Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 37 Complete by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 37 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✍️💋✊🔥

tun da motocinsu suka haura kan titi Aneelerh take ta tsuma ji take kamar ta ƙwace driving din daga hannun Abie don gani take kamar bai sauri, tsigar jikin ta sai tashi take, gaba daya ba ta da kwanciyar hankali..

Tsawon mintuna kafin suka ƙaraso anguwar su, baba mai gadi ya taso ya buɗe masu gate, motar abie ce farko ta uncle ɗan iya na abiye da bayan su, abie nayin parking hannunta na kerma ta buɗe motar ta fito ta nufi cikin gidan.

Mami tace ohni Aneelerh ko irin alkunyar nan babu, baka lura da yadda ta ɗaga hankalin ta ba tun agidan hajiya adama..." mami ce tay maganar tare da buɗe motar ta fito abie na dariya yace"ya'yan zamani kenan, ay su ba ruwansu da wata kunya indai akan ya'yan su ne idon su rufewa yakeyi.


Da sauri zahra ta fito tabi bayan Aneelerh, bayan ummi da uncle sun fito baba mai gadi ya karaso inda suke yayi masu barka da dawowa...


Lokacin da Aneelerh ta shiga falon ko sallama batayi ba saboda idon ta ya rufe, yaronta kaɗai takason gani muryarta na rawa ta furta"Ana! Ana! Ana...! Shiru ba'a amsa mata ba, a kan sofa ta wurgar da handbag dinta, ta nufi bedroom dinta da sauri don taga ko baby junaid na anan tana shiga ta iske dakin wayan babu kowa, fitowa tayi a fujajen ta nufi kitchen"Ana! Ana! Wai ina kika shiga ne?...." tana shiga kitchen ta taras babu kowa ranta ne ya bata kodai yana adakin Ana suna bacci"? Hakan yasa ta juya da sauri ta nufi hanyar dakin Anah 


"Aunty Anila..." zahra ce ta kira sunanta, shigowarta kenan ta hango Aneelerh ta nufi dakin Ana da sauri tabi bayanta, kafin ta karaso Aneelah ta ture kofar dakin, cike dasa ran zata gansu kwance kan gado, zura kafarta keda wuya idanunta suka sauka akan gadon Ana babu kowa akai, dakin gaba ɗayanshi a haukace yake kamar  anyi dambe a cikin shi, fululluka har biyu ta gani kan floor, ga zanin gado a yamutse yayi uban squeezing, wani abu da ya ƙara rikirkita Anila, dressing mirror din dakin data gani ya kife ƙasa, Wa'iyazubilla wani irin jiri jiri ta fara gani a cikin idanunta da wani irin azababban faduwar gaba ta ƙarasa shiga ciki kamar wadda aka zare wa laka, zahra tana abiye da bayanta sai faman zare idanu sukeyi cike da tashin hankali, tun daga kan yanayin dakin suka fahimci wani mugun abunne ya faru❗



"Mun shiga uku Aunty Anila! Meya faru da dakin Ana? Ta ina? Ina baby junaid..."? Aruɗe zahra take magana ita Anila gaba daya rudani Ya hana ta furta kalma, jikinta na kerma tasa hannu tayi knocking toilet door din dakin cike da sa ran Ana zata amsa mata, almost 3 times tana kwankwasa kofar toilet din babu alamun za'a tanka mata ko za'a buɗe kofar, da iya karfinta na karshe ta bangaje kofar da kafadarta nan take door din ta buɗe a slow ta bada wani sauti kiiiiiiiiii!


Da wani irin faduwar gaba ta zura kafarta cikin toilet din, A hankali take bin ko'ina da kallo, bata ga kowa ba, sai shower da tagani a kunne ruwa yana ta kwararowa ya malale kan floor, ga faucet ma a kunne ruwan dake 6ul6ulowa ta cikin shi Ya cika sink din harya fara gangarowa ƙasa.


Hankali atashe Anila da zahra suke karewa toilet din kallo..

Muryar Anila na rawa ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Zahra na shiga uku? Bangan su ba! Banga baby junaid ba! Ina Ana takai shi? Ina suka shiga!...



Ruƙo hannunta Zahra tayi"Auntyna ki kwantar da hankalinki, muje mu duba sauran dakunan watakil taje gyara dakin wani a cikin mu, ko kuma sun fita backyard.


