ZUWAN HAILA TARE DA YADDA ZAKI LURA DA KANKI
HAILA, al'ada, jini, mensis ko ace period duk sunayen abu guda ne. HAILA
Jinin Al'ada wata abace da Allah ya tsara ga dukkan 'ya'yan Adam mata wadanda suka cimma wasu shekaru na rayuwa na fara aikin wasu sinadaren halittun jima'i dake jikinsu da ake kira (estrogen And progesterone) a dukkan lokaci lokaci.
Haila itace babbar alama dake nuna mace bata da juna biyu, sannan itace babbar alama dake nuna jikin mace shirye yake da ya dauki juna biyu inhar da zata sami Jima'i tsakaninta da namiji.
Su sinadaran Progesterone da Estrogen dama jariri na samun su tun aciki yayin da halittar mutum takai sati 12, amma basa fara aiki sai mace takai shekarun balaga.
Balaga Kän bambanta wasu tun ashekara 9 suna iya fara haila don haka balagarsu kenan, wasu a shekara 11, amma da yawa sunfi farata daga shekara 13- ko -14, saide masu raunin wadannan sinadaren wasu sukan kai har shekara 17 basu fara ba koma 19. Irinsu ne saikaga ga girma da tsayi ajika amma inka kallesu babu bambanci da jikin yara wato ba fashewar kugu babu alamun fitowar nonuwa.
Haila a mafi yawa takan zo duk bayan kwana 28 kuma Sannan yawanci kwanakin basa wuce 5, saide dake Allah yai mana halittu daban-daban wasu sukan sami tazarar kwana 30 zuwa 37 sannan su kuma yin wata hailar, kuma haka jikinsu yake ba matsala bace. Wasu kuma duk bayan kwana 21.
Wasu sukan ga haila ta dauke musu har wata 1, 2 ko 3, toh idan mai aure ce idan haka ta faru yawanci juna biyu shine abunda muke tsammani, idan ma baki da aure kuma baki da kamun kai to kema haka muna tsammanin juna biyu ne.
Toh amma idan duk anyi gwaji babu juna babu ko daya to sannan ake fara tunanin wasu abubuwan dakan jawo daukewarta kamar:
☆ Idan mace tai fama da rashin lfy a tsakanin,
☆ Ko in mace ta bada gudun mawar jini,
☆ Ko macen dake shan kwayoyin bada tazara,
☆ Ko mai shan maganin larurar hawan jini,
☆ Ko Shan maganin ciwon suga,
☆ Ko sakamakon hatsari,
☆ Karancin jini
☆ Ko samun kai a halin kunci da damuwa (depressed),
☆ Ko sanun kai a halin tsoro da fargaba (Anxiety)
☆ Ko in wata mutuwa me zafi ta faru cikin dangi
Duk wadannan ka iya sa mace taga hailarta batazo ba matukar ba juna biyu gareta ba.
Wasu kanyi tambaya shin yana yiwuwa mace tai haila alhalin tana da juna biyu?
Magana ta gaskiya kuma Wacce nake ni akanta shine baya yiwuwa ace Mace nada juna biyu kuma tana haila. Abinda ke janyo wannan jinin yawanci daga bakin mahaifa ne
sakamakon Kila yawan saduwa da ita da ake hakan kasan cervix din yai rauni, wannan tasa bamason ake saduwa da mace mai karamin ciki akai akai har zuwa watanni 4 ko kuma adalilin yagewar wani sashi na mabiyiya ko kuwa inda mabibiyar (palcenta) ta dasa kanta ba daidai ba, ko hujewa kila sakamakon doguwar tafiyar mashin ko mota koma jirgin sama, Ko alamar dake nuna tsiron cikin mahaifa (fibroids), ko ciki a wajen mahaifa (ectopic pregnancy) ko kansar bakin mahaifa...
Ko kuma Kila d'an dake cikinta ne ya gicciye ba daidai ba, ko kuma
sakamakon wajen awo ansa hannu angyara Yaro ko wani abu wanda Kila daga nan jinin yaci gaba da fita. Amma gsky bazai yiwu ana goyon ciki ana haila ba saboda kwata kwata ma ayyukan hormones din sunyi hannun riga da hakan, don haka zataje aduba ta agane dalilin jinin abata magani.
Sannan ba'a cewa haila ta shiga matsala ko kuwa sa kai adamuwa harsai mace taga tai wata 6 batare da ganin hailar ba sannan zatai tunanin abunyi wanda shine muke Kira (amenorrhea) wato daukewar haila.
Amma dan tana samun tazarar wata 2, 3 zuwa 4 ko 5 wannan shi muke Kira abnormal wato (oligorrhea) tana al'ada amma ba akai akai ba, Bakuma matsala bace. Kila 1 daga cikin abubuwan dana lissafa asama ne ke faruwa
Macen da bata al'ada akai akai wannan kesa wasu aga suna fitar da gashi afuskarsu, wasu kuma gashin su ya rika zubewa naka, wasu yawan ciwon kai, wasu kuma su rika ganin ruwa in sun matsa Kän nonon su koda kuwa yan matane basu da aure.
WATA TA YI TAMBAYA, SHIN ZA'A IYA SAMUN CIKI KWANA 2 KAFIN AL'ADA SANNAN YA ALAMUNSA
Ai inde anga haila toh babu zancen ana da ciki. Sannan bako yaushe ciki ke shiga ba. Yawanci macen dake kwana 28 kafin haila ta zagayo kwanakin daukar cikinta kan kasance kwanaki 11, 12, 13, 14 koma 15 bayan daukewar waccan hailar ta baya.
