Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 38 Complete by Boss Bature
Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 38 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

 "Junaid Dan Allah ka daina kuka! Me ya faru dakai? Meyasa ka 6oye a cikin wardrobe? ina Anah? Kwata kwata baya fahimtar me take cewa, kuka yakeyi na fitar hayyaci hada kai hannu ya dunga bugun bayan ta, fashewa sukayi da kuka daga ita har zahra wani irin tausayin shine ya kama su, gashi sun rasa gane kan shi.


banko kofar dakin ummi da mami su ka yi daga waje suka jiyo sautin kukan junaid hakan yasa suka watso aguje suka fado dakin, lokaci ɗaya suka ci burki suna kallon Anila dake a rungume da junaid, waro idanu sukayi hadi da buɗe baki tsabar mamaki da al'ajabi ne ya kama su! Sam sun kasa furta magana na dan wani lokaci kafin mami ta matsa kusa da su, muryarta da rudu ta furta"ikon Allah kamar junaid nake gani! a ina kuka gan shi ne"? Shuru ba wanda ya bata amsa har saida ta ɗan daka masu tsawa saboda akagareta"bakuji ina magana bane? A ina kuka gan shi"? Dakyar Zahra ta tsagaita da yin kukan tana faman jan numfashi ta labarta masu komai.


Mami ta zagba salati tana tafa hannayenta, gaba daya sun shiga rudani, lamarin yayi matukar rikirkita tunaninsu sun rasa tunanin me zasuyi, kowa da abunda yake sakawa aranshi..."

Mikewa Aneela tayi ɗauke da shi, ta nufi mami tana kuka Yana kuka an rasa me lallashin wani"mami ku taimaka ku lallashe shi yaƙi yin shiru na rasa gane meke damun shi, junaid baya a cikin hayyacin shi, idanunshi sun kaɗa jawur sai sambatu yakeyi mana"

miƙa hannu mami tayi zata dauke shi aikuwa ya maƙe kafaɗa ya ƙara shigewa jikin mamanshi, sautin kukan shi ya cika kunnuwansu, sun rasa ya zasuyi da shi, gaba ɗaya suka yi mashi ƙawanya suna kokarin shawo kanshi ta hanyar lallashin shi kwata kwata baya sauraron su, adai dai lokaci su abie sun dawo daga masallaci kwatsam sukajiyo kukan junaid mai ƙaraji, wani irin faɗuwar gaba ne ya darsu a zukatan su, mahboob har yana tuntu6e garin saurin ya shiga ciki, gudu gudu sauri sauri uncle Ɗan iya da Abie Sukeyi suka nufi dakin Anila, suna shiga suka iske su mami tsaitsaye cirko cirko fuskokin su sharkaf da hawaye, kusan atare su abie suka kai dubansu ga junaid, arude mahboob Yace"Junaid! Aunty Anila a ina kuka gan shi? Ko Ana ce ta dawo da shi"? Abie ne yayi hamdala Yana fadin Alhamdulillah sun dawo kenan, dama saida raina ya bani wani wurin sukaje, Ina Anan take ne? Me kuma akayi mashi yake kuka.. "? Uncle ɗan iya yace"lafiya kuke kuka?Shima Yana kuka babu mai lallashin wani? Ina ita Anan"?


cikin shesshekan kuka zahra ta sanar da su inda suka gano junaid



"Abie, junaid baya sauraron kowa, kwata kwata baya acikin hayyacin shi, kuka kawai yakeyi, mun rasa gane kan shi..." tsantsar tashin hankaline akan fuskokinsu har sun fara murnar ganin shi azatonsu Ana ce ta dawo da shi ashe ba haka bane.


"Bani shi nan" abie Ya fada tare da miƙa ma Anila hannu, a firgice baby junaid Ya ƙankameta alamar bazai je gurin abie ba, cikin murya kuka tace"abie ya ki yarda da kowa, su mami sunyi kokarin lallashinshi amma Yaki sauraron su...."


Girgiza kai abie yayi tare da ambaton Inna lillahi wa inna ilahirraji'un kafin daga basani ya kalli anila dake ta sharar kwalla, tana jijjiga junaid

"Anila ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, ki daina kukan nan, Kina kara ɗaga mashi hankali, je ki zauna ki lallashe shi, ke kadai ce zaki iya shawo kan shi,  kiyi mashi addu'a ita yake bukata ayanzu..." amsa mashi tayi da toh, da sauri ta koma gefen gadon ta zauna, tare da sanya hannu ta talla6o kan shi, ta fara yi mashi kira'ar alkur'anin a cikin kunnanshi, su mami sunyi zungudum suna kallon su gwanin ban tausayi, cikin ikon Allah taji ya fara tsaitsayawa da yin kukan kafin a hankali taji yayi shiru ya nutsa kan shi a kirjin ta, fuskarshi tabi da kallo kumtunsa sunyi jawur, la66ansa sun kumbura suntum, hatta ƙwarin idanun shi sunyi jajir, siraran hawayene ke ta zarya kan kun cin shi, lokaci ɗaya taji ya fara sauke ajiyar zuciya a jere jere, nunfashin shi ya fara daidaita ba kamar ɗazu ba.


bata dakata da yi mashi kira'ar ba har saida ta tabbatar ya daina shesshekar kukan kafin tayi shiru tana duban shi, ajiyar zuciya su mami suka sauke hankalin su ya dan kwanta jin yayi shiru

Cikin sanyi murya ta furta sunan shi"junaid" motsa la66ansa yayi batare daya firta kalma ba...

