Kuskure Ɗaya page 7 Complete by Jiddah S Mappi


Health College

Kuskure Ɗaya page 7 Complete by Jiddah S Mappi

 

Kuskure Ɗaya

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

   *KUSKURE ƊAYA*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸


        Na

_Jiddah S Mapi_


*Chapter 7*


                  ~Tana fita ya zubawa kofan ido, yana samun nutsuwa idan tana zaune kusa dashi amma wannan sunan da take ambata yana hanashi nutsuwa har ma yaji gara ta tafi akan ta zauna tana ambaton wannan sunan.

meerah kuwa sauri take taje gida bata samu taxi ba, hankalinta gaba ɗaya ya koma kan najwa addu'a take Allah yasa bata tashi ba, sauri take tsakani da Allah kamar zata tashi sama, a fili tace "meyasa kike kula dashi meerah? meyasa hankalinki baya kwanciya idan kina tuna shi"


najwa birgima take akan gadon gaba ɗaya ta fita a hayyacinta, gashin kanta me tsawo da baƙi ya barbazu akan pillow, sai cije baki take tana cewa "unty meerah help mama zai kasheta"

da kyar ta buɗe ido tana kallon gefenta jin tana taɓawa ba kowa, waro ido tayi a firgice take kallon inda meerah take kwanciya, cikin tsoro tace "unty meerah?"

jin bata amsa ba ta tashi da sauri taje toilet tana dubawa "unty meerah! unty meerah ina kike?"

jin shiru yasa ta leka kitchen, bata ganta ba tace "unty meerah?"

wuta aka ɗauke atake gidan ya gauraye da dubu, bata iya ganin komai sai rafin riga da wando na baccin dake jikinta, ta tsani duhu ba abinda yake furgitata kamar taga duhu, rufe idonta tayi ta kwala ihu "unty meerah"

kuka ta fashe dashi tana lalube lalube tana kiran meerah, karo taci da kofan kitchen da sauri tayi baya ta zube a kasa tace "waye?...waye ya kashe wutan?"

ji tayi kamar sautin karan tafiyan Abba, baya baya ta fara tana murza kafafunta a kasa tana cewa "waye dan Allah?"

a cikin kunnuwanta taji saukan muryan da tun tana ƴar jaririya ya gama tsoratar da ita, muryan Abba ta tsinta yace "my teddy bear how you doing today?"

baki ta ware zata kwala ihu ya toshe mata baki, hanu tasa tana cire hanunshi daga bakinta, ganin ba zai cire ba ta fara dukanshi a kirji, rirrike hanunta ya fara yana haɗata da jikinshi, kiss yayi mata a goshi kana ya danna wani abu a hanunshi atake wutan gidan ya kawo, kallonshi tayi da idanunta wanda suka kara girma gashin kanta sun kara barbajewa ta koma kamar sabuwar kamu a hauka, kyakkyawan mutum ne yana matukar kama dasu amma sun fishi farin fata, yana sanye da riga da wando na yadin borno da kuma hula ɗinkin bama, cizo ta gantsara mishi a hannu, ba shiri ya zame hanun jin zafi ya ziyarceshi, a hargitse ta tashi zata gudu ƙafa yasa mata ji kake gim ta faɗi ƙasa da ruwan cikinta, ihun ma ta nemi yi ta kasa tsaban azaban daya ziyarceta, tashi yayi ya matso wajenta ya ɗagota ya manna mata kiss a saman goshi da kyar take iya tsayawa kafanta yana rawa kamar zata faɗi, cikin azaba tace "Allah ya isa ba zan taɓa yafe maka ba..."