Da sauri suka fito daga dakin, adai dai lokacin Su mami sun shigo suna zaune a falon suka hango zahra da Anila zasu gifta ta falon 

Muryar Mami ce ta katse su"Kai Ina zuwa haka? Kusan atare suka juyo muryar Anila na rawa ta ce"mami ba mu ga Ana da baby junaid ba, su muke nema..." jin wannan maganar Yasa ummi da su Abie suka mike tsaye

Ummi tace"kun duba ko'ina"? Zahra tace"yanzu zamu karasa dubawa..." ta fada tare da ruƙo hannun Anila suka nufi hanyar dakunan su Abie... 


Abu kamar wasa sai da takaiga ko'ina na gidan sun duba saƙo da lungu amma ba su gan su ba, nan fa hankulan mutanan gidan Ya tashi, hatta su abie saida suka tayasu neman Ana, kowan nan su Ya hada uban gumi kan fuskarshi, sai da suka tabbatar babu su agidan sannan suka dawo falo suka tsaya cirko cirko.


Fuskar mami A yamutse ta furta"to ina suka shiga ne? Ko dai sun fita daga gidan ne? Ummi tace"nima abun da nake tunani kenan, watakil ta fita da shi"



Abie ne Yace"bari nayi magana da baba mai gadi, in ma fitar su kayi zamuji a wurin shi, A hanzarce  Ya fuce daga falon Uncle dan Iya yabi bayan shi da sauri.


Baiwar Allah Aneelarh, tafi kowa jin jiki, kwata kwata babu nutsuwa atare da ita gaba ɗaya ta gama sarewa, tana zaune kan sofa, hannayenta biyu daddafe da kanta, tsantsar tashin hankaline da fargaba akan fuskarta.


Zahra dake a gefenta itama damuwarce akan fuskarta, ta dafa kafaɗar Anila tana kokarin kwantar mata da hankali, ganin yadda ta canza fuskarta tayi jawur cheeks dinta har kerma suke, dama abunda take ta zullumi kenan, tunkafin barinsu gidan hankalinta bai kwanta da yanayin da taga Anah ba! shiyasa take ta jin faduwar gaba dama sau dayawa in wani abu zai faru da bawa Allah na bashi haske kan al'amarin.


Mai gadi na zaune kan kujera Ya kure sautin radio dinshi, sam baiji Kiran da su Abie suke kwala mashi ba, har saida suka karaso gaban kujerar tukunna ya lura da su, da sauri Ya kashe radio din Ya miƙe yana kallon su


"Bayan fitar mu daga gidan nan! Wani ya ƙara fita ne"? Abie ne ya jafa mashi tambayar, girgiza kai yayi"yalla6ai babu wanda Ya fita..." can kuma yace au na tuna Mahboob ya dawo tare da junaidu, bayan shigar shi ina zaune sai ga mahbob ya fito ya shiga mota ya fuce, bayan shi babu wanda Ya ƙara fita...." bai kare maganar ba Uncle ɗan iya ya tari numfashi shi da cewa"kana nufin baga ka lokacin da Ana ta fita da junaid ba..." girgiza kai baba mai gadi yayi yace"a'a gaskiya ni banga gifcinsu ba, Ina zaune na kasa na tsare ko sauro bai isa Ya haura gate din nan batare dana kama shi ba..."  hankali atashe Abie da uncle dan iya suka kalli Juna.


"Yalla6ai wani abu ya faru ne"? Baba mai gadi ne yayi tambayar ganin kamar damuwa akan fuskokinsu...

Abie ne ya zayyana mashi abunda ke faru, baba mai gadi yace"ikon Allah! Amma yalla6ai kun duba ko'ina? Saboda wallahi ni banga fitarsu ba, Allah shine shaidata, ko gyangyadin bacci banyi ba, lokacin sallah kadai ke tada ni, kuma sallar ma abakin gate din nayita...." ba su tsaya jin karashen maganar shi ba, da sauri suka koma falon gidan, su mami na ganinsu suka mike har suna hada baki wurin tambayar abunda me ganin yace Abie ne ya kora masu jawabi.