"Dan Allah ka daina kuka, kasan bana son 6acin ranka, nasan nice na bata maka rai na tafi anguwa nabarka, ka yi hakuri ka yafe min junaid, wallahi bansan za'a tada ku da wuri ba..." shiru yayi bai tanka mata ba...

"Babyna, bazaka mun magna ba? Fadamin meke damunka? Kanka yanayi maka ciwo? Ko kana jin yunwa? Ina Ana? Meyasa ka yin kuka..." duk tabi ta rude sai surutu takeyi mashi, shidai yayi shiru bawan Allah shi kadai yasan bala'in da idanun shi suka gane mashi.


"Kada ki takura mashi Aneelarh, tun da mun samu yayi shiru, ki kyale shi Ya huta, Allah kadai yasan meya faru da shi wanda yayi silar rikicewar shi"! Mami ce tayi maganar

Ummi tace"ni ban ma san tunanin me zanyi ba wallahi, hankali na Ya tashi! abun da ya ɗaure min kai meya faru da su? Taya akai junaid yayi wayon 6oye kan shi a cikin wardrobe? To ko dai wani mugun abunne Ya faru da su bayan tafiyar mu, gaskiya ina ji araina Ana ce ta boye shi don kada a cutar da shi ko kuma shi ya boye kan shi sakamakon wani mugun abun daya gani, Allah daga ganin halin da junaid yake a ciki bana lafiya bane, Yaga wani abune daya razanar da shi" ta ƙare maganar tana kallon su


Jinjina kai uncle dan iya yayi"nima abunda nake tunani kenan, amma taya za'ay mu san ainihin abunda ya faru bayan tafiyarmu? Cikin shesshekar kuka Anila tace"Junaid zai iya fada mana idan Allah yasa ya dawo hayyacin shi"


Mahboob daya gama razana dakyar ya iya bude baki yace"ni damuwata yanzu ina Ana? Ga junaid ya bayyana saura ita baiwar Allah, bamusan meya faru da ita ba! Bamu san awani hali take a ciki ba..." bai kare maganar ba, Abie yace"in har wani abunne ya faru da su, zai iya yiwuwa itama ta boye awani wuri kamar yarda ta 6oye junaid..." jin wannan maganar yasa mahboob ruko hannun zahra yace mata tazo suje su kara nemo ta, da sauri suka fuce daga dakin bedroom dinta suka shiga, suka fara nemanta sako da lungu har karkashin gadon ta, da cikin wardrobe dinta amma basu ganta ba, sun duba ko'ina tun suna sa ran zasu ganta har suka fidda rai, kafin su fito daga dakin sai da mahbbob ya shiga toilet dinta Ya kashe shower din da aka bari a kunne da faucet, ruwa harya fara taruwa sosai har cikin dakin ta ya fara gangarowa, basu bar dakin ba sai da mahboob ya taimaka ma zahra suka gyara mata shi, kafin suka fito da sauri suka nufi sauran dakunan suna duddubawa, duk wani wurin sirri da mutun zai iya 6uya saida suka duba ko zasu ganta sai dai kash bata nan, ceilling ne kadai basu tsaga sun bincika ba don sunsan ba tayadda za'ay ta iya shiga ciki ta buya.

Badan sunso ba dole suka hakura da nemanta, jikinsu yayi mugun yin sanyi, zuciyarsu ta karaya, gani suke kamar ba zasu kara ganin Ana ba.



Anila taso takai baby junaid asibiti adaren saboda aduba mata lafiyar shi amma abie ya hanata yace mata ta cigaba da yi mashi addu'a in sha Allah zai samu lafiya, taruwa sukayi akan shi ɗaya bayan ɗaya kowannansu saida yayi mashi addu'a suka tottofa mashi a jikin shi, har indomie zahra ta dafa mashi ta kawo masu a plate amma yaƙi ci, ta koma kitchen ta haɗo mashi tea dakyar anila ta samu yasha tea din, jikin shi ya danyi sauki, zuciyar shi dai ce take bugawa da karfi, duk yadda taso ya bata hadin kai suyi magana don taji meke damunshi yaƙi mata magana kamar kurma sai dai yabi ta da ido, don dole ta hakura, gashi ya hanata sukuni ya manne mata kamar anta da jini, ko da zata shiga toilet ta  karasa alwala sai dai ta shiga da shi, bayan ta fito ta goya shi abayanta ahaka tayi sallah 💔


___________________________________✍️


*ALHAJI MUSA💪*


Da sassafe ya shigo katafaren falon gidan, jallabiya ce a jikin shi grey colour, ta ɗanyi tighting arms dinsa, kamar kullum fuskarsa a daure ba fara'a, ya zuba hannayenshi cikin aljihun jallabiyar.


Cikin takun izza yake tafiya yan aikin gidan dake kai komo suna yin aikace aikacen gyara falo dakai abinci dining suna ganin shi, suka fara gaishe da shi, ko kallo basu ishe shi ba, kaitsaye ya nufi dining room ya tsaya bakin glass door din yana kallon zungureran table din dake a kewaye da kujeru ancika shi da kayan breakfast, wani abu da ya ɗaure mashi kai babu kowa a kan kujerun  yayi mamaki sam ya manta da abunda ya faru jiya, saboda bayan ya gama balbalin bala'in shi gidan ya bari gaba daya bai ƙara dawowa ba, sai yanzu daya shigo da safen nan,baisan awani hali mutanan gidan suka kwana ba.


