakan uku uku, Muryarta adabarbace ta furta"UNAIZA❗❓ 

Arude Hajiya Layla ta maimaita sunan Unaisah

Dr Shureim yace"wacece Unaizah"? Cike da fargaba Unaisah ta nuna Zeenatu da yatsan ta"ita ce, Yar uwarmu Unaizah...." gaba daya ta rikita lissafin ƙwaƙwalwarsu, Zeenatu da ta gama ruɗewa idanunta Azazzare ta furta"bani bace! Ni bansan ki ba, ban ta6a ganin ki ba. ..." Sautin muryar Zeenatu ya ƙara rikirkita ta, runtse idanunta tayi brain ɗinta ta fara tariyo mata muryar Unaizah idan tana magana! Tabbas wannan Unaiza ce ta dawo...." 


fashewa tayi da kuka ta cakumi hannayen zeenatu"wallahi ke ce, Unaizah din mu, yar uwarmu wadda ta rasu tayaya akai kika rayu bayan kin mutu ..."? Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana.


Al'amarin yayi matuƙar ɗaure masu kai, Hankali atashe Benazir ta furta"babyna wacece Unaiza? Shiru Angel ta yi hawaye na sintiri kan fuskarta...

Dr shureim yace"kodai tayi maki kama da yar uwarki ne? Ita wannan sunan ta Zeenatu ba Unaizah ba, bayan haka naji kin ambaci yar uwarku wadda ta mutu in banda abunki wanda ya mutu ay baya dawowa watakil sunyi maki kamane...." kalaman dr Shureim Sunyi tasiri a cikin zuciyarta, amma taya haka zai yiwu? Komai nasu iri ɗaya kamar mutun ɗaya! farar fatarsu, da launin idanunsu blue, hatta blonde hair dinsu iri ɗaya, bugu da ƙari surar jikin su, tun daga kan sirantakar su har big boobs din iri ɗaya.


Gaba ɗaya ta jefa kanta aruɗani, su Benazir sun kafe ta ido suna kallonta,

Kokwanto ta fara yi kodai gizau fuskar Unaizah takeyi mata akan fuskar yarinyar? Nan take tayi believing da abun da zuciyar ta ke fada mata saboda tasan ba mai yiwuwa bane, wanda ya mutu ya dawo, abu ɗayane zaisa ta yarda da abun da idanunta suka gane mata, wanda bakomai bane face Ƴan uwanta suga yarinyar nan! muddin suka ruɗe suka ambaci sunan ta da unaizah to anan ne zata gasgata abunda idanunta suka gane mata...."


Lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya, sam takasa janye idanunta daga kallon fuskar Zeenatu, A hankali ta kau da idonta tare da kallon su shureim wata irin kunyarsu ce ta kama ta, muryarta na rawa ta furta"dan Allah, ku yi hakuri, na ruɗe ne, wallahi tayi min kama da wata dana sani, amma ita tama mutu tun da jimawa...." nannauyar ajiyar zuciya suka sauke, har suna hada baki wurin furta"Allah yajiƙanta da rahama.."


Yawu Unaisah ta haɗiya mai zafi a makoshin ta, kafin ta sake kallon Zeenatu dake kallon ta"sister kiyi hakuri dan Allah, na tada maki hankalin ki, kuskuren fahimtane...." murmushi zeenatu ta sakar mata, su kansu saida sukayi mamakin murmushin da tayi ma Unaisah

Cikin sanyin murya ta ce"Kada ki damu, babu komai...." miƙa mata hannu Angel tayi don su gaisa, da sauri zeenatu ta zira hannunta acikin nata sukayi musabaha, yau ne karo na farko da suka fara sanin junansu amma ga dukkan alamu sun kamu da kaunar juna, tabbas da ace lokacin da aka kawo masu Unaiza ta fada mata twins ne su wlh da ba abunda zai hana ta dafe alkur'ani tayi rantsuwar wannan Yarinyar Twin sister din Unaizah ce!! Ta dai bar abun aranta har zuwa lokacin da Allah zaisa ta hadu da su Batool sune zasu kara tabbatar mata da abunda take zargi na kamannin ZEENATU da UNAIZAH.........💔.


Kafin wani ya ƙara furta kalma a cikin su, wayar shureim ta fara ringing, a hanzarce ya curo wayar daga aljihu yai picking call ɗin


"Shureim! Ka dawo da zeenatu gida, Ina jiran ka" rass yaji gaban shi ya faɗi, tun daga kan yanayin muryar Alhaji musa ya fahimci ba lafiya, ko jiran amsar shi baiyi ba ya katse kiran.


"Wanene Ya kira"? Hajiya layla ta fada tana kallon fuskarshi


"Uncle ne, Yace in maida zeenatu gida"


Ta6e baki hajiya layla tayi ba tare da tace komai ba


Har lokacin Zeenatu bata cire hannun ta daga na Unaisah ba, sun ƙurawa juna ido kowa da abun da yake saƙawa aranshi......


"Muje zeenatu" muryarshi ce ta katse shirun nasu, sallama yayi masu hajiya layla, ya ruƙo hannun zeenatu suka tafi, Unaisah bata daina kallon su ba, har leƙen su tayi abakin kofar dakin itama zeenatun suna tafiya tana waiwayon ta hada ɗaga mata hannu tayi mata bye bye...💔


*CHIEF OWAIS🔥✊*

Slowly dankareriyar motar shi ta kunno kai cikin villa dinsa, yana daga zaune ya hakimce a backseat, su biyu ne a mazaunin baya big guy dake a gefen sa, kowan nansu kaki ne a jikin shi, da alama sun kwaso gajiyar aiki duba da yadda kowan nan su ya lumshe idanun shi kamar masu jin bacci.. .. bayan sun karasa parking space agent din dake driving nasu yayi parking 

A hanzarce Wani agent daga cikin jami'an dake kai komo a harabar ya karaso ya buɗe masu murfin motar.


