Bushewar Gaba ko Daukewar Ni'ima ga Mace

Bushewar Gaba ko Daukewar Ni'ima ga Mace


𝘽𝙐𝙎𝙃𝙀𝙒𝘼𝙍 𝙂𝘼𝘽𝘼, 𝙆𝙊 𝘿𝘼𝙐𝙆𝙀𝙒𝘼𝙍 𝙉𝙄'𝙄𝙈𝘼 𝙂𝘼 𝙈𝘼𝘾𝘾𝙀‼️

Saudayawa mata ke damuwa akan daukewar ni' ima ko bushewar gaba har sai sunyi amfani da lubricants.

Okkkk! Saurara da kyau ki ajiye hankalin ki ki fahimce wannan bayanin.

Amma mene ne alamomin bushewar gaba❓

1. Yawan jin kaikayi ko zafi a gaban macce.

2. Jin ciwo yayin saduwa.

3. Shan wahala kandan namiji yasami damar shigan macce.

4. Ganin jini lokacin saduwa.

5. Jin zafi lokacin saduwa.

6. Rashin jin sha'awar namiji.

7. Yawan zuwan infection akai akai babu dalili, musamman masu juna biyu

AKWAI MANYAN DALILAI DAKE KAWO BUSHEWAR GABA AMMA ZAN FADADA BAYANIN KOWANNEN SU. 

1️⃣ Infections: 

Duk lokacin da macce ke fama da infection, kowannen kalan infection ne(bacterial, fungal, viral ko protozoan vaginal infection) wadannan kwayoyin cutar zasu hana gaban macce yin aikin shi yanda yakamata, tayanda ruwan dake fitowa a gaban mace su daina zuwa saidai wasu ruwan masu wari ko karni na infection ko jini

2️⃣ Tsufa ko tara shekaru: 

Duk lokacin da shekarun macce suka haura 35, toh jikin ta zaya rage producing oestrogen hormone (shi wannan oestrogen shikesa gaban mace ya rika sako wadannan ruwan na niima, sannan shike kula da duk wani abu da ya shafi saduwa, jindadi, juna biyu da sauran su)

Akwai wasu dalilai dake sa Oestrogen hormone ya rage a cikin jini ko macce bata tara shekaru ba 15 zuwa 30 kamar haka.

1 yawan motsa jiki da aikin kiza kiza kamar namiji.

2. Tunani da damuwa.

3. Shayarwa idan macce ta haihu.

4. Shan sigari.

5. Shan giya da magungunan maye.

6. Rashin lafiya kamar hawan jini ko ciwon sugar.

7. Magungunan family planning.

8. Idan akayi macce theatre ga ovaries misali (PCOS).

9. Duk wadansu magungunan da zasu iya alaka da hormones kamar su DEXAMETHASONE da sauran su.

Duk wadannan dalilan suna kawo karancin OESTROGEN a jiki ta har yakai gaban macce ya bushe

SHAWARA KYAUTA GA MA'AURATA..... 

ANGO.

 Kasha maganin Infection fiye da kashe kudinka kan maganin karfin maza idan har kasan bakayi ISTIMNA'I ba.

AMARYA 

Kisha maganin infection fiye da matsi da gyaran jiki inhar kin yarda da kanki kuma kema bakiyi Istimna'i ba. 

90% na matsalolin rashin haihuwa yana da alaka da infetion. 

80% Mata idan zasuyi aure basa shan maganin  infection kafin auren su. 

Saboda wani lokacin sanyi baya nuna kansa sai bayan tsawon lokaci sannan zaki ga alamomin sa. 

Wata kuma tana samu infection ne lokacin da take matsi na gyaran jiki. 

SHAWARA ITACE: 

1. Ko kafin ki aure da kudin da zaki kashe na matsi kina budurwa, ki sha magani sanyi yafi miki wannan matsi. 

2. Iyaye Ku bada muhimmanci maganin sanyi fiye da gyaran jiki. 

3. Kafin saduwa kuyi hakuri ke da ango Ku sha maganin sanyi zai fi. 

4. Idan kina budurwa Baki da bukatar matsi. 

5. Ango ka sha maganin infection fiye da maganin karfi maza. 

HANYOYIN MAGANIN INFECTION:

1. GANYEN MANGWARO GUDA 12.

2. BAWON KANKANA 5.

3. GARIN HABBA.

4. GARIN ZAITUN. 

Za'a dafa kayan hadin sosai tsawon 30 minutes Ana sha Kofi daya kafin cin abinci safe da yamma.

Sai bayan 1 hour za'aci abinci. 

HADIN NA MAZA ZALLAH: 

1.  Garin Hulba cokali  6

2.  Bawon kankana 5.

3.  Ganyen magarya. 

Za'a dafa Ana sha Kofi daya safe da yamma. 

Sanna ki dinga zama cikin Bagaruwa da Ganyen Magarya kina tsarki.

Ayi Sharing Domin Yan Uwa suma su Amfana.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post