Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 52 Complete by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 52 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

"duk da ɗan uwanka Salsabeel da sauran Yan uwanka sun fada mana komai dangane da gidan kurkukun kaddara, Ina neman ƙarin bayani daga gare ka, saboda kafi su sanin komai" 

A tsanake Danish ya fara kora mashi jawabi tiryan tiryan bai 6oye mashi komai ba.

"Inaso Naji tayaya su ke mayar da mutun ya zama Giant ɗin su"? Ya tambaya yana kallon cikin idanun shi"


Wa'iyazubillah, Tunkan Ya karasa labarta mashi, chief Ya runtse idanun shi saboda fusatar da zuciyarshi tayi tamkar zata tarwatse tsabar bacin rai, bakomai yafi karya mashi zuciya ba face irin azabtarwar da suke yi masu kafin su mayar da su Giant, matasan yaran da basu ji ba basu gani ba, abu mafi muni rashin imanin da suke sanyawa su aikata abun ya munana sosai.


 wani irin tsantsar tausayin Danish Ne ya ƙara ninkuwa cikin zuciyarshi, abun ya ɗaga hankalinshi matuƙa.


 la66anshi na rawa ya furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un"! Ya ambaci hakan Yafi sau talatin..


Danish dake kallon shi Ya fahimci matsanancin tashin hankalin da ya ke a ciki.



Numfashi ya ɗanja yayin da siraran hawaye suka fara zarya kan kuncin shi..


Cikin raunanniyar murya ya furta"I can't describe the pain I felt in my heart, it saddened me hakika sun cutar da rayuwarku, yanzu da kananun shekarun ka, ahaka suka sanyaka ka aikata duk wadannan abubuwan, Wa'iyazubillah, what kind of disaster is that?" 


Jinjina kai ya yi "Allah baya barin hakkin wani akan wani, akwai sakayya, In sha Allah tun agidan duniya zasu fara gir6ar abun da suka shuka kafin su fuskanci mutuwar su.."


 Danish yayi shiru yana sauraron shi, bawan Allah Ya zama kamar saƙago jikinshi duk babu karsashi shi kadai yasan damuwar dake adabbarsa..


"ka faɗamin gaskiya dagaskene bakasan fuskokin su ba? Abun ya tsaya min araina tsawon shekara 20 tun kana jariri harka mallaki hankalinka amma baka ta6a ganin fuskar su ba"? Ya faɗa fuskarsa ayamutse yana mai dubashi.


"ba sanin su ke banyi ba, nasan fuskokin su amma bazan ta6a iya shaida su ba acikin mutane, saboda suna amfani da karfin sihirinsu  gurin canza kamanninsu dama halittar jikinsu shiyasa nace maka bansan fuskokin su ba"


 gyaɗa kai chief yayi na yarda dakai amma miye sunayen su daka san suna amfani da shi"? 



"Elder, shine shugaban kurkukun ƙaddara, Da iznin sa komai ke faruwa, bayan shi sai mataimakinsa Jan harshe shine mai zartawarwa, na ukun su Jan Wuya shine mai bada shawara kuma head na kula da bangaren bada horon Giant, na hudun su Jan Ido shike kula da bangaren safarar yaran da ake kaiwa gidan kurkukun ƙaddara.........." 


Tun daya fara magana Chief Ya nutsu yana sauraron shi har sai da yakai aya kafin yace mashi"Alfarmar da zan nema agurinka, kafin mu kai farmakin Inaso ka dinga bin mu zuwa headquarter donka taimaka ma Isod soldiers din mu da horon yadda zasu yi faɗa da Giants.."



Amsa mashi yayi da toh sannan ya faɗa masa date din daya kamata su je, kamar yadda tsohuwa Khala ta shawarce shi da su kai farmaki adaren ranar, amma bai sanar da shi daren menene ba.


Da tsantsar farin ciki Chief Ya ruƙo hannayen Danish  a cikin nashi ya ruke su gam.


"Bansan taya zanyi maka godiya ba, kalmomi sunyi kadan Danish, Ka faɗamin duk wani buri da kake son cimmawa, Ni kuma na maka alƙawarin In har baifi karfina ba zan cika maka shi" 


ya faɗa da ɗan murmushi kan fuskarshi, Danish bai furta komai ba, sai faman lumshe idanun shi yakeyi kamar gyangyaɗin bacci ya ke yi.


Lura da hakan yasa Chief ya ruƙo hannayen shi Ya taimaka mashi Ya kwanta kan gadon, wani irin bacci ne mai nauyin gaske yayi awon gaba da shi.


(Lallai Gadon Chief Yayi albarka, Unaisah ta kwanta, Ga Danish ma Yayi bacci akan shi😂 saura ni ma zan ɗana) 


_________________________________✍️


Da yammacin Ranar, Chief Ya kira Meeting din gaggawa wanda su kayi A headquarter din su tare da Manyan jami'an Isod dana Sojoji, da kuma U.s army, gaba ɗayan su suka hallara a meeting room ɗinsu, bayan Chief ya kunna masu audio ɗin daya dauka na tattaunawar shi da Danish, sunyi matuƙar yin mamakin amincewar shi, musamman big guy, sun kuma ji dadin yadda ya basu hadin kai cikin sauki batare da sun sha wahala ba, ba tare da 6ata lokaci ba, kowa Ya fara kawo shawarar shi dangane da yadda zasu kai farmakin, babu wanda bai tofa albarkacin bakin shi ba, basu suka tashi meeting din ba, har saida suka tsayar da kwanan watan da Danish Ya faɗa ma chief amatsayin Ranar da zasu kai farmaki.



Tun daga ranar su ka fara shirye shiryen tafiya Yaƙi babu kama hannun yaro, basu da wani hutu, gagarimin shiri suke na musamman kuma komai nasu cikin sirri suke yin shi saboda tsaro ba don tsoro ba, sun tanadi Miyagun Makamai da zasu yi amfani da su agurun gabzawar.


Tawagar Dakarun sojoji Uku ne zasu je kai farmakin, tawaga ta farko Isod Soldiers ne, bayan su sai Tawagar Sojojin Nigeria, Tawaga ta uku ta U.s Soldiers ce.


a bangaren Unaisah Da Danish tun ranar da ta tursasa mashi akan ya amsa zai basu hadin kai, basu ƙara haɗuwa da juna ba, walwalarsu ta ragu, rayuwarsu ta ƙuntata saboda tsantsar damuwar da suka shiga na fargaban kada su rasa junan su, bayin Allah ta ko'ina ba sauƙi, kokari sukeyi su saba ma kansu rayuwa batare da juna ba don su saukaka ma kansu radadin son juna da suke ji a zukatansu, sai dai abun yaci tura, abun sai ya zamana kamar suna kara rura wutar son da suke ma junansu ne.


Ba karamin maraicin shi takeyi ba, saboda shirya shiryen da sukeyi na tafiya yaƙi yasa baya zama gidan, atare da chief suke zuwa headquater saboda taimakon da yakeyi masu gurin ƙara wayar masu da kai game da kurkukun ƙaddara, Saida takaiga idan Chief yaje da shi headquarter din su jami'ansu ji suke da shi suna masa biyayya kamar dai chief din, wani irin farin jini gare shi, abunda yafi burge su da shi karfin da Allah yayi mashi, ga kaifin basira da Allah ya bashi, har jaraba shi sukayi ta hanyar haɗa shi da ƙarfafan Isod soldiers don suyi wrestling da shi, saboda su tabbatar idan giant basa jin bugu aikuwa sun sha ruwan mamaki, Isod Soldiers din da suka hada shi da su gurin damben su kusan hamsin saida Ya sumar da su, a hakan ma baiyi masu bugun da zasu raunata ba saboda baison yai masu illa shiko ko kwarzane ba su yi ma shi.