"Sir, mu shiga daga ciki" ya faɗa yana leƙen fuskar shi yayi shiru, soft lips dinsa sun bushe sun ɗan ciza kalarsu pink kamar bazai motsa ba, big guy yayi tsammanin bacci yakeyi hakan yasa shi kai hannu ya dafa shoulder din shi, da wata irin kasala ya buɗe reddish eye dinsa tare da kallon big guy


"Mun ƙaraso gida, nayi tsammanin bacci kake yi.." yamutsa fuskar shi yayi, da zolaya big guy yace"ka bani dama in goya ka mana.." harara chief ya jefa mashi tare da zura kafar shi ya fito daga motar, da sauri jami'an dake a wurin suka buga kafa tare da sarah mashi, ko ta kansu baibi ba ya nufi cikin gidan, big guy yana abiye da bayan shi....


Har ya kusa shiga main falo, wayarsa ta fara ringing, gajiya ta hana ya dauki wayar, kaitsaye ya nufi upstairs Yana shiga daki, Ya rage kayan jikin shi ya fada toilet....

Ganin ya shiga ciki yasa big guy yin kwana ya fita daga dakin..

After some mins, ya fito daga wanka waist dinsa a ɗaure da towel ya nufi walk-in closet dinsa ya shirya kanshi cikin hanley shirt tare da black trouser na shan iska..



Bakomai yake son gani ba face Danish, Yau da tunanin shi ya wuni a office, Yaron ne ya tsaya mashi arai, baisan meyasa yake jin shi sosai acikin ranshi....



Yana ƙoƙarin zama gefen gadonsa, phone dinsa ta fara ringing sai time din ya tuna da kiran da akayi mashi dazu


Ɗaukar wayar yayi daga kan pillow Ya duba sunan mai kiran nashi

Yayi mamakin ganin kiran ta! saboda basu cika yin waya ba...daidaita nutsuwarshi yayi kafin yai picking ya kara wayar a kunne tare da yi mata sallama ya gaishe da ita cikin girmamawa.


On the other hand muryar sheikha mujeedat ta amsa mashi sallamar shi cike da dattako ta fara yi mashi magana cikin harshen turanci tana hadawa da arabi


"My in-law, did you see the message I sent you on WhatsApp"!


"I just got back from work,  ban kaiga dubawa ba..."


"Okay, ka duba yanzu, ina so zamuyi magana dakai" amsa mata yai da toh ta katse kiran..


Zama yayi gefen gadon kafin ya shiga whatsapp dinsa, kaitsaye idanunsa suka sauka akan sakon gimbiya mujeedat, calmly ya fara karanta abun da ta turo ma shi


_*DNA Paternity Test Report* _


A tsanake yake bin bayanan da result din ya kunsa har yakai karshen sakamakon 


_"DNA Profile Match: 99.99%. Paternity Index: 100,000,000:1 (extremely high probability). Conclusion: The DNA analysis conclusively confirms that Danish is the biological son of Sheikha Mujeedat bin khalid AlMaktoum._


Lokaci ɗaya chief ya zabura ya miƙe jikinshi na tsuma, tsantsar ruɗani da al'ajabine akan fuskarshi, A kalla ya maimaita karanta sakon yafi sau ashirin kamar irin bai fahimci me aka rubuta ba saboda tsabar kiɗima da mamaki! Tayaya haka zai yiwu? wai ma Wani Danish din ne? Na wurin shi da yake ruƙo ko wani ne daban"? 


Gaba ɗaya ya ruɗe tayaya ma akai gimbiya mujeedat tayi DNA test din? A yaushe? kuma daga ganin result din original ne daga babban asibitin toronto"


 Wahallan Yawu ya hadiya da sauri yai scrolling ya shiga contact ya buga mata call yana faman fitar da numfashi mai ɗumi.


Kiran na shiga Gimbiya Mujeedat ta ɗaga..." la66ansa na kerma ya furta"mommy, ki yi min bayani, ki fahimtar dani! Na gaza yarda da abun da nagani I can't believe!  I was confused, is this DNA test true? ya fada hankali atashe.


Sanyayyar muryar gimbiya Mujeedat ce ta ratsa kunnanshi


"Owais, kamar yarda hankalinka Ya tashi ka shiga rudani, nima haka na shiga, zanma iya cewa fiye da yadda ka shiga! Owais tun arana ta farko danayi tozali da yaron nan naji a jikina ɗana ne! Jini na ne shi, duk da bani da tabbaci But what strengthened my suspicions is the unconditional love Hateem has for him" 


Shiru ta ɗanyi kafin taci gaba da cewa" na san zakayi mamakin tayaya akai nayi gwajin!" bayani ta fara kora mashi dangane da yadda ta yanki gashin danish batare da sanin shi ba.


 jikin chief yayi mugin yin sanyi kamar wanda aka zarewa laka, gaba ɗaya yasha jinin jikin shi, ya girgiza bilhakki..."


"My trusted doctor conducted the test. When the results came out, I was shocked, wlh har zazzabi nayi owais..." muryarta na rawa ta ƙare maganar cikin rauni na murya


"Owais ka fadamin me kake tunani akan yaron? Kaima kana zargin jininmu ne"?


Numfasawa chief owais yayi wata juwace ta nemi daukar shi da sauri ya koma ya zauna, yana faman jan numfashi sam ya kasa bata amsar tambayar ta, abunne ya rikirkita shi.


"Owais naji kayi shiru bakace komai ba! Ni raina yana bani Omair dinmune, jinjirin dana haifa ba araye ba, amma in shine tayaya zamu iya gano gaskiyar lamarin? ni dama tun time din dana haifi yaron hankalina baikwanta da yadda aka hana mu ganin koda gawarsa ba, na dade da radadin abun a zuciya ta..."dakyar chief ya samu kwarin gwiwar furta"kin fadama uncle sakamakon DNA test din"?