Agogon hannunsa ya duba don yaga ko time na yin breakfast dinne baiyi ba sai kuma yaga lokaci yayi

Ta6e baki yayi kafin ya dago ya kalli yan aikin, Tani ya hango da hannu yai mata alamar tazo, jikinta na bari ta nufe shi"yalla6ai gani"

"ya akai banga mutanan gidan ba? Ko baku fada masu an shirya masu breakfast ba"?

"Wallahi mun yi masu magana, ita zeenatu tace mun bazata ci ba, nayi nayi da ita taki kula ni, shi kuma shureim da naje dakin shi na iske shi kudundune cikin bargo kamar baida lafiya nayi mashi maganar breakfast yace min baijin yunwa in tafi kawai..."


bata kare maganar ba, rai a6ace ya ɗaga mata hannu da sauri taja baki tayi shiru duk tabi tasha jinin jikin ta, wucewa yayi azafafe Ya nufi upstairs, ya ture kofar dakin zeenatu ya shiga daga ciki, tana a zaune kan prayer mat, hannunta ruke da al'kur'ani tana karantawa sam bata ji motsin shigowar shi ba.


"Zeenatu"! Kakkausar muryarshi ce ta daki kunnanta, bata kula shi ba, tamkar bataji kiran da yayi mata ba, hakan ba karamun fusatashi yayi ba, kwatsam taji ya dauke kur'anin dake a hannunta, azabure ta mike idanunta sharkaf da hawaye ta furta"Daddy, give me my Qur'an..." ko kula ta baiyi ba ya rufe kur'anin ya nufi bookshelf din dakin ya daura shi asama kafin ya juyo ya kalle ta"fushi kike dani? Rai a6ace tace"daddy ba iya fushi nake da kai ba, haushin ka nake ji, dan Allah ka kyaleni in cigaba da karatuna ko na samun saukin abunda ke damuna..." fashewa tayi da kuka gaban hijab din jikin ta ya jike sharkaf da ruwan hawayen ta


"You don't want my happiness, Daddy. You don't want peace kullum burinka ka 6ata min rai, a haka kake son inyi alfahari dakai amatsayin mahaifina!"


ta faɗa tana zare mashi blue eyes dinta wadanda suka kaɗa jawur, ko kadan baiyi mamakin kalaman data furta mashi ba, ya riga da yasan meke damunta, wato saboda ya bata ma shureim rai jiya shiyasa take fushi da shi.


Matsawa yayi kusa da ita da sauri taja da baya tana girgiza mashi kai, wani irin fargaba da tsoron shi ne suka kamata tayi zaton zaiyi mata wani abune. Batai aune ba taji ya damƙi arm dinta ya janyota kan broad chest dinsa yayi hugging dinta.


softly yace"fadamin laifin me nayi maki? Meyasa kike fushi da daddynki? Cikin shesshekar kuka tace"ka 6ata ma ya shureim rai, jiya banji dadin kalaman daka gaya masa ba, daddy ya shureim baiyi maka laifin komai ba, amma ka rufe shi da fada harka shake wuyan rigar shi, baka dubi girman shi ba..." dakyar ta ƙare maganar, shafa bayanta yayi cikin sigar lallashi yace"yanzu me kike so nayi? Don in wanke laifina"? Ya faɗa tare da dago da fuskarta suka haɗa ido sai taji yayi mata kwarjini da sauri ta kau da idonta gefe murya na rawa tace"kaje ka bashi hakuri,  idan yace ya yafe maka nima zan daina fushi dakai" ɗaure fuska alhaji Musa yayi jin abunda tace wai shi zaije yaba shureim hakuri, girman kanshi ba zai barshi ba, amma dayake shu'umun kanshi ne sai yace mata"okey, mu sauka down, muje kici abinci" maƙe mashi kafada tayi"bazan iya ci ba, in ba atare da ya shureim ba"


"It's okey, muje sai in bashi hakurin" tace toh, ya ruko hannunta suka sauko downstairs.


A dining room ta tsaya kamar yadda ya bata umarni, Shi kuma Ya nufi dakin shureim time din daya shiga da sallama abakin shi, bai taras da kowa ba adakin, sautin ƙarar zubar ruwa yajiyo daga bathroom, alamar yana aciki yana wanka, zama yayi gefen gadon shi yana jiran fitowarshi,

Almost 15 mins yana jiran shi, har ya mike zai tafi don bayason jira arayuwarshi sai dai ajira shi, jin motsin buɗe toilet door dinne yasa shi dakatawa ya tsaya yana kallon shureim dake fitowa waist dinsa daure da towel, gefen fuskarshi yayi jawur kamar jini ya kwanta, hada sahun yatsun Alhaji musa shatunsu ya fito rudu rudu, sai yaji ba dadi aran shi, ganin irin illar daya yi mashi kuma yayi imanin zafin marin da yayi mashine ya haifar mashi da rashin lafiya a jikin shi kamar yadda yaji Tani tace bashi da lafiya.


Kwata kwata shureim bai lura da Alhaji musa ba, cikin rashin kwarin jiki ya nufi dressing mirror.


"Shureim"!Ya kira sunan shi, ɗaure fuska yayi batare daya kalli inda yake ba, duk da yayi mamakin jin Muryarshi a cikin kunnanshi aranshi ya ayyana kome yazo yi dakin shi?ya dai san ba hakuri yazo bashi ba abune mawuyaci.


"Da kai fa nake magana"! ya faɗa fuskarshi adaure, da farko yaso ya shareshi don yaga iya gudun ruwan shi amma sai ya fasa saboda mutunne shi mai matukar ladabi da biyayya yana ganin girman nagaba da shi bayan haka akwai na annabawa wato hakuri.