Kaf a kunnan Anila lokaci ɗaya ta rushe da kuka tana fadin"inna lillahi wa'inna ilahirraji"un..." daga kan sofa ta sauko kan floor ta zauna dirshan, taci gaba da kuka"wallahi saida raina ya bani wani abu zai faru da su, tun lokacin da muka bar gidan nan naketa jin faduwar gaba, ashe wani abu ne zai faru da junaid dina, na shiga uku mami  ku taimaka mun! Ku nemo min Ana ta kawo junaid dina.."!! Da sauri Zahra ta rungumota a kirjinta, ta cigaba da lallashinta..ita kanta zahran kukan ne ke shirin kubce mata.


"Haba Anila meye abun kuka? Kamar dai bakiyi tawakkali ba? Wayace maki wani abu ya faru da su?  Uncle ɗan iyane ya fara mata magana cikin tausasa harshe.


Ummi tace"ni abunda nake tunani kodai Mahboob ne Ya fita da su yakamata akira shi aji" da sauri Abie ya zaro waya ya danna ma mahboob kira yana dagawa ko sallamar shi abie bai amsa ba yace"mahboob kana ina"?


On the other hand mahboob yace"ina akan hanyar dawowa gida..."


"Ana tana atare dakai"?


Da mamaki mahboob yace"ana kuma abie? Ba tana agida ba? Ko bata nan ne"?

Katse kiran Abie yayi, tare da kallon su mami dake kallon shi

"Baya atare da su..." sautin kukan Anila ne Ya ƙara karaɗe kunnuwansu...

Mami tace"amma abun da daure kai! Ina Ana taje da shi? Ke zahra kira layin Ana muji..." sai yanzu dabarar kiranta yazo masu arai, cikin shesshekar kuka Anila tace"ko kun kira akashe zaku same ta, tun muna agidan hajiya adama inata kira baya shiga.." Zahra tace"bari dai a akara kira watakil ta kunna wayar" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Anah kira, nan take aka sanar da ita wayar akashe take, nan fa hankalinsu Ya ƙara tashi, Cire hula abie yayi zufa ta ko'ina ta fara tsastsafo mashi ta kan goshin shi, idanun mami tuni sun rune sun koma Ja, al'amarin yayi matuƙar ɗaga hankulan su 


fashewa zahra tayi da kuka tana fadin"Allah yasa Ana ba guduwa tayi da baby junaid ba! Raina yana bani itace ta gudu da shi..." cikin shesshekar kuka Anila tace"ni bana zargin Ana, bazata ta6a daukar min babay junaid ba, na yarda da ita sai dai idan wani abunne ya faru da su duka biyun."


Ummi tace"Anila raba kanki da ɗan adam ba abun yarda bane, na jikinki ma zai iya cutar dakai balle ita da take yar aiki bare, Allah kadai yasan meya faru! Ina suka shiga"?


Girgiza kai mami tayi hawaye nabin kuncinta tace"dan Allah ku daina waɗannan maganganun, dukkan mu babu wanda yasan meya faru da su? Ko ina suka shiga, bai kamata mu yanke mata hukunci batare da mun san ainihin abunda ya faru ba, dududu ba yanzu muka dawo ba, mu ɗanyi hakuri kafin dare yayi watakil ta dawo da shi, mu kyautata mata zato dan Allah..." dakyar ta kare maganar daurewa kawai takeyi


Ita dai ummi hankalinta bai kwanta da Ana ba, tafi zargin itace ta gudu da junaid, dama tun lokacin da ta fada masu tana yin mummunan mafarki tafara zarginta, yanzu gashi ta 6ace babu ita ba junaid, wama yasani ko yar kungiyar asiri ce shiyasa ta sace shi har baba mai gadi baisan da fitar su ba.


Ta dai bar abun a zuciyarta gudun kada ta daga masu hankali


"Anya baba mai gadi gaskiya ya fadi? Taya za'ay su fita batare da sanin shi ba? Ga shi mun duba ko'ina babu su babu alamar su! In har bata kofar gate suka fita ba ay babu wata kofa da mutun zai iya fita daga gidan nan in ba dai 6acewa tayi da shi ba kamar yadda naga yan kungiyar asiri sunayi"


Maganar ummi ba karamin firgitar da su tayi ba, cak Anila ta dakata da yin shesshekar kukan Idanunta jawur ta dubi ummi"bangane me kike nufi ba ummi! Dan Allah ki fahimtar dani!" kafin ummi ta buɗe baki, Uncle dan Iya ya wurga mata harara, Rai a6ace yace"baki da hankali ne? Ko so kike zuciyarta ta buga ne? meya kawo wannan maganar? Maimakon ki kwantar mata da hankali saima kara dagula mata tunani kike kokarinyi! Wallahi kar in kuskura in kara jin bakinki!!" faɗa sosai yakama yi mata kamar zai rufeta da bugu, har saida Abie ya dakatar da shi kafin suka samu yayi shiru.