maruka masu zafi ya wanketa dasu saida ta faɗi kasa tana dafe da kunci, ji tayi kamar an tsaga kumatunta an barbaɗa barkono, bakinta yana rawa idanunta sunyi jajur, durkusawa yayi a gabanta yana kallon yadda jikinta yake rawa tana kuma kankame kanta waje ɗaya, yace "my teddy bear banaso ina illtaki banason ganinki cikin wannan halin me zai hana ki biyawa abbanki bukata ki mallaka mishi abinda yake binki dashi hakan zaisa ya fita a rayuwarki, ko yau kika bani wannan abin wallahi ba zaki sake ganina ba har karshen rayuwarki"

murmushi tayi fuskanta ya kumbura idonta ya shiga ciki ciki, ta kwashe da dariya har tana rike cikin da yake mata tsananin ciwo, saida tayi me isanta tace "akan wannan abin saide ka kasheni, ko unty meerah batasan komai akai ba, kana tunanin zan iya mallaka maka ba tareda ka ɗanɗani raɗaɗi da zafin daka ɗanɗanawa mahaifiyarmu ba? kana tunanin zan yafe maka abinda ka yiwa mamana?"

wani dariyan da ta kuma yi kana tace "kafi kowa sanin najwa bata yafiya kuma bata mantuwa, kafi kowa sanin saina rama duk abinda akamin, wallahi wallahi wallahi nayi rantsuwa sau uku ko birgiman mutuwa naga kanayi ba zan mallaka maka ba, nafison ka rinƙa mutuwa a kowane rana kamar yadda naga kana mutuwa a yanzu"

cire hanu tayi daga cikinta data rike bakinta yana fitar da jini tace "IBRAHIM MAKAMA?"

da tsananin mamaki ya kalleta jin yadda ta ambaci sunanshi babu girmamawa ko kaɗan, ganin yadda ya mishi zafi tace "Ibrahim saika ɗanɗani kwatankwacin abinda mahaifiyarmu ta ɗanɗana"

wani marin daya kusa taɓa mata ƙwaƙwalwa ya ɗauketa dashi, kifa kanta tayi a kasa na ƴan mintuna kafin ta ɗago tana dariya

"kinada taurin kai amma zanyi maganin taurin kan naki, tunda nayi maganin mariya kece zaki gagareni?"

murmushi tayi tace "kyawun ƴa ta gaji uwarta, kayi maganinta nikuma nasan ba zaka taɓa kasheni ba domin idan ka kasheni burinka ba zai taɓa cika ba"

ta karashe maganan tana kara kyakkyala dariya, a fusace ya tashi ya taka kafarta cije baki tayi ta runtse ido cikin azaba, tafiya yayi yabar gidan, yana fita ta haɗa kanta da gwiwa ta fara rairai ɗan marayan, a fili tace "mama meyasa kika tafi kika barmu? wannan mugun ya kasheki saina rama miki mama, meyasa kika tafi mama?"

kuka takeyi sosai tana tuna halin da suka tashi a ciki, tana tuna irin baƙar azaban da Abbansu ya ganawa mama, rufe ido tayi tana ganin fuskan mama tana mata murmushi tana cewa "ki kula da yayarki ameerah batada matsala kuma tanada rauni, kuyi nesa da mahaifinku, nasan kece me karfin zuciya kece zan iya mallaka miki wannan abin, koda abbanki zai kasheki kada ki bashi wannan abin, ko ameerah banaso tasan yana tare dake, najwa ki kula da kanki kisha maganinki akan lokaci"

kukanta ne ya tsananta ta taƙure kanta a waje ɗaya, tace "meerah ina kike?"

cikin sanɗa ta shigo gidan ta rufe kofan tana cire takalminta domin kada aji karan tafiyarta, duk abinda takeyi idanun najwa akanta, harta shiga ɗakin najwa bata daina kallonta ba kuma batayi mata magana ba, ganin babu najwa akan gadon tace "Innalillahi ina taje?"

da sauri ta fito tana duba toilet "najwa!!! Ina kike?"

hankalinta ya fara tashi da sauri ta fara buɗe ko ina tana lekawa, atake idanunta suka cika da hawaye tashin hankali ƙarara ya bayyana akan fuskanta cikin san yin kuka tace "najwa ina kika shiga ki taimakeni kada kimin haka"

hanyan fita ta nufa domin dubata a waje ko kuma gidansu faty, har taje bakin kofa sai kuma ta dawo da baya tana kallon cikin kitchen ɗin, four eye's sukayi idanun najwa kar akanta, tsarguwa tayi ta kasa magana sai kame kame data fara, da sauri taje tans duba bakinta da fuskanta wanda suka kumbura, tace "najwa meya sameki?"

cikin muryanta daya dishe tace "kin damu ne?"

