Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 54 Complete by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 54 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

Yar dariyar takaici ta yi, "Elder kenan, ka jima kana nuna min fin ƙarfi, wlh tun ranar dana gane asalin wa nene kai, na ji ka fita araina, wlh na tsaneka kamar mutuwa, babu abunda nake kwaɗayi da ya wuce inga bayanka, dan Allah ka mutu mana, na gaji ! na gaji !! da irin baƙincin da kake ƙunsa mini, wai kai wani irin mutunne? ko sau ɗaya baka ta6a jin nadamar irin zunubban da kake aikatawa ba? Na jima ina kokwanton anya kai mutunne? Saboda babu zuciyar imani a ƙirjinka... "

 Bata ƙare maganar ba, ya daka mata tsawar da tayi silar rikicewarta tuni tasha jinin jikinta, nuna ta yayi da yatsan shi, "Bansan a ina kika samu ƙwarin gwiwar gaya min magana cikin idona ba, koda yake dama haka kike da kafiyar tsiya, ke kin sani bada son raina na jefa ki cikin kurkukun nan ba, kece sila, shisshiginki da bin kwakkwafinki ne suka ja maki, naso mu dawwama acikin farin ciki amma kin 6ata komai, wallahi ba don son da nake maki ba da tuni najima da kashe ki, amma saboda ƙaunar da nake maki shiyasa na killaceki anan saboda kada ki tona min asirina..." 


Cike da taikaici ta yi murmushi haɗi da ɗan girgiza kai ta ce, "Ai ni tuni kajima da kashe ni, me kuma ya rage? Tsawon shekaru ashirin rabona da inga hasken rana, tsawon shekara ashirin rabona da inga wani dangina, dan Allah ka kashe ni in huta, na roƙe ka Ka kashe ni mana...!" cikin jin kunar rai ta faɗa.


Lumshe idanunshi yayi akan fuskarta tare da buɗe su, da wata irin siga ta jan hankali yace,


"Idan na kashe ki, kamar na kashe kaina ne, nafison in ma mutuwar zakiyi mu mutu atare."


"Elder kenan, makomarmu ba zata ta6a zama ɗaya ba, ni da nake so In mutu Cikin rahamar ubangiji, taya za kai min fatan mu mutu atare?"


Tuntsirewa ya yi da dariya, cike da tsana take kallon shi....


"Bazan bari ki 6ata min ranata ba, yau ina cikin farin cikin zagayowar ranar da muka kafa gidan kurkukun ƙaddara, ko murna baki tayani ba..."


Wani kallon rainin wayau ta jefa ma shi a cikin ranta ta furta, "In Sha Allah yau ce rana ta ƙarshe da zaku yi black night a duniya, Ubangiji Allah Yasa su kawo maku farmaki su tarwatsa tawagar azzalumai..."


"Me kika ce?" Firgigit ta kalle shi cike da fargaban kada ace Yaji ta, duk da ta dai san a zuciya tayi maganar amma tasan yana iya karantar abunda take saƙawa acikin zuciyarta.


"Kaji nayi magana ne?" Girgiza mata kai yayi.


"Ni zan Shiga fadata, ko zaki raka ni?" Banza tayi da shi, 


"Ki kula min da kanki." Bai tsaya yaji amsarta ba, Ya 6ace ma ganin ta..


Me ya faru bayan Giants sun tafi da Gabriella?


Tana ta kuka tana tirjewa, a haka suka miƙi hanyar komawa cikin Kurkukun da ita, adaidai zasu karya wata kwana kwatsam saiga Tsohuwa Inno ta fito daga fadar elders karaf idanunta suka hango mata Gabriella...


A sukwane ta dakata da yin tafiya ta zuba mata idanu, yarinyar da take nema ruwa ajallo sai gata yau Allah Ya haɗasu..


Dariyar mugunta ta saki mara daɗin ji kamar haniniyar jaki, A firgice Gabriella ta kai dubanta ga tsohuwa Inno jin sautin dariyarta, Lokaci ɗaya yanayin fuskarta Ya canza ganin matar da ta tsana fiye da mutuwarta.


Ƙarasowa Inno tayi gaban su da sandarta ta tsaya cike da shaƙiyanci ta ce, "Wanake gani kamar Gabriella? Yarinya mai ran ƙarfe, ashe rai kanga rai? dama saida raina ya bani baki mutu ba, Kina nan da ranki, kai! amma fa nayi mamakin tayaya akai kika rayu bayan tiyatar dana sa giant yayi maki? Wani mai imanin ne yayi jinyarki? 


Banza tayi da ita, ta6e baki Inno tayi tare da kallon giants din dake a ruƙe da ita, "A wace Bola kuka tsunto sharar nan"? Wannan kalma ta ƙona ran Gabriella, ta ƙulu sosai.


Ɗaya daga Cikin Giant ɗinne Ya ce, "Daga ɗakin Khala, Elder ne ya bada Umarnin mu dawo da ita cikin yan uwanta." Ta6e baki Inno tayi, "Dama nasani, duk cikin kurkukun nan babu mai zuciyar imanin da zai iya jinyarki in ba ita khala ɗin ba, amma fa na tayaki baƙin ciki, da kin mutu da kin huta."


Ta faɗa tana leƙen fuskarta, warin bakinta duk Ya cika hancin Gabriella, wani irin yunƙurin amai ta fara Ji..


Bin ta da kallo tayi daga ƙasa har sama, saboda tsabar fitsara hada sanya hannu ta ɗage rigarta ta tura kai tana leƙen gabanta don taga aikin da akai ma wurin, duk tayi shiru bata hanata ba...


Ɗagowa tayi fuskarta dauke da shu'umin murmushi ta ce, "Kin ɗinku da kyau, wuri fa yayi kyau, naji dadi kinga yau Manyan Baƙin mu zasuyi badago a kanki..." ta faɗa tana sakin dariya.


Ƙululun baƙin cikine Ya tokare makoshin Gabriella sai huci take kamar zakanya, kashe mata ido tsohuwa Inno ta yi kafin ta kalli giants din dake a ruƙe da Gabriella ta basu Umarnin su tafi.



Kamar jira take Giants ɗin subar wurin dama zuciyarta ta kawo wuya, aikuwa tayi wani irin kukan kura da iya ƙarfinta na karshe ta daka uban tsalle tayi zaman yan bori akan Tsohuwa Inno, kamar Allah ya aikota ta dinga gartsa mata cizo da yakushi tsohuwa inno ta dinga kokarin Kayar da ita ƙasa amma takasa, sai da ta kekketa fatar ƙwalƙwalin kanta, duk ta ciccisge mata yar hurhurar dake a kan, tayi ma kwallan kan rantali da akaifarta duk ya yi jaga jaga da jini...


Wa'iyazubillah! Wata irin kururuwa tsohuwa inno ta saki tare da jijjige jikinta silar hakan yasa Gabriella ta kundumo ƙasa timm! nan take Inno ta rikiɗa ta zama wata mummunar halitta mai razanarwa, gurnaninta kaɗai Ya isa ya rikita kwakwalwar mutun.