"Ban fada masa ba, saboda bana so in daga mashi hankalin.." jinjina kanshi yai kafin ya furta"bazan boye maki ba, tunaninmu yazo ɗaya, nima ina zargin babyn da kika haifa ne! Amma har yanzu bamu da ƙwaƙƙwaran hujjar da zamu tabbatar da hasashenmu in gaskiyane! Dole saimun fara yin bincike mun gano tayaya akai jinjirin daya mutu ya rayu! Sannan su wanene suka sace shi daga asibitin da abun ya faru❓


"yanzu muna da shaida ɗaya a hannu, ki ajiye result din dakyau, kibar komai a hannuna nayi maki alkawarin zan binciko komai, in har yaron nan ɗankune zai dawo gare ku in sha Allah, sannan pls mommy kada ki bari uncle yaga result din nan..." ta amsa mashi da toh, kwantar mata da hankali yaci gaba da yi, daga bisani su ka yi sallama.


Shiru yayi jim yana tunani! idan har ya tabbata dan uncle dinsa ne to wanene ya sadaukar da shi? Yana jin fargaban ace hateem dinne ko wani daga cikin uncles dinsa tun da sadaukarwar na jininka ne kadai zai iya bada kai. ❗


Yana jin fargaban ranar da zai gano koma wanene! A sukwane ya fito ya nufi bedroom din Danish saboda ya yi maraicin ganin shi ya ƙara jin ƙaunar yaron a zuciyar shi fiye da kullum


Baijima da fita ba, sai ga big guy ya hauro up hannun shi ruke da wooden tray na kayan abinci, knocking kofar yayi jin shiru ba'a bude ba yasa shi tunanin koya yi bacci ne ko yana toilet

Yanke shawarar shiga ciki yayi, ya danna code din kofar ta bude kafin ya shiga da kayan abincin.


A bakin door room din Danish ya tsaya tare dakai hannu yayi knocking almost 3 times ba'a buɗe mashi ba, baya jin zai iya juyawa batare daya sanya shi a cikin idanun shi ba.


Tura kofar yayi tare da sakai ya shiga da sallama, yana zura ƙafar shi ya fara cin karo da papers din da ya kacaccala ya kekketasu akan floor, murmushi chief yayi aranshi ya furta hmm dakin ɗan koyo.


Ya yi ma bedroom din nashi kaca kaca, kamar ance ya ɗago da idon shi karaf Ya hango zanen da yayi akan white board din da yake koya mashi rubutu da shi, wata halitta ya zana kamar jagwalgwalo daya ƙura ido saiya gane maca ce, yar diyar roba da marker yayi zanan, kafafuwanta kamar na cokula, ga gashin kanta a haukace ko wacece wannan?


Murmushin gefen fuska chief ya saki kafin ya wurga eye balls dinsa kan bed dinsa a kwance ya hango shi, sai sharar bacci yakeyi kamar matacce, yar singlet ce a jikin shi fara kyal, tare da short ja, yayi wani fresh dashi.


Gaba ɗaya ya barbaza papers din da yayi amfani da su, ga notebooks dinsa daya watsar, hannun shi yana aruke da pensil da alama yana cikin yin practicing na rubutu bacci yayi awon gaba da shi.


Cikin takun sanɗa chief ya ƙasa daga gaban gadon ya zauna tare da sunkuyar da kanshi saitin fuskar danish ya ƙura mashi ido yana kallon shi, wani irin  bugu zuciyarshi ta fara doka mashi, kamannin shi sun 6aci da yaron hatta dogon hancin su, da launun hair dinsu, da shape din bakinsu iri ɗaya sak, uwa uba reddish eyes dinsu masu kyan gaske da jan hankali, yadda yake yin baccin cikin kwanciyar hankali ba karamin kayatar da chief yayi ba, har baisan sa'dda ya manna masa peck a forehead dinsa,  ya daura zira ziran yatsunsa saman tattausar farar fatar fuskar Danish mai kama data jinjiri saboda hasken ta da laushinta  ya shafa ta a hankali..


In a low voice ya furta"I hope you will be my cousin, I will be proud of you. I will give you all my care. If it is confirmed that you are my blood cousin, I myself cannot describe the joy I will feel. I will hug you tightly, I will shed my tears on you, kuma nayi maka alkawarin zan ƙwatar maka duk wani hakkinka na rayuwa da aka tauye maka! Waɗanda sukayi silar sadaukar dakai zansa suyi danasani mara amfani....." cak ya tsaya da magana ganin ya fara motsi, da sauri chief ya dago da kanshi batare daya dauke ido daga kallon shi ba, gyara kwanciyar shi yayi.


Ajiyar zuciya ya dan sauke ganin bai farka ba, hakanan yai sha'awar karanta rubutun da yayi a jikin papers din daya watsar kan mattress, paper din farko jagwalgwalone yayi bai iya gane komai ba, paper na biyune yaga ya rubuta I miss you, my Angel. Come back home..."

 

yayi mamakin handwritting dinshi cos yayi kokari ba kadan ba, har kokwanto yayi anya shi ya rubuta? ɗayar paper din ya dauko ya duba rubutun dake akai.


"I'm waiting for you, chief. Come back home..." murmushi chief yayi har dimple dinsa ya lotsa...

Next paper daya duba sunan Daddy hateem ne ya rubuta duk da akwai kuskure amma yayi kokari..." bayan ya kammala reading dinsu, ya ajiye mashi abun shi gefe daya, har zai mike yaji ya damƙi hannun shi, ya ɗan furgita saboda bai tsammaci zai farka ba..a hankali ya buɗe idanunsa sunyi ja dakyar yake ware su akan fuskar chief, da wata irin kasala ya furta"You're back."  jinjina mashi kai yai alamar eh..


Miƙewa zaune yayi tare da yin miƙa chief ya bi shi da kallo, ya jinjinama girman jikin shi, ba karamin kato bane ko'ina na jikin shi a murɗe yake irin na majiya karfi masu jini ajika.