Idan suka tafi Basu tashi dawowo gida, sai marece idan ya dawo agajiye daya samu yayi wanka ko abinci bai nema bacci yake yin awon gaba da shi, baya tashi farkawa sai lokacin da dare ya tsala kowa yayi bacci tukunna ya ke tashi yaci Dinner din shi.


dauriya kawai yakeyi amma kewarta na neman tayi mashi illa, haka itama ko abincin kirki bata ci, ta rame tayi haske sosai kamar babu jini a jikinta, kullum a bedroom ɗinsu take killace kanta bata son kowa ya ra6e ta, tafi son kadaici duk da ba karamin azabtuwa takeyi ba na rashin ganin shi, tun tana 6oye abun da ke damunta idan yan uwansu suka matsa mata musamman auntyn umminsu har takaiga sun gano da kansu saboda kauracewa junan da sukayi ita da Danish, nema take ta zauce kullum ciwo ba koshin lafiya, abinci sai aunty ummi tayi mata dole take cin shi akarshe ma ta amayar da shi a toilet ba tare da sanin su ba, bacci Ya kaurace ma idanunta idan dare yayi haka zatay ta juyi kan gado rungume da pillow a kirjinta, idan abun ya isheta nafilfili take tashi tayi kuma duk akansu takeyin sallar, wani lokacin akan prayer mat baccin ya ke yin Awon gaba da ita. wannan wani irin Azababben So ne❓



Gaba daya abunda ke faruwa Taj baisani ba, saboda shima ba zaune ya ke ba, ummi har yunkurin kiranshi tayi don ta fada mashi halin da Unaisah take a ciki na rashin Lafiya amma Unaisah ta dinga rokonta akan kada ta sanar da shi saboda gudun faɗan da zaiyi mata, dakyar ta samu Ummi ta fasa kiranshi bayan ta gindaya mata sharadi akan bazata ƙara fashin cin abinci ba, tace mata eh ta amince ahaka ummi ta samu ta ɗan shawo kanta.


Kamar yadda boyayyan mutumin nan Ya ba Chief shawarar  su sanya manyan Malaman addini suyi masu addu'a, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya tuntu6i shiekh Imam malik awaya, Ya nemi alfarmar yana son su haɗu anan gidan shi. 


Shiekh imam yace mashi in sha Allah zai shigo gidan.


After Magbrib Bayan sun kammala yin dinner din su, ba suje sun kwanta ba, gaba ɗayan su suna zaune a falo, sunyi shiru babu mai magana acikinsu, kwata kwata babu annuri akan fuskokin su, gashi dai sun sanya kayan baccin sai dai baccin Ya kauracewa idanunsu saboda damuwar da zuciyoyin su suka shiga, babban tashin hankalinsu jin za'a tafi da Garkuwarsu, babu irin magiyar da basuyi ba akan suma atafi da su amma Salsabeel yace bazai yiwu ba, suyi hakuri su biyu sun isa suyi ma Sojojin jagora.



Unaisah ta ƙwallafa rai akan son aje da ita kuma har yanzu tana akan bakanta don bazata bari su tafi da Danish batare da ita ba, abun daya daure masu kai har yau babu wanda ya faɗa masu date din da zasu je kai farmakin, duk in suka tambayi Taj ko big guy sai suce masu basu fidda lokaci ba, haka shima Danish yake fada masu, gaba daya sun yarda da maganarsu, Unaisah ce kadai hankalinta bai kwanta da zancen ƙin bayyana masu kwanan watan ba, ta fahimci sun haɗa baki ne, ranta yana bata tafiyar bazata zasuyi batare da sanin su ba shiyasa suka shirya hakan, tun da ta fahimci hakan kusan kullum sai ta addabi daddynta da Salsabeel akan su faɗa mata date ɗin amma suka ƙiya, tayi magiyar tayi rigimar duk abanza, harta hakura tadaina tambayar su, ta dai zuba ma sarautar Allah ido.


Fitowa Ummi tayi daga Bedroom dinta, jikinta sanye da doguwar rigar bacci, ta zuba hannayenta cikin aljihun rigar,


Daga inda take ta hango su zazzaune kan sofas na falo, sun zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki.


Girgiza kai tayi tare da zaro waya daga aljihu ta kira Layin Boss.


Bayan yayi picking suka gaisa cikin girmamawa kafin tace"yalla6ai akwai matsala fa, Yaran nan sunƙi zuwa su kwanta ga su can zaune falo sun zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki, Ni nasan bai wuci zancen tafiyarku bane Ya ɗaga hankalin su..." ta fada fuskarta ayamutse.


Muryarshi da damuwa ya furta"Ya sallam, Ummi pls ki yi koƙarin kwantar masu da hankalin su"


"Wallahi ba irin lallashin da banyi masu ba, amma duk abanza"


"Ummi, ki zauna dasu, yanzu zamu shigo gidan In sha Allah"


"Okay, Allah ya dawo daku lafiya"


"Ameen" da ga haka Su ka yi sallama.


Saukowa down tayi, har ta shigo falon ba su ankara ba.


Sau uku tanayi masu sallama babu wanda Ya amsa mata saboda Hankalinsu baya atare da su.


Binsu da kallo ta yi, daga wanda ya ɗage kai sama, Sai wanda Ya langwa6ar da kan shi jikin Sofa,  kowa dai da alkibilarsa da ya kalla


Bakowane Yafi bata tausayi ba, face Unaisah, baiwar Allah ita kadai ce kwance Kan rug, yadda kasan tsumma, ta nannaɗe guri guda kamar kifin gwangwani ko motsi batasan yi.



Kware murya tayi da karfi ta furta"wai bakwa ji nane"? A firgice suka zabura kowannan su Ya gyara zaman shi, kusan atare suka dube ta, In ka cire Unaisah wanda ko gizau batay ba, tana nan yadda take a kwance..


"Aunty ummi har kin bamu tsoro," hanna ce tay maganar.


Haris Yace"wai har yanzu basu dawo ba"?


"Aunty ummi, ko zaki kira mana su? Mun yi ma Unaisah magana tace wai batasan inda ta jefa wayar ta ba, kuma mun duba bamu ganta ba" acewar Batool..


Naufal yace"pls Aunty Ummi, nasan ba zaki rasa sanin ranar da zasu tafi ba, dan Allah ki faɗa mana wlh munyi maki alkawarin ba zamu faɗa masu mun sani ba"


Bata tanka masu ba, wuri ta samu kan Sofa ta zauna, batare data kauda ido daga kallon su ba.


Calmly tace"yanzu nayi waya da boss, Yace min suna akan hanyar su ta dawowa gida.." 


"Aunty ummi duk ba wannan ba, kawai ki fada mana ranar da zasu tafi, in ba haka ba hankalin mu bazai kwanta ba" acewar Naufal.


"ku yarda dani, wlh nima bansan date din da zasu tafi ba, har tambayar boss nayi yace min basu fidda rana ba, kunsan yanayin aikinsu na jami'in sirri, kuskure kadai zai iya lalalata shirin su, yakamata mu fahimce su ko"


 ta fada cikin kulawa tana kallon su.