Miƙewa Anila tayi, zuciyarta ta karaya, jikinta yayi mugun sanyi, ga wani azababben zazza6i da ciwon kai mai raɗaɗi da tafara ji, gaba ɗaya suka bita da kallo ganin ta miƙi hanyar fita daga falo kamar bata a cikin hayyacin ta.


da sauri Abie yabi bayanta ya damƙi hannunta fashe wa tayi da kuka tamkar ranta zai fita tadinga kokarin ƙwace kanta tana sambatu cikin fitar hayyaci ta furta"wayyo Allahna abie, dan Allah ka sake ni inje in nemo baby junaid dina, bana so na rasa shi, bana so acutar min da shi, kabarni abie, Junaid shi kadai ne jinin uzair da nake da shi, idan na rasa shi bansan inda zan tsoma raina ba..."


Tana cikin yin magana ta sarƙe kwatsam ta yanke jiki zata faɗi da sauri abie ya kwanto da ita kan kirjin shi, sai lokaci mami ta fashe da kuka kalaman Anila sun karya mata zuciya, zahra ma kukan takeyi haka itama ummi gida ya zama kamar na masu zaman makoki, adai dai lokacin mahboob ya shigo falon ko sallama baiyi ba sautin koke kokensu Ya cika kunnuwanshi, hankali atashe ya karasa shiga ciki yana faman raba idanu akansu, arude yake fadin mami! Ummi! Zahra! Me..me ya faru? Daddy..bai kaiga kiran sunan abie ba yai arba da anila wadda ke rungume jikin abie, kamar ba numfashi atare da ita, tsabar kiɗima Yasa mahboob sakin key din hannun shi ya faɗi ƙasa.


La66ansa na kerma ya furta"dan Allah kuyi min bayani meya faru kuke kuka? Meke damun Aunty Aneelerh?


dakyar Zahra ta shanye kukanta muryarta a disashe ta kwashe komai ta sanar da maboob da buɗar bakinsa sai cewa yayi"ban yarda ba, wallahi bazai yiwu ba! Ni da kaina na ɗauko yaron nan daga school kafin ma mu iso gida bacci ya dauke shi, bayan nayi parking din motata na goyo shi abayana na shigo da shi cikin gidan banga kowa ba a falo, raina ya bani watakil kun tafin unguwar da naji kunce zaku je, sai na wuce da shi dakin Ana, bayan nayi knocking din kofar ta buɗe min naga idanunta jawur kamar daga bacci ta tashi, har na tambayeta ina mutanan gidan tace min ai kun tafi tun ɗazu, sai na miƙa mata junaid nace ta kwantar da shi idan ya tashi daga bacci ta yi mashi wanka ta bashi abinci, ta amsa min da toh, ta tambaye ni ni bazan ci abincin bane nace mata sauri nake zan tafi kallon match idan na fita zan tsaya agidan su abokina zanci acan, mukayi sallama da ita na juya cikin sauri har nakusa fita falon naji ta kwala min kira na jiyo na kalle ta, a lokacin ta rungume junaid dake bacci a kirjinta, ganin tana kallona da murmushi akan fuskarta yasa nace mata lafiya? Ko akwai wani abu da take son fadamin ne? Ta girgiza min kai tace a'a wai nayi mata kyau ne, bance mata komai ba, na dai ɗaga mata hannu na mayar mata da martanin murmushin da tayi min kafin nasakai na fuce daga gidan...." gaba ɗaya su mami sun kasa kunne suna sauraron mahboob dake basu labarin rabuwar shi da Ana har yakai karshe.


"Tayaya za ku ce min ba ku gan su ba fisabilillahi? Idanunshi cike tab da kwalla yayi maganr,  duk da bai tabbatar da abunda suka fada mashi ba, amma zuciyarshi ta karaya dama tunda ya damka ma Ana amanar junaid ya fita daga gidan yake ta jin wani iri, idanunshi suka dinga tariyo mashi murmushin da ta sakar mashi.