"Fadamin kayi missing dina"? Daga mashi gira yai"nayi missing dinka sosai, tun dazu nake jiranka don muyi karatu baka dawo ba..." cheif yace"ai naga ka fara" ya fada yana nuna zanen dake akan white board din.


sunkuyar dakai danish yayi hadi da yin murmushi.


Da zolaya yace"abunda na koya maka kenen"! Girgiza kai yay "a'a!

"Wacece ka zana? Na kasa gane fuskar, Jemaima ce ko Azeeza"? Dagangan ya kira sunan su don ya bugi cikin shi...

Kasa ƙasa da murya ya furta"Angel" dariya ce ta kubce ma chief, danish ya kura mashi ido yana kallon shi.


"Haba my bro, Unaisah ce wannan Aljanar? Abu kamar agidan mahaukata, Ai ni dana ganta ƙarama nayi zaton jamaimah ne ." sunnar dakai kasa yayi batare dayace uffan ba...

nan take chief ya fahimci halin damuwar da yake aciki harya ɗan rame ta wurin kwarin idanun shi sunyi ja.


"Fadamin meke damunka.."?

Shiru yayi jim kamar mai tunanin wani abu

"Ina so Unaisah ta dawo gida, I miss her, I want to see her. She forgets me, Bata nema na..." kasa ƙarasa maganar yayi da sauri ya cusa kanshi cikin pillow.


wani irin tausayin shine ya kama owais cikin sanyin murya ya furta"am sorry danish, unaisah zata dawo gobe in sha Allah, kuma ka daina tunanin ta manta dakai, kana aranta...." muryarshi da rauni ya furta"har yanzu fushi take dani, bata sona"


har yau chief baisan soyayya ce atsakaninsu ba, yafi tunanin shakuwace mai karfi shiyasa ko kusa abun bai damun shi.


"Ina wayarka"? 


"Tana akan mirror," ya faɗa batare daya dago da kan shi ba

Miƙewa chief yai ya nufi mirror din ya dauko wayar, ya danna power ta kawo haske

Wayarsa ya curo yayi copying contact din Unaisah ya saka awayar Danish...


Kiran sunan shi yayi, dakyar ya amsa mashi na'am

Na sanya maka contact din angel a phone inka, zaka iya kiranta ku gaisa,  ko ka tura mata text message kamar yadda na koya maka..." dago da kanshi yayi wani irin dadine ya lullu6e shi, mika mashi wayar chief yayi yatsun hannun shi na kerma tsabar zumudi ya karba saida ya shiga wurin rubuta sakon ya kasa tabuka komai.


Miƙa ma chief wayar yayi"ka rubuta min..." girgiza kai chief yayi"kai ya kamata ka rubuta...yamutsa fuska yayi kafin ya fara kokarin rubuta mata sakon saida ya kammala chief ya duba abunda ya rubuta dakyar ya gane meya ke nufi a sakon ya hade kalmomin babu space babu ƙa'idojin rubutu irin dai na yan koyo,

"Kayi kokari" ya faɗa tare da mika mashi phone"ka danna send" ya amsa mashi da toh...

"Zan shiga gym ko zaka bini? Daga mashi kai yai akamar eh, da sauri ya mike chief ya ruko hannun shi kamar wa da kani suka fita a tare.💞


_________________________________✍️


Meya faru bayan komar dr shureim gida?


Tsaye yake gaban sofa ya goya hannayen shi kan kirjinshi, fuskar shi babu annuri idanunshi sun kaɗa jawur tsabar 6acin rai da fusata, abun da ya faru bayan fitar shureim da zeenatu kwatsam Motar su Alhaji musa ta kunno kai cikin gidan tunkafin bodyguard din dake driving dinsu yayi parking saiga kira daga likitan shi dr Mark, bayan yayi picking ko sallama baiyi ba muryar mark ta katse shi"yalla6ai! Da sanin ka dr  shureim Ya fita da zeenatu...." lokaci ɗaya yanayin fuskar shi ya canza zuwa tsantsar bacin rai


Saida ya mula yasha iska kafin ya furta"bada sani na ba"!


Dr mark yace"yalla6ai, dole fa sai kayi takatsantsan idan ba haka ba zamu iya samun gagarumar matsala, saboda mutane sun ɗauki hotunan dr shureim tare da zeenatu rungume da juna, a bainar jama'a sai yaɗa shi sukeyi a social media..." a kiɗime Alhaji musa ya furta"what! Are you sure"?


"Ƙwarai kuwa yalla6ai, ka duba whatsapp dinka, zan tura maka hotunan ka gani da idon ka..." katse kiran yayi, wani irin gumine Ya wanke fuskarshi saboda bacin rai! Har shi zai sanya doka agidan shi a karya"?


Alhaji ubaid dake zaune gefen shi Ya lura da yanayin shi

"Musa lafiya? Meya faru ne"? Ko kallo Alhaji ubaid bai ishe shi ba, Ya buɗe murfin motar Ya fito tamkar mayunwacin zaki Ya nufi gate security officers, suna ganinshi suka miƙe suna jiran tsammani

Wata irin tsawa ya daka masu da ta gigita dodon kunnuwansu, yana huci ya furta"da iznin ubanwa kuka bari dr shureim Ya fita da zeenatu huh!? Kafin in fita basaida na gargadeku akan kada ku kuskura ku bari ko kofar falo ta leƙo ko ba....." ya ɗage sai masifa yake zazzaga masu ta inda yake shiga batanan yake fita ba.


Alhaji ubaid Har ya fara kokarin lallashin shi aikuwa Ya daka mashi tsawa kamar ɗan cikin shi Ya nuna shi da yatsa yace"karka kuskura kasa baki, magana nake akan ƴata, ka wuce ka shiga ciki" jikin Alhaji ubaid na 6ari kamar mazari Ya juya ya nufi cikin gidan abisa umarnin Alhaji musa wato ƙanin shi 🤣



Hankulan gate officers din ba karamin tashi yayi ba, tsantsar tashin hankali da firgici ne akan fuskokinsu.