Juyowa yayi suka fuskanci juna 

Muryar shi kasa kasa ya furta"Uncle, barka da safiya? Ka tashi lafiya"? ya dan yi mamakin tarbar da shureim yayi masa, amma bai nuna a fuska ba,

"ka zauna inason magana dakai" kasa kasa ya amsa da toh, kafin ya juya ya shiga wurin closet dinsa, jim kaɗan ya fito sanye da jallabiya fara, a kan couch suka zauna shureim ya kau da idanun shi gefe ɗaya yana jiran jin dame yazo!


"Shureim dangane da abun da ya faru jiya bana a cikin hayyacina, kasan inada bad temper idan raina ya 6aci bana iya controlling kaina..." yanayin yadda yayi maganar ya ɗaurewa shureim kai har saida Ya juyo dakai ya kalle shi don ya tabbatar idan dagaske uncle musa ne ke yi mashi magana ba wani daban ba.


haɗa ido su kayi da juna da sauri dr. Shureim ya kau da idon shi gefe ɗaya, hakan bai dame shi ba yaci gaba da magana cikin tausasa harshe"inaso komai ya wuce shureim, ni bana son duk wani abu da zaisa mu samu sa6ani atsakanin mu..." sai da yai wannan maganar shureim ya dube shi dakyau yace"uncle ni wannan duk ba damuwata bace, bana ruƙe mutun a zuciyata, tabbas banji dadin kalaman daka jife ni da su ba, sun bata min rai, saboda ban ta6a tsammanin zaka iya furta min su ba, da ace wani na waje ne ya gaya min su bazan ji komai ba, amma kai da kanka uncle why? Saboda na fita da zeenatu yar uwata? Ko dan saboda rungumar da nayi mata wanda nikaina bada son raina nayi ba.." idanun shi cike tab da kwalla ya fada yana kallon cikin idon shi"saboda zafin kalaman daka furta min jiya ko bacci banyi ba, da bakin cikin su na kwana azuciyata" mood din fuskar Alhaji musa Ya canza sosai, kalaman shureim sun karya mashi zuciya sai yaji duk ba dadi.

Ruƙo hannun shi yayi a cikin nashi ya ruƙe su gam na ɗan wani lokaci kafin ya fara magana a tsanake"Allah ya huci zuciyarka shureim, na gane kuskurena kuma in sha Allah zan gyara.."ya faɗa yana ɗan jinjina kan shi.


"Da akwai wata tambaya da kayi min ajiya, dangane da kullan da ni ke yiwa zeenatu, kace ka fara kokwanto akaina! Shureim ina son jin dalilin dayasa kace haka? Wani irin kokwantone kake yi akaina..." ba tare da jin shakkar shi ba yace"ban yarda da kullan da kake yi mata ba, raina yana bani kamar akwai wani abu da kake 6oyewa shiyasa nake kokwanto akanka, ka hanata cigaba da karatu, ka hanata yin kawance da kowa, sannan ka hana ta fita, kamar baka son kowa ya ganta, ita kanta zeenatun ta fara korafi kan kullan da kake yi.


Shiru Alhaji musa yayi tamkar bazai yi magana ba, can kuma ya saki Murmushin gefen fuska kafin yace"zan fada maka dalilin dayasa nake kullanta, in har hakan zai goge zargin da kakeyi akaina.." ya fada yana kallon shi.


Kafin ya ɗaura da cewa"Dalilin dayasa nake kullan zeenatu, is that I'm a famous politician with many enemies who want to harm me. Zeenatu is my weakness, bayan haka itace ƴa ɗaya tak da nake da ita akusa dani, in har ban bata kariya ba, rayuwarta tana a cikin hatsari saboda akwai masu bin diddiginta, bana so inyi ganganci da rayuwarta, makiyana sun sha turo min sako akan zasu halaka zeenatu, shureim taya bazan killace ta agida ba"?  Maganar Uncle musa tayi tasiri a cikin zuciyar shureim jikinshi yayi sanyi zuciyarshi ta karaya, hankalin shi ya tashi da jin abunda ke faruwa da rayuwar zeenatu!


"May be zeenatu ta manta bata fada maka ba, lokacin da tana zuwa high school, kusan kullum in zataje makaranta sai an samu wadanda suka kai mata farmaki, don ma Allah yasa akwai bodyguards da suke kula min da ita ay da tuni zeenatu babu ita araye" ya faɗa tare da dukar da kan shi ƙasa ya marairaice fuska kamar ba Alhaji musa ba.


Cikin sanyin murya Dr shureim Ya furta"Uncle, hankalina ya tashi da jin maganar nan, yanzu na fahimci dalilin dayasa kake kullanta, ni kaina bazanso abun da zai cutar da ita ba, amma kullan yayi yawa tun da har ta fara takura, bai kamata saboda wasu ahanata jin dadin rayuwarta ba, bayan haka Allah shi yake tsare bawansa aduk inda yake, kuntata rayuwarta agida bashi bane mafita ba, wlh duk tsaron dake agidan nan bazai hana a cutar da ita ba, amma idan muka cigaba dayi mata addu'a, in sha Allah makiyanka ba zasu ta6a yin nasara akanta ba!" wasa wasa dr shureim ya 6uge dayi mashi nasiha har saida ya tabbatar Ya samu nutsuwa Kafin yayi shiru yana jiran jin me zaice..