Da mugunta ta durfafi Gabriellah, a lokacin so tayi ta kasheta ta hanyar handameta, aikuwa ta watsa aguje ta nufi wata doguwar hanya mai duhun gaske, bin ta Halittar ta yi aguje duk inda ta taka sai floor ɗin gurin ya girgiza saboda girman halittar, gaba ɗaya Gabriella ta rude ta razana ta rasa ina zata boye kanta, don tasan muddin Tsohuwa Inno ta kamata Sai dai buzunta...


Saƙo da lungu ta dinga bi, tana tsaka da yin gudun ta faɗo cikin wani ke6a66en wuri mai tarin komatsai ga shi babu wadataccen haske,


Gurnanin dabbar da ta jiyo ne yasa ta furgice ta soma ja da baya, cikin rashin sani tana ƙara ɗaga kafarta ta taka wani wuri gaba ɗaya ƙasan gurin ya rubza da ita ta zurma cikin wani rami wanda bakomai ne a cikinsa ba face zallar jini mai ƙarnin gaske ga ɗoyi, shi wannan tafkin asalin samuwar shi daga ɗakin fiɗa ne na gidan kurkukun ƙaddara, jinin mutanan da suke feɗewane idan ya gangaro ta cikin pipe kai tsaye yake shiga cikin tafkin anan ya ke taruwa in suka tashi amfani da jinin zuwa suke su dibe shi a cikin tuluna.


Wa'iyazubillahi! kamar zata haɗiye zuciya saboda azabar ƙarnin da ya toshe ƙofofin hancinta, jinin ya mamaye jikinta Iya wuyanta ne awaje sai ihu take tana kokawar fitar da numfashin ta.


Ko da tsohuwa Inno ta faɗo wurin ta hango Gabriella tana ihu cikin jini, nan take ta Rikiɗa ta dawo ainihin suffarta ta mutane, wata irin mahaukaciyar dariya ta saki, ganin haƙarta ta cimma ruwa, Saboda zalunci maimakon tabarta haka sai da tayi mata sihiri ta ƙarasa nutsar da ita cikin jinin kanta ya shige gaba ɗaya, tasan bazata rayu ba, sai dai a fito da ƙasusuwanta in namanta ya gama zagwanyewa.


A bangaren Tsohuwa Khala Hankalinta Yaƙi kwanciya, saboda fargaba da zullumin abun da zai biyo baya in har su Garkuwa basu kawo farmaki ba, baiwar Allah ta kwallafa rai akan zuwansu, ta kasa tsaye ta kasa zaune har gaban madubin ɗakinta ta je ta zauna kan kujerar gabansa, tayi siddabarun da ta saba yi donta samu damar yin magana da shi amma bata ga komai ba a cikin madubin, nan fa hankalinta ya ƙara tashi ganin har dare yayi❗



_______☠️👹☠️BLACK NIGHT💀👹☠️_______



Ƙarfe Goma daidai agogon Gidan kurkukun ƙaddara ta buga, adai dai wannan Lokacin, Dubban shahararrun matsafa suka fara tururuwar fitowa daga masaukin su na gidan kurkukun ƙaddara, adaren ranar duk wata halitta dake bacci a cikin dajin Evil forest da kurkukun saida ta farka saboda sautin bugun ganguna da busar sarewa daya karaɗe ko'ina tamkar za'a fasa ginin saboda Yadda kiɗan ke tashi..


takaitaccen tarihin Daren Black Night, shidai wannan dare, ya samo asaline aranar da Elder Ya Ƙaddamar da gidan kurkukun ƙaddara, Dare ne mai daraja a gurin su, suna alfahari dashi, kuma suna ɗokinshi saboda dare ne na sharholiya, kowa zaiyi bushasha suci karensu babu babbaka sannan a daren suna ƙara ƙarfin tsafinsu, agurinsu kenan, amma agurin Prisoners Daren black night kamar guguwar annobace saboda tashin hankalin da suke fuskanta adaren, kada na cika ku da surutu bari mu leƙa muga meke wakana adaren Black Night❗❓   


Ɗaya bayan ɗaya matsafan ke fitowa daga masaukinsu, Wasu a hawa na ukun bene, wasu suna a hawa na biyu yayin da wasu suke a hawa na farko, kowani matsafi Ya ƙure kuri adakansa, ƙarshen wanka na kece raini, matsafan ma jinsi jinsi ne.



Tawagar matsafan yankin Asia ne a hawa na farko, sunyi anko shigar su kamar irinta kayan gargajiya launin jajaye na ƙasar China, ga wani dogon gemu har kan tulun tumbinsu, uban goshin su kamar jirgi ya yi asubanci, ga wani uban sanƙo dake gare su, idanuwan nan nasu mitsi mitsi kamar na kifaye.


A hawa na biyu kuwa tawagar Matsafan India ne, Sun buga adon su kamar malaman majami'u, wasu irin mutane ne masu ƙaton tumbi da manyan mazaunai burguza burguza ga wani uban rantali akawunan su, Munanan gaske, duk sun yi fentin ja da baƙi a jikin su, kwata kwata babu sutura a jikin su, zir suke haihuwar uwar su sai jan fentin da suka shafe jikinsu da shi, ga mutum mai ƙyanƙyami in ya kallesu sau ɗaya bazai sake marmarin kallon su ba.



Tawagar matsafan kurkukun ƙaddara, Su kuma nasu wankan wasu dogayen rigunane a jikinsu baƙaƙe har ƙasa suke ja, sun lullu6e kawunansu da hulunan rigunansu, sun rufe fuskokinsu da mask mai suffar ƙwarangwal.


Tawagar matsafan yankin Europe da America suma ba'a barsu baya ba, suma sunyi ankon su na kece raini.


Gaba ɗayansu sun hallara a tsakar kurkukun, ƙwansu da ƙwarƙwatar su ko'ina ka kalla sune birjik.


Babu masaka tsinke, saboda shagalin yau, ko'ina na kurkukun saƙo da lungu wasu irin dakarun Giants ne majiya ƙarfi ke sintiri sai mazurai suke, Jira suke kawai suga badaidai ba su aiwatar da aikin su.


Ko sauro bai isa Ya ratsa kurkukun ba batare da sun gan shi ba, hatta dakin maduban tsafinsu makil yake da giants sun kasa sun tsare suna kallon komai dake wakana a kowace kusurwa ta kurkukun da dajin Evil forest don tabbatar da tsaro, duk da basu sama ransu wani zai kawo masu farmaki ba, saboda ba'a ta6a gigin yi masu kutse ba, shiyasa suka daɗe suna sheƙe ayar su.


Surutunsu Ya karaɗe ko'ina, da wani irin Yare mara daɗin Ji suke magana cikin harshen su na matsafa, sai raha suke suna hira cikin nishaɗi.