Dakyar wani daga cikin su ya samu kwarin gwiwar fadin"yalla6ai har tambayar shi mukayi da iznin wa zai fita da ita yace mana da izninka, munyi kokarin tuntu6ar layinka amma baka ɗaga ba...." bai ƙare maganar ba sakamakon zazzafan marin da Alhaji musa ya wanka mashi wlh daga tsaye duk girman jikin mutumin saida Ya durƙushe kan gwiwowinsa.


Kallon sauran gate officers din yayi waɗanda tuni sun sha jinin jikin su, babban tashin hankalinsu taya zasu fahimtar da shi cewa su ba laifin su bane? Alhaji musa bala'e ne, wani irin bauɗaɗɗan mutunne, bahago mai wuyar sha'ani.


Wani mai rabon shan duka daga cikin su ne Yayi shahada wurin furta"yalla6ai, har kiran hajiya sarah mukayi awaya muka tambayeta da izininta zasu fita tace mana eh, ta kuma ce kaima da sanin ka...." bai kare maganar ba, Alhaji musa ya daddage Ya kwashe shi da mari da tafukan hannayenshi biyu nan take bakin officer din ya fashe jini ya fara bulbulowa.

kallon sauran yayi yana jiran jin bayani daga gare su, sai tsuma suke yi suna ja da baya da alama sun razana....

"Ban ta6a sanin ku dakikai bane sai yau! Wallahi ku kuka da kanku! ....." zubewa sukayi akan gwiwowinsu suka dinga rokonshi sunayi mashi magiya don ya yafe masu, ko ta kansu bai bi ba, Ya nufi cikin gidan cikin takun nan nashi na izza,


bawan Allah Alhaji ubaid Ashe yana la6e ta window yana leken abunda Alhaji musa yakeyi ma masu gadin gidan, Yaji haushi ranshi Ya 6aci sai.......💔


Adaidai lokacin da motar dr shureim Ta kunno kai sai ga motar hajiya sarah yau ta dawo da wuri, atare suka nufi parking space bayan sunyi parking, kusan atare shureim da zeenatu suka fito, kafin hajiya sarah ta fito da sauri zeenatu taje ta rungume ta


"Sannu da dawowa mommy, ya aiki"?

Shafa kanta hajiya sarah tayi"lafiyalou my baby,..." ta fada tare da kallon shureim murmushi suka sakar ma junansu, 

"Sannu da dawo Aunty, ya aiki?

"Lafiyalou shureim ya mai jikin"?

"Mai jiki Alhamdulillah, taji sauƙi sosai, gobe muke sa ran za'a sallame ta...

da fara'a tace"Alhamdulillah, amma naji dadi, gobe in sha Allah tare dani zaku tafi..." atare suka jera suka nufi falon gidan, basu san bomb yana nan zaune yana jiran su ba.


Lokacin da suka shiga falon kusan atare suka ci burki suna kallon shi, akace labarin zuciya atambayi fuska, tundaga kan yanayin shi suka sha jinin jikinsu, Yana zaune kan sofa ya haɗe fuska kai kace bai ta6a dariya ba, ya murtuke fuska ga wani gumi da ya jike gaban rigar shaddar jikin shi, tsabar fusata zufa ta ko'ina take tsastsafo shi."


Kallon kallon suka fara jefa wa junansu, tsakanin dr shureim da hajiya sarah, kamar an dasa masu aya sun gaza ƙarasa shiga ciki....


"Daddy, yaushe ka dawo..."? Zeenatu ce ta ambaci sunan shi, da sauri ta nufe shi har takusa isa, Hajiya sarah tayi saurin cafko hannunta, shigowa ciki dr shureim yayi kamar jira yake su shigo ciki Ya miƙe agadarance ya nufi shureim Yana huci Ya furta"shureim da iznin ubanwa ka fita da zeenatu"? 

Har saida gaban shureim ya fadi saboda kalmar ubanwa da alhaji Musa ya furta.



 dakyar ya iya buɗe baki Yace"bada iznin kowa ba, ni na fita da ita saboda ta fada min tagaji da zama ita kadai agidan...." bai kare maganar ba Alhaji Musa ya damƙi gaban rigar shi ya jijjiga shi idanun shi jawur Ya kalli cikin idanun shureim.


Hankalin su hajiya Sarah ba karamin tashi yayi ba, Allah kadai yasan mai yayi niyar yi mashi amma sai ya fasa ya saki kwalar rigar ya cije la66ansa a zafafe ya ce"shureim ni kayiwa karya? Ka ce da iznina ka fita da ita? Dama malamai suna karya? Kai ko kunya baka ji ba? Ina tsoron Allahn da addinin naka huh? Runtse ido dr shureim yayi har cikin ranshi baiji dadin furucin Alhaji Musa ba, kuma bai ta6a tsammanin zai iya kallon tsabar idon shi ya gaya mashi hakan ba. 



"Ka bani mamaki shureim? A bainar jama'a ka rungume zeenatu a kirjinka, ƙato dakai baligi salon kaja min zagi a idon jama'a, so kake ka zubda min mutuncina da kimata..."? Fasa ƙara zeenatu tayi ta fashe da kuka tana fadin"Daddy ka daina yi mashi faɗa! banaso, Ka kyale shi! ba laifin Shi bane nice na rungume shi.." 


bata ƙare maganar ba, Ya dankara mata ashariya kamar bamaguje


watsawa tayi da gudu ta nufi  upstairs tana kuka tamkar ranta zai fita, tsautsayine Yaja Hajiya sarah ta buɗe baki furta"Yakamata kasan irin kalaman da zaka gaya mashi, wannan ba dacewa bane, shureim baiyi abun kunya ba kaine kayi abun kunya! Akan wani dalili zaka rufe shi da fada saboda kawai ya dauki yar uwarshi ya fita da ita! Shi ne laifi?...." kafin ta kare maganar Alhaji musa ya yai kukan kura ya ɗaga hannu zai ɗebe ta da mari da sauri Dr shureim ya shiga tsakaninsu, kai tsaye marin sauka akan fuskar shi, ji kake tasss! Waro ido waje hajiya Saratu tayi, zuciyarta ta hasala, Idanunta sun kaɗa jawur batasan sa'adda hawaye suka wanke fuskarta.