"Shureim nagode da shawararka, zanyi tunani akai in sha Allah, sannan akwai magana da nakeson yi dakai idan na samu lokaci..." bai kare maganar ba, wayar shureim ta fara ringing,

"Zan ɗaga kira"

"Okey, pls ka sameni a dining, zeenatu tana jiranka, tace bazata iya cin abinci in ba atare dakai ba..." jinjina kai shureim yayi bayan fitar Alhaji musa ya nufi gaban mirror ya dauki phone dinsa Ya duba sunan mai kira, mommyn su ce da sauri yayi picking ya kara a kunnanshi

Tunkafin yayi sallama muryar hajiya layla ta katse shi"shureim wai lafiya tun jiya inata kira bana samunka ko wani abu ya faru ne? 


Cikin sanyin murya yace"a'a mommy, kiyi hakuri, wayar tana a kashe ne ban jima da kunnata ba"


Yanayin muryarshi ya sa ta tunanin kodai ba lafiya gidan? 


"Ya jikin Benazir din? Ko har dr Ya sallame ku"


"Abun da yasa na kira ke nan, don in tuna maka, karfe 11 da rabi za'a sallame mu"


Agogo Ya kalla karfe 9, ajiyar zuciya ya sauke"In sha Allah yanzu zan shigo asibitin" amsa mashi tayi da toh, da sauri ya karasa shiryawa cikin shigar larabawa, ya ɗauki facemask ya zura a aljihun shi da niyar in sun fita zai sanya ma fuskarshi, don baison mommyn su taga tabon marin da Alhaji musa yayi mashi yasan muddin tagani sai ta tada 6alli.


Adai dai lokacin daya fito daga dakin, sai ga Hajiya sarah ta kimtsa cikin riga da skirt na atampa, ta kashe daurin kallabi mayafinta akan kafada ta daura shi, ta ruke purse dinta a hannu, kasa karasawa tayi gare shi ganin tabon dake akan fuskarshi cos tun jiya da abin ya faru kowa ya shiga dakin shi basu kara haduwa ba, taji nauyin hada ido da shi duk saitaji ba dadi.


"Aunty, barka da safiya, kin tashi lafiya" fuskarshi dauke da murmushi ya nufe ta.


Tuni taji idanunta sun ciko tab da kwalla cikin sanyin murya tace"shureim ka yi hakuri da abunda ya faru jiya, wlh bakin cikine Ya hana in leko dakin ka, banji dadin ganin yadda tabon marin ya bata gefen fuskarka..."

Cikin sauri yace"pls komai ya riga daya wuce, kada ki damu kanki, lafiya kalou, ay uncle dinma yazo har daki ya bani hakuri harma mun sasanta kanmu" kallon shi kawai takeyi gwanin ban tausayi, ta dade bata ga mutumin mai saukin kai da hakuri irin dr shureim ba.

Ganin tayi tsaye tana kallon shine yasa shi furta"nayi waya da mommy ta fadamin karfe goma za'a sallame su, yakamata muyi sauri muyi breakfast sai mu wuce..." girgiza kai tayi da sauri ta share kwallar data zubo mata, tabi bayan shureim suka nufi dining 

___________________________________✍️


Around karfe 10 na safe, Unaisah tana a zaune kan kujerar gaban gadon Benazir, har ta kammala shirin ta cikin abaya maroon colour, tayi rolling veil akan ta, baiwar Allah jikinta yayi sanyi, zuciyarta batayi mata dadi, sam bata son rabuwa da Benazir ta kamu da kaunarta, duk yadda take zumudin son tafiya don taga yan uwanta, saida taji ba dadi, sabo kenan turken wawa...


Gaba ɗaya ta shiga zurfin tunanin rabuwa da ita, benazir dake zaune gefen gadon ta ƙura mata ido tana kallon ta ko kyaftawa batayi, ta fahimci kamar wani abu yana damun yarinyar, ita kan ta faduwar gaba take ji kuma ranta yana bata kamar wani abu zai faru


"Babyna me kike tunani"! Cikin kun nanta ta tsinkayi muryar Benazir, wadda tayi silar dawo da ita daga duniyar tunanin data lula..


Numfasawa tayi a hankali take kallonta, tuni taji hawaye sun cika tab da idonta, hajiya layla tana a tsaye bakin kofar toilet tana kallon su fuskarta duk ayamutse, damuwarta halin da Benazir zata shiga idan aka raba ta da yarinyar, ita kanta ta shaku da yarinyar tana son ta, sai dai ba yadda suka iya dole su yi hakuri su rungumi kaddara.


Tattausar murmushi Unaisah ta sakar mata, tare da miƙa mata kwayar maganin dake a hannun ta"mamana ki sha maganin ki," dakyar ta ƙare maganar tamkar zata fashe da kuka saboda tasan maganin bacci ne dr jazz ya bata don ta ba benazir tasha, duk don su samu tayi bacci ko sun tafi da unaisah....


Baiwar Allah Benazir kamar tasan me suke kokarin yi gabanta sai faduwa yakeyi, buɗe baki tayi unaisah ta sanya mata kwayar maganin, ta kanga mata glass din ruwan hannunta ta shanye shi, ƴan mintuna ƙalilan Benazir ta fara gyangyaɗi idanunta suka fara kokarin rurrufewa wani irin karfi maganin ke gare shi dr jazz ya iya aika aika...cikin karyayyar murya ta furta"babyna, kada ki tafi ki barni, inaji ajikina kamar tafiya zakiyi..." ɗan zaro ido unaisah tayi da sauri tace"ki daina wannan maganar mamana, ina atare dake babu inda zanje" dafe kai benazir tayi da hannu ɗaya, dakyar take buɗe idanun ta masu ɗauke da matsanancin bacci ta ƙurama unaisah ido cikin sanyin murya tace"dan Allah ki yafe min Angel, nasan ban kyauta maki ba, amma kada kice zakiyi fushi dani, kada ki tafi ki bar ni, wallahi ina sonki, Allah shine shaida ta bada son raina na tafi nabar ki ba, nayi maki alkawarin zan baki gatan da kika rasa na rashin uwa atare dake, zan tarairaye ki in baki kulawa Angel"  a matuƙar ruɗe Unaisah ke kallon Benazir, kalamanta sun ta6a mata zuciya, sun fama mata ciwon dake a zuciyar ta, amma sai tayi tunanin watakil tana sambatune akan yarta da ta rasa.