Zahara tace"wallahi mahboob babu su, ko'ina mun duba, ba Ana ba baby junaid, ni abunda ya daure min kai, dakin Ana da muka gani a haukace babu gyara, duk an jefar da pillows ƙasa dressing mirror dinta ya kife ƙasa, daga gani wani abunne ya faru, maganar zahra ta ƙara jefasu a rudani...."


Girgiza kai mahboob yayi cikin tashin hankali ya watsa da gudu ya nufi dakin Ana, don ya gane ma idon shi kafin fitowar shi Abie ya kwantar da aneelerh kan doguwar sofa, mami ta ɗauko robar ruwa a fridge mai sanyi ta buɗe murfin ta yayyafa mata akan fuskarta, dogon numfashi taja tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, a hankali ta buɗe idanunta waɗanda suka kaɗa jawur ta dubi fuskokin su, biji biji take ganin su daƙyar ta iya motsa la66anta da suke bushe ƙamas ta furta"mami ina junaid ɗina? Ana ta dawo min da shi" 


shiru sukayi fargaban halin da zata shiga ya hana wani ya bata amsar tambayarta...

Abie ne yai karfin halin furta"kiyi hakuri Anila, basu dawo ba, amma yanzu zamu tafi neman su, in sha Allah zamu dawo maki da yaronki..." runtse idanunta tayi wasu irin zafafan hawaye suka wanke fuskarta...fitowa mahboob yayi daga dakin Ana yana tafiya kafafun shi suna harɗewa saboda rashin kwanciyar hankali, dawowa cikin falon yayi ya tsaya yana kallon fuskokin su.


"Zahra kun kira layin Ana ɗin"? ɗaga mashi kai tay"mun kira akashe" tsoki Ya buga tare da ruƙe qugun shi kafin wani ya kara magana a cikin su, sautin kiran sallar magrib Ya karaɗe kunnuwan su

Uncle ɗan iya yace"dan Allah ku kwantar da hankalinku, in sha Allh zasu bayyana cikin koshin lafiya, yanzu ku je kuyi sallah kuyi masu addu'a duk inda suke Allah Ya kare mana su, in sha Allah idan muka fita zamu bi gidajen makwabta mu duba watakil adace ko sun shiga ciki"



__________________________________✍️



*💋UNAISAH ANGEL💓*



Wunin ranar Unaisah bata jin dadin jikin ta, kamar mai fama da zazzabi tun da idanunta sukayi tozali da zeenatu bata ƙara samun nutsuwa ba, Yarinyar ta tsaya mata aranta tunanin zeenatu yayi mata ƙatutu a cikin zuciyarta, ta rasa meyasa take ta faɗo mata aranta, har takai ga da zarar ta rufe idanunta fuskar Zeenatu take gani.


Tana akwance kan darduma wani guntun baccine Ya ɗauketa bayan ta kammala sallar magrib, gaba daya ta kudundune kanta cikin hijab....


Benazir tana zaune gefen gadonta tana ta kallon ta, yayin da hajiya layla ke azaune kan sofa..


"Benazir..." dagowa tayi tare da kallon mami data ambaci sunan ta, kallon kallo suka shiga jefawa junansu, tuni benazir tasha jinin jikinta, dama tun dazu da abun nan ya faru na zuwan zeenatu ta lura da irin kallon da mami takeyi mata ga wani annurin farin ciki da take gani atare da ita...


"Ya jikin naki? ɗazu naga kamar kin samu lafiya.."


shiru tayi jim tana tunanin ta yadda zata 6ullowa mommyn nasu don bata shirya bayyana masu ta samu lafiya ba, tana da dalilinta nayin haka..



Jin tayi shiru yasa mami ta sake furta"dake fa nake magana? Hannu tasa ta ɗan sosa gashin kanta tare da kyafkyafta idanunta irin yadda masu tabin hankali sukeyi sam ta kasa buɗe baki tayi magana, hajiya layla ta kura mata ido tana kallon ta, ta ɗan rude da yanayin ta aranta ta ayyana ko dai har yanzu da sauranta"?


"Mami ina baby na? Ban ganta ba? ta faɗa tare da saukowa daga kan gadon ta fara ɗaga pillow tana nemanta, hada kokarin yaye zanin gado duk don tayi pretending kada hajiya layla ta gane ta samu lafiya.