Sarah tace"amma ay ba laifi bane in mun sani, zamu tayasu da addu'a ne kawai," 


Murmushi ummi ta ɗanyi"in zaku tayasu da addu'a ay ba dole sai kun san ranar da zasu tafi ba, wannan baya daga cikin sharuddan yin addu'a"


"Look aunty ummi, kin san komai, kawai kina boye mana ne" fuska a daure Sajeed Ya faɗa.


Yar dariya tayi"dama nasan zaiyi wuya ku yarda dani, in ma baku yarda ba toh kada Allah yasa ku yarda" ta fada tare da yi masu dakuwa da hannunta, tuntsirewa su Ka yi da dariya itama dariyar tayi


"Kun fiye taurin kai Allah, haba mana, kusan karfe tara, Yakamata kuje ku kwanta, ga little sisters dinku nan sai gyangyadin bacci sukeyi nasan saboda ku yasa suka ki zuwa su kwanta bacci" ta fada tana nuna Azeeza da jemimah da hannunta sun manne ma juna sai gyangyadi su ke yi..


"Hmm aunty ummi kenan, Salon muje mu kwanta bacci, lokacin da zamu farka ace mana sun tafi ko? Da fa wayon mu" dariya tayi sosai maganar javed ta sanyata nishadi.


Mikewa tayi ta nufi sofa din da su jemimah suke a zaune, ta dauki jemimah ta goya abayanta, kafin ta tada Azeeza tana layi ta mike kamar wadda tasha kwaya..


Ruko hannunta tayi, ta nufo bedroom dinsu dasu, sai da ta tabbatar sun kwanta bacci ta kashe masu switch din dakin tana kokarin fitowa unexpectedly Jiniyar motocin dake shigowa gidan ta karaɗe kunnuwan su.


Kusan atare suka mimmiƙe tsaye suna jiran shugowar su, Unaisah ce kaɗai bata motsa ba tana nan inda take akwance..


Cikin takun sauri suka fara shigowa falon, Chief ne agaba hannun shi ruƙe dana Danish daga bayan su Shiekah Imam Malik ne, Yayin da Boss da big guy hada ma Salsabeel su ke abiye dasu, mutun biyune babu kaki a jikin su, Danish da Salsabeel, black jean da white   shirts ne a jikin su kala ɗaya.


Tun da Ummi taji Sallamar shiekh Imam malik, ta kasa fitowa daga dakin su Jemimah..


Kusan atare suka ci burki suna kallon su, sun yi mamakin ganin su a tsaitsaye curko curko suna ganin Danish jikinsu har 6ari yake garin saurin su karasa gare shi, daya bayan daya saida yayi huggin din su duk da agajiye yake har wani jiri jiri yake gani acikin idanun shi..


Atare suka hada baki gurin yi masu sannu da dawowa, kafin suka gaishe da shikeh imam malik cikin girmamawa..


"Sheikh, mun jima bamu ganka ba, kamanta damu" sajeed ne yai magana


Tattausan murmushi shiekh imam Ya sakar masu"masha Allah na ji dadin ganinku cikin koshin lafiya, Yan jikokina, ban manta daku ba, kuna araina, duk in zanyi addu'a saina sanyaku a ciki" murmushin farin ciki suka saki..


Gaba daya hankalin Taj baya akansu, Yar shi Yake nema Yaga babu ita a cikin su, baisan awani hali take ciki ba, ya yi kewarta ba kadan ba..


"Bismillah, mu shiga ciki" big guy ne ya fada tare da nuna masu hanya


Kafin su karaso, da sauri Unaisah ta mike cike da rashin kwarin jiki ta zauna.


Bayan sun karaso cikin falon Prisoners gaba daya suka zauna kan rug, su Chief suka zauna kan sofas din. 


Kwata kwata basu lura da ita ba, ganin daddynta ya miƙe yana kokarin nufar dakinsu yasa tay karfin halin furta"sannu ku da dawowa, ya gajiyar aiki" atare suka dago suna kallon ta, haduwar idanunsu Cikin na jina yasa Danish yin saurin kawar da fuskarshi gefe daya saboda kallonta da yakeyi ba karamin karya mashi zuciya yakeyi ba, hakan da yayi ya sanyata jin wani iri a azuciyarta, gani take kamar fushi yake da ita..


"Unaisah Lafiyarki kuwa? Meke damunki"? Taj ne ya tambaya yana kallon ta..


Murmushi ta kakaro kan fuskarta"bakomai daddy, idan ma akwai abinda ke damuna, bai wuci zullumi da fargaban tafiyar ku bane"


 Jiki asanyaye Taj ya zauna gefenta, tare da ruko hannayenta acikin nashi.


Hankalin Chief gaba daya yana akansu, shi kanshi Ta bashi tausayi ya lura da ramawar da tayi.


"Pls ku bamu aron hankalin ku nan" big guy ne yai maganar, gaba daga suka dube shi, a lokacin Unaisah ta kwantar da kanta saman kafadar daddynta..


"Ina Auntyn naku take"? 


"Taje ta kwantarsu da su jemimah dakin su, har yanzu bata fito ba"


"Okay, wani ya kira mana ita"


Har mubeen Ya miƙe zaije kiranta, sai gata ta fito komawa yai ya zauna..


Tana karasowa, cikin sanyin murya tayi masu bangajiyar aiki, kafin ta dubi sheikah Imam malik kallon juna sukayi ido cikin ido daga gani sunyi kewar ganin junansu

Muryarta na dan rawa ta furta"ina wuni sheikh ya fama da jama'a.." tamkar bazai amsa mata ba, ya furta Lafiya..daga haka Ya kau da idanun shi gefe ɗaya.


"Bismillah, Ki zauna" big guy ne ya fada tare da nuna mata sofa, bayan ta zauna falon yayi tsit baka jin motsin komai kamar mutuwa ta gifta.


Gyaran murya sheikh Imam Yayi tare da duban Chief yace"Owais, meke faru ne? naga kamar wani abu na damunku, daga ku har yaran babu mai walwala, ince dai ko lafiya"? Jinjina mashi kai chief yayi"kada ka damu, babu wani abu." ya fada tare da kallon Omar batare daya furta mashi komai ba, da ido ya fahimci me chief yake nu fi..


A tsanake ya fara labarta ma Sheikh Imam, dangane da shirye shiryen da suke yi nakai farmaki, sai dai ba komai  ya faɗa masa ba, ya dai ce mashi miyagun yan'ta'addane kuma matsafa ne masu hadarin gaske zasu je kaima farmakin a kurmin daji..


Sheikh Imam Malik Ya jinjina lamarin, tun da big guy ya fara zayyana mashi, Yake ta dan jinjina kan shi alamar ya girgiza da jin zancen.


Chief Owais Ya daura da cewa"baba, alfarmar da muke nema agurinku, munaso ku haɗa kai da manyan malamanmu na addini don ku yi mana addu'o'i, sannan zamu bada abun sadaka abawa mabukata da marayu suma su taya mu da addu'a."