Kukane Ya kwacema Hajiya layla da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta saboda batason ta ɗaga masu hankali.


Baccin ne Ya rinjayeta, jikinta ya saki a sukwane ta kwantar da kanta saman pillow, ta lumshe idanunta har  lokacin bata daina yin sambatu tana ambaton sunan Angel.


A hankali unaisah take binta da kallo zuciyarta na harbawa da karfi da karfi gani take kamar in ta tafi ba zasu ƙara haduwa ba, lokaci ɗaya taji tsantsar tausayin matar ya kamata, tayi fatan ace zata cigaba da kula da ita sai dai tasan daddynta bazai barta ba, after that yan uwanta suna bukatarta ita kanta bazataso tayi nesa da su ba, ruwan hawayen da suka taru acikin idanunta ne suka fara yar tseral kan kuncin ta.


"Azeezaty! Ke nake jira muje ko"? Dr jazz ne yayi maganar yana daga tsaye bakin kofar ɗakin, miƙewa tayi daga kan kujerar, kamar wadda aka zarewa laka, ta sunkuyar dakanta saitin fuskar Benazir ta manna mata sumbata har sau biyu kafin ta juya taje ta ɗauko backpack dinta, ta kalli hajiya layla miƙa mata hannu tayi alamar tazo, da sauri unaisah ta ƙarasa gareta, hajiya layla ta rungumota a kirjinta.


"Toh Azeezaty, mungode Allah yasaka maki da alkhairi, Allah ya baki ilimi mai amfani duniya da lahira, Allah ya baki miji nagari, zamuyi kewar rashinki, ɗan zaman da mukayi dake mun saba dake, benazir zatayi kukan rashin ki, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarki, Allah yasakama iyayenki da alkhairi..." amsa wa tadinga yi da ameen kamar kar su rabu da juna.  


"Ki gaida min da mutanan gidan, in sha Allah zamu zo wata rana har gidan naku"


Murmushi Unaisah tayi"Allah ya kawo ku lafiya, Allah ya ƙara ma mamana lafiya, nima daddyna yace zai kawo ni gidan ku" murmushi hajiya layla tayi taji dadin maganar, sallama sukayi da juna, A hankali take tafiya tana waiwayon Benazir dake kwance tana ta sharar baccin ta....

Dr jazz harya fara gajiya da jiranta, sai faman duba wrist watch dinsa yake yi baya son chief ya karaso don yasan bai son jira.


Har fa ta kusa fitowa daga dakin sai kuma ta juya da sauri ta koma gaban gadon Benazir ta manna mata peck a goshin ta.


Ganin abun nata bame karewa bane yasa dr jazz shigowa dakin Ya tasa keyarta gaba suka fito, baiwar Allah tana tafiya tana waiwayon dakin hajiya layla tana tsaye bakin kofar room din, hawaye sun cika idanunta har saida suka bace ma ganin ta kafin ta juya ta koma ciki zuciyarta cike fal da kewar Azeezaty.


A dai dai lokacin da suka fito, hamshakiyar motar chief ta kunno kai ta entrance gate din asibitin yar uban su launin ash colour har salƙi take da daukar ido, yanayin yadda motar take tafiya slowly yayi matuƙar jan hankalin visitors dake zarya a arean wurin, suka bi da ido har saida ta tsaya a parking sace.


"Muje, Ina tunanin shi ne ya karaso" jaz ya fada tare da jan hannunta, tunkafin su ƙarasa take ta kallon hamshakiyar motar, tayi mata kyau, lokacin dayazo kawota ba irin wannan suka hau ba.


Bayan sun ƙarasa gaban motar, ta ciki aka buɗe mata cardoor din wani daddaɗan fragrance ne Ya daki hancinta, mai haɗe da sanyi A.c.


"Ki shiga ciki" jazz ya faɗa tare da nuna mata hanya, sunkuyar dakai tayi tare da shiga ta zauna, wurga ido tayi akan shi har saida taji gabanta ya fadi saboda wani kyau da taga yayi mata, ya kare gefen fuskarshi da phone dinsa, da alama waya yakeyi, fuskarsa tana asanye da mask.


Hadadden yard din dake ajikin shi Senator cotton material ne light sky blue, rigar short sleeve ce ta bayyana strong arms dinsa, na karfafan maza masu ji da kan su, lallausar sumar kanshi ta sha gyara, ya sabunta military hair cut din sa


 Sunnar da kanta ƙasa tayi ganin yana ƙoƙarin juyawa,  janye wayar yai daga kunnanshi, Ya ɗago suka haɗa ido da jazz sai faman sakar sakar mashi murmushi yakeyi

"babban yaya, sannu da zuwa barka da safiya"

Calmy ya furta"lafiyalou jazz, ina fata kaima haka"

"Alhamdulillah"

"Ya mai jikin?