Daga kan ground floor ɗin gurin wani haɗaɗɗen red carpet ne aka shimfiɗa tun daga fadar mai girma Elder har zuwa ƙarshen bango inda aka ƙawata wurin kamar karagar sarakuna, ga wasu jigunannun Armchairs guda shida an ƙawatasu da kayan ado.


Daga can gefe ɗaya a tsakiyar Ground floor din wani zungureran Table ne ɗauke da tsadaddun kayan shaye-shaye masu haɗarin gaske ga tulunan Jini da aka girke kan table ɗin, ga farfesun nama cike da farantai nau'ika daban daban irinsu, farfesun naman ɗawisu, na naman shanu kai hada farfesun yan cikin mutun, soye soye kala kala da kayan maƙwalashe.


Yayin da makaɗan suke ta yan kiɗe-kiɗe da raye rayen su, wasu gungun yan rawa manyan mata masu dirin jiki suka fara fitowa Kwata kwata babu sutura a jikinsu zir suke haihuwar uwarsu, wata irin rawar qugu sukeyi mai jan hankali, nan fa matsafan suka fara washe haƙora suna kallon su..


Gaba ɗaya sun ƙagara a fara shagalin, fitowar Elders kaɗai suke Jira..



Idan muka koma cikin fadar Elders kuwa, tattaunawa su ke yi a tsakanin su, Elder yana a zaune kan kujerar mulkinsa yayin da sauran Elders din suka kewaye shi suna a zaune kan carpet din fadar, Gaba ɗayansu sunyi shiga ta alfarma irin ta mai girma Elder, sun rufe ko'ina na jikin su baka iya ganin koda akaifar su ce, su shida ne cuf ba ƙari.


Cike da nishadi Ya soma magana Yana dubansu, "Me ya rage mana"? Ya faɗa yana bin su da kallo..


"Babu komai Elder, Mun riga da mun toshe kowace Hanya da za'a Iya kawo mana farmaki, dama duk burga ce, wane yaro! rijiya ay ba wurin gaɗar makaho bace, ƙananun kwarine su, in banda ma hauka ina su ina ja da mu? sunyi tunanin sauƙi ne Ja da mu, ko Dajin Evil forest basu isa su ƙetare ba, mune masu ƙarfin iko, da izinin mu komai ke wakana,  in muka so Da kalma ɗaya zamu shafe babinsu mu mayar da su tur6aya!"


Gaba ɗaya suka tuntsire da dariyar shaƙiyanci, bayan sun tsagaita da yin dariyar Elder Ya dubi wanda yayi maganar Jan Le6e, "Na ji daɗin bayanin ka.." Ya faɗa tare da maida dubanshi kan Elder din dake zaune gefen Jan Le6e ya ce, "Mutumina Jan wuya, Ko akwai labari? Ko kuwa sai mun sha mun bugu don nasan halinka da miskilanci kafi sakin baki idan ka hau kan network..." Cike da shaƙiyanci ya furta, "Musamman in akwai mata da giya anan linzamina yake kwancewa..." Dariya suka saka gaba ɗaya....


"Baka da matsala mutumina, yau ranarmu ce, saika za6a ka darje," Ƙasaitacciyar dariya jan wuyan ya saki.


"Jan kunne na ji ka yi shiru baka ce komai ba"? Ya faɗa Yana duban shi.


Muskutawa ya yi ya gyara zaman shi, "Elder, Ni bani da abun cewa, Hankalina Ba a kwance Yake ba, ban ta6a tsintar kaina a yanayi na jin faɗuwar gaba irin na yau ba..." gaba ɗaya suka maida hankali kan shi.


Da kakkausar Murya wani mai zafin rai a cikinsu wanda suke kira jan harshe Ya ce, "Wannan wani irin zancen banza ne? Ka kuwa san me hakan Yake nufi? Faɗuwar Gaban Elder yana nufin mummunar ƙaddara zata Iya afka mana, tun wuri Ka dakatar da zuciyarka, ba'asan Elder da raunin zuciya ba..." 


Yana ƙare maganar Jan Wuya Ya ce, "Ka gafarce ni, kaima kayi kuskure a maganarka Jan harshe, Elders sunfi ƙarfin mummunar ƙaddara, ita kanta ƙaddarar tsoron mu take ji, shiyasa bata ta6a gigin afka mana ba..." Da gadara suke magana.


(Duniya budurwar wawa, Wanda Ya 6ace Ya 6ace.....)


"Jan wuya, kai ɗin na dabanne, namijin duniya, wanda bai ta6a karaya ba, ina son ƙwarin gwiwarka mutumina..." Ya faɗa tare da yi masa alamar jinjina da babban yatsansa, kafin Ya dubi Jan Kunne "Kai kuma, kada na kuskura na ƙara jin ka ambaci faɗuwar gaba, nasan me ke damunka, da zarar kaga mata masu manyan mazaunai zaka wartsake..." Dariya suka saka gaba ɗayan su.


Kafin wani ya ƙara furta kalma a cikinsu, Evil Giants masu ƙirar samudawa har su Goma suka kewaye kofar shiga Fadar...ɗaya cikinsu mai wata irin ƙatuwar murya ne Ya ce, "Elders baƙi sun hallara, lokacin shagali ya yi, zamu iya tafiya..." jinjina kai Elder yayi tare da miƙewa suma sauran Elders din suka Miƙe cikin takun dattako suke tafiya akan jan carpet din da aka shimfiɗa masu, hannuwan su ruƙe da sandunan su na alfarma.


Lokacin da suka 6ullo ta ground floor ɗin makaɗan dake kiɗa suka ƙara kaimi gurin buga gangunan kamar zasu fasa su, ga wata daddaɗar busar sarewa dake tashi, wani irin kirari suka fara yi masu suna kurantasu da hura masu kai har wani rausayawa suke yi alamar kirarin yana kai masu karo.


Gaba ɗaya Hankulan matsafan Ya dawo kan Elders, Taurari masu haskaka duniyar matsafa, kowa burinsa ya ga Elders, musamman sababbin matsafan da basu jima da shiga harkar ba, saboda wani irin farin jini ne da su, sun shahara a fadin duniya.


Cikin girmamawa matsafan suke miƙo gaisuwa kamar zasu durƙusa masu saboda biyayya....bayan Sun ƙarasa gurin da aka ƙawata masu, kowan nan su ya zauna kan armchairs ɗin da aka tanadar masu.


Ɗaga hannu Elder ya yi cikin sauri masu buga gangar da masu raye rayen suka dakata ...


Duk faɗin girman gurin idan ya yi magana sai kowa Yaji shi kuma a hankali yake yin ta cikin nutsuwa.


"Ina yi ma kowa barka da zuwa, haƙiƙa bazan Iya misalta farin cikin da nake a ciki ba na ganin kowannanku, abun alfahari ne a gareni, ace waɗannan dubban mutanan saboda ni suka baro muhallinsu suka zo don su taya ni murnar zagayowar ranar dana Kafa GIDAN KURKUKUN ƘADDARA....."