SHAWARWARI AKAN YADDA ZAKU KULA DA KANKU
Sau da dama a lokacin jinin al’ada mata kan shiga halin tsantseni, inda waɗansunsu kan kauracewa shiga cikin mutane, wanda kuma ke takurawa rayuwarsu har su samu kansu kamar an sanya musu takunkumi.
Tunda a zahiri musamman haila a lokacin zafi har canjin smell ajika mace ka iya fuskanta kuma kota sa turare wata bata yadda da kanta ta saki jiki tunma ba me yawan zufa ba.
1]- KWANTAR DA HANKALI
Ki nutsu ba abin tashin hankali don kin fara jini, hakan zai sanya mata yan uwanki ko mahaifiya har su fahimci halin da kike ciki.
Don haka ki kwantar da hankalinki kamar babu wani abu da yake faruwa dake. Ki dauka kamar kowa kike babu kuma wanda zai gane komi inba kin furta ba. Shiga ai komi dake.
2]- Ki kasance sanye da ‘Pad’ a kowane lokaci don gujewa jin kunya, tunda wasu jinin na fita da yawa.
3]. CANZA ‘PAD’ AKAI-AKAI
Ya kamata ki rika canza ‘pad’ ko ‘tampon’ duk bayan awa 4 zuwa 8, idan kuma jinin yana zuba sosai sai ki rika canzawa lokaci zuwa lokaci koda awa bi-biyune, domin
lokacin da jinin ya gama jiqa ‘pad’ ko ‘tampon’ din barinsa ya daɗe zai ba kwayoyin cutar bakteriya din fata musamman wacce muke kira STAPH AUREUS damar growing inta hadu da normal bacteria, domin jini ba karamin daula ke zamewa kwayoyin cuta ba wajen rayuwa.
Wanda hakan kuma zai haifar miki da matsala ta kwayoyin cuta acikin jini da guiwoyi wato TOCIC SHOCK SYNDROME. Wanda inba a dau mataki ba mutuwa ma na iya biyo baya ko shan wahala musamman mace me karancin tsafta.
Shyasa nake kira ga yayye Maza muke taimakon kannenmu Mata da kudin pads duk wata kudena barinsu da roke roken samari, wasu ma saboda babu saide su nemi soson katifa ko dan kwali sui kunzugu dashi hakan matsala ne, kunga bai dace ba... don haka ku taimaka musu.
4]. LURA DA KAI
Daga lokacin da akace an fara al’ada, tsabtace kai na da matukar wahalar gaske. Musamman lokacin zafi, daga an yi zufa jiki ke fara canzawa mai.
Don gujewa hakan sai ki rika wanka lokaci zuwa lokaci, hade da shafa turare mai tafiyar da wari (deodorant), sannan ya kamata ki goge bakinki sau biyu ko uku a rana domin hakan zai magance miki canjin dakan faru na baki, lokacin. Bayan haka ki rika cin cingam mai kamshi, ko tsotsar minti ko cin cakulat.
5]. LURA DA KURAJE
Wadansu Matan idan za su fara ko kuma sun fara jinin al’ada kurajen kan fito musu, to idan kina daya daga cikin wadannan Matan, idan kurajen sun fito miki, kada ki fasa su, ko kuma ki rika taba su. Abin da za ki yi shine, ki rika wanke fuskarki sau biyu ko uku a rana. Ko kuma ki wanke fuskarki daga zarar kin fara gumi idan lokacin zafi ne.
6]. LOKACIN AL'ADA
Yawancin kwanakin al’ada basa wuce 3 zuwa 7. Duk lokacin da jinin al’ada yazo miki to zaki samu na gaba yazo a wani lokaci daban, duk
da cewa wadansu kan samu tazarar kwana 28 ko 35 kafin wani jinin yazo
musu. Don haka ina baki shawara ki ajiye karamar kalanda a dakinki ko ki saita kalandar cikin wayarki. Hakan zai ba ki damar fahimtar lokutan al’adarki, kuma zai ba ki damar lura da kanki ba tare da wani ya gane ba.
7. JIN ZAFI
Baban abinda ke jawo ciwon Mara lokutan al’ada shine kwaɓowar da bangon mahaifa keyi, domin mayanin ake canzawa, shiyasa ta kanzo da ciwon ciki, ciwon kai ko murdawar mara, hakan na faruwa ne sakamakon matso jinin da mahaifa keyi wato uterus contraction na Slough off,
Hanyar da za'a rage hakan shine ki rika motsa jikinki, ki zamo active, misali fita kai ziyara ko sayo wani abu, ko aikin gida, tare da haɗa tea me citta sosai asha. Ko gasa marar da ruwan dumi.
Sannan magunguna irinsu paracetamol, diclofenac, feldin, kan taimaka wajen tafi da zogin amma de atabbatar ana amfani dasu bisa ka'ida, hasali inda za'a jure ciwon anfison hakan.
Amma idan ciwon cikin, ko kai, ko kuma murdawar marar ya tsananta to a tuntubi likita.
Sannan akarshe ga masu fuskantar heavy bleeding wato jinin ya rika fita da yawa gaskya inde ko yaushe haka kike to ki daure kiga likita ba lafiya bane.
Share it pls!