"Taji sauƙi sosai"

"Naji dadin jin hakan, zamuyi magana anjima" amsa mashi yayi da toh, har time din bai kalli Unaisah ba, kamar baisan da zaman ta ba sai bayan da jazz ya rufe murfin motar, ta kamo belt zata daura taji ya ruko yana kokarin sanya mata ita wani irin shock taji, muryarta na ɗan rawa ta furta"ina kwana"

"Ina lafiya" atakaice Ya amsa mata, agogon hannun shi tabi da kallo kirar rolex daytona tayi bala'en yi mashi kyau....bayan ya kammala sanya mata ya gyara zaman shi, 

A hankali ya dago ido ya kalli senior Agent din dake zaune a driver seat"zamu iya tafiya" cikin girmamawa ya amsa mashi okey Sir,

Key yayi ma motar tare da yin reverse ya karya kwana motar ta fuce daga asibitin.


Ajiyar zuciya ta ɗan sauke idanun ta akan window glass din motar, asibitin take kallo cike da jin kewar Benazir matar ta kwanta mata aranta, amma idan ta tuna yar uwar chief ce sai taji hankalinta ya kwanta, ta wani bangaren ta kosa su koma gida ko dan taga yan uwanta almost one week tayi kewarsu"


Fragrance din turaren chief Ya hana ta sukuni, ta wutsiyar ido take satar kallon shi, dogon hancin nan nashi ba karamin tafiya yake da ita ba. Hankalin shi na akan phone dinsa da yake scrolling

Tayi tsammanin gida zasu wuce kaitsaye amma sai taga kamar sun canza hanya, ba wadda suka biyo ba aranar da zai kawo ta, aranta ta ayyana watakil wata hanyar ce da bata sani ba.

Tana tsaka da yin zancen zucinta, suka karaso wani katafaren Obie mall luxury plaza


Tayi mamakin haduwar wurin tunani ta farayi ko me zasuyi a mall din? Ta dai zubama sarautar Allah ido.


bayan shigar su ciki agent din yai parking a katafaren parking space na mall din. 


Shiru tayi zuru tana jiran jin me zaice, sai da ya shafe 5 mins kafin taji ya furta"Let's go inside." fitowa sukayi atare, da sauri senior agent din ya fito ya take masu baya, Hankalin Ta ba karamin tashi yayi ba ganin wayayyun ƴan mata da samari yan gayu suna zarya a wurin duk sai taji ta raina kanta, wata irin kunyace ta kamata, takasa motsawa daga inda take ganin idon mutane ya dawo kansu, duk da facemask din dake akan fuskar chief hakan bai hana mutane kallon shi ba musamman yan matan dake gifta wa wasu kamar zasuyi tuntu6e tsabar yadda suke kallon shi, ga shi ba halin tunkarar shi saboda senior agent din dake atare da su, wani basamuden mutun ne ƙarƙarfa babu annuri kan fuskarshi, ga bindigu dake soke a qugun shi.


Ganin bata da alamun motsawa ne yasa shi ruko hannunta a cikin nashi, rass taji gabanta Ya faɗi duk sai ta kama yan kame kame tana faman noke kai, duk da yadda taso ta daure kada tai kauyacin saida ta kasa a hankali take satar kallon mall din yayin da suka nufi main entrance, Security guard din dake tsaron wurin sun gane chief, sai miko gaisuwa sukeyi cikin girmamawa kamar zasu durkusa kasa, tun da taga haka sai ta fara jin kanta wata hajiya gata ga chief, murmushin gefen fuska ta dan saki tana wani tafiya taku dai daya tana hura hanci.


Senior agent din ne ya ruke mata shopping cart, ganin taki daukar komai sai kalle kalle takeyi ne yasa agent din yi mata gyaran murya ta kalle shi"ki dauki abunda kikeso, sannan ki daukarwa yan uwanki"


waro ido ta danyi tare da juya kai ta kalli chief, yana tsaye gefenta ya goya hannayen shi kan kirjin shi in a low voice ya furta"Do what he said" amsa mashi tayi da toh, nan fa tafara ruwan ido ta rasa me zata dauka ba sabon ba, ga mutane suna ta yin shopping dinsu hankali kwance ita ko kamar an daure mata hannayenta,


 Sun lura da yanayin ta ganin zata 6ata masu lokacine yasa chief kallan agent din ya bashi umarnin duk abunda yaga idanunta sun kalla ya daukar mata shi ko da mara amfani ne, ya amsa mashi da okey sir.


 juyawa chief yayi a hanzarce ya koma mota ya zauna saboda baison kallon da mutane sukeyi mashi.


Bayan fitar chief, Unaisah ta miƙi hanya, agent ɗin yana abiye da ita jira yake yaga me idonta zai kalla, ita kuma taki yarda ta kalli komai tunda taji umarnin da chief ya bada, tafi son tayi ta kallon yan mata da samarin dake shopping a wurin.


Adaidai wurin Confectionery, ta tsaya tana kallon chocolates din dake a jere ga cookies kala kala, da sauri agent din ya fara jidar mata su iri iri yana turawa a cart din duk abunda ta kalla saiya dauke shi, har saida ta kau da ido tukunna ya dakata. Tafiya ta cigaba dayi ta nufi gurin data ga an rubuta Female Fashion Floor, kayayyakine kala kala na mata da zarar ta kalli abu, cikin sauri agent din yake daukar mata shi koda kuwa mara amfanine kai har bras da pads saida ya kwasar mata saboda umarnin boss dinsa yake ki.


Gabanta har faduwa yakeyi ganin cart din ya fara cika, ita fargabanta ba tasan kudin kayanba kada su yi almubazzaranci.