 Ya ɗan dakata Yana bin matsafan da kallo tun daga kan hawa na Uku har izuwa na farko, sun kasa kunne suna sauraron shi..


"A daren yau, muna taya juna murnar nasarorin da muka samu, bamu ta6a faɗuwa ba, dukkan abunda muka sa gaba sai mun cimma shi, ina fata abokan harkar mu zaku tayamu murna." Sowa suka sanya da ƙarfi suke amsa mashi da, "Yeho! Yeho!! yehoo!!


Gyaɗa kai ya yi kafin ya ɗaura da cewa, "Kamar yadda kuka zo domin mu kuka faranta mana, muma zamu faranta maku, wannan yasa muka tanadar maku shirye shiryen da muka saba yi A kowane black night..."


Bayan Elder Ya gama kora jawabin shi, Jan Harshe Ya ɗaura da nashi...


"Gasar da zamu gabatar, faɗan gwada karfin iko ne, team da suka zo na ɗaya suka yi nasarar lashe gasar, zamu basu santala santalan yan mata har guda goma sha biyar, waɗanda suke tsaka da Yin jinin al'adarsu, don su biya buƙatarsu da su, bayan haka zamu basu matasan maza goma sha biyar suma su biya buƙatarsu da su..." Wani irin ihu matsafan suka sanya har sun fara saƙa buri akan suyi nasara saboda tsananin kwaɗayin mace mai jinin al'ada su ke yi..


Dakatawa yayi da yin bayanin, kafin ya ɗaura da cewa, "Tawagar da ta zo a mataki na biyu, mun tanadar masu jarirai goma sha biyar, tare da Tulunan jinin al'ada da muka tsuma, bayan haka zamu basu mata masu ɗauke da juna biyu su yi amfani da su sannan su sha jinin abunda ke acikin su..." 


Tunkan Ya ƙare maganar matsafan suka sake sheƙewa da shewar Murna.


"Tawagar matsafan da suka zo na uku, mun tanadar masu sabbin gawawwakin da muka tsuma, sannan zamu basu sassan jikin fursinonin mu." Wani irin ihun farin Ciki matsafan suka saki, su fa yau shar kakarsu ta yanke saƙa...


"Saura waɗanda basu yi nasara ba, suma ba zamu barsu hakanan ba, kamar yadda muka yi alkawari zamu faranta ma kowan nan Ku...."


Yana ƙare maganar Ya ɗaga hannu nan take masu buga gangunan suka ci gaba da gashi.


________________________________________✍️



Shigowa ta yi cikin katafaren Hall din da suka tara za6a66un prisoners da suka tanada saboda faranta ma baƙin nasu.


Hall ne mai faɗi da tsawon gaske ta cikin shi akwai ƙofofin ɗakunan dake a jere jikin bangonshi, Yana da dogayen benaye, a wani sashe na hall ɗin akwai wasu tsoffin rijiyoyi da suke a garƙame da murafen ƙarafuna, ga wasu kaskwayen wuta dake ci, hall ɗin ya kasance inda suke bada horon zama Giants zanunnukan dake a jikin bangon hall ɗin kadai ya isa ya razanar da mutun..Anan suke killace duk wani abu da suka tanada saboda baƙin su.


Tana ƙarasa shiga ta iske female giants ɗin dake shiryasu su ukku cikin kakinsu. 


Sun tu6e masu uniform dinsu, saboda basu buƙatar su shiga da su gurin taron da sutura, jikinsu sai kerma da kakarwa yake yi, daga ka kalli idanunsu zaka ga tsantsar tashin hankali, a ƙalla prisoners ɗin sun kai su arba'in da wani abu.


Female giants din na ganinta suka russina tare da gaishe da ita, ko kallo ba su ishe ta ba..



Zama tayi kan kujerar dake fuskantar su tana ƙare masu kallo, bayan ɗan lokaci ta kai hannu ta kware ƙasan rigar ta, tsamurarrun cinyoyinta ne suka bayyana,wani ƙyalle dake naɗe da ɗaya daga cikin cinyoyin nata ta fara warwarewa, Ya ilahi! wani irin uban wari ne ya buso yadda kasan gunyar ƙwai ta fashe lokacin data ƙarasa kwance wurin, wani irin ciwo ne ya mamaye wurin har wurin can ƙasanta kamar dai gyambo, da ƙyar in baza'a rasa yan ƙananun tsutsotsi a wurin ba, gyara wurin ta shiga ƙoƙarin yi,


Hankulan Prisoners din ba ƙaramin tashi ya yi ba, yunƙurin amai suka soma yi sakamakon ɗoyin ciwon da ya bugi hancinan su, aikuwa da kakkausar murya tace, "Duk ɗan iskan da ya kuskura ya yi amai a gurin nan sai na sa ya lashe shi da harshen shi...!" 


Waro idanu waje suka yi da sauri suka toshe bakunan su da tafukan hannayen su...


Tsautsayi ne Ya ritsa da wasu ƴan biyu maza dogaye sirara da su, irin masu ƙyanƙyamin nanne, duk yadda suka so su hana aman fitowa daga bakinsu saida ya kubce masu aikuwa suka fara amayar da abunda ke cikin su.


Murmushin mugunta tsohuwa Inno ta saki, "Ku ko wani tsautsayin ne Yaja maku yin amai?" Hankali a tashe suka fara yi mata magiya akan tayi haƙuri, Tsawa ta daka masu tuni suka sha jinin jikin su, da yatsa ta nuna masu wurin, "Ku zo ku sha daɗi.." Fashewa suka yi da kuka suna kallon sauran yan uwan su, wani irin tausayin sune Ya kamasu.


"Kada kubari in maimaita abunda nace!!" Ba yadda suka Iya, sun riga da sun san bala'en da zai biyo baya idan suka bijire mata..


Cike da jin shakkarta suka nufe ta, zuciyoyin su na tashi haiƙam suka durkusa kan gwiwowin su agabanta, Idanun su na kallon tashin hankali!



Da yatsa ta nuna na tsakiyarsu, "Kai zaka fara, Kafin na buɗe idanuna kayi hanzarin kafa bakinka..." Tana faɗa ta kulle idanunta.


Yawu Ya haɗiya, cike da kyankyami yake kallon wurin ga azababben warin yafi yawa da suka matso gab da ita gaba ɗaya ya kanainaye hancinsu..


Tsohuwa Inno har wani murmushin mugunta take saki jin hucin Numfashin su a jikinta.


Kwatsam! ba zato ba tsammani, kamar daga sama taji an buga mata wani abu mai azabar zafi a wurin, bugun har agaban ta.


Wata irin zabura ta yi ta miƙe tsaye, cikin ruɗu ta zare tsoffin idanunta akan Giant din dake tsaye a gabanta, hannun shi ruƙe da Ƙatuwar guduma ta ƙarfe.. tuni Jini Ya 6alle mata kamar pipe din ruwa ya fashe...