Numfasawa sheikh Imam yayi fuskar shi dauke da matsananciyar damuwa yace"Owais, Kunyi tunani mai kyau, tabbas tunkarar miyagun matsafa ba abune mai sauki ba, mutanene masu haɗarin gaske, amma ta inda kuka fi su ku kun dogarane ga Allah ne, kuma kun yi imanin shi ne zai baku nasara akan su..." ya fada yana ɗan jinjina kanshi


"In sha Allah Owais, tun da har kuka nemi mu taya ku da addu'a zamuyi aiki tukuru, bi'iznillahi ba zasu ta6a cin galaba akan ku ba, saboda kyakkyawar niyar da kuke da ita na ganin kun kawar da masu aikata fasadi adoron kasa.." gaba daya sunji dadin furucin sheikh Imam malik


"Zan iya sanin yaushe ne zakuyi tafiyar"? prisoners duk sun baza kunne suna jiran jin amsar da chief zai ba shi.


"bamu fidda rana ba, amma a kowani lokaci zamu iya tafiya"


"Okay, in sha Allah zuwa gobe da safe zan sanarwa yan uwana malamai yan team dinmu wadanda nayi imanin in har muka hada kai da su gurin yi maku addu'a babu wani mahalukin daya Isa Ya ci galaba akan ku, Sihirinsu bazai ta6a tasihiri a kanku ba, in ba wani iko na Allah ba....." 


Gaba ɗaya sunji dadi maganar shiekh Malik, 


"Amma, malam, Danish har yanzu bai musulunta ba" gaba daya suka maida hankali akanta, sunnar da kanta kasa tay, ganin irin kallon da daddynta yayi mata.


A hankali suka maida duban su ga Danish, wanda ya dafe goshinsa da tafin hannun shi


Salsabeel Yace"kamar kin shiga zuciyata Unaisah, wlh tun dazu nake ta zucci zuccin inyi mashi maganar shi, gaba daya mun damu da rashin addininsa" 


Chief yace"nima abun na damuna, ataimaka mana sheikh, a karkato mana da hankalin shi Ya kar6i shahada, kafin lokacin da zamu tafi"


Kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, babu wanda baiyi magana ba, akan damuwar su na rashin addinin Danish In ka cire Big guy ko kadan bai sanya baki a maganar ba.


"Danish, Har yanzu baka da ra'ayin kar6ar addinin musulunci"? Shiekh imam ne ya tambaya yana kallon shi..


Gaba daya sun kagara da su ji me zai ce


Sai da ya mula ya sha iska kafin ya firta"bani da ra'ayi,"


"Meyasa"? Shiru yayi bai tanka ma shi ba.


Hakan ba karamin karya zuciyoyin su yayi ba..


"Inason Yin magana dakai, a ɗakin  ka" bai yi mashi musu ba, Ya mike sheikh Imam Yabi bayan shi suka nufi second floor har dakin danish bayan sun shiga Shiekh Imam Ya kulle Kofar.


Gaba daya sun kagara da su fito, fatan su Allah yasa Ya kar6i musulunci.


Kasa kasa da murya Taj yace ma Unaisah"kun ci abincin daren ku"?


"Eh daddy,"


"Pls ki daina sanya damuwa aranki, banason ganin ki a rame haka babu walwala, in har saboda tafiyar da zamuyi ne addu'arki muke bukata ba damuwarki ba.."


"Toh daddy, zan daina, amma pls ka fadamin date da zaku tafi na maka alkawarin bazan sanar da kowa ba"


Aranshi ya ayyana ay ko da zan fada ma kowa Unaisah bazan fada maki ba, ni nasan me zai biyo baya in kikaji, rigima zaki sa sai mun tafi da ke ..


"Daddy ka yi shiru"


"Unaisah, Chief Yana kallon mu, kuma shi Ya hana asanar da kowa, kuma mun yi mashi alƙawarin zamu ruke amana, kinga bai kamata in zama mutun na farko da zanci amanar shi ba, amma ki ƙara hakuri zan nemi izni daga gurin shi In har Ya amince zan sanar da ke"


 yamutsa fuska tayi tamkar zata sanya kuka tace"ran nan ma haka ka ce min zaka yi mi shi magana akan in biku amma baka yi masa ba"


Shiru yayi bai tanka mata ba, ta fahimci wayou ya ke yi mata gashi takasa tunkarar Chief din da maganar wani irin nauyinsa ta ke ji.


Agogon Hannunsa ya duba karfe goma na dare, ɗagowa yayi tare da kallon Chief, Wanda Hankalinsa ke akan Phone dinsa da yake daddanawa..


Har saida suka fara gajiya da jiran sheikah Imam, A kalla sun shafe mintuna talatin Cuf, Wasu daga cikin Prisoners har sun fara bacci.


A lokacin da basuyi tsammani ba, sai ga sheikh Imam Ya fito daga dakin batare da Danish ba, tunkafin ya karaso su ka lura da yanayin damuwar dake akan fuskarshi, nan take suka fahimci ba ay nasara ba...


Har ya zauna ba su daina kallon shi ba, yayi shiru babu walwala akan fuskarsa


"Baba an dace kuwa"? Kallon chief yayi tare da girgiza mashi kai yace"ban ta6a yi ma wani ɗan adam da'awa irin wadda nayi mashi ba, kuma da wuya inyi har in gama mutun baiji imani ya shige shi koda bai musuluntan ba, amma banaso hakan Ya dame ku, kowa ni dan adam da irin tashi Jarabawar, wani har ya mutu baiyi imani da Allah ba, amma fa kada ku yanke kauna da shi, idan Allah yaso shi da rahama koda da numfashi na karshe ne in Allah ya nufa sai kuga ya furta kalmatusshahada..." bai ƙare maganar ba, Unaisah ta mike da gudu ta bar falon, gaba daya suka bita da kallo har ta 6ace ma ganin su.


Suma sauran yan uwan nata, kuka suka kamayi, shiekh imam ne yayi masu nasiha mai tsuma zuciya harya samu ya shawo kan su, 


Kafin tafiyarshi, sai da Ya ƙarfafa masu Chief gwiwa, Ya jima agidan har wuraren karfe sha daya kafin yayi masu sallama ya tafi.


Bayan tafiyar shi, Taj Yace suje su kwanta, jikin kowan nan su asanyaye suka mike ko sallama ba su yi ma su ba, kowa ya nufi ɗakin shi Ummi ma ta yi ma su sallama ta nufi nata ɗakin.


(After two days da zuwan Sheikh imam, Bayan kwana biyu)



Yau tunda sanyin safiya, kiran Taj ya farkar da Ummi tana tsaka da yin baccin ta, bayan ta daga sun gaisa Yace Ta shirya su Unaisah, tare da ita kanta, yana son su kawo ziyara part dinsa gurin Danejo, Ummi taji dadi dama Ta gaji da zama guri daya tafi son tana ɗan yawata.


Batare da 6ata Lokaci ba, taje dakunansu ta tada su daga bacci ta isar masu da sakon Boss, duk da halin da damuwar da suke a ciki hakan bai hanasu jin dadin zasu je part din daddy taj ba, Unaisace kadai Hankalinta bai kwanta da zancen zuwansu part din daddynta, saboda ranta yana bata yau ne kwanan watan da zasu je kai farmaki, shiyasa akayi masu wayau don a kawar masu da tunanin su, aikuwa ko brush batayi ba, wankan ma ta kasa yi, A karkashin gado ta boye kanta duk don kada tabisu.


"Sister! sis! Where are You, Mun fa shirya, ke kadai muke jira" muryoyin su Batool tajiyo a cikin kunnanta, shiru tayi bata amsa masu ba.