Hakan baisa ta juya ba sai ta nufi Boys' Corner kayan mazane tundaga kan suturu masu kyau da tsada har izuwa takalma, shades, caps, watches komai fa babu ce kadai ke babu, da sauri agent ɗin yafara jidar kayan da yaga idanunta suna kallo, saida yaga ta kau da ido kafin ya dakata, cart din har ya cika yayi sauro, hakan yasa agent din yayi magana da wani sales assistant dake akusa da su yace mashi ya dauko masu wani cart din da sauri yaje ya dauko ya ruke mashi suka cigaba da take mata baya, aikin yi fa ya samu, ita fa hankalinta ma baya akan kayan, kawai gurin ne ya burge ta shiyasa taƙi tafiya, idonta take ba abinci, a wani Tech zone ta tsaya tana kallon kayan dake gurin da sauri ta juya duk suna abiye da ita kamar wata sarauniya, mutane sai kallon ta sukeyi  suna mamakin kayan da ake kwasar mata, ko yar wacece?



Har zata gifta gaban wani education hub ta dakata tana kallon writting material din dake a gurin, bakomai ta tunaba face yan uwanta bata da burin dayawuce su iya karatu da rubutu, yanzu ne taga abu mai amfani da zata iya nuna tana so..harta buɗe baki zatayi magana idonta ya sauka akan agent din da assistant din sun dage sai kwasar mata kayan sukeyi, tun daga kan notebooks, Dictionary, pens, pensil, markers, drawing book, duk wani abu da idonta ya kalla saida suka ɗaukar mata shi, gaba daya sun kashe mata baki, kamar sakarya haka ta saki baki tana kallonsu, ganin abun nasu bame karewa bane yasa tayi saurin furta"dan Allah ku dakata Ya isa haka! wadannan kayan sunyi mana yawa.." 

Agent din yace"banga alamun sun isa ba, Ni umarnin chief nake bi, in kina so mu dakata to ki kau da idonki daga kan kayan da sauri ta juya baya ta fara kokarin neman checkout counter dakyar ta gano gurin ta tsaya tana faman sauke ajiyar zuciya kamar wadda tasha gudu, har cashier din sai da ta dan bashi mamaki, ganin yadda ta fado gaban counter din, bayan ya auna kayan da suka siya total 800k har saida taji yan hanjin cikinta sun kaɗa murya na rawa ta kalli agent din"dan Allah ku rage kayan su koma na dubu goma" maganarta taso ta basu dariya agent din yace"da alama bakisan wanene chief ba, idan duka kayan mall din kikeso zaisa a mallaka maki su, babu abunda zai ragu na daga tarin dukiyar da yake da shi.." jinjina kai cashier din yayi" amma dai yalla6ai, ita din bakuwa ce a family din su? Daga mashi gira agent din yai, murmushi cashier din yayi a lokacin har an kammala sanya masu kayan a cikin shopping bags har kusan huɗu, 

Agent din ya zaro master card din da chief ya bashi ya miƙa ma cashier din don ya ciri kudin, ƙin kar6a yayi fuskar shi dauke da murmushi yace


"Grandpa dinsa Ya hana a kar6i kudinsa, ku tafi kawai" girgiza kai agent din yayi"ka kar6a ka ciri kudin, chief baya son siyan kaya batare da an kar6i kudinsa ba, gani yake kamar sadaka aka bashi" dariya sukayi cashier din yace"nasan halin shi ay, har yau bai canza ba kenan, kudin ay duk nasu ne ko an kar6a hannunsu yake komawa, pls ka bashi hakuri ni bazan iya cirar kudinsa ba, zaija min ne..." duk yadda agent din yaso ya kar6i card din yakiya dole suka hakura yace ma unaisah su tafi, ita dai hankalinta yaki kwanciya, ta ruɗe da alamarin, taya zasu sayi uban kayan nan kuma aki kar6ar kudinsu? Abunda bata sani ba, mall din mallakin famiy dinsu ne, juyawa tayi da sauri ta nufi hanyar fita agent din yabi bayanta, ma'aikatan mall din suka bi bayansu da shopping bags din..


Bayan sun sanya masu kayan a boot din motar, agent ya bude mata car door din ta shiga ta zauna tare da kallon chief ya nutsu yana daddana wayar hannunsa, shigowa ciki agent din yai ya zauna a driver's seat ta mirror ya kalli chief.


 "Sir, we've completed the purchase, and the goods are in the boot."

 

Fuskarshi babu annuri Ya furta"Why didn't I receive a debit alert?


"Sir, grandpa ɗinka Ya hana su kar6i kudinka, ba yadda banyi da cashier din ba amma yaƙi kar6a yace baya son yaja ma kan shi" ta6e baki chief yayi kafin a hankalli ya dan juya suka hada ido da unaisah dake ta kallon shi, da sauri ta sunnar da kanta ƙasa cikin sanyin murya tace"mungode Allah yasaka da alkhai..." bata kare maganarba ya toshe mata bakin ta da yatsan hannun shi..idanunsu acikin na juna ko kyaftawa basayi wani irin kallo suke jefawa junansu hatta agent din dake driving dinsu sai satar kallon su yakeyi ta cikin mirror fuskar shi dauke da murmushi yajima baiga macen data dace da chief irin yarinyar nan ba, sun burge shi.


da sauri ta sauke idonta kasa ta kama yin yan kame kame kamar zata nutse kanta cikin cinyoyinta, zame yatsansa yai daga kan la66anta, laushinsu ba karamin fusgarshi sukayi ba, muryar shi tamkar tame  jin bacci ya furta"kada ki ƙara yi min godiya bana so" daga mashi kai tay"bazan ƙara ba"

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post