A tsananin ruɗe take kallon shi kafin ta dubi yan ukun dake tsaye bayan shi..da sauri ta dubi female giants din dake a wurin, wata irin razana ta yi ganin gawarwakinsu baje a ƙasa, Cike da al'ajabi ta furta, "Kai! wanene kai??"


*"GARKUWAR FURSINONI"*


 Ya faɗa tare da sanya hannu ya zare Mask ɗin fuskar shi, Tsabar mamaki da al'ajabi hadi da razana ya hana ta furta kalma, kusan suman tsaye tayi ganin Garkuwar Kurkuku, Zance ya 6aci! daƙyar ta haɗiye al'ajabinta, Muryarta na rawa ta furta, "Garkuwarmu! Kai nake gani dagaske ba mafarki nake ba?tayaya ka shigo kurkukun nan eye? Ka dawo gurinmu ne? Ni dama nasan bazaka Iya rayuwa batare damu ba...." Sai sambatu take yi mashi kamar wata zararra, abu biyu ya haɗe mata ga azabar zafin da gabanta keyi mata.


Wani ƙasƙantaccen Kallo Ya wurga mata mai tattare da ƙyama, cike da ƙwarin gwiwa ya furta, "Na dawo, amma ba a matsayin Garkuwarku ba, a matsayin garkuwar fursinoni." jikinta na kerma kamar mazari kafin ta furta wani abu ta jiyo sautin takalmansu ɗaya bayan ɗaya suke shigowa cikin Hall ɗin, ba zaka ta6a gane ba giants din kurkuku bane saboda kayan jikinsu sak irin Na giants ne.


Ɗaya bayan ɗaya suka soma cire mask din fuskarsu, waro idanu waje tsohuwa Inno tayi Ganin baƙin Fuskoki a gidan Kurkukun Ƙaddara.


Kallo ɗaya Chief Owais ya yi ma Prisoners din dake a gurin ya yi saurin kawar da idanun shi, Haka shima Big guy kasa jurewa yayi ganin babu sutura a jikin su, Taj da zuciyarshi ta gama karaya da tausayinsu ji yayi kamar ya fashe da kuka, a ranshi ya ayyana wai anan yarsa Angel tayi rayuwa har na tsawon shekaru, Ya salam!!!.


 Salsabeel kuwa tun shigowarshi idanun shi na akan Inno wani irin kallo mai cike da tsana yake jefa mata....



"Su wanene ku!.." bata ƙare maganar ba, sakamakon wani zazzafan Mari da Chief Owais Ya kwasa mata har saida wuyanta ya nemi jirkicewa, Kafin ta ɗago Ya daddage ya sakar mata mahangulba kan mummuƙenta...gaba ɗaya ta kife ƙasa a susuce ta furta,"kai, kai, kai, kai....."


Prisoners din dake a gurin gaba ɗaya sun ruɗe sun rasa gane su wanene wadannan baƙuwar fuskar? shin sun zo ne da niyyar taimakonsu? ko kuwa suma mugaye ne..?


"Kai ku maida Kayan ku" Big guy ne ya faɗa ba tare da ya kai idonshi kan su ba, jikinsu na kerma suka ɗauki uniforms dinsu dake yashe kasa suka shiga zirasu a jikin su.


Ƙululun baƙin ciki ne Ya tokare makoshin tsohuwa inno, tun da take wani ɗan adam bai ta6a gigin ta6ata ba da sunan bugu sai yau da Allah Ya haɗata da Chief, yunƙurawa tayi ta miƙe tana layi ta soma rarraba idanunta akan Salsabeel da Danish.


Tana huci ta ce, "Maciya amana! saina tona maku asiri gurin Elders" 


Ta faɗa tana kokarin Yin sihiri don ta 6ace sai dai wani iko na Allah kamar an ɗauke mata sihirinta, A ruɗe take kallon hannayenta ganin sun ƙi tasiri.


"Kina mamaki ne?" Danish ne ya faɗa tare da ɗaga mata gira, takaici ya ishe ta..


"Wai dama haka matsafan suke, munana, gasu ƙazamai, gwanin ban ƙyama." Fuska a yamutse Big Guy ya faɗa tare da watsa mata yawu kan fuskarta ya ce, "Daƙiƙiya, dama karfin naki na sihiri ne, yanzu da babu shi taya zaki faɗa ma Elders dangane da zuwan mu? Bayan mun riga da mun mamaye gidan kurkukun da dakarun sojojinmu, munyi basaja mun saje da Giants ɗinku, Yanzu haka ɗaya bayan daya sojojinmu suke bi suna yi masu kisan mummuke batare da sanin ku ba."


Dafe kai tsohuwa inno tayi da hannayenta ta fara jijjiga jikinta tana kokarin ta rikiɗa nan ma dai abun ya ci tura.


Batai aune ba Sai dai taji safkar wuƙa a makoshinta, Big guy ne ya farke ta har saida ya dire ƙasa, Jini ya dinga tartsatsi kamar pipe din ruwa ya fashe, gaba ɗaya gangar jikinta ta zube ƙasa tana bullayi ta dinga sakin wata irin kururuwar azaba har rai ya yi halin sa....



"Har yanzu nagaza yarda da abunda idanuna suke nuna min! Ina jin abun kamar a mafarki ashe dagaske komai ke faruwa!" cikin jin ƙunar rai Chief Ya faɗa kafin Ya dubi Sojojin dake a bayansu ya ce, "Ku tafi da yaran!" Cike da bada Umarni Chief Ya faɗa.


Kuka suka fara Yi masu jikinsu sai kakarwa yake yi, sun yi zaton cutar da su zasu yi, fahimtar hakan yasa Taj yi masu bayani ya ce sun zo ne don su taimakesu su ba masu cutarwa bane.


Waro idanu waje suka yi, wlh alƙalamina bazai Iya mistalta irin yadda suka yi mamaki da al'ajabin jin za'a taimaki rayuwarsu ba, batare da 6ata lokaci ba, huɗu daga cikin Isod soldiers dinsu suka tafi da yaran..


Duk wannan abun dake faruwa Babu wanda Ya san da zuwan su cikin kurkukun, sai mutun ɗaya wato tsohuwa Khala.


Saboda sautin bugun gangunan da makaɗa suke yi Ya hana Matsafan su jiyo sautin abun da ke faruwa..


Ajiyar zuciya suka sauke batare da jin fargaba ba, suka fito daga Hall din cikin tafiyar sanɗa suka nufi wata doguwar hanya mai kwana-kwana..


Duk Giant din da ya ankara dasu kafin yayi wani yunƙuri tuni suke fille kanshi da adda, Kisan Gilla su ke yi masu...



(SHIN TAYAYA AKAI SUKA SHIGO GIDAN KURKUKUN ƘADDARA?)