"najwa wani irin magana kike kamar ya ban damu ba? meya sameki waya taɓaki ki bani amsa"

a hankali tace "Abba ne yazo shine yamin haka"

a firgice tace "Abba kuma a daren nan? meya kawoshi? ya zama dole mu tattara kayanmu mubar gidannan najwa"

tayi magana tana jan hanun najwa alaman ta tashi su tafi, fizge hanunta tayi tace "har sau nawa zamu canja mazauni? har sau nawa zamu rinƙa gudu yana binmu duk inda mukaje? wannan karon babu inda zanje saide ya kashemu"


taɓa wuyanta tayi tace "kina lafiya kuwa? ko kinyi hauka ne da zakice ya kasheki? najwa ko dai akwai abinda kike ɓoyemin ne tsakaninki da Abba?"

murmushin takaici tayi tace "kina zargina ne?"

girgiza kai tayi 

najwa tace "ai kece ma ya kamata na fara zarginki sabida kin fita da dare ba tareda kin faɗi inda zakije ba, hakan baisa na fara zargeki ba sabida na yadda dake fiyeda tadda na yadda da kaina"

tafiya ta fara "let's go and sleep"

shiru tayi jikinta yayi sanyi, ruwa ta ɗiba a roba ne zafi da karamin towel, zama tayi a gefenta kan gadon, najwa ta rungume pillow a kirji ta zubawa fankan ɗakin ido, meerah cikin sanyi ta fara matse mata fuskanta da ruwan zafin, a hankali yake saɓewa daga kumburin da yaya, goge mata jinin dake gefen bakinta tayi kafin tace "na fita ba tareda kin sani ba, da ina nan nasan hakan ba zai taɓa faruwa ba ki yafemin"

murmushi tayi "karki damu watakila abinda kika fita yi abune me muhimmanci a rayuwarki, amma koma menene ina fatan kada ya fini muhimmanci"

tace "babu abinda zai fiki a wajena"

kwanciya sukayi da nufin bacci, meerah sai juyi take sam bacci ya kasa ɗaukanta sai murmushi take idan ta tuna yadda yake kallonta, pillow ta janyo ta rungume a kirjinta ta lumshe ido, kyakkyawan fuskanshi sai gizo yake mata, kara juyi tayi, najwa ta zuba mata ido ta cikin duhun dake ɗakin, ganin ta kara juyi tace "kina lafiya?"

shiru tayi kamar tana bacci, gaban najwa ya faɗi gani tayi kamar meerah ta faɗa soyayya, juya baya tayi a ranta tace "meyasa zaki damu dan ta faɗa soyayya ba kece kike mata fatan samun abokin rayuwa na gari ba? ba kece kike mata fatan samun mijin da zaiso duk abinda takeso ya bata soyayya yasa ta mance da komai ba? to da alama ta samu meyasa zaki damu?"

kara juyawa tayi tana kallonta, da mamakinta sai taga hakoran meerah wanda suke farare kat tana murmushi, ji tayi gabanta ya kuma mummunan faɗuwa, haka kawai sai taji batason wannan farin cikin da takeyi 

runtse ido tayi tace "relax najwa me kike tunani haka? da alama soyayya da faɗa da waye?" ras taji kirjinta ya bada mummunan sauti haka kawai taji bataso meerah taci gaba da wannan murmushin akan tunanin da take, a ranan duk cikinsu babu wanda yayi bacci, najwa ta rasa dalilin rashin sakinta da zuciyarta yayi akan soyayyan da take gani a fuskan ƴar uwarta, ita kuma meerah duk wani abinda ya faru tsakaninta da haydar take tunawa, babu abinda yake narkar da zucuyarta kamar murmushin da taga yayi mata a lokacin data shiga office ɗin, kyawunshi da rashin damuwanshi yana kara narkar da zuciyarta, kara rungume pillow tayi a hankali tace "i missed you"