Can tajiyo muryar Ummi tana fadin"Unaisah Ina kika shiga ne? Kun duba toilet ɗinta kuwa"? Ta fada tana kokarin tura kofar toilet dinta, koda Ummi ta buɗe kofar ta shiga ciki bata ga kowa ba, tayi mamakin ganin babu ita a ciki, rufe kofar tayi, tare da kallon su, sunyi tsaitsaye.


"Aunty ummi ki kira daddyn nata, Muji idan taje can ɗin" acewar Sajeed


Waya ta zaro daga Cikin Yar purse ɗinta, ta danna ma Taj kira almost 3 times tana kira baya shiga har ta gaji ta hakura da kiran nashi..


"Mu tafi, may be tana can din" fitowarsu keda wuya daga dakin sai ga big guy ya shigo part din su


Kaitsaye idanun shi suka sauka akan Ummi, from head to toe Yabi ta da kallo, fitted gown ce a jikinta ta material launin ash colour kamar ajikinta aka dinka kayan, ta kashe daurin dankwalinta sai ɗan gyalen data yarfa a kafadarta, ko makeup batayi ba amma tayi matukar jan hankalin shi.


Gaba daya sunyi mamakin kallon da big guy keyi ma Auntyn ummin nasu, ita sam bata lura ba da fara'a tace"Gm Sir, ya gajiyar aiki? dakyar ya haɗiye abunda ke ransa Yace"lafiyalou Ummi, Ina zuwa haka"? Ya tambaya kamar baisan da plan din su ba


"Zamuje kai ziyara a Part din Daddyn Unaisah" murmushin gefen fuska Ya sakar ta, kafin Ya dubi prisoners.


"Guys, Kunyi kyau, Muje na raka ku part din nasa" ya fada tare da nuna masu hanya, su ka yi gaba shi kuma Yajera da Ummi cikin nutsuwa suke yin tafiya.


"Kinyi mini kyau, badan Ina busy ba, da na daukeki mun fita yawan buɗe ido" 


"Banyi zaton kana Kula mata ba.." ta fada tare da kallon shi..


Murmushin gefen fuska yayi"nima fa banajin magana, tubabbe ne, daga baya na shiryu silar Owais.."


"Allah sarki Chief, Mutumin kirki, har kasa na kara jin kaunar shi saboda shi din na dabanne samun irin shi da wahala" still fuskarshi da murmushi yace"That's why I'm proud of him..."


"Kasan wani abu"? Girgiza mata kai yai saikin faɗa


"najima ina yi maka kallon sani, hatta muryarka tayi min kama data wani mutumina Allah, kuma kun ɗanyi kama da shi"  


"Zan iya sanin sunanshi"? 


"A'a, bana faɗi, amma ka fadamin sunan Family dinka"


Yar dariya yayi yana binta da wani shu'umin kallo, kamshin turarenta duk ya kashe mashi kuzarin shi musamam Yadda qugunta ke gogar nashi ba karamin tsuma shi take ba..


"Wayau zaki min Ummi, Ke kin ki faɗamin sunan mutumin naki sai ni zan fada maki sunan family ina, bazai yiwuwa ba Allah"


Murmushi tayi"na yarda kowa ya ruke nashi, amma kai ba hausa bane zalla ko? Cos kayi kama da ruwa biyu" ɗaga mata gira yayi.


"Meye Full name ɗinka"? 


 har ya buɗe baki zaiyi magana Muryar Sarah Ta katse su"Aunty Ummi, ke muke jira fa" Gaba daya sun shagala sunata fira sam sun manta da su, har sun karasa bakin kofar part din...


Karasowa sukayi, big guy ya kwankwasa kofar, almost 3 times kafin suka ji motsin bude kofar ta ciki


Taj Ne Ya fito Jikin shi sanye da kakinsa Yana ganinsu ya saki fuskar shi da fara'a suka gaisa da juna cikin girmamawa.



"Bismillah Ku shiga, madam Tana a ciki tana jiran ku..." murmushi suka saki gaba dayan su, har sun fara shiga ciki Taj ya lura babu Angel acikin su..


Da sauri Yace"Ina ita Unaisah din"?


Ummi tace"wlh bamu ganta ba, mun duba ko'ina har cikin toilet dinsu, mun yi zaton ta riga mu karasowa ne" 


Big guy yace"ni banma lura babu ita a cikin su ba, sai yanzu da kayi maganar nan.." fuskar Taj A yamutse Yace"ku shiga daga ciki, Bari naje na dubota" ya fada tare da kallon Big guy"muje" sai da ya fara kallon ummi Yai mata waving kafin Yabi bayan Taj, suna fitowa daga falon,yayi locking door din dama da biyu suka turo su nan.


Bin falon su ka yi da kallo, jin shiru matar gidan bata fito ba, ummi tace mu zauna mu jira ta.." 


da sauri kowannansu ya samu guri kan Sofas suka zauna.


Badajimawa ba, sautin takalamanta Ya karade kunnuwansu, kusan atare suka kalleta yayin da take saukowa down, ta dauki wankan abaya baƙa, tayi rolling akanta.


jinjina kai ummi tayi aranta ta furta masha Allah.


Sallama tayi masu, kamar tana jin shakkarsu, har yanzu bata saba da mutane ba..


A wayance Ummi ta mike tare da ruko hannayen Danejo Acikin nata, ta sakar mata murmushi"sannu madam, fatan mun same ku lafiya.." sai faman rarraba idanu takeyi akansu Rubina

Dakyar ta firta"lafiyalou"


Ummi tace"kamar baki gane su wanene ba, Ko dai Mijin naki bai fada maki zuwan mu bane" sai lokaci tayi murmushi"wlh ya fadamin, na shafa'a ne, da yake banganku tare da ƴartawa ba shiyasa na ɗan ruɗe amma yanzu nagane ku" Hugging ɗinta Ummi tayi, Kafin suka zauna kusa da juna.


Da sauri Prisoners suka gaishe da ita.


Da fara'a tace"tabarakallahu ahsanul khalikin, Kune Yan uwan Angel ɗin? Atare suka amsa mata da eh


"Masha Allah Jinsin kyawawa Naji dadin haɗuwa daku, amma Ina Unaisah ɗin take"?


Ummi tace"bata karasa shiryawa bane, shiyasa muka tafo, amma dadynta Yaje ya taho da ita" 


"Ke ce mommynsu ne"? Yar dariya ummi tayi"kina nufin wadda ta haife su? Daga mata kai tay, dariya ta kumayi kafin tace"kin iya zolaya, ni ina zan iya haifan wadannan har su goma sha, ko nayi maki kama da matar aure ne"?


 Ta tambaya tana kallonta, murmushi Danejo tayi"A'a amma dagaske baki ta6a yin aure ba"?


 ɗaga mata gira ummi tay, waro idanu waje Danejo tayi da mamaki tace"tab lallai, aradun Allah da a rigarmu kike da tuni Kin aje tatta6a kunne, Ko kina so ko bakisho dole ay maki aure" tuntsirewa sukayi da dariya gaba dayansu, hausarta ba karamin nishadi ta basu ba, kana jin maganarta zaka gane bafullatanar daji ce.


Sai dadi takeji ganin yadda ta sanya su nishadi


Maimakon ta dauko masu abunsha, sai ta kama basu labarin haɗuwar ta da Taj, har zuwanta birni da irin wautar da tadinga yi mashi, sunci dariya kamar zasuyi kuka.