Bata nufi ko'ina ba sai hall ɗin da madubban tsafinsu suke, tana shiga ta iske giants din dake kan duty, tasan muddin Su garkuwa suka ƙaraso sune na farko da zasu fara kawo masu cikas saboda suna kallon komai dake wakana a cikin kurkukun ƙaddara da kuma dajin evil forest, gyaran murya tayi masu, cikin girmamawa suka gaishe da ita, tace meya hanasu shiga filin taro? Bayan yau rana ce mai mahimmanci da buƙatar kowa dake a kurkukun ya halacci wurin shagalin, Giants din su ka bata amsa da ba'a basu umarnin subar aikin su ba, tsohuwa khala tace a matsayinta na matar Elder tana mai umartarsu da su aje aikinsu, suje suma ayi shagalin da su, ba suyi mata musu ba, saboda sun san wacece ita, kuma Elder ya gargaɗesu akan suyi mata biyayya sau da ƙafa, in har ta buƙaci wani abu kada suyi mata jayayya su dauka kamar shi ne ya basu umarni, tuna wannan yasa Giants din suka bar bakin aikin nasu.


 Murmushi Tsohuwa khala tayi, tana ganin fitarsu, ta bi madubban tsafin ɗaya bayan daya ta jefar da su gaba ɗaya suka faffashe.


 Fitowa tayi daga hall din tana cikin tafiya cike da fargaba, kwatsam ta hango wasu gungun matsafa a cikin baƙinsu kusan su takwas sun nufo wurin kamar dai suna ƙarewa ginin kallo ne, gyaran murya ta yi masu da sauri suka dubeta, fuskarta da fara'a ta nufe su bayan sun gaisa ta gabatar masu da kanta a matsayin Matar Elder, sai faman washe baki suke yi suna ƙara gaishe da ita tace masu in ba damuwa su biyota zata nuna masu wasu bangarori na kurkukun tasan zasu so su gani.

Basu kawo komai a ransu ba, suka bi bayanta ta nufi wani ɗaki da su, suna shiga ta datse ƙofar a ruɗe suka kalle ta ganin ta rufe ƙofa, kamar sun fara zargin wani abu, sai dai kafin su gano hakan Tsohuwa Khala ta yi hanzarin zare ƙaramar wuƙarta gaba ɗaya ta kashesu, ta zuƙunna ta cire kayan dake a jikinsu dama shine abun da take so..



6acewa tayi, bata dira a ko'ina ba sai a cikin ɗakinta, ta jefar da kayan saman gadonta kafin ta kuma 6acewa ta bayyana a wani ke6a66an guri inda Danish ya faɗa mata ta nan zasu biyo idan suka ƙaraso.


 Tana tsaye hannunta ruƙe da sandar ta, zuciyarta cike fal da zullumi, Allah Allah take su ƙaraso kamar ta fashe da kuka saboda bugun barazanar da zuciyarta ke yi mata, ta aikata 6arna ba kaɗan ba, har ta fidda rai da zuwansu zuciyarta ta fara raya mata ta kashe kanta kawai tun kafin Elders su ankara da 6arnar da tayi masu.


A lokacin da bata yi tsammani ba, ta fara jin motsi ta saman ceilling din da take, A hanzarce ta kalli silin din ta sauke idanunta kan wasu tsofaffin tagogine dake a kulle jikin shi.


Cike da sa rai take kallonsu, Unexpectedly taga Murfin windows din na motsi wlh tsabar farin ciki bata san sa'adda takai goshinta ƙasa tay sujjada domin nuna godiyarta ga Allah, tunkafin ma ta tabbatar in su ɗinne, Kafin ta ɗago daga sujjadar kunnuwanta suka jiyo mata ƙarar 6allewar murfunan tagogin, a zabure ta miƙe tana kallon kafafuwansu, ɗaya bayan ɗaya suka fara dirowa ƙasa, kamar ana jeho su.


Dariyar farin ciki ta saki duk da mask din dake akan fuskar Danish hakan bai hana ta gane shi ba, shima yana ganinta ya nufeta gaba ɗaya ta rungumeshi kamar zata maida shi cikinta, kai ƙarshe ma sai ta fashe mashi da kuka, cikin shesshekar murya ta ce,"Alhamdulillah, nagode ma Allah da ya nuna min wannan ranar da raina, har na fidda rai da zuwanku.."


 Ta faɗa tare da raba jikinta daga na Danish ta dubi sauran sojojin dake atsaitsaye ga wasu dake ta durowa ƙasa.


"Khala" Salsabeel ne ya ambaci sunanta, bata gane shi ba saboda mask din da ya rufe fuskarshi, cikin sauri ya matsa kusa da ita, ta rungumeshi nan ma ta kuma fashewa da wani kukan farin ciki, Allah abun godiya..


Bayan ta raba jikinta daga na Salsabeel, Danish ya gabatar mata da Chief Owais, wanda tun da ya duro hankalinsa ke akan ginin yana mai jinjina girmansa, amma lokacin da kunnuwansa suka jiyo mashi muryar Khala da ruɗu ya tsayar da idanunsa akanta, kamar yadda take kallon shi haka shima yake kallonta, muryarta na rawa ta furta, "Owais, kaine ka girma haka?" Tayi zaton a cikin zuciya ta yi maganar, gaba ɗaya sojojin sun ɗan ruɗe da jin yadda tayi maganar kamar tasan shi, shi kanshi Chief din ya ruɗe da jin muryarta kamar yasanta, sai dai ya kasa gane wacece saboda ta rufe fuskarta da tukunkumi.


 Idanunta kaɗai suke iya gani...

Bai aune ba, yaji ta cakume shi da hannayenta biyu ta rungume shi sosai fiye da yadda ta rungume su Salsabeel...Allah kaɗai yasan me take ji acikin zuciyarta..


Idanunta cike tab da kwalla, ta ɗago tare da kallon su,


"Ku kaɗai ne"? Ta faɗa ganin kamar sun gama shigowa kuma duka basu fi su hamsin ba,


Salsabeel ya ce, "Ba mu kaɗai bane, akwai sauran sojoji sama da ɗari biyar, suna akan hanyar shigowa." Ajiyar zuciya ta sauke, still idanunta akan Chief Owais, duk yasha jinin jikinshi da ganin irin kallon da tsohuwar take yi mashi,


"Ina yi maku barka da zuwa Gidan Kurkukun ƙaddara, a yanzu haka sun fara gudanar da shagalin Black Night basu san komai dake faruwa ba, saboda na toshe duk wata hanya da zasu iya ganinku ta madubin tsafin su, sannan akwai tanadi da nayi maku, ku biyo ni."


 Ta fada tare da juyawa suka bi bayanta, har suka isa ɗakinta basu ci karo da kowa ba.


Bayan sun shiga, Ta umarce Salsabeel da Danish da su fiddo kayan dake a karkashin gadon ta..