Dr shureim dake atsaye hannunsa dafe da kuncinsa, tsabar radadin marin da yaji har wasu taurari masu wutsiya ya gani suna gilmawa a cikin idanun shi, zafafan hawayene suka wanke fuskarshi, wani irin kululun bakin ciki ne Ya tokare makoshin shi, cikin karyayyar murya ya dubi Alhaji musa Ya furta"ni kadai yakamata ka hukunta saboda ni nayi maka laifi, saboda na ɗauki zeeenatu na fita da ita, kuma ni ne nayi karyar cewa da saninka, saboda ni a tunanina zeenatu yar uwatace ina da right din da zanyi iko da ita.."  ya fada yana kallon cikin idon Uncle din nasa.


"Duk akan Zeenatu kake tada jijiyoyin wuya? Meyasa? Kawai saboda na fita da ita munje asibiti duba yar uwarta! Wai duk kullan nan na menene? Ya jefa mashi tambayar, gaba ɗaya ya daure Alhaji musa da mamakin shi


"Uncle yakamata ka sani, mu fa ba makafi bane, duk wani motsinka akan yadda kake tafiyar da rayuwar Zeenatu muna lura, Wallahi abinda ka aikata yau ya sa na fara kokwanto! sannan inaso ka sani don munayi maka biyayya ba hakan yana nufin muna jin tsoronka ba, ni bana tsoron kowa sai mahallici na......" 


waro idanu waje Alhaji Musa yayi jin furucin shureim, yayi mamakin yadda ya iya kallon tsabar idon shi ya gaya mashi magana batare da jin shakkar shi ba, Hajiya Sarah taji dadin martanin da Shureim ya mayar masa.


gaba ɗaya kalaman dr Shureim a kunnan Alhaji Ubaid dake a la6e yana sauraron su, yaga komai daya faru akan idonshi, har hawaye saida ya zubar saboda yaji zafin kalaman da alhaji musa ya jefi shureim da su, sannan baiji dadin marin da yayi mashi ba, yaji takaici kamar ya binne kan shi. Yasan bazai iya yin komai ba shiyasa ya hana kan shi zuwa wurin su.


"Idan ka cigaba da yanke hukunci cikin fushi, wallahi zakayi danasani"!  Kamar sakarai haka Alhaji musa Yabi shureim da ido wato ta ko'ina ya daure shi da mamaki, Ya kasa furta kalma, ga wani gumi dake tsastsafo mashi...


"Shureim ka yi hakuri dan Allah!.." hajiya sarah ta faɗa idanunta cike tab da kwalla,"kada ki damu Aunty", A fusace Ya haura kafa ya nufi room din shi, girgiza kai hajiya sarah tayi rai a6ace ta nufi dakin ta.


Lokaci ɗaya Alhaji musa yaji jiri na niyar ɗibar shi, da sauri ya zauna kan sofa, ya dafe kanshi dake sarah mashi da hannu biyu"


_________________________________💋✍️


Lokacin da motocin su Baba Obie suka ƙaraso asibitin, a gaggauce nurses suka fito da Stretcher, Hajjaty da Abla suka ɗauko marwa da taimakon nurses suka kwantar da ita kan Stretcher, kaitsaye suka nufi cikin asibitin da ita, da sauri su Hajjaty suka mara masu baya tare da su Baba Obie, mutane sai miko gaisuwa suke yi cike da girmamawa musamman da ya shiga ciki Nurses da Docs kamar zasu durƙusa ƙasa tsabar yadda suke gaishe da shi cikin girmamawa, tuni labarin zuwan shi asibitin ya isa kunnan Md Dr. Jidenna dama mutumin shine, yare ɗaya ƙabila ɗaya sai gashi ya fito da sassarfa ya nufi Baba Obie tare da wasu daga cikin docs na asibitin, barka da zuwa suka yi mashi daƙyar yake amsa masu duk sun fahimci baya acikin kwanciyar hankalin....., a Waiting Area su Hajjaty suka zauna kamar masu zaman makoki, sai zullumi da fargaban abunda zai biyo baya suke yi na sakamakon ciwon marwa, babu wani mai kwanciyar hankali acikinsu, fuskokinsu sunyi jawur ruwan hawaye ya jiƙe su.Pravin kuwa Yana ruƙe da qugu ya haɗa uban gumi duk da sanyin A.c ɗin dake a wurin, ya kasa zaune ya kasa tsaye kamar mai fama da ɗan kanoma...


Su kan su likitocin da sukayi arba da Marwa saida suka ruɗe saboda basu ta6a ganin patient mai irin lalurar ta ba, ba wai kuturtar ba toshewar bakin nata kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba!! Wasu ƙwararrun Medical team ne suka fara bincikarta, kafin su fara aikinsu sai da suka fara tambayar me ya jawo mata ciwon!! nan fa su Hajjaty da su Abla suka kora masu  bayani dalla dalla dangane da yadda marwa ta tashi dare ɗaya da lalurar suka ce su kansu basu san menene makasudin ciwon nata ba...bayaninsu ya ƙara rikita Docs din, wannan wani irin ciwo ne farat ɗaya? 