tari najwa ta fara jin kalman da meerah ta ambata, batasan daga ina tarin ya fito ba, kawai dai ta tsinci kanta da yinshi, da sauri meerah ta tashi "sannu"

wuta ta kunna ta ɗauko ruwan dake cikin goran data dawo dashi, zuwa tayi ta buɗe ta kai bakinta, sha ta fara meerah saita tuna yadda shima yakeshan ruwan, murmushi tayi tana kallon najwa, ido najwa ta zuba mata ko kyafta ido batayi, ganin batama san ta gama shan ruwan ba, ta ture roban ruwan, sai a lokacin ta dawo hayyacinta tace "ya isheki?"

a hankali tace "kafin yau idan nasha ruwa kina gane ya isheni da kanki kike cirewa daga bakina, amma yau ina hankalinki ya tafi?"

da sauri ta ɗauke kai tace "babu kawai bacci nakeji"

shiru tayi mata kawai, amma hankalinta yaki kwanciya.


Haydar saida safe ya tafi gida jikinshi babu daɗi, momy ce a falo dama shigowanshi take jira, da sauri ta tashi ganin kanshi da bandage tace "haydar meya sameka? waya bigeka akai?"

a hankali yace "babu komai"

bai yadda ta kara magana ba yaci gaba da tafiya, tace "haydar ka daina wasa da rayuwarka, yau zaka iya tsira ba lalle gobe ka tsira ba"

cak ya tsaya ya juyo yana kallonta, murmushi tayi irin me nuna tana cikin damuwa ɗinnan tace "ba nice na haifeka ba amma inajin ciwon ganinka cikin ciwo, so tari ina nuna maka tsana amma cikin zuciyata ina zargin kaina, haydar ko sau ɗaya ka bani chance na nuna damuwata akanta na baka kulawa ko Allah zai dubeni ya bayyanamin ɗana kabeer"

jikinshi yayi sanyi ganin tana zubda hawaye, a hankali yaje inda take ya rungumeta yana bubbuga bayanta alaman lallashi, shiru tayi a jikinshi tana wani irin murmushi a kasan ranta, yasan ciwon rabuwa da ɗa dole ya lallasheta, s hankali tace "hakan ya nunamin ka bani second chance, na gode maka"

gyaɗa kai yayi a hankali ya saketa yace "bari na karasa"

jijjiga kai tayi tace "na taimaka maka"

rikeshi tayi ta ɗayan gefe har ta kaishi ɗakinshi, akan sofa ya kwanta tace "sannu bari nasa a kawo maka abinci"

gyaɗa kai kawai yayi ta fita daga ɗakin, rufe kofan tayi tana wani murmushin gefen baki, gashinta ta maida baya ta kara gyarawa fuskanta na asali ya bayyana tace "keep your friends close your enemy's closer"

dariya marar sauti tayi, caraf akan idon mami, duk abinda tayi mami tana kallanta, ta fito ne domin kishin ruwan daya dameta, hanunta ɗaure da chain kamar yadda kafarta ma yake a ɗaure, gashinta ya rufe mata fuska, fuskanta yayi baki kamar yadda jikinta yayi bakin, kallonta momy tayi sannan ta karaso inda take tana murmushin zalunci tace "mariya ko kuma ince kishiyata kinsan dai ba nice na saki a cikin wannan halin ba, to amma inajin daɗin ganinki cikin halin nan, ɗanki haydar ya dawo hannuna a karo na biyu, bana fatan dawowanshi karo na uku, sabida a karo na biyun zan karasashi, Allah sarki uwa tanaji tana gani za'a kashe mata ɗa batada bakin magana babu hanyan cetonshi"