Bayan sun fiddo Buhunhunan da akwatinan ta ce, "Makamai ne acikinsu, a gidan kurkukun nan ake ƙera su, na daɗe ina tara su a 6oye saboda burin da nake dashi na ganin na kawo ƙarshen zaluncin su." 



Ta ɗan dakata tana mayar da numfashi kafin ta daura da cewa, "Makaman dake a hannunku ba za su yi tasiri akan su ba, amma in har kukayi amfani da makaman nan cikin sauƙi zaku kashe su"


 Farin Ciki ne Ya cika su, a hanzarce Salsabeel da Danish suka kwance buhunhunan, sun yi mamakin ganin yawan makaman, Wuƙaƙe ne da adduna, harda takubba da kibiyoyi, ga gatari da manyan gudumomi, nan kowan nansu ya ɗauki makamin da ya kwanta masa arai, bayan sun kammala ɗauka, ta ce, "Ku fara kokarin ceto rayukan fursinoni dake a ciki kafin su ankara da shigowarku, Danish da Salsabeel kuyi masu jagora zuwa daƙunan da fursinoni suke." suka amsa mata da toh.


Ta ƙara da cewa, "Duk yaran da kuka taimaka, ku kawosu nan, zan taimaka masu su fita daga kurkukun..." 


With respect suka amsa mata da toh.


Akwatinan ƙarfen ta nuna masu, "Kakin giants ne a ciki, na tanadar maku sune saboda kuyi 6adda kama ku saje da su, duk da naga kakin ku sunyi shige da nasu."


Ta kuma nuna masu kayan Matsafan da ta kashe, "Ga wasu kayan nan ma."


Big guy yace, "Ba dukkanmu keda irin kakin ba, akwai sauran tawagar sojojin da zasu ƙaraso, in yaso sai wasu daga cikinsu suyi amfani da kayan." Jinjina kai ta yi, "Hakan yayi, zaku iya tafiya, Ina yi maku fatan nasara" Har cikin ran su sunji dadin taimakon da tsohuwar tayi masu, yaune karo na farko da suka fara ganinta amma ta kwanta masu a rai.


(Kunji yadda akai suka ƙaraso Cikin gidan kurkukun ƙaddara)


Suna cikin tafiya suka ci karo da wani bene mai kanannaɗa, Kwata kwata babu fargaba a tare da su, suka hau benen ya 6ula da su cikin wata hanya mai tarin kofofi, har zasu gifta ta wani ɗakin kwatsam wani gabjejen Giant ya fito sanye da lab coat fara a jikin shi gaba ɗaya suka sha jinin jikin su..


Da farko da ya kallesu yaso ya ruɗe amma sai ya ji a jikin shi ba Giants din su bane.


"Su wanene Ku?" Da wata irin ƙatuwar murya ya yi maganar, Yan hanjin cikinsu ne suka kaɗa aka rasa wanda zaiyi mashi magana acikin su..


kamar yaso ya ɗago su amma sai yayi azan daga cikin baƙinsu ne da suka zo.


Ƙarfin Hali Chief ya yi wurin furta, "Daga cikin baƙin kune, muna ƙarewa ginin kallo ne" Maraba ya yi masu tare da nuna masu ƙofar dakin da ya fito ya ce, "Ɗakin fiɗa ne, zamu iya shiga ciki idan kuna neman ƙarin bayani dangane da yadda muke gudanar da aikin mu."



Ya faɗa tare da buɗe kofar dakin ya shiga suka bi bayanshi, sun yi matuƙar girgiza da ganin fursinonin dake a kwance kan gadajen ɗakin, Hada mata masu ciki, jikinsu sanye da fararen kaya, Ga wasu gungun Gigantes medici dake tsaka da yin aikin fiɗa a gaban gadon fursunan da suka farke cikin shi, har sannu da aiki suka yi masu, giant doctor din da ya shigo dasu ya gabatar dasu ga sauran yan uwansa likitoci kafin yace masu su ƙarasa ciki, Ya nufi gaban wasu manya-manyan furizozi Ya bubbuɗe su, sun razana sosai da ganin sassan jikin mutanan da suka feɗe masu yawan gaske..


Hankulansu sun tashi matuƙa sai dai basu yi gangancin da zai sa a gano su ba, bayani ya fara kora masu game da yadda suke feɗe mutun su cire sassan jikin shi da yadda suke amfani da shi har safarar sassan suke yi zuwa wasu ƙasashen su siyar da su.


Chief da Big Guy sun harzuƙa matuƙa, jikinsu sai tsuma yake yi saboda tsabar fusata kamar su rufe shege da bugu.


Kwatsam yana tsaka da kora masu bayani Taj ya yi su6ul da baka gurin furta, "Amma dai baku da imani" kaitsaye maganarshi da dira cikin kunnan Giant doctor din.


Nan take ya dakata da kora masu bayanin da tsantsar ruɗani Ya furta,"Who are you?" Shiru suka yi, hakan ya ƙara ƙarfafa zarginsa akan su.


Wata irin gigitacciyar tsawa ya daka masu tamkar zai fasa dodon kunnansu da karfi ya ce,"baku ji ina tambayarku bane? Su wanene ku huh?" Maganar da yake yi ce ta janyo hankulan sauran Giant doctors

din dake aikin fiɗa, suka ajiye tiyatar da suke yi gaba ɗaya suka zagayesu kamar zasu rufe su da bugu, safunan hannayensu jaga jaga da jini..


Jin sunyi shiru sun ƙi basu amsa ne yasa ɗaya daga cikinsu ya kai hannu zai cire Mask din dake akan fuskar Chief, bai kaiga ƙarasa cirewa ba, Danish Ya zaro addarsa azafafe Ya datse hannunsa ya 6alle biyu jini ya dinga tartsatsi, koda ganin hakan sauran giants ɗin suka harzuƙa matuƙa, suka afka masu faɗa ya kaure atsakanin su, sun ci wahala kafin suka yi nasarar kashe su gaba daya suka zubar da gawarwakinsu akan floor. 


Sai haki suke suna nishi, Big guy ya dubi Taj da ya dafe cikin shi, "Next time kada ka ƙara maimaita kuskuren da ka yi, yanzu da ka ja mun rasa rayukanmu." daƙuwa Taj ya yi masa batare da ya furta kalma ba.


Fursinonin dake a kwance kan gadajen suna ganin abunda ke faruwa saidai sun kasa tashi zaune saboda alluran da suka banka masu sun kashe kuzarinsu, kwayar idanunsu ce kadai ke motsi..


"Ya zamuyi dasu"? Big guy ne ya tambaya.

Salsabeel Ya dubi Danish, "ka yi wani abu pls" duk suka maida hankali kanshi, shi kadai yasan me ya yi masu sai gasu sun miƙe kan ƙafafunsu.


Basu tsaya 6ata lokaci ba, wasu daga cikinsu suka tafi da fursinonin...