A ƙalla Medical team din sun ɗauki tsawon awanni wurin duba lafiyar marwa, abun ya fara basu tsoro, saboda sunyi gwaje gwaje da aune aune but every result came back inconclusive. No trace of infection, no signs of trauma, lamarin Ya rikirkita su, sunyi iyakar bakin kokarinsu amma still babu wani sakamako daya nuna cewa Marwa tana da wani ciwo ko wata lalura, saima wani abun ɗaure kai lafiyarta qalou....'!  Babu irin kokarin da likitocin basu yi ba akanta sun baje fasaharsu da kwarewarsu amma ba wani cigaba sakamakon dai ɗaya ne....❗


tun safe har wuraren karfe biyar na yamma babu wani abu da likitoci suka gano, 


Lokacin da likitocin suka fito, sun hada uban gumi akan fuskokinsu kai kace ba A.c a dakin, su kan su sun jigata basu ta6a cin karo da patient din da ya basu ɗan banzan wahala irin marwa ba, duk irin kwarewarsu da kwazon su basu iya gano komai ba....


Su Hajjaty suna a zaune bayin Allah, A asibitin sukayi sallah, ruwa ne kawai ya gifta ta makoshin su, tsabar tashin hankali Ya sa sun manta da yunwar cikin su, koda ganin Docs din sun fito jikinsu na 6ari suka miƙe suna kallon su, ganin sun nufi inda su Baba Obie suke yasa suka bi bayan su, kora mashi jawabi suka shiga yi cikin harshen turanci ɗaya daga cikin su ya fara bayani,


"Duk da irin ƙoƙarin da muka yi, mun kasa samun nasara." ya fada yana ɗan girgiza kan shi, "munyi iyakar bakin kokarinmu, munyi duk wasu gwaje gwaje amma bamu ga komai ba, babu wata cuta da tayi silar kamuwarta da ciwon kuturtan da kuma toshewar bakin" tsantsar rudani da tashin hankali ne akan fuskokinsu.. Dr din dake a gefen wanda ya yi maganar ya ɗaura da cewa, "sakamakon binciken da muka yi ya nuna tana da koshin lafiya....." A ruɗe Baba Obie ya ce, "Bangane me kake nufi ba doc! ta yaya haka zai yiwu? Ga abun nan kuna gani da idonku zahiran! amma kuce baku gano komai ba"? Su Hajjaty dake sauraron su sai faman zare idanu suke yi duk sun bi sun ruɗe jin bayanan Docs.

"Mun shiga uku! dan Allah docs ku taimaka mana, wallahi rana ɗaya ta kamu da cutar...." kallon su docs din sukai ɗaya daga cikin su softly ya furta, "We're sorry, but we cannot offer more help, ba abunda zamu iya yi mata......! su kan su Likitocin damuwace ƙarara akan fuskokinsu..


"Dama saida raina ya bani jinnu ne suka shafe ta, Baba abun da yakamata mu koma da ita gida a kira manyan malamai su taru akanta watakil a dace..." Hajjaty ce ta yi maganar tana matsar ƙwalla, idanunta akan Baba Obie wanda yayi jigum saboda damuwa....gaba ɗaya sun yi amanna da maganar Hajjaty dama tun kafin su zo asibitin babu wanda baiyi tunanin jinnu bane, saboda ciwo ne kwatsam Ya afka mata a dare ɗaya ba tare da dalili ba.....

"Dr ba yadda za'ay ku buɗe mata bakin ta? Baba obie ya faɗa yana kallon docs ɗin,

Girgiza kai ɗaya daga cikin su ya yi, "Sorry Sir, We cannot perform any surgery to open her mouth, because we don't know what is causing her illness. Without knowing the cause, we could potentially make things worse. Shawarar da zan baku shine a maida ita gida a nema mata magani." Sautin shesshekar su Abla Ya cika wurin bayin Allah duk sun bi sun ruɗe ga tashin hankali......


Dafa kafaɗar Baba Obie MD Doc Jidenna yayi cikin kwantar da murya ya ce, "Kada ku sanya damuwa in sha Allah zata ji sauƙi, kamar yadda Docs din suka bada shawara kuyi kokarin nema mata magani, saboda rayuwarta tana a cikin hatsari zata iya rasa ranta..." cikin harshen igbo ya yi maganar, 

numfasawa Baba Obie ya yi kafin ya ce "To amman yanzu ni babbar damuwata ta ya zamu koma da ita a wannan halin, bamu san ta ya zata ci abinci ba hakan kuma ka ga babbar matsala ne ace mutum ya zauna ba cin abinci balle kuma ya sha ruwa, ina ganin kamar zai fi a barta a nan tun da likitocin baza su rasa dubarar da zasu yi ba su bata abincin, zamu san abun yi kafin gobe" jinjina kai MD ya yi kafin ya juya kan ɗaya daga cikin likitocin cikin harshen turanci ya yi mashi bayanin buƙatar Baba Obie in zai yuwu, amsa ya bashi da bazasu rasa hanyar da zasu yi hakan ba dama da suna bincikar lafiyarta sun saka mata ƙarin ruwa da wasu allurai da zasu ƙara mata karfin jiki ganin ta galabaita. Duk sun ji daɗin hakan, Baba Obie ya roƙesu kan su bata kulawar da ta dace kafin zuwa gobe, cike da girmamawa suka amsa mashi da zasu yi ƙoƙarin hakan. Su Hajjaty sunso su ƙara ganinta kafin su tafi, saidai basu son ƙara karya mata zuciya don sun san yanzu dole tana cikin matsananciyar damuwa ba kamar da aka kasa shawo kan matsalar tata, ba don sun so ba suka tafi kowannan su da tsananin tausayinta a zuciyarshi.


Suna a kan hanyarsu ta  komawa gida Baba Obie ya tuntu6i layin Sheikh Imam Malik ya sanar da shi cewa yana son ganin shi idan yana kusa, Sheikh Imam ɗin ya sanar da shi baya a gari, amma zuwa gobe da asuba zai shigo Abuja...lokacin da Baba Obie yake yin wayar Pravin yana zaune a gefen shi, tun da yaji Baba Obie ya ambaci yana son ganin Shiekh Imam cikin shi ya katsa, ƴan hanjinshi suka motsa, wata irin kiɗima yayi ga sanyin A.c a motar amma wata irin zufa ce ke tsastsafo mashi, sai faman zare na mujiya yake yi....! 