Ta zaƙe sai zuba takeyi masu kamar aku, Har saida Parveen ta gaji da zuba na mazurai taji shiru bata kawo masu abinci ba, gashi ko breakfast basuyi ba suka taho


Hannunta dafe da cikinta tace"Aunty Danejo, mufa Yunwa muke ji, bamu ci komai ba muka taho" dan zaro ido ummi tayi tana kallonta, sarai parveen taga kallon da ummi tayi mata amma saita kawar da idonta gefe.


Mikewa Danejo tayi"i'm really sorry, na cika ku da surutu, kunsan mutumin dake zama cikin kadaici in ya samu abokin fira komai ma mantawa yakeyi, kuma fa tun dazu Nayi maku girki tunda daddyn angel ya sanar dani zuwanku..." 


har ta fara tafiya ta juyo tare da kallon su"wa zai bini kitchen din mu dauko kayan abincin"? Da sauri Parveen da Yasmeen suka mike atare suka nufi kitchen.


Ajiyar zuciya sajeed Ya sauke tare da kallon aunty umminsu yace"da farko dana ganta kyakkyawa nayi zaton miskila ce ashe ta iya dan banzan surutu" dariya ummi tayi tana fadin"Pls kadaina maganar nan kada taji ka, amma fa kamar ka shiga zuciyata, Nima nayi zaton hakan" 


Jemimah tace"gulma haramun, Allah In tadawo saina fada mata abunda kuka ce" Harara sajeed Ya galla mata"dako Kin ci na jaki Allah, Yar sa ido kawai" gatsina mashi hanci tayi tare da hararar shi, Ya janyo throw pillow Ya ɗan buga mata akanta.


Azeeza tace"Aunty Ummi, wai itace maman angel ne? Wadda Ta gudu tabarta acikin kwamin wanka" waro idanu waje sukayi


Batool tace"ke fa baki gane komai, Kin manta bafullatar dajin da Angel ta bamu labarinta? Wadda ta tsinceta acikin ruwa.." ta faɗa tana kokarin fahimtar da ita can tace"Yanzu na gane ta" ummi dake kallonsu a hankali ta sauke idanunta kan Deeja, data daura kanta saman kafadar Haris, hannunsu ruke cikin na juna tun zuwansu basuyi magana ba, aranta ta ayyana"Mun baro romeo da juliet agida, ga kuma layla da  majnoon"


Fitowar su Danejo daga kitchen ne Ya katse firarsu, kowan nan su ruke da farantai shake da kayan abinci , akan rug suka ajiyesu,


 kowannansu ya sauko kan rug din suka kewaye farantan,tun da kamshin abincin ya daki hancinsu suka fara hadiyar yawu


Har sun fara Cin abincin, Batool tace"ba zamu jira Unaisah ba"? Ummi tace"nima dai naji shiru bata karaso ba"danejo tace"kada ku damu, itama na ajiye mata abincin ta, duk lokacin data karaso sai taci"


 daga haka ba su kara magana ba, Kowa ya maida hankali kan abincin da yake ci da alama yayi masu dadi, su parveen ba baka sai kunne, Hannu baka hannu kurya, kwata kwata bata Iya bakunta ba. Ummi har alama tayi mata da ido donta daina loma amma ta wani basar kamar bata ganta ba


Danejo ko sai fadi take kuci ku koshi in ma bai isheku ba, akwai saura abincin dana aje mana..


_________________________________💔


Around ƙarfe 2 na rana da matsakaicin gudu motocin su suka kunno kai Cikin Villa din..


Su biyune zaune a back seat din Motar Chief, babu mai magana a cikin su, sunyi shiru daga gani ba karamar gajiya suka kwaso ba ..


Gently yake daddana wayar hannun sa, yana kokarin kiran daddy dinsa sai ga kiran shi ya shigo, yayi mamaki kamar yasan shi yake shirin kira..


Picking call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnansa yana niyar yi mashi sallama miryar Mai girma sharafudden Ta katse masa hanzarinsa"Owais Inason ganinka Yanzun nan..." har saida gabansa yadan fadi da jin yanayin muryar daddyn nasa.



"Am...daddy, Ina fata lafiya" bai kare maganar ba Yace"idan kazo zaka ji koma menene" daga haka Ya katse Kiran


Lamarin Ya daure mashi kai! Bai ta6a jin muryar daddynsa cikin fushi irin Na yau ba, fatan shi Allah Yasa ba wani abun bane ya taso.


A hankali Ya dubi Danish dake a hakimce kan seat, Ya langwa6e kan shi, Idanun shi suna a lumshe kamar ma bacci ne yayi awon gaba da shi.


"My Boy, Bacci kake Yi"? Cikin kunnanshi ya tsinkayi muryar chief a wahalce ya buɗe rinannun idanun shi batare daya iya furta kalma ba.


Adaidai Lokacin Motocin suka yi parking, agent Ya buɗe masu cardoors ɗin. .


Atare suka fito, adai dai lokacin Taj da big guy sun fito daga motarsu..


Gaba daya suka maida Hankali akan Chief da Danish..


"Daddy Ya kira ni yanzu a mota, Yace Yana son gani na, zan tafi.." ya fada yana kallon su


"Pls take care of my baby boy, he's very tired and needs your care. Ensure he bathes, eats, and then goes to bed and rests before the time is full..."


 yamutsa fuska Omar yayi kasa kasa da murya ya furta"sai kace wani jinjiri, kowa ma agajiye yake ay"


"Magana kake yi ne"? Chief ne ya fada yana kallon shi, Girgiza kai yayi"a'a," ya fada tare da kallon Danish baima san yanayi ba, hankalin shi baya atare da su..


"Sir, Allah ya dawo mana dakai lafiya, agaishe mana da mutanan gidan" amsa masu yai da ameen Kafin Ya koma cikin motar, basu bar gurinba, har saida motar chief ta 6ace na ganin su.


"Guy ina zuwa, Ka manta amanar da Chief Ya bamu"? Da zolaya ya fada yana kallon shi, a lokacin Danish Har yayi gaba abun shi..


Harara Ya galla mashi"Ya 6ata min rai, tarairayar da yakeyi masa tayi yawa sai kace wani jinjiri? Bai da magana sai ta Danish..." Yar dariya Taj yayi"wlh Omar Ka fara bani tsoro! Bana tunanin ko matar da zaka aura zaka yi kishinta makamancin wanda kakeyi ma Chief, kai dai bakaso kowa ya ra6e shi, bazan manta farkon zamana agidan nan ba, kiri kiri Ka fara jin haushina saboda kyautatamin da chief Yakeyi, naci wuyarka kafin muka saba da juna.." 


kayataccen murmushi Big guy yayi"ba zaka gane ba Taj, duk yadda zanyi maka bayani ba lallai ka fahimce ni ba, wlh ina tsananin kaunar chief son shi nake, fiye da yadda nakeson kowa nawa, nifa ji nake dama mu Twins ne ni da shi..."


 ɗan zaro idanun yayi maganar Omar ta bashi mamaki"nifa wlh ban ta6a zaton kai mataimakinsa bane saida na fara kar6ar training na isod, nayi mamki cos kamar ɗan aikinsa baka gajiya dayi masa hidima" yar dariya Big guy yai"kauna ce kawai, shima yayi fama dani akan indaina amma nakiya sbd banaso wani ya samu kusanci da shi."