Shesshekar kukan karya ta farayi hada yarfa hannu ta juyo ta kalli hajiya layla da ta saki baki sototo tana kallon ta.


"Mami kodai wani ya sace min ita ne? na duba banganta ba.." abun ya ɗaurewa hajiya layla kai, yanzu fa take zaune tana kallon yarinyar amma farat ɗaya ta nuna bata ganta ba.


Jinjina kai tayi aranta ta ayyana lallai haryanzu da sauranta, ganin yadda tabi ta ruɗe ne yasa mami yin saurin kiran sunan ta, a hautsine ta juyo tare da kallon ta

"Gata nan a kwance kan darduma.." girgiza kai tayi"mami ba itace ba, wannan ƙatuwa ce, babyna karama ce" waro ido waje mami tayi can kuma tayi tunani kodai don taganta nannaɗe cikin hijabine, mikewa hajiya layla tayi taje gaban prayer mat din, a hankali ta cire ma Unaisah hijabin ta fiddo da fuskarta.


"Kin ganta"? washe baki Benazir tayi tare da sanya tafukan hannunta, ta rufe fuskarta tana fadin"ashe itace ta lullu6e da hijabi, shiyasa bangane ta ba, mami gobe zamu koma gida da ita ko"? Shiru hajiya layla tayi gabanta na faduwa, jin abunda Benazir tace, yanzu ya zatayi gobe idan zasu tafi? Tasan dole Benazir ta sanya masu rigima muddin su ka ce zasu raba ta da yarinyar ba karamin daga za'ay ba.


"Mami kinyi shiru..." murmushi yaƙe ta sakar mata"kinji ki da wata magana, in bamu tafi da ita ba, a asibitin zamu barta ta kwana ne"? Yar dariya benazir tayi tare da jujjuyawa tana fadin"wayyo Allahna naji dadi mami, nayi farin ciki, zamu tafi da babyna gida...." ita dai hajiya layla jikinta yayi sanyi, Da harta fara murnar Benazir ta dawo hayyacin ta ashe har yanzu bata gama wartsakewa ba.


Ringing ɗin wayarta ne Ya farkar da ita, kaitsaye sautin ya daki kunnanta, a hanzarce ta tashi zaune ta cire hijab din jikin ta, idanunta har sun ɗan kumbura, ganin hajiya layla agabanta yasa ta ɗan firgita kaɗan.


"Yanzu nake shirin tada ki daga bacci naga ko dinner baki ci ba, sai gashi kinma farka da kanki..." hajiya layla ta fada da murmushi akan fuskarta.


"Babyna..." Benazir ce ta kira sunan ta, a hankali ta dube ta muryarta da kasalar bacci ta furta"na'am mommyna..." murmushi Benazir tayi"naji wayarki tana ringing, ki duba ki ga wanene ke kiran ki" amsa wa tayi da toh, ta mike ta nufi backpack dinta ta curo wayar a lokacin har kiran ya katse.


kallon su hajiya layla tayi sam bata son yin waya agabansu, kamar mara gaskiya ta zura wayar a aljihun rigarta, ta juya ta nufi toilet ta shiga daga ciki taja kofa ta datse.

Call ta danna mashi yana yin picking tace"daddy, barka da marece? Ka wuni lafiya"?

On the other hand taj Yace"lafiyalou daughter, halan daga bacci kika tashi naji muryarki wani iri"


"Eh, bayan na kammala sallah ne bacci yai awon gaba dani"

Okey, dama na kirane don in kara kwantar maki da hankali, daga gobe ne in sha Allah za'a sallame ku da wuri, mun ma yi magana da chief ya fada min shi zaizo daukarki...." murmushi tayi har cikin ranta taji dadin jin hakan

"Allah yakaimu lafiya daddy, amma zanyi kewar mommyna..." ta fada kamar zata sanya mashi kuka, dariya yayi"ke fa da kanki kikace kingaji da kallon ki da matar keyi..."


"Wallahi daddy ina sonta sosai, bansan rabuwa da ita, jiyan ma dana fada maka ta bani tsorone ina fa bacci ta tsareni da ido amma ni ina kaunarta"


"Kada ki damu, ko bayan kin dawo gida zan iya kaiki gidan su ki gidan ta" dadine Ya lullu6e ta, sun ɗan jima suna waya kafin sukayi sallama.