_______________________________✍️



A 6angaren su Aneelerh, tun Bayan sun gama kwasar girkin da akayi ma su, saida kowan nan su yayi kulu wash rabu hani'an kafin suka koma falon, firar yaushe rabo suka fara dama an kwan biyu ba ahadu ba.


Wuni su kayi agidan, kiran sallar azahar ne ya tadasu, dakin baki hajiya adama ta kai Aneelah da Zarah su mami kuma dakinta ta kaisu don suyi sallah, wato su mami sun shagaltu da kallon dakin hajiya adama an zuba kayan alatu kamar dakin wata basarakiya..


yayin da mazan suka tafi masallaci bayan sun dawo a falo suka ƙara hallara, akaci gaba da hira ga launch an kawo masu ita dai aneelah tun zuwansu gidan hankalinta ba kwance yake ba, Ana sai faɗo mata arai take, ga wannan faduwar gaban data dameta hakanan dai take daurewa, zarah ta lura da ita duk wani motsin Anila akan idonta, ta fahimci babu kwanciyar hankali atare da ita, so take su ke6e taji ko lafiya, kiran sallar la'asar ne ya sake tadasu inda kowa ya nufi dakin da yayi sallah dazu


Bayan sun gama sallah ta juyo da kallonta ga Aneelarh da dan yanayin damuwa tace "aunty aneelah miyake damunki tun zuwanmu gidan nan ina lura da ke kwata kwata kamar a takure kike ko duk tunanin Aunty benazir ne" yamutsa fuska tayi "A'ah zarah wlh Ana ce ta tsayamun a rai sannan tunda mukazo gidan nan gabana keta faduwa na rasa dalili raina ya bani kamar wani abu zai faru" cikin sanyin murya ta kare maganar, ruƙo hannunta zahra tayi a cikin mata suka kalli juna


"In sha Allah auntyna babu abunda zai faru sai alkhairi, ki daina sanya damuwa aranki sannan kicigaba da yin addu'a" 


Numfasawa tayi kafin tace"nagode da shawararki zahra, bari na kira Ana in tuna mata ta dafa ma baby junaid indomie dan kinsan daya dawo ita yake fara tambaya" murmushi zarah tayi "ina ruwan sarkin rigima" yar dariya Aneelarh tayi, tare da ɗaukar phone ta danna ma Anah kira tashin farko aka sanar da ita layin akashe yake!


kallon zarah tayi"na kira baya shiga!"


Zahra tace"maybe tana a kitchen tana aiki shiyasa ta kashe wayar, ki bari ɗan anjima kadan saiki sake kira"ta fada tare da cewa muje kar a jimu shiru"ruko hannun Aneelah tayi suka fito daga dakin, addu'a anila ta dinga karantawa a zuciyarta amma kamar ana kara mata faduwar gaban. Wannan karan tamkar ana mata dakan sakwara a kirjin ta.. A falo suka tarar da su ummi jiki asanyaye Aneelerh ta zauna tana ambaton sunan Allah, sam hankalin ta baya atare da su mami dake ta fira ko gajiya basayi, can ta tsinkayi muryar mami a kunnanta


 "Anila ya kamata ki kira mahboob ki tuna mashi kar ya manta yaje da wuri ya dauko baby junaid, kinsan bayasan jira muma yanzu zamu tashi mu tafi yamma tayi"dariya sukayi su duka ummi tace"gaskia kam" tashi Anila tayi ta koma gefe ɗaya ta kira layin mahboob yana ɗauka tace" please karka manta kaje ka dauko baby junaid da wuri... 

Katse ta yai da cewa "ohhh Aunty Aneelah saikace karatu kusan kullum sai an tunamin inje dauko sa? to ki kwantar da hankalinki baby junaid tun ƙarfe 2 yana a gida, yau da wuri aka tado su, saboda za'ayi wani taro a school dinsu, nima abokina ne dake koyarwa a school din ya kira ya fada min an tada su shine naje na dauko shi, halan bakuyi waya da Ana bane"?


Wani irin bugu zuciyar Anila tayi rass! Taji gabanta ya fadi zuciyarta ajagule ta furta"wai kana nufin tun karfe biyu junaid yana agida"?


"Kwarai kuwa, naga kamar kin daga hankalin ki, idan ma don saboda shine kada ki damu kanki yana atare da Ana ita na damka ma amanar shi"

Still hankalin ta bai kwanta ba tace"mahboob na kira layin Ana a kashe, pls ko zaka duba min su"?

voice dinta kamar zatayi kuka ga wani faduwa da gabanta keyi "ki sake kira kiji ni yanzu bana agidan na tafi kallon match" sallama sukayi ta kashe wayar hannunta har kyarma yake wurin kiran layin Ana still dai a switch off, cikin sauri ta koma falo ta gayama su ummi yadda tayi da mahboob mikewa mami tayi tare da kallon su uncle abdallah "to mufa baki zasuyi halinsu" ta fada tare da yar dariya, hajiya adama tace"wlh kamar ku kwana banso ku tafi Allah, kun ɗebemin kewa yau, Anya bazan biku ba" da zolaya uncle dan iya yace"shi kuma abdallan ina zamu kai shi? aikuwa su duka suka sa dariya, Aneelarh kamar jira take ta yafa mayafinta zarah ma haka gaba ɗaya suka fito compound din gidan inda sukayi parking car dinsu...

"Allah ya kiyaye hanya, mungode sosai, in sha Allah zanzo ganin jikana, agaida min shi..." Uncle abdalla yayi masu sallama akan idon su motocin suka fuce daga gidan hajiya adama hada kwallarta saboda bataji dadin tafiyar su ba, ruke hannunta uncle Abdalla yayi a cikin shi, suka koma cikin gidan su...

Nima na ruƙe hannun alƙalamina✍️

(Mu haɗe Jibi Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya🔥)

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post