ɗago ido tayi ta zubawa mami kana tace "koda kinada hanyan cetonshi ba lalle na barki ba mariya ya zama dole na kara gishiri akan ciwon dake damunki, kisa ido ko gani babu me shiga harkan balaraba ya fita lafiya, ina miki albishir ɗanki ya sama miki suruka amma kinsan me? ba zan taɓa bari ta zamo sirikarki ba, tanada kyau yarinyar kamar itace tayi kanta, saide matsalata da ita ɗaya ne kawai, ta shiga harkan da bai shafeta ba"

murmushi tayi mata kana ta buɗe wayarta ta nuna mata hoton meerah tace "kin ganta? sunanta Meerah, wayyo naso ace ɗana kabeer ne ya fara haɗuwa da wannan me kama da matan aljannan amma ba komai nan bada jimawa ba zai mallaki komai ciki harda wannan yarinyar zata zamo matarshi haydar ba zai taɓa samun abinda yakeso ba, yanzu zan nuna miki na isa dashi"

tafiya tayi ta barta a wajen, abinci ta hayo saman dashi tana taku irin na marasa imani, tura kofan ɗakin haydar tayi ta shiga, da sauri ta karasa tace "haydar maminka ta fito ya kamata kaje ka maidata ɗaki kafin abbanka ya dawo"

da sauri ya tashi jin ta ambaci mami, fita yayi ya ganta a tsaye ta kasa komawa ciki, maganun momy sunyi tasiri a zuciyarta, riketa yayi yace "mami let's go in"

a hankali ta fara tafiya yana rike da ita, dai kallonshi take tana jin kamar ace bakinta ya buɗe tayi magana kamar yadda kowa yake yi ta faɗawa ɗanta gaskiya ta bashi hanyan da zaibi ya kare rayuwarshi, saide babu hanya, hawaye ne suka zubo mata a ranta tace "Allah yasa wannan Meerah ta zamo kariya a gareshi"

ɗaki ya kaita ya bata ruwa dan yasan tana bukata, sha tayi ya share mata hawayen kafin ya tashi ya tafi, abincin yaci sosai kana yayi wanka yasa kayan bacci me taushi, hawa gadon yayi ya kashe wutan, rufe ido yayi, ya janyo pillow ya rungume, kyakkyawan fuskanta ya fara gani, lips ɗinta da take motsawa idan tana magana shi yake gani, juyi yayi akan lallausan katifarshi ya kuma kankame pillow yana jin shauƙi, maimata sunanta yayi "Meerah!"

da kyar bacci ɓarawo ya saceshi

washe gari baima san gari ya waye ba baccinshi yake cikin nutsuwa, harda mafarki, jamal ne yayita sallama jin bai amsa ba ya tura kofan ya shigo, ganin bacci ma yake harma da mafarki yanata juye juye yayi murmushin mugunta ya fara yimishi video, a hankali ya fara buɗe ido jin hasken waya yana haska mishi ido, waro ido yayi ganin jamal yana mishi video, yaye bargon yayi yai wurgi dashi, durowa yayi a gadon yana shirin kwace wayan, jamal ganin haka ya nemi hanyan gudu, haydar yayi nasaran rikeshi kwace wayan yayi zai goge jamal ya wufce, ɓata rai yayi ya haɗa giran sama da kasa yace "ka goge"

"idan naki fa?"

"ubanka zanci"

"to kaci mana"

kwacewa ya fara suka fara kokawa a ɗakin, momy ce ta turo kofan "good morning haydar" hanunta rike da cup ba tea, aje cup ɗin tayi tana cewa "A,a A,a me haka haydar da jamal yaushe kuma kuka koma yara? wani yaranta kukeyi haka?"

da jamal ya kwace ya fita da gudu, yana cewa "kayi wanka dai biyu dan bakada tsarki"

momy da mamaki tace "fitsarin kwance kayi naji yana wannan maganan?"

shiru yayi gaba ɗaya ya rasa me zaice, tafiya toilet kawai yana jin haushin jamal, tasan halinshi idan yaga dama ma ba zaiyi mata magana ba hakan yasa ta ajiye cup ɗin akan centre table na kusa da gadonshi ta juya ta fita, ita kaɗai tasan me take rayawa a ranta.....



*Kuskure ɗaya is ₦300 via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, show your evidence of payment via 08144818849*



_jiddah Ce...✍🏻_

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post