Tana sauke wayar daga kunnanta, idonta ya sauka akan text message din da aka turo mata da bakuwar number, cike da mamaki ta danna sakon ya buɗe kura ido tayi tana kallon jagwalgwalon rubutun 


Daya bayan ɗaya ta fara karanta shi.


_Deer swit angil, I mis yu soooo mutch Pleeease come hom to me, and I promis to met awl your condisions I wuv yu soooo mutch_ 


Dafe kai tayi da hannu daya zuciyarta cike fal da tunanin wanene yayi mata sakon? aranta ta ayyana daga gani ƙaramin yarone ya ɗauki wayar babarsa batare da sanin ta ba, ya danna wrong number shine aka tura mata sakon, tuntsirewa tayi da dariya da sauri ta toshe bakinta tunawa da su hajiya layla acikin dakinta...


Murmushin gefen fuska tasaki cike da nishadi ta ƙara maimaita sakon saboda nata fahimci me aka rubuta ba, nutsuwa tayi sosai tana kallon rubutun tiryan tiryan lokaci ɗaya taji gabanta yaɗan faɗi ganin kamar nick name dinta wato Angel


_My sweet Angel, i miss you so much, please come home to me, and i promise to meet all your conditions i love you_  



Tabbas sakon ba kuskuren akayi ba, ita aka turo ma shi, ko wanene? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, a kalla ta maimaita karanta text din yafi sau ashirin batare data iya gano wanene ya turo mata shi ba, reply ta mayar masa"Please, may I know who you are? Bayan ta tura mashi sakon ta fito daga toilet din, a lokacin dr jazz ya shigo duba jikin Benazir yana ganin ta ya sakar mata murmushi da sauri ta gaishe da shi ya amsa mata da fara'a, bayan ya kammala dubata, yayi masu sallama ya fuce daga dakin da sauri hajiya layla tabi bayan shi.


"Dr. Jazz! Ina son yin magana dakai" tsayawa yayi tare da juyowa yana kallon ta, agaban shi ta tsaya suka fuskanci juna


"Dr mungode sosai, kana kokari akan Benazir, ubangiji Allah Yasaka maka da alkhairi, Allah yabiya maka bukatunka..." addu'oi tadinga yi mashi yana amsa mata da ameen, da alama yaji dadin addu'arta


Jin tayi shiru kamar akwai wani abu dake damuntane yasa shi furta"naji kinyi shiru ko akwai wani abu" yarfa hannu tayi fuskarta ayamutse tace"dr bansan ya zanyi da benazir ba! Ta ƙwallafa rai akan yarinyar nan, Ni damuwata halin da zata shiga idan aka raba ta da yarinyar kar akoma yar gidan jiya"


ta faɗa tana marairaice mashi fuska, yama rasa amsar da zai bata don ya fahimci kamar so take abar masu yarinyar su tafi da ita abune da bazai yiwu ba"


Calmly yace"na fahimce ki, amma gaskiya sai dai kuyi hakuri, iyayen yarinyar nan sunyi kokari da har suka iya baku ita na tsawon kwanakin nan, saboda ba karamin so sukeyi mata ba, itace kadai yar su tilo" dafe kai hajiya layla tayi da hannu ɗaya, sai yaji ta bashi tausayi.


"Nasani dr, wlh sunyi mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, ni damuwata taya zamu rabata da yarinyar? Kana gani zata hakura"?


"Kada ki damu, ni nasan ta yadda zan raba su batare da an samu matsala ba, in sha Allah komai zai tafi dai dai" gyaɗa kai tayi"mungode dr, agaida mutanan gidan," sallama yayi mata kafin ya juya da sauri ya nufi hanyar fita daga asibitin.


______________________________✍️


Bayan tafiyar su Abie masallaci, mami ta kalli Aneela dake kwance tana faman share kwalla"kiyi hakuri ki daure anila, bana son kukan nan da kike yi, ku tashi kuje kuyi sallah kuyi masu addu'a...." jiki asanyaye ta miƙe kwata kwata babu kuzari kamar zata faɗi kasa da sauri zahra ta taimaka mata suka nufi bedroom dinta...

Cike da jimami ummi da mami suka nufi dakunansu domin yin sallah....