Murmushi Taj yayi" Allah yabar kauna tsakaninka Da Chief, Allah yasa mutuwace kadai zata rabaku"


 ya kar6e da cewa"ita ma mutuwar bana fata ta rabamu, nafison ta dauke mu atare ni da shi"


 murmushi Taj yayi bakomai ya fado mashi arai ba face ɗan uwansa kuma amininsa Ozair, har abada bazai samu abokin da zai maye masa gurbinsa ba.


tuni Yaji Kwalla ta cike idanunsa a fakaice Ya share Hawayen don kada Omar Ya gani raba hanya su ka yi da Omar, Ya nufi part din chief don Ya cika Umarnin sa na ba Danish Kulawa.


A lokacin Danish Har Ya shiga bathroom, Koda ya shigo bedroom dinsa bai iske shi ba, landline din kitchen ya kira ya isar da sakon su kawo ma Danish lunch dinsa.


Yana katse kiran saiga kiran Ummi Ya shigo Layinsa, Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnansa.



"Boss, Har yanzu Unaisah batazo ba, har jaraba kiran layinta nayi amma akashe, kuma naga kofar falon anyi locking ɗinta already.."


 dafe kai yayi da hannu ɗaya sam Ya sha'fa'a da batun Unaisah..


"Ummi, i'm really sorry, dazu mantawa nayi wlh, amma yanzu zan dubota" 


"Okay, sai naji daga gare ka"


Rejecting call din yayi, Cikin sauri ya fito daga dakin Danish, Ya nufi Bedroom dinsu shigarshi Keda wuya adai dai lokacin Tana kokarin fitowa daga karkashin gado ashe tun bata fito ba, anan bacci yayi awon gaba da ita sai yanzu ta farka.


Wani irin burki Yaci Yana kallonta cike da mamaki, Yarinya ta zama kamar aljana, kwata kwata bata lura da shi ba, dakyar take jan numfashi saboda zazza6in dake nema yafi karfin ta, ga wata matsiyaciyar Yunwa da take ji, Sleeping Gown ɗin jikinta tayi squeezing, Kamar yadda sumar kanta ta yamutse. 


Gyaran Muryar da yayi mata ne, Yasa tay firgigit Ta juyo ta fuskance shi da idanunta wadanda suka ƙankance...


Wani irin faduwar gaba taji, girgiza kai taj yayi"Unaisah, Irin Rayuwar da kika zaba ma kanki kenan? Bakya jin maganata Unaisah, soyayya ta rufe maki Ido kinbi duk kin hana kanki kwnaciyar hankali" jikinta na kerma ta girgiza mashi kai batare data Iya furta kalma ba


A faɗace Yace"Zoki wuce Kibi Yan uwanki, tun safe suke ta jiranki" 


Make mashi kafaɗa tayi cikin disasshiyar murya ta furta"daddy, ni bazan bi su ba, anan zan zauna, kuma ko wanka ma banyi ba"


Ɗaure mata fuska yayi"Uban me Ya hana Kiyi wankan tun dazu? Ai kina sane kika boye karkashin gado, kega mai wayau ko"? Marairaice mashi fuska tayi"Dan Allah daddy, Ka ƙyaleni bana son zuwa, nafison na zauna nan, Ni bazan bi su ba..." 


Ganin Yana tunkarota gadan gadan Yasa Ta fara kokarin gudu, yana kokarin Cafkota, ta kufce mashi ta watsa da gudu Ta fuce daga dakin, Aguje yabi bayanta sai dai koda ya fito baiga gifcin ta ba, kamar walkiya ta 6ace ma ganinsa, Ranshi Ya 6aci ba kaɗan ba.


________________________________✍️💔



Fitowa yayi daga Cikin toilet, waist ɗinsa ɗaure da white towel, motsin mutun yadinga ji acikin kunnanshi, hakan yasa shi dakatawa da tafiya, slowly yake bin bedroom ɗin nasa da kallo Unexpectedly eye balls dinsa suka sauka akan Curtain dakin dake motsi, alamar akwai mutun a ciki..


Yatsun kafafunta Ya hango ta ƙasan labulen daya ɗage sai kerma suke ...farat ɗaya Ya gane itace..yayi mamakin ganinta adakinsa bayan kwanakin da suka shafe batare da sun nemi junan su ba, kome ya kawota bedroom dinsa? Aransa ya ayyana hakan.


Yi yayi tamkar baisan da zamanta adakin ba, shaf shaf Ya shirya kan shi, Cikin Singlet fara da short.. kafin Ya koma gefen gadonsa Ya zauna tare da maida hankalinsa kan breakfast din da Taj yasa aka kawo mashi..


A tsanake Yake Cin abincin ta wutsiyar idanunshi Yake satar kallonta yayin da take buɗe labulen Tana leƙensa ji take kamar taje garesa tayi hugging dinsa sai dai ina wani irin shakkar tunkararshi takeji, saboda maganganun data gaggaya masa marasa dadi ita kanta bata tsammaci zai dyauki tsawon kwanaki bai kula ta ba ko kiranta awaya bayayi..


Gajiya tayi da tsayuwar, ta fito daga bayan curtain din tayi tsaye tana kallon shi.


Tayi zaton baiganta ba, cikin sanyin murya tace"My man, fushi kake dani? 


Banza yayi da ita hakan ba karamin karya mata zuciya yayi ba.



"Baka ga halin damuwar dana shigaba, saboda kai ko bacci bana iyayi,nasan komai ya faru laifina ne, nina ja ma kaina amma ka yi hakuri ka yafe mim, I don't know if we'll meet again, maybe this will be our last meet, duk da bansan date da zaku tafi ba, amma inaji araina yau ne, shiyasa daddyna yace mu tafi part dinsa mu zauna, ni kuma na boye saboda inason muyi bankwana kafin mu rabu..."


 ta faɗa idanunta cike tab da kwalla, So hana ganin laifi, duk yadda yaso Yaki jin tausayinta hakan ya gagare shi, kalamanta sun ta6a zuciyar shi.


slowly ya dubeta daga kasa Ya fara kallonta, Hankalinshi ya tashi da ganin irin ramar da tayi, daga gani bata samun isasshen bacci ko bata cin abinci yadda ya kamata ga shi babu gyara a jikinta, kamar zai zubda mata kwalla saboda matsanancin tausayinta dayaji yasan duk akan shine ta shiga halin Damuwa...


Da spoon din hannun shi ya nuna mata gefen shi, cike da rashin kwarin jiki ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya batare da ta kauda ido daga kallon shi ba..


Cup din tea Ya dauko Ya kanga mata abakinta, ganin taki buɗe baki yasa shi furta"kisha" la66anta har kerma suke da sauri take kur6ar shi, nutsuwa yayi yana kallon throat dinta dake moving slowly.


sai da ta shanye shi kaf kafin ya dauki fork duk tana kallon shi Ya nannaɗo noodles ya tura mata abaki, kamar yasan yunwa take ji, sakin jiki tayi ya dinga bata tana ci saida ya tabbatar taci ta koshi kafin ya aje spoon ɗin.


Ya ruko yatsun hannayenta a cikin nashi, bata ta6a jin kunyar hada ido da shi irin na yau ba, saboda rashin mutuncin data zazzaga mashi, sunnar da kanta kasa tayi


Cikin nutsastsiyar muryarsa ya ce"Ni ban ruƙe ki a zuciyata ba, baki min komai ba, amma yanzu kin min abunda banji dadin shi ba..." a rude ta kalle shi


"Meyasa zaki takura kanki akaina"?


 Cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri, nasan nina tursasa maka akan kaje aman wallahi ni kadai nasan radadin da zuciyata keyi min saboda zullumi da fargaban mezai biyo baya idan ka tafi, wallahi bana so na rasaka, kuma wallahi bada son raina na gaggaya maka magana ba, nayi ne kawai don in fahimtar dakai amma kaima kasan irin son da nake maka zan iya rayu wa dakai ahaka yadda kake, koda kuwa zaka makance ne ka kuturce, ka gurguce wlh zan rayu dakai bazan ta6a canza maka ba"


bata kare maganarba, ya rufe la66anta da yatsan shi, hakan yasa ta haɗiye sauran maganar da bata amayar ba..


Nutsuwa yayi yana kallon siraran hawayen dake sintiri kan kuncin ta..



"Basai kin yi min bayani ba, na fahimce ki, ina jin abun da kike ji..." lumshe idanunta tayi tana jin wani iri aranta...



"Listen to me carefully, now I need your peace of mind because that way, I'll have the confidence to do everything, maganganun da kika gaya min tabbas banji dadinsu ba, amma ta wani bangaren sun taimakamin gurin Farfado da tunanina..." Ya ɗan dakata Yana duban fuskarta, sill bata bude idanunta ba.


"Abu ɗaya da nakeso Kiyi min alƙawari shine, Ko bayan tafiyana kada kiyi kukan rashina, kada kiki cin abinci, ko ki hana idonki bacci saboda ni, and even if I don't come back, be patient, Endure a life without me"


(sannan koda ban dawo ba, kiyi hakurin Jure rayuwa batare dani ba)

 

 bai ƙare maganar ba, ta katse shi cikin shesshekar kuka tace"Bazan iya daukar maka alkawarin nan ba, saboda bazan iya jurewa ba, bazan ma iya rayuwa batare dakai ba.."


 fuskarta ya tallabo da tafukan hannayensa"meyasa zaki karaya Unaisah? Kin manta abunda kike ce? ...girgiza kai tayi"ka manta da abunda ya wuce, ba acikin hayyacina na fada ba.." murmushi takaici yayi 


"Ki sama ranki zan dawo da raina da kuma Lafiya na, Nayi maki alkawarin hakan, zan kare kaina bazan bari na mutu ba.." bai kare maganarba tay saurin furta"baka ce In sha Allah ba"? Shiru yayi bai amsa mata ba.  


Gyada kai tayi"tunda ba zakace ba, ni zanyi maka addu'a, Allah ya kare mun kai, Allah ya dawomin dakai da ranka da lafiyarka, in sha Allah, ko bayan kun tafi zan raba dare na biyu, rabi inyi baccin awanni kadan rabin In tashi tsakar dare inyi maku addu'a...." har cikin ranshi yaji dadin maganarta, kuma, Har time din bata buɗe idanunta ba.


Batai aune ba, Taji safkar Yatsunsa agaban rigarta, a firgice ta bude idanunta, wata irin kunyace ta kamata ganin Yana maida mata front buttons ɗin rigarta, sakamakon  gudun da tayi ɗazu gaban rigar ya buɗe batare da ta ankara ba, tun da yafara bata abinci yake ta kokarin gyara mata rigar saidai ya kasa saboda gudun masifarta.


Sunkunyar da kanta kasa tay, tasan yaga abun da take 6oye masa..


"Ranar dana dawo, what will you do when you see me?" 


Ya fada tare da zame yatsunsa daga gaban rigarta ya maida tafukansa kan shoulders din ta kamar kanwarsa.


"I can't imagine how happy I'll be, I'll cry for joy and hug you tightly"


 ha6arta Ya ɗago da hannun shi"shi kadaine abunda zaki min"? Jinjina mashi kai tay, 


"That won't be enough for me.."


 "Faɗa min me kake so"? 


Kunnanta ya ruko tare da yi mata raɗa bai ƙare maganar ba, tay sauri toshe bakin shi da tafin hannunta, kamar wadda taji wani mugun abu, jikinta har rawa yake, His shyness enveloped her, and his sexy words made her burn with desire he also set his soul on fire, lumshe idanun shi yayi tare da ware su cikin nata, harara ta ɗan watsa mashi tare da murguɗa mashi small lips din ta.., kashe mata ido ɗaya yai tare da ɗage mata gira batasan sa'adda ta saki murmushin gefen fuska ba, wato son da takema Danish irin unconditional love ne, idan tana tare da shi takan manta da komai, kamar dai yanzu da suke atare ta manta ma da hudubar da daddyn ta yayi mata kan hada jiki da sukeyi indai tana tare dashi mantawa take da komai shi kadai take gani kuma takeso ta kasance dashi. 


Yana kokarin janye hannunta daga bakinshi, ba zato ba tsammani suka ji anyi knocking ɗin kofar, kallon juna sukayi wani irin faduwar gaba taji, sam ta sha'fa'a ta manta da daddynta da ke neman ta.


Muryarta nawa tace"nasan baiwuci daddyna bane, ni bana so naje part dinsa nafiso Inga tafiyarku tukunna, pls kada ka fada masa ina aciki, Ni zan boye..." wani irin kallo yake binta da shi, jikinta na kerma ta mike da sauri ta boye bayan curtain


Daga waje sukajiyo muryar Taj Yana fadin"Danish, Ka bude min ƙofa" mikewa yayi yaje gaban room door din Ya bude mashi.


shigowa yayi fuskarshi babu walwala Yace"Unaisah tazo nan"? Danish dabai Iya karya ba, Ya nuna mashi Curtain din da hannun shi"tana ciki" cike da takaici Taj Ya nufi labulen Ya ɗage shi, wata irin gigitacciyar ƙara ta fasa kamar zata zauce, ta dinga ihu tana fadin daddy bazanje ba, Ka kyale ni, kabarni inga tafiyar ku"!



ga tausayinta yanaji amma ji yake kamar ya rufeta da bugu.


bai bata lokaci ba, Ya sungumeta kan kafadar shi, Ya juya ya nufi kofar dakin kuka ta dinga Yi tana mika ma Danish Hannu don Ya kawo mata dauki  bawan Allah Yana ji Yana gani Taj Ya fuce da ita, baisan ko wannan zai kasance rabuwarsu Ta karshe ba, yana jiyo sautin muryarta daga waje cikin shesshekar take sambatu


_"I love you, Danish! I really love you, i wanna be with you for the rest of my life, I can't live without you, My heart beats for you alone, My soulmate, I'm yours, I don't want you to go and leave me! Please come back to me! don't die! I'll wait for you..."_


Zubewa yayi kan gwiwowinshi a karshe Ya yada kafadunsa kan floor.....


Yadda take a haukace, Ahaka Taj Ya nufi part dinsa da ita, sautin koke koken da takeyi ne yaja hankulan jami'an dake kai komo A compund din gidan zuwa ga kallon ta, gaba daya hankalinsu ya dawo kan su, Kamar mazurai haka suka zuba ido suna kallon Unaisah dake ta kokarin kwace kanta daga jikin daddynta, sun kwadaitu da ganin santala santalan cinyoyin ta, Yar rigar baccin jikinta duk ta nannade dama bata wuci gwiwarta ba...Bacin rai Ya hana Taj Ya lura da abunda ke faruwa..


*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post