Fitowa sukayi daga ɗakin fiɗar, Suka faɗa dakin dake akusa dashi, nan fa suka ga abun da ya ƙara ɗaga hankulansu, jarirai suka gani a cikin containers, kamar bakwaini gwanin ban tausayi...Taj har ƙwalla saida ya zubda masu, Big guy ya ce, "ya zamu yi da su?"


"Dan Allah mu taimaka masu, kada mu barsu anan" Taj ne ya faɗa.


Salsabeel ya bashi amsa da, "Bazai yiwu ba, don ta yanzu, mu barsu kawai Allah yana atare da su." 


Fucewa suka yi daga ɗakin suka shiga ɗakin dake a gaba, rasss! gabansu ya hau faɗuwa ganin ɗarurrukan kwarangwal na mutane sagale jikin igiyoyi ga wasu nan zube a ƙasa har jikin bangon ɗakin ko'ina su ne na mutanan da suka kashe, wa'iyazubilla zuciyoyin su sun karaya ba kadan ba. Wata shari'ar dai sai A lahira wallahi.


Kusan zagaye kurkukun suka yi saƙo da lungu suka dinga shiga, sune har cikin treatment rooms din kurkukun, anan suka ga majinyatan fursinonin da suka kwantar, sun ci baƙar azaba a hannun masu jinyar su wurin yin faɗa dasu, da ƙyar suka kashe su kafin suka ceci majinyatan suma.


Saida suka gama kwashe fursinonin, kafin suka dawo baya, har sun kusa 6ula ground floor din da ake shagalin Chief Ya dakata da yin tafiya, kallon shi su ka yi, duk da basu san me ya hana shi cigaba da yin tafiyar ba, sun fahimci kamar Yana jin fargaban yaga wani dangin shi a cikin matsafan, dama da zargin mahaifinsa aransa ga kuma abun da ya faru tsakaninshi da tsohuwa Khala na furucin da ta yi akanshi.



Idan muka koma bangaren Elders, sun shagala suna kallon karawar da matsafan su ke yi a tsakar fili, kowani matsafi ya zage damtse gurin nuna ƙarfin sihirin shi, dambe ne na fitar shari'a suke yi kamar zasu kashe juna, idan bala'e yayi bala'i har rikiɗa suke yi su koma dodanni su cigaba da dambatawa a tsakanin su.


Saida aka zo zagaye na ƙarshe a wasan, Elders suka ji shiru ba'a zo da prisoners ba babu su babu alamar su...


Da yatsa Elder Ya yi ma ɗaya daga cikin Evil giant din dake bayan shi alamar Ya matso kusa, sunkuyar da kanshi yayi saitin fuskar Elder...


Cike da bada Umarni Ya ce, "Ka yi ma Giantesses magana, suzo da yaran da sauran kayan da aka tanada Yanzun nan...!" da buɗaɗɗiyar murya Giant din Ya amsa mashi da angama sir, daga Inda Yake bai matsa ba ya 6ace ma ganin shi.


Bai dira a ko'ina ba sai a hall din da suka tara prisoners, Nan Ya ga abunda Ya tada hankalinsa, gawarwarkin da ya gani baje ƙasa na female giants dinsu, Ga Gawar tsohuwa Inno...aruɗe da yana yi na mamaki Evil Giant din Yake bin ɗakin da kallo kamar a mafarki, Fitowa yayi daga Hall din saboda dakakkiyar zuciya irin nasu, neman waɗanda suka kawo masu hari ya shiga yi, don Ya aika su lahira.


Yana Cikin tafiya suka bangaji juna shi da wani giant, tun daga yanayin yadda yayi tangal tangal zai faɗi Evil giant din Ya gane ba nasu bane saboda giant basa bangazar juna.


Da kakkausar murya ya furta"Wanene kai?" Rasss ya ji gabanshi ya faɗi, yan hanjin cikin shi suka kaɗa, baima san ubanda ya janyo shi wurin ba shi kaɗai batare da kowa ba gashi sam ya kasa yin wani yunkuri don ya ce ci kan shi, ware faffaɗan tafukansa evil giants ɗin ya yi da niyar Ya tarwatsa ƙoƙan kanshi sai dai kafin ya yi hakan baiyi aune ba Yaji dirar Zarto saman kan shi, kwatsa kwatsa Ya faffasa kan nashi Kafin Ya ƙwalƙwalo idanunshi yabar gangar jikin shi yashe a ƙasa, ajiyar zuciya Taj ya sauke wlh har ya fidda rai da rayuwa badan Allah Ya hankaɗo Danish ba da tuni evil giant ɗinnan Ya aikasa Barzahu.


Duk da bawani sabawa suka yi da juna ba saida yaji kaunarsa ta shiga ranshi, cikin sanyin murya ya furta, "Thanks" Jinjina mashi kai ya yi tare da nuna mashi hanya, "Zamu iya tafiya." Bin bayanshi Taj yayi suka nufi sauran jami'ansu da sukai Basaja..


Jin shiru Evil giant din da suka aika bai dawo bane yasa Elder Sake tura wani, a karo na biyu yaji shiru bai dawo ba, wasa wasa har giant biyar suka aika basu dawo ba, lamarin ya ɗaure masu kai, Miƙewa elder ya yi Jan Wuya ya ce, "Ina zaka je?"


"Ina so naje na duba Hall din, tayaya zamu aika mutun biyar shiru basu dawo ba, kada a yi abin kunya!"


Girgiza kai Jan Wuya ya yi, "Ba kai yakamata ka je ba, bari na je na duba.." ya faɗa tare da miƙewa cikin takun ƙasaita ya fuce daga filin taron, bayan tafiyarshi, Elders suka Ji shiru shima bai dawo ba, hakan yasa Jan Harshe ya miƙe Ya tafi neman shi, shiru shima bai dawo ba, har saida ta kaiga gaba ɗaya Elders sun bar filin shagalin, Fitarsu keda wuya kwatsam! ba zato ba tsammani wata irin kururuwar Fashewar bamabamai ta karaɗe gidan kurkukun, Gaba ɗaya taron matsafan da ke a gurin shagalin babu wanda Ya tsira da ranshi, saboda mamayarsu aka yi sihirinsu bai amfane su da komai ba, Haka wuta ta dinga balbali tana Cin naman jikinsu, suka runƙa sakin wata irin kururuwar radadin azaba mai amon gaske.


Har Cikin Kunnan Elders yayin da suka je hall din don su ga meya hana giants din da ake aika dawowa.


Kowa ya shiga ciki wani irin burki yake ci sakamakon abun al'ajabin da idanunshi ya gani, a haka har suka haɗu su duka, Cak duk suka yi sun kasa yin wani ƙwaƙƙwaran motsi, da wani irin matsanancin mamaki da al'ajabi gami da ruɗanin tashin hankali suke duban junansu....ganin abunda basu ta6a zaton ga ni ba, ga kuma sautin da kunnuwansu suka jiyo masu. Wannan shi ake kira bazata!!!

*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post