Bayan shigarsu dakin, Anila ta zame hannunta daga na zahra, ta zauna gefen gadon, wani iri gumi ne Ya wanke fuskarta, Numfashin ta da hucin zafi yake fita. tsananin tausayinta ne Ya kama zahra, cikin sanyin murya tace"Aunty Anila dan Allah ki daure ki tashi ki shiga toilet kiyi alwalar, idan muka kammala sallar sai muyi masu addu'a...." 


idanunta jawur ta kalli zahra, Cikin disasshiyar murya ta furta"Zahra ki barni kawai, Ni kadai nasan raɗaɗin da zuciya takeyi min! Zahra in har Ana bata dawomin da junaid ba, wallahi zaku iya rasa ni, saboda bazan iya rayuwa batare da yaron nan ba, zuciyata zata iya bugawa in mutu...." kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya sarƙe makoshinta, fashewa da kuka zahra tayi"Aunty Anila ki daina wannan maganar! Bana jin dadi, Kina karya min zuciya ta! In sha Allah babu abunda zai faru dake, ba zaki mutu ba, kuma in sha Allah ba abunda zai faru da junaid, Zasu dawo cikin koshin lafiya..." lallashinta zahra ta ci gaba dayi dakyar ta samu ta shawo kan Anila, harta hakura ta mike ta shiga toilet yin alwala, bayan shigarta zahra ta nufi wardrobe din kayan Anila, don ta ɗauko mata hijabi, bayan ta bude murfin ta zura hannu cikin jerin hijaban Aneelarh dake a jere ta ruƙo ɗaya tana kokarin janyota kwatsam! ba zato ba tsammani idanunta suka sauka akan ɗan mutun dake kwance cikin shelve din wardrobe Ya kudundune kanshi atakure jikinshi duk ya sandare.


Rass taji gaban ta ya faɗi nan take ta saki hijabin dake ruke a hannunta ya faɗi ƙasa ta runtse ido ta daddage ta fasa ƙara tana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un jikinta ya fara kakarwa gaba daya tabi ta ruɗe takasa gane wanene ma ita dai kawai taga dan mutun kamar aljani, banko kofar toilet anila tayi da gudu ta fito jin sautin karar zahra, gabanta na faduwa ta furta"Zahra! Meye faru? Lafiya kike ihu? La66an zahra na kerma sam ta kasa magana sai nuna mata cikin wardrobe din takeyi da yatsan hannunta wanda ke ta kerma..


Adabarbarce ta furta"Aun...Aun... aunty Anila mutun! Ɗan mutun  a ciki! ...." a matuƙar ruɗe Anila ta nufi wardrobe din ta kai idonta inda zahra ke nuna mata lokaci ɗaya ta waro idanunta waje da karfi ta furta"baby junaid..." sai lokaci zahra ta sake kallon shi dakyau taga fuskarshi sharkaf da gumi ya sandare kamar matacce duk ya takure kanshi a cikin shelve din da alama ya dade a ciki, wani abun daure kai towel ne ɗaure a jikin shi daga gani har wanka anyi mashi.


 Allah kadai yasan meya faru da har ya 6oye kan shi cikin wardobe..  " A hanzarce Anila ta ɗauko shi ta zauna kan floor tare da kwantar da kanshi saman kirjinta, ta shasshafa fuskarshi, muryarta na rawa tace ma zahra ta dauko mata ruwa, da sauri zahra ta fuce daga dakin jim kaɗan ta dawo hannun ta ruke da bottle water mai sanyi ta miƙa ma Anila, yatsun hannunta na kerma ta buɗe murfin ta gumtsi ruwan abaki ta watsa mashi saman fuskarshi, wata irin firgita yayi jikin shi ya fara kakarwa kamar wanda sanyi ya kama...nannauyar ajiyar zuciya anila da zahra suka sauke.  Cikin sanyin murya anila ta ambaci sunan shi junaid! Firgigit ya ware idanun shi waɗanda suka kaɗa jawur har saida suka tsorata, Yana ganin fuskar mommynsa Ya ƙanƙameta ya cusa kanshi cikin kirjinta Ya fashe da kuka mai sautin gaske ya dinga sambatu na fitar hayyaci, hakan ba karamin ɗaga masu hankali yayi ba...lamarin yayi matuƙar daure masu kai? Meya faru da shi? Ya akai ya shiga cikin wardrobe ya boye kanshi❓hatta bugun zuciyarshi bana lafiya bane❗


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post